Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi yake sauri domin fita zuwa wajen aiki, kasancewar yau zai fara aiki.



Hango mace yayi da alamu mota take jira, har ya wuce sai yaga kamar ita dan haka ya dawo.


Ikhlas da ganin mota ta wuce ta dawo yasa ta dan matsa, a hankali ya zuge glass din motar.



Ganin shi yasa ta daure fuska, kallon ta yake yana murmushin mugun ta,juyar da kan ta tayi.



Cikin tafiyar kasaita ya fito, wajen ta ya nufo hakan yasa gaban ta faduwa,dan matsawa baya tayi.




Kima matsowa yayi, ganin ta sake matsawa yasa ya tsaya, kallon fuskar ta yake, ita kuma tayi kasa da kan ta gaban ta na cigaba da faduwa.



Cikin muryar shi me dadin sauraro yace"yau ba za'a bani charity din bane? ",shiru tayi.



Hannun ta ya rike yace"bana ce ki bar garin kaduna ba? ",kasa cewa komai tayi banda addu'ar da take yi.



Cikin zafin rai yace"ke bakyajin magana ko, wato mazan kano sun miki kadan shine kika zo kaduna ko?,me hali baya fasawa, to ki sani na fada na kuma fada, na tsani ganin fuskar ki".


Jan hannun ta yayi yace"muje na sauke ki a wajen da kike maula din", yau dai ikhlas babu baki.




Suna fara tafiya wayar ta tayi kara,da sauri ta kalli me kiran.



A natse ta daga wayar, tana murmushi me kayatarwa dan tama manta tare da wa take.



"Hello princess ko nema na baki yi ba? ".



Shagwabe fuska tayi tace"haba zuma na, kira kuma na nawa,kuma ka kashe wayar ka".



"To yanzu dai tashi na kenan nace bari na kira bugun zuciya ta don naji yaya ta tashi".



"Ai kada ka damu, bugun zuciyar ka ta tashi kamar yadda zuciyar ta tashi, dan ni kai ne zuciyar tawa".



"Hmm,da ace kowa na samun mai son sa kamar yadda na samu to da duniya ta sami zaman lafiya, wallahi kullum ji nake kamar daga ni sai ke a duniyar na".



"Nima haka ne a gare ni, banki mu zauna tare da kai ba iya tsayin rayuwa ta, yanzu dai bari na bar ka ka shirya domin tafiya wajen aiki".



"To shikenan gimbiya ta duk yadda kika ce haka ne,sai dai zan so ki kula mini da kan ki".



"Kada kaji komai, zan kula da kai na sosai, amma kai ma ka kula mini da kan ka".


"Insha allah,i love you".



"Bye i love........ "Kasa karasawa tayi, domin wani dogon brake daya ja.



A rude take kallon shi, idanun shi sun canza kala sun yi ja, ficiko ta yayi ya wurgi da wayar ya shake ta.



Cikin fusata yace"waye kuma kike yaudara yanzu dan na tabbatar dan kaduna ne? ", kasa magana tayi domin shakar da yayi mata bata wasa bace.



Hawaye kawai yake zuba a idanun ta,da kan shi ya gaji ya sake ta, yana sakin ta ta fara tari.



Cikin tsananin wahala tace"wai kai wane kalar mugu ne?, ka wani tare ni kamar uba na kana tambaya ta, shin garin kadunar uban ka ya gina da zaka ce na dena zaman ta, kayi rayuwar ka nayi tawa".




Bece mata komai ba yayin da ita kuma bata dena masifa ba, cikin fushi tace"bude mini na fita", banza yayi da ita.



Cikin tsawa yace"dalla ka bude mini na fita, bana son taimakon ko ana taimako dole ne?,banza mata-maza kawai".




Finciko ta yayi ya kalli idanun ta yace"mata maza ko, zaki tabbatar da cewa ni gwarzon namiji ne i promise you that",yana fadan hakan ya sake ta ya tada motar.



Komawa tayi ta zauna,ganin ya dauke hanyar makarfi road yasa ta zaro idanu tana fadin"ina kuma zaka kaini".


Be juyo ya kalle ta ba yace"zan tabbatar miki da cewa ni cikakken namiji ne ba mata-maza ba".



Cikin ta ne ya kado, da sauri ta fara fadin na shiga uku, ko kallon ta be yi ba ya cigaba da tsula gudu a titi.




Cikin ranta fadi take"na shiga uku ni ikhlas ina wannan zai kaini ne? ",hawaye taji yana niyar zubo mata cikin sauri ta mayar dashi.


"Ai sai ya raina ni idan na cigaba da nuna tsoro na", ta fadi hakan a ran ta,jakar ta ta bude ta dauko orbit ta bare ta saka a baki, sannan ta janyo wayar ta daya yardar a gefe ta kunna data tana chatting dasu feenerh tana dariya.




Ta gefen ido yake kallon ta,"lallai wannan ta wuce tunani na kada na daukowa kaina abinda yafi karfi na"ya fadi hakan a ran shi.




Cigaba yayi da tukin shi a ranshi ya kuma cewa"yanzu idan na sauke ta ai rainani zata yi ta dinga kallo na a matsoraci, bari dai naga iya gudun ruwan ta", daga haka ya cigaba da sake-sake a ran shi.


*naso muku typing yafi haka but hakan be samu ba dan haka ku kara hakuri, masoyana ku sani ni da ku*~one love~*😘







💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*


Wattpad @13 deeja

Or
Deeja1love.blogspot.com

*written
-by-
*Deeja one love*



*dedicated*
to
*Maryam*

Khadeejert haidar(*namesy tawa*) ke ta dabance a zuciya ta,allah ya kara basira ameen




Sanaz marubuciyar direban gidan mu,na gode sosai da yadda kika comments hakan yana kara mini karfin gwiwa.




*duk kuskuren da kuka gani kuyi hakuri domin dan adam tara yake be cika goma ba*.



39-40




Wani tangamemen gida yayi horn, kallon gidan tayi ta gefen ido, gaban ta ya fadi, kasa daurewa tayi hakan yasa sai da ta kalle shi.




Fuskar shi a daure take kuma gaban shi yake kallo, tunowa ko waye shi da baban shi a nigeria yasa ta koma ta zauna.




A hankali yayi parking sannan ya fita, tana kallon shi ya zagayo ya bude mata kofa, murmushi tayi sannan ta fito.




A natse take takawa kamar wacce zata shiga gidan ta hankali kwance, sai ma murmushi da take mai kayatarwa.




Shi kan shi kasa-kasa yake kallon ta yana mamakin irin yadda take abubuwan ta hankali kwance, wata zuciyar tace mishi "kaman ta yadda maza ke daukar ta suna ajiyewa", dogon tsaki yaja.




Ikhlas kuwa shigar su palour din ya dauke mata hankali, domin kudi dai an narka shi a gidan.



Idanu da baki ta saki tana kallo,kallon ta yayi ganin hankalin ta na kan gidan yasa ya wuce ya barta a wajen.




Ta kasa dena kallon yadda aka kayata gidan, gaskiya kudi suna inda suka, domin an tsara gidan yadda ya kamata, komai a gidan yana zaune a muhallin shi ne.



Jin numfashi daf da ita yasa tayi sauri ta dago,ganin shi kusa da ita yasa ta dan matsa baya kadan.



Murmushi yayi yace"meye na matsawa bayan kin san daya muke da ke".



Kallon kamar ya tayi mishi,murmushi ya kuma yi yace"har kin manta cewa tare da mata-maza kike".



Lumshe idanu tayi tana murmushi,hannun ta ya rike yace"wuce muje".



Da sauri ta kwace hannun ta tace"ka rabu dani meye haka ne?, ko ance maka ni yar iska ce da zaka kawo ni gidan ka, kazo ka fitar dani domin ina da aikin yi".




Kallon ta yake yi, cikin zafin rai ya fincike ta ya zaunar da ita akan kujera, kallon up and down yayi mata.



Yace"eh a hakan kike salaha, bayan mazan dake daukar ki suna ajiyewa ko? ",kauda kai gefe tayi.




Wayar shi ya dauko ya dannan sannan ya kara a kunne,tana ji yace"ikhlas ahmad yau baza ta samu damar zuwa wajen aiki ba".



Cikin sauri take kallon shi, be kalle ta ba sai ma cigaba da danna wayar shi da yayi.




Wani kiran ne ya shigo wayar, da sauri ya daga yace"sudeis bazan samu damar zuwa ba ka basu hakuri kawai".




Da sauri ta mike, kallon ta yayi yace"ki zauna mana tun kan na fara nuna miki ni cikakken namiji ne har kin tsorata? ".



A sanyaye ta koma ta zauna, zuciyar ta na bata shawarar ta bashi hakuri ko kuma dai ta tsaya taga gudun ruwan shi.




Ba tasan yazo kusa da ita ba, sai dai jin numfashi da tayi akan wuyan ta, da sauri ta juyo.



Shi kuwa dumin jikin ta tuni yasa ya fara barin kano,idanun shi a lumshe cikin sarkewar murya yace"ta..... In..... Ina..... Zamu fara".




Jikin ta ne ya dauki rawa a lokacin da ya fara kissing wuyan ta cikin zafi-zafi.



Babu abinda yake yi sai jan numfashi, ganin baya cikin hankalin shi ne yasa ta fara buge shi.



Rike hannun ta yayi, idanun shi yayi ja yace"yanzu kin fahimci da namiji kike ba mata-maza ba k har yanzu kallon mata-maza kike mini".



Cikin kuka tace"wallahi.....,. ", kasa karasawa tayi saboda wata damka da ya kai ma kirjin ta.


Runtse idanu tayi hawayen na zuba ta fara bashi hakuri,shi kam be ma san tana yi ba.





Sama-sama yake jiyo kukan ta, cikin kuka take fadin"kaji tsoron allah kada ka keta mini haddi na, kayi hakuri ka bari na yarda kai namiji ne".



Cak ya tsaya a hankali ya sake ta ya koma gefe ya kwanta,dafe da cikin shi idanun shi a rufe.



Surar jikin ta da halittun kirjin ta suke dimauta shi,sake damke marar shi yayi yana jan numfashi.




Ita kam ikhlas jin ya sake ta yasa ta yunkura ta dauki rigar ta, sai da ta kai kofa sannan ta tsaya ta saka.



Sai dai me kokarin budewa take yi amma abu ya gagara, zubewa a wajen tayi tana kuka mai cin rai.




Jin kukan har cikin kan shi yasa ya mike a daddafe,kamar me koyon magana yace"ki....... De.... Na... Kuka..... Ina..... Zu...... Wa", daga haka ya nufi cikin daki yana tangadi kamar wanda yasa kwaya..





Ganin ya shige daki be hana ta dena kukan ba, haka jikin ta be dena rawa ba.



Shikam sai da ya dinga shekawa kan shi ruwa, domin samun relief, idanun shi a rufe surar ta kawai ke mishi yawo, ganin bazai samu yadda yake so bane yasa ya yi wanka kawai ya fito.



A inda ya bar ta anan ya same ta, jiyo kamshin turaren shi yasa ta dago da sauri, ya canza kaya zuwa kanana, sai ta ga kamar wannan kayan sun fi amsar shi.



A sanyaye yace"kiyi hakuri na bar ki kina ta jira na", yana fadin hakan ya bude kofa ya fita ita kuma ta bigo shi a baya.


Wata motar ya dauko sannan ya bude mata ta shiga,babu wanda yayi magana a tsakanin su.



Da mamaki take kallon shi ganin ya kai ta har kofar gida, tunawa da tayi da baby ranar nan yasa tayi murmushi.



Yana parking,ita ma ana mata parking din motar ta,budewa tayi ta fita.


A hankali ta juyo tace"na gode", harara ya galla mata yace"dalla matsa ki bani waje, waya ce miki ina da bukatar cigaba da ganin fuskar ki".



Tabe baki tayi sannan ta wuce,mechanics din ne ya miko mata mukullin motar, sannan ya bude motar maleek ya shiga.




Gida ta wuce tana mamakin hali irin nashi,kamar wani mai juju, tsaki taja sannan ta kwanta.




Kiran feenerh tayi sannan tace"ina fa tunanin ranar friday na shigo kano din".



"Allah ya kaimu, akwai aiki a kasa ne?",feenert ta fada.



"Eh lallai tunda naku burin ya cika dole ku manta da nawa", tana fadin hakan ta kashe wayar.



Karfe biyar ta farka, cikin sauri tace"na shiga uka, baby yana makaranta banje na dauko shi ba".



Da sauri ta mike ta shige bathroom,wanka tayi shaf-shaf ta fito.



Riga gown yar kanti ta saka, kalar peach gyalen ta yafa,low fast ta saka shima kalar kayan sannan ta dauki key da wayar ta ta fito.





Da mamaki take bin shi da kallo, juyowa yayi yace"baby, kin tashi daga barcin ai na shigo kina barci".




"Waye ya dauko ka? ", tambayar da ta jefa mishi kenan,daga kai yayi yace"baby, daddy fa ne ya dauko ni",shiru tayi bata kuma cewa komai ba.





Bangaren maleek kuwa yana sauke ta gida kawai ya wuce, ko takan hajiya be bi ba da take ta faman surfa masifa.



Kan bed ya fada yana tunano moment din su tare,runtse idanu yayi yana fadin"me ke damu na ne?", tunawa yayi da yadda yake ganin ta da samari da yawa yasa yaja tsaki yana fadin"jiki na me tsarki nake hadawa dana wannan karuwar".




Cikin sauri ya mike ya shige bathroom ya sake yin wanka, yana fitowa ya kalli agogo ganin karfe uku da rabi ya tina mishi da sadik lokacin da yake tambayar shi, shi kuma yake bashi amsa.





Key ya dauka domin yaje ya dauko shi, a palour ya tarar da bintu ta ci uban kwalliya, key na dakin shi ya cilla mata yace"ki gyara mini kan na dawo", cikin rawar jiki ta amsa.



Hajiya ta tabe baki tana fadin"wahalalliya kawai",babu wanda ya tanka mata.



Kamar yadda ya zata kuwa, dan shi kadai ya samu duk an dauki sauran yaran.



Baby kuwa ganin wanda yazo daukar shi yasa ya fara murna, daukar shi yayi ya kai mota.



Suna tafiya shi kuma yana tambayar shi yana bashi amsa, a hakan ya dan san wasu abubuwa game da ita.



Sai da suka biya ya siya mishi kayan makwalashe sannan ya kai shi gida.




Yana ajiye shi ya wuce,dan yana tunanin kar ya shiga ta gan shi ta dauka wani abun ne.




Da dare yana zaune yana kallon yadda lovely din shi ke shiryawa,saifullahi ya kalle shi yace"wallahi yau baka da uzuri sai kaje kun hadu da princess".



Murmushi yayi yace"to ai kai nake jira ko kazo mu tafi yau dai na wuce gori", dariya suka yi gaba daya.




A palour suka sami mummy tana ganin su ta mike tana fadin"ga yan biyu na sun fito, sai ina hka? ",shafa kai suka yi.




Maleek yace"zamu je ganin princess yau",kara washe baki tayi tace"daga nan za'a wuce wajen queen ko? ",shafa kai yayi yana dariya.



Hajiya ta tabe baki tace"ayi dai mu gani",babu wanda ya kula ta,bintu data ji wannan maganar ta mike tana kuka ta wuce daki.



Sai da mummy ta raka su har prking lot tana musu addu'a sannan ta koma gida.


A mota ya kira ta yace"princess kin isa ko? ",cikin shagwaba tace"ku kawai nake jira tun dazu na iso".



Murmushi yayi yace"wannan zumudi haka", dariya tayi tace"ai dole nayi yau zan hadu da kanina da aka gama ja mini rai akan shi".



Light sparkling suka yi parking,da sauri suka shiga ciki, da sallama suka karasa kusa da ita.



Cikin sauri ta dago domin ganin wannan lilly din na zuman ta, shima haka a wajen shi yana so yaga wacece wannan princess din.




Idanun su na haduwa a tare suka zaro idanu, suka ja tsaki,maleek ya ya mutsa fuska yace" *ASHE KECE*dama princess ko karuwa dai".





💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*


Wattpad @13 deeja

Or
Deeja1love.blogspot.com

*written
-by-
*Deeja one love*



*dedicated*
to
*Maryam*


*Rukayyat ina godiya da kaunar da kike nuna mini*.

Deejency Allah ya baki lafiya wayyo bansan baki da lafiya ba.


41-42





Tsaki taja ta juya ta kalli saifullahi tace"dama wannan mata-mazan shine lily din? ",shi dai saifullahi mamaki kawai yake yi a ina suka san juna.





"Dama kun san juna ne?", ya tambaya,maleek yace"lovely wannan itace karuwar da na baka labari fa.


Da sauri saifullahi yace"a'a lily baka fahimce ta bane, amma princess ba karuwa bace",kallon tsana ikhlas tayi mishi tace"ptchewwwww, wallahi da ace na san cewa kai kanin sa ne da bazan taba yadda ya kawo ka nan ba, banza kwarto kawai".




Cikin zafin zuciya yayi kan ta,saifullahi yayi rike shi yana fadin"lily meye haka ne wai",fincike rigar shi yayi ya fice daga wajen.




Saifullahi ya kalle ta,cikin jin haushi ta ja tsaki tana fadin"aikin banza, aikin wofi kawai".



rasa wazai rarrasa a tsakanin su, hakan yasa ya zauna kawai, dagowa tayi ta kalle shi tace"ai da sai ka bishi kawai me kuma zaka tsaya ka ce mini".



Daga haka ta dauki jakar ta ta bar wajen, dafe kai kawai saifullahi yayi.



Cikin sauri ta bar wajen,tana tafe hawaye na zuba daga idanun ta"*KARUWA*, i hate the sound of this word", ta fada cikin karaji.



Tana zuwa gida kawai ajiye motar tayi ta shige cikin gidan, kan bed ta fada ta fashe da kuka tana mai takaicin fitar ta yau.




Cikin kukan take fadin"banda halin rayuwa ta yanzu nayi aure ko ina gida tare da yan uwa na, umma me yasa kika tafi kika barni, gashi yau ana kira na da karuwa".



Kukan ta ya tsanan ta,baby ya turo kofar ya shigo hawayen yake share mata yace"mummy daddy na ya saki kuka ko? ", girgiza kai tayi.




Rungume ta yayi yace"umma ce ko, duk ranar da muka hadu da ita zan rama miki kukan da ta saki",kasa cewa komai tayi banda hawaye da yake fita daga idanun ta.




Bangaren maleek kuwa yana fita ya figi motar cikin speed gidan da ya kai ta ranar nan ya koma.



Kamshin ta yana nan, hakan yasa ya lumshe idanu tuno wacece ita yasa yaja tsaki, sannan ya shige bedroom.



Kan bed ya zauna ya dunkule hannu biyu, yasa a hab'a, da karfi ya furta"IMPOSSIBLE!!! ",keys din ya sake dauka ya fice daga gidan.




Gida ya wuce, kamar koda yaushe yan zaman gulma suna nan, wannan karan ko barka da daren hajiya bata samu ba, wucewa kawai yayi.



Yana shiga falon mummy ya tarar da saifullahi a ciki, cikin sauri saifullahin ya mike shikam maleek juyawa yayi domin ya fice.




Mummy ta kira sunan shi hakan yasa ya tsaya,karasowa tayi ta riko hannun shi tace"daddyn ku yana neman ku".



Cikin sauri ya juya ya kalli saifullahi,kauda kai saifullahin yayi domin dukan su sun san kiran ko na meye.




Cikin sanyin jiki suka wuce side d'in daddy,a can suka tarar hajiya,a natse suka zauna.




Daddy yayi gyaran murya yace"to alhamdulillah,hakkin ku dake kaina duka allah yana bani ikon sauke su, sai dai kuma daya ne da har yanzu kun kasa taimaka mini na sauke shi, wato na aurar daku".



Yan nunfasa sannan ya cigaba da cewa"ganin na zuba muku idanu ba wai yana nufin kuyi yadda kuke so bane a'a hakan bazai yiwu ba, dan haka na baku nan da two months ku fito da matar aure, idan ba haka ba hukuncin da zan yanke bazai muku dadi ba".


Hajiya rabi tayi sauri tace"haba muhammadu ai wannan magana mai sauki ce, ga yan uwan su ba sai a hada su ba?".



Daddy yace"kada hakan ya zama da cutarwa a fara bari aga gudun ruwan su, sai maganar tafiya adamawa,inajin nan da sati uku zamu tafi domin muje mu sake gaishe da mai jiki".




Tabe baki hajiya tayi tace"allah ya kiyaye hanya", ameen, ke bazaki je bane? ", daddy ya tambaye ta.



"Eh, babu inda zan je,yaushe na dawo daga adamawar,kudai allah ya kiyaye hanya",daddy ya kalli su maleek yace"kuje sai ku fara shiri".




Cikin sauri suka amsa da"to", sannan suka tashi,hajiya tace"au tare zaku tafi kenan",daddy ya amsa mata da "eh, harda ma su shamsiyya".



Mikewa tayi tace"sai dai biyu ko daya su ta biku amma bazai yiwu a tafi a barni ni daya a gidan nan ba".




Murmushi daddy da mummy suka yi kawai, dan babu wanda ya tanka mata gudun kada k'ilu taja bau.




Su maleek kuwa suna fita,bangaren su suka nufa babu wanda yayi magana, kowa tunanin shi daban.




Sai da yayi wanka sannan ya sanya kayan barci ya kwanta, gaba daya kan shi ya kwance, nemo mata cikin abinda bai gaza kwana sittin ba abu ne mai wuya.




Ajiyar zuciya yayi yace"ya Allah! Help me,wannan wane kalar abu ne ke kusanto ni, ni maleek", Da k'yar ya samu barci yayi awon gaba dashi.




Bangaren saifullahi shima hakan ne, sai dai nashi da sauki tunda yana da princess, to amma tunanin shi shine anya iyayen shi zasu fahimci wacece ita? Babu wanda zai yarda dan shi ya auri macer dake zaman kan ta wannan bazai yiwu ba,da haka shima barcin ya dauke shi.




Ita kam ikhlas yau tafiyar umman ta da mutuwar su gwaggo ya dawo mata sabuwa, dan ta tabbata da suna da rai da duk baza ta fuskanci hakan ba.



Shafa kan baby tayi da yake barci tunanin ta shine baby yadda besan ko daya daga cikin iyayen shi ba.



Itakam dama bata saka ran yin aure dan tasan bata da iyayen da zasu d'aura mata auren.



To! Idan ma tana dasu,waye zai bar dan shi ya auri yarinyar da bata da asali, wannan bazai yiwu ba, dan ko saifullahi bata taba sawa aranta zasu yi rayuwar aure dashi ba.



Hawaye ta goge tana fadin"Abba kabeeru duk kai ka ja mini wannan".


Runtse idanu tayi wasu magan-ganu na dawo mata kai

_haba ikhlas kamar ba musulma ba baki yarda da kaddara bane,ko kin manta kowa sai ya mutu ne,ki daina fadan haka addu'a ya kamata ki rinka mishi ba wai kuka ba,dan ta hakan ne zai gane cewa ya bar 'ya ta gari da take mishi addu'a"_




_kayya meya kawo haka kuma haba ikhlas da bakin ki kike fadin haka ne,kamar baki yi karatu ba,kin manta kowa da kaddarar shi ne,kada ki manta ke musulma ce_






kuka ta fashe dashi domin tabbas tayi rashin mai mata nasiha,ganin kukan bazai yi mata bane yasa ta mike ta dauro alwala ta fara sallah.




Wanka yayi cikin sauri ya shirya, wayar shi ya dauka, cikin sauri ya danna wasu numbers, ana d'agawa yace"manager ina so ka kori ikhlas ahmad daga shoprite din ku".



Jim yayi kafin yace"amma yallab'ai kan wane dalili? ",cikin fushi yace"oh! Tambaya ta dalili kake yi?".




Cikin sauti yace"yi hak'uri yallab'ai zamu sallame tan",be ce komai ba ya kashe wayar.



Murmushin mugun ta yayi yace"zan ga kuma dame zaki dinga tak'ama dashi,filthy bitch".



A tare suka fito,maleek yace"good morning lovely",dariya yayi yace"morning lily".



A tare suka jera har suka fiyo falo, kamar kullum suna zaune suna kallon masu shiga da fice.




Saifullahi ya gaishe da hajiya shi kam maleek yace"ah! Hajiya barka da hutawa,har an fito kenan? ",harara ta galla mishi.




Cikin rawar baki bintu tace"ina kwana yaya maleek",be kalle ta ba ya bata amsa da"lafiya", sannan yace"lovely ka taso muje kada muyi late mana".



Nan fa hajiya ta dasa"wato kai ga mara mutunci, yayan ka shi da yake yasan darajar na sama dashi ya tsuguna ya gaishe ni amma kai baza ka iya gaishe dani ba, kaga maleeku ka kiyayeni".




Suna shiga falon mummy ta karaso, harara ta gallawa maleek da yake gaishe ta kafin tace"tun da na fara jiyo muryar hajiya a sama na san ka taho, wato kai baza ka dena tsokanar ta ba ko".



Kwantar da kan shi yayi a jikin mummyn yace"to ai itace mummy ta fiye sa ido wallahi, har fa tazo ta zauna a falo tana kallon masu shige da fice".




Mummy taja hannun shi ta kai shi kan dinning ta zaunar dashi,cikin sauri -sauri suka yi breakfast din sannan suka fice".






haka nan yaji kawai yana so yabi hanyar,yana isa kofar gidan motar ta na fitowa daga cikin gidan dan haka kawai ya rufa mata baya.




Sai da ta sauke baby a makaranta yana kallon ta sannan ta wuce,a bakin shoprite din tayi parking shima gefe yayi yana jiran fitowar ta.



Ikhlas kam bata ma lura dashi ba,tana shiga kamar yadda ta saba ta fara gaishe dasu, manager ya dube ta bayan ta gaishe dashi.



Yace"ikhlas ahmad nasan kina da hakuri, ki k'ara akan wanda kike dashi,ga wannan dan allah kiyi hak'uri bani da yadda zan yi ne shiyasa sak'o daga can sama kan na kore ki".



Murmushi tayi tace"kada ka damu manager, haka Allah

Please Login or Register in order to submit comment