Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

boy".



Daya daga yan matan parlour din taja tsaki,ko kula ta basu yi ba,suka shige ciki.




Kan dinning table ta ja shi, shi kuma sai zuba mata shagwaba yake yi,a baki ta dinga bashi har ya koshi sannan ta raka shi dakin shi, da kan ta ta hada mishi ruwan da zai yi wanka.





Yana shiga wankan ta fito mishi da kayan da zai saka,koda ya fito ya gani murmushi kawai yayi domin yasan aikin mummyn shi ne.




Yana gama saka kayan ta shigo, cup ne a hannun ta da fara'a tace"lily ga coffee din",karaso wa yayi ya rungime ta yana fadin"i love you my mummy".





Mika mishi tayi tace"love you too my lily, yanzu amsa ka shanye kaji",amsa yayi ita kuma ta fita.



Yana fara sha ya tuno da ita, yadda take wani juya ido ga wannan tsohon mutumin, ganin su da yayi a hotel, da farko ga sharrin da tayi mishi,tsaki ya ja sannan ya kara kurban coffee din.





Ajiye wa yayi domin jin coffee din nayi mishi daci,a hankali yace"to ma wai me yasa nake damuwa da halin ta ne? ",zuciyar shi ta bashi amsa da cewa"dan dai ita din bahaushiya ce kamar shi, da haka ya kwanta.





Ikhlas kuwa, da wuri ta shirya domin kai baby makaranta, haka kuma ta wuce wajen aiki,tana driving suna fira da saifullahi a waya.





Yace"princess kin san cewa lily fa ya dawo? ", da mamaki tace"bangane ya dawo ba".


Dariya yayi yace"wallahi da gaske nake,lily iz back,jiya ma ya wuce kaduna".


Ajiyar zuciya tayi tace"wai dan allah da gaske kake ne?", da sauri yace"eh mana da gaske wallahi".



Ajiyar zuciya tayi tace"tun da har ka rantse na yarda, amma me yasa ko nema na be yi ba".




Yace"ya neme ki mana, to amma kuma kina gombe, sannan kin dawo shi kuma ya tafi kaduna".





"To shikenan,nasan wata rana zamu hadu ne dashi", ta fada lokacin da take parking.



Cewa tayi"na zo wajen aiki zuma na, sai anjima zamu yi waya",yace"okay bye, ki kula da kanki, i love you".



Murmushi tayi kan tace"to insha allah i love you too", tana fadin haka ta kashe wayar.



Koda ta tashi wajen aiki, gida kawai ta wuce, wanka tayi ta canza kaya sannan ta tafi gidan hafsat.




Tana shiga, baby ya taho da gudu ya rungume ta,shafa kanshi tayi tace"am sorry banzo na dauke ka ba",girgiza kai kawai yayi.



Hannun shi ta rike suka shiga gidan tare,hafsat dake zaune tana waya tayi murmushi.

Tana ajiye wayar tace"kai cat eyes wankan yayi, ko tare kike da saifullahi? ",girgiza kai tayi tace"a'a.




Beelert ta fito daga daki tana murmushi tace"barka da dawowa, ina feenert din yau? "Tace"yau ko ganin ta ma ban yi ba dan ban biya wajen ta ba".




Beelert tace"jiya abdallah ya turo mini da number din kabeer", ikhlas tace"kada ki damu kiyi mishi magana ta whatsapp, kawai".




Hafsat tace"to ita feenert din fa, sannan ke ya kamata kuyi soyayya dashi", ikhlas tace"eh hakane but manager din mu ya tura ni branch din su da suka bude a kaduna, yanzu haka can zan koma, babu matsala suyi kawai, idan yaso sai ki tura mishi pics dina idan ya nema,gudun kada ya gane ki, tunda kinga baban ki babba ne a gombe ta yiwu ya san ki".




Beelert tace"hakane kuma, zan mishi maganar, amma ya zakiyi da baby tun da yana makaranta a nan? ".



Ikhlas tace"zan tafi dashi, idan yaso sai na nemar masa transfer kawai", hafsat tace"why not mu koma kaduna dukkan mu? ",ikhlas tace"ba zai yiwu mu bar feenert ita kadai baza ta ji dadi ba".



Beelert tace"hakane to shikenan",daga haka ikhlas ta mike domin tafiya.


Har bakin mota suka rakata suna kara tattauna abinda yake faruwa.



Kwance yake a kan bed din shi, filo yasa a kan cikin shi, idanun shi a rufe,kamar me barci sai dai tunani ya fada.




Duniya kenan, fuskar ta ce ke mishi yawo, yayin da zuciyar shi ke jin zafin yadda take wa wannan tsohon murmushi me tsada.



Zaune ya mike, a karo na babu adadi ya janyo wayar shi, number din lovely din shi ya zubawa idanu, kamar zai yi kira sai kuma ya fasa.



A sanyaye ya mike ya shiga bayi, nan ma dai tunanin ya kuma cigaba da yi, yadda take karya ba tare da dar ko shakkar shi ba.



Tsanar ta da haushin ta yake karuwa a zuciyar shi, tsaki yaja sannan ya fara wankan.



Yana fitowa ya shirya cikin wani farin yadi full text.


Suna zaune a falo ya kamshin tureren shi ya fara yi musu sallama a kofofin hancin su, maganar da suke yi suka dakata.




Wata siririyar budurwa ta taso da sauri tana fadin"sannu yaya, ya hanya? ",kallon ta yayi ya dan kauda kai, ya nufi hanyar dakin mummyn shi.




Babbar wacce take zaune tace"lallai maleek, ni zaka gani a zaune ka wuce ko, tarbiyar daka dauko daga can kasar turai din kenan? ", ta gefen ido ya kalle ta yace"barka da hutawa hajiya", daga haka ya wuce.




"Tabdijam wato ga 'yar iska, ni kake gayawa haka,maleek ubanka ma yayi kadan ballantana kai karamin alhaki, kuma wallahi ka sani, auren ka da bintu babu fashi, sai dai idan bana raye, uban naka zai zo ya same ni", tana fadin haka ta mike.




Harara ta gallawa bintun tace"shegiya wacce ta yardar da zuciyar ta kare ya cinye, idan ba haka ba kina bin namiji yana wulakanta ki".



Cuno baki tayi tace"ni dai hajiya do something pls",jan hannun ta tayi suka shige daki.





Maleek kuwa yana shiga dakin mummy ya tarar da ita a tsaye, alamun taji maganar da hajiya ke fada.



Kallon shi take da alamun damuwa, murmushi yayi yace"mummy stop worrying about what she has said, babu abinda zai faru, da kai na zan kawo miki surukar ki".



Harara ta galla mishi tace"gafara can matsa, yayan naka ma ya kasa ballantana kai da shekara nawa kana mini karya, sai dadin baki, dan kun ga na damu kuyi auren shiyasa kuke ta zillewa, shima daf nake da nace ya dawo gida".




Rungume ta yayi yace"i know definetly u will like her,the time i bring her here",idanun shi ta kalla tace"who? ", yace"your inlaw", kunnen shi ta kama tace"won't you stop lying? ",daga kai yayi yana dariya.



Rungume juna suka yi, cikin farin ciki yace"lovely ya riga da ya sami princess, ni ya rage na kawo miki queen",sausauta rikon tayi mishi tace"i don't believe you",cuno baki yayi yace"mum, u have to",dariya suka yi gaba daya.



Zaunar dashi tayi tace"oya, tell me how she looks like",dariya yayi yace"princess ko queen? ",harara ta galla mishi tace"duka mana".




Shafa fuskar shi yayi yace"princess dai bamu hadu da ita ba har na taho, queen ma haka har yanzu bamu hadu ba ita.......... ", hannu tasa ta dani bakin shi wanda yasa be karasa ba.



Wajen ya shafa ya kalle ta ya shagwabe fuska, tashi tayi tana cewa"mashirmanci", daga haka ta wuce bedroom din ta.





Sai yamma daddyn su ya dawo,cikin farin ciki ya tare shi,daddy ya rungume shi yace"welcome son",da fara'a yace"thank you".





Mummy ta amshi jakar shi tace"to yanzu muje kayi wanka ka shirya sai ka fito",sun juya kenan, hajiya tayi sallama ta shigo.





Kasa-kasa maleek ya ja tsaki,waje ta samu ta zauna tace"muhammad dama wajen ka nazo akan maganar wannan dan iskan yaron naka".




Da sauri mummy da maleek suka kalli fuskar daddyn, shi kan shi fuskar shi ta nuna rashin jin dadi, domin duk duniya bashi da wa'inda yake dasu sama da yaran shi guda uku.



Hajiya kuwa bata damu da yanayin su ba tace"ni ya gani dazu ya wuce wai ya cewa sannu da hutawa kamar wata tsarar shi".



A fusace daddy ya kalli maleek yace"da gaske ne abinda hajiya ta fada? ".


Sunkuyar da kai yayi yace"hakane daddy amma.... ", da sauri ya dakatar dashi ta hanyar daga mishi hannu yace"kada hakan ya kuma faruwa, domin hajiya yaya ta ce".




Kallon daddy yayi idanun shi yayi ja kamar mai shirun yin kuka,daddy ya daka mishi tsawa yace"ka tashi ka bani waje ko sai na saba maka".



A zafafe ya mike ya fita, mummy ta bi daddy da kallo sannan ta mike, cikin fushi daddy yace"dawo ki zauna".



Jiki a sanyaye ta dawo ta zauna,hajiya ta tabe baki tace"mace sai iyayi, da kamar wani ke kika haife shi, to ki sani duk tsiya ba'a canzawa tuwo suna", daga haka ta mike ta cigaba da sababi har ta bar falon.



tana fita mummy ta mike, cikin sauri daddy ya riko ta yace"dawo mana sarauniyar mata", jikin shi ta fada ta fashe da kuka.




Cikin kuka tace"da ace yau ban haihu ba da sai aji dadin mini gori, amma daddyn salma yarana biyu fa, dan ma allah yayi wa daya rasuwa ne, amma kullum hajiya sai tayi mini gori akan maleek".




Murmushi yayi yace"maryama tawa, ai ya kamata zuwa yanzu ki fahimci halin hajiya mana",hannun shi ta rike tace"da ace salma kafin ta rasu bata bar mini amanar maleek ba da nayi zuciya na daina kula dashi a gidan nan, amma ta bar mini amanar shi a waje na".






Daddy yayi dariya yace"maryama taso muje mu rarraso yaron naki", hannun su sarke da Juna suka nufi nashi dakin".




Maleek kuwa yana shiga dakin ya bude fridge ya Ciro rusa ya bude ya kwankwade,jefa da robar yayi ya daki bangon dakin.



Cikin sauri ya nufi bedroom din shi, wani hoto ya dauko, mace ce kyakkywa, gefen ta wani yaro ne, da alamu suna cikin farin ciki domin duka dariya suke yi.




A take hawaye ya fara zubo mishi, ringume hoton yayi yana kuka.



Mummy ta dafa shi, da sauri ya juyo, ganin ta yasa ya kwanta a jikin ta yace"mummy kin ga daddy ko?, daga dawowa na ya fara mini fada, ya dena sona ko? ".




Daddy ya tsugunna ya shafa kan shi yace"maleek taya zan dena son ka, bayan daga kai sai yayan ka nake da,kada ka manta kune kadai yaran dana ke da a duniyar nan, dan haka har gobe ina son ku, kuma bana fatan na dena gar abada".



Nufasawa yayi kafin yace"ina so ka dinga bin hajiya a hankali kamar yadda nake yi, kaji idan ka gan ta ka dinga gaishe ta", daga kai kawai yayi.




Daga haka daddy ya fita,mummy kuma ta cigaba da zama har yayi barci, sannan ta fita.



❤❤❤❤
❤❤❤❤one love😘.



💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)



*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~💫💫💫*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~❄we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*


Wattpad @13 deeja

Or
Deeja1love.blogspot.com

*written
-by-
*Deeja one love*



*dedicated
to
*Maryam khamis*




31-32


Ikhlas kuwa yau take hada kayan ta domin tafiya kaduna, tana gamawa ta fara fitar da kaya.




A waje parking lot saifullahi ne tsaye yana jiran ta, tana fitowa ya kalle ta ya kauda kai.



Murmushi kawai tayi, shi kuma ya budewa baby motar, hannu ya mika mishi suka yi musabaha, sannan yace"yaro na ka kula da kan ka".




Baby yayi murmushi yace"insha allahu uncle zan kula da kaina sosai",shafa kan shi ya kuma yi yace"good boy".



Yana juyowa yaga shi take kallo, basarwa yayi ya juya, murmushi tayi ta bishi a baya.



Yana bude kofa ta sa hannu ta mayar ta rufe, juyawa yayi ya kafa mata idanu,langwabar da kai tayi tace"am sorry zuma na, kaji".




Ajiyar zuciya yayi yace"ya zan yi, princess bazan iya fushi dake ba, kin ga yanzu kin sa dole na koma kaduna".



Lumshe idanu tayi tace"ashe zan taimaki mummy kenan",yi yayi kamar beji me tace ba.




Hannun ta ta rungume a kirji tace"to zan tafi,idan na isa zamu yi waya", kallin ta yayi fuska da damuwa yace"haba princess yanzu da gaske tafiya zaki yi?".




Ta kasan ido ta kalle shi tace"zuma na kasan bana wasa kalar wannan,kayi mini addua kawai",a sanyaye yace"allah ya kiyaye hanya,keys na gidan yana hannun mai gadin na mishi magana idan kin je sai ki amsa".




Daga kai kawai tayi, sannan ta bude motar ta ta shiga,yana tsaye yana kallon ta har ta fice daga gidan, a hankali yayi ajiyar zuciya sannan shima ya shiga motar shi ya fice daga gidan".




Awa biyu ya kai ta kaduna, abuja road a nan gidan yake, har ma yaso yafi na kano kyau, tana amsar keys din ta bude gidan, flat ne mai kyau, murmushi tayi a zuciyar ta tana wa saifullahi godiya.



Baby ta nuna wa dakin shi sannan ita ma ta shiga nata,sai da ta shiga tayi wanka sannan ta fito ta kara gyara gidan duk da saifullahi yasa an gyara mata.





Sassaukan girki tayi musu, dakin baby ta shiga, yayi wanka ya canza kaya, murmushi tayi domin sai ya tuna mata baban shi, shima akwai tsafta.



Kallon ta yayi yace"baby na zo ne", hannun shi ta rike tace"taho muje kaci abinci", tare suka ci abinci.



Suna gamawa baby ya kunna game, ita kuma ta dauko wayar ta domin kiran yan kano, da beelert ta fara sannan ta kira feenert.




Sai da ta katse sannan ya kira ta,a nutse ta dauka, ajiyar zuciya yayi yace"princess kin isa lafiya".



"Lafiya lau, ya kewa",ta fada cike da tsokana, cikin shagwaba yace"ai zaki sani ne da kika barni a kano".




Fira suka yi irin ta masoya sannan suka ajiye waya.



Washe gari da wuri ta tashi ta shirya, sai da taje wata makaranta,*HELIX MATHEW INT SCH*ta yiwa baby registration sannan ta wuce wajen aikin ta.




Sai yamma maleek ya farka, duba wayar shi yayi karfe biyar da rabi, wanka yayi sannan ya fito.




Tsaki yayi ganin bintu a zaune,ita kuwa tana ganin shi ta mike cikin sauri tace"sannu da fitowa yaya", kallon ta yayi kawai ya juyar da fuskar shi.




Bangaren mummy ya shiga, tun daga bakin kofa yake jiyo muryar hajiya tana surfa masifa, da sauri ya karasa shigowa.




Kallon-kallo suke yi shida mummy, girgiza mishi kai mummy tayi tana murmushi wanda daga gani bai kai zuciya ba.




Mai da maganar da yayi niyar yi yayi ya juya domin fita,hajiya ta galla mishi harara tace"to mara kunya shege mara mutunc, zo ka zage ni ne".



Be kula ta ba ya juya domin tafiya,hajiya ta kuma cewa"na gaya maka ko uban ka be isa ba balle kai karamin mara kunya, kai ko uwar ka da zata baro kabarin ta tazo nan ba zata iya da......... "Kasa karasawa tayi saboda yadda ya nufo ta a fusace.




Da sauri mummy ta tare shi,tana fadin"maleek a'a fa" jan hannun shi tayi amma ko motsawa be yi ba.




Hajiya ya kafe da idanu jijiyoyin kan shi sun fito rudu-rudu,jikin shi har rawa yake yi, mummy tace"wuce nace maka",ko motsi be yiba.



Ganin hakan yasa hajiya sulalewa ta fice daga bangaren.



Mummy tayi ajiyar zuciya, sannan taje ta rufo kofar sannan ta zo ta zauna ta dafe kan ta,daga kai tayi ta kalle shi har lokaci be motsa ba,hawaye ya zubo mata yaushe zata bar matsalolin dangin miji ne?.






Zama yayi kusa da ita ya dora kan shi a kan kafar ta.




*ASALIN SU*


Aisha shine sunan mummy, haifaffiyar garin biu ce dake borno, ta taso ta girma a jahar borno.




ta hadu da daddy ne a wani comference da akayi a abuja, lokacin yana da mata daya fatima,shekarar auren su, goma amma be taba haihuwa ba gashi suna matukar son junan su.




A haka ya nunu yana son aisha, be sha wahala sosai ba aka bashi auren ta, inda ya dawo kaduna tare da ita.



Zaman lafiya sosai suka yi da fatima, sai dai fa daddy yana da yaya guda daya wacce take jarababbiya, a dalilin jarabar ta mijin ta ya mutu shine ta dawo wajen daddy da zama, don bazata iya komawa wajen yayan su da zama ba dan yana da zafi sosai.



Tun da tazo ta sawa fatima idanu da habaici,da gori ana haka yayan su yazo ya takura ta ta kuma yin aure.




Shekarar aisha daya a gidan allah ya bata haihuwa,babu kishi ba komai fatima tayi farin ciki da yaron.



Ita ke mishi komai, idan ka ganshi a wajen aisha to nono zai sha,sun shaku da saifullahi sosai.



Sai dai fa duk da haka hajiya rabi takan baro gidan mijin ta tazo ta yiwa fatima gorin haihuwa.



Hakan ba karamin damun ta yake yi ba, amma aisha takan kwantar mata da hankali.


Soyayyar ta da saifullahi karuwa take wanda hakan ke kara mata kima a wajen mijin ta da abokiyar zaman ta.



Yau tun da ta tashi da zazzabi, kasancewar daddy baya nan yasa aisha ta kai ta hospital, gwajin farko a ka tabbatar da shigar cikin wata biyu.



Kowa yayi murna a familyn musamman saifullahi domin yana murnar samun aboki ko kanwa.



Lokacin saifullahi nada shekara biyar fatima ta haifi yaron ta kyakkyawa, murna wajen mutanen gidan ba'a magana.



Hajiya rabi babu kunya take dashe baki a dole dan uwan ta ya fara samun yara.



Ranar suna yaron yaci suna *abdul maleek*sun taso cikin son juna shida dan uwan shi.



Babu abinda suka nema suka rasa daga iyayen su, sai dai fa daga aishar har fatiman babu wanda ya kuma haihuwa.


Gorin hajiya rabi sai ya dawo sabo,wanda hakan ya kara daga hankalin su sosai.




Suna haka suna addu'a allah ciki ya bayyana a jikin aisha,to fa sabon farin ciki ya sake ziyartar gidan.




Cikin na kaiwa watan haihuwa allah ya azirtata da yarinya mace, sun yi murna sosai da sosai.



Sati na zagayowa yarinya taci sunan fatima, suna ce mata zahra.


Yarinyar nada shekara hudu a duniya taje makaranta aka neme ta aka rasa, wanda hakan ya daga hankalin yan gidan.



Maleek ya samo sunan *lily*ne saboda son *lily flower*da yake yi, wannan yasa duka gidan suke kiran shi da haka.



Shi kuma yake kiran dan uwan shi da *lovely*shekarar maleek takwas a duniya saifullahi kuma nada goma sha uku allah yayiwa fatima rasuwa.



Mutuwar data razana gidan gabaki daya kenan,rashin kwanciyar hankalin da yaran suka kasa samu yasa daddy tura su kasar india, inda suka cigaba da karatun su acan.

hajiya rabi kuma tana da yara mata guda uku, babbar su itace,shamsiyya sai sadiya da bintu.



Tunda bintu ta kyalla ido taga maleek zuciyar ta ta kamu da son shi, yayin da ita kuma sadiya ke mutuwar son saifullahi.



Ita dai shamsiyya ce babu ruwan ta da maza, harkar ta take yi kawai wanda yanzu haka business take.

Ita kam sadiya kamar ba hajiya rabi ta haife ta tana da saukin hali da hakuri, inda bintu ta debo masifar hajiya rabi.



Mutum daya take saurarawa maleek shima dan tana son shi ne, sai saifullahi shi kam dama baya shiga harkar ta.


*WANNAN KENAN*.


Yau ikhlas sauri take a tashi aiki ta wuce gida domin irin gajiyar data yi.




Tun da suka nufo ta ta gane shi sai dai bata wani tada hankalin ta ba,shikam maleek be ma lura da ita ba.



Yana faman yiwa abokin shi idris, ajiye kayan yayi domin ta irga, cikin natsuwa ta fara irgawa har ta gama.



Juyowa yayi domin mika mata atm suka hada ido, dogon tsaki yaja sannan ya kalle ta kallon kyama da tsana yace"ke kam akwai mayya uban me kike a kaduna kuma? ",




Matsowa ya kuma yi yace"wane tsohon najadun kike tunanin zai kwashe ki?, wato kin gama dana kano da gombe kin dawo kaduna,to ki sani matukar baki tattara kayan ki kin bar kaduna ba zaki sha mamakin abinda zan yi miki, banza karuwa kawai".



Murmushi tayi tace"sir your balance is 89k",shako ta yayi yace"kada ki kuma yi mini magana idan ba haka ba zan wulakan ta rayuwar ki, banza karuwa".



Manager da sauran mutanen wajen ne suka karaso, cikin sanyin murya manager din yace"sir kayi mata hakuri dan allah baza ta kuma ba",kallon gargadi ya aikawa manager din kan ya sake ta ya juya ya fice.




Ikhlas na ganin ya fita ta koma ta zauna, manager ya fara mata fada,"haba ikhlas muna jin dadin aiki da ke yanzu kuma kina so ki saka wasa a ciki", fada sosai ya kama yi mata wanda ran ta ya bace sosai.




Kuka ta fashe dashi me tsanani,kifa kan ta tayi a table din gaban ta wannan waye yake kokarin dagula mata lissafi"banza karuwa",kalmar da ta rinka yawo a kan ta kenan.


Wani tsanar shi taji a zuciyar ta wato tabar kaduna kamar wani garin uban shi,to bata gano izan unan shi meda kadunar.




Kwankwasa table din idris yayi, dagowa tayi ganin abokin shi ne yasa taja tsaki ta galla mishi harara, kallon ta yake yana murmushi cikin zafin rai tace"lafiya malam? ".


Atm card ya miko mata, fuzgewa tayi sannan ta saka a atm machine din ta cire iya kudin su, sannan ta ajiye mishi ta mike tabar wajen.



Da idanu ya bita yana murmushi, wata abokiyar aikin ta ta kira ita kuma ta bude wata kofa ta shige.



Dariya yayi sannan ya dauki kayan da atm card din ya fice, besa ran maleek zai jira shi ba, haka kuwa be jira shin ba, mai keke napep ya tare sannan ya fada mishi inda za shi.




Yana tafe yana tuno yadda take masifar ta da komai yana burge shi yayi, a hankali ya furta"maleek rigimamme kenan, wato tsabar masifa data rufe mishi idanu be lura da kyan yarinyar ba".



Can kuma yace"to kodai love fight ne? ", mai keke yace"malam magana kake ne", idris yace"a'a cigaba da aikin ka kawai".




Bangren maleek kuwa a zuciye ya bude motar ya fito bayan ya isa gida.



Bintu dake faman mishi magana, cikin fusata ya juyo ya tsinke ta da mari, hajiya tace"kai maleek ka fita ido na tarinyar tawa kake duka, to kuwa baka da mata sai ita".



Cikin fushi yace"idan ke zaki daura auren ba sai ki auren ita na gani ba, me zan yi da wannan abu kamar muciya da zani".



Yana fadin haka ya wuce ya bar ta tsaye tana faman surfa masifa, bangaren shi kawai ya wuce.



Kan gado ya fada yana huci, lallai yarinyar nan zata dagula mishi lissafi dole ya takura ta tabar kaduna ko kuma shi ya bar ta, haka ma za'a yi domin ko matsalar hajiya ta ishe shi.









💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍


*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*


Wattpad @13 deeja

Or
Deeja1love.blogspot.com

*written
-by-
*Deeja one love*



*dedicated
to
*Maryam khamis*


*sis harira aliyu (jinnul aashique) wannan page din na sadaukar dashi gare ki, kiyi yadda kike so dashi*.

Na gode da yadda kike bibiyar littafi na.






33-34



Ita kuwa ikhlas tana shiga, rest room ta fashe da kuka_banza karuwa_wannan kalma ita tafi mata ciwo a rai.




Wajen manager taje ta dauki excuse,domin tafiya gida, shi kam manager ganin abinda ya faru yasa ya barta.




Makarantar su baby ta wuce ta je ta dauke shi sannan ta wuce gida,gaba daya bata da walwala.



Tana zuwa, wanka tayi ta kwanta ta shiga tunani, baby ya turo kofar ya shigo, ganin ta a kwance ya zauna kusa da ita.




Cikin kulawa yace"baby baki da lafiya ne? ", daga mishi kai kawai tayi,bed side drawer ya bude ya dauko sudrex ya miko mata.




Fita yayi babu dadewa ya dawo da ruwa a glass cup, murmushi tayi sannan ta amsa ta sha,gyara mata blanket yayi sannan ya ja mata kofa.




Yana fita tayi murmushi domin yaron allah ya bashi hankali,wayar ta ta fara ringing,a hankali ta janyo wayar.




Cikin nutsuwa take amsar wayar, zaro idanu

Please Login or Register in order to submit comment