Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsarinsu kana suka shirya ta gayawa mami abinda ta shirya gaya matan,cikin tausayawa mami tace ayi mata sannu Allah ya qara sauqi,idan sun isa zata kira su sai ta bata ta mata sannu

๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚

tun daga qofar gidan ta soma ganin alamun cika,mutanene maza da mata keta kai kawo,a haka ma ba'afara gudanar da bikin ba kenan ina ga kuma an fara,gefe driver din ya samu yayi parking,akwai sabo tsakaninsu da mutunci da girmama juna duk dacewa ya kusa shekaru hamsin dattijon mutum ne mai hankali da nutsuwa,malam baaba direba ya kalleta bayan ya fito
''to malama meramu(haka yake kiranta sunan diyarahi ce ta fari data rasu),Allah ya sanya alkahairi yasa ayi a sa'a,ayita haquri da rayuwa,mu sai ranar daurin aure idan mun dawo daga na mai gida abdullahi''
kanta a sunkuye tace''na gode sosai baaba,Allah ya nuna mana''ya bude boot din motqr yana cewa
''bari in shigar miki da kayan ko''da sauri ta amshi jakar da ya fara fitowa da ita
''a'ah baaba,ka barshi ga yara zansa su shigar min da su''tayi kirqn yaran maqotan dake zaune can gefe da su wadanda da wasan qasa suke tayi da yan guje gje ganinta yasa suka bar abinda suke suka tsaya kallonta,kiransu tayi kunsan amarya da farinjini a guje suka taho dukkansu har ana rige rigen zuwa,kqn ta qarasa mqganar ma sun fara zundumar kqyqn,nata suna shige mata da su cikin gida,dubu biyar ta qirgo cikin dubu dari biyun da mami ta bata tace ta riqe a hannunta tasan amarya kudi basa zama a hannunta,da fqri qin karba malam baaba yayi


''idan da ni mai wadata ne meramu ai nine mai baki ma a matsayin gudun mawa,ke yarinya ce ta gari merama,babu komai tsakaninmu dake saidai muyi miki sai fatan alkhairi''
sai ya kuma karya maya zuciya
''indai ka daukeni 'ya baaba ka karbi kudin nan,ayi min addu'a''da qyar ta shawo kansa ya karba yana sa mata albarka,sukayi bankwana ta shige gidan ta juya don shiga gidan,tun daga qofar gidan ta fara ganin canji,yasha fenti radau ruwan madara tun daga waje har cikin gidan


mutanene da suka kusa dosan ashirin a tsakar gidan,hira ce kawai ke tashi cike da farinciki,dangin mamanta ne da na babanta na nesa,na garin gaya da sauran garuruwa,sallamarta ya sanya su saka guda atare kowa na fadin albarkacin bakinsa ganin yadda tayi kyau ta canza tamkar ba maryam din ba ,kunya ta kamata ta qarasa gurinsu suka gaggaisa,maryam mai alkahiri,ce duk da yanayin gidansun hakan bai hanata idan ta dauki albashinta ta duba mabuqata sosai cikin dangin nasu ta taimaka musu da dan abinda ba'a rasa ba iya abinda zata iya


daga nan dakin mamanta ta wuce,nan din ma da mutane dakin yayi kaca kaca da kayyaki samiru da kayan robobi wadana aketa kwashewa za'a tafi jere,suka gagggaisa ta shige dakin gadon mama,ita da hindatu ne a dakin kayan sawa ne zube saman gadon sunata aiki,gefan gadon ta samu ta zauna ta soma gaida maman,dafe bakinta hindatu tayi
''la la la adda maryam,tabdijan irin wannan canzawa haka gaskiya mami ta iya kiwo,za'a gigita ya abdur rahim kenan''alamu tayi mata da ido tayi shiru don Allah


''qaraso maryamu ki fidda kayan da kike so za'a bada na bayarwa''
''um um mama kawai a bawa wadanda za'a bawa dim babu komai''hindatu ta janyo jakar bakko gaban maryam din tana fadin
''duba kayan nan adda maryam dinkunanki ne jiya adda raliya aiko idris direba ya kawosu gobe zata amso miki sauran''
da daidaya ta dinga daga kayan,ba qaramin burgeta dinkunan sukayi ba duk ciki babu na kushewa
''Allah ya saka mata da alkhairi''ta fada bayan ta kammala dubawar


A bakin fanfo ta fito yin sallar la'asar ta tadda jamila ta fito ita kuma daga bandaki,gaba dqya ta fige ta lalace kamar mai cutar qanjamau,wani banzan kallo ta yiwa maryam din tare da jan tsaki,bata kulata ba ta bude fanfon ta kunnashi ta fara alwala,bata kai ga gamawa ba taji an bangajeta tayi taga taga kamar zata fadi sauran qiris ta qume goshinta Allah ya taqaita mata ta dafe kan fanfon,miqewa tayi tana duban bayanta,binta ce a tsaye cike da tsabar rashin kunay tana girgiza,ta arkade jikinta da ya debi qura kana ta kalleta
''baki gani ne binta kika bugeni๏ผŸ''
''ina gani mana sai me๏ผŸ,dama jiran dawowarki nake cikin gidan nan,tsofaffin munafukai maciya amana masu aure mijin yar uwarsu''
duk da kalamanta sun mata ciwo amma sai da ta bata dariya,tsayawa tayi kallonta kawai,cikin yaran gidan susu goma sha bakwai binta ita ce qanwarta ta tara,aqalla ta bata ahekaru kusan goma,sai taga ada ma ba ni ta kanta take ba sai ayanzu,ranar tqrihi a rayuwarsu,kada kai tayi tana sake yin murmushi ta juya don ci gaba da alwalarta kafin tace
''duk wadanda kika kira da wadan nan sunayen ai aun riga da sunsan kansu,kinga kenan bada ni kike ba''
''dake nake mana,kuma idan kin isa ki tanka kiga yadda ake ruwan bala'i cikin gidan nan''
ta zubar da ruwan dake bakinta ta gyara daurin dankwalinta kana ta dafa kafadar bintan
''mai abun fada baya fada,harkar girma muke da mutunci bata bala'i da masifa,ina da damar da zan miki dukan tsiya binta hakan ba gagarata zaiyi ba,amma bazanyi hakan ba abinda kuka shuka kuke girba ma kadai ya isheku duka mai taba qololuwar zuciya''ta sake mata kafada tayi dakinsu


''ki dakeni mana kinji ko karuwa kawai''
''ke kuwa tunda bata kulaki ba ai sai ki shafa mata lafiya''inji kulu dake diban ruwan wanka
''babu ruwanki munafukai,dama tun jiya naga kunatavrawar kai ke da uwarki a kansu''kulu ba haquri kamar yadda bintan keji da kanga,take suka hau dambatawa,ragowar dangin babansu da basu je jere ba ne suka rabasu


Dawowar yan jere suka hau hirar gidanjan su maryam din yadda Allah ya musu baiwar samun mazauni mai kyau da qayatarwa ta,maganar ta qara hasala hadiza da yaranta wadanda suka zame mata qawaye,suke kuma tayata haukan da take ta faman yi,don tuni jikin huwaila yayi sanyi,saidai atafau hindatu ta hanata shiga jikinsu,tace sam baza'a maimaita abinda ya faru shekarar bara ba,an dai fidda kayan sawa jakanku na da takalma cikin kayan maryam din an bawa yaranta kuku lubabatu da batulu,da murnarsu kuwa suka arba koba komai sun samu na fitar biki,wannan karbar ma da sukayi saida ya zama bala'i,hadiza da yayanta suka fito suna zubda ruwan rashin mutunci cikin dangin ubansu,hali kam sun saidashi,wanda baisan halisu ma ba ada ayanzun ya sani,kowa ya budi baki tir yake da halayensu

๐ŸŽ„๐ŸŽ๐ŸŒฒ๐ŸŽ๐ŸŽ„๐ŸŒฒ

Tara ga wata ya kama ranar talata ranar sukayi kamu,washegari laraba sukayi budan kai duk shigar da sukayi iri daya ne komai da komai ita da hindatu hatta da yari,alhamis aka musu wani wani dan reception na fulani wanda shiga ce ta fulani kowa da kowa yayi,ba qaramin qayatarwa tsarin nasu yayi ba,komai a tsare cikin nutsuwa da kwanciyar hankali


Ranar juma'a ya kama daurin aure,a gaya aka tsara za'a daura auren wannan karon,dalili da yasa kenan gidan ya zamto sai mata kawai mazan duka sun tafi gaya


Da yammacin gidan maman zahra suke zaune maqotansu,tana tsakiyar qawaye da 'yan uwa,tayi kyau cikin shadda 'yar ubansu lemon green da akayiwa adon light blue,rigace da zani dinkin ba qaramin mata kyau yayi ba,tamkar wata fure haka ta koma,raliya na gefanta tana zuba mata abinci cikin plate kana ta miqa mata
''maryam,karbi kici,tunda aka fara sabgogin nan baki ci abincin kirki ba fa''
ya mutsa fuska
''banajin dadin bakina raliya,faduwar gaba nake fama da ita tun da safe''
murmushi tayi
''fargabar shiga sabuwar rayuwa ce,kowacce mace najin hakan har da bacin rai ranar daurin aurenta,wasu ma har kuka suke kafin suji sanyi cikin zuciyarau,kiyita ambaton Allah''


kafin tace komai waurta ta fara kuwwa,a kasalance ta ciro mami ke kiranta,mirmushi tayi sanan tace
''Allah sarki mami na''
''tun da safe naso kiranki maryam,nasan tuni an daura tun safe ko diyata girma ya hau kanta an zama manya''murmushi ta sake yi tace
''na yamma ne mami,suna can dai''
''to Allah yasa ayi a sa'a a gaida maman kice ina mata Allah ya sanya alkhairi''
''ameen mami,na gode''


batulu tayi sallama falon sanye da daya daga cikin kayan da maryam ta bata an gyara mata daidai ita,sun mata kyau kuwa don duka yaran gidan nasu babu laifi akwai kyau irin na fulanin usuli
''adda maryam kizo kinyi baqi suna falon mama''cike da mamaki ta kalleta,gau ta zama adda,sunan da koda wasa bata taba jin wani daga cikin uaran gidan ya kirata da shi ba idan ka dauke hindatu,hatta da isyaku autan gidan
''kice ina zuwa''ta bata amsa tana janyo mayafonta ta lullube jikinta,ta dubi suwaiba dake zaune gefe tace tazo ta rakata
da qyar ta samu ta kutsa ta ahiga gidan nasu saboda yawan jama'a musamman da masu kidan qwarya suka baje hajarsu cikin qwarewa don daga cikin gidan sarki aka daukosu


qannenta shamsiyya,azara,balaraba da yasira na zaune daga gu guda an samu abinci suda yaransu anata kwasa,sannu tayi,musu kafin ta shigesu,yasira da shamsiyya suka danyi qus qus kana suka tabe baki
''an samu duniya''inji azara
tayi sallama falon,maman ma zaune tayi kyau cikin dinkin atamfarya,sai ta koma kamar yarinya mai qananan shekaru,Allah ne kadai yasan farincikin da take ciki,babu shakka komai yayi farko zaiyi qarshe,aure kuwa lokaci ne idan yazo ko ba'a shirya ba sai anyi shi,fata dai kada gaggawar anason ayi auren tasa aje ayi zaben tumun dare
abokan aikinta na na gurin haj atika,taji dadin zuwansu kuwa qwarai da gaske


qarfe shida suka fita meena event center suka gabatar da wata qwarya qwaryar dinner,ta maryam ce ita da qawaye da iyayenta,su hindatu kuwa tuni jabir yazo ya dauke matarshi suka wuce dinner,fir maryam tace ma abdur rahim bata buqatar wata dinner,su din ma da zasuyi sai sun dawo,hindatu da jabir na mata dariya sukayi tafiyarsu,bashi kuwa ya dawo da ita gida ba sai daya saura na dare,maryam din zata soma mata fada tayi shigewarta bargo tayi kwanciyarta
''hindatu rawan kan amarci ya fara tabaki kenan''cewar raliya wadda ke gyara kwanciyar fadil,suna jinta tana musu dariya

๐ŸŽ„๐ŸŽ๐ŸŒฒ๐ŸŽ๐ŸŽ„๐ŸŽ๐ŸŒฒ


tun qarfe biyar da rabi na yammacin ranar asabar motoci suka cika layin har suka musu kadan,tilas ya sanya wasu motocin suka dinga parking a bakin titin unguwar,moto cine na kere sa'a waccan tana wace wannan haka wannan ma haka,a nutse kowa ke zaban wadda zai shiga kasancewar tare za'a tafi,sai hindatu ta raka maryam din tukunna.


''da Allah malama kihi ki foto,kunzo kun sanya uwarku a tsakiya kuna neman sata kuka,ina cewa ba'a kanku aka fara aure ba,haba da Allah''inji yayar mama hajiya aysha,hindatu da maryam dinne duqe gaban maman,maryam ta soma qoqarin taahi amma kuka yaci qarfinta ya hanata,sanye take da atamfa riga da simple zani an lullubeta ruf da wadataccen mayafi,hajiya aushan ce ta taimaka mata ta miqe ganim da gasken ta kasa miqewar,addu'o'in fatan alkhakri ta biyo yayan nata da shi.


caraf sukaji an damqe hindatu,jamila ce a zabure kamar mahaukaciya sabon kamu surutai take zage zage da sumbatu kala kala
''shegiya tsinanniya,wallahi babu inda kika isa kije,gidan mijina nawa ne ni kadai,wallahi bazan baki damar cin irin daular da naci ba don uwar ubanki''ganin abin na gaske ne daya daga cikin qannen malam amadu sailuba ta qaraso ta daga hannu ta zabgawa jamilan mari
''saketa 'yar iskar yarinya mai kama da 'yar Allah bani,dul abinda kika aikata akayi muku shuru ba'ace muku komai ba bai isheku basai yau ranar da Allah ya tashi nina muku kuskurenku,shekara nawa kuna cutar amina baiwar Allah ta taba tadakai ta kalli waninku,tunda aka fara bikin nan baku,bar mutane an zauma lafiya ba,uwarku dai ta cuceku wallahi,kuma ki saketa tun kafin ki debi haqoranki a hannu,idan tsiyace kowa ma ya iyata''ba shiri ta saki hindatun taja da baya sai gata yaraf a qasa.


da gudu inna hadiza ta qaraso gurin,hannu ta dora a ka cikin qaraji tana fadin
''huwaila amina dake kanki sailuba,zaku kashemin 'ya,munafukai tsinannu,dama ai na dade da sanin kun fi son amina saboda 'yar garinku ce,to Allah ya fiku kina ranar daukan fansa na tafe''
babu wanda yabi ta kanta,hssalima zamewa kowa ya dinga yi ko ruwan da za'a kwarawa jamilar an rasa me miqowa,su kansu sauran 'ya'yan nata na qofar gida suna jallin yadda motocin sukayi farin dangon daukar amare,kwalliya kowaccensu taci tare da fatan daya daga cikin mamallakan motar ya taya


ta dubi sailuba sata zo wucewa tana sauri don kada ta rasa motar tafiya
''da Allah sailuba miqo min ruwa na kwarawa jamila kinga bata numfashi''kallon banza tayi mata
''kici mutuncinmu kici na uwarmu kice zaki moremu,saidai ki nemi wata ta baki wallahi badai ni ba''ta buga qafa tayi ficewarta,tilas ta saki jamilan ta debo ruwan ta sheqa mata kana ta jata zuwa cikin daki tana fyace majina.


Gwanin sha'awa motocin ke tafiya cikin tsari da nutsuwa,sam babu irin mahaukscin gudun nan da 'yan kai amarya keyi,mitoci ne kimanin guda arb'in banda na security guda goma


wani matsananciyar faduwar gaba take fama da shi idan ta tuna izuwa gidan aurenta fa take tafiya,addu'o'i ne fal cikin zuciyarta na samun sa'a da nasarar sabuwar rayuwar da zata fuskanta

๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ


sau uku tana sako qafarta waje da niyyar fita saidsi ta kasa,sakamakon mutanen dake giftawa bata da buqatar kowa ya ganta,aiki ne na sirri wanda bata da buqatar haduwarta da wani,wayarta ta fara vibration jikinta na rawa ta daga,muryar nene ta cika dodon kunnenta
''kada fa kiyi kuskuren da zaki jawo mana bacin aiki,wannan ce damarmu ta qarshe''murya can qasa take fadin
''na gama aiwatar da komai nene,fitowata ce ke neman gagara mutane na kai kawo a gun''
''kada ki kuskura ki wuce mintina talatin baki baro area din ba,wuce hakan na nufin bacin komai''din din din wayar ta katse,hankalinta ta msida sosai kan hanyar ficewarta,wuf ta faki idanu ta fice ta nufi bangaren nasu cike da farincikin nasarar aikinsu

๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ

Qarfe goma da rabi ne na dare,gefan lallausan gadon dakin nata take a cure guri guda,tafiyar yan kawota da mintina ashirin yayyafi ya fara sauka wanda ya haddasa sanyi da garin yayi hade da qamshin qasa,bai kankama ba ruwan hakanan yayyafin bai tsaya ba,kusan tunda suka tafi suka barta anan take zaune bata ko motsa ba


hayaniyan data soma ji cikin paflour na muryoyin maza daban daban suka qara mata fatgaba,ta runtse idonta tana jin yadda zuciyarta ke dukan uku uku kamar zata yi tsalle ta fito


''ko baka fadi ba ba shiga muma za muyi ba don an dade da daina wannan''ta jiyo muyar wani daga cikinsu,tun tana jin hayaniyar tasu sama sama har taji dif alamun basu cikin sun fice kenan


da gudu gudu sauri sauri ya qaraso cikin parlojt din saboda ruwan da ya sake danyin qarfi,duk da haka ya jiqa masa fararen kayanshi,ya tsaya ya kulle ko ina ya rage yawan qwayayen dake kunne kana ya doshi dakin kai tsaye


a hankali ya tura qofar dakin kana ajjiye tarin ledojin dake hannunshi,qamshin dake dakin kawai ya isa ya tabbatar maka rana ce ta musamman,tsaye gayi hannunshi harde a bayanshi,sai ya lumshe idonshi yana zuqar qamshin qasa hade da turaren jikinsa da na dakin baki daya yadda suka hadu suka fidda wani qamshi na musamman kuma na daban,gwagwarmayar da ya fada kacin samunta ta zama mallakinsa ya dinga dan tunawa,a hankali ya bude idanun nashi ya tsaya yana qarewa shigar tata kallo


gaba daya jikinsa ya saki lokacin da wani tunani ya darsu a ransa wanda ya qada maaa qwarin gwiwa da azamar isa gareta,tamkar mai tausayin gadon haka ya hau ya dinga rarrafawa har ya isa gareta kana yayi zaman dirshan a gabanta


sannu a hankali ya dinga yaye mayafin dake kanta har ya cimma nasarar cireshi duka fuskarta ta bayyana,saidai ya cimma idanunta aruntse ne,ya karyar da kai yana ci gaba da kallon fukartata irin kallon da bai taba samun dama ya tsaya yayi mata shi ba,kyawunta yaci gaba da fito masa muraran,sosai ya shagala har baison abinda zai shiga tsakaninsa da yanayin


Qememe zuciuarta taqi amincewa da daina mugun tseran gudun da take,gashi ya sata agaba,nauyi da kunyarshi sun hanata bude ido,jin shirun yayi yawa ya sanyata yanke shawarar bude idanun nata ko yama fita adakinne ma bata sani ba


da kadan da kadan ta dinga budesu har sai da suka kammala buduwa tar,da qafafunshi ta soma tozali a hankali ta dinga daga kan nata har ya sauka bisa fuskarshi da ruwan sama ya jiqa har ruwan da ya soma taba kanshi ke diga kadan kadan,batasan lokacin data ta wuntsila gefe ba cike da *TSORO RAZANI DA FIRGITA BA* sakamakon wanda ta gani


*ABDALLAH* ne cikin daren nan cikin gidanta kan gadon aurenta๏ผŸ,idanunta ke mata gizo koko meye๏ผŸ,me yake faruwa ne๏ผŸ,hauka ce ta samu qwaqwalwar abdallah ko bashi bane bama gaba daya aljanu kesan mata wasa da qwaqwalwarta da tunaninta,ina abdur rahim da ya bar abdallah ya keto dakinsu na sunnah๏ผŸ
dimbin tambayoyin da suka nemi jirkita mata qwaqwalwa kenan tashi guda ba tare da tasan duka amsoshinsu ba





*mrs muhammad ce*๐Ÿ‘‘



๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“šโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ

๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ *ABADAN*๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐Ÿ’–

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–
ยฉ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*๐Ÿ’ก
*_home of expert and perfect writers_*

โ–ถ3โƒฃ8โƒฃ


*_JIRGINSO ZAYA TASHI KE DAI AKE JIRA ...'YAR GATA DUNIYAR SO.... KECE DA SARAUTA_*๐ŸŽถ๐ŸŽถ

*_na dawo gunki nazo baqo da sallama....kai kawo nayi qarshe...a qauna na tsunduma....kin jawo nayi roqo nazo ki ban zuma....na sawo dubi tufata mai kyau da karrama....ke naiwa kwalliyata shiga ta alfarma....._*๐ŸŽถ๐ŸŽถ
*_soyayya gaskiya ce ya zanyi in raina....wanda yake aac cikintaaa nima don na zauna.......nayi dare ban masauki gidanki in kwana....zo ka shige har abinci zan maka kwadon rama....._*๐ŸŽถ๐ŸŽถ

*_riqe sirri sai mai sirriiii....da fari a cikin taurariiiiii...._*

*wannan waqar na sadaukarwa da readers don jin dadinsu kana iya sauraronta bayan kammala karanta wagga shafi*
๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚






Matsowa kusa da ita ya sakeyi tattausan murmu kwance bisa kyakkyawan fuskarshi,duka hannayenshi ya ware da nufin ta iso gareshi,take jikinta ya soma bari,qwaqwalwarta so take ta tsaya cik da aiki saidai ta ware qwanjinta wajen hana hakan faruwa,bata da buqatar tsayawar tunaninta a yanzu,tama fi buqatarshi fiye da ko yaushe,ya sake matsowa gareta yana nufin janyo ta jikinshi


wata hadaddiyar tsawa ta sakar masa bayan ta dira daga kan gadon jikinta na qyarma,tuni zuciyarta ta karye hawaye ya soma sintiri bisa fuskarta,dukkan tunaninta sun gama vata fyade abdallah yazo yi mata,tunda ba wannan ne karo na farko data taba ganinshi kebe da diya mace ba,amma wanne irin tsoro abdur rahim kewa abdallah da ua bashi irin wannan damar๏ผŸ,ko wani abu yayiwa abdur rahim din nsta har ya kai ga shigowa dakinta shi daya ba tare da wani qwaqqwaran motsi ko hayaniya ba.


Abdallan ya sake motsawa don biyota qasan,cikin daga sauti hargagi fushi bacin rai da tashin hankali ta dakatar da shi
''dakata marar tsoron Allah,me kake nema da ni๏ผŸ,me ya shigo da kai dakina๏ผŸ,kana shirin tozarta sunnar ma'aiki๏ผŸ,kana shirin cin mutuncin matar da bata yi maka komai ba๏ผŸ,to Allah ya fika''
jikinta na rawa ra fara daddan na wayar dake hannuna tun dazun da aka kawota lubabatu ta danqa mata a hannunta


Numbers din abdur rahim ne guda uku,saidai duka wadda ta kira sai taji ringin dinta cikin aljihun abdallah,cike da wani tsoron ta dago ta dubeshi,hawaye ne kawai ke kwaranya da sintiri kan fuskarta
''abdallah๏ผ,ina abdur rahim๏ผŸ,me kayi mishi๏ผŸme ka yiwa mijina๏ผ๏ผŸ''ta qarasa maganar cikin qaaraaji


baisan sanda yayi alkafura ya diro daga gadon ba,gadan gadan ya nufeta don ya riqeta ganin yadda take kuka tuquru tana dafe bango,saidai kafin ya kai ga riqeta ta goce
''kada ka tabani,kaji tsoron Alkah kasan cewa ni matar wani ce''cikin cool voice dinsa mai cike da jarumta da mazantaka wadda a yau rauni ya cikata ya saje maidata sassanya yace
''pls cool down mana,ki natsu in miki bayani kinji,ki saurareni''


''bazan nutsu ba,in nutsu ka cucu ne,me kake nufi abdallah,me nayi maka,ka shigo dakin aure na,banga mijina ba,na kira wayoyinshi suna jikinka,ka gaya min me ka masa๏ผ๏ผme kayi masa๏ผ๏ผ๏ผ''
duk yadda yaso tayi shiru ta saurareshi abun ya faskara,idanunta sun rufe bisa dukkan zatonta ko abdallah ya kashe abdur rahim ne
''ki zauna ki fahimceni...'''
''bazan fahimceka ba.....ina mijina.....ina ka kaimin mijina abdu........''


''maryam๏ผni ne nan mijinki,ni ne mijinki ba abdur rahim ba,ni abdallah da ni aka daura miki aure๏ผ''ya fada yana nuna kanshi shima cikin daga murya har jijiyar wuyanshi na tashi
sai kukan nata ya tsaya cak,ta tsaya tana kallonshi tamkar doluwa ko sakarya,jin maganar tayi tamkar cikin mafarki,da saufi ta kama hanunta ta mintsina sai ta tabbatar cewa gaske ne,girgizq kantq ta shiga yi tana fadin
''ba kaine mijina ba,bakai ka aureni ba ni zaka yaudara๏ผŸ''


''bari in baki shaida don ki tabbatar''ciro wayarsa yayi ya kira wasu nimbers,ga mamakinta sai ga muryar abdur rahim radau
''kai,bakasan ganganci bane kiran ango daidai wannan lokacin ba๏ผŸ,ko baka shiga dakin marya bane๏ผŸ''yake tambaya cikin sigar zolaya
''hmmm,abdul maryam zata amince nine mijinta kuwa๏ผŸ''
dariya yayi
''a'ah,mai zai hana,idan ma taqi ta amince ka dauketa kuje gidansu tunda su sun sani kaine ka aureta din,ko ni inzo gobe sai in dauko gimbiya muzo in mata bayani''


baiga qarasowarta ba sai waftar wayar da tayi,cikin rawar jiki ta kara wayar a kunnenta
''abdur rahim,ka cemin kaine mijina ba abdallah ba,ka gaya masa don Allah''
''kiyi haquri maryam bani na bada sadakinki ba bani ke neman aurenki ba,duniya bani ta shaida a matsayin mijinki ba duka wannan abdallah ne,nine *abdurrahim a fili a boye kuma abdallah,nike neman aurenki a gaban idonki a bayan idonki abdallah ne*,banyi hakan ba don komai sai don *DACE DA JUNA* da kukayi ke da shi,babu wadda ta dace ta zauna da abdallah saike......''


bata bari kunnuwanta sun qarasa ji mata kalmomin da ta yiwa laqabi da munanan kalmomi ba ta saki wayar ta tarwatse agun,taji daga baki mai tushe to shin kuma wa take jira๏ผŸme take jira da zai tabbatar mata fiye da abinda taji yanzun๏ผŸbabu,babu shi,take taji garkuwar jikinta na raguwa,qarfinta yana yin qasa,sai ta soma sulalewa agun


da gudu abdallah ya isa gareta ya tallafota,tabbas da tana da isashen qarfi bazata yarda ta sauka ajikinshi ba,rungumeta yayi yana jijjigata,numfashinta na fita hakanan idanunta akansa suke hawaye na bin gefan kunnenta saidai numfashin na gware ne gurin fita,rungumeta yayi tsam cikin jikinsa cikin wani tashin hankalin,daukarta yayi tsam tamkqr wata 'yar tsana ya komar da ita kan gadon ya shimfideta.


mahaukacin bugu yaji ana yiwa qofar bangaren nasa ,sai ya sake diriricewa,cikin qanqanin lokaci kuma ya gayyatowa kansa dakiya da jarumta yana tafiya yana waiwayen maryam din tamkar wanda aka ce masa kafin yaje ya dawo zata bace ya sauko ziwa bakin qofar ya saka key din ya bude


jikinsa ta fado tamkar wadda aka hankado,cikin hanzari yasa hannunsa daya ya cireta daga jikinsa yayi gefe da ita saidai ita qoqarin dawowa take zuwa jikin nasa tana gunjin kuka duk ta wani burkice kamar mahaukaciya
''wai meye haka zubaidq๏ผbana son hauka fa๏ผ''ya fada cikin hargagi
''bazan iya ba abdallah,wallahi bazan iya jure rashinka ba,ka tausaya min abdallah,ta yaya muna cikin gida daya zaka kwana da wata abdallah๏ผŸ''
ya tabbata idan yace ma zaya tsaya bata baki ne wahal da kansq kawai zaiyi don ba zata taba fahimtarsa ba,kai infact ma a yanzu bai da time baijin yana da time din wani a yanzu a duniya koma bayan maryam,ya tabbata idan yayi sake kwabarsa zatayi ruwa ne tsululu kuwa,a nashi zaton da hasashen abun bazai kai bacn haka ba,yayi zaton cewa duk randa maryam din ta samu labarin shine miji a gareta zatayi farin ciki ne fiye da kowa kodon,dimbin dukiya da Allah ya mallaka masa


ganin yadda take faman ahigewa jikinsa kamar hauka yasa yq cira hannu hankadata baya tayi taga taga kamar zata fadi
''ki shiga hqnkalinki zubaida,bana cike da iskanci da hauka kina jina ko,bace min da gani''
maimakon tayi kamar yadda yace din sai ta qara tasowa kansa,cikin zafin nama yaja qofqr ya rufe ya maida muqullin,ta kuwa fada jikin qofar ta saki wani kukan tana bubbugawa iya qarfinta
''ka bude min don Allah abdallah,wallahi na kasa barci,na kasa cin abinci,na gaza jurewa,ka bude min abdallah''haka ta dinga fada tqnq bubbuga qofar,yana jinta hqr ya haura sama ya barta anan
ruwan roba mai azabar sanyi yq ciro ya hado da cup ya koma dakin,yadda ya barya haka ua sameta sai qaruwa da ruwan hawayen fuskarta sukayi


ajjiye cup din yayi a side drower ya haura gadon,ya zame mayafin dake jikinta ya wulla shi gefe,ya janyo cup din ya tsiyaya ruwan yana tsoma hannunshi cikin ruwan yana shafa mata a fuskarta zuwa wuyanta,duk da yanayin da yake ciki hakan bai hanashi kin laushi da santsin fatarta ba,duk lokacin da hannunshi ya taba fuskarta ji take tamkar yana dora mata wuta ne a jikinta,zuciyarta,cike

1 Comments On ABADAN
avatar
maryam-said

7 months ago

Reply

Thank you

Please Login or Register in order to submit comment