Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take tamkar ma itace maryam din
''wani hanin ga Allah baiwa ne maryam,yau gashi Allah ya musanya miki da jabir,sun sanya bawan Allah a tsaka mai wuya har yau yana cikin damuwa,shekaran jiya yazo gidan nan yake tambayar abban fadil ke,yana son ya nemeki amma wai kunyarki yake ji,shegiyar yarinya marasa tsoron Allah itavda uwarta,duk jabir ya fita hayyacinshi kmar bashi ba,roqon Allah ne masa ya dawo cikin tuna ninshi cikin lokaci qanqani haka''


ajiyar zuciya ta saki
''duk wanda ya debo da zafi ai bakinsa raliya,nikam wanna ya riga ya wuce tamkar wani mafarki na daukeshi''
ta zura hannunta cikin jaka ta soma laluben wayarta dake ringing hade vibration ta cirota,kiran abdur rahim ne tasan shi dinne tun kafin ta ciro saboda special tune da ta sa masa
''ranki ya dade duka yau ban jiki ba ko cigiya ta baki yi anya kuwa''ya fada cikin salin zolaya bayan sun gama gaisawa
murmushi ta saki
''yau na tashi ne cikin sabgogi amin afuwa''
''ayyah,da kinyi magana ai da nazo na tayaki,ina fata basu wahalmin da ke ba''
''alhmdlh tunda tuni na kammala yanzun nake shirin in koma gida''
sai ya danyi duf kana yace
''me yasa baki tambayeni ba da zaki fita,saiki dinga fita kanki tsaye maryam ana ganemin ke''
murmushi ta saki
''mantuwa nayi ashe fa yanzun ina da miji,baza'a sake ba''



''matsalar ban iya fushi dake maryam,yanzun dai sgikenan kimin kwatancen gidan da kike zanzo yanzun nan na maidake gida,naga hadari na haduwa kada ruwa ya dakarmin ke ya barni da zazzabi''
ba qaramin nishadi maganar ta saka ta ba ,take ta masa kwatancen inda take din sukayi sallama ta ajjiye wayar
suka hada ido da raliya tare suka saki murmushi
''gaskiya na fuskanci ba qaramin ji dake abdul din nan yake yi ba,Allah ka nuna mana wannan rana''
dariya tayi gami da dukan gefan cinyar raliyan tace
''har ya kama qafar nasir abban fadil''suka sake sa wata dariyar raliyan na fadin haba wane mutum


minti goma wayar ta sake kadawa,abdur rahim tayi tsammani shi dinne kuwa
''kiyi min afuwa maryam zuwa na bazai samu ba wani aiki ne na gaggawa yanzu aka turamu dole kuma na kasance aciki idan ba haka ba akwai matsala,amma kiyi sauri don Allah ki koma gida hadari ne sosai a garin kada ruwa ya tabaki''
macace mai sauqin kai da fahimta don haka tace masa
''babu damuwa Allah ya bada sa'a''
ya saki ajiyar zuciya
''na gode da kika fahimceni sai munyi waya''


ta dubi raliya bayan ta miqe tana hada jakarta,ta tavbata hadarin ne don tuni garin ya lumshe har ta soma jin quginsa
''wucewa zanyi raliya an samu matsala abdul bazai samu zuwa ba aikin gaggawa nebya taso muau yanzu a office''
''a'ah,yanzu da uban hadarin nan zaki tafi?ki jira abban fadil ya dawo sai ya kaiki''kama baki tayi bayan ta gama rolling mayafinta
''girkin kuma na barwa wa?,so kike kenan yau abdallah ya samu nayi ko,cikin watan nan ya tairi wani abu ko kunu ne idan bani nayiba sai ya gane,yanzun sai yace a salary dina''
ta dage girarta sama
''haka ne fa,muje in taka miki,amma jirani in shiga in fito''cewar raliyan tana shigewa bedroom dinta na qasa


kwalbar turare ta fito da shi hade da baqar leda qarama ta miqa mata
''turaren da kike ce min kina son irinsa nasa abbn fadil ya aiyo manaamma kiriqe da kyau saboda yana leeking,sai bra din nan qualitative one da mukayi maganarta jiua da muka fita na siyo mana''
''kai qawata,bani da bakin magana,Allah ya raya mana fadil ya bar mana zumuncinmu,ya tsone idon maqiya''
''ameen raliyan ta fada tana bin bayanta,haduwar jadarin ya sake rudata har ta kasa saka kayan cikin jaka,a bakin get suka rabu ta soma sauri gashi ita ba gwanar saurin bace


har ta kai bakin titin su raliyan bata ga abun hawa na haya ba,kusan dama haka yanayin unguwar tasu yake ko jama'a baka fiya gani ba,bare yanzu yanayi na azumi kowa yayi likimo cikin gida,hankalinta bai daga ba sai data tsaya atitin,taga motoci dake karakaina ma baifi ka irga au ba,adaidaita uku ne suka wuce biyu daga cikinsu duk cike take da mata dayarkuma maza ne cike har gaba kusa da mai tuqin,a hankali iska ta soma kadawa mai qura alamun dake nuna hadarin ya gama nuna a sama sauka kawai yake da buqatar yi,addu'a kawai takeyi cikin zuciyarta a haka ruwan saman ya soma sauka


tsamo tsamo tayi don ya fara jiqata ta soma hade jikinta guri daya,motoci uku ne qirar land cruisser baqaqe wul hatta da glass dinsu suka tsaya a gabanta,gabanta yayi mummunan faduwa,tuni ta somacwaige waigen neman inda zata fake idan gudun ceton rai ya kama


glasan motar farko nagaba mazaunin mai tuqi suka sauka qasa,hassan ta gani daya daga cikin direbobin abdallah,sai a likacin taji ta samu nutsuwa,murmush yayi nata itama ta maida masa
''madam yi sauri ki shigo kina ta jiqewa''
taji dadi sosai kuwa,da saurinta ta qaraso ta bude mazaunin gaba ta shiga tana fadin
''na gode qwarai,amma ba tare kuke da og.....''
''me muka tsaya yine hassan?''
muryar data fito daga sit din baya ta katsse mata sauran magan
''nun dauko madam ne''ya fadi yana qoqarin tayar da motar
''waya baka izini ko tsabar iya sayawa mutum raini ne?''
''sorry sir,naga gida zamu ne,kuma itama gidan zata.....''
''ni na gaya maka haka?''ya tambaya murya a kaurare


''am sorry sir naga madam nada kirk.......''
abdallah ya katseshi ta hanyar fadin
''mtswee,shutup malam sauka ka barmin mota ka koma motarsu auwal''
da saur maryam ta kuma riqe jakarta wadda garin saurin ledar hannun ta har ta subuce ta fadi qasan motar bata sani ba
''kayi haquri,ni ya kamata na fita ba hassan b.....''
''hey,bana son iyayi shi nace ya fita din bake ba''


tuni hassan ya bude motar ya fice ganin hakan ya sanya itama ude na bangarenta tana qoqarin fita
''idan kija sake kika fita sai na karya sillar qafar taki inga ta rashin kunya''
tilas tana ji tana gani ta koma ta zauna
''rufemin mota malama don idan ruwa ya jiqata sai kin busar da ita tas a yanzu yanzu''taja qofar garam ta rufe cikin haushi,tana iya gano ragowar motocin suka zagayesu suka wuce


mujallar da yake research kanta tun dazun ya sake janyowa ya bude yaci gabavda karuntunshi hankalinshi kwance tamkar yana cikin dakinshi ne,sanyin a c din motar ya soma takurata gashi tayi mata kusa da yawa,tuni kanta ya fara sarawa ta qudunduna gu guda tarw da jingina jikin makarin motar ta lumshe idanunta tana ci gaba da jin yadda ciwon kan ke dada yin gaba


'yar qaramar qara taji tamkar ta waya ''siiit''a hankali sai dumi ya maye gurbin sanyin ac din,bata tantama maidashi akayi banaren dake bada dumi,duk da taji dadin hakan amma babu abinda ya rage mata daga ciwon kanta


mintina kusan arba'in basu tafi ba kamar yadda ruwan bai tsagaita ba,ta bude idanunta a hankali ta miqe ta zauna daidai,a karo na biyu ta kuma sanya hannunta kan mabudin qofar don ta qudiri aniyar ficewarta zatayi kome zaiyi mata saidai yayi,saidai taqi buduwa da alamu an saka lock,ya ajjiye mujallar hanun nashi ya jawo baqin space ya mannawa idanunshi sannan ya bude 'yar qaramar kyakkyawar baqar lemar dake kusa dasji ya fito ya dawo mazaunin driver


amadadin ysyi hanyar gida sai taga sun csnza titi,batason kulashi amma ya zama mata dole
''ina cewa gida zammu ko''
banza yayi da ita,ta qufula amma bata fasa sake fadin
''girki fa na can na jira na gashi yanzu hudu harda rabi''
''karki cika ni da hayaniya,baki da zance sai na girki kamar dinshi aka halicceki,ai bake daya kika iya girku cikin gian ba ko''
ya fada udanunshi na bisa kwalta,bata sake tofawa ba ta maida kanta gefe daya


cikin wata unguwar taga sun shiga wadda take kama da tasu mamun wajen kyau da tsari,qofar wani katafaren gida taga ya tsaya,ita kanta sai da ta bi gidan da kallo,duk kyau na gidansu mamin wanna ya dokeshi,bude motar yayi yay ficewarsa ba tare da da yace mata komai ba


zaman kusan awa guda da rabi tayi kafin ta sake ganin fitowarsa,a dan bakin qofar ya tsaya kafin ya qaraso tana iya hango jikin wanda suke magana tare,da alama macece don ga gefan mayafi nan,ba qaramar qufula tayi,ba cikin zuciyarta
''zance yazo kenan ya barni a mota ko yaya?''ranta sai ta kuma ji ya baci,ya bude motar ya shigo
''zance da ranar Allah cikin watan azimi,wanne wane irin tsari ne''ta ja tsaki,saidai cikin subutar baki tsakin ya fito


juyowa yayi kalleta
''wa kike ma tsaki?''sai ta juyo tana kallonshi itama
''idan kika sakemin tsaki sai kin fita min a mota tunda bada kudinki aka siya ba''sai idanunta suka wal
''daina kallona''ya fada bayan ya dauke kanshi da sauri daga cikin idanunta
''kada ki cuceni''ya fadi can qasa yana lumshe idanu tarw da yiwa motar key,bata kawo komai cikin ran ta ba ta dauke idonta cike da jin haushinsa

🎄🌲🎄🌲🎄🌲

Ashirin ga azumi mami ta bata kayan sallarta,a dinke suke dinki ne na gayu wadanda suka mata cif a jiki,atamfofi uku lace daya material daya,sai codelace shima daya,duka atamfofin dogayeb riguna aka mata don mamin ta fuskanci tana sonsu,jaka biyu takalmi biyu sai mayafi biyu hijabi daya,sannan tace ashirin da biyar ga azumi zasu fita sai ta zabi fashion da zatayi amfani da su,bata fasa yiwa mami gidiya ba duk da ta gaya mata diyarta ta yiwa no need tace sai ta gode mata,godiya kuwa ai tamkat wajibi ne tayi mata don ko daga gurin mahaifinta bata taba samun makamancin irin wannan gatan ba


abida kam akwati guda medium abdallan ya hada mata bayan takurawar da mami tayi masa kan ya hada matan,don shi totally baiyi niyyar mata komai ba


cikin irin kyautar da mamin ke yawan yi mata ta fidda atamfa biyu ta baiwa tela ya dinkawa mamanta,ta siya mata mayafi takalmi da jaka,albashinta na watan ciki ta cira ta baiwa hibdatu tayi siyayyar salkarta babanra ma shadda ta siya masa kala biyu ta hada mishi da kudin dinki da takalmi da hula daidai,kai kada ksso kaga baqinciki,ina wuta a saka maman da iyalsnta,godiya kam gun baban ba'a magana
''sai yanzu nasan na haifa,yanzu ne na fara cin albarkar haihuwa''baban ya fada lokacin da yake gwada hular da ta kawo masan


''oho dai,wlh malsm ka guji ranar da zaka karbi shegen jika cikin gidan nan,ka gama cin dadin dai wuyar na tafe,shi yasa gata nan har yau babu mashinshini yo kowa yasan aikin tsiyar da take aikatawa''
inji baba hadizar don daga ita har huwailsn babu wanda yasan da zancan kawo kudinta,ranar kamar Allah ya kadasu duk suka fice unguwa suda qananun 'ya'yansu,huwaila tayi gurin boksn boginta ita da uwale hadiza ma ta bazama ga nata bokan,sunacan yawon asara har yan kawowar suka tafi,'yammatan da zawarawan kuma na nade a gado suna bacci don wadan nan sukan kai sha biyu da rabi zuwa daya basu tashi ba


huwaila kuwa cewa tayi''mu namu ai shegensu mukayi muka shigo dasu gidan ko,ko ince tsinannu ne''shidai babu wadda ya kula cikinsu ya kwashe kayanshi ya shige dakinsa

🍃🍂🍃🍂🍃🍂

Qarfe goma suka dawo daga siyan kayan kwalliya da suka fita harda mami da abida,tayi sallama da mamin ta shige dakinta don da wuri take son yin bacci ta tashi akan lokaci sallar dare saboda yau an kai azimi ashirin da shida zuwa anjima daren ashirin da bakwai zai shi daren da akesa ran dacewa acikinsa


zuwa sha daya na dare takammala komai ta haye gado bayan ta gama addu'o'in kwanciya ta karanta saqon abdur rahim fuskarta fal da murmushi,kusan cikin watn gaba daya wayarsu bata fi aqirga ba sai tex akai akai,yace shikam bazai iya jurar jin muryarta ba,tana shirin kashe wayar kira ya shigo,ta zubawa lambobin ido tana kallonsu,tana tunanin inda ta taba saninsu


tabbas ta taba sanin numbers din,har wayar ta tsinke ta kasa dagawa,second biyar tsakani wani kiran ya kuma shigowa,jiki babu qwari ta sanya hannunta ta daga ta kara akunnenta
''assalamu alaikum wa rahmatullah''itace abinda yavdaki sodon kunnenta,mummunar faduwa gabanta yayi,babu inda zata ji muryar ta kasa ganeta,amma tan tama take kiran nata ne ko batan kaine,ta sake cire wayar akunnen ta tayi ta kuma duba screen din wayar mai kiran dai na bisa layi kuma ita din aka kirar




*mrs muhammad ce*👑


📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[9/17, 12:54 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*

▶3⃣4⃣

*_daga abu hurairah Allah ya qara yarda da shi yace:an tambayi manzan Allah s a w wanne musulmi ne yafi falala?,sai yace:wanda musulmi suka kubuta daga sharrin harshensa da sharrin hannunshi(ma'ana bai cutar da kowa da harshensa ta hanyar magana,ko kuma da hannunshi ta hanyar ayyukansa,daure ka/ki zama daga cikin musulmin da suka fi falala,abun ba wuya 👌🏽matuqar ka jajirce kafi qarfin zuciyarka,Allah ta bamu iko ameen)_*

''wa alaikumus salam''ta fada asanyaye
shiru ya dan ratsa tsakani kadan
''da alamu baki ji dadin jina da kika yi ba ko maryamu?,hala ma kin manta da ni?''
''ko daya,ban kuma mance da kai ba''
''da fari kafin nace momai maryam,nasan bani da kalmomin da zasu gamsar da ke gurin ban haquri,amma duk da haka ina roqarki don Allah don annabi ki yafemin,ba da gangan abinda ya faru tsakaninmu ya faru ba,bada sani na bane maryam,ki yafewa jabir masoyinki''

tausayinshi ya kamata ta dan kumshe idonta kadan ta bude
''kada ka bata bakinka gurin bani haquri jabir,tuntuni gaskiya ta dade da yin halinta,anyi walqiya komai ya bayyana''
yaja dogin numfashi kana ya sauke ajiyar zuciya
''alhamdulillahi rabbil aalamin,dukkan godiya ta tabbata ga Allah,babu shakka ke din jaruma kuma nagartacciyar masoyiya ce,bana tantama zaki zama mace ta gari uwa ta gari gurin 'ya'yanta,bazanyi nauyin baki ba ba kuma zanyi qauro ba maryam inason ki bani damar fitowa neman aurenki karo na biyu,tare da cikakken fatsn babu wani da ya sha gabana''

sai da gabanta ya fadi,tayi shiru tana son daidaita bugun zuciyarta sannan daga bisani tace
''qaddara ta riga fata jabir,Allah ya qaddara run da dama ni ba matarka bace,hakaza matar mutum kabarinsa,bai wuce sati biyu da kawo kudin aure na da wani ba''
''la haula wala quwwata illah billah''ita ya dinga maimaitawa tsawon mintina biyar
''yanzu kina nufi maryam na rasa ki kenan,zaki auri wani na?,ki bani dama maryam mai rabo shi zaya samu tunda har yanzu ba'a daura aurenku ba balle kice kin haramta a waje na''

''kai mai sani ne jabir bakin gwargwado,ka sani cewa nema akan nema haramunne,baya ga haka ma daga ni har kai babu wanda aka bawa qudirar rubuta kundin qaddararsa da kansa,kuma buwayin sarkin dake rubuta msna din mai dumbin adalci ne,babu yadda za'ayi ya rubuta mana abinda zai zama zalunci ne a garemu''
''haka ne maryam,alhndlh Ala kulli hal,na gode maryam,na gode matuqa da gaske,bazan taba iya mantawa dake cikin kundin rayuwata ba,na barki lafiya''

tafi minti biyar riqe da wayar ra kasa ajjiyeta,tausayin jabir dinne kadai ke dawainiya da ita,babu shakka bazata iya manta dumbin alkhairansa gareta ba,koda ta tashi sallar dare bata mantashi cikin addu'o'inta ba,ta roqa masa alkhairi mai yawa kamar yadda a baya yayi nufinta da shi

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

Washegari mai lalle tazo yi musu,babu yadda mami batayi da abida ba amma qememe taqiya,tabe baki tayi
''nifa mami ba za'a batan hannu ba hakakawai da wannan abun''
''banda abinki ai shi jan lalle ga mace sunna ce baya ga haka ma ado ne''inji mami
ta sake ya mutsa fuska
''um um,a muku dai,mukam a turkey bamu irin wannan abun''ba wanda ya kuma tanka mata cikinsu nanta kwanta tun tana kallin qunshin har bacci yayi awon gaba da ita

kamar ko yaushe suna table don cin abincin buda baki u ukun maryam mami da abdallah,ta zubawa mami da abida ta soma zuba na abdallah,ya dago da sauri don yaga iya wanda zata zuba din don vaiso ta cika masa plate kamar na jiya,idanunshi suka sauka kan zara zaran fararen yatsunta da qunshin yayi kwanciyarshi kai ya sake fidda kyawun hannunta,farar fatarta ta sake shar

Zanen ya burgeshi duk da ya saba gani lokaci lokaci gun maminshi,duk kuwa sanda tayi din tun yana yaro ya dinga cewa tayi kyau kenan,maryam ta janye hannunta bayan ta ajjiye nasa plate din ta koma mazauninta,sam babu wanda ta lura sai abida,kishi ya cikata har taji kamar ta guntike hannun maryam din,ya janye idanunshi daga kan lalken suka hada udanu da abidan
''ke ina naki kwalliyar?''
''abida kam ai ta manta gargajiyar al'adarta,tace bataso bata mata hannu za'ayi,bayan shi kanshi ma ganine''
caraf abidan tace
''naga kamar ya burgeka ko,ba damuwa sai amun gobe''

tabe baki yayi ta daga kafadarshi hade da ware ya tsunshi
''no,idan ta nine kada ki sauya ra'ayinki ki bata hannunki''ya qarashe zancan yana jan plate dinshi ta soma cin abincin

zahariyya ce tayi sallama hannunta duka biyun dauke da foodflask masu azabar kyau da tsada,fuskarta a washe da faea'ar data qiqirarwa kanta ta qaraso gun,ta fara da dora flask din duka saman teburin wadanda tunda aka shigo dasu maryam take jin matsananciyar faduwar gaba ta kuma kasa daina kallonsu,mami ta gaida kana abdallah,tsakanin ita da abida kuwa babu wanda ya kula wani kowa na ji da danbanzan girman kanshi rawanin tsiya

''favourite food na ya abdallah nene ra tashemu sai da mukayi masa wai yadda ta saba sanda alhj baaba(alh abdulkareem mai nasara kenan mahaifin abdallah)yana raye wai yanzun ma ba zata fasa ba''
murmushi mami tayi tana janyosu gabanta tare da fadin
''kai kice mata kam mun gode qwarai,kamar kuwa tasan yau bamuyi girki ba nace maryan ta bari sai sahur aikin yayi yawa''inji mami sanda take hude flask din,rake kuwa qamshi ya cika gurin
''ki mata godiya''inji mami sanda zahariyyan ke nufin fita
''zata ji kam''ta amsa mata lokacin da take qoqarin sanya qwayar idanunta cikin ta maryam a fakaice,cikin sa'a kuwa suka hada idon,wanu mummuna kallo mai cike da gargadi da jan kunne tayi mata kana ta fice

Gaba daya ta saki cin abincin ta zurfafa cikin tunanin yadda zata salwantar da abincin ba tare da tabar kowa ya dandana ba,tayi imani komai zasu mata ba zata iya bari tana gani gaban idonta wannan ahli su salwanta ba,qarshen butulcin da zata musu kenan wanda ba zata iya yafewa kanta ba har abada,cikin haka taga mami na kiciniyar bude food flask din zata zuba,da sauri ta miqe tana fadin
''mami barshi in zuba miki mana ''tuni har ta isa gabanta ta karba don kada ta yanke mata hanzari tace ta barshi,ta jawo flask din miyar gaban table din sosai ya zama rabi kan tebur din yake zaune rabi kuma free ba matokari,sai ta jawo na abinci ta bude,da plate a gabanta amma sau tayi dabarar miqa hannunta tavdauko na can sashen da abida ke zaune

Tana daukar plate din ta sakeshi kan flask din miyar take nautin tangaran din ya rinjayeshi sukayi qasan table din suka tarwatse kan tiles,tangaran din ya koma piece,taja baya da sauri tana salati tate da kallon gun da abincin suka kife
''subhanallahi ya haka maryam?''
''for god sake mami yanzu wannan wane irin kidahumanci,ita din qaraman yarinyace da zata kifar da abinci flask biyu,kayi magana kuma yanzun mami ta ji haushinka ta saka a black list''ya qarashe maganar cikin bacin rai yana yayyarfa hannu da jujjuyawa hagu da dama kan kujerar da yake zaune

harara ta balla masa sannan ta kalli maryam
''ina fata baki ji ciwo ba maryamu''
kai ta gyada zuciyanta na wani irin gudu gefe daya kuma tana hamdala ga madaukakin sarki da ya bata nasara a sauqaqe ta rabasu da abinda zaya hallakasu,ita ta tsaya ta gyara gurin duk da momi tace ta bari sai ta huta tukyn amma sam ta qiya,bazata iya ba don ko quda bata fata ya dandana abincin,balle ma ta tabbata ban da awa biyu ko uku indai da gubar abincin zai fara ratattakewa

ta gyara gurin tsaf ta kwashe bayan ta rage kadan ta samu yar roba ta zuba hade da miyarshi ta shige da shi dakin gadonta ta tura ahi qasan gado,sai da ta gama komai kafin ta kwanta ta jawo robar don dubawa,cikin awa uku abincin ya fita kamanninsa kamar wancan,batasan lokacin da hawaye suka soma zuba daga idonta ba

mutum abun tsoro Allah abun tsoro
yanzu dan uwanka bil'adama kake da buri yaci wannan abun?
waishin wanne rin laifi ne abdallqh ya yiwa mutanen nan ne haka da zafi da suke da burin rabashi da soron duniya?
sai kace mudin an mana wahayin tabbata acikinta?
kwana nawa ne kaima ka hada ya naka ya naka ka qara gaba?
koda shekara miliyan zakayi wataran dai sai sun qare din ka tafi.
itakam ko kadan batq ga abun morewa ba wajen cutar da wani bayan ka san cewa Allah bazai taba qyaleka ba sai yabi kadi,duk wanda yaci nanin nanin dole ta cishi

cike da kasala da mutuwar jiki ta shige toilet dinta tayi plushing din duka abincin ta wanke robar ta wullar a dust bin

🍃🍂🍃🍂🍃🍂

Sallah bikin daya rana,cike da walwala farinciki bikin sallah ya soma gudana cikin duniyar musulmi baki dayanta,sai a lomacin mayama ta dinga ganin dangin su mami da na mahaifin Abdallah,don kusan kullum ne sai sunyi baqi,saboda haka bata samun zama aosai,damuwarta daya ma kada abdur rahim yace zaya zo ya samu bata da lokaci sai gashi bai ma nemi zuwanba iyakaci waya sai saqon,barka da sallah daya turo mata na credit din dubu goma yace kuma ta jirayi kayan salarta duk ranar da zaya zo

Ta fuskanci ba kadan bane maso sun abdallah cikin danginsa daga na mamin har na abbaanshi,kishi ke hana abida zama ciin gidan tayi ficewarta yawo sai dare
''rashin sani yafi dare duhu''maryam kan fadi hakan cikin zuciyarta ko kuma tace
''bonono rufin qofa da barawo''a duk sanda taga abida na wannna haukar kishin nata don bata da masaniyar kai kudi abdallah daga ita har zubaidan bare salma da saddiqa da bama ganinsu ake ba,har ga Allah tausayinta takeji kan fadawa son botsatstsen mutum irin abdallah,wanda koda yana sonki zaki sha wuya da shi bare kuma baiyi da ke a ganinta

hudu ga salla suka fara samun sararawar baqin duk da ana cikin dai hidimar sallah da shagulgulanta
da la'asar ne babu dadewa da gama salla wayarta ta fara ringing,tana kan cinyarta din haka ba jinkiri ta daga,muryar jabir ta tsinta yana mata sallama,ta amsa masa kana suka gaisa amutunce
''mai yayi zafi haka ido zaici wuta maryam,a qalla dai ai ko barka da salla a kirani ayimin''
ta dan saki murmushi
''kayi haquri,na ahiga sabgogi ne da yawa,ayyuka sun kacame min kusan yaune ma kadai na dan samu kaina''
''gaskiya ne,ai manya dama sai da uziri''dariyar zolayan da yayi mata tayi,kafin tace komai ya dora da fadin
''ko zan iya ganinki,maryam?''tavdan fiddo ido waje kamar yana ganinta
''yanzu?''
''eh idan da zan samu yau din da nace miki na gode,amma da zakimin alfarma da sai mace miki mu hadu gobe''

tunaninta daya ina zata ce mishi su hadun?,sam bata da sha'awar kawoshi nan gidan kamar yadda ko kusa ba zata yarda su hadu gidansu ba
ajiyar zuciya ta saki
''babu damuwa,muna iya haduwa gobe kamar hudu na yamma a gidan zoo ko?''
''kin ko san a itin kwanakin nan cika yake,anya zamuyi magana anutse kuwa?''
''eh nafison gurin jama'a din ai,kuma akwai bangaren da zamu iya zama da babu cikowar''
''shikenan babu damuwa na gode,amma baki tambayeni,mai yasa nake da buqatar mu hadun ba''

murmushin ta kuma yi
''a tun sani na da kai da alkhairi,na sanka,don haka yanzu bazan canza in maka zaton sharri ba,kaga kenan ina tsammatar jin alkhairi ne daga bakinka''sosai yaji dadin irin shaidar da tayi masa,har yau bai fasa yaba kyawawan halayen maryamu ba,kowa tana masa kallon mutumin krki ne kamarta,hakanan tana kowa kallin mai kyakkyawar zuciya kamar yadda ita din take

🎄🌲🎄🌲🎄🌲

Qarfe hudu suka fita daga gidan zuwa gidan zoo din ita da hindatu,dukkaninsu cikin kwalliyar atamfa suke riga da skert,sunyi kyau kam masha Allah

a can suka taddashi har yana zolayarsu sai yaci tararsu sun mishi african time,yayi kyau abinshi cikin dinkin kufta ya dswo jabir dinshi na ainihi,kyakkyawan matashin saurayin nan mai yawan ado da fara'a jabiru

gurine kebantacce dake can cikin ainihin gidan ajiyar namun dajin na garin kano,tamkar lambune ska yishi na musamman kudin shigarshi ma daban yske kusan ba kowa ne ma yasan da gurin ba,kujera ce irin ta siminti suka zauna a dayan shima ya zauna a dayan,sabuwar gaisuwa suka sake,maryam ta dubi jindatu tace dan bamu guri kadan to tace kana ta miqe,jabir din yace
''ai da kin qyaleta ma don maganan ya shafeta''ta yi gaba amma ta jiyo abinda yace din sai gabanta ya fadi hakanan

''maryam,haqiqanin gaskiya na yaba da kyakkyawar tarbiyyar da kuka samu,sannan nayi baqinciki qwarai

1 Comments On ABADAN
avatar
maryam-said

7 months ago

Reply

Thank you

Please Login or Register in order to submit comment