Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bai samu ba. Suka afka wa juna da sara da suka, can sai Barkaiku ya sami sa'a ya kwantara wa Gazanfaru takobi a tsakiyar kai. Amma da yake Gazanfaru na sanye da kwalkwali wannan sara bai yi masa wata illa ba, sai dai takobin ya tashi sama kamar an sari dutse. Wannan sara ya harzuka Gazanfaru, ya jinjina mashinsa ya jefi Barkaiku da shi iya karfinsa, mashi kuwa ya shiga ta cikin goshinsa ya fita ta keyarsa. Nan take ya fado daga kan giwa bai ko shura ba.

Ganin haka sai wani sadauki ya fito a sukwane, bakinsa na kumfa, ya daka wa Gazanfaru tsawa, "Kaiconka! Me ya sa ka kashe mini dan uwa? Za ka yi da-na-sanin aikata haka." Kafin Gazanfaru ya farga har sadaukin nan ya jeho shi da mashi, mashi kuwa ya cake masa ga cinya. Gazanfaru ya yi kara don zafi, ya zare takobinsa ya dauke kan dan uwan Barkaiku. Kan ya fadi can gefe, hakora na cizon kasa, gangar jiki ta fadi gefe daban, jini ya cika wurin kamar an yanka sa.

Yayin da Sarki Kafidu ya ga ya rasa sadaukai biyu, sai ya yi tsawa ga rundunarsa, "Ku afka musu gaba daya, kada ku bar daya ya tsira daga cikinsu." Shi ma Sarki Daigamusu ya yi wa mutanensa tsawa. Nan take bangarorin biyu suka hadu da juna tare da wata irin tsawa mai karfin gaske tamkar tsawar da ke fita yayin da girgije ya hadu da girgije idan ana ruwa. Wuri ya hargitse, dawaki na haniniya, giwaye na ruri, mazaje na kuwwa ga sashe, karar ganguna na tashi, kasa kuwa kamar za ta tsage don girgiza. Karar saran takubba da sukar masu ta cika wuri, mazaje suka rika zuba kamar 'ya'yan kanya, jini ya gudana kamar korama. Aka ci gaba da gwabza yaki yaki mai tsanani, tun da safe har rana ta koma ga Ubangiji. Daga nan sai rundunonin biyu suka ja da baya, kowa ya koma sansaninsa.

Sarki Daigamusu ya duba rundunarsa ya ga an kashe masa mutum dubu biyar an kuma tarwatsa sahu hudu na mayakansa, ransa ya baci. Shi kuwa Sarki Kafidu sai ya ga an kashe masa manyan sadaukai dari shida, an kuma tarwatsa masa sahu tara na mayaka. Rundunonin biyu suka ajiye makamai domin su huta tsawon kwana uku. Sarki Kafidu ya dauki takarda ya rubuta wasika zuwa ga wani Sarki da ake kira Fakuna Alkalbu yana neman taimakonsa. Shi wannan Sarki babban aminin Sarki Kafidu ne, kuma ya tara rundunar mayaka mai yawa. Da sakon Sarki Kafidu ya iske shi, sai nan da nan ya hada rundunarsa ya same shi a fagen daga.

Sarki Daigamusu na zaune sai ga wani mutum ya shiga wurinsa jiki na rawa, ya fadi ya yi gaisuwa ya ce, "Allah ya ba ka nasara, mun hangi wata kura daga nesa ta tokare sararin samaniya ta nufi sansanin Sarkin Hindu."

Sarki ya tayar da 'yan leken asiri su binciko masa ko kurar mecece. Suka ce, "Mun ji, mun karba." Nan da nan suka hau dawaki. Cikin dan lokaci kankani sai ga su sun dawo da labari, suka ce wa Sarki, "Allah ya ba ka nasara, "Da muka yi kusa da hanyar da rundunar nan za ta wuce sai muka sauka muka make a bakin hanya. Mun kidaya sahu bakwai na mayaka, a cikin kowane sahu akwai dakaru dubu uku, dukkansu mahaya dawaki ne, sun nufi sansanin Sarki Kafidu."

Lokacin da Sarki Fakuna Alkalbu ya isa ga Sarki Kafidu, bayan sun gaisa sai ya tambaye shi, "Menene sababin wannan yaki da kuke ciki?"

Sarki Kafidu ya amsa masa, "Ashe ba ka san cewa ba ni da wani babban makiyi ba kamar Sarki Daigamusu? Shi ne fa wanda ya kashe mini mahaifi da 'yan uwa. Na fito yanzu domin daukar fansar abin da ya yi mana."

Sarki Fakuna ya ce, "Rana kuwa na tare da kai. Babu shakka kai ke da nasara." Sarkin Hindu ya ja Sarki Fakuna Alkalbu zuwa tantinsa suka ci suka sha suka yi farin ciki. Wannan shi ne al'amarinsu.

Al'amarin Janshahu kuwa ya kasance cikin dakinsa, cikin damuwa da bacin rai don rashin masoyiya, tsawon wata biyu ba tare da ya bar kowace kuyanga ta shiga inda yake ba. Tsawon wannan lokaci kuma sai ya ga mahaifinsa ya dauke kafarsa kwata-kwata daga zuwa inda yake. Ya tambayi bayin da ke yi masa hidima, "Lafiya kuwa mahaifina ya daina zuwa wurina?" Suka ce masa ai Sarki na can na yaki da Sarki Kafidu.

Yayin da Janshahu ya ji haka sai ce, "Ku kawo mini doki, ina so in ga mahaifina."

Suka amsa masa, "Mun ji, mun karba." Suka tafi nan da nan suka yi masa sirdi. Ya sa aka shirya masa dawaki dubu tare da mahayansu. Suka nufi sansanin yaki, mutanen gari na cewa ai zai tafi ne domin taimakon mahaifinsa yaki. Ba su san cewa Janshahu bad-da-bami ne ya yi musu ba. Shi babu abin da ke ransa sai tunanin yarinya Shamsiya da yadda zai yi ya sake ganin ta. Ya ce a cikin ransa, babu makawa in koma Birnin Yahudawa, watakila Allah ya nufa in sake haduwa da tajirin nan da ya tura ni bisa tsauni, ya sake aikata kamar yadda ya aikata mini. Wa ya sani ko ta wannan hanyar zan sake haduwa da abar begena.

Janshahu ya tafi tare da mahaya dubu tun safe har duhu ya soma yi. Da dare ya yi sai suka sauka domin yin barci kafin gari ya waye su ci gaba. Can da dare ya yi tsakiya, Janshahu ya lura da duk mutanen nan sun yi barci, sai ya tashi ya daura damararsa ya hau doki ya sulale ya yi gaba da nufin zuwa Bagadada, ya bar mutanensa nan suna ta aikin raggo. Da ma ya taba ji lokacin yana a garin Yahudawa cewa ayarin Bagadada na zuwa birninsu duk bayan shekara biyu. Ya nufi Bagadada da nufin bin wannan ayari mai zuwa birnin Yahudawa.

Da gari ya waye mutane suka farka ba su ga Janshahu ba, ba su ga dokinsa ba. Nan da nan sai wasu daga cikinsu suka hau dawaki, suka warwatsu kudu da arewa, gabas da yamma, amma ba su gan shi ba. Sai suka dunguma suka nufi wurin mahaifinsa, suka shaida masa abin da ya faru. Nan take hasken da ke fuskar Sarki Daigamusu ya juye zuwa duhu. Idanunsa suka juye jajir kamar garwashin wuta. Ya cire kambin sarautar da ke bisa kansa ya jefar ya buga salati, "Babu tsimi babu dabara face daga Allah Madaukakin Sarki. Shi ke nan na rasa dana, ga abokan gaba sun zagaye mu!" Wazirai da hakimansa suka yi ta tausarsa suna ba shi hakuri.

Janshahu kuwa ya ci gaba da tafiya, babu tsayawa dare da rana, yana zubar da hawaye saboda rashin masoyiyarsa da kuma bakin cikin sake rabuwa da mahaifinsa, yayi ta keta dazuzzuka da rairayin hamada. Amma Sarki Daigamusu tun daga ranar da aka zo masa da labarin tafiyar dansa, sai ya yi umurni ga jagororin yakinsa cewa a koma gida haka nan. Suka juya da baya, suka koma cikin birnin Kabila aka rufe dukkan kofofin shiga da fita birnin. Sarki Kafidu kuwa ya bi shi har kusa ga birninsa, aka kafsa yaki na kwana bakwai. Daga nan sai mutanen Sarki Daigamusu suka shige cikin birni aka rufe kofofi. Shi kuwa Sarki Kafidu sai ya kafa sansaninsa a nan bayan birni, aka kafa tantuna. Haka dai wadannan Sarakuna biyu suka kasance cikin yaki da juna tsawon shekara bakwai.

Janshahu kuwa ya ci gaba da tafiya bisa dokinsa. Ya yi ta keta dazuzzuka da koramu da kwazazzabai da rairayin hamada. Idan ya tarar da gari sai ya tambayi hanyar zuwa Takanni Fadar Jauhari, amma bai sami wanda ya taba ko jin sunan wurin ba. Daga karshe sai ya yanke shawarar tambayar hanyar zuwa Birnin Yahudawa. Ya kuwa yi sa'a, ya sami wani falke wanda ya ce masa, "Akwai ayarinmu da zai tashi a cikin wannan watan daga wani gari na cikin kasar Hindu mai suna Mizirikan." Ya ci gaba da cewa, "Birnin Yahudawa na can nesa kusa da karshen duniya gab da Dutsen Kaf. Idan za ka bi ayarinmu za mu bi ta Hurassana mu shige ta Birnin Shima'una da Birnin Kwarazmu. Daga Birnin Kwarazmu tafiyar shekara daya da wata uku ce zuwa Birnin Yahudawa."

Janshahu ya ce ya gode amma shi ba zai jira lokacin da ayari zai tashi ba domin yana ujila ne. Ya zauna wurin wannan falke kwana uku ya huta, daga nan ya yi ban kwana da shi ya dare dokinsa ya nufi Birnin Mizirikan.

Za mu ci gaba da karfe tara na dare (9:00PM), in sha Allah.

Allah ya kai mu.15. HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Daga Littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassarar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.

Janshahu ya ce ya gode amma shi ba zai jira lokacin da ayari zai tashi ba domin yana ujila ne. Ya zauna wurin wannan falke kwana uku ya huta, daga nan ya yi ban kwana da shi ya dare dokinsa ya nufi Birnin Mizirikan. Da shigarsa birnin sai ya shiga tambayar labarin Takanni Fadar Jauhari. Da dai ya ga bai sami wani abin kamawa ba sai ya yi gaba zuwa Birnin Hurassana. Da isarsa birnin sai ya sauka gidan wani mutum ya huta kwana biyu, dokinsa ma ya huta. Bayan ya huta sai ya tambayi hanyar Shima'una, aka aza shi ga hanya. Ya yi ta tafiya ba dare ba rana har dan guzurinsa ya kare. Yunwa da kishirwa suka kusa hallaka shi tare da dokinsa, can sai ya fara hangen Birnin Shima'una. Ya shiga cikin birni ya sami abinci ya ci, ya ciyar da dokinsa. Da karfinsu ya komo sai ya tambayi hanyar Birnin Yahudawa. Aka aza shi ga hanya.

Ya haye dokinsa ya ci gaba da tafiya kwana da kwanaki, Allah da ikonsa ya nufe shi da zuwa wurin nan da ya taba tsira daga birai. Ya kara kaimi har ya iso ga koramar nan wadda a tsallakenta ne Birnin Yahudawa yake. Ya zauna bakin koramar ya jira zuwa ranar Asabar, yayin nan koramar ta kafe da kudurar Ubangiji Madaukakin Sarki. Ya tsallake koramar ya shiga cikin birnin Yahudawa. Ya tasar wa gidan Bayahuden nan da ya sauka gare shi a zuwansa na farko. Bayahude ya marabce shi, ya yi murna da sake ganin shi. Aka kawo masa abinci da nama da abin sha. Bayan ya ci ya sha ya yi hani'an, sai Bayahude ya tambaye shi, "Ina ka shiga bayan rabuwar mu da kai?"

Ya amsa masa, "Ina cikin kasar Ubangiji mai girma da daukaka."

Janshahu ya kwana tare da Bayahude. Da gari ya waye sai ya shiga cikin birni yana zagayawa, sai ya ji mai shela yana shela da murya madaukakiya, "Ya ku jama'ar gari. Wa zai karbi dinari dubu da kyakkyawar kuyanga ya yi mana aikin yini guda?"

Nan take Janshahu ya je ga mai shela ya ce, "Ni zan yi wannan aiki."

Mai shela ya ce, "Biyo ni." Ya ja shi zuwa gidan tajirin Bayahuden nan da ya taba zuwa a baya. Ya rusuna ya ce, "Ya shugabana, wannan saurayi ya ce zai yi aikin da ka nema."

Tajiri ya tashi ya kama hannun Janshahu, ba tare da ya shaida shi ba, ya kai shi a cikin wani kayataccen daki. Ya kawo masa nama da abin sha. Janshahu ya zauna, ya ci ya sha ya koshi. Tajiri ya kawo jaka mai dinari dubu ya ba shi, ya kuma kira kuyanga ta kwana tare da shi. Da gari ya waye Janshahu ya dauki kudi tare da kuyanga ya kai wa Bayahude mai masaukinsa, ya ce ya ajiye masa sai ya dawo. Ya koma wurin tajirin Bayahude aka daura musu siridda ga alfadarai biyu, suka hau suka nufi bayan gari. Can bayan rana ta sunkuya suka isa ga dogon dutsen nan.

Suka tsaya a gindin dutsen, tajiri ya zaro wuka da igiya ya ba Janshahu ya ce, "Daure alfadarka ka yanka ta." Janshahu ya nade hannuwan rigarsa ya kayar da alfadara ya daure kafafunta sa'annan ya yanka ta. Ya cire kai da kafafunta, ya fede fatar. Ya fafe cikinta, kamar dai yadda tajiri ya umurce shi. Bayan ya fafe cikin sai tajiri ya ce masa, "Shiga cikin wannan alfadara in dinke ka. Abin da duk ka gani a ciki ka sanar da ni, wannan shi ne aikin da na biya ka jingarsa."

Janshahu ya shige cikin alfadara ya yi kudundune. Tajiri ya kawao zare da basilla ya dinke cikin. Ya sami wuri nesa da inda alfadarar take ya make, yana kallon abin da zai faru. Can bayan sa'a guda sai ga wani katon tsuntsu ya sauko daga saman dutsen nan, ya fyauce alfadar ya tashi sama ya koma kololuwar dutsen da ita. Tsuntsu na shirin fara cin alfadara ke nan sai Janshahu ya keta cikinta ya fito. Tsuntsu ya razana ya tashi sama. Janshahu ya leko daga saman dutsen ya hangi tajiri daga kasa kamar dan tsuntsu, ya daga murya da karfi ya ce masa, "Ya tajiri, mecece bukatarka?"

Bayahude ya amsa da karfi, iska ta kwashi muryarsa ta kai ga Janshahu, "Jeho mini duwatsun da ke nan kusa gare ka, ni kuwa in gaya maka yadda za ka sauko."

Janshahu ya yi dariya ya ce, "In maye ya manta ai uwar 'ya ba ta manta ba. Ni ne fa wanda ka taba kawo wa nan, shekaru biyar da suka wuce, ka barni cikin yunwa da kishirwa da tsananin wahala, ba don ina da sauran shan ruwa gaba ba da tuni na halaka. Wallahi ba ni jeho maka komai." Yana gama fadin wannan magana sai ya gangara ya nufi hanyar fadar Sheik Nasar, Sarkin Tsuntsaye.

Ya yi ta tafiya cikin duwatsu cikin zafin rana da wahala. Idan ya ji yunwa ya ci daga 'ya'yan itacen da ke bisa dutsen ya sha ruwan koramu idan ya samu, kwana da kwanaki bai tsaya ba har ya fara hango hasumiyar Fadar Shugaba Sulaimanu. Ya kara azama, can bayan 'yan kwanaki ya isa ga kofar fadar, ya iske Sheik Nasar zaune a bakin kofa.

Ya matsa kusa gare shi ya sumbaci hannuwansa. Sheik Nasar ya yi masa barka da zuwa, sa'annan ya tambaye shi, "Ya dana, me ya dawo da kai wannan wuri bayan na mayar da kai gida tare da yarinya Shamsiyya, mai sanyaya idanuwa, mai kwantar da zuciyar masoyi?"

Hawaye suka zubo daga idanun Janshahu, ya kwashe labari duka ya gaya wa Dattijo, ya kara da cewa, "Ta ce mini idan har da gaske ina son ta, to, in same ta a Takanni Fadar Jauhari."

Sheik Nasar ya yi mamaki matukar mamaki, ya ce wa Janshahu, "Na rantse da Allah ya kai dana, ban taba jin sunan wannan wuri ba, kai ko lokacin Shugaba Sulaimanu ban taba jin wani ya ambaci sunan wannan wuri ba."

Hankalin Janshahu ya tashi, wasu sabbin hawaye suka kubce masa, ya tambayi Dattijo, "To, yanzu yaya za ni yi? Wallahi son ta zai halaka ni."

Sheik Nasar ya dafa kafadarsa yana ba shi hakuri, ya kara da cewa, "Ka jira lokacin zuwan tsuntsaye sai in tambaye su labarin Takanni Fadar Jauhari, na tabbata ba za a rasa wanda ya taba zuwa wurin ba."

Hankalin Janshahu ya dan kwanta, ya shiga cikin fada, ya shiga cikin soron nan wanda kofarsa daya ta ke fita a cikin lambun da ya hadu da 'yan mata. Ya shiga cikin lambun ya yi ta zagayawa wai ko zai sake ganin 'yan matan nan. Amma ina. Yana nan tare da Sheik Nasar, wata rana suna zaune sai Dattijon ya ce masa, "Ya dana, lokacin zuwan tsuntsaye fa ya kusa zuwa."

Janshahu ya yi farin ciki da jin wannan albishir. Bayan 'yan kwanaki kadan kuwa da yin wannan magana, sai ga tsuntsaye sun fara zuwa kungiya kungiya. Sheik Nasar ya ce masa, "Ya dana zan koya maka wasu kalmomi, domin za ka tsaya tare da ni lokacin da tsuntsaye ke kawo gaisuwarsu." Dattijo ya koya masa kalmomi, sa'annan ya ce masa ya shirya su fita tariyar tsuntsaye.

Suka fito gaban fada suka tsaya. Daga nan sai tsuntsaye suka fara zuwa rukuni-rukuni suna yin gaisuwa ga Sheik Nasar. Kowane rukuni ya zo sai ya tambaye su labarin Takanni Fadar Jauhari, sai dai dukkansu amsa daya ce, "Ba mu taba jin sunan wannan wuri ba." Yayin da Janshahu ya ga babu alamar nasara, sai ya fashe da kuka, nan take zuciyarsa ta buga ya fadi kasa sumamme.

Za mu ci gaba da karfe tara na dare (9:00PM), in sha Allah.

Allah ya kai mu.

16. HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Daga Littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassarar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.

Yayin da Janshahu ya ga babu alamar nasara, sai ya fashe da kuka, nan take zuciyarsa ta buga ya fadi kasa sumamme. Aka yayyafa masa ruwa ya farfado.

Bayan ya farfado sai Sheik Nasar ya kira wani katon tsuntsu, ya aza Janshahu a kansa ya ce wa tsuntsun, "Ka tafi da shi kasar Kabila, kasar mahaifinsa." Ya yi masa kwatancen kasar. Sa'annan ya juya wurin Janshahu ya ce masa, "Ka zauna daidai, kada ka karkata ga wani bangare domin kuwa za ka fado ka halaka. Kuma ka toshe kunnuwanka gudun kada karar iska da rugumniyar juyawar duniya su kurumtar da kai." Janshahu ya yi sallama da Sheik Nasar yana kuka, tsuntsu ya tashi da shi cikin iska. Bayan sun yi tafiyar kwana daya da yini daya sai tsuntsu ya sauke shi a gaban fadar Sarkin dabbobi mai suna Sharu Badaru. Ya ce masa, "Ai kuwa na bace hanya, bari na koma da kai wurin Sheik Nasar."

Jansahahu ya tambaye shi nan ina suke. Tsuntsu ya gaya masa cewa suna gaban fadar Sarkin Dabbobi ne mai suna Sharu Badaru. Janshahu ya ce wa tsuntsu ya bar shi nan wurin Sarkin Dabbobi, tun da dai bai sami abin da ya fito nema ba ya fi so ya mutu da ya koma gida. Tsuntsu ya bar shi a fadar Sarkin Dabbobi, ya kama gabansa.

Sarkin Dabbobi ya tambayi Janshahu, "Samari, wanene kai? Me ya sa wannan tsuntsu ya kawo ka nan?"

Janshahu ya kwashe labarinsa tun daga farko har karshe ya fada masa. Sharu Badaru ya yi mamaki da jin wannan labari, ya kara da cewa, "Na rantse da Shugaba Sulaimanu, tun da nake ban taba jin wani wuri mai suna Takanni Fadar Jauhari ba. Amma zan binciki dabbobi idan akwai wanda ya san wannan wuri zan yi masa kyauta mai yawa domin ya kai ka wurin."

Janshahu ya yi kuka kuka mai tsanani, daga karshe ya hakura ya zauna tare da Sharu Badaru. Wata rana sai Sharu Badaru ya kawo masa wani allo ya ce, "Ya dana, hardace wadannan kalmomi da ke rubuce cikin wannan allo domin idan lokacin zuwan dabbobi ya yi tare da kai zan fita, mu tambaye su labarin Takanni Fadar Jauhari."

Janshahu ya hardace kalmomin da Sarkin dabbobi ya umurce shi. Ba a dade ba sai ga dabbobi nau'i daban-daban sun fara zuwa yin gaisuwa ga Sharu Badaru. Duk wadanda suka zo sai ya tambaye su Takanni Fadar Jauhari, amma sai su amsa masa, "Ba mu san wannan fada ba, ba mu taba jin sunanta ba."

Da Janshahu ya ji haka sai ransa ya baci, zuciyarsa ta yi duhu don bakin ciki. Da Sharu Badaru ya lura da halin da yake ciki sai ya ce masa, "Kada ka yi bakin ciki ya dana. Zan aika da kai wurin wani dan uwa nawa mai suna Sarki Shimak Babba, wanda yake ya girme ni ga shekaru. Shugaba Sulaimanu ya taba tsare shi a kurkuku saboda wani laifi da ya yi masa. A cikin aljanu yanzu babu tsararsa, shi da Sheik Nasar. Shi ne ke mulki da dukkanin aljanun duniya bayan rasuwar Shugaba Sulaimanu. Watakila shi ya san inda wanna fada take."

Sharu Badaru na gama fadar haka sai ya kira wata babbar dabba, ya aza Janshahu bisa bayanta. Ya kawo wasika ya ba shi, ya ce ya kai wa dan uwansa Sarki Shimak. Dabba ta nausa da Janshahu cikin daji, ta yi ta tafiya da shi kwana da kwanaki har ta iso ga fadar Sarki Shimak. Suna zuwa kusa da fadar sai dabbar ta hango Sarki Shimak, ta ja ta tsaya, ta ki karasawa inda yake. Yayin da Janshahu ya ga haka sai ya sauka ya nufi wurin Sarki Shimak. Yana zuwa wurinsa sai ya fadi ya yi gaisuwa, ya jawo wasikar da Sharu Badaru ya ba shi ya mika wa Sarki Shimak.

Bayan Sarki ya karanta wasika ya fahimci sakon da ke cikinta sai ya yi jugum zuwa wani dan lokaci. Ya daga kai ya dubi Janshahu ya nisa ya ce, "Na rantse da Allah ya dana, tsawon rayuwata ban san wannan fada ba. Kai ban ma taba jin sunanta ba sai yau." Ganin hawaye sun fara kwarara daga idanun Janshahu sai ya ci gaba da cewa, "Gaya mini labarinka. Wanene kai? Kuma daga ina ka fito?"

Janshahu ya duka ya kwashe labarinsa duka ya gaya wa Sarki Shimak. Sarki ya yi al'ajabi gayar al'ajabi ya ce, "Amma wannan fada da ban mamaki take. Ba na tsammani Shugaba Sulaimanu da kansa ya san inda wanna fada take ko ya taba jin sunanta."

Ya yi shiru yana tunani, can sai ya ce, "Ya dana, zan aika da kai wurin wani bawan Allah mai yawan ibada wanda ya tsufa kwarai har babu tsararsa yanzu a duniya. Dukkan tsuntsaye da dabbobi da aljanu suna biyayya gare shi, ba sa saba umurninsa ko kadan. Ya mallaki dukkan sarkunan aljanu don karfin ibadarsa da rokon Ubangiji. Ni kaina, duk taurin kan nan nawa, ya taba daure ni ya jefa cikin kurkuku bisa ga umurnin Shugaba Sulaimanu. A lokacin kuwa babu wani aljani da ya isa ya matso kusa gare ni balle har ya kama ni. Tun lokacin nake matukar jin tsoronsa kuma ko da wasa ba na saba wa umurninsa. Babu inda wannan bawan Allah bai leka ba a cikin duniya. Ya san kowace kasa dake cikin duniya, biranenta da kauyukanta. Ya san dukkan tekuna da duwatsu da tsibirai da kwarurrukan dake bayan kasa kamar yadda ya san tafin hannunsa. Ba na tsammani akwai wani wuri a fadin duniyar nan wanda wannan bawan Allah bai sani ba. Zan aika ka zuwa gare shi domin ya aza ka bisa ga tafarkin zuwa Takanni Fadar Jauhari. Idan kuwa har ya ce bai san wannan fada ba, to, sai dai ka hakura domin kuwa ba na tsammani tana cikin wannan duniya. Na manta ma ban fada maka wani abin mamaki ba game da wannan bawan Allah. Ya taba karya wata sanda ya yi mata guntu uku. Ya dasa kowane guntun sandar a kasa. Ya yi wasu addu'o'i, sai guntun sanda na farko ya rika fitar da soyayyen nama da zuma. Guntun sanda na biyu ya rika fitar da madara mai zaki. Guntun sanda na uku kuma ya rika fitar da alkama da masara. Daga nan sai ya cire sandunan ya hade su suka zama sanda guda kamar yadda take da farko. Ya shige cikin fadarsa wadda aka gina da danyen lu'ulu'u. Haka kuma wannan bawan Allah sadauki ne na karshe, komai yawan runduna yana ganin bayanta. Ya kware kwarai wajen iya siddabaru iri-iri, sunansa Yamusa. Gare shi zan aika da kai yanzu tare da wani tsuntsu mai fikafikai hudu da zai dauke ka a bayansa.kowane fiffike yana da tsawon awo talatin, kafafunsa kuwa kamar na giwa suke. Yakan tashi cikin sararin samaniya sau biyu a shekara, sa'annan yakan yi kalaci da rakuma biyu manya manya a kowace rana wadanda wani aljani mai suna Timshuna yakan samo daga kasar Iraki."

Sarki Shimak ya kira wannan tsuntsu ya aza Janshahu bisa bayansa, ya ce masa ya kai shi ga bawan Allah Yamusa. Tsuntsu ya kada kai alamar 'na ji na dauka' ya tashi sama cikin iska. Suka yi ta tafiya cikin iska dare da rana har suka iso ga tsaunin da fadar Yamusa take. Tsuntsu ya sauka a kan tsauni. Janshahu ya sauka daga bayan tsuntsu ya nufi fadar Yamusa da aka gina da danyen lu'ulu'u, ya iske shi zaune yana wuridi. Bayan ya idar da wuridi sai Janshahu ya matsa kusa gare shi, ya durkusa ya gaishe shi da ladabi.

Yayin da Yamusa ya gan shi, sai ya yi masa maraba da zuwa. Ya tambayi labarinsa da dalilin zuwansa wannan wuri. Janshahu ya kwashe labari ya gaya masa, daga karshe ya shaida masa cewa ya fito ne garin neman Takanni Fadar Jauhari. Yamusa ya cika da mamakin jin wannan

Please Login or Register in order to submit comment