Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi tace"zuma na da gaske ranar juma'a zaka dawo kaduna? ".



Yace"princess bazan iya jurar rashin ki bane shiyasa, kawai na ajiye aiki gwara na dawo kaduna na cigaba".




"To yanzu idan ni kuma na koma kano din fa? ", ta fada cikin tsokana.



Cikin sauri yace"kin isa ma, tab aikuwa da nima kano din zan dawo", dariya suka yi gaba daya.



Haka suka cigaba da firar su har ta manta da abinda maleek yayi mata.




Sai yamma sannan ta tashi, wanka kawai tayi ta shirya sannan ta fito parlour, baby dake zaune ya juyo yace"baby wannan wankan fa? ".




Dariya tayi tace"nayi kyau ne", yatsu biyu ya hade mata alamar yayi,cikin farin ciki yace"ko zamu shiga gari ne? ",ya fada yana kashe ido daya.



Gaban ta ya fadi, domin sak yadda baban shi yake yi kenan,ajiyar zuciya tayi tace"shirya muje kaji".




Da sauri ya tashi yaje ya shirya, cikin annashuwa suka fice daga gidan,wajajen shakatawa suka dinga zuwa.




Kowa ya gansu sai yayi tunanin dan data haifa ne, dan mutane da yawa suna son zuwa wajen ta amma ganin baby sai yasa su fasa domin suna tunanin ko tana da miji.



Amma da yawa sukan ce wannan wane kalar wawan miji ne da zai bar mace kamar wannan tana yawo a gari.



Suna parking a fahad stor, baby yace"ah baby ki shiga bari na dawo", kallon shi tayi kamar zata ce wani abu sai ta fasa.



Da sauri ya koma ita kuma ta shiga ciki,sauri yake domin ya dauko tab din shi dan yana so suyi pics da mum din shi.




Yana rufewa shi kuma ya bude kofa, faduwa yayi, jin zafin da yayi yasa yayi kara,cikin sauri na motar ya fito.



Ganin yaro kyakkyawa yasa yayi saurin dago shi,shafa kan shi yayi yace"sannu fa aboki me kake a nan? Ina maman ka da baban ka? ", duka ya jefo mishi tambayar.




Baby ya bi tab din shi da kallo, da sauri shima ya juya yana kallon inda tab din take,"oh gosh! Ya haka?, da sauri ya dauko.



Ganin taci screen yace"aboki sai dai mu shiga ciki a canza ta domin wannan ta sami matsala".


Matse kafada yayi yace"akwai abubuwan da nake so a wannan, beside ma ban san ka ba sai na bika".



Murmushi yayi yace"sunana daddy, muje ciki", yana fadin haka ya rike hannun shi suka shiga.



Ikhlas kuwa ganin ya dade be shigo ba yasa hankalin ta tashi, cikin sauri ta fito domin neman shi.



Ganin baya wajen motar yasa gaban ta ya fadi, a rude take tamabayar mutanen wajen ko sun gan shi.


Dama neman damar suyi mata magana suke nema hakan yasa suka fara mata kwatance, kowa da hanyar da zai nuna mata ya bi.


Cikin tashin hankali ta shiga mota tana bin hanyar da suka gaya mata,wayar da bata gani ba yasa ta gane tana wajen shi hakan yasa ta fara kira, amma iz not reachable.





Cikin tashin hankali ta dawo bakin super market din,clashing suka yi wanda kayan hannun shi sai da suka zube.




Da sauri ta tsuguna domin kwashewa, shoma haka,bayan ta gama ta dago don bashi hakuri,suna hada ido ta daure fuska.




Cikin fusata ya daga hannu ya tsinke ta da mari,hannu ya daga ya nuna ta yace"ni kam na tsane ki wallahi, wai ke wace kalar mayya ce, ki dena bibiya ta haka, banza karuwa kawai, mtsewww", yaja tsaki.




Juyowa tayi ta kalli compound din, kusan kowa harkar gaban shi yake yi,ganin hakan yasa tayi ajiyar zuciya.



Shi kam maleek, hannun baby wanda shi wasa yake da teddyn hannun shi be lura da abinda ya faru ba.



Juyawa tayi ta kalle shi,ganin baby a tare dashi, zaro idanu tayi tana mamakin me ya hadasu.




Cikin fusata ta nufi wajen, finciko shi tayi sannan ta kwace kayan hannun shi ta wurga mishi.




Nuna shi tayi tace"gwara ni a karuwan ci na tsaya bana satar yaran mutane,sannan ka sani kamar yadda ka tsanane ni haka na tsakane ka, banza mata-maza kawai".



Tana gama fadin haka ta ja hannun baby ta bude mota ta saka shi ta tada ta bar wajen, cikin sauri.



Bangaren maleek kuwa tsayawa yayi kawai kamar statue, tabbas yarinyar nan ta fara crossing limit din ta.




Cije lips yayi tunowa da yayi wai "mata-maza",kamar yayi ihu haka ya ji,kallon kayan da ta watsa mishi yayi ya juya a fusace ya bar wajen.



Baby kuwa a mota sai kuka yake yi, ganin ba zai yi shiru bane yasa ta tsayar da motar tace"kayi mini shiru ko na wanka mari, wawa wanda baya kishin mum din sa".



Shuru yayi yana ajiyar zuciya, ita kuma a fusace ta tada motar ta bar wajen.




Tana zuwa gida tayi parking, ko kula shi bata yi ba ta fice daga motar,bedroom din ta ta wuce kawai ta haye kan bed din ta.




Cikin sanyin jiki ya shigo dakin,tunda ta dago ta kalle shi ta maida kan ta,ajiye key din motar yayi ya hayo kan bed din.





Juya fuskar ta tayi,a hankali ya rungume ta yace"mummy kiyi hakuri kinji, bazan kuma zuwa wajen wani wanda ban sani ba".




Banza tayi dashi, hakan yasa ya fara kuka, jin kukan ahi yasa tayi saurin mikewa, ta kalle shi tace"baby kayi shiru kaji komai ya wuce".




Kan shi ya dora akan kafar ta yace"mummy kece kika ki kula ni",shafa kan shi tayi tace"ya wuce yanzu muje muyi girki".




Da sauri suka mike suka nufi kitchen din hannun su sarke da juna, indomie suka dafa sannan suka dawo parlour suka ci kamar babu abinda ya faru.





Bangaren maleek kuwa a fusace ya isa gida, bangaren mummy ya shiga tun daga parlour yake kwala mata kira.





Cikin sauri ta fito, rungume ta yayi yana fadin"Mummy a yau an yi disgracing dina", da sauri tace"subhanallah! Waye wannan? ".



"Wata yarinya ce", da mamaki tace"maleek mace fa kace?, haba dai yanzu ai bana tunanin akwai macen da zata wulakanta ka, kodai kai kayi mata laifi?".




Shafa kai yayi yace"mummy yaron ta na taba shine fa ta wulakanta ni",kallon shi tayi tace"tashi ka bani waje maleek, matar aure kuma? ",.



Cuno baki yayi yace"mummy bafa tada aure",murmushi tayi tace"oh! Dama kasan ta kenan",da sauri yace"a'a mummy, ni yau na taba ganin ta",dariya kawai mummy tayi.








Ikhlas ke zaune bayan sallar isha'i baby kwance kan kafar ta yana barci, wayar ta ta fara ringing.



Dubawa tay, ganin nabeelert yasa ta daga, cikin farin ciki tace"baby ya dai? ".




"Dole zaki fadi haka mana, tunda kin koma yar kaduna, kin manta damu ko?,ko dan kiran nan bakiyi".




"Haba dai beelert ba haka bane, wallahi kin san yanayin aikin mu,babu hutu sosai da sosai yadda ya kamata, to yanzu ya su hafsat da feenert".




"Feenert nacan gidan su, hafsat kuwa gata nan, nima gobe nake son shiga gombe, domin naga ya harkokin can yake tafiya".




"Hakan yayi amma ki bari, sai next week domin bana so a sami matsala, kin san idan bamu gama da wancan dan iskan ba akwai matsala".




"Kamar ya fa?,kin san da bukatar naje can din ko, saboda meetings din da za'ayi".



"Kada ki damu zan kira asp abdallah sai ya je can din, kin san dai company din ki babba ne, yan jarida zasu iya bukatar fira da CEO na company din, kin ga kuma kabeer a garin yake".



"Hakane kuma,shikenan zan hakura din idan yaso mext week din sai na je".




"Ai kada ki damu beelert, amma zuwan ki gombe ki hakura ba yanzu ba, na fiso ki bari idan kabeer yazo kaduna sai ki je can".



"Hmm, hakane kuma, yaushe zamu zo kadunan? ".




"Nan da two week, insha allah,idan kun zo sai kuji plans din, sannan zan kira asp abdallah na gaya mishi".




"Shikenan, ki shafa mini kan baby",daga haka suka rabu.



Tana ajiye wayar wani kiran ya shigo, cikin farin ciki ta daga.




"Assalamu alaikum, zuma na",ajiyar zuciya yayi kafin yace"wa'alaikumus salam, princess har na kosa gobe tayi na dawo wallahi".




Dariya tayi tace"kada ka damu zuma na,insha allah da yau da gobe duka daya ne",haka suka cigaba da firar su cikin nishadi kafin suyi sallama.





Maleek ya kalli yayan shi yace"lallai na yarda princess ta murza kambun ta, babu yadda mummy bata yi ba akan ka dawo kaduna kaki amma yau a dalilin princess ka dawo".





Yace"kasan me yasa bana son dawo wa garin nan da zama, na farko matsalar mummy da zata dame ni akan na fito da mata, na biyu kuma wannan rigimammiyar hajiyar".




Jin ya ambaci hajiya yasa ya ja tsaki,hannhn shi saifullahi ya rike yace"ka tashi ka shirya muje wajen princess yau".




Maleek ya gyara kwanciyar shi yace"lovely na gaji sosai, sannan ina tsoron na fita yanzu a kaduna wallahi, saboda ina fita nake haduwa da wannan karuwar".




Dariya saifullahi yayi yace"haba dai kamar wata aljana, kun hadu a kano kaje gombe kun hadu yanzu ma a kd kace zaku hadu? ".




Tabe baki yayi yace"wallahi kamar ka sani, shiyasa ni yanzu tsoron fita nake, dan na tsani ganin ta wallahi".




Daga kafada yayi yace"shikenan next time kaje, amma yanzu tashi ka raka ni wajen mummy".




Hannun su sarke da juna suka fito daga bangaren su.




A palour kamar yadda suka saba, su uku ne a ciki, zaman dai da maleek ya sa mishi zaman sa ido.




Kusa da ita saifullahi ya karasa yace"ina wuni hajiya", da fara'a ta amsa, sadiya kuwa sai murna take.




Bintu kuwa jiki na rawa ta fara gaishe da maleek,hajiya rabi ta ja tsaki tace"wahalalliya ga wanda ya gaishe da uwar ki baki gaishe shi ba, amma jiki na rawa kina gaishe da wanda ko kallo ban ishe shi".




Murmushi yayi ha kama hannun saifullahi yace"haba lovely ai sai ka gaya mini hajiya na wajen", juyawa yayi ya kalle ta yace"yi hakuri hajiya ban lura dake a wajen ba, sannu da hutawa".



Yana fadin haka ya ja hannun saifullahi suka wuce,hajiya rabi kuwa ta dasa masifa, dariya yayi domin ya san yau sai Allah.



Suna shiga wajen mummy ta taso da farin ciki,rungume su ta yi tace"yaishe rabon da na gan ku a haka".



Cikin jin dadi saifullahi yace"to mummy ya zamu yi,kai da gidan uban ka wai amma tsoron zuwa kake".



Mummy ta harare shi tace"rife mini baki, kai ma zama da wannan yasa ka fara koyan wannan halin ko? ", ta fada tana nuna maleek.



Maleek yayi dariya yace"kai mummy waro ni na koya mishi ma kenan? ",kallon su tayi tace"sai ina kuma? ".



Saifullahi ya sosa kai yace"mummy wajen wani aboki na zani",juyawa tayi ta kalli maleek tace"kai fa? ".



A shagwabe yace"mummy bani da wajen zauwa da ya wuce wajen ki", ya karasa yana dora kan shi a kafadar ta.



Ture shi tayi tace"dalla matsa ka bani guri, ka girma baka san ka girma ba, ka wice ka shiga gari ka nemo mini queen din har yanzu ya gagara".



Juyowa tayi ta kalli saifullahi tace"yauwa, ina princess din ma da akace tana kaduna, sai yaushe za'a kawo mini ita? ".



Kallon maleek yayi yace"kai kam ba'a sirri da kai wallahi har ka wani zo ka gaya",dariya yayi yace"to mummy ta tsare ni da tambaya ba dole na fada ba, kin san me ma mummy, yanzu ma wajen ta zai je".



Da sauri yace"amma dai kai.... ", ya juya ya fice da sauri, dariya suka yi gaba daya, mummy ta daga murya tace"ka gaishe ta".



Kara kwashe wa suka yi da dariya, kallon maleek ta yi ta galla mishi harara tace"wawa, ai ya fika tun da shi ya yunkunro".



Gyara zama yayi yace"wato mummy idan kika ga queen di ta ko, kyakkyawa ce, gata da hanci,kin ga idanun ta zabba'u",mikewa tayi shima ya mike ya bita yana zuba mata surutu a tare suka nufi bedroom din ta.





*~khadeeja ahmad (deeja one love)~*๐Ÿ˜˜








๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

โœโœโœโœโœโœโœ
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
โœโœโœโœโœโœโœ


*~โ„We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*


Wattpad @13 deeja

Or
Deeja1love.blogspot.com

*written
-by-
*Deeja one love*



*dedicated
to
*Maryam khamis*



*sis deejency i dash you this page saboda kin cancanci fiye da haka, kuma na gode da sadaukar mini da daya daga pages na novel din ki TAGAYYARA nida group dina muna godiya, love you irin sosai din nan*.



Amatul mannan where are you ne, haka ki boye da yawa anya lafiya kuwa?,


_Sis shamsiyya m magaji thanks for your support_.




35-36


Yau beleerh da feenerh da hafsat suka shigo garin kaduna,asp abdallah sai gobe domin yana da ayyuka da yawa.




Cikin farin ciki suka tari juna,hafsat ta zauna tace"cat eyes kina hutawar ki".




Ikhlas tayi murmushi, kitchen ta shiga ta dauko duk abinda da ta shirya musu domin kuwa sun riga da sunyi waya kan su iso hakan yasa ta tanada musu abin dasu ci before su karaso.




Beelerh tace"kai sis wannan irin girki haka",dariya feenerh tayi tace"wallahi kin cika santi da yawa".




Suna ci suna firar yaushe gamo, a haka har suka gama.




Tare da feenerh suka je suka dauko baby daga makaranta.



Yamma nayi suka fito domin shakatawa,peach palace suka yada zango.



Ikhlas tace"ni dai bazan iya zama babu wani abun da zai sani nishadi ba, bari na siyo ice cream".



Hafsat tace"ke kam kina nan da halin ki, wai kuwa zaki girma kuwa?", beelert ta amshe da"banga alama ba, kullum shan zaki da sanyi kamar yarinya, idan kuma baby yayi ta hana shi".



Juyawa tayi ta kalli baby, harkar shi kawai yake yi, maida kallon ta tayi kan beelert ta galla mata harara sannan ta wuce.




Hango shi tayi ya juya baya, da alamu magana suke yi da na kusa dashi tsaki taja ta murguda baki.



Kamar ance ya waigo suka hada ido,hade rai yayi ya kauda kan shi,agogon hannun shi ya kalla, lovely ya shanya shi, gashi wacce yake gudun su hadu sai da suka hadu.




Ikhlas kuwa ice cream din ta ta siya,ta gefen shi tazo wuce wa, kafa ya saka mata wanda ta kusa faduwa, sanin cewa shi yasa mata kafa yasa ta karkatar da robar ice cream din zuwa jikin shi.



Aikuwa ya zubar mishi, wata irin zabura yayi ya mike,kallon kasan ido ta bishi dashi, kasa cewa komai yayi.




Murmushi tayi irin na cin nasara tace"am sorry gaba ka dinga lura ina zaka saka kafar ka, koda yake kamar masaki haka nake gani ko?".



Dan duban shi tayi kafin ta bude purse din ta ta ciro 3k ta mika mishi, kallon rainin wayo ta mishi tace"gashi ka wanke kayan sauran canji kuma ka rike, charity".



Kasa motsi yayi har ta janyo hannun shi ta saka mishi kudin sannan ta juya ta tafi, da karfi ya bugi table na gaban shi.



Hanyar da tabi ya bi domin baya jin zai iya hakuri da wannan disgracing din shi da tayi.


Ikhlas na zaune kawai suka ga mutum akan su, da sauri suka fara fadin "lapiya malam kazo ka tsaya mana a kai".


Be ce komai ba sai ikhlas da yake bi da kallon tsana,murmushi take ita kuwa mai kayatarwa,kallon su tayi tace"muje kawai".



Har ta juya ya finciko ta, fuskar ta ya kalla yace"tunda har kika bani charity to i promise you that i will make sure i make your life miserable",yana fadin haka ya hankade ta ya fice da sauri.




Baby ne ya fara kwala mishi kira, cak ya tsaya ya juyo ya zuba mishi idanu, shima kallon shi a yake yi, a hankali ya bude mishi hannu alamun ya taho.



Da gudu baby ya nufe shi ya rungume shi, jan hannun shi yayi suka fice ko kallon ta be yi ba.



Motar su tabi da kallo tana kara maimaita sunan da baby ya kira shi"*daddy*"jinjina kai tayi tana huci tace"aikin banza".



Tun a mota suke so su tambaye ta waye wannan amma sun kasa, can dai feenerh tayi karfin halin cewa"waye wannan ne ikhlas".



Huci tayi tace"wani kwarto ne, ya bibiye ni naki yarda shine yake bina duk inda naje,kuma fa mata-maza ne".



Duk yadda suka daure sai da suka yi dariya,hafsat tace"ikhlas kin san me kike cewa kuwa*maleek muhammad NGM*kike fadawa haka.




Zaro idanu beelerh tayi tace"hafsat da gaske wannan shine? ",daga kai hafsat tayi tace"eh mana ance yana da yaya sai dai ban san shi ba, shima wannan dalilin d'an ogan daddy na ya san shi domin abokai ne".



Feenerh tace"waye be san mahaifin shi ba, tab lallai ma, to ke meye hadin ki da wannan".



Cike da jin haushi tace"ubana ne, ko zaki hana uba zuwa wajen 'yar shi ne", rike haba feenerh tayi tace"Allah ya baki hakuri", daga haka babu wanda ya kuma magana har suka isa gida.




Ko a gida bata da wata walwala,hafsat tace"nifa na lura da cat eyes wannan na daban ne".



Kallon meye tayi mata, hafsat ta cigaba da cewa"ban taba ganin wanda yayi miki abu kin fusata har fuskar ki ta nuna ba sai wannan".




Iska ta furzar tace"wallahi nima ban san me yasa bana iya jure abinda yake mini, ta hanyar rashin nuna wa a fuska".




Feenerh tace"to yanzu dai muyi abinda ya kawo mu",beelert tace"kada ki damu, ai sai anjima zai iso, yana dai hanya".





Ikhlas tace"to asp abdallah fa?naga ya kamata ace ya iso".




Hafsat tace"hakane but ai yace zai fara sauka a diamond hotel, may be yana can".


Sai bayan magrib, baby ya shigo, yadda yayi tunanin zata yi mishi fada kuma sai ba haka ba, ikhlas kuwa yi tayi kamar bata san komai ba.



Dan taji lokacin da motar ta ajiye shi kuma ta tabbata shine ya kawo shi, kayan daya kawo kuwa ko kallon su bata yi ba.



Baby tace wa"ka kwashe kayan nan before ka tunzuro ni nayi maka abinda baka shirya ba", sanin halin ta yasa ya dauke domin zata iya aikata abinda tace.

Karfe tara na dare, kabeer ya iso garin kaduna, ikhlas ita ta tare shi, kamar yadda beelert dama hoton ikhlas din take tura mishi.




Da idanu yake bin ta dashi domin gani yake a fili tafi kyau, sai faman lashe lips yake kamar maye.



Dama ta riga da tayi booking room, dan haka direct suite hotel suka wuce.




Dai dai shiga, idanun ta ya sauka a nashi, wanda tare suke da wannan abokin nashi da ta gan su a gombe, murmushi me kayatarwa ta aika mishi, sannan ta ciza lip din ta na kasa ta suka wuce.




Suna wucewa maleek ya ja tsaki, sudeis ya kalle shi yace"lafiya dai aboki na? ".



Ajiyar zuciya yayi yace"abinda bana son gani shi na gani".



Jinjina kai sudeis yayi yace"to yanzu dai muje kawai dan na gaji ina so na huta".


Harara ya galla mishi yace"duk ba kai ka ja mini ba,ka wani zo ka kama daki, kasa ina haduwa sa karuwa".



Dariya sudeis yayi yace"wai maleek me yasa kake damuwa da ita ne?",harara ya kuma galla mishi sannan yace"zaka tafi ko kuma nayi tafiya ta".




Da sauri ya bishi dan yasan halin shi, kuma baya so ya tafin, ko a mota haka yayi ta jan tsaki, shi dai sudeis bece mishi komai ba.




Bangaren ikhlas kuwa suna shiga, ya kalle ta yace"baby wallahi a fili kin fi kyau, har na kosa".



Dariya tayi wacce ta kara tafiya da imanin shi tace"kada ka damu, in sha allah yau ni taka ce, yanzu dai ga drinks ka sha, bari na shirya".



Dariya yayi irin ta yan duniya yace"ina jiran ki baby",bathroom ta shige, shi kuma ya dauki juice ya cigaba da sha........





*afuwan da kwana biyu kuka jini shiru,wa'inda suke ta cigiya ta na gode sosai, wallahi ina lafiya, babu abinda ya faru, kawai na shiga makaranta ne, na gode sosai da sosai nasan kun damu dani da messages sai da na gaji da budewa na tambayar lafiya ta, am very happy for dat nasan cewa da wanda suka damu dani thanks alot.*



Deejerh one love๐Ÿ˜˜






๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)



https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

โœโœโœโœโœโœโœ
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
โœโœโœโœโœโœโœ


*~โ„We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*


Wattpad @13 deeja

Or
Deeja1love.blogspot.com

*written
-by-
*Deeja one love*



*dedicated*
to
*Maryam khamis*




*Feenerh(matar soja) wannan ma naki ne aunty wallahi haka kawai Allah ya dora mini sonki idan zan sadaukar miki da duk littattafan dana rubuta da wanda zan rubuta ba zai kai matsayin son da nake miki a zuciya ta ba, nasan wannan daga Allah ne bazan iya kwatanta miki yadda nake jin ki a raina ba*




37-38





Bata jima ba ta fito, a zaune ta same shi tunda ta fito ya zuba mata idanu kamar zai cinye ta.




Murmushi tayi wanda ya kasa jurewa ya taso, hadata da bango yayi, yana kokarin hade bakin su ta soka mishi allurar hannun ta a wuya.



"Ashhhhhh"ya furta daga nan ya zube, wanda yayi dai-dai da kwankwasa kofar, cikin sauri ta bude.




Tana budewa suka hada ido da asp abdallah, jinjina yayi mata da hannu๐Ÿ‘ sannan ta basu hanya suka wuce.




Sai bayan minti goma sha biyar ya dawo hayyacin shi, cikin tsananin mamaki yake bin su da kallo.



Idanun shi ya tsayar a kan ta, cikin sauri yace"nafeesert, kece",kallon tsana ta aika mishi tace"ba haka ka so ba ko kaso na mutu ko rayuwa ta ta wulakance ko? ".



Sunkuyar da kai yayi,kallon shi asp abdallah yayi yace"yanzu babu bata lokaci zamu yi aikin daya dace damu".



Kallon shi kabeer yayi yace"ina ji",asp abdallah yayi murmushi yace"zaka saka hannu farko a wannan takardar", mika mishi yayi.



Cikin sauri ya amsa ya yi signing akai,"yanzu kasan me sa hannun ka yake nufi? ",girgiza kai yayi.



Asp abdallah yace"to abinda yake nufi shine yarjejeniya kayi akan zaka dinga zuwa kana duba yar ka, sannan kuma zaka dauki dawainiyar ta, haka kuma idan lokaci yayi da zata yi aure zaka dauke yarinyar ka".



Jin hakan sai da feenert ta kalle shi,kabeer yace"na yarda da hakan", tabe baki asp abdallah yayi yace"idan ma baka yarda ba to zamu maka ka kotu".





Kabeer cikin sauri yace"wallahi na yarda zan dinga zuwa",abdallah ya kuma cewa"wannan kuma ya rage naka, yanzu sai kaje ka gayawa iyayen ka".



Daga haka duka suka fice daga dakin,asp abdallah ya dawo, kallon shi yayi yace"and idan kayi yinkurin guduwa zaka yi dana sani wanda baza ka taba mantawa a rayuwar ka ba".




Daga haka ya juya ya fice,shi ya ja su a motar, gidan ikhlas suka wuce, sai da ya ajiye su sannan ya wuce nashi masaukin.




Beelerh tace"ni fa ban ganewa asp ba gaba daya kinga wani daure fuska da take yi".



Ikhlas da ta shigo bayan taje ta dubo baby tace"nima haka nake gani, sai wani daure fuska yake yi anya kuwa babu komai a kasa".




Feenert tace"ku dai kuka sani,kun cika saka ido",beelerh tace"in tayi wari zamu ji ai",ikhlas kam dariya take, ita kuwa feenerh murmushi kawai tayi, hafsat kuwa bata kula su ba.




Washe gari suka wuce kano, domin cigaba da aiki,hafsat kuwa abuja ta wuce wajen baban ta, asp abdallah ne ya kai su kano daga nan ya wuce.



sun tafi sun bar ikhlas da kewa, yau ta shirya domin wucewa wajen aiki.




Ta sauke baby a makaranta motar ta tayu faci, wani haushi ne yazo mata rai,number din saifullahi ta fara gwadawa amma yaki zuwa.



Tsaye tayi a bakin titi, gashi abin hawa yana wuya domin ranar monday ne, kowa yasan yadda ranar monday take kasancewa.



Duk motar da zata tsayar a cike take,ga lokacin sai kurewa yake yi.



Maleek da tun da ya

Please Login or Register in order to submit comment