Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da gaske da rasa ki da nayi duk da nasan cewa komai qaddara ce daga ubangiji,saidai ina kwadayin hada iri da ku maryam,ina neman wata alfarma guda daya,Allah yasa wannan karon bazanyi failing ba''
cikin tattara dukkan hankalinta a kanshi tace
''babu wata alfarma da bazan iya maka ba indai ina da iko kima bata keta haddin shari'a''
''be keta ba maryam''ya fada yana murmushi wanda ya qara masa kyau da kamala
''so nake ku bani hindatu''

idanu ta zazzaro tamkar taga wani abun tsoro idanunta kan jabir din
''jabir........shin ka manta alaqar dake tsakanin hindtu da jamila ne?,ya da qanwa ne fa?''
''koda na taba sanin jamila a matsayin diya mace hindatu bata haramta gareni ba tunda igiyar saki ta raba tsakaninmu balle babu abinda ya taba shiga tsakanina da ita na auratayya,yadda aka kaimin ita haka na dawo musu da ita,so kika babu maganar janamin auren hindatu kenan''

kai ta girgiza''haba jabir,yau ko maqota muke mu da su jamila ai duniya ta zagemu balle iba daya''
''ya kamata kiyi amfani da ilimin da Allah ya huwace miki,ki dinga saka addininki gaba da al'adarki,babu wani abu da ya jaramta min auren hindatu koda kuwa ke na aura matuqar mun riga da mun rabu''
cikin girgiza kai tace
''haba jabir,amma dai ai ana barin halas don kunya''

take yanayin fuskarsa ta sauya
''gwara maryamu ki fito kanki tsaye kice min ba kyason tarayyata da hindatu,gwara ki cemin jabir ba zamu baka hindatu na tafi qarfinka
wace iriyar kunya kike magan akanta ne maryam?
su waye kima wadan da za'aji kunyar?
ko kin manta jin kunyar mara kunya asara ce?
har kin manta da abunda suka miki ne,shin a lokacin da suka aikata din ba'a halicci kunya ba ne ko kiwa akwaita sune basu da ita?''ya qarashe maganar cikin bacin rai,ta bude bakinta zata yi magana ya dakatar da ita da hannunshi kana yace
''dakata maryam,bana buqatar kice komai,tun yanzun na cireki daga batun nan,ban neman kimin komai,zan yiwa kaina yaqin samun hindatu,naki kawai ido addu'a da fatan alkhairi''bai bata damar cewa komai ba ya tashi ya nar gin yabi hanyar da hindati tayi

kimanin minti talatin ta gaza tashi a gun,wani bangaren na zuciyarka na gaya mata bata kgautawa jabir ba,mai son naka ai ya gama maka komai,yayin da wani,bangaren kuma ke ganin dai dai tayi,don rigima ce zata riri ba qarama ba cikin gidan,daya barin uace mata,to sai me?,da ba naki bane jabir din suka aikata abinda suka aikata suka maidashi nasu?to ai dama idan mai guri yazo mai tabarma nade kayarshi yake

shiru shiru hindatun ma bata dawo ba,ta ciro wayarta tayi kiranta,abun mamaki sai taji jabir ne ya daga,kafin tace wani abu ya rigata
''kada ki cikata da fada gamu nan zuwa''hangame baki tayi tana kallon wayar,bata qarasa daskarewa ba sai da ta jangosu sun jero suna tafe suna qyalqyala dariya hannun jabir din riqe da fararen ledoji masu dauke da tambarin sahad store
duban hindatun tayi saivtaga yarinyar ta waske mata tamkar babu wani abu da tayi,kabir me ya katse kallon da take mata ta hanyar ajjiye mata leda daya kusa da ita
''kada ki cinye min gimbiyata ki barta hala,s
duka sauran tuhumarki ki hadiyeta na karbi tutar hindatu''
bata data cewa kallinsu kawai take,haqiqa ta san cewa indai hindatu tayo,nasarar auren jabir bata da sauran matsalar rayuwa,miji na gari kam ta gama samunshi,suka qaraci mata shaqiyancinsu suka miqe don tafiya,nan ma ya kasa ya tsare kan shi zai kaisu,hindatu ta takura tolas suka bishin ya ajjiyau har qofar gida

suna shiga soron gidan maryam tayi saurin janyo hindatu da har tayi gaba
''hindatu ashe baki da tunani?''
ta zumburo baki
''me kuma nayi adda?''
''kin manta waye jabir tsohon mijin yayarki jamila?''
sai ta kwashe da dariya har maryam na toshe mata baki kada ta dauko hankalin mutanen gidan
''nice ta biyu wajen sanin waye jabir bayan ke ta farko,to wai ma anty don autukina yaje aikin hajji sai in kasa zuwa in sauke farali nima saboda kunya?,jabir yayi min adda don na tabbatar yana da nagarta tunda har kika amince da shi a baya''
sai ta kuma yin qasa da murya
''baya ga haka adda wannan wata qatotuwar dama ce garemu ta rama duka cin kashin da aka mana,wallahi sai na dauki fansar duk baqincikin da suka cusa mana''

ta fuskanci da gaske hindatun take
''Allah ya taimaka''ta fada kana ta shigeta cikin zuciyarta tana musu addu'ar tabbatar lamarin cikin nasara da farinciki

🎄🌲🎄🌲🎄

Batasan ya akayi ba itadai taji an kawo kudin hindatun har da kudin sa rana jimillar naira dubu dubu dari uku dubu dari kudin aure dubu dari biyu kuma kudin sa rana,hakan ya sanya baba yace ta shaidawa abdur rahim ya turo a saka rana,su din ma kudin sa ranar suka bada naira dubu dari biyar,kudin sun bawa maryam din mamaki,murmushi abdur rahim din yayo yace
''ko nawa na bada kudin aurenki yayi kadan maryam,kinfi qarfin haka,me din mai tsada ce''murmishi kawai tayi tana sake ganin qima da darajar son da yake mata

duk abin nan da ake jama'ar gidan basu da masaniya,kusan duk ranar da za'azo din basu gidan suna yawon asara yawon bidar asiri,asara goma da ashirin babu kudinsu ba imani

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[9/17, 12:54 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*



▶3⃣5⃣


👇🏾 *wannan page naku ne*

👉🏾 *_haske writers asso_*
👉🏾 *huguma conversation and novels rooms_*
👇🏾 *da kuma*
👉🏾 *Zauren biebie isah*
*Allah ya bar qauna*👍🏽❤🤘🏽



*_Ankarbo daga imam bukhari r.a,manzan Allah s.a.w yace_*
*_(qarami ya yiwa babba sallama,matafiyi ya yiwa wanda ya taras,jama'a 'yan kadan su za suyi yawa masu yawa)_*

*_a wani hadisin da imamu muslim ya rawaito daga annabin rahama s a w yace(wanda a zuciyarshi akwai girman kai daidai da qwayar zarra bazai shiga aljanna ba)_*

*Allah kayi mana tsari kada ka haramta mana aljannarka,ka hanamu dukkan wata baiwa ko ni'ima taka da zata yi sanadin zamowa masu girman kai*







Fadar irin farincikin da mama da iyalinta ke ciki ma bata baki ne,sunyi amanna cewa wannan ce shekarar farincikinsu,addu'o'in da suka dade suna qwanqwasawa qofa yau kam an bude musu dukkan qofofin,duk wani tsohuwar ajiya ta mama data jibanci kadara ta daga ta saida,ta yiwa bikin shiri matuqa da gaske,ga dangi masu zuciyar yi mata da Allah ya hadata da su


takanas suka ziyarci gaya ta saida manyan gonakinta na gado guda biyu,ba qaramin kudi ta samu da su ba kasancewar yadda a yanzu kowa ya koma noma gonakin daraja suke,tuni ta fidda kudin kayan gado kayan kitchen da sauran tarkace na hindatu,maryam kam dama da yan kudadenta da take sa ka ran zasu isheta sayan kayan gado,ga mamakinsu saiga kudade baban su ya damqa masu a boye yace sukaje su zabi kayan gadon da suke so,shi din ma gonakinsa biyu ya siyar dake gayan,dama bashi yake amfana da su ba yan uwansa ne,cikin rufin aairi, Allah sai gasu sun tashi da kayan gado na kere sa'a masu kyau tsada da aminci


bata sake shiga farinciki matsananci ba sai da mami ta damqa mata passport dauke da visa ta qasashe biyu saudiyya da china
''maryam,inason inje siyayyar lefen abdallah ne,sannan ke kanki ina son in miki siyayya irin wadda uwa take wa diyarta,naso 'ya mace amma Allah bai bani ba,to a yanzun kuma sai Allah ya bani ke,naso ace lokacin bikinki da abdallah bai hade ba da ina mai tabbatar miki anan gidan zaki zauna har akammala taro a miqa ki gidanki,saidai duk da haka bikin magaji ai bazai hana na magajiya ba,zamu fara zuwa china muyi siyayya sanan mu dawo saudiyya muyi umara,kuyi addu'a kowannanku ya roqawa kanshi alkhairi kan sabuwar rayuwar da zaya shiga,ni da ke ne da abdallah''


rasa bakin da zata gode mata tayi saidai ta tsinci kanta cikin zubda qwallar farinciki,tabbas uwa ce,mami uwa ce wadda tasan ciwo da darajar 'ya'ya,babu shakka ko ita ta tsugunna ta haifeta iyakacina binda zata mata kenan,haduwars ta tabbatar daga Allah yake,bata manta yadda taqi taji batason aikin gidan mamin ashe alkhairi ne Allah yake nufinta da shi,gaskiya ne maganar Allah haka take da yake cewa cikin alqur'a ninshi mai girma
(zaku iya qin abu kuma alkhairi ne agareku,sannan zaku iya son abu kuma sharri ne a gareku,Allah shine ya sani ku baku sani ba)


mama kam rasa mai zata fada tayi,babu shakka duk yadda kaga Allah yayi da rayuwarka baiyi don zalunci a gareka ba,yayi ne saboda shi ne mafi sani ga abinda ya dace ga bawansa
raliya har da hawayen farinciki
''damuwarki tazo qarshe diyana,Allah ya yanke miki,maqiya kuma sai su kashe kansu don baqinciki''abinda ta dinga fadi kenan fuskarta qunshe da murmushi
hindatu kam buri ya cika,don tace ko iya haka Allah ya barsu sun gode masa,Allah ya nuna isa da buwayarshi,itama tata visa din umarar na nan jabir ya tanadar mata bayan sun angwance da wata daya

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

qarfe biyu na azahar jirgin ethopian airline zai debe su zuwa ethopia inda anan zasu fara yada zango kafin su isa qasar sin,cikin masu rakiyar tasu harda jabir da hindatunshi,abdulrahim sai zubaida,raliya da yaronta fadil,


ranan ne abdulrahim suka fara haduwa da jabir,tuni ya dade da sanin waye jabir din da kuma matsayin da yake kai a yanzu a gun maryam din,don haka gaisuwar mutunci sukayi tamkar sun jima da sanin juna,kusan dukkansu sama sama suka gaisa da abdallah yaja gefe yana faman cin magani tamkar wanda aka yiwa dolen tafiyar,ita kuwa zubaidan bata damu da ta qyaleshi ba ganin yadda yake faman fuskewa ba tana liqe da shi tana zuba rawar kai yayin da shi kuma yayi mata dif ko kanzil yaqi tanka mata da ita cikin hirarta
cike da bege da qaunar juna suka yi sallama lokacin da aka soma neman matafiyan


maryam ce qarshe saboda tsayawan da sukayi da abdulrahim
''abun mamaki banga irin sallmar nan da masoua kanyi ba yayin rabuwa da juna abdulrahim meke faruwa?''
murmushi ya saki yace
''me kika gani maryam?,kina tuhumata ne kan rashin damuwa da tafiyar da zakigi ki barni?''
''dole in tuhumeka mana abdulrahim,ba sau daya ba basau biyu nasha kamaka da laifin qin sakin jikinka idan muna tare matuqar abdallah na agun,wai shin tsoronshi kake ne ko meye?,aure fa zamuyi nan da sati uku kowa yasan da zamanka,ko wata barazana yake maka aboue wadda mu bamu san da ita ba''
sai taga ya tuntsire da dariyar har yana dan duqawa
''babu tsoro balle barazana tsakanina da shi,ke kika dai fuskanci hakan,hasalima abinda kike zaton ba haka bane,Allah shine mafi sani ga abinda yake cikin zukatan bayinshi,Allah ya kaimun ke lpy ya dawo min da me lpy,ki kula min da kanki matuqa,ki yiwa kanki addu'a mai yawa maryam,kada ki kashe wayarki da wuri zan kiraki kafin ku tashi''sallamar da sukayi kenan


koda ta shiga gurin tayi tsammanin ya dade da wucewa tunda sun rigata shigowa da wajen minti goma sha biyar,sai gashi tana gaba gun screening shi kuma yana tsaye a bayanta,gaba daya sai ta takura,tana ji a jikinta tamkar yana qare mata kallo ne kawai,gashi doguwar riga ta saka sai rolling da tayi wanda iyakacinsa kafada,hill shoes ta saka wanda sanadiyyar hakan yasa ta kusa kama abdallan a tsawon


ko cikin jirgi ma number din sit din nasu daga shi sai ita,mami na a sit din bayansu,tamkar ta zura a guje ta bar sit din haka ta dinga ji,tunda take basu taba zaman kusanci na tsawon lokacin da zasuyi yanzu ba,ta njtsu tsaf tamkar ace ket!ta zura aguje
wayarta tayi tsuwwa ta duba saiga kiran abdur rahim,tamkar ance mata ta kalli gefanshi sai ta tsinci idanunshi a kanta,wani irin kallo yake mata da ta kasa fassara ma'anarsa,shi ba harara ba ba kuma normal kallo ba,ya kafeta da mayun idanunshi masu cike da kwarjini,sai ta tainci kanta da kasa dagawa har wayar ta tsinke,gani tayi ya ciro tashi wayar ya fara danne danne hakan ne yasa tayi saurin jan tata wayar ta soma dubutawa abdulrahim din saqon karta kwana kan bazata iya amsa waya ba a yanzun cikin yi masa sallama da bankwana,saida kamfanin layin sadarwa suka tabbatar mata da yake sanna ta sauke idanunta daga kan wayar,ta sauke siririyar ajiyar zuciya daidai kokacin da taji shi kuma anasan bangaren yaja tsaki qasa qasa ya furta
''fool''
dayar wayarshi data fara ringin taga ya janyo ya zura earpiece
''hello baby......muna jirgi yanzu zamu tashi.....ok...ok bye take care,i will missed you too''ya kashe wayar gaba daya ya ajjiyeta guri daya


''janye cat eyes dinkin nan daga kaina,yanzun zansa a canza miki gurin zama indai kika ci gaba kallona,bansin kallo kin gane?''
ji tayi kanar ta hukunta idon nata da har yayi kuskuren kallonshi
''me zan kalla wanda babu shi jikin abdul dina?''ta fada cikin dakiya kamar ma bada shi take ba,kanta na kallon wani sashin
''there ar many,ko skin dina kawai batayi kama data baqin mijinki ba mai zubin ta 'yan garuwa,after all ma kinsan da hakan kike qarewa mijin wata kallo,kinsan kina so tun farko bakiyi magana a taimakeki ko a qwarqwara kixo,yanzun kam its too late qwalelanki''


maganan ta mata baqi da yawa,tayi qoqarin control din bacin ranta don ta samu maida masa amsa yadda ya kamata
''shi dan garuwan ai Allah ne ya halicceshi......''
''eh mana,da ke kika halicceshi''ya katsi numfashinta ba tare data idar ba
da sauri ta dora don kada yaci da rabonta ba tare data samu ta rama ba
''ba kyau ko kudi nakeso ba mutunci nake bida da daraja,kai din kuma ai inama kallon mace ne 'yar uwata kaga babu yadda za'ayi ince inason jinsina,abdul dina yafimin kowanne namiji cikin jinsin maza,ko a mai min shara bazan iya daukarka ba da dai mai wankin toile......''


''qarya kike wlh ya fada cikin fushi da dan daga sautinshi,ita kanta ta dan tsorata don qasa qasa suke maganar lokaci daya ya daga muryarshi,idanunshi data kalla kawai suka sake sata a zulumi,sai a lokacin ta tuna waye fa,abdallah ne,ta runtse ido tana jin zafin matsar da ya yiwa yatsunta kamar zai karya su ya kuma qi saki
''meye ne abdallah''mami ta fada tana dan leqo da kanta
''babu komai''yace
''ko baka jin dadi ne?''
mami ta tambayeshi cikin yar damuwa jin sautin muryarshi ya canza lokaci guda
''am fyn''ya fada a taqaice
''ok,to ku kashe wayoyinku''tace mishi bayan ta koma ta zauna daidai ksn sit dinta


sai da ya fara hucewa da kanshi sannan ya sakar mata hannu,zuwa lokacin tuni ta fara share qwalla don azaba,jin hannun take kamar ba'a jikinta ba sanadiyyar taruwar jinin da taji ya mata,tuni har jirgin ya daidata a sama,da qyar ta janye hannun tana yarfar da shi tare da fatan jin ya sake daga daurewa da zugin da yaje mata,ko da aka tamvayesu abinda zasu ci cikin jirgin kasa ma mafa na tayi,tanaji yasa aka kawo baqin coffe aka ajjiye musu,itakam ko kallo ma bai isheta ba


a hankali suke sauka daga jirgin daya bayan daya,gaba daya qafafunta sun mata tsami ga hannunta na damunta,itace a gaba abdallah a bayanta mami a bayanshi,rashin qwarin jiki ya sanya qafarta hardewa ta tafi luu zara gangara daga matattakalar
a tsorace mami tace
''subhanallahi,abdallah tarota''
tuni ya tallafota ta dawo jikinsa
''kin zame mana kaya wallahi,dama so kike a rungumeki din an miki hankalinki ya kwanta,amma net tine kika qara sai nayi maganinki''ya fadi yana tureta daga jikinsa
''sannu'' mami ke ta mata har suka sauka,duk da yanayin rashin dadin jikinta baihanata ganin qawatuwar garin ba


gida ne mai hawa ashirin cikin unguwar,gini ne qawatacce mai kyawu matuqa da gaske,cikin hawa na takwas nasu gidan yake,gida ne mallakinsu abdallan da suka siya da kudinsu,da fari falone madaidaici sai corridor daga damanka wanda idan ka shiga zaka tadda kitchen wani corridor dinne yake kallan kitchen din shi kuma dakunan bacci ne guda uku kowanne dactoilet cikinsa,sai valcony 'yar qarana mai kyau daga fuskar kowanne hawa na gidan wanda ta nan kana iya gano ainihin cikin unguwar da layinku da kuke an qawatashi da kyawawan kujeru guda hudu da yan shuke shuke


daki daidai kowa ya dauka,tunda ta shiga dakin tayi wanka tayi akwala tayi sallah ta nade a gado sai bacci,tun la'asar dinsu sai da aka kusa idar da sallar magariba sannan mami ta tadata tayi sallah,tuni sunyi order din abinci an kawo musu har gida don haka shi kowa yaci,ba damar girki an dai siyo dan abinda zasu buqata kafin su gama kwanakinsu kamar ruwan roba qwai suger da sauran abinda zasu iya buqata,tana shirin basu guri don taji sun fara lissafe lissafen siyayyarsu mami ta tsaidata.
''maryam gaya min dame dame kike so,don gobe insha Allahu zamu fita bana son mu wuce kwana hudu,muje muyi kwana goma ko sha biyu a makka mu wuce gida lokaci na qurewa''
a kunyace tace
''bani da zabi mami,duk abinda kika zabarmin yayi''
bata ce mata komai ba ta miqa mata takarda da biro tace taje tayi mata list din duka abinda takeso nan da goma ko sha daya tazo ta kawo mata,hannu biyu tasa ta amsa ta koma daki


sai ta rasa ma me zata rubuta,bata da layin qasar balle ta kiraliya ko hindatu suyi shawara,wani tunani tayi ta koma falon,nan ta samesu yadda ta barsu,saidai wannna karo sunyi kace kace cikin takardu,rubutu kawai kowannansu ya duqufa yana yi
''hmmm,gaskiya ne,ai dole ayi bikin da babu kamarsa,da daya tilo''maryam tace cikin zuciyarta
''ya akayi maryama,har kin gama?''mami ta tambayeta bayan ta dago kanta ta maida kan rubutun da takeyi
''ummm...mami cewa nayi don Allah ko zaki aramin wayarki in dan kira gida?''
''ayya nima kuwa bani da layin qasar nan duk sanda muka zo sabo nake siya wancan faduwa yake,sai gobe idan Allah ya kaimu zan siyi wani''


har ta juya zata koma dakin mamin ta sake kiranta
''maryama zo....abdallah naga kai har ka hada naka layin ara mata tayi wayan''
yayi wani kicin kicin da rai ya saci idon mamin ya harareta kana ya ciro wayar daga aljihun trouser dinashi ya miqo mata
ta miqo hannu zata karba
''idan kinsan wannna baqin basamuden zaki kira da wayata ma gwara kiyi tafiyarki ki barmun abata,don wlh kika sake kika cinyemin credit sai na zara asalary dinki,don shi na fuskanci baya da arziqin da zai iya biya na''ya fada qasa qasa yana kallon paper din hannunshi da yayi rubutu,sai ka rantse ba da ita yake ba,murguda mishi baki tayi bayan itama ta harareshi kana ta karba duk da cewa bai ganinta,shi baisan yadda ta tsaneshi bane,idan banda lalra babu abinda zai hadata da wayarshi ma.


Ta loda numbers din raliyan ta kirata,sosai taji dadin shawarar data samu na abinda ya dace ta siya dim,ta kira hindatu ta zabi abinda itama takeso sai ta rage nata ta hada da na hindatun,kasa jurewa tayi don haka ta saka numbers din abdulrahim ta kirashi,sun taba hira sanna ta kashe,tana shirin ajjiyewa wani kiran ya shigo
*my suger* ta gani a rubuce,ta zubawa numbers din ido tana kallo,sai ta tabe baki sanna tayi rejecting.


ci gaba akayi da kira ita kam bazqta taahi ba sai ta gama rubuta duka abinda zata rubuta din ta fita gaba daya,kiran yaci gaba da shigowa ba qaqqautawa,tsaki ta ja ta janyo wayar ta daga kana ta kara akunnenta
''kada a cika mana kunne mai wayar bayi kusa''dum akayi kana taji ance
''ok''can qasa qasa


wayarta mata kyau ta dan juyata a hannunta,garin cire lock ta taba gurin pictures,daya bayan daya ta dinga bin folders din tana kalla,abinda ya daure mata kai ganin hounan abdallah da yammata kala kala,tana kalla tana tabe baki,wannnan guy din dan garari ne,waishin ma a ina yake haduwa da yammata haka zuqa zuqa yadda yake nuna he was always busy,ta shafe aqalla awa guda har taso shagala,duka hotunan babu na yarwa ya iya wanka kam babu ja a wannna tana iya bashi maki hundred parcent cif


larm din da agogon dakin yayi na qarfe goman dare ya tunasar da ita,garin sauro ta manta bata sauka daga folder din pics din ba ta kashi takardar ta fita falon,shi kadaine yanzun sai gun da mamin ta zauna,da alama yanzu ta tashi kuma ba dadewa zata yi ba,jin fitowarta bai sanyaahi daga kanshi ba,wayar ta miqa masa kana cikin cool voice dinta tace
''na gode''ya amshi wayar baiko dubeta ba,sai da ya bude screen din yaga inda ta shiga sanna yace
''awa ukun da kika kwashe wayar na gurinki hoton mitum daya dama kika tsaya kalla?''ya tambayeta idonsa cikin nata


ta dan zaro ido tana duban wayar,sai lokacin takula hotonshi ne a kai,yayi kyau cikin shigar suit yana murmushi,da alama ba'a qasar aka dauki hoton ba,bata kai ga cewa komai ba mami ta shigo falon
''kin gama maryamu''
''eh mami''ta fada tana miqa mata takardar,ta karba tana dubawa kuma tana qoqarin zama kan kujerar
''an gaisheki maryam,duk tsawon awoyin man iya ka kadai wadan nan abubuwan kika rubuta?,sunyi kadan''tace tana sake qarewa takardar kallo tana girgiza kai''
kararki tayi yawa dama nasan ba iyawa zakiyi ba,jeki kawai,zanyi amfani da wannan din da kuma wadanda na rubuta''
tana murmushi ta juya ya shige dakin ta barsu nan suna ci gaba da lissafe lissafensu

🌲🎄🌲🎄🌲🎄

ta riga su tashi kamar yadda ta rigasu kwanciya su sai yanzu suke nasu baccin gajiyar,kafin su farka harta kammala breakfast taci nata,sai tayi zaune a parlour tana kallo abinta cikin riga da wando na pakistan orange da baqi,ya mata kyau kuwa sosai


takun da taji shi ya ja hankallinta abdallah ne ke fitowa sanye da riga armless da wando three quater,fuskar an ahade kirtif ya qarasa gaban freezer ha ciro fresh milk da ta hada sanyi ya balle robar ya soma sha,baifi rabi ba ya ajiye saman freezer din ya nufi kitchen sai gashi da plate da cup,mamaki tayi yau da kanshi ya zuba baiko nemi ta zuba masa ba lallai da alamu tunwa ce ta koroshi ma,zaya zo yana wani ciccin magani kamar wanda wani ya zageshi


can gefe guda ya samu ya zauna kan ya fara break din,duk sai taji kamar ya cika falon,zaman ya daina mata dadi,neman dalilin da zaisa ta tabar falon kawai takeyi,don bata buqatar ko qanqani zama inuwa daya ya dinga hadata da shi ko naminti dayane idan ba lalura ba
''ke''taji yace sai tayi banza da shi kamar bata jishi ba,ta fuskanci wani jan bala'i gake nema da ita tunda suka taho,ita kuwa kodan daraja da kunyar mami bazata bari su raba abun fada ba


''bakiji kashein da na miki jiya ba kenan sai da kika kira wani da phone dina ko,to ki gayawa rubabben saurayinkin kada ya kuma kiran numberta don ba sa'anshi bane ni''ya miqe yana dauke cup din tea tare da bari plate din a gun,bai kai ga shiga corridor din ba sukayi kacibus da mami tana fitowa da hijabi jikinta qafarta sanye da silifas
''mami ina zaki?''
''zan sauka ne floor na qasa mu gaisa da maman farida,jiya kaga ban samu na ahiga ba saboda gajiya''
''pls mami ki taimakeni kada ki cewa zeenah tare muke,wallahi kika bari ta sani tofa na banu kafin mubar qasar nan nacinta sai yasa na rame,ango kuma da rama ami ai babu kanta kada ta koro miki ni tace na mata rama da yawa''
dariya ma ya bata gani irin marairaicewar da yayi
''ka maida ni kakarka Allah abdallah,kakannin naka ma ka shafa musu lpy a kaina abun yake qarewa,ni dai Allah ya kusa rabani da alaqaqai gwara kayi auren ko kunnuwa da idanuna zasu huta da ganin yammata,ka shirya kafin na dawo mu fita da wuri so nake a yau a gama siyayyar baki daya''


tayi gaba suka gaisa da maryam ta fita,tayi zaton ya shige dakinsa tana zuwa sukayi kacibus bakib qofa,tana mura handle din dakin da qoqarin shigewa ciki taji yace
''kika sake mami ta miki tayin fita kika ce zaki bimu wata siyayya sai na qarasa targaden da na miki jiya''wuf ta shig dakin ta saka maqulli tadan daga murya
''to baaba na'' sanna taja tsaki,gado ta fada cikin jin haushinsa,dama ita bata sha'awar zuwan ma sam,dadai ba da si din zasu je ba shine,amma indai da shine zamanta a gida ya fiye mata dadi,qofar ya tsaya yana kallo,dan qaramin murmushi irin na gefan baki ya subuce masa ya cije lebansa na qasa kadan kana ya tura qofar nashi dakin ya shige ya cire kayan jikinshi ya fada wanka






*Mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[9/17, 12:54 PM] 80k: *ABADAN*36
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*_home of expert and perfect writers_*
*_annabi muhammad s a w ya tambayi sahabbansa_*
*_''shin ko kunsan waye matsiyaci?''_*
*_sai sahabbai suka ce''matsiyaci shine wanda bashi sa dirhami ko dirane''ma'ana bashi da cin yau bare na gobe_*
*_sai annabi yace musu''matsiyaci shine

1 Comments On ABADAN
avatar
maryam-said

7 months ago

Reply

Thank you

Please Login or Register in order to submit comment