Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

labari ya ce, "Na rantse da Allah ya kai dana, ban taba jin sunan wannan fada ba balle in san inda take. Duk tsawon rayuwata, tun lokacin Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), nake mulkin tsuntsaye da dabbobi da aljanu amma ban taba jin wannan suna ba wai Takanni Fadar Jauhari.

....

KASH! Ya zama wajibi na diga aya a nan saboda kada mu shiga cikin hakkin wadanda suka yi rijista. Idan Allah ya kai mu ranar Asabar za mu fara kawo wata hikayar sabuwa fil.

ME YA SA BA MU KARASA LABARI?

Da yawa idan mutane suka ga an gutsere labari, sukan damu matuka, wasu marasa hakuri har sukan fara guna-guni, masu karancin tarbiya kuma sai ka ji sun biyo da zagi. Akwai dalilan da ya sa ba mu kai labari har zuwa karshe.

Dalili na farko shi ne, mun fada muku cewa za mu buga littafin ne mu fitar kasuwa, to idan muna karasa dukkan labarun da muka dauko daga cikin littafin, idan littafin ya fito, wa za ya saya? Kun rigaya kun karance littafin tun a nan, ke nan idan mun fitar da shi kasuwa zai yi kwabaso, za a bar mu da tarin takardu ke nan, bayan mun kashe kudinmu wajen bugawa. Amma idan muka katse labarin, za ku nemi littafin ku saya domin jin karshen labari. Ai don a ci riba ake kasuwanci, ba don a fadi ba.

Dalili na biyu kuma shi ne, akwai 'yan amana da muke tare da su, wadanda ba mu taba ganinsu ba, ba su taba ganinmu ba, suka zuba kudinsu, wuri na gugar wuri, tun daga Naira 1,000 har zuwa Naira 10,000, suka yi rijista domin su karanta cikakken littafin a nan facebook. Lokacin da muka yi ta yayata bayanin rijistar a nan, http://bukarmada.wordpress.com/2014/02/03/dare-dubu-da-daya mutane da yawa sun dauke mu mayaudara, 'yan damfara, cima-kwance, babu irin maganganun da ba mu ji ba. Wadannan mutanen ne kadai suka yarda da mu, suka yi rijistar, su ma watakila ko don wawancinsu ne, ko ko ba su san darajar kudi ba ne, ya sa suka yi rijistar. To, ko ma dai mene ne, bukatar tasu ta biya, domin babu daya daga cikinsu da ya taba yin da-na-sanin zuba kudinsa.

Alhamdulillahi, mun gode wa Allah da ya sa muka fita kunyarsu. Da a ce damfara ce muka shirya, da tuni labarin ya watsu a facebook kamar wutar daji, ku ji ana ta gargadi cewa kada wanda ya yarda ya yi rijista da zauren DARE DUBU DA DAYA, 'yan damfara ne. To saboda Allah, wasu sun biya kudinsu domin karanta cikakken littafi, sai kuma ga shi nan ana zubewa kyauta, kowa da kowa na karantawa, to ina amfanin yin rijistar ke nan?

Dalili na uku ba wani dalili ba ne mai kwari, sai dai shi ma abin dubawa ne. Ya kamata a cikin kowane al'amari na duniya a rinka kwatanta adalci. Mun san cewa duk labarin da muka saki a nan, to ya zama na kowa da kowa. Kowa zai iya 'sharing' masu kwasa kuma za su kwasa su kai zauruka ko shafukansu, a facebook ko a whatsapp. Ba mu hana 'sharing' ba, kuma ba mu hana a kwasa a watsa ko'ina ba, sai dai idan za a watsa, to a fada wa jama'a daga inda aka dauko labarin. To, amma akwai hankaki masu mayar da diyan wasu nasu. Wasu za su kwasa su kai shafukansu, suna masu fada wa mabiyansu cewa, su ne suka fassara labarin. Idan muka gutsire labari, kun ga ai an buge bakin tsanya da tabarya. Idan har su suka yi fassarar, sai su ci gaba daga inda muka tsaya. Idan mabiyan nasu sun matsa musu da son jin karshen labari, sai ka ji su kuma sun dawo mana nan, za ka ji wasu na cewa, ai 'idea' ce ta kare mana ko kuma, ai mu ma ba mu san karshen labarin ba shi ya sa muka datse shi, idan gaskiya ne a ci gaba mana. To mun gano wayon naku, mun ki ci gaba, idan kuna son ganin karshen labarin ku nemi littafin.

Wasu kuma za ka ji suna cewa, ai mu ma satowa muka yi, tun da ba mu muka kirkiri labarin ba. Wannan gaskiya ne, ba mu muka kirkiri labarin ba na asali, fassara ce kawai muka yi, kuma fassarar ce wadda muke karewa, ba labarin ba. Af, ko ka dauka fassara ba ta cikin fasaha? Tafi dauko Alfu Laila na Larabci, ko Arabian Nights na Turanci ka yi taka fassara, babu mai hana ka. Ca nake da fassara Abubakar Imam ya yi zarra a cikin marubuta?

SABON TSARIN RIJISTA' MASU BUKATAN KARANTA HIKAYOYINMU DA DAMA CIKI KUWA HARDA KARASHIN WANNAN SUNA IYA YIN RIJISTA AKAN 200 KACAL DA KATIN MTN DON MOREWA TSARIN' ZAKA KARANTA HIKAYA HARNA TSAWON WATA GUDA A ZAURENMU BISA WANNAN MUTANE DA DAMA SUNA WANNA TSARI A YANZU'.

DON NEMAN KARIN BAYAN
WHATSAPP
+1248032767547

Incomplete

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment