Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba har sai sun tafi


Dukkaninsu suka rakosu har bakin mota cike da kewa,maryam kam harda qwallanta don tasan zatayi kewar qauyan ba kadan ba
''ka shiga motar hisham kai da hisham din idan yaso ma taho a tawa ni da maryam''
cikin shagwaba irin wadda ya sabawa mamin yace
''gaskiya mami qafata qafarki,a zamu raba mota ba''qememe yaqi yarda kuma ya kasa ya tsare maryam ba zata shiga kowacce mota ba


Dole hisham ya shige motarsa shi daya,maryam da abdallah na gaban motar mamin ita kuma mami na baya,gaba daya ta hade gabas da yamma na fuskarta don mami ce tace dole ita zata shiga gaban,shi kam dadi ya kamashi ya dinga satar kallonta yana son ta kalleshi ya tsokaneta,kamar kuwa tasan da hakan taqi uarda ta dubeshin


Yana shirin tashin motar mero ta leqo daga soron gidansu da alamu tana labe ne tun dazun a nan,idanh shabe shabe da hawaye,sai abdallahn ya kashe motar ya bude murfin ya fice yana fadin
''ina zuwa''
maryam na kallonshi ya qarasa inda meron take,sai ta rufe fuskarta da mayafi ta hau kuka sosai,tana iya hango yadda bakinsa ke motsi da alamu wani abun yake gaya mata,daga qarshe dariya ta saka,yasa hannunshi cikinaljihu ya fiddo da dubu biyar cikin kudin da jiua hisham ya rakashi cikin gaya ya ciro a ATM machine


Sai sata shige gidansu sunan ya juyo ya dawo cikin motar,yana shirin daura belt mami da hankalinta ke kan wayarta tace
''ita kuma waccan yarinyar fa wace๏ผŸ''
murmushi yq dan saki kana yace yana kunna motar
''zan miki bayani idan mukaje gida''
bata amsa masa ba ya tashi motar bayan yayi addu'a ta matafiyi ya soma tafiya


La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu kinaz zalimin ta dinga maimaitawa cikin zuciyarta sakamkon wani irin daci da take ji,yana tuqin shima yana satar kallonta,so yake ta kalleshin kuma taqi kallonsa,ya juya ya dubi seat din baya mami ta kashingide abinta tana gyangyadi,ai dole kam sam tunda tazo garin bata yi wani barcin kirki ba tana ta 'ya'yanta


Ya cire hannunshi guda daya daga kan sitiyarin ya saka cikin tafin hannunta
''baby,me ya faru๏ผŸ,naga kamar baki farinciki da dawowarmu gida''
zame hannun nata tayi cikin hade rai
''ka kula fa malam da kyau,tuqi kake,kada kaje ka zubar da mu''murmushi ya kuma yi yana qoqarin sake lalubar hannunta
''mutane biyu wadamda duk duniya babu wanda ke muhimmanci a gurina sama da su fa nake tuqawa,kinga ya zamarmin dole na kula iya kulawa''


bai qyaleta ba sai da ya kuma kamo hannun nata yana murzawa a hankali kuma atausashe yana lumshe ido,ta sake zamewa wannan karon tana fadin
''ada ka jimin ciwo bana bayan kai ka adana taka amaryar''
ba don ya daure ba saura kadan ya sheqe da dariya,ya sami sarai abinda ke cin zuciyarta kenan
''anzo gurin kadan kika gani yarinya,nayi alqawari kuma sai ya cika,da bakinki zaki furtawa abdallah kina sonahi,sai kinsam ABDULLAHI ba kanwar lasa bane,a jininmu yake''ya fada cikin zuciyarsa,a fili kuwa shima sai ya janyr hannunshi ya maida kam tuqinshi yana fadin
''au haka ne fa,am sorry''sauran qiris ta fashe amma bangaren zuciyarta ya tausheta

๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚


Dan qaramin biki suka je suka tadda anayi a gidan duk na taryar abdallah,duka 'yan uwan mahaifi da mahaifiyarshi ne da sukasan halin da ake ciki,saidai babu wanda baiyi mamaki ba ganin abdallahn kamar ba wanda ya kwanta cuta ba,ya sani sarai hakan ya samu asali ne daga kyawun weather na garin ni'ima da kuma kyakkyawa kuma cikakkiyar kulawa da ya samu daga maryam


Cikin mahalarta taron harda SALMA da JIDDA wadanda ke ta binshi da kallon sha'awa da kishi,kishi kuma na banza,eh na banza mana don tunda ya kwanta babu wadda ta tako qafarta da niyyar gaisheshi,a zatonsu abdallan ya gama aiki ne cutar data sameshi ba qaramar mummunar cuta bace babu ranar warkewa
to ko dama can shi ba yinsu yake ba ballanta na a yanzu da yasan ajin kowa


babu batun komawa bangarensa a yanzu don mami tace bata yarda da gidan ba ma baki daya balle bangarensa don haka cikin dakunan dake corridor din nan guda hudu tasa aka gyara biyu,abdallah ya dauki daya maryam ta dauki daya,tana sane ta raba musu dakin don tuni tayi magana da hajiya laila ta sudan next weak ta zata shigo nijeria zata yiwa diyar mr presdent gyara jiki na bikinta da za'ayi so zata sauka gidan mamin don sabon gyara mamin tace tana so ayiwa maryam din,a cewarta ba zasu tare sabon gidansu da tun asali a can aka yi jeren maryam ba sai ta gama gyara diyarta,daga maryam din har abdallan ba eanda ya sani,ita dai maryam raba dakin da mamin ta yi musu da kanta ba qaramin dadi yayi mata ba don nata son ko yaya tayi wani abu da zai fallasata gurin mamin,shi kuwa abdallah ckkin tunani mamin ta sakashi da tunanin ko maryam ta gaya mata wani abu ne game da yadda aurensu ya samo asali๏ผŸ

๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ

Ita kanta tayi mamakin baccin da tayi,ta jima sosai rabon da tayi bacci irin wannan,don a qauyen ni'ima yawanci daga ta idar da sallar asuba bata komawa,zama take kan abun sallah tayi addu'o'inta da karatun qur'ani sabida lokaci ne mai falala da akeson yin addu'a a cikinsa,gari na yin shaa zata jiyo kwaramniyar inna wuro take zata fito su hau aikin kintsa gidan da hada abun kari,bata farka ba tunda ta kwanta sai shida,tayi sallar asubahi ta sake komawa,sau biyu abdallah na leqota ba tare da ta sani ba tunda bata qulle dakin ba ta kwanta


sai sha daya na safe ta kuma tashi,kayan jikinta ta cire ta daura towel ta shiga wanka,bayan ta fito tayi tsaye gaban madubi tana goge ruwan jikinta kana ta ja dressing chair ya zauna akai tana qoqarin fara shafa mai
''amma fa yau garin kamar da zafi zafi,ki shafa kadan kada ya saki gumi da yawa''taji an fada,a tsorace ta waiwayo,yana kwance abinsa daidai kan gadon nata hankalinsa kwance kamar a dakinsa yake,sanye yake da t shirt fara qal mak gajeran annu sai three quater shima din fari ne tas,yayi saisaye da gyaran fuska ya sake yin kyau kmar wanda aka canza shi daren jiya


A hanzarce ta miqe da gudu ta koma cikin bandaki gqulli,tsaye tayi jikin qofar bandakin,takaici ya sake cikata data bi jikinta da kallo,yanzun qila gwanin kallon mutane ya gama qare mata kallo,ta waiwaya ga babban madubin dake maqale a bangon bandakin ta kalli kanta,daga cinyarta ne kawai zuwa qirjinta a rufe amma ko ina na jikinta awaje yake,tuni qwalla ta cika mata ido,ta koma ta sake keqashi ta jikin qofar,yana kwance bashi da niyyar tashi,danne dannensa ma yake a waya abinsa
''idan zaki fito ki fito abinki,ni zuwa nayi mu gaisa kuma na tambayeki,ba abinda kike zata bane''yq fada yana sake gyara kwanciyarshi


taja baya da sauri din gani take yana kuma hangota ne,idan banda rainin hankali irin na abdallah a haka zata sake fitowa๏ผŸ,kuma haka ake shiga dakin mutum ba neman izini bakasan ma ya shigo ba
tana tsakq da neman mafita taji ana knocking qofarta,kafin ta kai ga amsawa taji muryar mami na fadin
''maryam,baki tashi bane๏ผŸ''
gyara muryarta tayi kana tace
''na tashi mami na farka tun dazun''
''ok to bude min''
rarraba ido ta fara yikamar wadda ta yiwa sarki qarya,gaba daya ta rude,abdallah so yake ya ja mata abin kunya,haka kawaj mami ta raba musu daki ta gansu kuma tare,ita ga towel a jiki ta fito daga wanka,ta matso jikin qofar sosai yadda abdallah zai iya jinta cikin rawar murya tace


''kaga abinda ka jawo mana ko,yanzu meye haka don Allah''
tana kallo shi yana dariya
''ni ban jawo komai ba,kwato ne ni balle kice idan an ganni a dakin za'a jefeni ko ayimin bulala,ki fito kawai ki canza kayanki ki bude mata''haushi ya qara kama ta ganin yadda ya maida abun ba seriouse ba,cikin qunan rai tace
''Allah ya sawwaqe wallahi na fito ka gani a haka''
yayi wani irin juyi yai ruf da ciki saman gadon yana fadin
''mu shekara a haka mana yammata''


''maryam,me kika ce๏ผŸ''inji mami,sai tsoro ya sake kamata kada dai ace taji muryoyinsu,ta dan daga muryarta tace
''am...am...cewa nayi...cewa nayi dama ina bandaki ne wanka nake''ta fada cikin tsoro
''ok,to shikenan nari na shiga gun abdallah dukkanku baku karya ba shima daga cemin zaije wanka shiru,idan kin fito ki samemu a dining''ajiyar zuciya ta saki da taji alamun mamin ta tafi


Miqewa yayi ya sauka a gadon jin mamin ta soma qwaqwasa qofar dakin nashi,tana kallonshi ya murza key ya bude dakin,lallima *SAMUN WURI*(by maman farida),har ma wani key ya saka mata a daki kamar nashi dakin,bata tanka masa ba har ya fice don kada kulashi y sake dawowa ba qaramin dan neman magana bane kadan daga aikinshi


Yana fitowa suka hada ido da mami,duk sai ya dububurce,kunyarta yaji ta kamashi ganin yadda ta harde hannunta aqirji ta zuba masa ido,sai ya soma shafa qeyarsa,dariya ma ya bata ta kama hannunshi suna tafiya dining tace
''yaushe abdallah ya fara kunyar maminshi๏ผŸ,hala maryam ce ta koya masa๏ผŸ''baice komai ba sai murmushi da yayi


Cikin atamfa ta shirya super sharaton kalar lemon green da milk,ba qaramin kyau tayi mata,duk da ba wani makeup tayi ba amma hodar data shafa tabi fuskarta sosai ta qawata farar fatarta,ta sanya dan kunne sa sarqa na fashion lemon green


Tun daga nesa ya kasa kaucewa kallonta,wani kishinta da sonta na ratsashi,tayi masa kyau matuqa da gaske don bata yafa mayafi ba ma,tayi hakan ne sabida mami,tasan zata iya ganin baiken yafa mayafin da tayi bayan su biyu ne cikin gidan



Ta rusuna ta gaida mamin cikin kunya da girmamawa,ta amsa tana murmushi tare da dubansu
''nikam ai gaba dayanku kun fini kyawun gani,fatarku tayi kyau kamar ma ba'a qauye kuka zauna ba,lallai su inna wuro sun iya kiwo,dole ne kam mu nuna godiyarmu''dukkansu dariya sukayi ta ja kujera ta zauna tana gaida aliyun,ta qasan ido yake dubanta kana yayi qasa qasa da murya
''baby kinyi kyau fa ''banza tayi da shi kamar bata jishi ba,bata mantashi ba bai kunyar idon mamin yanzun sai ya jawo mata abun kunya tana zaman zamanta


Duk da haka bai qyaleta ba ganin taqi kulashi,hannu ya dinga sawa cikin kwanonta yana cinye mata chips dinta,nan ma qin biye masa tayi,saidq mami ta kula tukun
''a'ah,abdallah ya haka๏ผŸ,ga naka cikin olate nan kuma ma naga tare muke ci da kai ko๏ผŸ,don me yau zaka matsa mata''shi kansa sai ya danji kunya da ya tuna tare fa suke ci da mamin ko yaushe amma yau ya manta da ita


Ringin na wayarta ta jiyo wadda ta tabbata abdallah ne ya kunna mata don ta ajjiye ta ne kawai bata kai ga kunnawar ba,ta miqe daga cin abincin ta nufi dakin
sunan hindatu ta gani kan screen dinta,dan uwa mai dadi,wani farinciki taji ya kamata ta haye kan gado kana ta amsa
''yar uwa rabin jiki''inni hindatun,dariya maryam ta saki sannan ta qarashe mata
''banga mai kamarki ba''
''da gaske adda maryam kun dawo ya abdallah ya samu lafiya๏ผŸ,yanzu mukayi waya da mama ta gayamin mamin abdallah ke fada nata jiya bayan dawowarku,wallahi kinganni bani da lpy amma har naji na warke''
''eh da gaske mama take hindatu yanzu haka muna gida,ya gida ya mai gidan......''
katseta hindatun tayi cikin zumudi
''inaa,wlh adda maryam,bazan iya zama ba,ki duba hanya gani nan zuwa''tun kafin ta amsa ma ta katse wayar,ta dubi wayar tana murmushi
''hindatu uwar rawar kai da karadi,har yau ba'a canza hali ba''



Tana fitowa sukayi karo da baaba uwani na fitowa daga kitchen,cike da murna baaba uwani ta kalleta
''a'ah maryamu''
''baaba uwani''itama ta amsa mata fuskarta dauke da murmushi,sai da suka bata mintina suna hira a gun kafin ta wuce



ko da ta koma dining din tuni su mami sun kusa kammalawa,daman ita tuni taji ta qoshi zuwan hindatu kawai yasa ta qoshi,don haka jujjuya abincin kawai take
''har yanzu banga abun kirkin da kika ci ba maryam''
''na qoshi mami''ta fada tana mirmushi
''ko a ni'ima ma haka takeyi mami,batason abinci''inji abdallah cikin salon jan fada


Ya dan ja kujerarsa baya alamun ya qoshi yana hamdala abayyane
''mami,tun jiya fa aka soma turo min saqon komawa gurin aiki,don watanni da muka diba sun cika,so jiya bamu jima da dawowa ba saiga tex dinsu,zamu zauna da mr presdent gobe a abuja insha Allahu''
shiru mami tayi na dan lokaci kana tace
''anya Abdallah ba za'a haqura da aikin nan ba kuwa๏ผŸ''
murmushi yayi kadan bayan yayi miqa
''ba komai mami,ai duka aikin taimakon al'umma ne,idan lokacin barin yayi za'a barshi,yanzun aikin da na fara nakeso na idar da shi,alhj hamza mai qusa ina da zargi mai qarfi akansa''
''Allah ya taimaka,yanzun yaushe zaka tafi''
''da la'asar in sha Allahu,jirgin yamma ne''
''Allah ya kaimu''
satar kallon maryamun yake yaga ya yanayinta yake saidai sam taqi yarda su hada ido





*mrs muhammad*๐Ÿ‘‘


๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“šโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ
[7:06pm, 10/6/2017] Huguma๐Ÿ‘‘: ๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ *ABADAN*๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐Ÿ’–

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–
ยฉ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*๐Ÿ’ก
*_home of expert and perfect writers_*

โ–ถ5โƒฃ7โƒฃ


*Daga sahal dan sa'ad Allah ya yarda da shi yace''wani mutum yazo wajen manzan Allah S A W,sai yace,ya manzan Allah,nuna min wani aiki wanda idan na aikatashi Allah zai soni mutane zasu soni๏ผŸ,sai manzan Allah S A W yace: KA GUJI DUNIYA(dadin dake cikinta da qyale qyalenta) Allah zai soka,sannan KA GUJI ABUN HANNUN MUTANE MUTANE ZASU SOKA*
*_ruwayar ibnu maaja_*






Sam taqi dubansa,hidimad gyara gurin da suka kammala cin abinci kawai takeyi,ya san tana sanen rayi haka
''idan kinsan wata baki san wata ba yammata,duk abunki sai na dan more kan na tafi''ya fada cikin zuciyarsa yana danne danne waya,kansa ya dago kamar wanda ya tuna da wani abu da gaske ya dubeta
''af,maryam,taimakamin ki dauko mim wasu takaddu cikin cupboard please''kamar ba zata je ba haka taji saboda kunyar idon mami amma sai taga mamin ma ta sauko daga kan dining din ta koma cikin falo tayo zamanta kan kujeru,ba tare da tace komai ba ta miqe ta nufi inda ya aikata din.


Ta kusa aqalla minto goma tana dube dube cikin dakin nasa amma sam bata ga abinda yake fada din ba,dole ta juyo ta fito don ta sanar masa,a kusa da maminta tadda shi yana zaune yana nuna mata abu a waya,ta dan rusuna kadan''ban gansu ba''tace da shi,ba tare da ya dago ya dubeta ba yace
''ki sake dubawa dai da kyau,suna nan ciki ko locker din mirrow dina''a yanzu kam jikinta ya fara bata aiken bogi ne,don iya dubawa tq duba ko ina din,amma sabida bata son musu yasa ta miqe ta koma.


Ko minti biyu batayi da komawar ba ya dafe kai yana fadin
''af,na manta asge na sauya musu gu shi yasa ta kasa ganinsu,bari naje na dauka''ya fada yana satar duban mami,bata ko dubeshi ba har ya miqe yayi hanyar dakin,binsa tayi da kallo tana murmushi can qasan ranta tana fadin''dama ai bazan hanaka kebewa da matarka kuyi sallama a abdallah'',tattare itama ya nata ya nata tayi ta haye sama abinta



A hankali cikin sanda ya tura qofar dakin ya shiga,tana duqe ta duqufa neman takardu
''har yau maryam ke yarinyace na yarda da hakan ba wuya a miki wayo''ya fada cikin xuciyarsa
jingina yayi da qofar ya harde hannayenshi a qirji yana kallonta son ranshi,sai datq gaji da dubawa kana ta dago,ta juyo da niyyar fita amma hankalinta na kan gado tana dubawa ko nan ya ajjiye,dalili kenan da yasa bata ganshi ba har sukayi karo,baya ta ja da sauri,tana yarfe hannunta tace
''na duba ko ina ban gansu ba nikam''.


Hannun nata ya kama yana fadin
''ba wasu takardu dama,son ganinki kawai nakeyi dama kafin nawuce,ma tabbata idan ba haka ba bazaki bari na ganki din ba sai a gaban mami''
so take ta qwace amma ya gwada mata qarfi irin na 'yan maza sai da ya kaita gefan gado ya zaunar da ita kana yayi tsalle ya fada gadon,kwanciya yayi ruf da ciki,kanshi ya dora saman cinyarta ya saka hannayenshi ya zagaye qugunta,ya gama kanainaye jikinta bata da ikon motsi
''ummm,baby,har yau bansan matsayina a gunki ba baby kin barni cikin duhu fa๏ผŸ''ta dan hadiye wani abu,yana nufin yace har yau bai fuskanci komai daga gareta na ko so yake sai ya qureta ya sata fadin abunda bata yi niyya ba
''ka riga da ka san matsayinka tuni a gurina ba tun yau ba''shiru ya danyi kana yace''na riga ni kuma da na manta baby,pls ki sake gayamin''.


Shiru ta sake yi don ya sakata cikin kokwanto biyu,idan ta buda baki abinda duk zata gaya masa ta tabbatarwa kanta qarya take a yanzu,idan kuma ta fadi gaskiyar wanne kallo zai mata,jin taqi cewa komai ya saka shi juyowa da sauri ya koma rigingine duka akan cinyar tata yana kallin fuskarta,sai tayi saurin runtse idonta,murmushi yayi ya saka yatsanshi ya lakace mata hanci
''yar qauye kawai,shi kenan tunda kin barni cikin duhu,idan kuma na mutu kafin na dawo burinki ya cika kenan ko๏ผŸ''
bata san lokacin da ta bude brown oily eyes dinta ta watsasu cikin nashi ba tana zazzaro su,shima kallon nata ya tsaya yi can qasan zuciyarsa wani sanyi na ratsashi
''mutuwa kum....''sai ta kasa idawa ganin yana sake fadada murmushinsa yana lumshe ido,idanun nata ta sake ja ta rufe ba tare da ta qarasa din ba
''a hakan ake so ace ba'a sona๏ผŸ,bansan lokacin da kika koyi yima kanki da kanki qarya ba''.


Bugun zuciyarta ya qara gudu jin yadda ya kama tafin hannunta yana mata tafiyar tsutsa,wani abu take ji yana bin jikinta,da hanzari ta janye hannun ba tare da ta bude idon ba,yana qoqarin sake kamowa tace
''ka bari,ba dadi''
''da dadi''ya fada cikin wara iriyar murya
cikin lokaci qanqani gaba daya yake son burkita mata tunani,hot kises ya dinga aika mata da su wadanda bata taba koda kin labarin irinsu ba,romancing dinta yake sosai kamar ba abdallah,duk da jikinta na amsar saqon amma a tsorace take matuqa hakanan bakinta bai mutu ba da fadar kalmar ''ka bari abdallah,bana so,ka bari don Allah''
ko kadan bai saurareta ba sai da ya ragewa kansa zafi,kallonta yayi idanunshi sun juye tamkar bugagge muryarshi ta koma can qasa sosai,a rufe idanunta suke gashin kanta da ribbom din ya dade ta zamewa ya warwatsu har fuskarta,wata kasala yakeji sosai a jikinsa don haka ya koma ha kwanta kamar dazu kanshi bisa cinyarta kwanciyar rigingine yana maida numfashi.


A hankali ta dinga bude idonta kamar mai tsoron cin karo da wani abun,ta dube abdallah dake kwance daidai kan cinyarta,idanunsa na a rufe numfashinsa na sauka a hankali,ta rabbatar bacci ne ya daukeshi,so take ta miqe amma ta kasa saboda gaba daya ya sakar mata nauyinsa,sai ta miqa hannunta ta dauki ribbom dinta ta hada gashinta guri guda ta dauki dankwalinta ta mayar,fuskarsa taci gaba da kallo,wani kyau baccin yayi masa sosai kamar ba mai bacci ba.



Ta riga ta yarda kyau kam Allah ya bawa abdallah shi,irin kyawun da ba kowa Allah ke azurtawa da shi ba
kusan awanni daya da rabi ya samu yana baccinshi tana zaune tamkar mai gadinsa duk motsinsa na kan idanunta,a haka taji an soma knockong qofar,ta fara qoqarin tureshi daga jikinta jin muryar mami ne amma qememe yaqi,tamkar ma yana sane sai ya sake kanannadeta abinsa yaci gaba da baccinsa,a hankali mamin ta murda qofar jinta abude yasa ta dan turo kadan tana sallama,amsa mata maryan tayi sai ta leqo da kanta,karo na biyu ta soma yunqurin maida shi gefe ta kasa cikin jin kunya,murmushi mamin ta mata kana ta mata alamar tayi shiru ta zauna kada ta tasheshi ta ja qofar ga rufe musu,ta sake kallon fuskarsa gumi taga yanayi duk da sanyin rabar dake dakin,tattausan tafin hannunta ta saka tana share masa tare da hura masa iskar bakinta,caraf taji an kama hannun naga an riqe,tsoro da kunya suka kamata sai tayi wuri wuri da ido,ya bude idonsa a hankali ya sumbaci hannun kana ya tashi zaune yana ambaton ''la'ilaha illal lah muhammadurrasululluh sallallahu alaihi wa sallam'' yana miqa


ya dubeta tana qoqarin miqewa yace mata
''sannu baby am sorry na danne miki cinya ko''bata ce komai ba tana qoqarin fita cikin zafin nama ya rigata isa bakin qofar ya saka key ya qulle,ta kalleshi cikin alamu na tambaya kafin ta furta tambayar ma ya bata amsar
''babu inda zaki je,idan kinga kin bar dakin nan nazo tafiya ne''sai ta bata fuska kana tace
''to waishin ma ni matarka ce๏ผŸ,bayan kace temporary ne''
girarsa ya dage kana yace''yes har yau matata ce ke,dole kici gaba da yimin abinda nakeso kafin lokacin da maryara zata iso''kasa magana tayi shi kuma ya zare key din ya jefa aljihun three quater dinsa
''daga tashina a bacci kinsani magana my mero'',jin ya ambaci sunan meron ua sake hasalata
''ai ba meron bace,sabida haka kada ka sake kira mana sunanta,kayi qoqari mu rabu lpy''shikam da yar qaramar dariyarsa ciki ciki ya zari towel dake saqale kan murfin cupboard ya shige toilet


A darare take zaune gefan gado tana bin dakin da kallo a haka ya fito ya sameta,da sauri ta dauke kanta don yaune karo na farko data taba ganinsa haka,rigar wankan jikinsa ya kunce zaren dake riqe da ita ta fadi a gun ya zama daga shi sai gajeran wando,cikin qunquni tace
''nikam naqi jinin rashin kunya''
a hankali ya tako gabanta ya durquso inda take a zaune har tana jin qamshin sabulun wankanshi da ragowar dumin dumin ruwan da yayi amfani da shi
''me kike fada๏ผŸ''ya tambayeta da wata iriyar murya ta daban,baya ta dan ja tana sake tsuke fuska don kusancin nasu yayi yawa
''nikam babu abinda nace''dagowa yayi yana dariya
''da kin sake kin maimaita yarinya yau da kinga yadda ake ruwan rashin kunya,yau da saidai mami tayi jinyarki ni kuwa na gudu abuja kinga ko fada ba zata samu damar yi min ba''sarai ta fuskanci me yake nufi,wai gabuntar dan fari ke damun Abdallah ko tabarar auta๏ผŸ,ta rasa wanne ne daga ciki,sai kuma ta tuna cewa itama 'yar farin ce take ta bawa kanta amsar saidai tabara ce kawai irin ta auta.


Babu wanda ya sake cewa dan uwansa komai har ya kammala shiryawa,itakam sai dauke kanta kawai tayi wani sashen don harkarsa yake kamar shi daya ne cikin dakin,wannan karon ma t.shirt din ya sanya saidai baqa ce long sleeve haka ma three quater dinashi baqine,wani kyau suka yiwa farar fatarsa,ya fesa turarrurrukansa,ga tunaninta ta dauka zai bude musu qofa ne su fice sai taga ya soma sauko da wasu tsadaddun akwatuna baqaqe masu kyau qana nan set ne guda uku ya ciro biyu babban da qaraminsu ya ajjiyesu
''bismillah madam,a hadamin kayan tafiya''ya fada yana dauki pillow daga saman gado ya jefar a saman rugs din dakin ya kwanta rub da ciki yana kallonta
''ammafa mami tazo nemanmu dazun kana bacci'',girarsa ya dage
''ba matsala nasqn ba wata damuwa bace indai mami ce,bamu da damuwa da ita'' qi tayi duk don ua qyaketa ta fita hakan yasa ya janyo wayarsa ya kira mamin ya tambayeta
''a'ah,ba wani abu ne,dama baqi ne suka zo matan baffa salisu ne kuma sun tadda kana bacci,har mun gaisa ma sun wuce sauri suke suna zasu''
''ok mami''ya fada ya katse wayar yana duban qwayar idonta
''sarkin kuka,komai kuka komai kuka,bayan qiri qiri baki da gaskiya''ya fada cikin zuciyarsa yana murmushi,bai ce mata komai ba har ta gaji da kallon da yake mata ta miqe ta isa ma'ajiyar kayanshin don yanzu kuma bata da wata dabarar ta kubce masa.


Tsaye tayi a gun,ta rasa ma wanne zata dauka masa,kaya ne bila'adadin iya ganinta,a sanyaye tace
''wanne da wanne zan dauka maka''
''na baki zabi,nikam,bani da ta cewa''ya fada yanajin dadin yanayin da suke,ji yake kamar ya riqe lokaci suyita zama a haka,a hankali ta dinga zaban kayan tana shiryawa cikin akwatin,tsit dakin yayi lokacin da take aikin,duk wani kotsinta yana binta da ido don,ba qaramin burgeshi take ba,komanta cikin nutsuwa,ta gama da suite suite ta saka masa yadi biyu shadda biyu tunda tasan tafiyar tasa majority sai yafi amfani da suite din,sannan ta saka masa na shan iska,ta kammala ta rufe qaramin kuma ta saka masa sauran tarkace na buqatar yau da gobe,shi kansa yanayin yadda ta tsara masa kayan ya burgeshi qwarai,komai a tsari,ta gama shima ta zuge tana fadin
''an gama'',sai da ya lumshe idonsa ya bude kana yace
''thank you verry much,shukran jazilan''
ya tashi ya zauna soasai yana fadin
''bari na qarasa daya nau'in godiyar ko''kafin tace komai ya jawota jikinsa,irin saqonnin dazu ya fara aika mata har suka so sufi na dazun zafi,nauyin da saqon nasa ya mata ya sata sakin

1 Comments On ABADAN
avatar
maryam-said

7 months ago

Reply

Thank you

Please Login or Register in order to submit comment