Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

babbar ta ce da saura, "Ya 'yan uwana, ni fa ina jin tsoro kamar akwai mutum a cikin rumfar can make yana kallonmu."

Sai mai bi mata ta ce, "Ya 'yar uwata, kin manta ne tun bayan rasuwar Shugaba Sulaimanu babu wani mahaluki, mutum ko aljani, da ya taba shiga cikin rumfar."

Karamar kuwa ta ce, "Na rantse da Allah, yadda nake ji a jikina, idan ma har akwai wani wanda ya labe yana kallonmu, babu wadda zai fi mayar da hankali a kanta kamar ni."

Suka ci gaba da wanka suna wasa da ruwa suna dariya. Duniya ta yi musu dadi. Zuciyar Janshahu kuwa kamar ta tsaga kirjinsa ta fito saboda bugawar da take yi da karfi. Soyayya da bege suka dabaibaye shi. Yana nan labe dai a bayan bishiya, yana kallon su amma su ba sa iya ganin shi. Sai ya ga sun yi iyo sun nufi tsakiyar tabkin, suka bar tufafinsu a bakin gaba. Yana ganin haka sai ya zabura da gudu kamar an harba kibiya, ya nufi bakin tabki. Kafin 'yan matan nan su farga da shi har ya dauke tufafin karamar, wadda wutar begenta ke tafarfasa zuciyarsa. Sunanta ya kasance Shamsiya. Ya make tufafin a karkashin hammatarsa.

'Yan mata suka juyo a firgice suka dube shi. Suka kara boye jikinsu a cikin ruwa don kunya. Suka yi ninkaya suka zo bakin gabar tabki. Suka dube shi suka gan shi saurayi kyakkyawa, mai annurin fuska kamar farin wata. Suka tambaye shi, "Wanene kai? Daga ina ka zo nan? Don me ka dauke tufafin 'yar uwarmu Shamsiya?"

A'a, wai har sun manta da ni ne? Lallai aljanu suna da saurin mantuwa. Janshahu ya ja da baya ya ce musu, "Ku zo nan kusa gare ni in gaya muku labarina."

Shamsiya ta ce masa, "Me ya sa ka dauke tufafina? Don me ba ka dauki na 'yan uwana ba?"

"Haba hasken idaniyata! Ki zo nan kusa gare ni mana, in gaya miki dalilin da ya sa na zabe ki daga cikin 'yan uwanki."

Shamsiya ta langabe kai, ta dube shi ta yi masa fari da ido, sa'annan ta kwararo masa wani murmushi mai rikitar da zuciya, ta ce masa, "Ya shugabana, sanyin idaniyata, abincin zuciyata! Ba ni tufafina in suturta jikina, sa'annan in zo gare ka."

Ya amsa mata da cewa, "Haba sarauniyar kyawawa, yaya za a yi na ba ki tufafinki, ki tafi ki bar ni. Yin haka ai kamar na soka wa kaina wuka ne. Ni kam ba zan ba ki tufafinki ba har sai Sheik Nasar, shugaban tsuntsaye, ya dawo daga wurin karbar gaisuwar tsuntsaye."

Shamsiya ta ce, "To, ka kawar da kanka daga gare mu 'yan uwana su suturta jikinsu. Ni kuma ka samo mini wani abu wanda zan suturta jikina."

"Na ji, na amince." Ya tafi ya ba su wuri, ya shiga cikin rumfa ya zauna bisa karaga. 'Yan mata suka fito daga cikin ruwa suka sanya tufafinsu na gashi. Suka ba Shamsiya wani yanki na tufafinsu ta suturta jikinta, sai dai ba za ta iya tashi sama ba. Bayan sun sanya tufafinsu sai suka iske Janshahu a cikin rumfa, suka tsaya daga bakin kofa. Shamsiya ta wuce zuwa gare shi ta tsaya gaba gare shi. Ya dube ta ya gan ta tamkar wata dan daren goma sha hudu, kai ka ce ita barewa ce a cikin tsanwar ciyawa.

Bayan ta yi jim tsaye, sai ta zauna bisa abin zama. Ta gayar da shi cikin harshe mai dadi, sa'annan ta ce, "Ya kai mai kykkyawar fuska, hakika ka aikata mana abin da wani mahaluki bai taba aikatawa ba gare mu. Amma gaya mini labarinka da kuma abin da ya sa ka dauke mini tufafi."

Yayin da Janshahu ya ji wadannan kalamai nata, sai idanunsa suka karyo da hawaye har sai da gaban rigarsa ya jike da hawaye. Da Shamsiya ta ga haka sai tausayinsa ya kamata. Babu shakka wannan kykkyawan saurayi ya fada cikin kogin sonta, so kuwa mai tsanani. Ta dawo kusa gare shi ta zauna. Ta sa hannunta tana share masa hawaye, ta ce da shi, "Ya mai kykkyawar fuska, ka daina kuka ka gaya mana labarinka."

Bayan ta rarrashe shi, ta kwantar masa da hankali. Sai ya kwashe labarinsa duka, tun daga fitowarsa gida har zuwa wannan wuri, ya gaya mata. Ya kuma gaya mata dukkan abubuwan da ya gani.

Yayin da ta ji labarinsa, sai ta yi ajiyar zuciya, fuskarta cike da tausayinsa. Ta ce masa, "Ya shugabana, tun da dai har ka nuna kana matukar kaunata, to, ka ba ni tufafina in tafi tare da 'yan uwana zuwa kasarmu, in sanar da uwayena halin da ake ciki. Daga nan sai in dawo in kai ka kasarku."

Da Janshahu ya ji haka, sai wasu sababbin hawaye suka kwararo daga idanunsa. Ya dube ta ya ce, "Ya abar kaunata, yanzu saboda Allah na cancanci ki sare ni da takobi da hannunki?"

Ta tambaye shi cikin mamaki, "Assha! Ni kuwa me zai sa na sare ka da takobi? Laifin me ka yi mini?"

Sai ya amsa mata, "Ai idan na ba ki tufafinki, za ki tafi ki bar ni. Ni kuwa na tabbata kina bari na kaunarki za ta kashe ni. Kin ga kamar kin sa takobi kin sare ni ne."

Za mu ci gaba da karfe tara na dare (9:00PM), in sha Allah.

Allah ya kai mu.9. HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassarar

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.

Janshahu ya shiga cikin lambu, ya boye a bayan wata babbar bishiyar inabi, inda babu mai iya ganinsa, yana kallon tabkin nan. Yana nan labe yana jiran zuwan 'yan mata tun da safe har dare ya yi ba su zo ba, ya kwana a wurin. Washe gari ya ci gaba da jira, yana kallon sararin samaniya ko ya hango su tafe, amma babu su babu dalilinsu har duhun dare ya mamaye lambun. Hankalinsa ya tashi, hawaye suka yi ta kwarara daga idanunsa. Da ya tuna da yarinyar nan da irin kyawonta, sai shaukin bege ya buge shi, ya fadi kasa sumamme.

Bai farfado ba sai da gari ya waye. Wannan ita ce rana ta uku. Ya yi zugum yana tunani, yanzu idan ba su zo ba wane irin hali zai shiga? Ya tashi ya duba sama ko zai hango su, ya duba tabki ko zai gan su suna wanka, zuciyarsa cike da tsananin bege. Can bayan rana ta yi zawwali sai ya hango tsuntsaye guda uku, cikin sararin samaniya, sun nufo wannan lambu. Suka sauka a bakin tabkin nan, Janshahu ya gan su kamar yadda ya gan su da farko, cikin surar fararen tattabaru amma girman kowace daya kamar na mikiya.

Bayan sun sauka bakin tabki, suka duba dama suka duba hagu, ba su ga kowa ba na daga mutum ko aljani. Daga nan sai suka tube tufafinsu na gashi suka ajiye gefe guda. Suna tube tufafin nan sai suka rikide zuwa kyawawan 'yan mata, kai ka ce su watanni ne don kyawunsu. Suka fada cikin tabki suna wanka suna wasa da juna cikin dariya da farin ciki. Dariyar da Janshahu ke jin kamar ana busa sarewa don dadin muryoyinsu.

Suka ci gaba da wanka, Janshahu na make bayan bishiya yana kallonsu. Jikinsu sai sheki yake yi kamar danyar azurfa. Can sai ya ji babbar ta ce da saura, "Ya 'yan uwana, ni fa ina jin tsoro kamar akwai mutum a cikin rumfar can make yana kallonmu."

Sai mai bi mata ta ce, "Ya 'yar uwata, kin manta ne tun bayan rasuwar Shugaba Sulaimanu babu wani mahaluki, mutum ko aljani, da ya taba shiga cikin rumfar."

Karamar kuwa ta ce, "Na rantse da Allah, yadda nake ji a jikina, idan ma har akwai wani wanda ya labe yana kallonmu, babu wadda zai fi mayar da hankali a kanta kamar ni."

Suka ci gaba da wanka suna wasa da ruwa suna dariya. Duniya ta yi musu dadi. Zuciyar Janshahu kuwa kamar ta tsaga kirjinsa ta fito saboda bugawar da take yi da karfi. Soyayya da bege suka dabaibaye shi. Yana nan labe dai a bayan bishiya, yana kallon su amma su ba sa iya ganin shi. Sai ya ga sun yi iyo sun nufi tsakiyar tabkin, suka bar tufafinsu a bakin gaba. Yana ganin haka sai ya zabura da gudu kamar an harba kibiya, ya nufi bakin tabki. Kafin 'yan matan nan su farga da shi har ya dauke tufafin karamar, wadda wutar begenta ke tafarfasa zuciyarsa. Sunanta ya kasance Shamsiya. Ya make tufafin a karkashin hammatarsa.

'Yan mata suka juyo a firgice suka dube shi. Suka kara boye jikinsu a cikin ruwa don kunya. Suka yi ninkaya suka zo bakin gabar tabki. Suka dube shi suka gan shi saurayi kyakkyawa, mai annurin fuska kamar farin wata. Suka tambaye shi, "Wanene kai? Daga ina ka zo nan? Don me ka dauke tufafin 'yar uwarmu Shamsiya?"

A'a, wai har sun manta da ni ne? Lallai aljanu suna da saurin mantuwa. Janshahu ya ja da baya ya ce musu, "Ku zo nan kusa gare ni in gaya muku labarina."

Shamsiya ta ce masa, "Me ya sa ka dauke tufafina? Don me ba ka dauki na 'yan uwana ba?"

"Haba hasken idaniyata! Ki zo nan kusa gare ni mana, in gaya miki dalilin da ya sa na zabe ki daga cikin 'yan uwanki."

Shamsiya ta langabe kai, ta dube shi ta yi masa fari da ido, sa'annan ta kwararo masa wani murmushi mai rikitar da zuciya, ta ce masa, "Ya shugabana, sanyin idaniyata, abincin zuciyata! Ba ni tufafina in suturta jikina, sa'annan in zo gare ka."

Ya amsa mata da cewa, "Haba sarauniyar kyawawa, yaya za a yi na ba ki tufafinki, ki tafi ki bar ni. Yin haka ai kamar na soka wa kaina wuka ne. Ni kam ba zan ba ki tufafinki ba har sai Sheik Nasar, shugaban tsuntsaye, ya dawo daga wurin karbar gaisuwar tsuntsaye."

Shamsiya ta ce, "To, ka kawar da kanka daga gare mu 'yan uwana su suturta jikinsu. Ni kuma ka samo mini wani abu wanda zan suturta jikina."

"Na ji, na amince." Ya tafi ya ba su wuri, ya shiga cikin rumfa ya zauna bisa karaga. 'Yan mata suka fito daga cikin ruwa suka sanya tufafinsu na gashi. Suka ba Shamsiya wani yanki na tufafinsu ta suturta jikinta, sai dai ba za ta iya tashi sama ba. Bayan sun sanya tufafinsu sai suka iske Janshahu a cikin rumfa, suka tsaya daga bakin kofa. Shamsiya ta wuce zuwa gare shi ta tsaya gaba gare shi. Ya dube ta ya gan ta tamkar wata dan daren goma sha hudu, kai ka ce ita barewa ce a cikin tsanwar ciyawa.

Bayan ta yi jim tsaye, sai ta zauna bisa abin zama. Ta gayar da shi cikin harshe mai dadi, sa'annan ta ce, "Ya kai mai kykkyawar fuska, hakika ka aikata mana abin da wani mahaluki bai taba aikatawa ba gare mu. Amma gaya mini labarinka da kuma abin da ya sa ka dauke mini tufafi."

Yayin da Janshahu ya ji wadannan kalamai nata, sai idanunsa suka karyo da hawaye har sai da gaban rigarsa ya jike da hawaye. Da Shamsiya ta ga haka sai tausayinsa ya kamata. Babu shakka wannan kykkyawan saurayi ya fada cikin kogin sonta, so kuwa mai tsanani. Ta dawo kusa gare shi ta zauna. Ta sa hannunta tana share masa hawaye, ta ce da shi, "Ya mai kykkyawar fuska, ka daina kuka ka gaya mana labarinka."

Bayan ta rarrashe shi, ta kwantar masa da hankali. Sai ya kwashe labarinsa duka, tun daga fitowarsa gida har zuwa wannan wuri, ya gaya mata. Ya kuma gaya mata dukkan abubuwan da ya gani.

Yayin da ta ji labarinsa, sai ta yi ajiyar zuciya, fuskarta cike da tausayinsa. Ta ce masa, "Ya shugabana, tun da dai har ka nuna kana matukar kaunata, to, ka ba ni tufafina in tafi tare da 'yan uwana zuwa kasarmu, in sanar da uwayena halin da ake ciki. Daga nan sai in dawo in kai ka kasarku."

Da Janshahu ya ji haka, sai wasu sababbin hawaye suka kwararo daga idanunsa. Ya dube ta ya ce, "Ya abar kaunata, yanzu saboda Allah na cancanci ki sare ni da takobi da hannunki?"

Ta tambaye shi cikin mamaki, "Assha! Ni kuwa me zai sa na sare ka da takobi? Laifin me ka yi mini?"

Sai ya amsa mata, "Ai idan na ba ki tufafinki, za ki tafi ki bar ni. Ni kuwa na tabbata kina bari na kaunarki za ta kashe ni. Kin ga kamar kin sa takobi kin sare ni ne."

Whatsapp: +2348032767547

Za mu ci gaba , da karfe tara na dare (9:00PM), in sha Allah.

Allah ya kai mu.
10. HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Daga Littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassarar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.

Da Janshahu ya ji haka, sai wasu sababbin hawaye suka kwararo daga idanunsa. Ya dube ta ya ce, "Ya abar kaunata, yanzu saboda Allah na cancanci ki sare ni da takobi da hannunki?"

Ta tambaye shi cikin mamaki, "Assha! Ni kuwa me zai sa na sare ka da takobi? Laifin me ka yi mini?"

Sai ya amsa mata, "Ai idan na ba ki tufafinki, za ki tafi ki bar ni. Ni kuwa na tabbata kina bari na kaunarki za ta kashe ni. Kin ga kamar kin sa takobi kin sare ni ne."

Gimbiya Shamsiya ta yi dariya tare da 'yan uwanta; ta ce masa, "Kwantar da hankalinka, sanya ranka cikin ruwan sanyi. Na yi alkawari zan aure ka." Tana fadar haka sai ta jawo shi ta rungume ga kirjinta. Ta sumbaci goshi da kumatunsa. Suka rungume juna tsawon wani lokaci, sa'annan suka saki juna suka koma wurin zamansu.

Babbar daga cikin 'yan matan ta shiga cikin lambu ta tsinko 'ya'yan itatuwa masu zaki, da furanni masu kamshi, ta kawo cikin rumfa. Suka zauna suna cin 'ya'yan itatuwa suna wasanni tare da dariya. Janshahu saurayi ne mai kwarjini da haiba, ga shi kuma kyakkyawa. Jikinsa madaidaici ne kamar iccen turare, shi ba mai kiba ba, kuma ba ramamme ba. Fuskarsa kuma kamar wata don haske, bakinsa madaidaici da hanci dogo siriri kamar alkalami. Idanunsa dara-dara, har sun fi nono fari.

To, suna cin 'ya'yan itace gimbiya Shamsiya na satar kallonsa. Duk lokacin da ta kalle shi sai ta ji sonsa ya karu cikin zuciyarta. Har dai ta kasa hakuri ta ce masa, "Ya shugabana, Wallah zuciyata ta kamu da sonka matuka. Ni yanzu ba zan iya tafiya na bar ka ba."

Lokacin da ya ji haka sai kirjinsa ya yalwata don farin ciki. Ya yi murmushi har sai da hakoransa suka bayyana. Suka ci gaba da cin 'ya'yan itatuwa suna zance da juna. Suna cikin haka sai ga Sheik Nasar ya shigo wurinsu. Har ya gama karbar gaisuwar tsuntsaye. Suka tashi gaba daya suka gayar da shi da lafazi mai dadi. Ya amsa musu gaisuwarsu, ya yi musu maraba da zuwa, sa'annan ya ce su zauna.

Bayan sun zauna sai ya dubi Shamsiya ya ce mata, "Hakika wannan saurayi ya kamu da sonki matuka. Ki yi wa Allah ki saurare shi. Ki sani cewa yana daga cikin mutane masu daraja, domin kuwa dan sarki ne jikan sarki. Ubansa shi ke mulki da kasar Kabila. Ita kuwa kasa ce babba wadda ta tattara manya-manyan dauloli a karkashinta."

Gimbiya Shamsiya ta sunkuyar da kanta kasa ta ce, "Na ji, na amince da bukatarsa, ya baffana." Ta kama hannun Sheik Nasar ta sumbata, sa'annan ta mike tsaye gaba gare shi cikin girmamawa.

Sheik Nasar ya ce, "Idan har abin da kika fada haka yake har cikin zuciyarki, to, ina so ki rantse nan a gabana cewa ba za ki yaudare shi ba tsawon rayuwarki."

Gimbiya Shamsiya ta rantse, rantsuwa mai girma, cewa ba za ta taba yaudarar Janshahu ba tsawon rayuwarta. Kuma ta yarda za ta aure shi. Ta kara da cewa, "Ka sani, ya kai baffana, ba zan taba rabuwa da shi ba har abada."

Sheik Nasar ya amince da rantsuwarta, ya dubi Janshahu ya ce, "Godiya ta tabbata ga Allah, wanda ya daidaita tsakaninku." Shi kuwa Janshahu baki har kunne. Farin ciki wurinsa ba sai an fada ba. Ya zauna tare da Shamsiya da 'yan uwanta, da Sheik Nasar a cikin wanna lambu tsawon watanni uku. Su ci, su sha, su yi wasanni. Bayan wannan lokaci sai yarinya ta ce da Janshahu, "Ina so in tafi tare da kai zuwa kasarku, daga can sai a daura mana aure."

Janshahu ya ce ya yarda. Ya nemi shawarar Sheik Nasar, shi kuma ya ce masa, "Ku tafi tare, na damka maka amanarta, ita ma na damka mata amanarka."

Yarinya ta ce da Sheik Nasar, "Ya baffana, ka umurce shi da ya ba ni tufafina na gashi." Nan take ya umurci Janshahu da ya dauko mata tufafinta. Ya tafi cikin rumfar nan ya kwakwalo su daga inda ya boye, ya kawo ya ba ta. Ta karba ta sanya, ta ce masa, "Hau bisa bayana. Amma ka rufe idanunka, kuma ka sami ganye ka toshe kunnuwanka don kada hayaniyar juyawar duniya ta dimautar da kai. Sa'annan ka kama gashina ka rike gam-gam don kada ka fado."

Janshahu ya yi kamar yadda ta umurce shi. Ta mike fikafikanta kenan za ta ta shi, sai Sheik Nasar ya dakatar da ita. Ya ce, "Bari in kwatanta miki yadda birnin Kabila yake don kada ki bace hanya."

Ta dakata har ya gama gaya mata yadda birnin Kabila yake, da yanayin birnin da tsarin gine-ginensa. Bayan ya gama bayyana mata yanayin birnin sai ta yi sallama da shi, ta juya wurin 'yan uwanta ta yi ban kwana da su ta ce idan sun koma gida su gaya wa mahaifansu abin da ya faru gare ta don hankalinsu ya kwanta. Ta kada fikafikanta ta tashi sama da sauri cikin iska, kamar an harba kibiya. 'Yan uwanta suka tashi suka nufi kasarsu.

Yarinya ta ci gaba da tafiya cikin iska, tun da hantsi har rana ta take, Janshahu na makale bisa bayanta. Daga nan sai ta hango wani wadi wanda ya burge ta ainun. Ta gan shi cike da itatuwa da koramu ko'ina suna gudana. Sai ta ce da Janshahu, "Ya kamata mu sauka a wannan wadi, mu debe kewa daga itatuwa da koramunsa. Mu huta, zuwa wayewar gari sai mu ci gaba da tafiya."

Janshahu ya ce mata, "Aikata abin da ranki yake so."

Sai ta yi kasa-kasa har ta sauka cikin wadi. Janshahu ya sauka daga bayanta, ya sumbaci goshinta. Suka zauna a bakin gabar korama suna kallon yadda ruwa ke gudu. Bayan sun huta a bakin korama, sai suka tashi suna zagaya wadin. Suna tsinkar 'ya'yan itatuwa suna ci, suna raha da juna, har dare ya yi. Suka sami karkashin wata itaciya suka kwana.

Da gari ya waye suka farka daga barci, Shamsiya ta umurci Janshahu ya hau bisa bayanta. Ta tashi sama da shi. Suka yi ta tafiya cikin iska har rana ta gota daga tsakiya. Daga nan sai ta fara hangen irin gine-ginen da Sheik Nasar ya kwatanta mata. Ba shakka wadannan gine-gine na binin Kabila ne, ta ce a cikin ranta. Sai ta sami wani fili, mai yalwar itatuwa da ciyawa, a bayan birnin ta sauka. Janshahu ya sauka daga bayanta, ya sumbaci goshinta. Ta tambaye shi, "Ya masoyina, sanyin idanuna, shin ka san ko tafiyar kwana nawa muka yi a cikin wadannan yini biyu?"

Ya amsa mata, "A'a."

Ta ce, "Tafiyar watanni talatin muka yi."

"Godiya ta tabbata ga Allah da ya saukar da mu lafiya." Janshahu ya ce.

Suka sami wuri suka zauna, bayan sun tsinko 'ya'yan itatauwa. Suka rika cin 'ya'yan itatuwa suna hira irin ta masoya, fuskokinsu cike da fara'a. Suna cikin wannan hali sai ga wasu bayin Sarki su biyu sun zo inda suke. A cikin bayin nan kuwa har da wanda Janshahu ya bari tsaron dawaki a bakin teku lokacin da za su shiga jirgi don bin barewa. Shi ma dayan yana cikin wadanda aka tafi farautar tare da shi.

Suna ganin Janshahu sai suka shaida shi. Nan take sai suka zube kasa suka yi gaisuwa. Suka ce, "Allah ya ba ka nasara, ka yi mana izini mu tafi ga Sarki mu kai masa wannan babban albishir na dawowarka."

"Ku tafi ga mahaifina ku yi masa albishir da dawowata. Sa'annan ku yi maza maza ku kawo mana tantuna, za mu zauna a wannan wuri tsawon kwanaki bakwai kafin a gama shirye-shiryen bukin tariya ta."

Whatsapp: +2348032767547

Za mu ci gaba da karfe tara na dare (9:00PM) in sha Allah.

Ina amfani da wannan dama domin mika ta'aziya ga abokiyar gwagwarmaya a harkar rubutu, Hajiya Rahama Abdulmajid, wadda ta rasa mijinta, Manjo Auwal Sa'ad, a daren jiya, yayin da suke fafutukar kawar da 'yan kungiyar Boko Haram. Shi ma marigayin ba a bar shi a baya ba a bangaren rubutu, duk da yake babban soja ne, ya rubuta wani littafi mai suna Linzami Da Wuta. Haka ma sun rubuta wani littafin, shi da mai dakinsa Rahama, mai suna Hanji Waje.
Muna rokon Allah ya ji kan sa da rahama, shi da dukkan Musulmi da suka riga mu gidan gaskiya. Allah ya sa aljannah ce makomarsu, amin. Idan tamu ta zo, Allah ya sa mu cika da imani. Allah ya kawo mana karshen kungiyar Boko Haram a Nijeriya da Afirka gaba daya.

Mu hadu ranar lahadi

11. HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.

Janshahu ya ce da bayi, "Ku tafi ga mahaifina ku sanar da shi zuwana. Ku yi maza-maza ku dawo mana da tantuna, za mu zauna a wannan wuri tsawon kwanaki bakwai kafin a gama shirye-shiryen bukin tariya ta."

Bayi suka zabura da gaggawa suka tafi ga Sarki Daigamusa, suka ce masa, "Mun zo maka da babban albishir, Allah ya ba ka nasara."

"Wane babban albishir ne wannan? Ai, yanzu babu wani babban albishir da ya wuce na dawowar dana."

Bayi suka ce, "Allah ya ba ka nasara, sai ka ce wanda aljanu ke kawo wa labari? Ai danka Janshahu din ne ya dawo. Yana nan a filin nan mai yawan itatutwa da ke bayan gari."

Yayin da Sarki ya ji haka sai ya cika da farin ciki. Saboda farin ciki sai da ya fado daga kan garaka a some. Aka shafa masa ruwa ga fuska ya farfado. Bayan ya farfado sai ya umurci Waziri da ya ba bayin nan da suka kawo wannan albishir riguna na alfarma tare da kudi masu yawa. Waziri ya ce, "Na ji, na karba." Ya tafi ga ma'aji, ya karbo abubuwan da Sarki ya ce a ba su ya kawo musu. Ya ce da su, "Ku karbi wannan kaya, shi ne goron albishirin da kuka kawo wa Sarki. Idan karya kuke yi kuwa, wannan tskaninku ne da Sarki."

Suka ce, "Allah ya taimake ka, ina mu ina yi wa Sarki karya! Ya ma ce mu koma masa da tantuna, zai zauna a can tsawon kwana bakwai kafin Sarki ya gama shirye-shiryen tariyar sa."

Sarki ya tambaye su, "A cikin wane hali kuka ga dana?"

Suka amsa masa, "Mun gan shi cikin farin ciki da annashuwa. Yana tare da daya daga cikin 'yan matan Hurul Aini, wadanda muke jin labarin su a cikin Aljanna."

Sarki Daigamusa ya ba da umurni a buga tambura don murna. Ya tada bayi su je su gaya wa mahaifiyar Janshahu da matan manyan hakimansa wannan labari mai dadi. Ya kuma umurci mai shela ya shiga gari ya sanar da jama'a. Sankira ya shiga ko'ina a cikin birnin Kabila ya sanar da jama'a dawowar dan sarki.

Sarki ya hau tare da fadawansa, wasu bisa dawaki wasu a kasa, suka dunguma bayan gari inda Janshahu ya sauka tare da yarinya Shamsiya. Suna zaune suna hira da juna, suna dariya, sai Janshahu ya hangi kungiyar mutane ta nufo su. Sai ya tashi ya yi gaba domin taron su. Yana isa inda suke sai ya ga ashe mahaifinsa ne tare da fadawansa. Fadawa na ganinsa sai suka shaida shi. Suka sauka suka yi gaisuwa gare shi, sa'annan suka yi masa jagora zuwa ga mahaifinsa.

Yayin da Sarki Daigamusa ya ga dansa, sai ya sauko daga kan dokinsa, ya rungeme shi ga kirjinsa. Hawaye suka yi ta zuba daga idanunsa don farin ciki. Fadawa suka hau dawaki suka yi zarya da su, hagu da dama, don girmamawa ga dan sarki. Sa'annan aka tafi bakin korama aka kafa tantuna. Masu ganguna suka goce da kida, masu busa na yi, masu waka na yi. Sarki ya sa aka kafa wa Gimbiya Shamsiya wani tanti na jan alharini. Aka kawo mata tufafi na alfarma, ta cire tufafinta na gashi. Ta shiga

Please Login or Register in order to submit comment