Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna cikin haka Hussain ya shigo suna gaisawa ya kalli Hassan cikin damuwa yace Bros Fateema fa xuwa a asibiti ya kamata wlh yanxu a ka kawo wasu bayin Allah sunyi hatsari duk sun kakkarye munyi ta kiranku Amman bakwa dagawa Hassan ya dan kalleshi yace toh ina Doctor Usman Hussain yace dan Allah Fateema tashi mu tafi Alhj babba yace Hassan kuje Ku hamzarta ai taimako ne Ammi tace ai shi haka yake komai sai yasa ra'ayinshi Abba ma yace maza kuje haka dai suka dunguma harda Zubaida ta bisu*******************suna shiga hospital en kai tsaye inda aka kontar da majinyata Hussain ya nufa dashi da Zubaida shikuma Hassan da Fateema suna tafe a jere suna isa Fateema ta fara aikinta ba gaggautawa ta gama gyaran karayan da yaron yaji yaro fari tas ta kalli Hussain tace yaya ina iyayen yaron yace gashinan a bayanki ta juya abin mmki malaminta ta gani Uncle Sulaiman cikin mmk tace mlm yaronka shima cikin mmk yace yar Fulani kece kece doctor Fateema Hassan Aliyu saraki tace Mlm duk iyalanka ne yace eh ita wannan matatace ai*** Allah sarki duniya indai kai alkhairi to zakaga alkhairi haka Hussain da Fateema da Hassan dama saran doctors en suka yi musu aiki cikin kulawa sune basu gama aikinba har goshin maggariba tsayuwar da Fateema tai mai yawa shi ya fara isarta da gyar dai ta samu ta gama sun gama kenan ta juya zasu fita sai ta fara ganin duhu yana giftawa a idanta kafin wani lokacin sai jiri a hankali tace Hamma duhu ya rufemin ido bana gani jiri nakeji kafin ta rufe bakinta tai luuuuuu zata fadi da sauri cikin gudu Hassan ya ture doctor Usman ya je ya tallabota ta fada jikinshi jikinta sai bari da sauri cikin rudewa ya ciccibeta ya nufi office enshi da ita sauran doctors suka bisu a baya abin kamar wasa sai gashi har dare yayi sai ta bude idanta sai taga gaba daya office en Na juyawa hatta mutanen dake kantan sai taga suna juyawa tsai tai saurin rufe idan da sauri shi kam gaba daya Hassan ya rude yana gefenta Zubaida ko na can gefe a rakube sai hawaye kebin fuskarta Hassan ya kama hannuta ya riqe ya dan sunkuyo kanta cikin muryar damuwa yace Fateema ki bude idanki nine fa Hammanki ne ki bude idanki ki gayamin meke damunki ta dan girgiza kanta tace Hamma ina Zubaida da sauri zubaidan ta matsota tace gani Anty Fati ta kamo hannuta tace Zubaida kiramin Ammi kice su zo mutafi gida,,, Hassan ya qara dimaucewa itako Zubaida tuntuni takira su Umman ta shaida musu a hankali doctor Halima da doctor Sadiq suka dugufa kanta dan gano meke damunta dr Sadiq shike aunata itoko Dr Halima cikin hikima da qorewa take jefamata tabbayoyinta ta kama hannun Fateema tace dr Fati meke damunki idanta a rufe tace duhu nake gani gakuma jiri taci ga tabbayarta kina cin abinci kuwa tace mata eh tace yaushene ganin period enki na qarshe tace sati uku da suka wuce cikin sauri dr Sadiq yace dama kwana nawa kikeyi tace kwana 4 yace toh yanxu kuma kwanawa kikeyi tace 2 days yace OK ya sunkuya ya danyi rubuce rubucensu Na litotici ya miqawa Dr Halima itama ta danyi rubutun Hussain kam da Nazir sai binsu da ido suke cikin muryar dry Dr Sadiq yace Alhamdulillah Dr Hassan matarka Na dauke da ciki har Na tsawon 5 mont Hussain ne yace mekace Sadiq abar batun wasafa Halima tace wlh ai ba wasa Hassan miqewa yayi yana dry cikin tsananin **farin ciki Nazir ya kalli Dr Sadiq da Dr Halima cikin far in ciki yace Goron albishirinku kujerun hajji aikuwa sukai ta murna da godiya Hassan kam sujjada yayi a gun cikin farin ciki da godiyar ubangiji Hussain cewa Dr Halima yayi yau duk majinyatan asibitinnan komai ayi musu kyaita dan yau muma munsamu farincikin samun kyautar Allah ita kam Fateema tunda taji batun cikin duk tajita ta watsake ta rinqa binsu da ido Hassan ya qaraso gun ya rinqa kissing enta yana Fateema kin biyani ngd Allah ya miki albarka Fatima mai zanmiki in saki farin ciki a dai dai lokacin** su Ammi suka iso haqiqa a wannan ranar Fateema taga tsantsar qauna da kulawa a wannan zuriyar sai dataji kunya Na kamata yau hatta Ammi farin cikinta ya kasa boyuwa Ammin tace toh fa gida zamu koma da ita sai ta qara samun qarfin jikinta shi kam Hassan dan dole ya yarda badan ya soba aiko suna shan sintirinsa ko shabiyun dare zuwa yake ba ruwansa baya iya boye Sonta da tattalinta gaban kowama gwada mata qauna yake *""""""""""""***

by garkuwan Fulani
[4/12, 6:14 PM] Aisha Aliyu Garkuwa: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
Y'ar Falani part 49 Na Aysha Ali Garkuwa
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

A hankili dai cikin har ya cika wata 6 yauma kamar kullum garfe 8 dai dai ya isa cikin gidan duk suna porlor suna break fast sai Umma d Fateema sune basa gun Amir ya dauki pilet ya zuba mai abinci ya Dan ya mutsa fuska yace ni fa banjin cin abincin ba yanzuba ya fada yana kallon Ammi itama shi take kallo tace toh Dan tsari ai mu duk bamu iyaba sai kai kaima Amir mgninka mutum da ba amai goninta sai kuita rawar qafa a kanshi ta kalli Hassan tace tunda anxuba kuma ba azumi kakeba Dan haka ci kaban fili ya danyi murmushi ya jawo pilet en ya fara ci yana Dan gyatsina fuska a ranshi kuma cewa yake Ammi sarkin fada duk dai wai Dan nine Dan fari karta goda sona ace tai rashin kunya kai fulaku sai a hankali wani lokacin sun gama karin ya miqe ya nufi dakin da Habibatinshi take

Zaune suke ita da Umma sai Hajja inna ta miqe qafafu daga dukkan alamu ta danci abinci ne ya matsa yana Dan murmushi ya gaida su Umma itako ta gaidashi ya Dan zauna dab da ita ya kalleta yace ya dai madam fatan kina lfy ko? ta Dan karya wuya tace wlh Hamma banda lfy ni qafata tana yawan kamamin ko tafiya sai Na kasa... ya kalli Umma da Hajja inna yace Umma dama ana irin wannan cikin ciki har ya kai wata 5 ba asan da shiba gashi har ya ciki wata 6 Amman kallifa ya Sa hannunshi ya jawo rigar da ke jikinta zuwa Dan sama kadan yace Umma ki ganifa ba wani alamun ciki a jikinta kuma ni da kaina nayi bincike a kan cikin ga ciki yana nan daram baby ma lfyanta qalau kuma har motsi tanayi Amman Umma ciki baya girma nikam gsky abin yana bani tsoro ya fada cikin karaya da Al ajabin abin. cikin qarfafa musu guiwa Umma tace kwantar da hankalinka ana haka mana ko wanne da da inda yake buya a jikin mahaifiyarsa Hajja inna tace Amman dai kai bansan wanne irin likita bane kai dama can baka gane tana da cikinba sai da kukaje asibitin toh in banda abinka ai alamun ciki sun dade da bayyana a jikinta kuma da kake cewa cikin baya girma ka duba yadda gigunta da cinyoyinta suke cika mana ciki dama ko wanne da salonsa wasu kuma haka sai nonunasu ne sui ta habaka su goyi cikin ta qirjinsu haka dai suka rinqa basu qarfin guiwa sannan suka fita suka tafi

Ya Dan jawota jikinshi yana Dan shashshafata da Dan bubbuga bayanta ya Dan dago kanta yace Habibati yaushe zaki koma dakinki kinsan Hammanki Na buqatarki a kusa dashi.. ta danyi rau rau da idanu sai hawaye shar😭 tace Hamma ko Na koma bazan iya komaiba Hammana ka kallifa yadda Na zama qafafuna sunfi qarfina jin jijiyoyin qafar nake kamar zasu tsinke cikin sauri ya toshe bakinta da nashi sai bayan wani Dan lokaci ya zare bakinshi a nata yace cikin kasala bana so bana son jin irin furucinnan zaki aihu lfy ba abin da zai sameki insha Allahu haka ya rinqa bata baki har tai bacci ya dagata ya dora a gado ya rufeta ya mannamata kiss a goshi ya shafa dakalallen cikinta ya fita ya tafi
Haka dai Fateema ta rinqa fama da kamewar qafa kamar dama cikin jira yake a ganosa ya fara bata wuya

Yau Monday misalin bayan azahar suna zaune a parlor maimartaba da Hajja inna da alh babba da su Ammi sai su Hassan kamar ko da yaushe Al adar gidan in mace nada ciki da zaran cikin ya shiga wata 7 Inna waziri zata fara hada mata magunguna da Addu oi ana bata tana sha Na samun sauqin naquda toh yau shine za,a fara bawa Fateema ta gama hadawa (insha Allahu zan lissafo mana itatuwan koda a qarshen lbrin ne) Umma da kanta taje ta kirawo Fateema tana gaba Fateema Na binta a baya har suka shigo inna waziri tace matso nan yata ta daga qafarta da niyar takawa ta qarisa gun inna waziri qafa kam ta kama gim taki sakewa ba gaba ba baya a take taji tamkar ana Jan jijiyoyin qafafun cikin jin azaba tace wayyo Allah Na gaba daya suka juyo gareta Umma kam harta isa gunta har suna hada baki gun tabbayarta Meke faruwa cikin jin zafi ta riqo hannun Umma tace Umma bazan iya tfy ba qafata ta kama Hassan ya qariso gunta ya kamo hannuta cikin tausa yawa yace zo In taimaka miki taka a hankali ya Dan jata cikin jin azaba ta danyi qara sai hawaye ke bin fuskarta tace tana yarfa hannu bazan iyaba Hamma bazan iyaba qafata zata balle ta qarisa mgn cikin kuka abin gonin tausayi cikin jin tausa yinta ya tsuguna ya ciccibeta gaba daya ya kontar da ita kan kujera duk sukai ta mata sannu cikin kulawa inna waziri ta bata mgunguna da addu,oin shi ya sake daukarta kamar yarinya ya mai data dakinta ya ta runqumoshi ta rinqa rera kuka yai shiru yana saura ronta ya gadai bata da niyar barin kukan sai ya Dan zame jikinshi a nata ya durqusa guiwa bibbiyu yace Fateema Dan Allah kibar kukanna haka ki gayamin meke damunki kinji wlh jin kukanki nake tamkar ana sokamin Mashi. cikin kukan tace Dan Allah Hamma ka kaini asibiti a ciremin cikinnan wlh cikin zai kasheni in baka cireminba ..........
Da sauri cikin razana da jin furucinta yace haba Fateema anya kuwa kina cikin hayyacinki cikin nawa kike cewa muje a cire ai zafin ciwo ba shine mutuwa ba kuma in ba so kike a illatakiba ya za,ayi cikin da ya shiga wata 7 a cireshi haka ya rinka dannarta d bata baki Amman abin yaci tura duk randa qafar ta tada azabarta sai tai ta kuka ita dai a cire cikin har su Umma ta gaya musu kokuma ta zauna tai tamasa kuka ita kam ya maidata gun bappanta gashi cikin ikon Allah da isarsa cikin tunda ya kai wata 7 din sai ya rinqa wani irin girma na ban mmk qafa kuma sai qaruwa take jikinta kuma da fuskarta sai wani kyau da kyan haiba take ga wani annuri da yake wanxu a jikinta..


By garkuwan Fulani
[4/12, 6:14 PM] Aisha Aliyu Garkuwa: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
Y'ar Fulani part 50 Na Aysha Ali Garkuwa
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

Yau Alhamis tun da safe da qafar ta kama har yanzu da yamma taqi sakewa ko sallah ta kasayi ga uban ciki a gaba ya girma tamakar Na watan aihuwa ga abinci Amman ta kasa ci doctors kusan 5 suke ta zirga zirga a kanta Amman qafar taki naduwa sai tana miqe zat an murza qafar har ta gaji dama shi kam Hassan tana ganinshi zata kamo hannushi ta rinqa surfan kuka ita dai aje a cire cikin Zainab kam itama kuka sosai take tayata da Zubaida Na,ima ko cewa tai indai haka ciki da aihu yake ase sai ta godewa Allah Hassan har tsoron shiga gunta yake Dan abinda zata cemai shi kuma bazai iya mata yadda take son enba Dan baya qaunar abinda zai taba lfyarta lallai yana son baby Amman sonta kuma da banne a rayuwarsa yakan shiga damuwa da rudu inyaga tana Neman abinda bazai mata ba bayan sunyi la,asar ya shigo dakin ya sameta dasu Ammi ya zauna gefenta ya kalleta cikin tausayawa yace ya qafar ta fara sakewa ko ? ta kalleshi cikin yanayi anya kuwa kana tausayamin ta tura baki ta murxa ido alamar zata fara sabon nata cikin kukun ta kalli Ammi tace Ayyah Ammi Dan Allah ki sashi ya kaini a cire cikin ta kamo hannun Umma tace Umma kuyi mishi mgn ya kaini a cire cikin kar ya kasheni ko ya maidani gurguwa Ammi ta kalleta cikin tausayawa tace kiyi haquri fati ai in an cire cikin kema zaki cutu gashi baiyi qwariba kuma ma ai komai da lokacinsa ta daqo ta kalli Ammin ta fada jikinshi tace toh Ammi kice ya kaini gun bappana ta fada cikin kuka tace Ammi tun da nazo garinanfa sau daya naga bappana randa yazo daurin aurensu Nazir inna takam ban sake ganintaba kusan shekara 5 ban gantaba Hammana ka kaini Dan Allah kar Na mutu ban sake ganintaba
Cikin kulawa Ammi da Umma sukace zakije Fati zai kaiki kinji ko kontar da hankalinki suka fita suka barsu
a parlor Ammi da Umma suka yiwa maimartaba bayanin komai cikin mmk yace Amman dai Hassan halinshi sai Allah ace kana zaune da yarinya ka hanata ganin iyayenta kai kuma kamar Dan yaye kullum sai kazo gun naka iyayen a take ya bada damar su shirya gobe jumma suje da kanshi ya shiga dakin ya samesu tana kwance a gefe shiko ya riqe kai da hannu bibbiyu ya kallesu da kyau yace Fateema ki dina kuku Hassan ka shirya gobe zaka kaita garinsu aiko cikin jin dadi ta rinqa godiya wani farin ciki ya rufeta Abban Na fita ta Dan ja qafar da qarfi ta matso gunsa tace Hamma tashi ka tayani shiri wancan babbar jakar zaka miqomin insa ka yana ya kalleta da kyau ganin yadda lokaci daya ta koma cikin farin ciki shima sai yaji sanyi a ransa ya jawota ya rinqa tsokanarta.

Garin Ardo yabani gari mai dadi gari mai tarin albarkatu d ni,imomi garin Fulani da ma noma garin dake qushe cikin qoramai da itatuwa masu dumbin tarihi a garin buba yero tun da suka iso kwadan ta hanqo tsaunukan dake yiwa garinsu katanga da babban titinnan da zai kaika dadin kowa isakar wurin mai sanyi ta fara ratsa jikinta ta lumshe idanta ta rinqa ajiyar zuciya tana shaqar qamshi. Furannin tsurran wurin ta maida kanta ta jingina da kujarar motar dai dai lokacin Hassan ya Dan karya kona ya dauki yar siririyar hanyarnan da zata sadasu da wuro yabani a daidai lokacin ta bude idanta ta zubawa lambu kam dake zagaye dadu ido cikin mmkin gani wani irin canji da wurin ya samu hanyace lafiyeyyiya ke kwance daga gefe kuma anyi burtali Na zamani gun da dabbbobi zasu bi can Dan gefe kuma qoraman ne aka sarrafasu cikin hikima akai kwami kwami inda dabbobin zasu sha ruwa ga can wani faffadan fili kuma da aka zagayeshi da woya mai raga raga inda dabbobin suke rayuwa ga wasu abubuwa kuma Na tatsar nono cikin sauqi
kai saiwa lissafin yadda garin yabani ya zama babban aikine ita dai ido kawai ta ware har suka isa farfajiyar qofar gidansu abin mmk a nan yake cikin mmk ta kalli Hassan dake ta murmushi ganita cikin farin ciki ga wani ya nayi da yake tunawa Na zamansa a nan gun tsawon wani lokacin da ya shude abin ya rinqa dawomar kamar a film duk ran jumma,a Hassan a garin yabani yake sallan jumma,a anan yake cin abinci Amman duk zuwan da yake bai tabajin shauqiba sai yau da yazo da Habibatinshi tace Yaya ko dai mundanyi batan hanyane ya kalleta cikin ido da shauqi ya shafa cikinta da ya fito ras a jikinta yace Fateema kin taba ganin inda da ya manta gidan ma haifinshi tace a a yace toh ke dai biyoni ya bude qofa ta fito ya zagaya ya bude mata gefenta tana sako qafa bappanta Na fitowa daga wani wuri da yafi kama da asibiti mai kyau Na zamani ganin Hassan ya nufoshi da fara,a yace a a Dan Bappa kana hanya kenan yau baka iso da wuriba duk bai lura da Fateema dake ta dingisowa ba ta samu ta qarisa gunsu Bappa yaci gaba da cewa muje ka karya nasan ba abinda kaci ya juya kenan ya hanqo Fateema cikin yanayin haiba da ribar aure a jikinta gonin Sha,awa da tausayi cikin mmk da tsantsar farin ciki ya iso gareta yace mamana Allah sarki mamana ya Sa hannu ya karbi jakarta cikin qaunar yarsa yace Alhamdulillah mamana yau innarki zata samu farin ciki yau zataji saukin kewarki dake damunta Fateema kam sai hawaye take zubdawa har suka isa cikin gida da farin cikin ya dauko abin zama ya shinfida musu a qarqashin bishiyar manqoro da dabine dake tsakar gidan yana mai kiran inna ta fito daga cikin kitchen tana riqe da aqoshi da sabon faifayi rufe dashi aiko ganin yarta guda daya tilo yau kam inna farin cikinta yaqi boyuwa da sauri ta iso gun ta tallabo Fateema ta zauna ta kalleta cikin tsatsar qauna tace mamana kenake gani ba mafarkiba tai dry ta fada jikinta cikin jin dadi tace inna kema kinyi kewata Amman shine kika qi zuwa ki ganni har tsawon lokacin nan bakijin lbr Na Bappa yai dry yace ai mukam kullum muna jin lbrinki kullum jumma,a sai mai gidanki yazo garin nan anan mike sallan jumma,a tare kinga yadda ya gyara mana rugarmu gashi har asibiti da masallacin jumma,a ya gina mana Hassan yai dry yace Bappa kenan Na gina ko ka gina tunda kaqi barina nai da kudina kawai saida kasa naka inna tace ai ka kyautamin Dan Bappa yau ka kawomin mamana Bappa da kansa ya rinka kawo musu abinci Dan dama sun San Hassan zai zo komai an dafa mai abin da yakeso inna kam Tamkar zata hafiye yarta takeji

Haqiqa Fateema tayi mmkin sabo irin Na Bappa da Hassan sun zama uba da daa sat komai Na duniya sai sun shawarci juna duk yanzu Hassan ba jin kai din sai alkunya da qauna Bappa yace innar Fateema tashi mubasu gu su karya ta miqe suka tf Fateema ta rinqa bubbude kwanukan abinci ba abinda babu a kwashi cike yake da zabbi Inna tamusu irin gashi sunan Na mutan daban Fulani ga daya kwanon kuma tuqeqqiyar shinka fashe da miyar danyar kubewa tasha man shanu ga naman rago mai zaqi da taushi ya daddage a ciki sai qoriyar damemmen nono da fura Dan asali gangariya sai daya koriyar kuma madaran shanunne tafashshe sai daya koryan kuma fruits ne cike sai kwanon Sha da yake cike da run sanyi da yake fitowa ta cikin dutsen lammunsu daga dai kwariyar kuma kunun nonon shanune da garin danyar shinkafa fari tas Hassan da kanshi ya samusu tare sukaci tai mmkin mijinta sosai yadda ya zage yake cin abincin Ya dauki damemmen nonon da ludeyin duma mai kyau yasha zane ya rinqa Sha yana lumshe ido ta kalleshi tace dama kana cin abinci cikin son ran kane yace kamar Yaya tace toh gani nai sai mama tana saka dole ya danyi dry yace ai abinci Ammi Na da ummana da innata bana haufi a kai sukai dry

dama kullum in yazo sai sunje lambu tare da Bappa su kuma yi tatsar nono tare haka yauwa suka shirya tafiya aiko itama tace zata Bappa zai hanata yace ai bazaki iya tafiyarba Hassan yace abarta zasuje da mota haka sukaje yai ta daukarsu pictures cikin lambun sai garfe 1 suka dawo sukai shiri suka tf masallaci itako da innarta sukai ta hirar yaushe gamo biyar dai dai suna ta hiratsu ya kalleta yace Fateema ki shirya mu tafi ko kinga yamma tayi ai a take sai hawaye tace Dan Allah Hammana ka barni ni sai Na huta yai shiru yana kallonta Bappa yace a a mamana tashi kibi mijinki kinji ko kinsan bana son taurin kai kibi umurnin mijinki Hassan ya kalleta yace aima yanxu bazaki kuma dadewa baki zoba inkin aihu dai zan kawoki kuma innama zataje ita dai sai hawaya badon tasoba suka tursasata ta bishi Bappa yasa su gaini suka dauko jarakunan man shanu da qworen qwon zabbi da Na nono sai zabbin aka loda musu a mota ya hada mata mgnin qafar ya bata tana kuka suka tafi haka ta rinqa rusa mai kuka a mota yai ta lallashi taki har suka isa cikin gombe kai tsaye sahara hotel ya wuce da ita daukarta cidak yayi ya shige da ita har kan gado

Ta rinqa tureshi ya yajawota ya Dan matseta tai qara ya shafa cikinta ya lonqobar da kai cikin shogoba kamar yaro yace ayyah Habibati yau kadai a taimakamin tunda yau baby Na ta sakar miki qafa a tai maka a dagawa Abbanta qafa shima ya Dan samu nitsuwa da Sa,ida ya kara jawota jikinshi ya fara kiss inta ta rinqa tureshi cikin shogoba da fushi tace ni dai ka barni Na gaji ya Dan kwanto jikinta yace plzz my Habibati wlh ina cikin matsi ki taimaka min Na tuba tace toh ni da qaton cikinnan ya zanmaka ya danyi dry yace ni dai bani ixini kawai ni zansan yadda zanyi Na samu abina ya jawota ya jinginar da ita jikin gado cikin hikima ya samu gamsu ya rinqa sabbatu sai qarfe 11 suka isa gida aka shigar musu da tsarabarsu su Ammi da Umma sukai ta gdy ya bawa Abba ma saqonsa shima yaita gdy

Yanzu dai ciki ya kai aihuwa ko yau ko gobe kuma qafa ta sake tada tsiyarta ba dama..

```Sai dai Fatan. Allahu rabbi ya sauki dukkan yan uwa musulmai lfy ya bawa kowa gajerar naquda```


By garkuwan fulani
[4/12, 6:14 PM] Aisha Aliyu Garkuwa: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
Y'ar Fulani part 51 Na Aysha Ali Garkuwa
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

Yau dai ta samu qafar da Dan sauqi har ta fito babban parlor ana Dan taba hira da ita Zubaida Na zaune daga gefenta duk mgnar da suke akan shirye shiryen auren zubai danne da Na Amir tun dazu Hassan ya shigo bayan gaisawa da sukayi bai sake cewa komai ba sai dai ya qurawa matarsa ido in ta kalleshi ya danyi murmushi ya murza manyan idanunshi da sukayi ja suka qanaqce sai ya Dan kwanta jikin kujera ya shafa kwanceccen sajenshi ya Dan leshi lips
inshi sarai ta gane damuwarsa sai dai tayi kamar bata ganeba can ya danyi miqa da 😡 Hussain ya kalleshi cikin wasa yace kai doctor naga dai ba aikin dare kaiba jiya da zaka xo kai ta mana 😡 ya dan harareshi yace to sarkin Sa ido can dai dabara ta fado mai ya dauki phone enshi ya tura mata message kamar haka (ayyah Habibati ban sanki da hakaba bafa plzz ki tausa yawa Hammanki wlh Na kasa daurewa Na kasa sarrafa kaina ki ji tausayin mijinki kar nashiga wani hali ) ta karanta ta kalleshi ta share ya sake tura mata wani sai taqi karan tawama can dai sai ya miqe yace toh nikam sai da safe Dan ina da aikin safe ya kalleta ya danyi dry mugunta yace Fateema kizo muje ki bani pakalana Dan ina da buqatarsa yanxu aikinshi zanje nai ya qarisa mgn yana tsareta da ido tace ni kuma bata qarisaba ya katseta taso sauri nake Umma tace jeki bashi sai ki kwanta ki huta haka ta tashi da qyar take takawa tana shiga dakin

Ya jawota jikinshi ya mannamata kiss a lips enta ta Dan tureshi ta zauna bakin gado ya maso

Please Login or Register in order to submit comment