Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin tanti ta harde bisa wata karaga da aka haka mata.

Tana nan zaune sai ga Sarki Daigamusa da dansa Janshahu sun shigo wurinta. Ta tashi da hanzari ta gayar da Sarki cikin girmamawa. Sarki ya zauna, ya zaunar da Janshahu dama gare shi, ya zaunar da Gimbiya Shamsiya daga hagunsa. Bayan Sarki ya yi wa Gimbiya barka da zuwa, sai ya juya ga Janshahu ya ce,"Ya dana, gaya mini abin da ya faru gare ka bayan da muka rabu a wajen farauta."

Janshahu ya kwashe labari kaf ya gaya wa Sarki. Sarki ya yi mamaki, matukar mamaki. Ya dubi Shamsiya ya ce, "Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya sanya ki sanadiyyar sake saduwata da dana. Allah abin godiya! Ki fadi dukkan abin da kike so, ni kuwa zan yi miki shi."

Sai ta ce masa, "Ya Sarki, ina so ka gina mini kasaitacciyar fada da lambu mai furanni da 'ya'yan itatuwa da koramu na gudu a cikinta."

Sarki ya ce, "Na ji, na karba."

Suna nan suna mai da zance, kwaram sai ga mahaifiyar Janshahu ta shigo wurin tare da dukkanin matan wazirai da hakimai da manyan fadawan Sarki. Da Janshahu ya gan ta sai ya mike cikin hanzari, ya je ya tare ta. Suka rungume juna cikin farin ciki, hawaye suka yi ta zuba daga idanunta. Don murna har ta wake wadannan baitoci:

"Farin ciki ya mamaye mini zuciya,
Don murna idanu na zubar da hawaye.

Idanu sun saba zubar da hawaye,
Na bakin cikin tafiyarka ba waiwaye.

Amma yanzu kukan da nake yi,
Na farin ciki ba sauran tsumaye.

Suka ba juna labarin bayan rabuwa da kuncin da zuciyoyinsu suka shiga don rabuwa da juna. Sarki ya koma fadarsa, Janshahu kuwa ya tafi tare da mahaifiyarsa zuwa tantinsa suka zauna suka ci gaba da hira har zuwa lokacin da kuyangin yarinya Shamsiya suka shigo wurinsu. Suka ce ga shugabarsu nan ta zo domin gaisawa da Sarauniya, mahaifiyar Janshahu. Yayin da Sarauniya ta ji haka sai ta tashi ta tafi bakin kofa ta taryi yarinya Shamsiya. Bayan yarinya ta gayar da ita cikin ladabi, sai Sarauniya ta ja hannunta suka koma cikin tantin ta zaunar da ita kusa gare ta. Bayan sun gama gaisawa, sai Sarauniya da rukunin matan da ta zo da su, suka tafi tare da Shamsiya zuwa ga tantin da aka shirya wa ita Shamsiyar, suka zauna can suka ci gaba da hira.

Sarki Daigamusu kuwa ya yi ta rarraba wa talakawa sadakar tufafi da abinci da kudi saboda murnar dawowar dansa lafiya. Aka zauna a bayan gari a ci mai dadi a sha mai dadi, ana kade-kade da wakoki har tsawon kwana goma. Daga nan Sarki ya sa aka shirya wata irin gagarumar daba, domin komawa cikin birni. Ya hau doki, matarsa na gefensa na hagu, dansa na gefensa na dama, ita kuwa yarinya Shamsiya tana gefen mahaifiyar Janshahu. Askarawa suka saka su tsakiya, wasu a gaba wasu a baya. Wasu a gefen dama, wasu a gefen hagu. Aka dunguma da kade-kade da bushe-bushe, aka nufi cikin birni. Birnin kuwa an kawata shi matuka, kowane gida an shafe shi da fenti launi daban-daban. A kan hanyar da dawaki za su bi kuma an shimfida dardumomi. Ba a jin komai sai amon ganguna da algaitu da muryoyin zabiyoyi. Aka raka Sarki har fadarsa.

Aka ci gaba da shagali har tsawon kwana goma. Yarinya Shamsiya ta yi farin ciki matuka, ta yi mamaki da irin wannan karramawa da ta gani. Bayan an tsagaita da shagali, Sarki ya kira kwararrun masu gini, ya bayyana musu irin gidan da yake so a gina wa yarinya Shamsiya. Magina suka dukufa domin cika umurnin Sarki. Yayin da Janshahu ya ga masu gini sun dukufa ga aiki, sai ya nuna musu wani katon dutse ya ce yana so su rarake masa cikinsa, su mayar da shi kamar akwati. Suka yi kamar yadda ya nema. Ya dauko tufafin nan na gashi, na yarinya Shamsiya, ya sanya a cikin dutsen. Ya sa aka rufe bakin dutsen da narkakkar darma. Aka yi gina mai zurfi, daidai inda za fara aza ginin gidan, aka rufe wannan dutse. Aka dora gini samansa.

Cikin 'yan kwanaki kadan sai ga gida ya tsahi, kamar dauko shi aka yi daga wani wuri aka aza. Gida ya zama kamar yadda yarinya ta bukata, har ma ya fi yadda ta ce kyau. Bayan an kammala gida, sai kuma aka shiga hidimar bukin daurin auren Janshahu da yarinya Shamsiya. Aka daura aure, aka yi shagulgula masu yawa. Aka kai amarya sabon gidan da aka gina mata. Tana shiga gidan sai ta shaki kamshin tufafinta na gashi, nan take ta gane inda aka boye ta. Ta kudurce a ranta cewa za ta dauki abarta ta gudu. Ta bari sai da dare ya raba, yayin da Janshahu ya dulmiya cikin barci, ta lallaba ta tafi inda aka binne tufafin. Ta yi gina mai zurfi a kasa, sa'annan ta rarake kasan wurin har ta cimma wurin da aka boye su a cikin dutse. Ta bambare dalmar da aka toshe bakin dutsen da ita, ta sa hannu ta ciro tufafin ta sanya su ga jikinta.

Ta raurawa da farin ciki ta kada sama cikin iska. Ta haye bisa rufin wani soro, ta ce da bayin da ta gani ba su yi barci ba, "Ku kirawo mini Janshahu in yi ban kwana da shi." Bayi suka shiga ciki suka gaya wa Janshahu abin da ke faruwa, nan take ya fito da hanzari. Yana fitowa sai ya hange ta can kololuwar rufin soro sanye da tufafinta na gashi. Sai ya tambaye ta, "Me ya sa ki aikata wannan abu?"

Ta amsa masa masa, "Ya masoyina, sanyin idanuna, farin cikin zuciyata. Wallahi ina son ka, so mai tsanani. Kuma na yi farin ciki matuka da na hada ka da mahaifanka da sauran 'yan uwa da abokan arziki. Yanzu idan har kana so na kamar yadda nake son ka, to, ka shirya ka same ni a kasar Takanni Fadar Jauhari." Tana gama fadar haka sai ta tashi firrr ta nufi kasarsu wurin mahaifanta da 'yan uwanta. Janshahu na ganin haka sai ya fadi kasa magashiyan, kamar matacce.

(c)

Za mu ci gaba , da karfe tara na dare (9:00PM), in sha Allah

Allah ya kai mu.12. HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassarar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.

Janshahu ya ce wa Shamsiyya, "Me ya sa ki aikata wannan abu?"

Ta amsa masa, "Ya masoyina, sanyin idanuna, farin cikin zuciyata. Wallahi ina son ka, so mai tsanani. Kuma na yi farin ciki matuka da na hada ka da mahaifanka da sauran 'yan uwa da abokan arziki. Yanzu idan har kana so na kamar yadda nake son ka, to, ka shirya ka same ni a kasar Takanni Fadar Jauhari." Tana gama fadar haka sai ta tashi firrr ta nufi kasarsu wurin mahaifanta da 'yan uwanta. Janshahu na ganin haka sai ya fadi kasa magashiyan, kamar matacce.

Yayin da bayi suka ga haka, sai hankalinsu ya tashi. Suka bazama da gudu suka gaya wa Sarki Daigamusu halin da dansa yake ciki. Cikin tsohon daren nan Sarki ya hau doki, babu ko sirdi, ya nufo gidan da dansa yake. Ya same shi kwance bisa kasa, yana numfashi sama-sama. Ya yayyafa masa ruwan wardi a fuska. Da Janshahu ya farfado ya ga mahaifinsa rungume da shi, sai hawaye suka karyo masa. Ya san cewa lalle ya rasa abar begensa. Sarki ya tambaye shi abin da ya faru. Sai ya amsa masa da cewa, "Ya mahaifina, ka sani cewa, yarinya Shamsiya ba mutum ba ce, tana daga cikin jinsin aljanu. Abu kaza da kaza ya faru a tsakaninmu." Ya kwashe dukkan abin da ya faru tun lokacin da ya fara ganinta har zuwansu wannan birni, ya gaya wa mahaifinsa.

Yayin da Sarki ya ji labarin da dansa ya gaya masa, sai ya cika da mamaki, ya ce masa, "Ya dana, don wannan kada ka tayar da hankalinka. Zan sa a tara mini dukkan fatake da matafiya da tsofaffi, in tambaye su game da Takanni Fadar Jauhari. Na tabbata za a sami wani wanda ya san kasar. Ka ga sai mu tafi, har da ni, wurin mahaifan Shamsiya mu nemi izinin dawowa da ita. Da yardar Allah na san za su amince da bukatarmu." Haka dai Sarki ya yi ta kwantar wa da dansa hankali har gari ya waye.

Gari na wayewa Sarki ya kira Waziransa hudu ya ce su tara masa fatake da matafiya, su tambaye su labarin kasar Takanni, Fadar Jauhari. Ya kara da cewa, "Duk wanda ya san wurin zan ba shi tukuicin dinari dubu hamsin domin yi mana jagora zuwa can." Wazirai suka tafi da sauri suka aikata kamar yadda Sarki ya umurce su. Amma babu daya daga cikin fatake ko matafiya da ya taba jin sunan wata kasa wai ita Takanni Fadar Jauhari, balle har ya san inda take. Suka koma suka gaya wa Sarki. Sarki ya yi jugum yana tunanin halin da dansa zai shiga idan ya ji wannan labari. Sai ya sa aka zabo masa kuyangi kyawawa. Aka gayyato kwararrun zabiyoyi da makada molo da sauran kayan kida, wadanda babu wani Sarki da yake da irinsu. Nufinsa wai ya tura su ga Janshahu domin su kawar masa da tunanin yarinya Shamsiya a cikin ransa. Haka kuma ya aika da 'yan kwarbai da dukiya mai yawa a cikin kasashe domin su tambayo masa labarin kasar Takanni Fadar Jauhari. Suka tafi, bayan wata biyu suka dawo babu wani labari. Sarki ya cika da bakin ciki mara misaltuwa. Ya tashi ya nufi wurin dansa, ya same shi zaune a tsakiyar kuyangi, molo da sarewa na tashi, wata zabiya ta karkace kai tana ta rera waka. Amma duk wannan budiri bai hana Janshahu tunanin yarinya Shamsiya ba.

Bayan Sarki ya shiga wurinsu, sai ya yi shiru ya kasa gaya wa Janshahu cewa ba a sami labarin kasar Takanni ba. Can dai ya kinne ya ce masa, "Ya dana, babu mutum daya, a duk fadin kasar nan da kewayenta, wanda ya taba jin sunan kasar Takanni Fadar Jauhari, balle har ya san inda take. Amma ka kwantar da hankalinka, zan sa a tara maka dukkan 'yan matan kasar nan, ka zabi wadda ma ta fi Shamsiya kyau, sai a daura maka aure da ita."

Da Janshahu ya ji haka, sai idanunsa suka hauye, sai hawaye shar shar. Ya rera wadannan baitoci biyu yana cewa:

"Hakuri yakan kare wani lokaci,
Soyayya takan dore a cikin zuciya.

Yaushe zan sake ganin ki masoyiya?
Jikina yai rauni don rashin ki Shamsiya."

Wannan ke nan game da Janshahu da yarinya Shamsiya.

To, ashe kuma akwai wata dadaddiyar gaba tsakanin Sarki Daigamusu da wani Sarkin Hindu mai suna Sarki Kafidu. Shi wannan Sarki yana da karfi sosai, domin kuwa ya tara rundunar mayaka babu adadi. A cikinsu akwai sadaukai da jarumai masu taurin rai da karfin hali. Sarki Kafidu na da hakimai dubu, a karkashin kowane hakimi akwai dagatai dubu, kowane dagaci yana da rundunar mayaka adadin mutum dubu hudu. Sarki Kafidu na da Wazirai guda hudu. Kowane Waziri yana da kananan hakimai da dagatai a karkashinsa, su ma duka suna da rundunonin mayakansu. A ma tsaya bayyana irin karfin Sarki Kafidu bata lokaci ne kawai.

Sai dai duk da irin wannan karfi na Sarki Kafidu, Sarki Daigamusu ya taba yi masa kaca-kaca wurin yaki, har ma ya mayar da wasu hakimai a karkashin mulkinsa, kuma ya sami ganima mai yawa. Tun daga wannan rana Sarki Kafidu bai kara daga wa Sarki Daigamusu hannu ba balle har ya ce zai yake shi. Kwaram sai ya ji labarin ai Sarki Daigamusu ya watsar da duk wasu lamura na mulki, hankalinsa ya karkata kacokan wurin dansa da ya fada cutar so. Ya sami labari Sarkin ba ya kula kome na sha'anin mulki, hatta myakansa sun yi sanyi, kansu ya rabu saboda babu mai tsawata musu.

Don haka sai Sarki Kafidu ya tara Waziransa da manyan hakimansa ya ce musu, "Kun sani sarai yadda Sarki Daigamusu ya fatattake mu, ya kashe mana iyaye, ya kwace mana kasa da mata ya maishe su kuyangi, ya kwashe mana dukiya. Yanzu na sami labari cewa ya yi watsi da al'amurran mulki, ya tare a gindin dansa Janshahu yana jiyyarsa. An ce mini askarawansa duk sun rarrabu, kansu ba hade yake ba, saboda ba ya kula su. Ina so mu yi amfani da wannan damar mu afka masa ba tare da ya shirya ba, mu fatattake shi kamar yadda ya fatattake mu. Don haka yanzu kowa ya tafi ya shirya askarawan da ke karkashinsa, a hada shirin yaki sosai, mu afka wa Sarki Daigamusu ba ya da sanannen ciki. Mu kashe shi, mu kashe dansa, mu mallake kasarsa.”

Hakimai suka amsa gaba daya, "Mun ji mun amince."

Daga nan sai aka shiga shirin yaki, askarawa suka yi ta wasa takubba da masu, suka tamke baka aka tsoma kibau cikin dafi. Aka yi wata uku ana shiri, runduna ta hadu a bayan gari kamar farin dango. Da aka hadu Sarki ya fito aka buga kugen yagi, aka daga tutoci. Runduna ta dunguma diii, aka nufi Kabila. Karar kofatan dawaki kuwa kamar za ta tsage kasa. Bayan mahaya dawaki kuma akwai mahaya giwaye. Bayan tafiyar kwana da kwanaki, Sarki Kafidu da rundurarsa suka fara shiga yankin kasar Kabila, kasar Sarki Daigamusu.

Da shigarsu kasar sai suka fara lakwame 'yan kauyukan da ke kan hanya. Suka rika kashe tsofaffi da matasa suna kama yara da mata. Yayin da labari ya kai ga kunnen Sarki Daigamusu sai ya cika da fushi, fushi kuwa mai tsanani. Nan da nan ya tara wazirai da hakimansa ya ce musu, "Ku sani cewa Kafidu ya shigo mana kasa da shirin yaki har ya fara kona mana wasu kauyuka. An ce ya zo da rundunar mayaka da sadaukai wadda Allah kadai ya san adadinta. Yanzu menene abin yi?"

Suka amsa da cewa, "Allah ya ba ka nasara, ai babu abin da yafi sai mu tare shi da yaki a kafsa, mu nuna masa ruwa ba sa'an kwando ba ne."

Whatsapp: +2348032767547

Za mu ci gaba da karfe tara na dare (9:00PM), in sha Allah.13. HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassarar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.

Hakimai suka amsa wa Sarkin Kabul da cewa, "Allah ya ba ka nasara, ai babu abin da yafi sai mu tare shi da yaki a kafsa, mu nuna masa ruwa ba sa'an kwando ba ne."

Sarki ya ji dadin amsar da suka ba shi. Ya umurce su da shirya dakaru. Mayaka fa suka shiga shiri, kowa ya shiga cikin sulke da buke ga kuma kwalkwali bisa kansa. Wasu rike da takubba, gaya-wa-jini-na-wuce, wasu kuma rike da masu. Wasu kwari da baka, wasu da wargaji da dai sauran makamai masu hadarin gaske, wadanda kome jaruntar sadauki za su iya aikawa da shi barzahu.

Bayan rundunar askarawan Sarki Daigamusu ta shirya tsaf, sai Sarki ya fito ya shige gaba, aka buga kugen yaki. Runduna ta motsa ta tunkari rundunar Sarki Kafidu. Yayin da suka yi kusa da rundunar Sarki Kafidu, sai Sarki Daigamusu ya umurci askarawa da yin sansani a wani kwari mai suna Zaharana. Sarki Daigamusu ya rubuta takarda zuwa ga Sarki Kafidu, a cikin takardar yana cewa:

Ka sani abin da ka aikata aiki ne na barayi da 'yan ta'adda, ina mamaki wai ace kai Sarki ne dan Sarki. Da ace kai cikakken Sarki ne mai ji da kansa, da ba ka fada wa kasarmu da yaki ba, ba tare da saninmu ba. Wannan ya nuna kai matsoraci ne, wanda tarihi ba zai taba mantawa da wannan abin kunya da ka yi ba. Ka sani cewa, da na san da zuwanka, tun wuri da na zo da sadaukaina mun murje ka, kamar yadda ake murje cinnaka. Amma duk da haka, mu ba za mu shammace ka ba, mu afka maka ba cikin shiri ba. Ina sanar da kai cewa ka yi gaggawar ficewa daga kasarmu, idan ka yi haka ka rufa wa kanka asiri. Idan kuwa ba haka ba, to mu hadu da kai a filin daga domin banbancewa tsakanin aya da tsakuwa.

Sarki ya nade takarda ya ba wani sadauki domin ya kai wa Sarki Kafidu. Ya kuma tura 'yan leken asiri a sace domin su samo masa labarin irin shirin rundunar Sarki Kafidu. Dan aike ya riki takarda ya sukwani dokinsa har ya isa kusa ga sansanin abokan gaba. Ya ga an kakkafa tantuna bila'adadin masu launi iri-iri. Wasu da tsanwar launi wasu da shudi, wasu rawaya wasu farare. A tsakiyarsu ya hangi wani babban tanti, mai jan launi, wanda duk ya fi sauran girma, an kawata shi da jauhari. Ya ga askarawa sun kewaye wannan tanti. Ya tunkari wannan tanti, da ya zo kusa gare shi ya tambaya sai aka ce masa na Sarki Kafidu ne. Ya tarar da shi ya harde bisa wata karaga ta jauhari, waziransa da hakimai sun zagaye shi. Dan aike ya zaro takarda, wani jarumi da ke nan ya fyauce ta daga hannunsa ya mika wa Sarki. Kafidu ya warware takarda ya karanta sakon da ke ciki. Sai ya rubuta amsa kamar haka:

Ba sai mun gaishe ka ba a cikin wannan takarda. Muna so Sarki Daigamusu ya sani cewa mun zo ne domin daukar fansar abin da ya yi mana shekaru da dama da suka wuce. Za mu kashe tsofaffi da matasa, mu bautar da yara da mata, mu kwace mulkin da kake takama da shi. Da ma ance ramuwar gayya ta fi gayya ciwo. Ka fito gobe mu hadu da kai filin daga, wannan karon za ka gane cewa rayayyen kare ya fi mataccen zaki.

Ya ninke takarda ya ba dan sako, wanda shi kuma nan take ya kai wa Sarki Daigamusu. Ya kuma gaya masa irin yawan jama'ar Sarki Kafidu da ya gani, ya ce "Allah ya ba ka nasara, Sarki Kafidu ya zo da jama'a masu yawa, wasu a kan dawaki wasu a kasa, Allah kadai ya san iyakar su." Kamar dai yadda 'yan leken asiri suka kawo wa Sarki labari.

Yayin da Sarki Daigamusu ya karanta takarda ya ga sakon da ke cikinta, sai ya cika da fushi. Ya kira Waziri Ainazari ya umurce shi cewa, ya kwashi askarawa dubu ya kai hari ga rundurar Sarki Kafidu a cikin dare yayin da suke barci. Waziri Ainazari ya amsa, "Na ji, na amince." Nan take ya zabi sadaukai dubu, dare na rabawa suka darkaki sansanin Sarki Kafidu.

To, ashe cikin daren kuma Sarki Kafidu ya kira wani Wazirinsa mai suna Gatarafanu, ya umurce shi da ya debi sadaukai dubu biyar mahaya dawaki, su kai hari ga sansanin Sarki Daigamusu. Gatarafanu ya aikata kamar yadda Sarki ya umurce shi, suka zaburi dawakai suka nufi sansanin Sarki Daigamusu. Can zuwa dare tsaka sai rundunonin nan biyu suka hadu a hanya. Waziri Gatarafanu da jama'arsa suka afka wa Waziri Ainazari da jama'arsa, nan take yaki mai tsanani ya rincabe a tsakaninsu, sashe na tsawa ga sashe, maza suka gauraya. Wuri ya hargitse da karar saran takubba, da kuwwar sadaukai, da haniniyar dawaki. Ba a daina gwabzawa ba sai da safiya ta waye. Da mutanen Waziri Gatarafanu suka lura sai suka ga an yi musu ta'adi mai yawa, suka juya da baya a razane, ba su zame ba sai gaban Sarki Kafidu.

Yayin da Sarki Kafidu ya ga dakarunsa sun dawo babu nasara, sai ya cika da fushi mai tsanani, ya daka musu tsawa, "Allah ya wadaran ku! Me ya juyo da ku haka a razane? Ina sauran dakarun?"

Suka amsa masa, "Allah ya huci zuciyarka, ya Sarkin duniya. Muna cikin tafiya mun tinkari sansanin Sarki Daigamusu, har mun yi rabin tafiya ba mu da sanannen ciki sai muka yi taho-mu-gama da rundunar abokan gaba karkashin jagorancin Waziri Ainazari. Muka hadu da su a kwarin Zaharani, sashe ya fuskanci sashe, muka afka wa juna. Yaki mai tsanani ya rincabe a tsakaninmu, muka yi ta kafsawa tun da dare har gari ya waye. Maza suka kwanta dama daga kowane bangare, Waziri Ainazari da jama'arsa suka yi ta saran dawakanmu suna yi musu tsawa. Dawaki suka firgita suka juyo da baya. Kura ta turnike wajen har babu mai ganin na kusa gare shi, jini kuwa a wurin kamar ruwan korama mai gudana. Da muka ga ba dama, sai muka juyo da baya domin mu kawo labari, ba domin haka ba, da mun halaka dukkan mu."

Yayin da Sarki Kafidu ya ji haka, sai ya kara kumbura ya ce, "Rana ta la'ance ku! Sakarkarun wofi, ku bace mini da gani ko in fille kawunanku."

Waziri Ainazari kuwa da ya koma sai ya kwashe labarin abin da ya faru ya gaya wa Sarki Daigamusu. Sarki ya yi murna da wannan nasara da aka samu, aka buga tambura don farin ciki. Daga nan Sarki ya tara dukkanin rundunarsa, ya ga cewa sadaukai metan ne suka kwanta dama a gwabzawar da aka yi cikin dare. Dakaru suka yi maci zuwa cikin wani makeken filin yaki, Sarki ya sa suka yi sahu-sahu har sahu goma sha biyar. Kowane sahu da sadaukai dubu goma wasu bisa dawaki wasu a kasa, kuma a kowane sahu akwai jagororin yaki dari uku, kowane daya daga cikin jagororin nan na iyar mayar da linzamin doki dari, dukkansu kuma suna haye bisa giwaye. Aka tayar da tutar yaki, aka buga ganguna, aka kada kugen yaki. Runduna ta motsa, aka nufi filin daga.

A bangaren Sarki Kafidu kuwa, dakaru sun yi sahu-sahu bila adadin, a kowane sahu a kwai sadaukai dubu zambar dubu. Shi kuwa Sarki ya fito yana takama, a bangarensa na dama da sadaukai dubu goma, bangaren hagu ma haka. Aka cira tutocin yaki sama, aka nufi filin kece raini.

Sassan nan biyu suka hadu da juna, yaki mai tsanani ya barke a tsakaninsu. Kasa ta yi kamar zata tsage saboda rugugin sadaukai da kukan dawaki da na giwaye. Kunnuwa suka kurumta da bugun ganguna da karar kuge, da karar kofatan dawaki, da kuwwar mazaje. Kura ta turnike sararin samaniya, wuri ya duhunta kamar hadari ya taso. Sadaukai suka gauraya, sai karar takubba ke tashi, kyas kyas kyas. Ba a rabu ba sai da rana ta fadi, duhun dare ya fara shigowa. Kowace runduna ta ja da baya, suka koma sansaninsu.

Da Sarki Kafidu ya yi holin dakarunsa sai ya ga an kashe masa mutum dubu biyar, ya cika da fushi fushi mai tsanani. Shi kuwa Sarki Daigamusu ya yi asarar dakaru dubu uku mahaya dawaki, ransa ya baci matukar baci.

Da gari ya waye Sarki Kafidu ya fito da rundunarsa filin daga, ya tarar tuni Sarki Daigamusu ya fito yana jiransa. Rundunonin biyu suka shata daga suna kallon abokan gaba. Sarki Kafidu ya yi tsawa ga dakarunsa ya ce, "A cikinku wa zai bude mana fage da yakin fito-na-fito?"

Nan take kuwa sai ga wani sadauki, wai shi Barkaiku, ya fito a kan toron giwa yana hamhama yana tunzura. Ya zo gaban Sarki ya sauka daga kan giwa ya dauki kasa gabansa, ya nemi izinin shiga filin daga. Bayan Sarki ya ba shi izini, sai ya hau giwarsa ya shiga fage ya kalli rundunar abokan gaba yana kirari, "Ina wani mai ji da kansa ya fito mu gwabza? Wa kwanansa ya kare ya fito ga ni."

Yayin da Sarki Daigamusu ya ji haka sai ya dubi rundunarsa ya ce, "Wa zai fita ya kara da wancan sadaukin?"

Nan take wani barde ya zaburi dokinsa yana huci, ya zo gaban Sarki ya yi gaisuwa sa'annan ya nemi izinin shiga fagen fama domin tunkarar Barkaiku. Bayan ya sami izini sai ya tunkari Barkaiku. Barkaiku ya tambaye shi, "Wanene kai har da za ka yi karfin halin tunkara ta?"

Sadaukin nan ya amsa masa, "Sunana Gazanfaru dan Kamkilu."

Barkaiku ya ce, "Ai kuwa ina jin labarinka a kasarmu, yau kuwa ko kai ne gazara ba Gazanfaru ba kwananka sun kare."

Twitter: @bukarma08032767547
Whatsapp:
Instagram: Yusuf Abdullahi jibaga

Za mu ci gaba, da karfe tara na dare (9:00PM), in sha Allah.

Allah ya kai mu.14. HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Daga Littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassarar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.

Barkaiku ya ce, "Ai kuwa ina jin labarinka a kasarmu, yau kuwa ko kai ne gazara ba Gazanfaru ba kwananka sun kare."

Da Gazanfaru ya ji haka sai ya jawo mashinsa na bakin karfe ya daga shi sama ya yi kururuwa ya tasar wa Barkaiku. Shi kuwa Barkaiku sai ya zare takobinsa daga cikin kube, ya zaburi giwarsa ya nufo Gazanfaru yana huci kamar macijin da ya kawo sara

Please Login or Register in order to submit comment