Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kssa daukan kanki a matsayin diyata ko?,shikenan tunda ba zaki ci da mu ba zauna muyi hira tare idan na kammala mu wuce''
tilas ta koma ta ja kujera daya ta zauna kanta na sunkuye a qasa,lokaci lokaci mami na jefata cikin hirar don ta sake cikinsu saidai kaifin idanun abdallah ya hanata,duk tunda ta zauna din qurar da ta kwasota ma bai duba ba duka ya tattara hankalinshi kan maminshi da plate din abincinsu
abdalla ne ya soma tsame hannunshi yana fadin
''mami turomin daya plate din''ta tura masan tana ci gaba da cin tuwonta don ita duka wadannan yame yamen basu dameta ba
hannunshi ya saka ua dauki guda daya,lokaci guda wata matsananciyar faduwar gaba da sameta,rashin yarda da patatoes balls din ya kamata cikin tazarar lokacin da bai wuce second biyar ba
kai balls din bakinsa yayi daidai da saukar hannun maryama kan nashi hannun ta buge da qarfi har yaji zafi,ba 6ata lokaci balls din ya fadi saman teburin cin abincin ya wargaje,wani ruwa yellow din ruwa ya soma fita daga tsakiyanshi wanda idan ba sani kayi ba zaka yi tsammani ruwan curry ne,wannan shi ya taimaka daga abdallah har mami basu kula da shi ba
zuciyarta taci gaba da tsananin bugu,tsoro qarara ya bayyana cikin fuskarta,tana tuna giftawar data gani dazu cikin kitchen da ta rasa ta waye?,sa'an nan ta dawo da tunaninta kan dalilin daukota don kula da abincin abdallah,guba ne fa?guba abdallah yaci sau biyu a baya,kada fa ayi amfani da damarta a aikata wani mummunan abu,a zafafe abdallah ya kalleta,ranshi yayi tsananin bacin da har ya gaza tambayarta sai mami ce tace
''a'ah,ya haka maryamu?''
''barta mami,ai dama daga ganin wannan yarinyar bata da kunya,in banda tsabar rashin mutunci ya mutum yana.....''
dakatar da shi tayi tana kallon maryam wadda ke qoqarin daidaita natsuwarta don lalubo dalilin da zata bada wanda har ya kai ta aikata abunda ta aikata din yanzun
ba shiri ta tsinci bakinta na fadin
''mam...mi na manta ne ba gishiri da magi cikin balls din,da muka tafi asibiti ashe ban zuba ba,kada kuma yaci yaji babu dadi a bakinsa''
''amma banda abun maryamu ai sai kice mishi kawai kada yaci,next time ba haka ake gyara ba kin fahimta?''
da sauri take gyada kai tana cewa''eh mami,kayi haquri''
ta fada tana kallin abdallah,fararen idanunshi da ya zuba mata yana kallonta shi ya kuma sakata rudewa har ta rasa me zata aiwatar,ba shiri ta shiga tattara fasashen balls din dake gabanshi tana niyyar kwashewa taji ya riqe tsintsiyar hannunta
a razane ta dago idanunta suka shiga cikin nashi,ta danyi kusa da shi hakan ya sanya yaji kaifin idanun nata har qwaqwalwarshi
''daina kallona da idanu sai kace na mage''maganar ta subuce masa
ya maye gurbinta a dan tsawace da fadin
''qarya kike,wannan bai kai dalili ba,na gano wani abu daban cikin ranki,akwai dalili amma ba wannan ba''
tuni qwalla suka cika mata idanu,cikin son kare kanta tace
''da gaske nake,ba qarya nayi ba ka yadda yaya abdallah''
''akan me zan yarda dake,bayan ire irenki biyu sun so ganin qarshen numfashi na a baya,kema kin biyo sahu ne?''ya fada yana huci
tuni qwallan da ta tara a idanunta suka cika suka zama hawaye,ba b'ata lokaci suka soma gangarowa kuncinta,kuja ta qwace mata,tsoro da rauni suka mamayeta
''me kakayi haka ne abdallah,sakar mata hannu''mami ta fada cikun fushi
''mami yarinyar nan ban yarda da ita ba,baki ga reaction dinta bane?,aikina kenan mami nasan reaction din masu laifi''
''ina ce nan ba a office din SS muke ba,ai kin naka baka gwadashi a baya ba sai akan maryam,comon bani son sakarci sakar mata hannu tun kafin in sabar maka''dolenshi ya saketa amma duk da haka bai barta ba binta yake da ido
''oya maryam,tattara kayan nan ki tafi kije ki kwanta gani nan tahowa''jikknta na rawa ta dinga hada kwanukan,tausayinta fal zuciyar mami tana ganin abdallah ne ya tsoratata
''abdallah,ka saurareni da kyau,ba da ka zan dauko maka maryam a matsayin cook ba,nayi bincike mai kyau game da ita,nasan halayenta gaba da baya,baya ga haka nasha yin istihara game da zamanta da mu jikina na bani alkhairi ce ita,saboda haka ina mai tabbatar maka maryam ba zata taba iya cutar da wani dan adam ba balle mu,ni maminka nake gaya maka wanna maganar ba wata ba ka fahimceni?''a ladabce ya amsa mata
''kada ka sake mata irin haka,gaba daya ka tsoratata,ka kiyaye gaba,''
''insha Allahu bazan sake ba''tafiya taso yi amma ya kasa ya tsare ya hanata,sai da ya sata dariya kana ya mata rakiya har bedroom dinta sannan ya dawo bangarenshi
maryam kuwa jiki na rawa ta isa dakin baccinta bayan ta tabbatar ta yiwa patatoes balls din mugun boyon da babu mai ganinshi sai ita,sam bata qaunar tashin hankaki a rayuwarta,kuka ta zauna tanayi riris a bakin gadonta,lijaci mai tsawo ta dauka a haka kafin ta gane cewa kuka babu abunda zai amfanar da ita,ta tabbatar da cewa rayuwar cikin gidan akwai wani qulli da su su mamin basu san da shi ba,fargabarta daya kada wani abu ya samu abdallah ta sanadinta,idan ta fada wannan shingen wazai fiddata
bata da wannan gatan saidai yadda Allah kawai yayi da ita
har kusan uku na dare ta kasa runtsawa,sai da wayarta ta buga alarm na qarfe uku da rabi wato dai dai lokacin tashibta sallar dare kenan sanna ta shiga toilet ta daura alwala
kusan dadewarta ta yau tana addu'a tafi ta kullum har sai da kiran assalatu ya rusketa,sallar asuba tayi ta dora da azkar zuwa qarfe bakwai ta fita kitchen
sam jikinta babu kuzari kamar yadda zuciyarta babu dadi,fuskarta kadai ka kalla ta isheka amsa saboda ja da ta hada da kuma tasawa da idanunta suka danyi,a kasalance take hada musu break din wanda ya kaita har qarfe goma bata kammala ba saboda rashin qwarin jiki
goma da minti ashirin da shidda ta ji sallamar mami cikin kitchen din,a hankali ta dago tana amsa mata kafin daga bisani ta rusuna ta gaidata bata damu da amsawa ba ta dora da tambayar maryam din cikin fuskar rashin jin dadi
''maryam,lafiya?,me ya samu fuskarki?,kada kice min kwanan kuka kikayi?,abdallah ne ko?''
zuciyarya ta danyi rauni amma sai ta dake,ta dan murmusa kadan hadi da kada kanta
''ko baki fada ba na sani shine,kiyi haquri kinji maryam na mishi fada kuma insha Allahu haka ba zata sake faruwa ba,ni zan fita,ga wannan albashinki ne na wannan watan''ta fada tana zaro rafar kudin daga jakarta sababbi kar da su
hannu biyu ta saka ta amsa sanna ta mata godiya
''nice da godiya maryam,inajin dadin zama dake,kina da kyawawan halaye da mutane da dama suka rasashi a wannan lokacin,fata na Allah ya baki miji na gari maryam wanda zai riqekibisa gaskiya da amana''
kunya maganar ta bawa maryam wanda yana daya dqga cikin halayenta dake burge mami
lura tayi da akwai magana a bakin maryam din
''kamar kina son cewa wani abu ko?''
''dama yau inason inje gida ne''
''hoo,maryamu,wannan din ne kika kasa fada,banda abunki ai kinyi kara ma wata guda baki gansu ba,babu matsala zan yiwa driver magan ki shirya sai ya kaiki idan zaki dawo ki masa waya yazo ya daukeki,idqn baki dawo da wuri ba ma babu damuwa ni da wuri zan dawo gida yau in yaso sai na mana dinner dinko,ki gaishemin da mutanan gidan da kyau kinji,zan ajjiye miki saqo a parlour idan kin tashi tafiya ki tafi musu da shi''
godiya sosai ta yiwa mamin tare da yaba karamcinta,tana kammala breakfast din ta shirya a gurguje cikin baqar abaya wadda ta sake fidda sirrin kyawunta ta kuma haska farar fatarta wadda ta sake fresh saboda zama gu daya da kuma sanyin a.c,kitchen ta koma ta juye duka patatoes balls din cikin leda bag ta daure ta jefa shi cikon jakarta,sai da ta tabbatar ta qulle duk inda tasan idan an shigo shi za'a iya samun matsala gun abinci ko abunsha da zasuyi amfani da shi sannan ta fita,hatta da breakfast sai data nemi alfarmar baba uwani ta kula da shi kafin abdallan yazo yaci
cikin motar ta zaro wayarta ta lalubi number din raliya,har tayi ringing ta katse ba'a daga ba sai da ta sake kira,bugu daya ta daga
''sorry sis,fadil ne ya rudani da kuka na kasa daga kiran''sama sama suka gaisa,tana shirin tsokanarta taji muruarta ba yadda ta saba ji ba sai kawai ta share
tambayarta tayi zata iya samun nasir abban fadil a asibiti ko bai fita ba
''tun dazun ya fita,ina tsammanin ma yakai awa uku acan''godiya ta mata ta kashe wayar,kamar ta tambayeta lafiya?sai kuma taga bai kamata ba,idan da buqatar taji maryam ba mai boye mata bane,a mutunce ta cewa driver din zooroad zasu fara zuwa ya amsa mata sanna ya sauya akalar motar
*mrs muhammad ce
[9/17, 12:52 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
🌺💖🌺💖🌺
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
🌺💖
💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺 ▶2⃣1⃣




_yar fadakarwa_

_*shin ko kinsan gwalagwalan kwanakin da muke ciki 'yar uwa?,kwanaki ne masu matuqar tsada da daraja har agun Allah madaukaki,kwanaki ne da ayyukan alkhairi suka fi soyuwa agun ubangiji a cikinsu,kwanaki ne mafi daukaka cikin kwanakin shekara,an karbo hadisi daga imamu bukhari r.a,annabi s.a.w yana cewa(babu wasu kwanaki da kyawawan ayyuka sukafi soyuwa agun ubangiji kamar kwanakin goman farko na watan zulhijja,sahabbai suka ce da annabi hatta jihadi saboda Allah?,annabi yace eh har jihadi,saidai mutumin da ya fita jihadi da ranshi da dukiyarshi bai dawo da komai ba),shin me kike aikatawa na neman lada?,kada ki yarda su shude ba tare da kin amfana da komai ba,baki da tabbacin ganin na wata shekarar,Allah ya karbi ibadun mu yasa mu dace ameen*_

🕋🕋🕋🕋🕋🕋🕋


Minti talatin suka isa asibitin da nasir ke aiki,ta taradda marasa lafiya da suka rigata zuwa,hakan yasa tabi doka itama ta hau kan layi,don ta sani indai tace masa ta zo babu makawa sawa zaiyo ta ahiga kawai ita kuma ba zata so shiga haqqin wani ba


ko kafin azo kanta tuni ta qosa,jira ne na tsawon awa guda da rabi kafin ta samu shiga,da mamaki yake dubanta tare da fadin
''yau kuma an tuna da mu kenan''
dan qaramin murmushi tayi kan ta haye kujerar da masu buqatar ganinshi ke zamansa
gaisawa sukayi yaso ya dan tsokaneta yadda auka saba sai kuma ya fuskanci yanayonta ba yadda ya saba ganinta bane


madaidaiciyar handbag dinta ta zuge ta fidso da leda bag din ta dorata saman table dinshi
''taimako nake buqata daga gurinka nasir ko zaka iya yimin shi?''
''me zai hana maryam indai ba kaucewa addini ba''
''abunda ke cikin nan nake da buqatar a duba min ko akwai poising a ciki?''
ido ya dan zuba mata kamar mai buqatar qarin bayani,gganin bata da niyyar qara masa haske yasa ya kauda idonshi kana yace
''ok,ba damuwa,ga kujera can zauna bari na kira lab azo a dauka''


cikin mintina uku kacal wani matashi ya shigo sanye da farar labcoat ya dauki ledar ya fice


mintina arba'in din da yayi kafin ya dawo jinsu tayi kamar awa arba'in ne,tuna ni babu kalan wanda bata yishi ba,dawowarahin tayi daidai da kammala ganin patiente da nasir yayi,hakan ne ya bawa matashin damar zama tare da miqawa nasir result din ya ajjiye ledar a qasa yana duban fuskar nasir din


nuni ya yiwa maryam din da hannu kan ta taso idanunshi na cikin takardar,a sabule ta iso gaban teburin ta samu kujera daya cikin biyun dake gun ta zauna
''maryama....taya aka samu irin wannan mummunar gubar cikin abinci?,kinsan nau'in guba iri wannan bamu da ita ma sosai cikin qasar nan?,guba ce da ke iya kashe mutum cikin mintunan da basu gaza biyu ba,baya ga haka hatta da gawarka ma bata qyaleta ba sai ta narka duka kayan cikin mutum,dubi yadda ta maida wannan dankalin''ya mata nuni dashi dake cikin ledar da yasa matashin ya bude


A hankali ta maida firgitattun idanunta kan ledar,dankalin ya zagwnye ya koma kamar ruwan kunu,hakanan gabaki daya kalarshi ta sauya zuwa kore da baqi,kumfa ce kawai ke tsattsafa a samanshi tamkar ya ahekara ne da sarrafawa ba kwana daya ba,wani irin tsoro ya sake kama maryam,da sauri ta maida idonta kan nasir,cikin rawar murya tace
''ko zan iya ganinka kai daya?''
''why not?,sadam dan bamu guri''


office din ya rage daga ita sai shi,a hanakli ta zayyana masa dukkan abunda ta sani,ya jima yana jinjina kai kafin yace
''maryam akwai hadari mai girma tattare da gidan,saidai abu guda da ban goyi bayanki ba barin gidan da kike shirin yi,barinki gidan ayanzu dai dai yake da mutuwar abdallah da maharfiyarshi,bayan kin gano matsalar da su basu san da ita ba,shawarar da zan baki shine kawai ki zama mai matuqar kula da takatsantsan,abu na gaba shine ki riqe addu'a,qarfinta da kaifinta ya sha gaban duk wani kaidi da zalunci''


sun shafe fiye da mintuna talatin yana bata shawarwari wadanda syka sa taji hankalinta ya kwanta,nutsuwarta ta dan dawo,da kanshi suka zagaya can bayan asibitin sukayi haqa ya binne ledar patatoes din
''yanzun kuma sai ina?''ya tambayeta bayan sun isa bakin get din asibitin
''gida na nufa inje inga mama''
''gashi wani aikin yanzu zan koma ciki na qarasa kinga ai da na kaiki''
''ba damuwa,zan hau adaidaita sahu yanzun zaka ga naje''


a gabanshi ta hau napep din ya biya mata ta wuce bayan ta masa godiya,murmushi kawai yayi
''kada ki damu,ke da raliya duka abu daya ne''


har qofan layinsu dan adaidaitan ya direta saboda babu damar shiga layin nasu,ba dob matsi ba sai don yawan kwatoci da suke da su budaddu wadanda ke wa ababan hawa cikas gurin wucewa,sannu a ankali take takwa har ta isa qofar gidansu


Ba laifi akwai ahige da ficen al'umma wanda baka rasa gidan da shi sakamakon yawan 'ya'ya da sana'a da auke da shi,musamman a irin wanna lokaci da ake shirin tada sallar azahar masu neman abincin rana nata hada hadar siya,wanda ayanzun huwaila ce kadai keyi don inna hadiza na ganin yanzun ta girmewa haka


da ''zan wuce zan wuce''ta samu shiga cikin gidan saboda yawan mazan dake soron suna dakon a miqo musu abincinsu,can tsakiyar yara ta hango lubabatu da daurin qirji tana zuzzuba abincin a kwano tana mita,alamu dake nuna cewa inna huwaila bata nan kenan ita aka bari da aikin abincin,qofar dakin inna hadiza kuwa labule ne asake qarar music na fita,kada kanta tayi cikin zuciyarta tana fadin''fidan mu,gidan mu kenan,ya Allah ka daidaita shi kamar kowanne gida''ta cire takalmanta tashige dakin mamanta


daidai lokacin da maman ta fito daga dakin da suka maida kitchen dauke da farar roba da ta zuba shinkafa danya aciki,da alama girki take wato yau baban nasu yayi tsiyar kenan kowa kansa yau zai ciyar
murmushi ya subucewa maman kamar yadda ya bayyana fuskar maryamu,wani farinciki dukkansu suke ji wato da da uwa ba wasa ba,ta isa gaban maman tana niyyar amsar robar hannunta yayin da mamar ke cewa
''maraba,yau kece atafe,a'ah barmin kayana yanu zan kammala ai,daga ahigowarki ko hutawa baki yi ba''dole ta qyale maman ta fita waje ta wanko shinkafar ta ta zuba sanna ta dawo ta zauna


hira sosai suke da mamar nata har ta kammala shinkafa da wake da an quli hade da salad tumatir albasa da cocumber,zasu tada sallar kenan hindatu ta shigo,murna kamar ta cinye maryam,cewa tayi itama ba zata zauna ba bari ta fara sallar,ta yada takardun jarrabawarta saman kujera ta fita ta yo alwala


Dari biyar maryam ta fitar ta bawa hindatu da kanta taje ta aiyo musu serdine soyayye suka zauna hankali kwance suna cin abincinsu suna hira,hindatu sai santin maryam take
''wallahi adda maryam kada kiso kiga yadda kika koma,kin zama wata hajiya skin dinki tayi wani freah,qiba ce kawai baki qara ba,kinga kiwa da kin dada qiba tsawon nan naki raguwa ziyi''
dariya ma ta basu mama tace
''to sarkin zance,kiyi a hankali dai kada ki qware''cikin nishadi auka kammala hindatu ta guara gurin ta dawo suka sake bude sabon babin hira,da daidai da daidai take jin matsalolinsu,sai taji dadi jin cewa basu da wata matsala mai yawa,mama tana cikin lemonta sosai don haka sai dan abunda ba'a rasa ba,wanda shina mafi yawa kan karatun hindatu ne


duka albaahinta ta fidso ta damqawa maman tana fadin ta fadi abunda ya dace ayi da su
''um um maryamu,ke din mai hankali ce,na tabbata ko bance komai ba zaki yi duka bunda ya dace din''
tana lissafawa mama abunda takeso tayi din maman na sa mata albarka,ciki harda aiyqn kayan abinci ta ajjiye agidan nasu tunda albaagin nata ya tasamma dubu dari


''hmmm um''hindatu ta fadactana turo baki,maryam ta juya ta dubeta
''ya akayi bakin ki da magana kenan''
''wlh akwai,haka kawai zaki narka albashinki ki siyi abincin gida wanda har wadancan mutanen za'aci,jamila ma da suke qaryar arziqi bata taba siyan gallon din mai ta ajjiye tace kowa yayi amfani da shi ba sai ke da kike nema da guminki,a jikinta kawai zaki ga samunta ita babarta da 'yan dakinsu''


_kumin afuwa kuyo maleji da wannan,a bini bashi_



*mrs muhammad ce 👑*



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:52 PM] 80k: *ABADAN*22
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
murmushi maryam tayi
''akwai bambanci tsakanin jamila da maryama,mama ce mu ta haifemu uwa ta gari,mai nuna mana hanyoyin alkhairai da samun dacewa duniya da lahira,yayin da su kuma inna hadiza ce ta haifesu,kowanne mutum da kika gani yana kyauta ne da abunda yake hannunshi yake kuma da shi na alkahairinsa ko sharri,ma'ana duk abunda mutum yayi miki na sharri to abunda ke hannunsa kenan sharrin,ke kuma kada kice za kiyi amfani da abunda yake hannunki na sharri ki maida masa da martani,nuna masa ke alkhairi ne da ke,kada ki damu da sai wani yayi abu zakiyi,idan kina da dama kiyi din,kuma ki qudurce cewa kinyi ne saboda Allah,to sai kiga koda wanda kika yiwa din bai gani ba baki da haufi don kinyi ne domin Allah kuma ahike bada lada da sakamako''
cikin hikima maruam ta ragewa hindatu haushin da take ji na abunda tayi shirin yi a gidan nasu,har ta rakata super market din dake bayan layinsu ta siyi cartoon na macaroni taliya da couse couse,galoon na manja da man quli,dan madaidaicin buhun shinkafa,ta siyawa mamanta kayan tea complete,har da su cornflakes saboda hindatun
ledar da mami ta bata ta atamfofine guda biyar ciki da sabulai masu tsada sinqi biyu mamanta bawa guda biyu hindatu daya ta ware biyu zata bawa huwaila da hadiza,yara suka samu suka dauko musu kayan hindati na biye da su yayin da maryam tayi gaba
sallamarta atsakar gidan tayi arba da baban nata,cikin fara'a ta nufeshi tana shirin tsugunawa tace
''baba,barka da warhaka''yayin da shi kuma ya tareta cikin hade fuska ba kuma tare da amsa gaisuwar ta ba yana fadin fadi
''lafiya ,ya akayi me kika zo yi?''
''ya salam,taya za'a raba mjtum da gidan mahaifinshi koda kuwa aure yayi ballantana ita da bata yi aurenba?''take zantawa ita da zuciyarta
''zuwa nayi na gaidaku baba,kusan wata guda ban ganku ba''
''amma dai maryamu ina cewa.....''maganar tasa ta katse lokacin da yara suka soma ahigo da kayan suna ajjiyewa
''yaya,kai,wannan kuma daga ina?''
''siyayyar adda maryam ce''hindatu ta bashi amsa lokacin da take sallamar yaran da naira goma goma ladan dako
''uwarta ta siyowa kenan?''baban ya fada yana duban kayan
''a'ah baba,na dukka gida ne,ga wannan baba a sa mana albarka''ta ce tana ciro naira dubu biyar ta miqa masa
washe baki ya shiga yi
''ah,lallai haihuwa mai rana,maryamu dukka haka,basuyi yawa ba?''
mirmushi ta danyi zuciyarta fal mamaki
''basuyi ba baba''
''ah lallai wannan gidan aiki ya karbeki,to Allah yayi albarka ya bada miji na gari''ya fada yana irga kudin fuska qunshe da fara'a
ko banza taji dadin addu'ar da yayi mata,tunda dai uba uba ne ba'a canzawa tuwo suna,sai take jin ranta yana mata dadi
ina wuta inna hadiza ta saka maryam,qememe taqi karbar atamfar da ta bata din ai ita tafi qarfin atamfa wallahi,su yanzu atamfa saidai su bayar,ita kuwa huwaila hannu ta saka ta amshe kayarta tana tunanin gobe idan Allah ya kaimu taje kasuwar bakin rimi ta saida barta ko dubu biyar suka bata ta rage son tuni bokan uwani suka soma tatsarta,ita kuwa hindatu ta kalmashe tace gaba ta kaita,
''aikin banza aikin wofi,wa ma yasan daga inda kudin suka fito,an tura yarinya yawon karuwanci tana samo kudi tana kawo muku kuna karbewa an fake da gidan aiki aka kaita,a dai juri zuwa rafi da tulu diban ruwa wata rana zai fashe,ke kuma na dawo gareki munafuka makwadaiciya,an baki abu kinsa hannu kin karbe,to ni nafi qarfin atamfa wlh ehe''
''Allah ko?,Allah sarki,mu gani a qasa mana wai inji kare ance ana suna a gidansu,idan akwai uwar makwadaita ta duniya to kece kakarta,kwadayin ne ya sakk cusa 'yarki inda bata da gurin zama,kuma da sannu unguli zata koma gidanta na tsamiya''ta yaue labulen dakibta ta shige tabar inna hadiza na ci gaba da babatu da sharrence sharrance kala kala
lokacin da maryam ke sallama da mama tana shirin ficewa daga tsakar gidansu zuwa soron jamila ta danno kai zuwa,ta cake ado cikin wata yar ubansun shadda dinkin riga da skert na rashib arziqi,qam rigar ta kamata har boobs dinta na yowa sama,babu zancan mayafi sam atattare da ita sai daurin zamanin nan da ake kira ture kaga tsiya,waya take tana taku cikin isa da qasaita tamkar wata diyar qaruna
''yanzun nan na fito daga gidan mu hadu kawai a ni'ima guest palace din,amma fa gaskiya wannan karon bazan kuna ba gida zan koma,ok sai na iso''daidai lokacib da ta kammala wayar,bangazar kafadar maryam din tayi sannan ta juyo a wulaqance ta qare mata kallo,wata mahaukaciyar dariya ta saki tana ci gaba da kallonta
''sannu adda maryam,ana nan ana fama ko,ko da yake dai....''ta fada tana kuma kallonta daga sama har qasa
''ba laifi naga kin dan canza,ko an fara bin kwalta ne?''
waniabu ne ya tokarewa maryam dim maqoshi,rainin hankalin ya fara isarta dukan ya mata yawa,tayi mata uwarta ta mata,batasan lokacin da ta daga hannu ta zabga mata mari ba,ba ita kadai ba hatta da hindatu tayi mamaki,tsawon shekarun da suka dauka bata taba gwada yiwa wata cikin maraina wayon ta haka ba
''kan can uba,kut,me nayi miki,ko ko tsabar baqin ciki da qyashi ne...''
''kika ci gaba da magana ina mai tabbatar miki zaki kwashi haqoranki a qasa,banza jahila dabba wadda batasan inda yake mata ciwo ba''
tsit tayi da bakinta don taga irin bacin ran da bata taba gani cikin idanun maryama ba,gaskiyar hausawa dake cewa wargi ma guri shika samu
daga haka bata dada ba ta mewayeta tayi wucewarta,dadi kam tamkar maryama ta taka rawa saboda farinciki,mama ma wannan karon bata ce uffan ba,don tsan yau da gobe tafi qarfin wasa,fitarta waje babu inda idanunta suka kai sai kan jabir dake zaune mazaunin direba,idanunshi qur bisa qofar gidan tamkar dama an sanar da shi maryam din na fitowa,mamaki da tausayi suka cika maryam,jabir ne wannan,jabir ne ya koma haka,ina gayu davtsaftar jabir suka tafi?,me yake faruwa da jabir me ya sameshi?,mamakinta bai sake daduwa ba sai da taga ya dauke kansa daga gareta tamkar ma bai taba saninta ba
cikin matuqar sanyin jiki take takawa har ta isa bakin titi ta tari napep tayi gida
lokacin da ta isa gidan tuni anyi sallar magariba duhu ya riga ya shigo,ba haka taso ba taso ne ta koma da wuri ta dora musu dinner din,saidai lokacin ya riga ya qwace mata,kitchen din ta nufa kai ysaye bata ko doshi dakinta ba,mami,ce gaban gas din tana ta hidimar hada abincin,yayin da kuna dan shagwabar nata ke tayata da dauko wannan dauko wancan
''idan banda rigimar abdallah don Allah ina kai ina girki?,nace ka...''sallamar maryam ta katseta
''sannu mami da gida,har kin dawo?''ta fada tana ahirin amsar aikin daga hannunta
''yauwa maryamu ya kika barosu?''
lafiya mami suna gaidaki?''
''kinga maruamu barmin nayi yau dai daya ki huta kema,nima na wasa qwaqwalwata ko?''mami ta fada tana hanata aikin da take qoqarib karba
''ayyah,mami da wuri ma naso na dawo lokaci ne ya qwace min''
tsaki abdallah ya ja hadi da barin miqo albasar da yakewa mami ya koma ya zauna
''ki bata mami aikinta ne,idan baki bata ba ma acikin albashinta na wani watan''
yau ranta abace yake tana jinta daidai da duk wanda ya taba tane,hakan ne yasa ta maida masa raddi
''babu damuwa,mami ina jinta ne tamkar mama na ne saboda haka babu ciniki tsakaninmu,ko ba kudi qimar shekarunta sun biya in mata aiki''
baki ya tabe kamar mace
''gaskiya ne naga kina amsar albashinki,ai da,sai kice kin yafe''
murmushi tayi cikin gatse,sanann cikin qasa da murya ta yadda mami da ta tafi sink wanke albasa ba zata ji ba
''kada ka manta haifata akayi yadda akayi yadda aka haifeka,aiki nake kamar yadda kake wa qasarka aiki da albashi ake biyanka,am not a servant,ciniki

1 Comments On ABADAN
avatar
maryam-said

7 months ago

Reply

Thank you

Please Login or Register in order to submit comment