Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu dadi",iman tace"ki bari gobe sai mu tambaye shi tukuanna sannan mu tafi kin San hali dai".




Ikhlas tace"ke kuma matsoraciya dai kawai",haka suka gama abin da suke yi sannan suka wkwanta.



Sai bayan la'asar ya dawo,a zaune ya same su a tsakar gida, ikhlas na jajjage,ita kuma iman tana hada wuta, gwaggo kuma ta fita makwabta.



Sannu da zuwa suka yi mishi,kallon ikhlas yayi yace"beauty zo kinji",Dan murmushi tayi kafin tace"yaya girkin fa?",hade rai yayi yace"yau ku bar girkin mana".daga kafada tayi alamar ok.



Hannun ta yaja yayi waje da ita,murfin motar ya bude ya saka a ciki,bece da ita komai ba yaja ya fara tafiya,ganin haka itama taja bakin ta tayi shiru.




Wani k'ayataccen wajen shakatawa ya kaita,bayan sun zauna ya kalle ta yace"beauty gaya mini gaskiya me yasa kike sons?",sunkuyar da kai tayi bata ce komai ba.



Can tayi murmushi tace"nima yaya bansaniba nidai naji kawai ina sonka ne",murmushi yayi yace"ni kuma ina sonki ne saboda kina da yawan kula da addini sannan kina da duk abinda nake son matata ta kasance tana dashi",haka dai suka cigaba da firar su ta masoya kafin yamma tayi.





A shahara restaurant yayi musu take away,suna komawa tayi alwala tayi sallah sannan suka zauna zaman cin abinci.







๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)



*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~โ„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*


Wattpad @13 deeja

Or
Deeja1love.blogspot.com

*written
-by-
*Deeja one love*



*dedicated
to
*Maryam khamis*

15-16


Washe gari da wuri suka tashi sai sa suka gama ayyukan su sannan suka shirya domin zuwa saloon.



Gidan su Islam suka biya sannan suka wuce,abin ka da me gashi na ikhlas yafi ba kowa yin kyau, sai da aka gyara musu farce sannan suka taho.



Suna dawowa gida suka yi sallah,sun daura girkin dare kenan Abba kabiru yayi sallama,gaishe dashi suka yi sannan suka cigaba da aikin su.




Yaya sadik yayi sallama ya shigo,dakin gwaggo ya shiga,ya jima kadan sannan gwaggo ta kwala musu kira.



Cikin sauri suka shiga,waje suka samu suka zauna,Dan da alamu maganar tana da mahimmmanci.



Abba kabiru ya fara magana"alhamdulillahi yanzu kun gama secondary school, kuma ku kunsan cewa amana ce agareni ku,Dan haka duk wani nauyi naku ina kokari wajen ganin ba sauke shi,Dan haka jiya sadik yazo mini da maganar yana so ya auri ikhlas domin sun shirya kan su".



Numfasawa yayi sannan ya ci gaba"to a lokacin nace mishi ya bari nazo mu zanta da gwaggo,sai dai zuwa yanzu take nuna mini da cewa auren ka da ikhlas ba abu bane mai yiwuwa,domin iyayenka tun suna da rai suke da burin hada auren ku kai da yar uwar ka iman",shiru ya ratsa dakin.


Gwaggo ta gyara murya kafin tace"to sadik mun ji wane sako ka aiko dashi,sai dai ka sani ba wai mun ki abinda kazo mana dashi bane,sai dai mun yi farin ciki da hakan, amma wannan abin wasiyyar iyayen ka ne ina kuma fatan ka fahimce mu,kuma ba zaka saba umarnin da iyayen ka suka yi ba".




Sadik ya dubi gwaggo yace"insha Allah gwaggo na hakura da ikhlas,zan rike yar uwata da amana, Allah yasa hakan shi yafi alkhairi(samari nawa da yan mata nawa ke wannan tunanin,da zaharar ance ai ga Wanda ake so ta aura abinda zai zo ranta a farko shine ai a littafin wata marubuciya ba karanta star din da za'a mata auren dole guduwa tayi,to shikenan jeki da kanki zaki gane kinyi kuskure wallahi, ko kema kina tunanin wa'inda marubuciyar ta rubuta sun taimaki star din kema zaki hadu dasu ne???)allah yasa mu dace, ameen.





Kowa yayi farin ciki da abinda ya fara,Abba kabiru yace"ikhlas kada kiji wai mun nuna miki banbanci,a'a kema 'yar muce kinji,Allah ya baki nagari Wanda zai kula dake,sannan jarabawar ku ba fitowa zan nema miki admission ki cigaba da karatu har zuwa lokacin da Allah zai fito miki da naki mijin".




Kan ta na kasa ba zaka shaida ya yanayin ta yake ba tace"babu komai Abba wallahi ban dauke ku da komai ba sai iyaye,ai kun yi kokari ma tun da gashi wacce ta haife ni ma ta tafi ta barin",ta karashe maganar hawaye ja zubo mata.



Abba kabiru yace"kayya meya kawo haka kuma haba juwairiyya da bakin ki kike fadin haka ne,kamar baki yi karatu ba,kin manta kowa da kaddarar shi ne,kada ki manta ke musulma ce",nan dai suka musu nasiha sannan suka sallame su.




Abba kabiru da gwaggo su suka tsara cewa nanda wata biyu za'a daura auren,sannan ya tafi.




Ikhlas zaune ita da iman,sadik yayi sallama ya shigo,kallon juna suka tsaya yi kafin ta janye nata idanun,kusa da ita ya tsugunna.




Iman tace"sannu da zuwa yaya",be kalle ta ba yace"yauwa iman,zubo mini abinci ki saka spoon biyu",amsawa tayi da to,sannan ta fita.





A hankali ya kira sunan ta,kasa dago idanun ta tayi, hannu yasa ya dago fuskar ta,idanun ta yayi ja alamun tana so tayi kuka.




Cikin sanyin murya yace"ikhlas kiyi hakuri da hukuncin da iyaye ba suka yanke domin basu yi mana adal.....,da sauri ta rufe bakin shi tana girgiza kai,hawaye ba zubowa daga idanun ta.




Kasa rarrashin ta yayi domin ko shi yana bukatar me rarrashin shi,shiru dakin yayi an rasa mai yin magana.sautin kukan ikhlas Kawai ke tashi.




A hankali ya fara ajiyar zuciya, dago fuskar ya yayi, idanunta a rufe suke amma Da alamun baby barci take yi ba.



Dagowa tayi sannan tayi murmushi face"angon iman kenan, kuma ka sani na baka amanar ta idan ka bata Mata rai zan zo har gida na ja kunnen ka kamar haka", hannu tasa a kunnen shirt ta ja kadan.




Kara yayi yana rike hannun ta, dariya suka yi gaba data, gwaggo dake zaune a waje tayi murmushi, domin tunanin ta ikhlas zata kullace su.




Sai daya tabbatar da bata da wata damuwa sannan ya fita.



Da dare tana kwance, Iman ta shigo, kusa Da ita taje ta zauna.



A sanyaye race"kiyi hakuri Da abinda ya faru wallahi bawai Abba kabiru da gwaggo sun gayi haka bane Dan wai basa son ki ba a'a sunyi hakane domin cika umarnin iyayen mu".



Dafa ta ikhlas tayi tace"kada ki damu Iman dani dake duka daya ne..... Sannan Abu daya ne zai sa na damu shine idan ya kasance baku son junan ku, but alhamdulillahi nasan kuna son junan ku to dan me zan damu? ".




Zaro idanu Iman tayi tace"waye ya gaya miki haka ikhlas?ni bana son yaya sadik haka shima kowa yasan ke yake so",murmushi ikhlas tayi tace"Iman kada ki manta idan har na tsaya fira da yaya sadik kwana kike kina fushi dani meye wannan?ko kin dauka bansan lokacin da kike kwana kina kuka bane?har fa leken mu kike yi idan muna waje shima ba so bane? ", murmushi kawai Iman tayi.





Yau suka dubo exams din su kuma alhamdulillah duka sun ci.



A yau saura sati daya bikin sadik da iman, iklas da islam sune kirjin biki duk wata kawar su da suka yi makaranta tare sai da suka kai mata cewing gum.



Da dare bayan sun raka islam gida, a hanya iman ta dubi ikhlas tace"sis kin san me nake tunani?"ikhlas ta girgiza kai,islam ta numfasa tace"mai zai hana mu auri yaya sadik duka mu biyu? "Ikhlas da tunda ta fara magana ta zuba mata idanu tana gama fadin haka ikhlas tayi ajiyar zuciya ta fara tafiya.



A haka islam ta cigaba da binta tana mata maganar, ikhlas kam bata ce komai ba har suka je gida.




Washe gari da wuri suka tashi domin cigaba da abinda ya kamata.




Sai da suka yi wanka sannan suka cigaba da shiry-shirye, da yamma yaya sadik ya kira islam, ikhlas ji tayi wani abu ya tokare mata kirji, kokarin dannewa take amma duk da haka sai da hawaye ya zubo mata.




Islam dake gefe tana danna wayar gwaggo tace"wai ke me yake damunki ne haka ina tuni kin hakura da yaya sadik ne?"yake tayi tace"eh mana sai dai kin san a hankali zan dena son shi ko? ", jinjina kai kawai tayi.



Islam tayi sallama suka amsa mata tace"ku tashi muje yaya na kiran ku, da kamar ikhlas tace bazata je ba sai taga rashin dacewar haka.




Yana tsaye shida hafeez sai wani abokin shi wanda suka yi karatu tare,bayan sun gaishe su, dayan yace"to yan mata me dame kuke bukata? ", itadai ikhlas bata ce komai ba,islam ce me lissafawa, haka suka basu sannan suka tafi.



Ana gobe biki,suka je saloon bayan an gama musu aka kuma yi musu lalle,yayi kyau sosai.



Sai yamma suka dawo, sosai lallen ya burge gwaggo da sauran tsiraren yan uwa na nesa da suka zo.



Daddare islam tace"ikhlas har yanzu baki bani amsar magana ta ba?", ikhlas tace"me kenan fa? ", islam tayi murmushi tace"nace ki yarda mu auri yaya sadik tare mana", dariya suka kwashe dashi wanda ya kular da iman.




Islam tace"lallai baki da hankali iman kina ganin dan kun taso tare shine zai sa baza kuyi kishi ba to wallahi irin wannan ma yafi zafi sosai ke kima dena kawai kada wani yaji", cikin dariya ikhlas tace"gaya mata dai wallahi.




Bayan an sauko daga massalacin juma'a aka daura auren *iman mustafa ibrahim azare*tare da *abubakar mustapha ibrahim azare* alhamdullillah daurin aure yayi jama'a sosai.





Suna zaune a daki suka ji guda alamun an daura, nan fa gida ya kacame wanda sai kayi mamakin cikarsa idan kayi la'akari da rashin yawan familyn.






Da yamma bayan sun shirya tafiya da amarya nan tace bata san wannan maganar ba, domin kamkame ikhlas tayi suna kuka, da kyar aka raba su, gwaggo da kanta ta saka ta a motar sadik yaja suka tafi.





A ranar kam ikhlas ji take kamar ta rabu da wani bangare na rayuwar ta, tun suna yara suke tare yau gashi aure ya dauke daya ya bar daya(ni dai nace auren kenan ikhlas๐Ÿ˜ shi yasa ake cewa aure yakin mata).





Haka taron biki ya watse alhamdullillah komai ya tafi lafiya lau, sai dai fatan zaman lafiya tsakanin ango da amarya.




Sati uku da biki aka fara sakin admission,ikhlas fatan ta kullum shine allah ya taimake ta abba kabiru ya cika alkawarin daya dauka na sama mata admission.




Yau tunda ta tashi ta gama abinda take yi, wanka tayi sannan ta zauna ta tsantsara kwalliya ta gani ta fada, wata doguwar riga ta material ta saka kalar dark blue,veil da takalmin data saka kuma light pink, tayi kyau sosai.




Gwaggo ta zaune tana kallon ta sai da ta gama ta juyo tace"ya dai nayi kyau gwaggo? ", dariya gwaggo tayi tace"wallahi ikhlas kin rainani da yawa", itama dariyar tayi tace"gwaggo kika sani ko yau na samo miki miji", rike haba tayi tace"ikon allah to allah yasa hakan ta faru, kema ki tafi ko na huta", hade rai tayi tace"ai ko zanyi aure tare dake zan tafi", gwaggo tace"ke dallah matsa ki bani waje da yake a garin gaba-gaba muke ko"?



Daga gira daya tayi tace"eh mana my sweet gwaggo", dauko carbi tayi wanda yasa ikhlas fita da sauri tana dariya,daga murya tayi tace"na tafi gidan abba kabiru daga can zamu wuce gidan iman",daga haka ta karasa fita.



Gwaggo tayi murmushi ita hankalin ikhlas na burgeta duk da tasan anyi mata ba dai-dai ba amma duk da haka bata nuna ba, da iman ce kuwa da har yanzu tana nan tana nurkufancin tsiya.




Cikin natsuwa take tafiya har ta karasa gidan,duk da irin samarin dake binta amma hakan be dame ta ba.



A bakin get ta tarar da yaya sadik da yaya hafeez, duka idanu suka zuba mata har ta karaso inda suke, a cikin nutsuwa ta gaishe su,sannan ta wuce.



Ajiyar zuciya duka sukayi, kallon juna suka yi kuma sukayi murmushi, hafeez yace"bro bari naje kai ka fara yin gaba domin nidai may be rabona yana nan"yi yayi kamar be ji me yace ba, yaja mota ya tafi.





Hafeez yayi murmushi sannan ya shige gidan, a falo ya same su da islam sai faman fada take yi, ikhlas tace"wallahi da nasan baki shirya ba babu abinda zai sa na biyo tanan", islam tace"mara mutunci yanzu ma zaki iya tafiya kuma wallahi ta zama haramiyar ki",da alamun tambaya ikhlas tace"me kenan? ", islam ta mike tace"bani minti biyu na shirya sai na fito mu tafi.



bata jima ba ta fito, hafeez dake parking lot ya dube su yace"yan mata sai ina? ", islam tace"gidan amarya zamu je", kallon ikhlas yayi yace"to kuzo muje na kaiku", babu musu suka shiga.




Ikhlas na gaba, islam na baya,ita dai ikhlas gaba daya sai a hankali take ji domin yanayin kallon da hafeez ke mata na kurulla kamar wani maye, yanzun ma dago idanu tayi suka hada, harara ta aika mishi sannan ta murguda baki, besan lokacin da dariya ta kufce mishi ba.



State lowcost gidan yake, gidana ya hadu sosai da sosai, suna parking ikhlas ta bude murfin ta fita da gudu tana kwallawa islam kira.




Tana bude kofa suka hade,rungume juna sukayi suna murna sosai, nan suka baje, islam ta dubi iman tace"ah lallai yarinya aure ya amshe ki irin wannan ja haka kin wani kara kumatu", dariya sukayi gaba daya.



Iman tace"ba wani nan bayan sai yau kuka wani zo mini wai tunda aka kawo ni sai yau ai wallahi kun kyauta, tun washe gari nake sa ran zuwan ku amma shiru", dariya suka yi kafin ikhlas tace"to sannu so kike muyi ta zuwa gidan har yaya sadik ya gaji ya kore mu".



Turo baki tayi tace "wallahi kuwa da sai dai mu tafi tare", dariya sukayi islam tace"kai albshirin ku", a tare suka ce"me ya faru? ", kwalin waya ta ciro guda uku.



Kamewa suka yi kamar statue kafin ikhlas ta kai mata duka tace"wallahi bakida kirki mu taho tare amma kika kasa gaya mini", islam tayi dariya tace"to ko ni tawa ban yi amfani da ita ba so nayi dama sai mun hadu kowa sai ya dauki wacce yake so.



Infinix not 5 ikhlas dama light purple ta dauka, islam kuwa light light blue, iman kuma light pink, sai murna suke yi.



Nan suka wuni har sadik ya dawo, cikin murna iman ta tafi da gudu ta rungume shi tana nuna mishi wayar, amsa yayi yace"baby waye ya baki wannan?, dariya tayi tace"abba ya aiko mana da ni da ikhlas da islam", jinjina kai kawai yayi sannan ya rike hannun ta suka shige ciki.




Wajen minti talatin sannan suka fito ya canza kaya daga suit daya shigo dashi zuwa jeans da t shirt.



Zama yayi sannan ya daure fuska yace"ba naji cewa an baku waya ba saura rawar kai ya karu barin ma ke ikhy dan nasan ki da rawar kan samari, kema islam ki kiyaye tam.



Babu wanda yace komai har ya gama,sai bayan isha sannan yace su tashi ya kaisu gida, ikhlas tace"yaya daka barshi dama yaya hafeez yace zai zo ya kai...... ", kasa karasawa tayi saboda kallon daya jefo mata.





Cikin tsawa yace"kun tashi ko sai na saba muku", jiki a sanyaye suka mike duka,ikhlas na gaba islam na baya, ta wajen kareem suya spot ya biyo dan haka ikhlas ta kalle shi tace"yaya pls zanci", karamin tsaki yayi kafin ya bude kofa ya fita.



Mintina kadan ya dawo da leda uku a hannunshi, islam ya fara sauke wa sannan ya wuce da ita, yana parking tana kokarin fita taji ya saka lock.



Kallon shi tayi tace"yaya pls ka bude mini mana na fita, wayar shi ya ciro ya fara waya kafin ya ajiye ya juyo ya kalle ta yace"me hafeez yace miki dazu? ", kallon shi tayi da mamaki tace"ni babu komai dan bama muyi wata magana ba", ajiyar zuciya yayi sannan ya bude mata kofa ta fita.



Har ta fara tafiya ya kira ta ledar ya mika mata yace"ki gaishe da gwaggo sai da safe", da kai ta amsa ta juya ta tafi.








๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)



*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~โ„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*


Wattpad @13 deeja

Or
Deeja1love.blogspot.com

*written
-by-
*Deeja one love*



*dedicated
to
*Maryam khamis*


17-18



A yau ikhlas ta shiga garin kano domin yin registration saboda ta nema a ATBU bauchi bata samu ba sai ta samu a BUK hakan yasa ta tafi registration.



Tasha wahala babu sosai domin kuwa babu wani wanda ta sani haka abba kabiru shima babu wanda ya sani a wajen,mass com suka bata, babu laifi duk da bata wani son course din.





Tana dawowa ta fara bawa gwaggo labari, ita kanta gwaggo tayi mata murna.


Washe gari taje gidan iman, yaya sadik ta samu yana ta faman aiki, dariya abin ya bata, hade rai yayi yace"meye na dariya dalla ni amsa ki karasa", shiru tayi kawai ta amsa ta cigaba da aikin, dan danan ta gama, yana zaune ganin ta gama yace"jeki bedroom dina ki gyara mini",kai ta jinjina sannan ta wuce.





Ko'ina sai da ta tsaya ta gyara shi ya gyaru sannan ta wanke bathroom tasa room freshner ta kunna turare ta fito,a tsaye ta same shi kallon ta yayi yace"shiga kitchen ki dafa mana break fast", cuno baki tayi sannan ta wuce.




Egg rolls da coffee ta hada sai indomie, a zaune a falo ta same shi, gefen shi iman ce ta daura kanta a kan kafadar shi, tabe baki tayi sannan ta ajiye musu.



"Thanks "kawai ya furta sannan ya sauko da iman kasa, a baki ya dinga bata, ita kuma sai wani kara shagwabe wa take yi, ikhlas dai kallon ikon allah take.



Dagowa yayi yace"ya akayi kika kafe ni da idanu? "Tabe baki tayi tace"dama nazo na gaya muku ne na sami admission a BUK har ma nayi registration", hade rai yayi yace"ok ni ban kai matasayin da zaki zo ki gaya mini cewa kin sami admission naje nayi miki registration ba ko? Wato yanzu raini ya shiga tsakanin mu?ai shikenan allah ya gani ina yin iya kokarina wajen kula da amanar da aka bani", mikewa yayi ya fice.




Shiru ya biyo baya kafin iman tace"sis na tayaki murna wane course? ", ikhlas tace"na gode mass com, wai ke kam lafiyan ki? ",murmushi iman tayi tace"banza kin kusa zama mummy kina can kina shirme", daka tsalle ikhlas tayi tana fadin"kai alhamdulillahi ah lallai naga sabuwar shagwaba", dariya suka yi gaba daya.



Nan ta wuni duk abinda iman ke so shi take dafa mata, iman ita kanta har mamaki take, kan kace me ta kira islam da gwaggo ta gaya musu, iman kam dariya kawai take yi mata.


Tun daga ranar kullum ikhlas tana gidan, ita ke zama tayi mata duk ayyuakan gida, haka islam idan bata da lectures ita ma takan zo.


Ana gobe ikhlas zata tafi kano,a kitchen suke duka su ukun, ikhlas ke soya kwai yayin da islam ke yanka cucumber da karas, iman kuwa na zaune tana shan abarba.


Ikhlas tace"ni wallahi kamar kada na tafi haka nake ji", islam data dauko cabbage da tomato tace"saboda me? ", tace"saboda baby mana ", dariya sukayi gaba daya.



Islam tace"wannan ko ke kikayi cikin ai sai haka", iman tace"ko dai ku kuka yi cikin ai sai haka, wallahi wannan yaron dan so ne, kina gani yaya hafeez kullum sai ya kira wai me nake so, ina gaya zai aiko a kawo mini ko kuma idan darling zai dawo ya bashi", islam dake kwashe dan wake tace"dan so kenan ai wannan da kedai allah ya kawo shi lafiya ", duka suka amsa da ameen.



Suna gamawa suka fito suka zauna tasa ta suka yi a gaba kamar zasu yi mata dura, a haka sadik ya shigo ya same su.


Dariya abin ya bashi yace"to wannan da yana da iyaye da yawa", murmsuhi sukayi sannan suka gaishe shi, amsawa yayi sannan ya ajiye ledar hannun shi.


Yace"gashinan inji hafeez yau kin sa shi yawo da kyar aka samo gorubar wallahi har tausayi ya bani",iman tayi dariya tace"to ya za'ayi ", kallon islam tayi islam ta hade rai dariya tayi tace"bake zance ki banbare mini ba malama", dariya akayi gaba daya.




Ikhlas ta mike tace"kinji islam taso muje mu banbanre mata ya zamuyi", islam ta harari iman tace"wallahi samun wajene", itadai iman dariya kawai take yi.



Washe gari ikhlas ta wuce*kano ta dabo tumbin giwa, koda me kazo an fika, garin daba kano ba dajin Allah(amma banda zaria aradu๐Ÿ˜)*





Sun fara daukar lectures cikin kwanciyar hankali, amma fa kullum sai ta kira gwaggo haka iman, shidai sadik abin farin ciki yake sashi domin yasan suna son dan da zai haifa, iman ita kullum tafi son mace, ita kuma ikhlas tace namiji, ita kam islam cewa take Allah dai ya sauke ta lafiya.





tunda taje bata da kawa ko guda daya har suka cinye first da second semester, suna cikin third semester ta hadu *nafeesert jibreel jasawa*ita amma yar kano ce hakan yasa daga gida takan zo makarantar.

Bayan sun fito daga lectures ikhlas tace"yauwa feenat muje jifatu dan Allah ina so nayi siyayya", nafeesa tace"babu komai muje kawai amma fa daga can gida zan wuce", ikhlas tace babu komai", ikhlas ke driving kasancewar tun tana bauchi suka koya a motar yaya hafeez.




Suna parking suka fito waya ce a hannun ikhlas tana fadin"bari na kira maman baby yau kwata kwata ban kira ta ba", dariya safeena tayi tace"ai kuwa ya kamata", amsar da tayi niyar bata ne ya tsaya saboda karo da tayi da mutum har wayar ta ta fadi shikuma ledar dake hannun shi ta fadi.



A tare suka tsugunna domin tattaro kayan, shikam kokarin daukar wayar tata yake yi, wanda hakan yasa tayi saurin fara tattara nashi, dakatar da ita yayi yace"am sorry ki barshi zan kwashe kawai"murmushi tayi tace"ok na gode", juyawa tayi suka shiga ciki.



Ikhlas kuwa siyayyar take tana tunanin wannan mutumin tabbas bafulatani ne daga ganin shi, domin fari ne kuma kyakkyawa,murmushi kawai tayi, suna gama siyayyar suka fito.


Abin mamaki a tsaye suka same shkenanjingina da motarshi yana danna waya, feenat tace"to ikhy gashi ki hau mota ki koma", kallon kin raina mini wayo tayi kawai ta cigaba da tafiya.



Tana fita bakin titi motar tayi parking a gabanta glass din ya sauke ya leko yace"princess muje ko", kamar zata ce wani abu sai ta fasa kawai ta bude ta shiga ", murmushi yayi yaja motar.



Sunyi nisa da tafiya ya dube ta yace"ni sunana saifullahi muhammad yunusa gimi muna zaune a kaduna anguwar rimi, aiki ya kawo ni kano kefa?, sai da ta numfasa sannan tace"sunana juwairiyya muhammad ni ina zaune ne a bauchi karatu ya kawo ni kano".


Murmushi yayi yace"which school? ", ta bashi amsa da"BUK,mass com dept",dariya yayi yace"ai ban tambaye ki ba", itama murmushi tayi tace"ai nasan tambayar gaban kenan". Har bakin hostel dinsu ya ajiye ta.


Fitowa yayi yace"to baki bani number din ki ba", fari tayi tace"ta siyarwa ce",dariya yayi yace"how much",it's very expensive that you can't buy it",ta bashi amsa, murmushi yayi yace "to ai nace ki gaya ne",juyar da kai tayi tace"ban shirya shan duka wajen madam ba".



Dariya yayi yace"ashe ma ke matsoraciya ce", juyowa tayi ta kalle shi sannan tace"ni ba matsoraciya bace zan iya baka amma kada ka bari ta gani", dariya kawai yayi ya miko mata wayar, number din tasa mishi, a take a wajen ya kirata yace tayi saving shi kuma ya shiga mota ya tafi.





Washe gari ta bawa feenat labari, dariya kawai tayi tace"ai dama na kusa gano haka sai dai kin san me? ", gurgiza kai tayi, safeenat tace"lecturer ne a makarantar nan ke matsayin doctor gare shi", zaro idanu tayi tace da gaske", daga kai tayi alamar eh.



Yanzu cikin iman yana da wata takwas, a lokacin kuma tsakanin

Please Login or Register in order to submit comment