Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi mini?"

Janshahu ya amsa masa, "Kwarai kuwa, a shirye nake."

Tajiri ya umurci bayi su kawo musu alfadarai guda biyu. Ya hau daya, Janshahu ya hau daya, suka nufi wajen birni. Suka yi ta tafiya tun da safe har rana ta take. Suka isa ga wani tsauni, tsawonsa babu iyaka. Da suka kawo ga gindin tsauni, sai tajiri ya sauka daga kan alfadara, ya umurci Janshahu cewa ya sauka daga kan tasa alfadarar. Bayan Janshahu ya sauka daga kan alfadara, sai tajiri ya zaro wuka da igiya, ya mika wa Janshahu ya ce, "Ina so ka yanka mini wannan alfadara."

Janshahu ya karbi wuka da igiya, ya nade hannayen rigarsa da kafafun wandonsa. Ya tattare habar rigarsa ya cusa cikin wandonsa. Ya kayar da alfadara, ya daure kafafunta da igiya. Ya sa wuka ya yanke mata makogwaro. Tajiri ya ce, ya fede ta ya cire kan da kafafu. Ya aikata kamar yadda aka umurce shi. Alfadara ta zama kamar wani tarin nama ne wuri guda.

Tajiri ya ce, "Ka farke cikinta, ka fitar da kayan cikin waje, ka shiga ciki in dinke ka. Ina so bayan na dinke ka a cikinta ka gaya mini dukan abin da ka gani. Wannan shi kadai ne aikin da za ka yi mini."

Janshahu ya farke cikin alfadara, ya zubar da kayan cikin waje. Ya shige cikin cikinta ya kudundune. Tajiri ya sa zare da allura ya dinke cikin alfadara, ya koma wani wuri da nisa ya make yana kallon abin da zai faru.

Can sai ga wani katon tsuntsu, girmansa kamar rakumi, ya fyauce alfadarar ya tashi sama da ita. Ya nufi kololuwar tsaunin nan ya sauka da ita. Bayan tsuntsu ya fara yin kalaci a kan alfadara, sai Janshahu ya barke dinkin ya fito waje. Da tsuntsu ya gan shi sai ya tsorata, ya tashi sama ya bar shi nan saman kololuwar tsauni.

Jansahahu ya mike tsaye cikin mamaki, ya duba dama da hagu bai ga kowa ba, sai gasusuwan mutane da dabbobi birjik a wurin. Ganin haka sai ya buga salati ya ce, "Babu tsimi babu dabara face daga Allah Madaukakin Sarki."

Ya zo bakin tsaunin ya leka kasa, ya hangi tajiri can karkashin tsaunin tamkar dan tsuntsu. Yayin da tajiri ya hango Janshahu sai ya yi kira da karfi ya ce, "Jeho mini duwatsun da ke kusa gare ka in nuna maka hanyar da za ka bi ka sauko." Iska ta kwashi muryarsa ta kai ga kunnen Janshahu.

Janshahu ya jeho masa kamar duwatsu metan, wadanda suke duk yakutu ne da jauhari mai tamanin gaske. Bayan ya gama jefa masa, sai ya bude murya da karfi ya ce, "Nuna mini inda hanya take in kara jeho maka wasu."

Tajiri bai ko tsaya sauraren Janshahu ba, sai ya tattara duwatsun da ya jeho masa ya kulle su cikin rigiza, ya aza wa alfadararsa ya koro ya nufi gida yana cewa, "Ai kuda wajen kwadayi yakan mutu." Ya bar Janshahu saman tsauni, tasa ta fisshe shi.

Yayin da Janshahu ya ga tajiri ya tafi ya bar shi saman wannan tsauni, kuwwarka banza. Ya yi nadamar karbar kudin tajiri, ya ce a cikin ransa, "Babu shakka masu iya magana sun yi gaskiya da suke cewa, 'kwadayi mabudin wahala.'" Ya yi kuka har ya gaji. Da ya ga dai kuka ba zai fitar da shi ba, sai ya daga hannuwansa sama ya roki Allah ya kubutar da shi daga cikin wannan hali. Ya zauna cikin wannan hali tsawon kwana uku. Daga nan sai ya tashi ya yi ta tafiya saman dutse har tsawon wata biyu, yana cin abin da ya samu na daga 'ya'yan itatuwa da ciyayin da ke saman dutsen. Kwanci tashi yana tafiya, har ya kawo karshen tsaunin ta bayansa. Ya ga wata hanya ta gangara ta nufi kasan tsaunin. Ya bi wannan hanya, bayan ya yi 'yar tafiya mai tazara, sai ya hangi wani kwari, daga can kasan tsaunin, mai yawan itatuwa masu 'ya'ya. Ya ga tsuntsaye masu launi iri daban daban suna ta kai da komowa, daga wannan bishiya zuwa waccan, suna rera wakoki da kukansu.

Janashahu ya yi farin ciki da ya fara hangen burbushin kasa. Ya ci gaba da gangarowa daga kan tsauni tsawon sa'a guda, ya tarar da wani kwararo kamar bututu, wanda ruwa ke gangarawa zuwa ga kwarin nan da ya hanga. Ya bi ta cikin wannan kwararo yana tafiya har ya bulla cikin kwarin. Ya tsaya ya duba dama, bai ga komai ba. Ya duba hagu, sai ya hangi wani gini mai wata irin doguwar hasumiya. Sai ya nufi wannan gini, zuciyarsa na dar-dar.

Za mu ci gaba

Allah ya kai mu!

_____7. HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Daga Littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassarar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada

Janashahu ya yi farin ciki da ya fara hangen burbushin kasa. Ya ci gaba da gangarowa daga kan tsauni tsawon sa'a guda, ya tarar da wani kwararo kamar bututu, wanda ruwa ke gangarawa zuwa ga kwarin nan da ya hanga. Ya bi ta cikin wannan kwararo yana tafiya har ya bulla cikin kwarin. Ya tsaya ya duba dama, bai ga komai ba. Ya duba hagu, sai ya hangi wani gini mai wata irin doguwar hasumiya. Sai ya nufi wannan gini, zuciyarsa na dar-dar.

Yana isa ga ginin nan sai ya tarar da wani dattijo, mai farin gemu, annuri na fita daga fuskarsa. Yana tsaye a bakin kofar wannan gini rike da sandar lu'ulu'u a hannunsa. Janshahu ya yi wa dattijo sallama. Dattijo ya mayar masa da sallamarsa, ya kuma yi masa lale marhabin. Ya jawo abin zama ya ba shi, ya ce ya zauna. Janshahu ya zauana.

Bayan ya zauna dattijo ya dube shi, fuskarsa cike da mamaki, ya tambaye shi, "Ya dana, yaya aka yi ka shigo wannan kasa wadda wani dan Adam bai taba takowa ba, face Shugabanmu Sulaimanu Dan Dawuda?"

Da Janshahu ya ji tambayar dattijo, sai hawaye suka karyo masa, ya yi kukan bakin ciki domin rabuwa da kasarsa. Dattijo ya dafa kafadarsa ya ce, "Bari kuka ya dana. Kukanka yana kona mini rai." Yana gama fadar haka, sai ya tafi ya kawo masa abinci da abin sha, ya ajiye a gabansa ya ce, "Ci."

Janshahu ya ci abinci ya koshi. Ya godewa Allah Madaukakin Sarki. Yayin da dattijo ya ga hankalinsa ya fara komowa jikinsa, sai ya ce masa, "Ya dana, gaya mini labarinka, da abin da ya fito da kai daga gida, da kuma dalilin zuwanka nan."

Janshahu ya kwance wa dattijo bakin jaka. Ya gaya masa kome tun daga fitowarsa gida har zuwa wannan wuri. Dattijo ya cika da mamaki, matukar mamaki. Sa'annan Janshahu ya tambayi dattijo, wanene shi? Wa ya mallaki wannan kwari da fadar da ke cikinsa?

Dattijo ya amsa masa, "Ya dana, wannan kwari da kake gani, da fadar da ke cikinsa, mallakar Shugaba Sulaimanu Dan Dawuda ce (Amincin Allah ya tabbata a gare su). Ni kuwa sunana Sheik Nasar, nine mai kula da tsuntsaye dukansu. Shugaba Sulaimanu ya gina mini wannan fada, sa'annan ya sanar da ni harshen tsuntsaye na duniya duka, ya nada ni a matsayin Sarkinsu. Karshen kowace shekara, tsuntsaye sukan zo nan gare ni, rukuni-rukuni, in duba su in kuma yi hukunci a tsakaninsu. Wannan shi ne dalilin zamana wannan wuri."

Yayin da Janshahu ya ji jawabin Dattijo, sai ya yi kuka, kuka mai yawa ya ce, "Ya baffana, ya ya za a yi na koma kasarmu?"

Dattijo ya amsa masa, "Ka sani cewa ya kai dana, kana kusa ne da Dutsen Kaf. Ka zauna nan tare da ni har zuwa lokacin da tsuntsaye za su zo gare ni, sai in hada ka da masu zuwa wajen kasarku su tafi da kai. Zan bude maka wannan fada ka zagaya cikinta. Ka ci ka sha dukkan abin da ranka yake so."

Janshahu ya zauna tare da Sheik Nasar a cikin kwari, yana ci daga 'ya'yan itatuwa masu zaki da dadi. Yana shakar kamshin furanni, yana sauraren wakokin tsuntsye. Saboda kyawun kwarin nan sai bakin cikin Janshahu ya yaye, zuciyarsa ta yi fari, ya kasance cikin annashuwa da farin ciki har lokacin zuwan tsuntsaye ya gabato. Da ranar zuwan tsuntsaye ta zo, sai Sheik Nasar ya dauko mabudan fadar nan ya mika wa Janshahu ya ce masa, "Ya dana Janshahu, karbi wadannan mabudai, ka shiga cikin wannan fada ka kashe kwarkwatar idanunka kafin lokacin komawarka gida. Amma akwai wata kofa daya, wanda aka kulle da kwadon zinariya, to kada ka kuskura ka bude ta balle har ka shiga cikinta. Idan kuwa ka bijirewa wannan gargadi nawa, ka shiga cikin wannan kofa, to kuwa za ka shiga cikin taskun rayuwa." Ya jaddada wannan gargadi ga Janshahu, ya kara jaddada shi har sau uku, sa'annan ya ba shi mabudai ya nufi inda yake tsayuwa domin amsa gaisuwar tsuntsaye. Tsuntsaye suka rika zuwa gare shi kungiya-kungiya, suna yin gaisuwa gare shi. Wannan shi ne al'amarinsa.

Amma al'amarin Janshahu kuwa shi ne bayan ya bude fada sai ya shiga cikinta, ya rika zagayawa yana kallon abubuwan mamaki da ke ciki. Ya rika bude kofofi daya bayan daya, yana shiga cikinsu har ya zo ga kofar nan da Sheik Nasar ya gargade shi da shigarta. Ya ga kofar duk ta fi sauran kofofin kyau, an rufe ta da kwadon zinariya. Kyawun wannan kofa sai ya kayatar da shi, ya tsaya yana wasi-wasi yana zancen zuci, "Babu shakka abin da ke cikin wannan kofa ya zarce sauran kofofin nesa ba kusa ba, ni kuwa na so in ga abin da ke cikin wannan kofa." Ya yi kamar zai wuce, sai kuma wata zuciyar ta dakatar da shi. Ya kara cewa a cikin ransa, "Shin wai ma don me Sheik Nasar ya hana ni shiga cikin wannan kofa? Babu makawa in ga abin da ke ciki! Ai duk abin da zai sami bawa na kaddara rubutacce ne, tun kafin ya leko duniya." Sai ya sa mabudi ya bude kwadon kofa, ya tura kofar da hannu ta bude, ya kutsa kai ciki.

Yana shiga cikin wannan soro sai ya dimauta da abin da ya gani na daga kyawon wannan soro. A tsakiyar soron ya ga wani tabki da aka gina da farin dutse, daga gefen wannan dan tabki akwai wani dan daki karami da aka yi da danyen zinari, aka kawata shi da azurfa da buluri. Dan dakin na da wata taga ta farin karfe, an daje bakinta da yakutu da ruhham da zubarjadi. Da Janshahu ya shiga cikin wannan dan daki sai ya ga an dabe kasansa da tsanwar balhashi da zumarrazi. Ya ga wani dan tabki karami da aka gina da zinariya, da wani bututu na azurfa a tsakiyarsa yana aman ruwa. A zagaye da tabkin akwai surorin tsuntsaye iri daban-daban, wasu an yi su da zinariya wasu da azurfa, wasu da tagulla. Wasu daga cikin tsuntsayen nan suna fitar da ruwa daga bakunansu, ruwan na komawa cikin dan tabkin. Wasu kuma suna rera wakoki da irin kukansu idan wani dan bututu ya busa musu iska.

Daga gefen wannan tabki Janshahu ya ga wata kofar, ya shiga cikinta sai ya tarar da wani makeken lambu, mai yawan itatuwan wardi da furanni, koramu na gudana ko'ina, da tsuntsaye suna rera wakoki. A cikin lambun kuma akwai wata rumfa ta alharini, sandunanta na zinariya. A tsakiyar rumfar an kafa wata babbar karaga irin ta masu mulki. Wannan karaga ta lu'ulu'u ce, an layyace ta da zubarjadi da zinariya da azurfa da jauhari iri-iri. A saman karagar kuma an kafa wata laima ta tsanwar alharini, mai fadi da tsawo awo hamsin. Wannan laima an yi ma ta cin baki da zinariya da azurfa da lu'ulu'u da dangin jauhari. Daga gefen wannan karaga an shimfida dardumar Shugaba Sulaimanu Dan Dawuda (Amincin Allah ya tabbata a gare su).

Janshahu ya yi mamaki da kyawon wannan wuri matukar mamaki. Ya shiga cikin lambu yana zagayawa, kamshin furanni duk ya cika wurin da wakar tsuntsaye mai kwantar da hankali. Ga iska mai sanyi tana kadawa, rassan itatuwan na rangaji gwanin ban sha'awa. A karkashin kowace bishiya ta cikin wannan lambu an kafa gado na zinariya da shimfidu masu daraja.

Bayan ya gama yawo cikin lambu sai ya dawo inda rumfar nan take, ya dare bisa karaga sai ka ce wani Sarki. Bai dade da zama ba sai barci ya yi awon gaba da shi.

Bayan ya yi barci na wasu 'yan sa'o'i kadan sai ya farka. Ya tashi daga kan karaga ya tafi inda wani abin zama da ke karkashin wata itaciya ya zauna. Yana nan zaune karkashin itaciya yana mamakin wannan wuri, sai ya hangi wasu tsuntsaye guda uku cikin sararin Subahana, sun yiwo wa lambun nan tsinke. Da suka yo kusa sai Janshahu ya ga jikin tsuntsayen irin na tattabaru ne farare, girmansu kuwa kamar mikiya. Suka zo suka sauka a gefen wani tabki da ke cikin lambun. Daga inda Janshahu yake zaune yana hangen su, amma da yake a bayan bishiya ne, tsuntsayen ba su iya ganinsa.

Bayan sun sauka sai suka dan yi wasanni da juna, daga nan sai Janshahu ya ga sun cire fukafukansu na gashi, suka yi girgiza, nan take sai suka rikida zuwa 'yan mata, tsarar juna, suna haske kamar watanni. Tsarki ya tabbata ga Mahaliccin wadannan 'yan mata, wadanda Janshahu bai taba ganin kyawawa kamarsu ba.

(c) 2015 Taskar Bukar Mada

Za mu ci gaba in sha Allah.

Allah ya kai mu lafiya!8. HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Daga Littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassarar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.

Bayan tsuntsayen nan sun sauka sai suka dan yi wasanni da juna, daga nan sai Janshahu ya ga sun cire fukafukansu na gashi, suka yi girgiza, nan take sai suka rikida zuwa 'yan mata, tsarar juna, suna haske kamar watanni. Tsarki ya tabbata ga Mahaliccin wadannan 'yan mata, wadanda Janshahu bai taba ganin kyawawa kamarsu ba.

Suka fada cikin tabki suna wanka suna wasa da ruwa. Daga inda Janshahu yake zaune yana jiyo dararrakunsu kamar ana busa sarewa. Ya yi mamaki da kyawonsu, da tsarin siffar jikinsu. Da suka gaji da wanka sai suka fito daga cikin tabki, suka shiga cikin lambu suna zagayawa fuskokinsu cike da annurin farin ciki.

Yayin da Janshahu ya ga wadannan 'yan mata sun fito daga cikin tabki sai ya kidime, bai san lokacin da ya tashi ya bi su ba a baya. Da ya cim musu sai ya yi musu sallama. Suka juyo, ba tare da yanayin fuskarsu ya canja ba, suka amsa masa sallamarsa. Da ya ji sun amsa masa sallama sai ya ji sanyi a ransa har ya tambaye su, ko 'ya'yan wane Sarki ne su? Kuma wai daga ina suke?

Sai karamarsu ta amsa masa, "Mun fito daga wata duniya da ba ta ganuwa ga 'yan Adam. Mun zo wannan lambu domin debe kewa, kamar yadda mukan yi duk shekara."

Janshahu ya kara kidimewa domin kyawonsu. Ya dubi karamarsu, wadda ta zarce sauran ga kyau, ya kwantar da muryarsa ya ce, "Ya ke wannan sarauniyar kyau, Wallahi zuciyata ta raunana da ganinki. Ki ji tausayina, ki share mini hawayen bakin cikin rabuwata da kasarmu. Ke kadai ce maganin wannan rauni na zuciyata."

Ta yi dariya don jin zancensa, ta ce, "Bari wannan zance don ba mai yiwuwa ba ne. Kai dai kama gabanka kawai." Hawaye suka zubo daga idanunsa, ya yi ajiyar zuciya, ya wake wadannan baitoci:

"Ta haskaka dukkan lambu,
Da tufafi tsanwar launi.

Gashin kanta da sheki,
Ga iska nata kada shi.

Rigarta abin kallo ce,
Sakarta ta alharini.

Mi sunanki? Na tambaya,
Sai ta amsa sunana Ni.

Zuciya kan konu da kyanta,
Zafin ya fi wuta ko gaushi.

Sonki ya raunana zuciya,
Maganinsa yana hannunki.

Murmushinki ya narke dutse,
Balle wata tsoka zuci.

Zuciyarki da karfin dutse,
Maishe ta ruwa don taushi."

Yayin da 'yan mata suka ji wakarsa sai suka yi dariya tare da kekkewa. Suka rera nasu wakoki, suka yi wasa da dariya. Janshahu ya tafi ya kawo musu 'ya'yan itatuwa da abin sha. Suka zauna suka ci tare, suka sha abin sha. Suka kwana cikin wannan lambu har zuwa wayewar gari. Daga nan sai 'yan matan nan suka sanya fukafukansu na gashi, nan take suka koma cikin siffar tsuntsaye. Suka kada cikin iska suka koma inda suka fito.

Lokacin da Janshahu ya ga 'yan matan nan sun tashi sama sai hankalinsa ya tashi, ya ji kamar sun sace ruhinsa sun tafi da shi. Ina ma a ce shi ma yana da fiffiken da za ya bi su? Sai ya yi wata kara, kara mai tsanani, ya fadi kasa sumamme. Ya kasance cikin wannan hali tsawon wannan rana.

A cikin wannan hali da Janshahu ya tsinci kansa, Sheik Nasar ya gama karbar gaisuwar tsuntsaye. Sai ya shigo cikin fada yana bidar Janshahu don ya hada shi da wasu tsuntsaye da za su kai shi kasarsu. Da ya duba ko'ina cikin fadar nan bai gan shi ba, sai ya kitsa a cikin ransa, babu makawa ya shiga kofar nan wadda ya hana shi shigarta. To, dama ya ce wa tsuntsaye, "Akwai wani saurayi da kaddara ta koro shi nan daga kasa kaza. Ina so ku tafi da shi zuwa ga kasarsa." Tsuntsaye suka karba masa, "Mun ji mun amsa."

Sheik Nasar dai ya ci gaba da neman Janshahu har ya zo ga kofar nan, ya tarar da ita a bude. Ya shiga cikinta, ya shiga cikin dan daki ya fita cikin lambu. Ya rika zagayawa a cikin lambu har ya iso inda Janshahu yake kwance karkashin wata itaciya sumamme. Ya debo ruwan wardi ya yayyafa masa a fuska, nan take ya farfado, ya mike zaune. Ya duba dama, ya duba hagu amma bai ga kowa ba sai Sheik Nasar. Ya yi nannauyar ajiyar zuciya, ya wake wadannan baitoci:

"Ta haske dukan wuri tamkar farin wata,
A lokacin cika da batsewarsa.

Surar jikinta da kyau da daukar hankali.
Tufafinta na haske don fari nasa.

Girarta kamar baka bakinta duhun dare,
Balle Idanunta don haskensa.

Lebbanta jan launi tamkar furen wardi,
Hakoranta kan leko idan ta murmusa.

Na rantse da Allah ba zan iya rayuwa ba,
Face ga ni ga wannan masoyiya a kusa."

Da Sheik Nasar ya ji wannan waka tasa sai ya ce, "Ashe ban gargade ka ba akan bude wannan kofa? Ya dana, gaya mini menene ya faru gare ka."

Janshahu ya gaya masa dukkan abin da ya faru tsakaninsa da 'yan matan nan guda uku. Sheik Nasar ya yi kasake yana saurarensa. Da ya ji ya kai karshen labarinsa sai ya dafa kafadar Janshahu ya ce masa, "Ya dana, ka sani cewa wadannan 'yan mata da ka gani 'ya'yan aljanu ne. Sukan zo wannan lambu domin debe kewa a cikin kowace shekara, daidai wannan lokaci. Idan suka zo sukan kwana daya da yini sa'annan su koma kasarsu. Ba su dawowa kuma sai wata shekara."

Janshahu ya tambaye shi, to ina ne kasarsu? Dattijo ya amsa da cewa, "Na rantse da Allah, ya kai dana, ban san daga inda suke fitowa ba."

Dukkansu suka yi shiru na dan wani lokaci, daga nan sai Dattijo ya ce, "Aje zancen soyyar nan ka tashi yanzu in hada ka da tsuntsayen da su mayar da kai kasarku."

Yayin da Janshahu ya ji cewa Sheik Nasar bai san inda wadannan 'yan mata suka fito ba, sai ya yi wata kara, ya fadi kasa sumamme. Dattijo ya kara yayyafa masa ruwa ya farfado. Bayan Janshahu ya farfado sai ya ce wa Dattijo, "Ai ni yanzu ba ni da burin komawa kasarmu. Babban burina yanzu shi ne in kara ganin 'yan matan nan. Wallahi ba zan bar nan wurin ba har sai na kara ganinsu, ya kai baffana."

Daga nan sai hawaye suka karyo masa, ya ce, "Ganin fuskar wadda nake so ya fi mini kome da ke cikin duniyar nan." Ya fadi kasa, ya kama kafafun Sheik Nasar yana sumbuta yana kuka, yana cewa, "Ka tausaya mini Allah ya tausaya maka! Ka taimake ni in ga wadda nake so, kai kuma Allah ya taimake ka!"

Dattijo ya amsa masa da cewa, "Ya kai dana, Wallahi ban san kome ba game da wadannan 'yan mata. Ban san kasarsu ba balle inda suka fito! Amma idan har akwai wadda kake so a cikinsu, to, ka zauna nan tare da ni har zuwa wata shekara, daidai wannan lokaci, babu shakka za su sake dawowa. Idan lokacin zuwansu ya kusa, sai ka boye a bayan wata bishiya dake cikin wannan lambu. Da zarar sun zo ka ga sun cire rigunansu na gashi sun fada cikin tabki suna wanka, sai ka lallaba ka dauke na wadda kake so. Idan suka gan ka za su fito daga cikin tabkin. Kowace za ta nemi tufafinta ta sanya, wadda ka dauke nata kuwa idan ta gan su ga hannunka, za ta fara yi maka magiya tare da murmushin jan hankali tana cewa, 'ya dan uwana, miko mini tufafina in suturta jikina.' Idan ka kuskura ta yaudareka da hilarta har ka mika mata tufafin, to, idan suka tafi ba za su sake dawowa nan ba, don haka kai da ganinsu har abada. Amma idan ta ce ka mika mata tufafin, to, ka kara makalkale su gam karkashin hammatarka. Idan na gama karbar gaisuwar tsuntsaye zan zo gare ku. Sai in daidaita tsakaninku, idan ta amince sai in daura muku aure, in sa tsuntsaye su dauke ku, kai da ita, su kai ku kasarku. Wannan shi ne kawai taimakon da nake iya yi maka, ya kai dana."

Yayin da Janshahu ya ji haka, sai farin cikinsa ya komo. Ya yi murmushi har hakoransa suka bayyana, ya gode wa dattijo. Janshahu ya ci gaba da zama tare Dattijo, kullum yana lissafin kwanaki har shekara ta zagayo. Da ranar zuwan tsuntsaye ta zo sai Dattijo ya ce masa, "Ka tafi ka aikata kamar yadda na gaya maka game da rigar gashin nan. Ni zan tafi domin amsa gaisuwar tsuntsaye."

Janshahu ya ce, "Na ji, na karba, ya baffana."

Ya shiga cikin lambu, ya boye a bayan wata babbar bishiyar inabi, inda babu mai iya ganinsa, yana kallon tabkin nan. Yana nan labe yana jiran zuwan 'yan mata tun da safe har dare ya yi ba su zo ba, ya kwana a wurin. Washe gari ya ci gaba da jira, yana kallon sararin samaniya ko ya hango su tafe, amma babu su babu dalilinsu har duhun dare ya mamaye lambun. Hankalinsa ya tashi, hawaye suka yi ta kwarara daga idanunsa. Da ya tuna da yarinyar nan da irin kyawonta, sai shaukin bege ya buge shi, ya fadi kasa sumamme.

(c) 2015 Taskar Bukar Mada

Instagram: @maganajari
WhatsApp: +2348032767547

Za mu ci gaba daidai wannan lokaci, karfe tara na dare (9:00PM), in sha Allah.

Allah ya kai mu.9. HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassarar

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.

Janshahu ya shiga cikin lambu, ya boye a bayan wata babbar bishiyar inabi, inda babu mai iya ganinsa, yana kallon tabkin nan. Yana nan labe yana jiran zuwan 'yan mata tun da safe har dare ya yi ba su zo ba, ya kwana a wurin. Washe gari ya ci gaba da jira, yana kallon sararin samaniya ko ya hango su tafe, amma babu su babu dalilinsu har duhun dare ya mamaye lambun. Hankalinsa ya tashi, hawaye suka yi ta kwarara daga idanunsa. Da ya tuna da yarinyar nan da irin kyawonta, sai shaukin bege ya buge shi, ya fadi kasa sumamme.

Bai farfado ba sai da gari ya waye. Wannan ita ce rana ta uku. Ya yi zugum yana tunani, yanzu idan ba su zo ba wane irin hali zai shiga? Ya tashi ya duba sama ko zai hango su, ya duba tabki ko zai gan su suna wanka, zuciyarsa cike da tsananin bege. Can bayan rana ta yi zawwali sai ya hango tsuntsaye guda uku, cikin sararin samaniya, sun nufo wannan lambu. Suka sauka a bakin tabkin nan, Janshahu ya gan su kamar yadda ya gan su da farko, cikin surar fararen tattabaru amma girman kowace daya kamar na mikiya.

Bayan sun sauka bakin tabki, suka duba dama suka duba hagu, ba su ga kowa ba na daga mutum ko aljani. Daga nan sai suka tube tufafinsu na gashi suka ajiye gefe guda. Suna tube tufafin nan sai suka rikide zuwa kyawawan 'yan mata, kai ka ce su watanni ne don kyawunsu. Suka fada cikin tabki suna wanka suna wasa da juna cikin dariya da farin ciki. Dariyar da Janshahu ke jin kamar ana busa sarewa don dadin muryoyinsu.

Suka ci gaba da wanka, Janshahu na make bayan bishiya yana kallonsu. Jikinsu sai sheki yake yi kamar danyar azurfa. Can sai ya ji

Please Login or Register in order to submit comment