Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daya ya zauna. Wannan karaga sai ta tuna wa Janshahu da mahaifinsa da sarautarsa da kasarsu. Ya yi tunani a cikin ransa, ko wane hali mahaifinsa da mahaifiyarsa ke ciki? Wannan tunani ya sa hawaye suka karyo masa. Ashe su ma mutanen nan da ke tare da shi babu abin da suke yi sai tunanin gida.

Suna nan zaune suna kahon dandi, sai suka jiyo wani irin gunji, kamar kururuwar dubban mayaka, yana fitowa daga wajen da suka ajiye jirginsu. Dukansu suka yi zumbur suka mike tsaye suna kaduwa. Suka yi waje da gudu. Su duba haka, daidai inda suka daure jirginsu, sai suka hangi rundunar birai babu iyaka, sai ka ce farin dango. Sun darkako gidan suna gunji, suna tsalle-tsalle. To, ashe wannan tsibiri na biran nan ne. Bayan sun dawo daga yawo sai suka ga jirginsu Janshahu daure a bakin gaba, suka kakkarya shi suka watsar cikin teku. Daga nan sai suka yiwo wa fadar nan tsinke, inda Janshahu da mutanensa ke ciki.

Da Sarauniyar Macizai ta kawo nan da labarinta sai ta dakata kadan. Sai ta dubi Hasibu ta ce, "Ya Hasibu, duka wannan labari saurayin nan ne wanda Bulukiya ya iske a cikin tsibiri a gaban kaburbura yana kuka, yake labarta wa Bulukiya shi."

Hasibu ya ce, "Ya Sarauniya, to me ya faru ga Janshahu da mutanensa tare da birai?"

Sai Sarauniya ta ci gaba da labarinta, Janshahu da mutanensa na nan tsaye a bakin gidan nan, suna kallon birai sun nufo inda suke. Kowanensu kamar ransa zai fita saboda tsoro. Yayin da birai suka iso wurinsu, sai duk suka fadi suka dauki kasa a gabansu, sa'annan suka mike tsaye, kowane ya dora hannayensa bisa kirji ya sunkuyar da kai, alamar mubayi'a. Suka ja hannun Janshahu suka zaunar da shi bisa karaga, suka zaunar da mutanensa kusa gare shi. Su kuwa duk suka zauna bisa ababen zama, suka zagaye shi.

Can sai ga wasu birai sun zo da wata barewa, gasasshiya. Aka yayyanka namanta aka aza bisa wani babban faifai na zinariya, suka kai faifai gaban Janshahu da mutanensa, suka yi musu ishara da su ci. Dan Sarki ya ci nama tare da mutanensa har ya ishe su. Daga nan kuma biran suka kawo musu 'ya'yan itatuwa da ruwa. Bayan sun ci sun koshi, sai Janshahu ya tambayi birai, da ishara, menene labarinsu? Wane Sarki ne ya mallaki wannan kasaitacciyar fada?

Suka amsa masa da ishara, "Ka sani cewa wannan fadar shugabanmu ce, Shugaba Sulaimanu dan Dawuda (Amincin Allah ya tabbata a gare su). Ya gina wannan fada a cikin wannan tsbiri ne musamman domin shakatawa, a lokacin da yake raye. Yakan ziyarci wannan fada sau daya a cikin shekara.

Birai suka ci gaba da cewa, "Amma yanzu kai ne shugabanmu, mu kuwa duka bayinka ne. Wannan tsibiri da wannan fada da duk wani abu da ke cikin su, kai ke da iko da su yanzu. Ka ci ka sha dukkan abin da ranka ke so. Ka umurce mu da aikata maka kome kake so." Suna gama fadar wannan magana sai duk suka fadi suka kara yin gaisuwa gare shi. Daga nan sai duk suka kama gabansu, sai 'yan kadan aka bari.

Janshahu ya kwana tare da mutanensa a cikin fada, shi yana kan karaga su kuma suna zagaye da shi bisa ababen zamansu. Da gari ya waye, bayan hantsi ya dubi ludayi, sai ga birai hudu sun zo wurinsa. Wadannan birai sun kasance su ne wazirai gare shi. Suka zo tare da askarawa masu dimbin yawa, duk suka cika fadar saboda yawansu. Askarawa suka yi holi a gaban dan sarki Janshahu. Waziran nan hudu suka matsa kusa ga Janshahu suka yi masa ishara da cewa, ya mulke su da gaskiya, ya yi adalci a tsakaninsu. Birai suka yi ruri gaba daya, daga nan sai duka suka watse sai 'yan kadan da aka bari wadanda za su rika yi wa Sarki hidima.

Can kuma sai ga wasu birai sun zo da wasu irin karnuka manya-manya, girmansu kamar dawaki. Kowane kare an daura masa ragama da linzami. Janshahu da mutanensa suka yi mamakin irin wadannan karnuka. Birai suka umurce su da cewa kowa ya hau kare daya su biyo su. Suka hau karnuka suna mamakin girmansu. Wazirai ma suka hau nasu karnuka suka shige gaba Janshahu da mutanensa uku na biye da su har suka fito daga cikin fada.

Suna fitowa sai suka tarar da birai birjik, kamar tururuwa, a bakin fadar, suna jiran fitowarsu. Waziran nan hudu suka shige gaba, Janshahu da mutanensa suka bi su a baya. Biran da suka tarar a bakin fada kuma suka dafa musu baya diiii.... kamar farin dango, wasu a kan karnuka, wasu suna tafiya kasa, suka nufi bakin teku. Da suka isa bakin teku sai Janshahu ya dubi inda suka daure jirginsu, sai ya ga wasu 'yan kiraren itace na jirgin a kasa, sauran jirgin kuma sai ya tabbatar da cewa an jefa shi cikin teku. Ya tambayi wazirai me ya faru ga jirginsu? Suka amsa masa da cewa, "Allah ya ba ka nasara, ai tun lokacin da muka ga kun shigo cikin wannan tsibiri muka san da cewa kai ne Sarkinmu da muke ta faman jiran zuwansa. Kuna fita daga cikin jirgin muka zo muka kakkarya shi, muka jefa cikin teku, gudun kada wata rana ka ce za ka gudu daga gare mu."

Yayin da Janshahu ya ji haka sai ya juya ga mutanensa ya ce musu, "Hakika ba mu da sauran hanyar tsira daga hannun wadannan birai, tilas mu dangana mu ga abin da Ubangiji zai yi da mu." Suka ci gaba da tafiya suna bin gabar teku har suka iso ga wata korama. Daga tsallaken koramar kuma wani babban tsauni ne ya yi sama kamar zai shiga cikin gizagizai. Da Janshahu ya dubi tsaunin nan da kyau sai ya ga wadansu irin halittu masu siffar mutane, amma sun fi mutum girma nesa ba kusa ba. Dukkansu farare ne, irin farin haske, kamar da hasken aka halicce su, sai ka ce fatalwa. Ga su nan dabu-dabu a jikin tsaunin kamar kuda sun daddabe nama.

Janshahu ya tambayi Waziransa, "Wadanne irin halittu ne wadannan?"

Suka amsa da cewa, "Allah ya ba ka nasara, ya Sarki. Wadannan halittu abokan gabarmu ne, kullum sai mun yake su. Su kashe mu, mu kashe su. Yanzu ma mun zo ne domin yakar su."

Koda suka kara matsawa kusa, sai Janshahu ya yi mamakin ganin halittun nan haye bisa wasu irn dawakai masu girman gaske, ya tsorata da irin wadannan halittu da bai taba ko jin labarinsu ba a cikin tatsuniya. Domin kuwa wasu daga cikin halittun na da kai irin na jaki, wasu kawunansu irin na rakuma, wasu kuma irin kawaunan shanu gare su, har da kahonni.

Yayin da halittun nan suka yi arba da rundunar birai, sai suka gangaro daga kan tsauni suka tsaya a bakin korama. Sai ya kasance wannan korama ta raba tsakanin rundunar birai da rundunar halittun masu kama da fatalwa. Daga nan fa sai halittunnan suka rika sungumar duwatsu, manya-manya, suna jifar birai da su. Duk yawan halittun nan sukan yo jifa lokaci guda, sai duwatsun nan su sauka, kamar an yo ruwansu daga sama, cikin rundunar birai. Birai suka rika zuba kasa matattatu kamar ana girgiza bishiyar mangwaron da 'ya'yanta suka nuna tibis.

WhatsApp 080327675747
Za mu ci gaba gobe, da karfe tara na dare (9:00PM), in sha Allah.

Allah ya kai mu!4. HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassarar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.

Yayin da halittun nan, masu kama da fatalwa, suka yi arba da rundunar birai, sai suka gangaro daga kan tsauni suka tsaya a bakin korama. Sai ya kasance wannan korama ta raba tsakanin rundunar birai da rundunar halittun masu kama da fatalwa. Daga nan fa sai halittunnan suka rika sungumar duwatsu, manya-manya, suna jifar birai da su. Duk yawan halittun nan sukan yo jifa lokaci guda, sai duwatsun nan su sauka, kamar an yo ruwansu daga sama cikin rundunar birai. Birai suka rika zuba kasa matattatu kamar ana girgiza bishar mangwaron da 'ya'yanta suka nuna tibis.

Da Janshahu ya ga halittun nan na ta karkashe birai babu kakkautawa, sai ya yi wa mutanensa uku tsawa, ya ce su dana kibiyoyi ga baka su harbi halittun. Nan take kowa ya jawo bakansa ya dana kibiya suka sakar wa halittun, nan take wadanda aka harba suka fadi kasa matattu. Janshahu da mutanensa fa suka yi ta yi wa halittun nan ruwan kibau, suna zubar da su kasa matattu. Da halittun nan suka ga haka, abin da biran nan ba su taba yi musu ba, sai suka tsorata suka fara ja da baya. Janshahu da mutanensa suka ci gaba da sakar musu kibau. Suka kuma birai da suka ga abokan gabarsu sun fara ja da baya, sai suka yi ruri gaba daya suka tsallaka koramar nan suka tasar musu. Da halittun nan suka ga haka sai suka juya da baya da gudu suka haye saman tsauni, suka gangara bayansa suka bace.

Janshahu da birai suka bi su har suka kai saman tsauni. Da suka ga halittun sun gangara kasa sun bace, sai suka kyale su. Birai suka yi ta tsalle-tsallen cin nasara. A saman tsaunin Janshahu ya tsinci wani allon icce da rubutu na farin kwallin kura, rubutun na dauke da sako kamar haka:

Ya kai wannan dan Adam da ka tsinci kanka a cikin wannan kasa. Ka sani cewa za ka zama Sarkin biran da za ka tarar a cikin wannan tsibiri. Ka sani kuma ba ka da wata hanyar kubuta daga gare su face ko dai ta hanyar da ta yi gabas daga wannan tsauni, ko kuma hanyar da ta yi yamma daga gare shi. Idan ka bi hanyar da ta yi gabas, za ka fada cikin kasar wasu halittu masu kama da fatalwa. Bayan su ma akwai miyagun namun daji da ifiritai da maridai masu hatsarin gaske. Idan ka yi nasarar fita daga wannan kasa, bayan tafiyar watanni uku, za ka tarar da wata babbar teku, wadda ruwanta ya zagaye duniya. A nan za ka sami jirgin da zai dauke ka zuwa kasashen bil'Adamu.

Idan kuwa ka dauki hanyar da ta yi yamma daga wannan tsauni, bayan ka yi tafiyar wata hudu, za ka isa wani kwari da ake kira Kwarin Tururuwa. Wannan kwari yana da matukar hadari, amma idan ka wuce shi, ka yi tafiyar kwana goma.... Bayan tafiyar kwana goma za ka iso ga wata korama wadda ruwanta yake gudana da sauri kamar walkiya. Don tsananin saurin gudun ruwan idanu kan iya makancewa idan aka tsaya kallon shi. Wannan korama takan tsiyaye duk ranar Asabar, ta zamo babu digon ruwa ko daya a cikinta. Daga tsallaken wannan korama akwai wani babban birni na Yahudawa, wadanda ba su yadda da addinin da Muhammadu zai zo da shi ba, duk kuwa da cewa sun karanta labarin zuwansa a cikin littafinsu. Babu mutum daya mai burbushin addinin Islama a cikin wannan birni. Don haka zai fi dacewa a gare ka ka tsaya tare da biran nan kana matsayin Sarkinsu. Muddin kai ne Sarki a cikin biran nan, to, halittun nan masu kama da fatalwa ba za su taba samun nasara a kansu ba. Wanda ya yi wannan rubutu shi ne, Shugaba Sulaimanu Dan Dawuda (Amincin Allah ya tabbata a gare su).

Da Janshahu ya gama karanta sakon da ke jikin allo sai hawaye suka karyo masa, ya gaya wa mutanensa sakon da ya karanta. Daga nan sai suka gangaro daga kan tsauni tare da rundunar birai, suna tsalle-tsalle suna murnar samun nasara bisa ga abokan gabarsu, har suka iso fada.

Haka dai Janshahu ya ci gaba da zama a cikin birai, yana mulki da adalci har ya kwashe shekara guda cur. Wata rana sai ya ce wa Waziransa yana so a hada masa askarawa domin yana da sha'awar fita farauta. Aka shirya fita farauta, suka kutsa cikin daji mai yawan itatuwa da namun daji. Bayan sun yi kwana da kwanaki suna farauta, suna kara kutsawa cikin daji, rannan sai suka tunkari Kwarin Tururuwa.da ganin wannan wuri sai Janshahu ya gane shi, domin ya karanta siffarsa a jikin allon nan da ya tsinta a saman tsauni.

Da suka zo gab da wannan kwari sai Janshahu ya ce a sauka a ci abinci a huta a wannan wuri. Aka kafa tantuna, suka zaunan wannan wuri suna ci suna sha tsawon kwanaki goma. Ranar kwana na goma sha daya, cikin dare da Janshahu ya lura da cewa birai sun yi barci, sai ya kira mutanensa gefe guda ya ce musu, "Ina so mu tsere daga wadannan birai, mu bi ta cikin Kwarin Tururuwa mu isa ga birnin Yahudawa. Daga can mu nemi hanyar komawa birninmu. Idan Allah ya yi mana gyadar dogo sai mu koma gida lafiya."

Suka amsa masa, "Mun ji mun amince."

Suka bari sai da dare ya tsala, suka tashi suka saka sulke, suka rataya takubba, suka soke wukake ga gindinsu. Suka kama hanya da hanzari, suka nufi yamma. Suka yi ta tafiya har gari ya waye. Da gari ya waye birai suka farka daga barci ba su ga Janshahu da mutanensa ba, sai suka tabbatar da guduwa suka yi. Nan da nan suka hau karnuka masu kama da dawaki, suka rabu gida biyu, wasu suka nufi gabas wasu kuma suka yi yamma inda Kwarin Tururuwa.

Da yake su Janshahu a kasa suke tafiya, su kuwa birai a kan karnuka suke masu gudu da sauri, nan take suka fara hango Janshahu da mutanensa suna gab da shiga Kwarin Tururuwa. Birai suka kara kaimi domin su cim musu. Yayin da Janshahu da mutanensa suka hango birai sun nufo su a sukwane sai suka afka cikin Kwarin Tururuwa, amma ina, ko da suka shiga cikin kwari har birai sun tarar da su, suka afka ciki tare. Lokacin da birai ke shirin kama Janshahu da mutanensa, sai kuwa ga rundunar tururuwa ta taso wa biran nan kamar farin dango. Kowace tururuwa girmanta kamar kare. Da ma can abokan gaba ne tsakaninsu da birai.

(c) 2015 Taskar Bukar Mada
http://bukarmada.com
[email protected]
Twitter: @bukarmada
WhatsApp: +2348021218337
BBM: 2BDDD505

Za mu ci gaba gobe da karfe tara na dare (9:00PM), in sha Allah.

Allah ya kai mu!5. HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Daga Littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassarar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.

Lokacin da birai ke shirin kama Janshahu da mutanensa, sai kuwa ga rundunar tururuwa ta taso wa biran nan kamar farin dango. Kowace tururuwa girmanta kamar kare. Da ma can abokan gaba ne tsakaninsu da birai.

Nan take yaki mai tsanani ya barke tsakanin dakarun tururuwa da na birai. Sai kawai tururuwa ta kama biri da bakinta mai kaifin gaske, sai dai ka ji kyas! Ta raba shi biyu ta yarbar. Haka su ma birai suka shiga saran tururuwa da takubba, suna kashe su. Aka ci gaba da gwabza yaki har zuwa marece. Rundunar tururuwa ta fi ta birai yawa, don haka suka sami galaba a kan birai suka kashe su da yawa. Da Janshahu ya ga hankalin birai ya dauku ga yaki, sai ya sulale da mutanensa, suka bi tsawon kwarin, suka ci gaba da tafiya, tun da marece har dare ya yi, har gari ya waye ba su tsaya ba. Birai sun shagala da yaki da tururuwa, da gari ya waye haske ya bayyana, birai suka lura da Janshahu ya sulale da mutanensa sai suka bar yaki suka bi bayansu a sukwane, cikin kankanin lokaci suka tarar da su.

Da Janshahu ya gan su sai ya yi wa mutanensa tsawa, ya ce, "Ku jawo takubbanku ku yi shirin yaki." Kowa ya zare takobinsa ya tsaya yana jiran isowar birai. Da birai suka matso kusa gare su, sai mutanen nan suka yi kukan kura suka fada musu da sara, ba ji ba gani, suka yi ta zubar da su kasa matattu. Can sai wani katon biri, mai hannu kamar kafar giwa, ya husata ya bugi daya daga cikin mutanen da hannunsa. Saboda karfin wannan biri, mutumin ya karye gida biyu, ya fadi kasa bai ko shura ba.

Ganin haka sai birai suka kara himma, suka taso wa Janshahu da sauran mutanensa. Da Janshahu ya ga haka sai ya umurci mutanensa da su gudu. Suka kara kutsawa cikin Kwarin Tururuwa. Janshahu ya hangi wata babbar korama, ruwanta yana gudu, daga gefenta kuma rundunar tururuwa ce babu iyaka. Tururuwa na ganin Janshahu da mutanensa sai ta taso musu ta zagaye su. Ganin haka sai daya daga cikin mutanen Janshahu ya fara saran su da takobinsa, yana raba su gida biyu. Tururuwa fa suka husata suka kyale Janshahu da mutum daya da ke tare da shi, suka rufar wa wannan mai saran su. Suka kama shi suka daddatsa gunduwa-gunduwa da bakunansu. Daga nan kuma sai ga biran nan sun taso za su yi wa Janshahu sukuwar salla. Da ganin haka sai Janshahu ya ja hannun mutum dayan nan da ya rage, suka runtuma da gudu suka fada cikin ruwan koramar nan.

Janshahu ya yi iyo har ya isa bakin gaba. Allah ya taimake shi ya kama reshen wata bishiya da ya sunkuyo cikin ruwa, ya hau. Ya sauka a kan kasa. Abokin tafiyarsa kuwa sai igiyar ruwa ta ja shi ta fyada ga wani dutse, nan take rai ya yi halinsa, ruwa ya tafi da shi. Shi kuwa Janshahu sai ya tsaya daga tsallaken koramar yana hangen tururuwa da birai, wadanda yaki mai tsanani ya rincabe a tsakaninsu. Da birai suka ga ba dama, tururuwa na neman karar da su, sai suka juya da baya cikin tsananin bakin cikin rabuwa da Janshahu.

Janshahu ya tube tufafinsa ya matse, ya shanya su bisa yashi, ya zauna yana bakin cikin rabuwa da mutanensa. Da dare ya yi ya sami wani kogo ya shige, amma saboda tsoro da kuma kadaici bai yi barci ba har gari ya waye.

Bayan gari ya waye, ya fita daga cikin kogo ya kama hanya ya yi ta tafiya ba dare ba rana, yana cin 'ya'yan itatuwa yana shan ruwan koramu har ya kawo ga tsaunin nan mai haske kamar wuta. Ya raba shi ya wuce, daga nan sai ga wani katon kogi ya bayyana a gabansa. Ruwansa na gudu kamar walkiya don sauri. Daga tsallaken kogin ya hangi wani babban birni, wanda yake shi ne birnin nan na Yahudawa da ya karanta labarinsa a cikin allon Annabi Sulaimanu.

Ya zauna a bakin gabar kogin yana jiran ranar Asabar ta zagayo. Ranar na zuwa kuwa sai kogin nan ya kafe. Janshahu ya bi ta cikinsa ya tsallaka zuwa birnin Yahudawa. Ya shiga birnin ya yi ta yawo amma bai ga kowa ba. Da ya gaji da yawo sai ya je ga kofar wani gida ya tura ta, sai ya ga ta bude. Bai yi wata-wata ba sai ya kutsa kai cikin gidan. Ya iske mutanen gidan zaune a tsakiyar gidan, sun yi shiru babu mai magana da wani, kamar masu zaman makoki.

Janshahu ya ce musu, "Ni bako ne, mayuwanci. Ko za ku taimake ni da abinci?"

Mutanen suka nuna masa abinci da abin sha, suka yi masa ishara da hannu cewa, "Ci ka sha abin da ranka yake so, amma kada ka yi magana."

Ya zauna ya jawo akushin abinci gabansa, ya nada dayan cikinsa, ya sha ruwa ya yi gyatsa. Ya kwana tare da mutanen nan. Da gari ya waye, mai gida ya yi masa maraba da zuwa, sa'annan ya tambaye shi inda ya fito da kuma inda za shi?

Wannan tambaya sai ta tuna wa Janshahu da gida, ya tuna mahaifansa da jama'arsa, sai ya fashe da kuka. Da ya natsa, sai ya kwashe labarinsa duka ya gaya wa mai gida. Ya gaya masa shi dan Sarkin kasar Kabila ne. Bayahude ya yi mamaki da jin labarin Janshahu, ya ce, "Ba mu taba jin sunan wannan kasa taku ba. Amma mukan ji fatake na labarin wani babban birni wai shi Al-yaman, wanda ke yammacin wannan birni namu."

Janshahu ya tambayi Bayahude, "Menene nisan wancan birni na Al-yaman daga nan?"

Bayahude ya amsa masa, "Fatake sun ce tafiyar shekara biyu da watanni uku ce a kan rakuma."

"Yaushe ayarin fatake ke tashi zuwa can?" Janshahu ya tambaya.

Bayahude ya amsa masa, "Suna nan suna shiri. Nan da shekara daya za su tashi."

Da Janshahu ya ji haka sai hawaye suka karyo masa. Ya yi kuka domin rabuwa da mahaifinsa da mahaifiyarsa, ya tuna mutanensa da suka mutu. Bayahude ya rarrashe shi yana cewa, "Daina kuka dan samari. Ka zauna tare da mu kafin ayarin fatake ya gama shiri, sai mu hada ka da su. Idan kuka isa birnin Al-yaman sai su hada ka da wasu fataken masu zuwa kasarku."

Janshahu ya zauna a gidan Bayahude tsawon wata biyu. Kullum yakan fita yawo, ya shiga cikin birni sako-sako, lungu-lungu, yana kashe kwarkwatar ido. Ran nan yana yawo cikin birni, kamar yadda ya saba, sai ya ji wani mutum yana shela yana cewa, "Wa zai yi mini aikin yini guda in ba shi dinari dubu da kyakkyawar kuyanga?" Amma babu wanda ya ce wa mutumin nan ci kanka.

Da Janshahu ya ga babu wanda ya daga kai balle ya kalli mai shelar nan, sai ya ce a cikin ransa, "Babu shakka aikin da mutumin nan ke son a yi masa yana da matukar wahala. Ba don haka ba me zai sa ya sa kudi haka tsagwagwa har da kuyanga a kan aikin yini guda?" Janshahu ya ci gaba da tunani a cikin ransa, "Amma kuma fa an ce da rashin tayi a kan bar araha. Bari in karbi kudin mutumin nan in ga wane irin aiki ne wannan. Mai rabon ganin badi ko ana dakawa a turmi ai zai gani."

Ya tafi wurin mai shela ya ce masa, "Ga ni. Zan yi aikin da ka bukata."

Mutumin ya ce masa, "Zo mu je." Ya shige gaba Janshahu na biye da shi har suka isa ga wani babban gida, abin kawata da kwalliya. Suka tarar da wani Bayahude, attajiri, ya harde bisa wani abin zama da aka yi da labunus. Mai shela ya matsa kusa ga attajirin nan, ya sunkuyar da kai cikin ladabi ya ce, "Ya shugabana, na yi shela tsawon wata uku a cikin wannan birni, ban sami wanda zai yi aikin da kake so ba sai wannan saurayi."

Da tajiri ya ji haka, sai ya yi marhabin da Janshahu. Ya mike daga kan abin zamansa ya kama hannun Janshahu ya shiga da shi cikin wani kawataccen daki. Ya umurci kuyangi su kawo masa abinci. Kuyangi suka tafi suka dawo da akussa cike da nama, suka ajiye a gaban tajiri da Janshahu. Aka kawo musu ruwa suka wanke hannuwansu, suka ci nama suka koshi. Suka jawo gorunan sha, suka sha daga cikinsu.

Bayan sun gama cin abinci, sai tajiri ya tashi ya fita. Ya dawo da jaka mai dinari dubu a cikinta tare da wata kyakkyawar kuyanga. Ya ce wa Janshahu, "Dauki wannan kudi da yarinya, mallakarka ne. Ka kwana a cikin wannan dakin, sai gobe da safe zan dawo mu tafi zuwa ga aikin da za ka yi mini."

(c) 2015 Taskar Bukar Mada
http://bukarmada.com
[email protected]
Twitter: @bukarmada
WhatsApp: +2348021218337
BBM: 2BDDD505

Za mu ci gaba

Allah ya kai mu!
6. HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassarar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.

Bayan sun gama cin abinci, sai tajiri ya tashi ya fita. Ya dawo da jaka mai dinari dubu a cikinta tare da wata kyakkyawar kuyanga. Ya ce wa Janshahu, "Dauki wannan kudi da yarinya, mallakarka ne. Ka kwana a cikin wannan dakin, sai gobe da safe zan dawo mu tafi zuwa ga aikin da za ka yi mini."

Janshahu da yarinya suka kwana wuri guda, suka dumama jikin juna. Da safiya ta yi, tajiri ya sa aka kai Janshahu gidan wanka, aka shirya shi cikin tufafin alharini, na alfarma. Suka zauna a cikin dakin shakatawa, tajiri ya sa kuyangi suka hallaro da molo da dundufa da sarewa. Aka shirya abubuwan ci da na sha, a cikin akussa da goruna. Suka ci suka sha. Kuyangi suka yi rawa da waka. Ba su gushe ba kan haka har dare ya tsala. Tajiri ya tashi ya nufi dakinsa, ya umurci Janshahu ya koma nasa dakin, sai gobe za su tafi zuwa ga aikin da zai yi masa.

Janshahu ya koma dakinsa, suka kwana tare da kuyanga. Da gari ya waye aka kai shi gidan wanka, aka ba shi tufafi na alfarma ya sanya. Bayan ya dawo daga gidan wanka sai tajiri ya tambaye shi, "Shin ka shirya a kan aikin da za ka

Please Login or Register in order to submit comment