Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

001. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA

Wani namiji ya kasance mai daukar kaya (dako) a cikin birnin Bagadada. Ya kasance gwauro ne, ba shi da mata. Ana nan wata rana daga cikin ranaku, yana tsaye a wata rumfa ta kasuwa ya na neman wanda zai daukarwa kaya, sai wata mace, kyakkyawa, ta zo gare shi, tana lullube da mayafi, wanda aka yi wa kwalliya da zane-zane na alharini, an yi masa ado da zinariya, ta ce masa, dauko gammonka ka biyo ni.

Dan dako bai gasgata abinda kunnuwansa suka jiye masa ba, daga bakin wannan kyakkyawar mace, har sai da ta kara cewa da shi, dauko gammonka, ka biyo ni. Sannan ya dauka ya bi bayanta, suka shiga cikin kasuwa.

Bai gushe ba yana biye da ita har suka zo gun rumfar wani Banasare, ta dauko dinari ta ba shi, ya karba ya ba ta zaituni. Ta saka a cikin kwandon Dan dako. Ta ce, dauko biyo ni.

Ya dauki kwando ya bi ta, suka tsaya a rumfar mai sayar da kayan marmari. Ta sayi dukan abin da take bukata na daga kayan marmari ta zuba a cikin kwandon Dan dako. Suka wuce gaba har zuwa rumfar mahauci, ta sayi nama awo goma, ta nade shi a cikin ganye ta saka a kwandon Dan dako. Ta ce dauko biyo ni, ya kai Dan dako. Ya dauka ya bi ta.

Ta tsaya kan rumfar mai alawa, ta sayi faifai ta cika shi da alawa kala-kala, da soyayyun abubuwa, da dadada, da zakaka, da kamsasa, duk ta jefa su a cikin kwandon Dan dako. Ta ce da shi, ka dauko mu tafi, ka amince da bi na!

Ta tafi, shi na biye da ita, ya na cewa, “Da kin sanar da ni za ki yi sayayya da yawa ai da na taho da alfadarata na dora mata wannan kaya, ya shugabata.” Ta yi murmushi, ta tafi, yana bin ta a baya.

Yayin nan ta tsaya bisa ga rumfar mai turare, ta sayi ruwaye goma na daga ruwan wardi, da ruwan sandal, da shashimi, da wadansun wadannan, ta karbi sukar, ta wuce, Dan dako ya bi ta. Ta ce ta manta, ta komo ta karbi lubban, da ambar, da miski, da shama’ar askandariya, ta aza dukkan wadan nan a cikin kwandon Dan dako, ta ce ka dauko ya Dan dako, ka biyo ni, yanzu kam na gama sayayya, gida za ka kai mini kayan.

Dan dako ya dauki kaya ya bi matar nan har suka iso wani gida, mai kyawo, mai doguwar katanga, da fararen soraye, da madaukakan sassa. Kofar gidan ta kasance shafaffiya da labunus, gogaggiya da zinariya, gambunta na jan dinari. Yarinya ta tsaya a gaban gidan, ta kwankwasa kofa, kwankwasa mai taushi, kamar ana kida dundufa.

Daga nan kofa ta bude, ta ce da Dan dako ya shigo. Suka shiga ciki, Dan dako ya yi duba izuwa yarinyar da ta bude musu kofa, ya ganta yarinya ce shiryayya, mai kyakkyawar fuska, da kwarjini, da haiba tamkar jinjirin wata. Idanunta dara dara, farare tas, tamkar na barewa, fuskarta na haske, tamkar wata daren goma sha biyu.

Yayin da Dan dako ya ganta, sai hankalinsa ya tashi, kayan da ke bisa kansa suka yi kusan faduwa saboda kyan wannan yarinya da ya gani, ya ce a cikin ransa, “Da dai idaniyata ba ta taba ganin wani abu mai kyau da ya kai kyawun wannan yarinya ba.”
Yarinya, mai jiran kofa, ta ce, “Marabanku.” Suka tafi har suka isa ga wani daki yalwatacce, adantacce, mai wuraren zama da yawa. Suna shiga dakin, sai Dan dako ya ga wata yarinya kuma, tana kwance bisa wani gado na azurfa mai dan karen kyau. Gadon na rufe ne da rumfar zannuwan mirmir madaukaki, anyi musu ado da lu’u lu’u da jauhari. Wanna rumfar gado ba ta hana ganin wanda ya ke kwance a kan gadon ba.

Yayin da wannan yarinya ta kan gado ta ji shigowar Dan dako da Jekadiya mai siyo kaya, sai ta bude labulen gadon, ta fito. Idanunta tamkar raba, da fuska marinjayiya daga rana, mai haske, ka ce ita tana daga taurarin duniya. Dan dako yaga kyawun da bai taba ganin irinsa ba.

Tana saukowa daga kan gado, sai ta yi tafiya kadan, ta zauna a kan kujera, ta ce da wadda ta siyo kaya da kuma wadda ta bude kofa, “Ya kuka yi tsaye? Me kuke jira ne? Ku sauke kaya daga kan wannan miskini ku biya shi sallamarsa, ya tafi.”

Jekadiya ta zo ta gaban Dan dako ta rike kwandonsa, yarinya mai jiran kofa ta rike kwandon daga baya, ita kuma ta ukun, shugabarsu, ta taso ta rika musu daga tsakiya, suka sauke kayan daga kan Dan dako. Suka zube kaya, suka aje kowane ga muhallinsa, suka ba shi kwandonsa tare da dinari biyu. Suka ce da shi, “Ka fuskanta kan tafarkinka, ya kai wannan miskini.”

Dan dako ya yi dubi izuwa ga wadan nan yam mata guda uku, da abinda suke ciki na daga kyawo da dabi’o’i kyawawa, da dai bai ga kyawawa tamkarsu ba, amma babu maza a gare su. Ya duba abinda ke gare su na daga sha, da abin marmari, da abin maye, da wadansun wadannan, ya yi al’ajabi, gayar al’ajabi. Sai ya ki ya fita daga gidan.

Shugabar yan matan nan, wadda aka iske kwance bisa gado, ta ce, “Me ke gare ka, ya kai wannan miskini, da ba ka fita? Ko kudin dakon kayan sun yi maka kadan ne?” Ta waiwaya ga wadda ta siyo kayan, ta ce, “Ki kara masa dinari daya ya fita ya ba mu wuri.”

Dan dako ya ce, “Wallahi ya shugabata, kudin da kuka ba ni sun fi karfin jingar dakon da na yi muku, domin jingata rabin dirhami ce, amma ga shi kun ba ni har dinari biyu. Cewa ni, zuciyata ta shagala ne da farin cikin ganinku. Kuma ina cikin tunanin ya ya kuka kasance ku uku haka, kyawawa, amma babu maza a tare da ku, babu namiji daya mai debe muku kewa? Shin ko kun san rumfa bata tsayuwa face da akwai shishshiniya hudu? Ban ga hudun ba a gareku.”

Sai yan matan nan suka ce da shi, “Mu yam mata ne, muna tsoron kada mu ajiye asiri ga wurin da ba a kiyaye shi. Mu, mun karanta wakoki a cikin labarai, sun ce: ‘Kiyayi asiri da wanin asiri, kada ka ajiye a gare shi, wanda ya ajiye asirinsa ga wani abokin asiri, ya tozarta kansa'”.

Da dan dako ya ji jawabinsu, sai ya ce, “Ni, namiji ne, mahankalci, amintacce, na karatanta littattafai, munana da kyawawa, sun bayyana gareni, ni, mai bayyana alheri ne, mai boye mugunta, cewa asiri a gareni ya kasance a cikin daki kublalle, wanda mabudinsa ya bata kofar ta na rufe. Me zai hana ku barni na kasance tare da ku, in zama mai debe muku kewa, har zuwa wayewar gari?”

Ko da suka ji zancensa, da tsarinsa, suka ce da shi, “Kai ka sani, mu, muna da bukata da dukiya bisa ga wannan matsayi, ko kana da abinda za ka bamu? Mu ba mu barinka ka zauna garemu, sai in zaka bamu dukiya mai yawa, wanda kuma kai ba mu ga alamun kana da ita ba. Ko kana tsammanin haka nan zamu bari kana kallon fuskokinmu, kyawawa ba tare da ka bamu komai ba.”

Mai gidan ta ce, “Idan so ya kasance ba da dukiya ba, bai yi dai dai da kwayar kasa daya ba.” Mai jiran kofa ta ce, “In wani abu bai kasance a gareka ba, na daga dukiya, ka maraita, ba ka samun kome garemu.” Jekadiya, mai siyo kaya, ta ce, “Ya ‘yan uwana, mu rike shi a garemu, tunda ya zo garemu ya bayyana so, mu aje shi, ya rinka ba mu dariya. Idan kuwa ya fada ma waninsa sirrinmu, ransa ba zai yi tsawo ba, balle zama tare da mu.”

Dan dako ya yi murna, ya ce, “Wallahi ba ni da wani abu na daga kudi, wanda ya isa in gabace ku da shi.” Yam mata suka ce, “Zauna tare da mu, mun karba bisa ga kai da ido.”

Suka ci gaba da shan kayan shaye-shaye da tande-tande, suna hirar duniya, suna masu annushuwa da jin dadi. Ba su gushe ba cikin wannan yanayi har duhun dare ya shigo. Yam mata su ka ce da Dan dako, “Tashi ka fuskanta ya zuwa tafarkinka.” Dan dako ya ce, “Wallahi fitar rai ita ta fi sauki daga fitata wannan gida a cikin wannan dare.”

Suka ce, “Hala ba ka san ko gidan wane ne ba wannan?” Ya tambayesu ko gidan wa ne? Suka ce gidan Abal Mansur. Ya ce na gode da Allah ya sa na zama makwafinsa. Sai Jekadiya ta ce, “Na rantse da raina sai ku bar shi ya kwana a nan gidan, yayi barci a kan gadon da bai taba kwanta irinsa ba, mu na yi masa dariya, gobe da safe sai ya kama gabansa.”

Sauran yam mata suka ce da shi, “Za ka yarda ka kwana garemu bisa ga sharadi, ka yarda da umurninmu, kome ka gani, kada ka tambaya, kada ka nemi sababinsa.” Ya ce, na’am!

Suka ce, “Tashi ka karanta abin nan da ke rubuce a kofar gida!” Ya tashi zuwa ga kofa, ya iske rubutu bisa ga kofar gidan da ruwan zinariya da cewa, ‘Kada ka kula da abin da babu ruwanka, kada ka yi zance cikin sha’anin da ba naka ba, ka ji abin da ya yarda da kai, ka yi abin da aka sa ka’

Bayan Dan dako ya karanta rubutun nan, sai ya ce da su, “Ku shaida ni ba ni zance ga abin da bai shafe ni ba.” Yayin nan Jekadiya ta tashi ta dauko musu abinci, suka ci, suka kunna shama’a da itace, suka zauna cikin ci da sha. Daga nan sai suka ji ana kwankwasa kofa.

Ba su jima ba a cikin zamansu, sai mai jiran kofa ta tashi daga garesu zuwa ga kofa, yayin nan ta komo, ta ce da yan uwanta, “Ni, na iske a bakin kofa Ajamawa uku, masu ido daya-daya, kowane daya daga cikinsu ya aske gashin gemunsa da sajensa. Wannan al’amari ya na da ban mamaki, su mutane ne baki, sun sun ce sun fito ne daga wajen kasar Rum. Akwai ga kowanne dayansu kama da sura abar dariya. Idan ku ka amince su ka shigo, hakika za su nishadantar da mu da dariya.”

Mai jiran kofa, ba ta gushe ba ta na rudin sauran yam matan nan, har ta ce da su, “Mu bar su su shigo, amma mu shardanta musu kada su yi magana ga abin da babu ruwansu a ciki.” Saura suka amince. Ta koma ta shigo da su.

Bakin nan maza ne guda uku, halshensu na rawa ga zance, gashin bakinsu abin dariya, dukkansu suna da ido daya-daya, ko wane dayansu ya aske gemunsa. Suka shigo, suka yi sallama, suka jima su na tsaye, su na jiran izni. Yam mata suka zaunad da su. Mazajen nan uku suka ga Dan dako, da irin tufafin da yake sanye da su, suka ishe shi yana cikin maye. Suka ce da junansu, “Wannan talakka ne, dan uwammu, me ya kawo shi wurin wadannan kyawawan yan mata?”

Koda Dan dako ya ji wannan zance nasu, sai ya ce da su, ku zauna babu yawan magana, hala ba ku karanta abin da aka rubuta a bakin kofa ba?

Yam mata suka yi dariya, suka ce da junansu, mu yi dariya ga talakkawa da Dan dako duka, sun zama abin dariya. Yayin nan suka ajiye kabakin abinci ga talakkawan da Dan dako, suka ci suna zance. Mai jiran kofa na shayar da su abin sha. Yayin da kasko ya zaga tsakaninsu, Dan dako ya ce wa mazan nan uku, “Ya ‘yan uwana, shin ko akwai wata hikaya a gareku, koda daya, abar marmari da debe kewa ku zanta mana ita?”

Mai jiran kofa ta halarta musu da molo, Ba-Irakiyi, da gurmi, Ba-Ajamiyi. Bakin nan suka tashi, dayansu ya zauna bisa ga tambari, dayansu ya riki molo, dayansu ya riki gurmi, suka buga da launi mai tada hankulan ma su jinsa. Yam mata suka yi waka, da muryoyinsu masu dadi, suka daukaka sautinsu. Suna cikin wannan hali, na maye da annushuwa, sai suka ji ana kwankwasa kofa.

Mu hadu gobe domin kashi na 2002. HIKAYAR DAN DAKO DA YAM MATA

Yam mata da bakinsu, Dan dako da Samari uku masu ido daya-daya, sun rafkana cikin kida da waka, sai suka ji ana kwankwasa kofar gida. Yarinya Mai jiran kofa ta tashi domin duba me kwankwasa musu kofa cikin wannan dare.

Ashe masu kwankwasa kofar nan sun kasance Halifa Haruna Rashid da Wazirinsa Ja’afaru da sarkin fada Masrurus Siyafi. Ya kasance daga al’adar Halifa, ya juye siffa tasa, ya shiga gari domin ji da ganin abin da ke faruwa a tsakanin talakawansa.

A wannan daren ma, Halifa da Wazirinsa da Sarkin Fadansa, sun juye siffarsu, suna yawo cikin gari, sai tafarki ya kawo su a unguwar da gidan yan matan nan ya ke. Za su wuce ke nan sai suka ji ana kida da waka mai dadi a wannan gida, shi ne musabbabin kwankwasa kofar gidan.

Yayin da yarinya mai jiran kofa ta bude kofa sai ta ga mutane guda uku, tsaye a bakin kofar. Yayin nan Waziri Ja’afaru ya gabata, ya ce da ita, “Ya shugabata, mu fatake ne, matafiya, kwananmu goma cikin Bagadada muna siyar da kayan fataucinmu, mun sauka ne a dakin baki. Babban maigidanmu ne ya kirayemu a cikin wannan dare, ga wannan sa’a, ya yi mana iznin tafiya. Muka fito cikin daren nan, sai demuwa ta kama mu, muka mance hanyar masaukinmu. Muna so a cikin alherinku, ku saukar da mu wannan gida, mu kwana gare ku, ku samu ladarmu.”

Mai jiran kofa ta dubesu, ta gan su da siffar fatake, ta ce, “Ku jinkirta in sanar da ‘yan uwana!”

Ta shiga ta sanar da sauran yam mata akan wadan nan fatake. Suka ce, “Je ki, ki shigo da su.” Ta bude musu kofa, suka ce da ita, “Yalla mu shigo da yardarki?” Ta ce da su, “Ku shigo!” Halifa ya shiga da Ja’afaru da Masruru a halin suna a siffar fatake.

Yayin da yam mata suka gan su, kuma suka ga suna da almar dukiya a tare da su, sai suka tashi suka tare su da fara’a, suka gaishe su, suka girmama su. Suka ce, “Marhabin, maraba da bakinmu, mun yi murna da ganin ku, amma mu na da sharadi guda a wannan gida, kada ku yi magana a kan abin da babu ruwanku a ciki.” Su ka ce, “Na’am, mun amince da wannan sharadi.” Suka zauna, yam mata suka kawo musu abinci da abinsha.

Bayan sun zauna, sai Halifa yayi duba izuwa ga dan dako da samari uku, sai ya ga samarin nan uku duka ido daya-daya ke gare su, kuma duka na hagu ne. Ya yi al’ajabi a kan wannan abu. Ya yi duba izuwa yam mata uku da abin da ke gare su na kyawo da cikar halitta, ya dimauta, ya yi al’ajabi. Suka zauna cikin hira da zance. Yam mata suka zo wa Halifa da giya tatacciya, ya ce, “Ni Alhaji ne!” Ya tashi daga cikinsu.

Yarinya mai jiran kofa, ta tashi ta dauko tasa, zananniya, ta sa ruwa a cikinta, ta wanke ta sosai, ta zuba madara a ciki, ta diga ruwan sanyi ta garwaya shi da sukar ta rufe, ta dauko ta ajiye a gaban Halifa. Ya dauka ya sha, ya gode ma ta, ya ce a cikin ransa, “Babu makawa in saka wa wannan yarinya gobe bisa ga aikinta na alherin kyautatawa bako.” Yayin nan suka koma ga zancensu.

Yayin da dare ya kusa rabawa, sai shugabar yam matan nan ta tashi, ta rike hannun Jekadiya, ta ce da ita, “Ya ‘yar uwata, ki tashi bisa ga biyan bukatata, mu biya bukatarmu.” Ta ce, “Na’am, ya ‘yar uwata.” Yayin nan kuma Mai jiran kofa ta tashi, samari uku, masu ido daya, suka bi bayanta, ta na bayan shugaba, Jekadiya na gabansu. Suka mika tsakiyar gida, suka shiga cikin wani daki. Bayan sun shiga ciki, suka yi kiran Dan dako, suka ce da shi, “Kai ne na farko da zuwa a wannan gida, don haka kai ba bako ba ne.” Ya ce da su, “Me kuke so in yi muku?”

Sai suka nuna masa wasu karnuka guda biyu, daga babbakun karnai, da dagumi a wuyansu. Yam mata, suka ce da shi, “Ka taimaka mana ka jawo mana wadan nan karnuka zuwa tsakiyar dakin nan.” Dan dako ya rike su, ya shigo da su tsakiyar daki.

Shugabar yam mata ta tashi, ta zare damuttsanta, ta dauki bulala, ta ce da Dan dako, “Gabato mini da karya daya daga cikin karnukan.” Ya jawot a da daguminta, ya gabatar da ita. Karya na kuka, tana rauda kanta zuwa ga yarinya. Yarinya ta sabkar mata da duka. Karya na kuka tana kururuwa, ba ta gushe ba tana dukan ta, har damuttsanta suka gaji, yayin nan ta yar da bulala daga hannunta, ta rungume karya a kirjinta, tana shafe mata hawaye, tana sumbatarta.

Yayin nan ta ce da Dan dako, “Ka mayar da ita ka kawo ta biyun.” Ya zo da ita, ta aikata mata tamkar yadda ta aikata wa ta farko. Duk wannan abu ya faru a gaban samari uku da Halifa da Waziri da Sarkin Fada.

Zuciyar Halifa ta dimauta, kirjinsa ya kuntata da wannan abu da ya gani, ya kyibci Ja’afaru, ya tambaye ta dalilin aikata wannan abu. Ja’afaru ya yi masa ishara da tuni akan sharadin yam mata. Sai ya yi kawai.

Sai shugabar yam mata ta dubi yarinya Mai jiran kofa ta ce, “Ki tashi ga zuwa biyan bukatar ki.” Ta ce, “Na’am, ya ‘yar uwata.” Yayin nan shugabar yam mata, ta hau kan gadonta na marmar, jikinsa na dinari, kafafunsa na azurfa, ta ce wa yarinya Jekadiya, “Ku zo mini da abin da ke gareku.”

Mai jiran kofa ta hau bisa gadon daga gefenta. Jekadiya ta shiga cikin taska, ta dauko jaka ta handalas, koriya, ta tsaya gaba ga yarinya, shugabar yam mata, ta warware jaka ta fitar da molo daga cikinta, ta gyarta tsakiyarsa, ta kada molo, ta yi waka, waka mai dimauta zuciyar ma’abota bege.

Jekadiya na cikin rera wakarta ta soyayya, sai shaukin bege ya debi yarinya mai jiran kofa, ta tashi ta yayyaga tufafinta, ta fadi kasa somammiya. Yayin da jikinta ya yaye, Halifa ya gani a gare shi tabo na dukan bulala. Ya yi al’ajabi da haka, gayar al’ajabi.

Jekadiya ta tashi, ta dauko ruwa, ta yayyafa mata a fuska. Ta farka, ta kawo mata tufafi, ta tufasashsheta. Halifa ya juya ga Ja’afaru ya ce, “Ko ka lura da tabo na bugun bulala a jikin wannan yarinya? Ni bani da ikon na yi kawai a kan wannan al’amari, lalle ne mu tambaye su akan kasancewar wadan nan al’amurra.”

Ja’afaru ya ce, “Ya shugabana, sun shardanta mana a kan kada mu yi magana kan abin da babu ruwanmu a cikinsa, kuma mun amsa musu haka.”

Samarin nan uku, masu ido daya-daya, suka ce, “Kaiconmu, da ba mu shigo wannan gida ba, mun kwana a wurin kwananmu, hakika kwananmu a nan ya gurbata mu da masifar da tsatso ke yankewa a gare ta.”

Halifa ya waiwaya zuwa gare su, ya ce da su, “Don me haka?” Suka ce, “Zukatanmu sun dimauta, mun tsorata da wannan al’amari.”

Halifa ya ce, “A’aha, dama ku ba nan gidan kuke ba?” Suka ce, “A’a, muna zaton gidan wannan namiji ne.” Suka nuna Dan dako. Ya ce, “A’a, wallahi, da dai ban san wannan gida ba face yau da na yiwo dakon kaya, kaito, gwanda a ce na kwana bisa ga wutar tsire da a ce na kwana a cikin wannan gida.”

Duka suka ce, “Ga mu, mu maza bakwai, su mata uku, mu tambaye su bisa ga kasancewar halinsu, idan basu amsa mana da lallashi ba, su amsa mana dole.”

Suka taru su duka bisa ga wannan shawara, Ja’afaru ya ce, “Wannan hankali bai yi dai dai ba da mu tambayesu, domin mun yi musu alkawari ba za mu yi magana ba a kan abin da babu ruwanmu a cikinsa.”

Yayin nan ya kyibci Halifa, ya ce, “Dare bai saura ba face sa’a daya. Mu bari gobe mu hallara su a gabanka, ka tambaye su ga kissarsu.” Halifa ya ki, ya ce, “Ba ni da sauran hakuri ga tambayar labarinsu.”

Jayayya ta yawaita a tsakaninsu, yayin nan suka ce, wa zai tambayesu? Dayansu ya ce, Dan dako, shi muka fara iskewa a cikin gidan.

Da yam matan nan suka ji mutanen nan na ta jayayya, sai suka ce, “Ya ku jama’a zancen me kuke yi?” Dan dako ya tashi zuwa ga shugabar yam mata ya ce, “Ya shugabata, na roke ki domin Allah, na gama ki da shi, ki labarta mana ga halin karnuka biyun nan, da wane dalili ki ke azabtar da su, kuma ki koma ki yi kuka, ki sumbace su? Ki labarta mana dalilin tabon bulala da ke jikin wannan yarinya, da abin da ya sa idan ta ji waka sai ta fadi sumammiya. Wannan ita ce tambayarmu, wassalam!”

Yarinya, Shugabar yam mata ta dubi sauran mutanen nan ta ce, “Gaskiya ne wannan shi ne tambayarku?” Suka amsa mata da cewa, “Gaskiya ne mun yanke shawarar yi muku wannan tambaya, amma mutum daya ne bai amince da mu tambayeku ba, domin shi ba ya so ya karya alkawrin da ya yi daku.”

Yarinya ta ce, “To, ku kun cika alkawari ke nan? Haka muka yi da ku kafin ku shigo nan?” Suka ce, “Hakika ba mu iya hakuri a kan abin da
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment