Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata masu aji.🌚
[11/25, 7:00 AM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*


©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

Free page 7

🥳 in ka ji busa tabbata Sarauniya ce ta ƙaraso, ina kuke matan ƙwarai, mata ba muna mata ba, shin kin jaraba kayan *HONEY-DROPS* me kike jira har yanzu?, Manyan mata, mata masu aji na ta dafifi wajen kwasar kayan gyara, me ya sa za ki kashe kanki da ƙuruciyarki, ko tsohuwar ma na zuwa karɓar nata, kina fama da matsalar bushewar gaba, ɗaukewar sha'awa da ni'ima, ƙaiƙayi ko ƙurajen gaba, jin zafi yayin tarawa da maigida, sanyi ya taɓa miki mahaifarki?, Kina ta allura da shan magunguna ba su miki aiki ba, wane kalar infection kike fama da shi?, Staphylococcus, Gonorrhea, Syphilis, UTI, STDs ne?, Share hawayenki kukanki ya ƙare je ki nemi *HONEY-DROPS INFECTION FLUSHER* ke da sanyi sai dai ki ba da labari, kin gama cacar kuɗi, cikin kwana uku zaki fitsarar da duk wani sanyi da dattin da ke tattare a mararki, ki gyara zamanki gidan aurenki don sanyi kashe mace yake har buzunta, duk wani magani da za ki sha muddin da sanyi a jikinki iyakar shi cikinki, ba zai sauka ba. Magani ne ingantacce made of herbs, In kin gama da wannan akwai na gyaran other room, akwai Exclusive Gumba ta manyan mata ke nan, ko matar Gwamna ita take sha, ga Gumbar babbar mace mai tada tsohuwar soyayya, akwai fa tsuumi na matan gaske, akwai *HONEY FLOOD TSUUMI* kan ƙiftawar ido ni'ima ta yi ta kwararo miki, akwai BUJENTA JAGAB, da Tsuumin Ɗafau, daga jin sunan kun san akwai zance na bar muku ku ƙarasa, akwai sauran kaya masu zafi🔥

Muna da bridal package

Diamond - 100k
Gold - 50k
Silver - 30k

Ga kuma na postpartum (wanda suka haihu don dawo da martabarsu)

Diamond - 50k
Gold - 30k
Silver - 15k

Kuna iya samun mu ta 08167888934, ko 08067770852


Girma da siffar Badakaren ne suka sake hargitse lissafin rayuwata, a hankali na sake ja da baya ya yin da yake sake tunkaro mu gadan-gadan hannunsa ɗauke da wani mummunan ƙarfe wanda aka naɗe jikinsa da manyan ƙusoshi, a zafafe ya ɗaga da niyyar buga min a tsakar ka cikin shammata mahaifina ya kai masa duka a wuyansa. Take suka fara kokawa ganin haka ya sa mahaifina ya yi mini alama da mugudu ni da Kandala, gudu muke kamar ranmu zai fita don na gama tsorota da yanayin azzaluman mutanen da suka fito daga baƙar daula. A yadda na bar mahaifina da Badakaren ina jimamin halin da mahaifina yake ciki don na tabbata zai yi wuya idan bai yi wa mahaifina taron dangi sun hallaka shi ba, sai da muka yi tafiya mai nisan gaske sannan muka raɓa cikin wata bishiyar ɗorawa mai duhu muka zauna muna hutawa, waige-waige nake yi don ganin hanyar da zan samu ruwan da zan ɗebo mana musha saboda zafin ranar da ya busar da maƙogaronmu. A wahalce Kandala ta kalle ni idonta na zubda ƙwallah tana faɗin, "Kyauta ƙishirwa za ta kashe ni maƙoshina ya bushe." Jijjiga jaririn nake saboda kukan da yake ta tsalawa wanda na tabbata kukan wahala ne sannan na furta mata, "Riƙe min shi ki kula da kyau zan duba mana ko da ƙorama a kusa idan muka sha sai na duba ko zan samu wani naman dawan na gasa mana." Karɓarsa Kandala ta yi na miƙa cikin dajin ina duba hagu da dama ko zan samu ƙaramar ƙoramar da zan ɗebo mana ruwan, ko kaɗan ban yi tunanin wurin da zan ɗebi ruwan ba babban burina bai wuce mu samu ruwa kowanne iri ba ne. Daga can nesa na hango wani bafulatani yana tafe da shanunsa wanda hakan ne ya tabbatar min da kiwo yake, gudu-gudu sauri-sauri haka na rinƙa tafiya don na ƙarasa na cimma masa koda zai sa ya taimaka min, yana ganina ya fara bina da kallon tuhuma don ko bai faɗa ba na san suturar jikina yake kallo wacce ta bambamta da irin ta shi, kallon kaina na yi daga ni sai guntuwar fatar da ta rufe min ƙirjina da wacce na suturta al'aurata, sannan na ɗago na kalle shi yana sanye da farar rigar saƙi ta kala-kalan zarurruka, sandar hannunsa ya ɗaga na ji yana yin yaren da nake tsammanin fullaci ne sannan ya yo kaina da sauri zai sauke min ita. A razane na ja da baya cikin hakki ina faɗin, "Abar bauta bata wanzar da zalinci a doron ƙasa ba don haka kada ka cutar da ni." Sauke sandar ya yi ƙasa sannan ya furta, "Hai meye abar bauta kuma? Ke kam aljani ne ko mutum?" Dafe kaina na yi saboda matsanancin ciwon da yake min sannan na furta, "Ni mutum ce tare nake da ƙanwata ka taimaka mana ka ba mu ruwa mu sha." Kallon da yake min ne na tabbatar min da har lokacin bai gama aminta da ni ba, don haka na ga ya runtse ido yana ci gaba da fulatanci sannan ya kara sandar hannunsa a saitin kaina. Ya ɗan jima a haka sannan ya buɗe idonsa ya ce, "Zan taimaka maka ina ƙanwar taka?" Hanyar da na baro su Kandala na nuna masa, ya ƙurawa wurin idanu sannan ya ciro kurtunsa ya miƙo min. Har na ɗaga kai zan sha na tuna halin da na baro su Kandala, da sauri na sauke shi na ce masa. "Ka taimaka ka cika ladanka ka bar ni na kaiwa ƙannena su sha. Idan ka yi haka abar bauta za ta albarka ci kiwonka." Ɓata fuska na ga ya yi don haka gabana ya faɗi, ina shirin roƙonsa na riski muryarsa yana faɗin, "Kada ki sake danganta ni da abin bautarku domin Yesi Almasihu zai yi fushi da ni saboda na haɗa bautarsa da waninsa." Shiru na yi ina mamakin maganarsa domin a iya sanina bayan abar bauta babu wani abu da ake bauta wa a faɗin duniya. Da yake ina cike da son biyan buƙatar kaina sai na gyaɗa masa kai cike da godiya, har na juya zan nufi hanyar na ji yana faɗin, "Ki bar hanyar ɓata ki dawo kan shiriya ko za ki samu gidan daɗi wato aljanna domin mu mabiya Yesu Almasihu mun kasance masu karamci da taimakawa saboda Allah." Ko kaɗan ban gane abin da yake nufi ba don haka ban amsa masa ba, sai na kawar da maganar cikin amsar da na bashi da cewar, "Zan gaggauta kai wa ƴan uwana akwai jariri ina tsoron kada ya mutu." A hargitse ya fura, "Jariri kuma?" Na gyaɗa masa kai, jin haka ya sa ya kaɗo shannunsa ya rufa min baya muka tunkari wurin da su Kandala suke. A galabaice muka same su don haka cikin hanzari na karɓi jaririn na fara bashi a lokacin tuni ya gaji da kuka ya sake yin bacci, sai da ya sha ya ƙoshi sannan na miƙa wa Kandala ita ma ta sha ta rage mini. Tausayin Jaririn ne ya kama shi ya dube ni yana faɗin, "Idan ba za ki damu ba ko na tatso masa nonon Naggen can ya sha." Ban san lokacin da murmushi ya suɓuce min ba na furta masa, "Na gode sosai da taimakonka." Nonon saniyar ya tatsa da ɗuminsa ya miƙo mini na ɗan riƙa bashi kaɗan-kaɗan yana sha. Sai da na lura ya ƙoshi sannan na miƙa wa Kandala ta shanye sauran, miƙe wa na yi na yi na yi masa godiya muna shirin tafiya ya furta min, "Yanzu ina za ku tafi ke da kika ce baki da kowa?" Idanuna ne suka ciko da ƙwalla na furta masa, "A da ni ƴar gata ce gaba da baya, sai dai a yanzu ba ni da kowa ban san inda za mu tafi ba." Tambaya ya sake jefo min nan take ya bashi labarin abin da ya baro mu daga yankinmu, ya tausaya mana sosai don haka ya yi alƙawarin kai mu rugarsu domin ya taimaka mana, duk da ya gargaɗe ni a kan na ɓoye addinina idan kuwa na bayyana shi a rugarsu za su iya korata daga garin. A yadda ya ba ni labari tun tasowarsu iyaye da kakanni babu wani addini da suka sani face Kiristanci, a kan shi suka kafu Yesu Almasihu suke bautawa don haka ba su yadda akai musu kowanne irin addini saɓanin nasu ba. Ba ni da zaɓi don a lokacin burina bai wuce mu samu mutsuguni ba duba da ɗanyan goyon da muke tare da shi, a yadda na ayyana da ace daga ni sai Kandala ne za mu ci gaba da tafiya har mu nufi wani yankin da ba sa tsauwala wa game da addinin da ni kaina na gaje shi tun iyaye da Kakanni. Jiki babu ƙwari na sake rungume jaririn muka fara tafiya, ya wuce gaba shi da shannunsa muna biye.

Ba ƙaramin artabu aka sha tsakanin Badakaren da Mahaifin Kyauta ba, ganin mahaifin Kyauta na yin neman yin galaba a kansa ya sa Badakaren yin fito nan take wasu daga cikin Dakarun suka yi dirar mikiya a wurin, duka suka riƙa kai masa ta ko'ina sannan suka fisgo shi da ƙarfin tsiya suka ɗaure hannunwansa a jikin murtukeken itacen da tuni aka ɗaure mafi yawa daga cikin mutunen garin mazansu da matansu. Ƴaƴayen da aka raunata iyayensu aka ɗaɗɗaure su sai bi suke suna dafe ƙafafuwansu suna kuka, haka waɗanda aka kashe iyayensu suna kwance akan gawarwakinsu suna tashinsu suna ihu gwanin ban tausayi. Mata masu ciki da tsofaffi haɗe da ƴanmatan yankin duk an ɗaure su jikin itacen da aka zura musu shi cikin kafaɗunsu. Duk wannan azabar da ake gana musu garin tsit ya yi sai kukan ƙananan yara saboda duk wanda aka ji ya yi ihu zane shi suke yi da bulalar hannunsu ba za su bar dukansa ba har sai sun kwaile masa fatar jiki. A haka suka tasa ƙeyar mutanen garin gabaɗaya suka tafi da su, har sun yi nisa shugaban Dakarun ya sa wasu daga cikin dakarun suka koma suka tarkato ƙananan yaran, waɗanda aka lura da suna kwance kan gawarwakin iyayensu sune aka tasa ƙeyarsu ya yin da waɗanda suke kuka suna bin iyayensu da aka ɗebi wasu, wasu kuma aka bar su a wurin. Tafiya ce mai nisan gaske ga babu ruwa balle abinci babu hutu balle su samu salamar azabar da ake yi musu, idan suka lura gungun itace ɗaya ba sa sauri gabaɗaya suke haɗa wa su zane su, ilahirin jikinsu a farfashe yake yana tsattsafar da jini ya yin da ƙananan yaran da aka tafi da su saboda wahala wasu suka riƙa faɗuwa suna suma. Duk yaron da ya suma ba sa bi ta kansa sai dai su wuce idan kuma da kogi ko rami a wurin sai dai su wurga shi a ciki. Ƙalilan daga cikin yaran ne suka samu ƙwarim gwiwar ci gaba da tafiya a haka har dare ya riske su, a kan dole suka yada zango a wani baƙin daji. Duk da kasancewar su a wurin babu abin da aka ba su da sunan ci ko sha, kuma a yadda suke a ɗaure haka suka ci gaba da zama. Mutum ko fitsari da kashi yake ji sai dai ya yi a wurin, suna ji suna gani Dakarun suka yo farautar naman dawa suka gasa suka ci amma su ko ruwa ba su samu ba. Wani tsoho daga cikinsu ne ya galabaita da ƙishirwa don haka a wahalce ya roƙe su akan su bashi ruwa ya sha, wani gajere daga cikin dakarun ne ya ɗebo garwashin wuta kai tsaye ya yi kansa gadan-gadan. Ganin haka ba ƙaramin ɗaga hankalinsu ya yi ba, nan take jikinsu ya fara karkarwa. Yana zuwa ya buɗe bakin tsohon ta ƙarfin tsiya ya zuba masa garwashin a ciki. Saboda azaba nan take tsohon ya fara sakin kashi da fitsari cikin fitar hayyaci, Dakarun na ganin haka suka bushe da wata irin mahaukaciyar dariya har da masu kwanciya a cikinsu saboda ƙeta. Sai da suka yi mai isar su sannan suka dube su cike da izgilanci suna faɗin, "Waye zai kuma cewa zai sha ruwa a cikinku?" Wurin ne ya yi tsit ba tare da wani ya furta koda kalma ɗaya ba, sai da tsohon ya gama galabaita sannan suka ɗauko wani wurtu da ɗan ƙanƙanin ruwa a ciki suka ɗaga kansa suka sheƙa masa. Ruwan da ya shiga bakinsa ko cikin tafin hannu ɗaya ba zai cika ba, ya yin da sauran ya wanke masa fuska gabaɗaya. A na cikin haka ɗaya daga cikin masu matan da ke ɗauke da tsohon cikin ta fara naƙura gadan-gadan, a galabaice take yunƙurin tashi saboda yadda take jin kan jaririn na iya ratsowa ta ƙarƙashinta. Duk yadda ta kai ga ganin ta miƙe ta gagara sakamakon yadda hannuwansu yake ɗaure a jikin itacen kuma a ƙallah sun kai su goma sha biyar a jikin kowanne itace ɗaya. Kururuwa take cikin azaba da neman ɗauki, mijinta da ke ɗaure a wani itacen ya gagara haƙuri duk da zuciyarsa na bugu saboda fargaba ya dubi Dakarun yana faɗin, "Ku taimakawa mai cikin can haihuwa za ta yi." Ɗaya daga cikin su ne ya fara takowa yana sakin murmushin mugunta ɗauke da muguwar manufa, sai da ya ƙarasa gabansa sannan ya wurga masa tambaya, "Ko dai matarka?" Ƙara matar tashi ta sake ƙwallawa a hargitse ya kalli wurin idanunsa na fidda ƙwallah. Suna haɗa ido ta fakaici idon Badakaren ta girgizawa mijinta kai alamar kada ya nuna mijinta ne, ganin irin kallon da mutumin yake yi wa ɓangaren matar ya sa Badakaren ya kalli wurin, a hankali ya miƙe ya ƙarasa wurin matar ya ɗora hannunsa akan cikinta yana shafawa har zuwa gabanta, jaririn da ke cikinta ya ji yadda yake mutsu-mutsu ya waiga wurin mutumin sannan ya sake kallonta ya ce, "Amma mijinki yana tausaya miki da alama yana ƙaunarki sosai." Cije baki ta yi saboda azabar da take ji gumi na ci gaba da keto mata, cike da ƙarfin hali ta girgiza kai murya na rawa ta ce, "Ba mijina ba ne."

Ta faɗi haka ne don ta lura a lokacin da mijin nata ya yi magana ya taso gadan-gadan don aiwatar masa da mugunta, wannan dalilin ya sa ta yi wannan badarar ko mijinta ya kuɓuta daga azabarsu. Jin abin da ta faɗa ya sa Badakaren bushewa da dariya, ajiyar zuciya mijinta ya sauke ya sunkuyar da kai ƙasa sai dai duk abin da yake faruwa yana kallonsu ta gefen idonsa. Cikin shammata Badakaren ya saka hannu ya bigi tsakiyar cikinta da ƙarfin gaske, azaba ce ta ratsa ilahirin jikinta ta saki razananniyar ƙara. Ganin haka ya sa jikin mijinta ya riƙa karkarwa ransa ya yi mummunan ɓaci, yana shirin yunƙurawa don yin magana Mahaifin Kyauta ya zungure shi a fakaice cikin raɗa ta furta masa, "Ka da ka yi wani yunƙuri don komai zai iya faruwa daga kai har mai ɗakinka." Babu yadda ya iya haka ya koma ya yi laƙwas yana yin hawayen zuci saboda ɓacin rai, Badakaren ne ya miƙe ya koma wurin zamansu don irin dukan da ya yi mata a ciki ya tabbata idan mijinta ne zai magantu, ganin mijin nata bai tanka ba kuma bai yi wani yunƙurin dakatarwa ba ya sa ya yadda ba matarsa ba ce. Sabon ciwo ne ya taso mata gadan-gadan ganin haka dabara ta faɗowa sauran mutanen da suke ɗaure a jikin itace ɗaya, yunƙurawa suka yi da ƙyar suka tashi suka tsugunna don sun tabbata idan ba haka suka yi ba babu yadda za a yi ta iya haihuwar abin da yake cikinta lafiya ƙalau. A daidai lokacin da suka tsugunna kan jariri ya taho cikin azaba ta ƙwallah wata gigitaciyyar ƙara sai ga jariri ya faɗo, jaririn ne ya fara wutsul-wutsul a cikin ƙasa da gwiwoyin ƙafarta take yunƙurin ɗaukansa amma ta kasa. Kukan jaririn ne ya cika dokar dajin don haka tausayinsa ya ratsa zuƙatan mutanen wurin, mahaifiyarsa ta kifa kanta a kansa ta rushe da wani irin matsanancin kuka.

Tamkar dirar mikiya haka ta ji maganar babban Badakaren a kanta, tana ɗagowa ta riske shi ya ɗauki jaririnta. Tsugunnawa ya yi ya ciro wata kaifaffiyar aska ya yanke masa cibiya sannan ya saka aka kwanceta. Mamaki ne ya kamata sai kuma take ganin kamar tausayinta ya ji har ya sa aka kwance ta. Jaririn ya miƙa mata sannan ya sa aka ɗaure mata sarƙa a ƙafafuwa biyu, saitin fuskart ya koma suna fuskantar juna sannan ya ce, "Kin samu wannan rangwamen ne domin biyan buƙatar kaina, yau ita ce ta kasance ranar shaƙatawa a Daularmu don haka zan fanshe ranata a kanki." Ƙirjinta ne ya buga sakamakon yadda take jin gabanta yana yi mata wani irin raɗaɗin azaba, uwa-uba ga babu wani gyara da ta samu a matsayinta na mai jego. Kallon jikinta ta yi ta ga yadda jini yake bin ƙafarta kace-kace, kasa tanka masa komai ta yi sai hawaye da ke bin idanunta. Tana ji tana gani haka Badakaren ya sa aka rirrriƙeta ya fara biyan buƙatarsa da ita a gaban mutane, saboda azabar da take ji sai da ta yi suma biyu sannan ta farfaɗo ta dawo hayyacinta. Jikin sauran mutayen wurin ba ƙaramin sanyi ya yi ba, mijinta ban da huci babu abin da yake yi. Fatar da ta rufe ƙirjinta ta ciro ta naɗe jaririnta a ciki ta rungume, tana haɗa ido da mijinta ya sunkuyar da kai cike da tausayawa. Yadda suka ga rana haka suka ƙarasa ganin daren, gari na yin haske Dakarun suka tashe su suka ci gaba da tafiya, a galabaice suka ci gaba da cira ƙafafuwansu suka ƙara ɗaukan hanya da yin tafiya mai nisa. Sai da suka shafe wuri guda sannan suka ƙarasa babbar ƙofar da za ta sada su da Daular. Dakarun bakin ƙofar ne suka fara yi musu barka da zuwa, domin su ne tawaga ta biyu a cikin Dakarun da sarki ya tura fataucin bayi waɗanda suka dawo. Saura tawaga biyu da ake saka ran ganin ta hanyar da za su ɓullo.

Mun yi tafiya mai nisan gaske kwatankwacin wacce muka yi a baya, ni da Kandala ba ƙaramin galabaita muka yi ba. Har haƙurina yana shirin ƙare wa zan tambayi ɗan fulanin sai muka fara hango bukkokinsu daga can nesa, a bayan gari ya tsayar da mu ya wuce cikin rugarsu don cemin ya yi matuƙar muka shiga da irin shigar jikinmu cikin rugar ba makawa za su yi mana korar kare kuma babu wanda zai taimaka mana, domin shigarmu ta saɓa da irin shigar da suke yi. Ya dakatar da mu ne domin ya je wurin mahaifiyarsa ya sanar mata da komai kuma ya karɓo kayan ƙanwarsa a sirrance ya kawo mana mu saka ni da Kandala. Ya ɗan jima da tafiya sannan ya dawo, sai da ya ba mu wuri muka kintsa sannan muka wuce cikin rugar hatta Jaririna sai da na naɗe shi da zanin da aka saƙa shi da fari da kalolin zare. Bayan mun gama shiryawa kafin mu wuce ya dube ni yana faɗin, "Ku saurare ni da kyau ku ji abin da zan gaya muku, bayan ni da mahaifiyata babu wanda ya san su waye ku. Idan muka shiga rugar mu zan ce musu tsintarku na yi a cikin daji ku ba ƴan nahiyar nan ba ne, garinku ne aka ci shi da yaƙi kuke neman wurin matsuguni babu maganar wani addini bayan na Yesu Almasihu, idan ba haka ba za a samu matsala." Yana gama magana na gyaɗa masa kai cike da gamsuwa na fara jera masa godiya sannan muka wuce, kamar yadda ya gaya min haka ya gaya musu kuma ba su nuna ƙyama a gare mu ba. Hasali ma ba ƙaramin tausayinmu suka ji ba, mahaifi da mahaifiyarsa suka shiga hidima da mu ya yin da aka ci gaba da kula da Jaririna, duk wata kyakkyawar kulawa muna samu amma tunanin iyayena da halin da suke ciki ya addabi gangar jiki da ruhina, babu lokacin da zan kwanta bacci ban yi mafarkinsu. Tun su Inno wuro ba su fara fuskantar halin da nake ciki ba har suka fara tambayata, ban ɓoye musu ba na sanar da su damuwata, sun tausaya min matuƙa haɗe da kwantar min da hankali. Kwananmu uku a cikin rugar da wata asuba muka wayi gari da mummunan tashin hankali sakamakon farmakin da masu fataucin bayi suka kawo. Sun cunna wuta a dukkkan bukkokin rugar, ganin su ya tabbatar min da zargina ya tabbata dai gudun gara muka yi muka faɗa gida zago. A zuciyata nake ayyana ina ma ba mu yi wannan guduwar ba duk abin da zai same mu gara ya same mu tare da iyayena, irin baƙaƙen Dakarun da suka farmaki yankinmu sune suka kawo farmaki wannan rugar da muka sauka, babu yadda muka iya muna ji muna gani suka riƙa azabtar da mu suna ɗaure mu a jikin wasu murtuka-murtukan ita ce, jaririna na zura cikin wata jakar fata na saƙalo shi da gefen kafaɗata zuwa cikina, a itace ɗaya aka ɗaure mu da Kandala muna ji muna gani aka tasa ƙeyarmu cike da azabtarwa.

😰 Shafin akwai ban tausayi, wasan yanzu zai fara💃🏼🤣

*KU MATSO KU TAHO*💃🏼

Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananin ban tausayi😰 ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.

Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼

Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera 'yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰
Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na'isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba'a nuna masa hanya, sa'a dai 'yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER'S* Amanar Marubuta La'ilaha'illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚

*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
[11/25, 7:00 AM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*


©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

Free page 8

🥳 in ka ji busa tabbata Sarauniya ce ta ƙaraso, ina kuke matan ƙwarai, mata ba muna mata ba, shin kin jaraba kayan *HONEY-DROPS* me kike jira har yanzu?, Manyan mata, mata masu aji na ta dafifi wajen kwasar kayan gyara, me ya sa za ki kashe

Please Login or Register in order to submit comment