Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take,ya aureta ta sigar 'yar burum burum,zata barshi yaci nasara a kanta ya sameta a bulus ya sameta ta sigar qarfa qarfa da banga banga?,wani sashen na zuciyarta ke mata qarfafa ata gwiwar alqawari ya daukar mata,kuma ta riga da ta cika masa gabar farko na yarjejeniyarsu,bata jin kuma zai karya alqawarin

daga qasa kuma hannunta yaketa yamutsa mata cikin wani irib salo da yake sa taigar jikinta tashi saboda nata hannun na kife ne cikin nashi tafin hannun,dob samun hanyqr tsira do son cire hannunta daga nashi tayi saurin cewa
''na karba mami,insha Allahu''cikin zuciyarta tana sauya qudirin ma'anar na karba in don kada Allah ya tuhumeta

Mami dake sauri ta koma gun mutane sai gata ta rashe a cikinsu,hira sabuwa ta barke duk da maryam na rakube gefe guda,ga zaton mami surukuta ce da kunya irin wadda tasan maryam din ko da can baya da ita bare yanzun,saidai ga maryam kuwa takura ce data sanyawa zuciyarta na nemo amsoshin tambayoyin abdallah,sai ta hada amsar sai taji duka sun wargaje,idan ta kamo nan ta qulla da can sai ya tsinke,ita kanta ta rasa dalilin da ya sanyata kasa barin gidan a lokacin da ta fahimci abunda ke faruwa,dik da tana ta bawa kanta amsar cewa girma da darajar mami ne saidai ita a karan kanta take jin amsar ba gamsashshiya bace bare ta doshi abdallah da ita

''ina zuqa,bari naje kitchen indauko wayat na kira mr stephien,dinner nakeso a shirya mib sabuwa daga nan zuwa takwas na dare a compound din gidan nan''mamin ta fada ikin zumudi da farinciki tana fita daga dakin

bayan fitarta shiru ne ya biyo baya,abdalla nata qate mata kallo ba tare data sani ba don kanta na duqe ne
''sai faman duqar da kai kike kamar wata mai gajeran wuya,amma dai ba haka mukayi da ke ba ko?,sauran qiris ki wargaza wannan matakin da kika kusa kammalashi,ki tashi ki dauko drink cikin fridge ki zuba kin,ki kuma zauna agaba na har sai maki tazo ta ganmu a haka dn mu sake wanke zuciyarta''

batasan lokacin da ta dago ba ta kalleshi da oily eyes dinta ba ta balla masa harara,idanu ya lumshe yana jin wani abu na tsirga masa,ko banza buqatarsa ta biya,burinshin dama ya kalli oily and brown ayes nata wanda tun jiya rabonshi da su
''ka isa ma?''
''haka kika ce?''
''eh''ta bashi amsa kanta tsaye tana kawar da kanta daa kanshi,gyada kansa yayi cike da mamakin tsiwarta
''za kuwa kiga kalar tawa isad,ki bar gani na kodaki gaban mami na baki muhimmanci,ina iya qin sakin naki naga wanda ya isa ya sani in sake ki''

bata san lokacin da kuka ya qwace mata ba
''tabbas abdallah ya gama raina mata hankali,a daki mutum a hanashi kuka haka ake,ita da ya kamata a lallaba ita ake raina ma wayo
dauke kanshi yayi gefe guda tamkar bsi damu bs,saidai shi kadai yasan zugin fitar hawayenta da yakeji,hakan ya sashi gaggawar fadin
''Allah ya baki sa'a kici gaba sa kukan har mami tazo ta ruskeki a haka,idan tabi ba'asi kuma na warware mata zare da abawa kinga daga haka ta daina ganin girma da mutuncin mu baki daya,ni kuma naqi sakinki tunda igiyar na hannu na,qarshe kiyi biyu babu''

Jin hakan ya sanyata miqewa da hanzari kuma cikun nutsuwa ta durfafi fridge din,binta tayi da kallo a sace sakamakon yadda rigar tabi jikinta ta fidda surarta,ta ciro lemon ta dauki glass cup saman fridge,gabanshi tazo ta tsaya ta tsiyaya mishi ta miqa masa,qi karba yayi sai harara ma da ya gallamata
''kina tsammani idan mami ta shigo ta taddaki a haka kina bani abu ba zata zargi komai ba?kin min tsaye a ka kamar zamu shiga filin yaqi''
cikin qufula da hasala tace da shi wasu hawayen sabbi na bullowa
''ya isheni ya isheni fa,don me zaka dinga juya ni kamar wata waina,wannan wanne irin abu ne?''

sake dauke kanshi yayi
''har yanzu ke din a matsayin matata kike,ko babu yarjejiya tsakaninmu dole kiyimin dukka abinda nace tunda ban sakekin ba,ruwanki ne ki rusuna ki bani ruwanki ne ki bar leminki nima na riqe aure na''
ba maganar da taqi jinin ya fadeta kamar wannan,tilas ta rusuna ta miqa masa,sai da ya wani sha qamshi kafin ya karba,bayan zuciyarshi cike take fal da tausayi da qaunarta,daga shi sai Allah sukasan abinda yake ji cikin zuciyarsa

Ai kam a hakan mamin ta samesu
''a'ah me ya sameki maryam?''caraf ya karbe
''don nace ta miqon drink''girgiza kanta mami tayi tana miqar da ita tsaye
''a'sh banson sharri,bansan maryamu da qiwa ko ganda ba bare kan mijinta,halan bata da lafiya tafiyanne batasonyi ko?''ta fada tana kallon maryam,sam ita bata fahimci ma'anarta ba rashin sanin me zata ce yasanyata saurin gyada kai don shine kadai mafita
''ayya sannu,hau gado ki kwanta bari in lalubo miki magani,kai kuma banason takura ka qyaleta ta huta har ta warke,ko kuma na riqeta anan idan bakayi wasa tayi sati''

Wayyo Allah,ai duka sai a lokacin suka fahimci inda ta dosa,a tare suka hada ido ita da abdallah,wata iriyan kunyanshi da bata taba jin irinta ba ta saukar mata,da sauri taja idonta ta qulke gam,shi din na da sauri yaja qafafunshi ya fice a dakin don bazai iya hada ido da mamin ba tunda kallon da take masa kenan,ita kam ko a jikinta,cikin gurin da take ajiyar magungunanta ta duba ta fito da pain killer da paracetamol ta hado da ruwa ta kwowa maryam din
''tashi kisha kinjk marya,kada ki biyewa abdallah ya cutar da ke ba tare da kin warke ba,idan kinga ma da takura kimin magana zan maganinsh don nasan halinshi da rawar kai sarai,idan kinki jikin bai miki daidai ba ki sanar min sai a haqura da dinner din''ita dai kamar qasa ta tsage ta shige haka ta dinga ji,wannan abun kunya har ina,sai da taga ta sha ta kwanta taja mata bargo sannan ta fice a dakin

Tayi nisa sosai cikin saqe saqe da tunani taji dumin mutum a bayanta wanda sam bata san lokacin da ya shigo din ba,a zabure ta miqe zata sauka ya damqeta da hannu daya
''kiyi a hankali kada ki fama ciwon naki''ya fada cikin salon rainin wayo,kasa motsi tayo abdallah zai kasheta kam wallahi,sai kuma ya hade rai
''kikaci gaba da kuka zuwa anjima idanunku zasu kumbura,kinga idan anzo dinner sai ki tanadi amsar basu''ya miqe tsam daga gadon ya fice abinsa adakin bako waiwaye,ajiyar zuciya ta saki,sai da ya fita din sannan taji kamar ta bishi ta rufe da duka,gaba daya ma shi babu abunda ya shalleshi,babban isue da ya kamata ace yana cikin rashin nutsuwa amma ko a jikinshi.

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

Bayan ta kammala sallar magariba mami ta shigo
''yaya maryamu jikin,dinner din zai yiwu kuwa?''
kanta a duqe ta amsa mata da eh don kawar da zargin da mamin keyi na wani abu ya faru da ita,amma a zahiri ba don wannan zargin da mamin keyi ba da cewa zata yi bazata iya zuwan ba,saboda har yanzu zuciyarta cikin qunci take,nan mamin ta sakata ta shiga tayi wanka duk cikin dakin,mai makeup ta tadda na jiranta,hakanan tanaji tana gani ta zauna aka zuba mata kwalliya ta gani ta fada aka sata ta shirya cikin wedding gown irin ta larabawa fara tas mai dige digen adon zaiba kadan kadan,rolling aka mata sak irin na larabawan wanda iyakarsa saman qirjinta,hill shoes shima da earings sarqar hannu data qafa duka ruwan zaiba ne.

Kada kaso kaga kyawun da maryam din tayi,kusan duka cikin event din bikin da suka gabatar wannan itace shiga mafi kyau da tayi.

Tana zaune nan cikin bedroom din shiru kamar yadda mami ta umarceta,qofar taji an turo wanda kafin ma ta daga kanta taga waye qamshin turaren data jiyo ya sanar mata,saboda haka taci gaba da dauke ganinta daga bakin qofar,tsayawa yayi kawai ya zuba mata ido cike da sha'awa da burgewa,tayi masa kyawu fiye da tunani,bai qara amanna da kyawun da Allah ya bata ba irin yau,kasa controlling din kanshi yayi ya miqa hannunshi da nufin shafa lebenta da yaci jambaki maroon colour,har ya kusa da ita kome ya tuna kuma sai yayi saurin janye hannunsa ya daidaita nutsuwarsa hadi da cunkushe fuska
''ki tashi muje mu ake jira''
sai a sannna ta daga kai ta kalleahi cikin sakannin da basu wuce uku ba ta qare mishi kallo
eh yes ta yadda abdallah mai kyau ne,sanye yake cikin jacket mai bala'in tsada da kyau fara tas da ita komai nashi farine idan ka cire necktied dinshi takalmi da agogonshi duka ruwan zaiba kalar nata shigar sak,kau da kanta gefe tayi don bata son fiya hada inuwa da mutumin da ya yiwa rayuwarta karan tsaye
''kayi naka wuri nima nayi nawa''sunkuyowa yayi saitin fuskarta har numfashinsu na gware
''kin manta a idanun duniya mu masoya ne da mukayi auren qauna,qwarai ni airen qauna nayi amma ke da aka yiwa auren dole na fada miki dole ki ari acting na ma'abota so ki dorama kanki matuqar kina buqatar cikar burinki,wannan ne magana ta da ke na qarahe,harshe na ya gaji da yi miki tuni''

Kanta ta sake kaudawa ta yadda babu yadda zai iya ganin hawayen dake qoqarin fita a idanunta,cike da zafin rai tace
''saidai kayi dukkan abinda kaga zakayi,kaga,nifa na gaji da wanna game din naka,kawai ka sallameni a yanzu na san inda dare yayi min''
''idan anqi fa?''
ya fada bayan ya miqe tsaue ya goye hannauenshi a qirjinsa yana leqa dan qaramin bakinta dake raahin kunya
''tilas ma ka sakeni tinda nace bana so bana yi akai gaba wataqila asamu mai tayawa''

Yaji zafin maganarta amma son biye mata balle a gamu da matsalar da tafi ta baya
''lallai kam yarinya wuyanki yayi kauri,naga alama kinga makwancina da yawa,don kin samu kamar ni abdallah na nuna sonki har na aureki kikeda bakin fadin haka,kinsan kalan 'yammatan dake rububi da fatan na zame musu miji ba tare da aisin kwabo na ba ma?''
A sukwane ta juyo tamkar mai jiran ya gama fada,ido cikin ido tace masa
''ni ba irinsu bace,na sha ban ban dasu nesa ba kusa ba,baka yimin ba sam ko kusa ko alama,kuma na fada na gaya maka bana sonka bana buqatar igiyar aurenka a kaina,ka ssakeni mana dole ne,kaje ka auri masu rububin naka,idan ka taya akace ba'ayi ai sai ka matsa ga masu yi inda kake da muhalli,bawai ka tsaya ka nace a inda babu muhallinka ba''

Mamaki kam kusan kasheshi yayi a tsaye,gadan gadan ya nufota yana fadin
''ba irin mu mace ke kalla kai tsaye tace bata son mu ba duk isarta da tsadarta,bamu cewa muna so ace ba'a son mu,ni abdallah na miki alqawari sai na azabtar da zuciyarki da kalar soyayyar da baki taba yiwa wani da namiji irinta ba''bai bata damar furta komai ba ua sirute gaba daya ita da wedding gown din nata harda 'yar purse dinta marching na kayan,dike doke da zille zille ta fara tana fadin ya saketa ita ba 'yar iska bace yana sauka daga step din benen zuwa falon mami na qasa yana fain shi kuma tantirin dan iska ne sai yaya kenan?

kafin su qaraso falon tuni ta soma jiqa fuskarta da hawaye,ajjiyeta yayi saman kujera ya dora qafansji daya saman kujerar kusa da cinyarta yana huci kadan kadan,sai da ya gama qare mata kallo kana ya bude 'yar jakarta dake hannunshi yaci sa'a kuwa ya samy tissue turare da powder,cirosu yayi ua cilla mata
''ki gyara fuskanki nan da minti biyu''
cikin muryar kuka tace
''idan naqi fa?''
wani dan gajeran qayataccen murmushi irin na gefan baki yayi idanunahi sun kada sunyi ja don ta soma bashi headach bai taba fuskantar irin wanna trouble ba daga gun mace,idan suka botsare basu da dadin sha'ani saidai ka bisu ta yadda suke so ka ka musu jan ido.

''meyi baya fada,kiqi yin kiga mai zai faru a aikace kinga ai yafi dadi akan na fada miki da baki''ya sauke qafanshi ya nufi fridhe ya ciro sassanyar ruwan swan na madaidaiciyar roba ya soma daddaka,sai da ya shanye tas ya juyo inda take,tuni har ta gyara atsoronta na kada ya hanata takardarta,tamkar ya qyalqyale da dariya sai kuma ya maze yasha mur
tana shirin miqewa ya hangi igiyar takalminta ta kwance da sauri ya duqa don daure mata zata ja baya ya riqe qafan gam ya soma daure mata,lokacin mami ta ahigo tana fadin har yanzu basi fito ba me suka tsaya yi ne?,yanayin data gansu ya matuqar burgeta ta sake amanna da soyayyar dake tsakaninsu,tayi murmushi tana tunanin tana tsakiyarsu basu taba nuna mata soyayya suke ba saima fada kullum ashe ninketa suke baibai.

Compound di ya cika babu laifi da jama'a,wanda kusan rabinsu duka 'yan uwane irin mugun na jikin nan sai daidaikin maqota da abokai,tayi mamkin yadda adan taqaitaccen lokaci irin haka ma aka tara jama'a mai dan dama har haka,ko ina ka duba gurin walwali yake da decoratiom na farin yadi da wasu fararen fitilu,komai na gurin fari ne hatta da kayan mahalarta taron farine
tayi mamaki da ganin raliya da nasir lubabatu qanwarta batulu harda hindatu da jabir,to wama ya gaya musu wa ya gayyacesu?,daga sashi guda kuma nene ce da adnan sai zahariyya,idanun zahariyya da nene na kan abdallah duk wani motsi nashi suna ankare da shi,fatansu daya suga mummunan sauyi tattar da shi,yayin da adnan ya tattara nashi ma mujiyar kan maryam wanda babu abinda yake sai aukin hadiyar yawu,cikin zuciyarsa yana yiwa nene Allah ya isa da ta hanashi mallakar maryam din har abdallah ya sameta,gefe guda kuma yana tainewa abdallahn yana fadin duk taurin ranshi ne ya jawo,amma yaci alwashin da zarar burinsu ya gama cika kota tsiya kota arziqi sai ya mallaki maryam din,ko nenen na so ko bata so,kai baiqi ya kawar ma da duk wanda zaice zai kawo masa cikas ba,zubaida na gida nene ta qulleta cikin dakinsu kana ta qullen bangaren ma baki daya,ta rantse ta maya babu inda zata fito har a watse.

cikin wani irin salo mai qayatarwa dinner din ta dinga gudana,kowa ranshi fari tas cikin burgewa,tana zaune a muhallinta suka mutane suka dinga zuwa suna gaisawa da taya su murna,saidai babu daya cikin yammatan da suke son Abdallah data gani a gun,da alamu kuwa hansu zuwa gun akayi,kodai iyaye ko yan uwansu,qarfe aha daya aka taahi kai tsaye mami tace su quce bangarensu maryam taje ta kwanta ta huta.

Yana iya hangota cikin dan qaramin hasken fitilar barci takure saman gadon yayin da shi kuma ke kwance saman sofa din dake cikin bedroom din,a haka sai kayi tsammanin bacci suke saidai ko kadan kowannansu da duniyar daya shiga ita nata tunanin har yau kan amsar tambayoyinne da takeson bada su a gobe batasan ta samu failure,ya miqe ya ciro paper cikin ma'ajiyar da yake ajjiye takardu yar qarama dake can qasan gadon wanda sai ka danna wani abu take iya bullowa ya hada da biro ya dawo yayi kwanciyar rigin gine ya soma rubutu ajiki.

a qalla mintina goma ya samu kyawawa yana ruutun,a hankali yaji jikinsa ya soma masa nauyi tamkar an dora masa dutsen dala,ya sake yunqurawa da nufin daga hannun nashi a karo na biyar saidai ko alamar motsawa baiyi ba,wasa wasa sai magana ta zama babba,ya bude bakinsa da niyyar yin magan amma sai yaji kamar super glue aka saka aka manne fatar lebansa ta sama da qasa saidai.

Cikin mintina da basu gaza ashirin ba komai nasa ya daina motsi face idanunshi da kunnuwansa dake iya jin abinda ke motsi da qara baya ga haka babu wani abu dake moruwa,tuni takarda da biron hannunshi suka sulale suka fadi qasa,hannayen suka zube gefe guda,gasu a jikinsa amma ji yake kamar an cire masa su su da qafafunsa.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*

▶4⃣1⃣

👂🏾👂🏾👂🏾👂🏾

*shin ka/kina da labarin mutune guda bakwai da zasu shiga inuwar al'arshin ubangiji ranar da babu wata inuwa sai tasa?,ranar da rana zata matso daf da kawunun al'umma ta dinga tafasa qwaqwalwansu?,to ku matso kuji daga bakin da baya qarya*

*_An karbo hadisi daga abu hurairah R A yace:Manzan Allah S A W yace: mutane guda bakwai Allah zai saka su cikin inuwarshi,ranar da babu wata inuwa sai tasa_*
1⃣ *_shugaba adali_*
2⃣ *_da saurayi matashi ko matashiya da suka rayu cikin bautawa Allah mai girma da daukaka_*
3⃣ *_da mutumin da zuciyarsa ke rataye da masallaci,ma'ana wanda ko yaushe jira yake yaji anyi kira zuwa sallah ya tafi masallaci_*
4⃣ *_da mutane guda biyu da suka so junansu saboda Allah,don Allah suka hadu kuma suka rabu donshi ma'ana badon wani harkar banza ba ko duniya_*
5⃣ *_da mutumin da mace ma'abociyar kyawun sura tayi kiransa zuwa yin zina ko aikata wani fasiqanci yaqi yace mata ni ina tsoron Allah_*
6⃣ *_da mutumin da yayi sadaka ya boye yin sadakar da yayi har hannun hagunsa baisan me damansa ta ciyad kota bayar ba_*
7⃣ *_da mutumin da ya tunq girma Allah a kebe shi kadai idanunsa suka zubda hawaye saboda tsananin girma da tsoro Allahn_*

Duk yadda abdallah ya kai ga son motsa sassan jikin nasa bun ya faskara,ya yarda ya kima saddaqar da cewa wani mummunan abu ya gama faruwa da shi,tamkar wanda dannu ya danneshi haka yake ji
babu tsumi babu dabara sai Allah haka yake ta faman ambata

sam bata san halin da ake ciki ba,saidai gaba daya ta nemi bacci a idonta ta rasa wanda ta alaqanta hakan da damuwar dake cunkushe cikin ranta,tayi juyi kan gadon yafi a qirga,ba zata iya tantance lokacin da bacci yayi gaba da ita ba

🍃🍂🍃🍂🍃🍂

qarfe biyar da rabi na asuba ta farka daidai lokacin da wasu masallatan suka kai tsakiya a sallarasu,da ddu'ar tashi a bacci ta farka a bakinta kamar yadda ta saba sannan ta lalubi wayarta don jaska dakin da babu wadatar haske a ckinsa sakamakon kashe qawayen da akayi,sai data lalubi makunnin ta kunna sanna ta sauko daga gadon,a hankali idanunta suka sauka kan abdallah wanda zuwa lokacin ya rufe idanunsa gam zuciyarshi kawai ke aiki,ya gama amanna cewa tashi ce ta zo qarshe abinda yake jira kadai shine fitar ruhinsa daga gangar jikinsa,kamar ta wuceshi sai kuma taga bai kamata ba tunda dole dai ya tashi yayi sallah.

ta tsaya saitin kanahi cikin muryar dake nuna alamun yanzu aka tashi daga barci tace
''ka tashi kayi sallah lokacin sallah yayi,anyi asuba''jin ahiru ya sanya tayi zaton ko bai farka bane,amma wannan wace idiyar kwanciya ce haka yayi ya yada hannun?,sai ta dan duqa tana bubbugar filon da ya dora kanshi tana sake fadin
''anyi sallar asuba an kusa idarwa''

jin muryarta ya sanyashi bude idabun nashi a hankali tamkar mai tsoron ganin wani abun,sai ta dan zuba masa ido ganin yadda qwayar idanun tayi jazur,a sanyaye ta juya ta ahige toilet ta daura alwala ta fito ta tada sallah,ganin har ta idar bai tashi ba ya sanyata tayi zatob ko komawa ya sakeyi ne

kanshin ta kuma komawa ga mamakinta sai taga idanuwanshi biyu
''lokacin ta zaya fita alfijir na ahirin ketowa''
''bazan iya taahi ba maryam duk yadda naso hakan,ji nake kamar an daddaureni,ki taimakamin in tashi''abinda yake aon fada kenan saidai ina bakin yayi nauyi,ci gaba kawai yayi da kallonta,saita tsinci kanta itama da kallon nashi,lokaci guda kuma taji jikinta ya mutu murus,komawa tayi bakin gadon ta zauna ta inda take iya fuskantarsa suna ci gaba da kallon juna

kusan mintina talatin suna a haka har shida da rabi
''rana fa ta fito ba zakayi sallar bane?''sai taga ya maida idanun nashi ya lumshe,hakanan gabanta taji yayi wata mummunan faduwa,sai ta kasa zaman ta qarasa inda yake,abu na farko data fara lura da shi shine hannunshi da ya zamo qasa tunda ya farka bata ga ya gyara kwanciyarshi,ta sanya hannunta tadaga hannun taga ko zai gyara saidai tan sakinshi ya biyo ta,ta sake gwadawa har sau biyu babu banbanci
batasan lokacin data furta
''abdallah lafiya kuwa kake!''cikin tsorata da rudani
idanun nasa dai taga ya kuma zuba mata tamkar zai hadiyeta,sai ta shiga kiran sunansa a jejjere saidai ko guda bai amsa mata da shi ba

Lokacin da zuciyarta tayi mata hasashen abinda ya samu abdallahn jiri ne ya debeta ta zube a nan tana fadin
''me ya sameka?,me ya sameka don Allah abdalkah,ka bude baki ka gaya min''
inda zai iya da ya mata maganar amma babu iko

sai kuma ta zabura ta miqe da gudu ta fice a sashen nasu tayi bangaren mami

da sauri nene ta toshe bakin zahariyya da ta dan saki ihun farinciki ganin shigewae maryam bangaren mamin a hargitse
''nene Allah yasa ya sambade lahira''
''ko bai mutu ba to yana kan hanyarshi ta mutuwar''ta fada tana duban zahariyya
''don da ya kammla wucewar da ihun kururuwatsu kadai ta ishemu albishir''

saman mamin ta haura kai tsaye ta fara bubbuga qofar dakin nata ba qaqqautawa,tunda taji bugun ta tabbatar ba lafiya ba,ga zatonta ma abdallah dinne,tunda ta tashi dama takejin jikinta ba normal ba yadda ta saba jinsa,da hanzarinta ta murza muqullin ta bude qofan,kama hannun maryam tayi wadda taga tsagwaron rashin hankali kwance kan fuskarta
''lafiya maryam ne ya faru?''
fara jan mamin tayi
''mami zo kiga abdalkah,zo ki ganshi mami...''ta qarashe cikin rushewa da kuka

''Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa anta taj'alil hazna iza shi'it sahla''addu'ar da mami keta maimaitawa kenan fili da zuciyarya cikin sassarfa take biye da maryam suka gifta su nene dake labe jikin window dinsu suna jiran jin abinda zai biyo baya

Yadda ta barshib hakan suka sameshi,a raunace mamin ta isa gaban kujerar ta zube,gaba daya rungumoshi tayo tana kiran sunanshi,ita din ma saidai kallo da ido daga bisani ne hawaye ya gangaro daga ianunshi saboda ganin mamin nashi na kuka haiqan babu kuma baki ko hannun lallashinta,kjran sunan Allah kawai sike daidai lokacin da nene ta shigo dakin a rude kamar gaske

kallon da abdallahn yake mata ya sata tasha jinin jikinta,saidai ta nasar kawai don babu baki ko qarfin yin wani abu a kanta,tana ma sa masa tsammanin wuta zai qara zuwa lahira,
wani kallo ta jefi maryam da shi tare da zabura ta kai mata duka''me kika yi masa muguwa azzaluma''
mami ce ta tare dukan
''haba nene''cike da haqiqancewa tace
''wlh ban yarda da yarinyar nan ba bintu,daga aure jiya jiyan nan ace mutum ya kamu da irin wanna lalurar?,anya ba mayya ya aura ba bintu?''
''me ya kawo duka wannan zancan nene,muyi ta lafiyarsa ma mana''
kuka ta dinga yi haiqan tana fadin duk daren dadewa asirinki sai ya tonu shegiya mayya daga jiya zuwa yau kin lashe kurwar yaro saboda tsabar shahara a maitadaga bisani saiga zahariya da adnan,abun nasu ma sai ya zama over acting,don mamin ce ke masu suyi shiru

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

Ranar basu kwana gidan ba cikin asibitin amalam aminu kano suka kwana,cikin kwana biyar babu irin gwajin da basuyi masa ba,saidai komai ya nuna normal yake qwaqwalwarsa spinal code dinsa da zuciyarsa kai har hanta da qoda duka sai da suka duba saidai result sai yazo komai normal

A lokacin zaka tausaya wamami da maryam idan kaga yadda suka koma,duk da qoqarin boye cutan da ake saboda yanayin aikin abdallan,shi kanshi ya rame saboda tashin hankalin da yake gani cikin qwayar idanun maminshi da maryamu

cikar shi sati guda suka koma gida mami ta bada umarni ayi musu visa cikin satin zata fita da shi,kafin nan daya daga cikin manyan security dinsa mubarak wanda yake babba ne cikin masu tsaron lafiyanshi da hisham amininshi ke taimaka su mamin gun kula da abdallah,kamar daga shi zuwa toilet da sauransu,mutum ne mai matuqar kirki mubarak kamar hisham,har albashinmubarak din mami tace zata dada yace baya buqata,babu irin alkahirin da abdallah baya musu don haka bashi da abunda zai sakq masa da shi sai ta wannan hanyar,haka hisham babu komai tsakaninsa da mamin sai fatan alkhairi da sa masa albarka.

Batun fitar da abdallahn da za'ayi yayi masifar daga hankalin nene ta soma zaton kada fa a kaishi wajen ya samu sauqi haj bintu ta dawo musu da hannun agogo baya,don nene ta gama tsorata da irin kallon da abdallan ke binsu da shi duk lokacin da suka shigo duba shi
bata bata lokaci ba ta koma gun malam na hayi ta zazzage masa bakin jaka tare da qarin buqatunta

🌲🎄🌲🎄🌲🎄

Misalin qarfe sha daya ne na safiya suka gama waya da mama ta kirata don jin jikin abdallahn,tana shirin ajjiye wayar

1 Comments On ABADAN
avatar
maryam-said

7 months ago

Reply

Thank you

Please Login or Register in order to submit comment