Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da halin mom din tashi.




Ita kuwa ikhlas sauri kawai take yi,hotoro gidan hafsat ta shiga,wanda yayi daidai da isowar feenert, murmushi suka yiwa juna sannan suka shiga.




A zaune suka tarar da hafsat tana tapping computer, ita kuma beleert tana chatting a waya.



Feernert ta daka mata duka, tace"kina kwance kina chatting ko,wallahi idanun ki zasu sami matsala",





"Meye naki a ciki? Idan na zo aron naki idanun kada ki bani",hafsat da ikhlas suka yi murmushi.




Ikhlas tace"yanzu dai fada mana meya faru ake neman mu? ".



"Alhaji yahya hassan kaura ya shigo gari, yanzu haka ma yana cikin garin kano, feenert ta fada.



Ikhlas ta dora da cewa"yana zaune a diamond hotel,room 47,yazo taron da yan siyasa suka yi dazu karfe hudu zuwa shida, yanzu haka yana so a bashi takara ne,yaje haske store domin neman mai taya shi kwana".




Numfasawa tayi kafin tace"sannan yaje dorayi karama,wajen wani abokin shi alhaji ibrahim gwala-gwalai,daga nan ya wuce government house in da suka yi taron su,yana fitowa ya wuce zango acan yayi sallar magrib da isha, daga nan ya wuce masaukin shi".




Kallon su tayi ta daga gira daya,feenert tayi ajiyar zuciya tace"yaushe kika yi wannan binciken?".




"Lokacin da kike can kina shirme", ikhlas ta bata amsa", duka suka yi dariya.



Hafsat tace"to yanzu ya za'a yi? ",ikhlas ta mike tace"kada ki damu, dazu mun hadu a haske wanda hakan yasa yake bincike a kaina, ko ince yayi bincike a kaina, yanzu zuwa gobe zai zo inda nake domin kuwa an bashi irin labarin da yake son ji".




Beelert tace"wane kala kenan?,ikhlas ta bata amsa da"zaman kaina nake, a yawon karuwan ci har da nake da".





Hafsat tace"kenan ke zaki shiga kuyi soyayya?, to kamal din fa? ",ikhlas ta ce"eh zan je muyi soyayya tare dashi, ke kuma feenert zaki tafi gombe domin kiyi mana traping wancan dan iskan".



Kai kawai feenert ta daga,beelert tace"ni kuma zan cigaba da zuwa miki wajen aiki",hafsat tace"zan dinga saka idanu in case ko za'a sami matsala".



Murmushi ikhlas tayi,cikin farin ciki,wayar dake hannun ta tayi kara,ganin me kiran yasa ta mike tace"babies ni nayi gida, sai da safen ku".




Mikewa feenert tayi ta biyo ta, a tare suka fice daga gidan.



Tana komawa gidan, ta shiga da sauri domin ta gashi tana son hutawa.



Kallon-kallo suka tsaya yi, agogon ya kalla daya da wajen minti talatin.



Cikin dakiya tace"me kake yi anan har yanzu baka yi barci ba? ",jiki a sanyaye yace"nayi barci yanzu haka ma ruwa na fito sha".



Bata ce komai ba ta wuce, bin ta da kallo yayi kafin ya juya ya shiga daki, ruwan da be sha ba kenan.




Washe gari da safe, da wuri ta tashi, sai da tayi shirya sannan ta fito.



Doguwar riga yar kanti ce a jikin ta,purple da ratsin fari,takalmin ta da gyalen ta duka fafarare ta saka.



Tana fitowa main palour ta samu baby yana karyawa, kallon ta yayi yana murmushi ya gaishe ta, itama murmushin tayi mishi sannan ta zauna.




Tare suka yi break fast, sannan ta daukar mishi jaka da lunch box, suka fito.




Ta bude mota kenan, a ka bude get, motar ta shigo, kallon motar take tana murmushi.




Jersey ne a jakin shi, da wani kallon yake bin ta dashi, wanda ita kadai take gane mai yake nufi.




Baby kuwa hade rai yayi ya shige motar,yana karasowa ya rike hannun ta yace"good morning princess ",da kai ta amsa mishi.




Tace "saukar yaushe? ",yace"jiya mana ai na kira ki baki daga ba,yanzun ma lecture zan yiwa dalibai, amma zuciya ta taki hakura wai sai ta zo taga mamallakiyar ta", daiya suka yi duka.



Kallon motar ta tayi tace"zuma na zan tafi kaga kada baby yayi late".



Girgiza kai yayi yace"ok, shikenan adawo lafiya ".



Daga haka duka suka shiga mota, suka tafi.

Sai da ta ajiye baby sannan ta wuce, wajen aikin ta, kowa yana matukar murna da ita.




Daya daga wanda suka shigo wajen ya dubi abokin shi yace"kasan saboda wannan babyn nake son zuwa mundassir", dariya suka yi suka tafa.



Abokin yace"kai ai akwai kayan morewa a jikin ta, sai dai fa bata sakin fuska, ni wallahi sai naga ta cika shagon ne, saboda kwarjinin ta".



"Kai wallahi baby din nan karshe ce,ina ma ta bani dama koda dare daya ne",wanda yayi magana da farko ya fada.



Abokin ya dube shi yace"kai yanzu idan aka bar ka da wannan ya zaka yi da ita? ", harara ya galla mishi yace"tasa ta zan yi a gaba in ta kalla, wawa kawai".



Wani daga can gefe yace"kai dan allah idan aka barka da wannan ai an gama maka komai, nifa sai nake ganin anya ba hurul aini bace a duniya", dariya suka kuma yi.



Ita dai ikhlas bata ma san da zaman su a wajen ba.




Wajen uku,motoci suka fara tsayawa, ckkin sauri escorts din shi suke shigo, sai da suka tabbatar da lafiyar wajen, sannan suka bashi waje ya shigo.




Gefen table din ta ya tsaya,idanu ya zuba mata yana hadiyar miyau, cikin duniyan ci yace"kayan mai tsada".




Lip din ta na lasa ta ciza, ta cigaba da aikin da take yi, wannan abin da tayi ya sake dulmiyar dashi cikin tsananin sha'awar ta.




Jan numfashi yayi yace"zazzafa ce ke",dago kai tayi ta dan yi murmushi tace"oga ina kayan daka siya? ",wayar shi ya miko mata, tare da bandir bandir din dubu dai-dai guda hudu.




Idanu ta lumshe, sannan ta fara jera mishi, numbers din ta,wani magnet yake ji yana fuzgar shi.



Amsar wayar kawai yayi ya fita, escorts din shi na bin bayan shi.



Yana fita taja dogon tsaki,tana dago ido suka hadu da nashi.



Kallon tsana yake bin ta dashi, dama an gaya mishi akwai karuwai a naigeria da yawa amma bai yarda ba sai yau.




Cikin sauri ya fice daga shoprite din, ikhlas kuwa daga kafada tayi sannan ta cigaba da abinda take yi.





Shikuwa cikin zafin rai yake tafiya, allah ne kawai ya kai shi gida, gashi yayan shi baya nan,key din ya cillar ya bude fridge ya dauko c'est bon ya kwankwande, ya cillar da bottle din.






Zama ya koma yayi yana ajiyar zuciya, can zuciyar shi tace"to kai meye naka na fusata, daga ganin ta ko sunan ta ma fa baka sani ba",tsaki kuma yaja kafin ya mike.




Ita kuwa ikhlas tana tashi ta wuce gidan hafsat ta dauki baby sannan suka wuce gida,da yamma tana zaune a garden tana hutawa, amma fa a badini tunani ne take yi.




Tabbas mutum mugun ice ne,ji fa wa'inda bata tunanin zasu cuce ta sune suka cuce ta, mutumin da take girmama wa.



Ringing na wayar ta ya dawo da ita daga duniyar da ta shiga sai da tayi tsaki sannan ta daga.




Jin muryar shi yasa ta kara hade rai,da kyar take amsawa, a haka har suka yi sallama, saving number din tayi da sugar daddy sannan ta mike.




Wanka tayi ta daura alwala,tana idar da sallah tasha wankan ta sannan ta fito parlour.




Tare da baby suka yi dinner, sannan ta koma kan kujera, shima babyn home work din shi ya dauko, a hankali take kara fahimtar dashi.




Saifullahi yayi sallama ya shigo, tun da sadik ya gaishe shi be kuma cewa komai ba,





Kusa da ita ya zauna, kan ya kalle ta yace"princess ya kike? ",murmushi tayi tace"lafiya lau ya hanya? ", dariya yayi yace"nazo miki da suprise",





Lumshe idanu tayi tace"suprise na me kenan? ",langwabar da kai yayi yace"wayo zaki yi mini kuma", a tare suka yi dariya.





Haka ikhlas ta cigaba da ita da saifullahi, gefe kuma alhaji yahya hassan da suke soyayyar su.




Yau ikhlas tare take da asp saleh abdullahi, wanda yake a gombe, suna tattaunawa domin nan da kwana biyu, zasu je garin ita da alhaji yahya hassan.




Murmushi yayi yace"kada ki damu, aunty in dai wannan ne baki da matsala akai".


Gefen ta ta kalla,wannan fuskar da suka hadu a muddasir take gani still dai kallon tsana yake aiko mata dashi.



Wannan waye da yake neman matsamin, tsaki ta ja sannan tace"abdallah mu bar wajen nan", shi ya daukar mata jaka, suka fita suna fira.




Ajiyar zuciya yayi,ga kyau har kyau amma babu hali,iska ya furzar yana mai jin zafi, ranar nan ya gan ta da wani, yau ma haka.


Kai wasu matan basu da hali mai kyau,gata da kyau amma ta zabi kyan ta ya zamar mata jari.



Murmushi yayi tunowa da yadda take wani cizar labe,daga gani babbar karuwa ce.





Kallon wanda ke kusa dashi yayi yace"kasan allah sudeis halin matan garin nan yana bani mamaki kaga mace kyakkyawa amma babu hali ".





Da mamki sudeis ya kalle shi yace"malik yaushe ka fara damuwa da harkar wasu ne? ".



Mikewa yayi yace"sudeis zan tafi nasan yanzu lovely ya dawo, sai mun hadu jibin kada ka manta ka shirya da wuri".




Sudeis yace"insha Allah zan shirya da wuri", daga haka suka fice daga wajen.




๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)



*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~โ„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*


Wattpad @13 deeja

Or
Deeja1love.blogspot.com

*written
-by-
*Deeja one love*



*dedicated
to
*Maryam khamis*

27-28



Ikhlas ta kai baby gidan hafsat kafin tace"hafsat ga amana ta nan sannan ki tabbatar ya je makaranta.




Hafsat tace"kada ki damu babu abinda zai same shi, insha allah",peck tayi mishi a goshi sannan ta tafi.




A kofar gidan ta tarar da alhaji yahya hassan,
Shiga kawai tayi suka wuce, sai faman zuba yake a mota wai shi nan a ganin shi ya burge ne.




Wayar ta ta dauka ta turawa da feenert sako akan sun taho,bayan minti biyu ta turo mata da amsa akan sun wuce jos wato suna gaban su.




Karfe hudu suka shiga garin gombe, hotel ya kama musu,ita dai ikhlas bin shi da kallo take kawai.



Bayan ta idar da sallah tace"honey yunwa fa nake ji", dashe baki yayi yace"bari nayi miki order",shagwabe fuska tayi tace"haba dan Allah mu fita mana".



Wayyo har wani turo wuya gaba yake yi,kashe mishi ido tayi tace"ina so na zagaya gari ne",jiki na rawa yace muje.




Wani hadadden restaurant suka yada zango,alhaji yahya sai faman jin dadi yake, domin ko'ina suka ratsa sai an kalle ta.


Kara wani bubbudewa yake, wato a dole yana tare da classic baby, sauran yan matan wajen kuwa kowacce raina wankan ta tayi.



Suna gama cin abincin ta mike domin su tafi, daidai wajen shigowa suka yi clashing, wannan dai kallon na tsana shi yake bin ta dashi.


Juyar da kan ta tayi ta cigaba da tafiya, dai dai bakin motar aka kira alhaji yahya a waya, wanda yasa yayi escusing kan shi ya bar wajen.



Kallon abokin shi sudeis yayi yace"ina zuwa yanzu zan dawo",sudeis ya bishi da kallo yana murmushi.



A jikin motar ya tarar da ita, cikin kyama yace"wai ke wace irin dabba ce haka?, ki rasa wacce sana'a zaki yi sai wannan, amma dai iyayen ki sun yi asarar haihuwar ki".


Bin shi da idanu take tana murmushi,alhaji yahya yace"baby mai ya faru? ",ya gaya yana bin maleek da kallo.



Lumshe idanu tayi tace"sugar wai zuwa yayi na taimaka masa da number ta,domin wai nafi dacewa da sabin jini, na kyale ka".



Cike da fushi alhaji yahya yace"kai baka da hankali ne, ka sani wannan kaya na ce, dan haka wannan zan daga maka kafa amma ka kuma zaka sha mamaki ".


Daga haka ya bude mata kofa yana fadin"gimbiya sarautar mata bismillah,zazzafa me sa maza zufa",juyowa tayi ta kalli maleek ta kashe mishi ido daya sannan ta shige.



Har suka ja motar ya kasa motsawa saboda tsananin mamaki,sudeis ya girgiza shi yace"maleek wane kalar tunani ne haka? ".


Ajiyar zuciya yayi, idanun shi yayi ja, har jijiyoyin kanshi sun fito, fizgar hannun sudeis yayi be damu da mutanen dake wajen ba.



Motar ya bude ya jefa shi, shi kuma ya zagaya ya shiga motar ya ja da gudun tsiya.



Tafiya yake amma abun da ta fada yana dawo mishi kanshi,how dare her zata hada kan ta dashi, karuwa!shi kuma tsarkakke,ita da ta raba wa maza jikin ta a titi shi kuma da koda yayi zaman kasar waje be taba kusantar zina ba".



Buga steering motar yayi yana fadin"damn it", da karfi, shi kan shi sudeis da yake gefe sai da ya tsorata yana fadin"maleek control your temper remember you are driving fa".



A hankali ya bashi labarin abinda ya faru, sudeis yayi murmushi yace"aboki na ka dena damuwa da irin wa'in nan matan domin kuwa haka rayuwar su take".



Jinjina kai yayi yace"tabbas abunda ka fada gaskiya ne, to amma na rasa me yasa tun da naga yarinyar naji na tsani abinda take aikatawa.





Dai dai lokacin da ya shiga hotel din, idon shi ya hango mishi ita a gefen alhaji yahya zasu shige ciki.




Ran shi a bace ya dubi sudeis yace"kalle ta fa da wancan tsohon", murmushi kawai sudeis yayi, har suka shiga dakin shi mitar da yake yi kenan.





Sudeis ya dube shi yace"maleek ka fahimci wani abu,kamar yadda kasar daka baro indi kowa yana da 'yan cin yin rayuwar shi haka ma fa nigeria muna da wannan, ka cirewa kan ka wannan damuwar fa,ni na tafi sai da safe", daga haka ya fice.






Ikhlas kuwa a ranta fadi take"ni na shiga uku da maye, wai wannan shi duk inda zanje sai ya bini ne haba", tsaki taja kasa-kasa.



Alhaji yahya yace "ya dai zazzafar ko dakin be yi miki bane? ", girgiza kai tayi a ran ta tayi tsaki tace"ji shi wannan wawan zai kwanta da yar cikin shi amma wani murna yake yi".



Hollandia ta bude ta zubo musu a cup, cikin farin ciki ya amsa, a tare suke sha suna fira, suna gamawa,ta mike tace"bari na canza kaya ",tana fadan haka ta shige toilets.





Minti kadan ta fito, kamar yadda ta zata ya sheme da barci,dariya tayj sannan ta daga waya tace"ku shigo kawai dan yayi barci".




Receptionist din kuwa ganin da dan sanda yasa ta basu key din dakin,suna kwan kwansawa ta bude musu.




Kallon shi suka yi sannan asp abdallah yayi mata thumb like alamar jinjina.



Da sauri abdallah yace"to yanzu feenert fara naki aikin",feenert tace"angama yallabai".





Matsawa tayi kusa dashi, rigar jikin ta ta cire, sai gata daga ita sai mini skirt da riga half, asp ya dubi beelert yace"fara dauka kinji kiyi da sauri kafin escort din shi su same mu a nan",cikin sauri ta fara dauka.




Suna gamawa suka fice daga dakin cikin sauri suka fice daga hotel din gaba daya.





Bangaren maleek kuwa,waya suke da lovely din shi, yace"gobe insha Allah zan dawo.




Saifullahi yace"to lily ka kula da kan ka sannan ka sani, daddy yana can yana jiran ka".




Murmushi yayi yace"kada ka damu zan dawo da wuri, amma sai ka hada ni da princess mun gaisa tukunna".



Saifullahi yace"bayan ranar nan naso ku hadu ka wani ce ba zaka je ba, gashi yau ta tafi gombe sai jibi zata dawo".


Lily yace"bana baka labarin wannan shegiyar karuwar bace ta bata mini rai ba, kuma gashi a nan ma sai da muka kara haduwa har ta nemi ta mini sharri,banda allah ya kiyaye ni", ya karasa da shagwaba.



Saifullahi yace"wai ko dai son ta kake ne?naga baka cika damuwร  da matsalar wani ba sai a kanta".



Cikin bacin rai yace"lovely kasan dawa kake hadani kuwa? Me kwana a hotel da sa'an uban ta? ",yana fadin hakan ya kashe wayar.




Tagumi yayi yana tuno yadda take juya idanun ta wanda suke nuna wayewar ta, tabbas wannan daga gani tafi karfin karamar karuwa, tsaki yaja sannan yace"wai meye nake bata rai na akan wacce ko sunan ta ban sani ba", daga haka ya kwanta.






Washe gari,alhaji yahya ya farka, ganin shi a wani dakin yasa ya zaro idanu, tunani ya fara to me ya kawo shi nan ne?.



Yana nan yana tinani aka turo kofar aka shigo,cikin mamaki yake bin su da kallo,idanun shi ya tsayar akan beelert.




Cikin tsananin mamaki yace"nabeelert! ",matsowa tayi ta wanke shi da mari ta kuma kara wanka mishi mari tace"eh, nabeelert abdulmalik fantami, ashe baka manta ni ba? ".




cikin zafin rai ya kalli ikhlas yace"zazzafar....... ", be karasa ba ta dakatar dashi ta hanyar cewa"baka da hankali ne, wai zazzafa,baka san duk lokacin dana ji ka kira sunan nan wani zafi nake ji a rai na ba".



Dariya yayi yace"lallai kin ce wani abu, to amma naga a yawon dandi har tsaraba kika samo gashi nan kina raino a gidan ki".



hannu nabeelert ta daga zata kuma marin shi ikhlas tayi saurin rikewa tace"baby kada ki bata lokacin ki kyale shi yanzu muyi abinda ya kamata kawai".





Files feenert ta miko mishi tace"sign here", kallon ta yayi yana murmushi yace"haba yan mata an gaya miki ban san na meye bane? ".





Ikhlas tayi murmushi tace"tun da ka sani kayi sign akai",shiru yayi yana kallon takardun.



Asp abdallah yace"da alamu bazai yi signing yadda muke so ba, feenert nuna mishi",wayar dake hannun ta ta mika mishi.




Jiki a sanyaye ya amsa, feenert tace"play d video mana",jiki a sanyaye yayi playing, abinda ya gani yasa jikin shi ya dauki rawa.




Beelert tasa hannu ta amshi wayar, kallon tsana ya bita dashi yace"me yasa zaki mini haka ki yaudare ni ki cuce ni a rayuwa, haba nifa a matsayin mahaifi nake a wajen ki", mari ta wanke shi dahi.




Tace"kada ka kuma hada kanka da ni, zaka yi signing ko sai mun saki, a social net da gidajen television domin mu nuna musu yanda kake neman mata, kaga daga nan da kan su zasu yankan maka takardar takara ta din-din-din", ta karasa tana kashe ido daya.




Jiki na rawa ya amsa yayi signing din,ikhlas tace"yauwa good boy, yanzu ka zauna nan da five minutes escort din ka zasu iso su tafi da kai, ga wannan",dubu daya ta ajiye mishi tace"kasha ruwa a hanya", ta karasa da murmushi a fuskar ta.




Sun juya zasu tafi yayi dariya yace"kun kashe maciji ne baku sare kan shi ba, domin dole sai da sa hannun dana sannan komai zai koma nata ".




Feenert tace"me yasa kwakwalwar ka bata ja ne?, ai ya kamata kayi tunanin ya akayi takardun suka zo hannun mu? ", daga haka suka karasa ficewa.



Shuru yayi yana tinanin ya akayi hakan ya faru?, da sauri ya furta"kamal! ",cikin sauri ya mike ya fice daga dakin, hotel ne ma ashe ya fada yana jan tsakin.




Gidan shi ya nufa a fusace,yana shiga ya sami kamal a zaune yana hutawa, cikin karaji ya cakumi wuyan shi yace"waye ka bawa takardu na? ".



Cikin rashin damuwa yace"wajen wata baby naje to daman na taho da takardun saboda cewa da kayi na taho dasu shine na manta dasu a can amma anjima zan je na amso maka".




Wanke shi da mari yayi cikin tashin hankali yace"kamal ka kashe mu, wannan yarinyar kawar nabeelert ce yanzu haka tuni nayi signing akai, kamal ina dai bakayi signing ba".





Cikin sauri yace"ban yi ba amma kuma ai ta iya signing dina", alhaji yahya yana jin haka ya dora hannu a kai ya fasa ihu.




Matar shi ta fito da gudu tana tambayar lafiya kuwa? ", wajen zama kawai ya nema yana fadin"kamal ka kashe mu, yanzu takardun ka dauka ka damkawa wata, sannan in banda jakan ci meye na koya mata signing din ka? ".




Matar da jin haka tace"shikenan abinda nake tunani ya faru alhamdulillahi ", cikin zafin rai alhajin yace"baki da hankali ne", ta bashi amsa da "dama fa dukihar marayu muke ci to tunda ta amsa ai ta taimake mu ne".



Be kuma cewa komai ba, kamal yace"ni dai dan allah abba kasan yadda zaka yi nabeelert ta dawo waje na wallahi ina son ta".



Kallon mara hankali ya fara mishi,sannan yace"kamal ka farka daga barcin da kake ka sani nabeelert yanzu tafi karfin ka", daga haka ya mike ya shige cikin gidan.




Bangaren su ikhlas kuwa, suna barinhotel din suka wuce, gidan asp abdallah anan feenert tayi signing papers din



Washe gari, suka tura wani yaron asp a matsayin wanda ya siye gidan,yana gayawa alhaji yahya yace"to, jiki a sanyaye ya koma gidan.




Hada kayan su sukayi suka bar gidan cikin damuwa.



Ni dai one lurv nace"a koma gida a dau fatanya๐Ÿ˜.






๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)



*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~โ„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*


Wattpad @13 deeja

Or
Deeja1love.blogspot.com

*written
-by-
*Deeja one love*



*dedicated
to
*Maryam khamis*

Yawan comments yawan typing domin comments din ku shi zai sa naji karfin yi muku typing.



29-30



Su kuwa ikhlas a ranar suka koma kano,beelert tace"na gode allah ya bar zumunci ban san wane irin godiya zan yi muku ba".





Asp abdallah yace"kada ki damu we are all family, ke dai ki kula, sannan ki nemi wanda zai rike miki amana ya taya ki rike companies din".




Murmushi tayi tace"why not kai ka taya ni idan yaso ko da ace lokaci zuwa lokaci ne".




Jim yayi kafin yace"a'a bazai yiwu ba sai dai zan hada ki da wanda zai taya ki, kin ji".




Ikhlas tace"to yanzu dai ka rike mata har zuwa lokacin da zamu gama abinda muke yi, daga nan sai ta zo ta amshi kayan ta", duka sun yarda da wannan shawarar.




A haka suka watse,feenert tace"yanzu ikhlas baki tunanin alhaji yahya yazo gida yayi miki wani abu? ".



Girgiza kai tayi tace"ai yanzu baya da kudin da zai yi hakan domin yanzu neman na ciyar da iyalan shi yake yi".





dariya suka yi gaba daya,sannan kowa ya nufi hanyar gidan su.





Bangaren maleek kuwa, washe gari da wuri ya bar gombe,koda ya isa kano ya tarar yayan shi saifullahi yana nan.





Da farin ciki yace"ya dai lily an dawo kenan? ",daga kai yayi kawai ya fara hada kayan shi domin tafiya kaduna ".




Saifullahi yace"ina zuwa haka? ", a takaice ya bashi amsa da "kaduna zan tafi yau, ina so naje naga mommy".




Saifullahi yace"ba zaka tsaya ku hadu da princess din ba? Kaga dazu ta dawo daga gombe ita ma".



Jin haka yasa ya hade rai, domin shi fa tunda yaga wannan halayyar macer yaji ya tsani yan mata.




A dake yace"ka bari next time kawai", daga haka ya mike.



Wanka yayi ya shirya, saifullahi yaso ya bari sai washe gari amma yaki, haka ya kyale shi ya tafi.




Awa biyu da wani abu ya isa kaduna, domin irin gudun daya dinga zubawa a titi,anguwar sarki ya shiga.



Gida je na alfarma ya dinga ratsawa, can gaban wani gidan tsantsararre ya danna horn, me gadi yayi sauri ya bude mishi.




Cikin sauri yayi parking ya fito da sauri, cikin gidan ya nufa da tafiyar da tafi kama da sassarfa.




Da sauri ya wuce parlour din farko ya nufi wani corridor,wata kofar ya bude, wani parlour din ya shigo tun daga nan ya fara kwala kiran"mommy na".



Masu aikin wajen sai gaishe dashi suke yi, daga musu kai kawai yake yi,burin shi a lokacin kawai ya hadu da mahaifiyar shi.




Yana shiga ya fara ware idanu ta ina zata bullo,yan matan dake parlour suka kalle shi suka tabe baki.




Kofar da yake kallo a ka bude aka shigo, tsayawa suka yi suka zubawa juna idanu,murmushi dauke a fuskar su.



Macece daka kalle ta ta kalli saifullahi zaka tabbatar da mahaifiyar shi ce, domin kamar da suke yi.



Da sauri ya karasa ya rungume ta, suna sakin wa juna wani kalar murmushi, fadi take"welcum back home my

Please Login or Register in order to submit comment