Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina sonta"Adeeb ya kai karshen zancen sa cike da faduwar gaba,yana fatan Allah yasa su amince da batunsa.

Ajiyar zuciya suka sauke dukansu, hakika wannan batun yayi matuƙar daɗaɗa musu rai,domin Adeeb mutum ne wanda duk wasu iyaye zasuyi fatan ya kasance mijin ga yarsu,dan haka ta bangaren su Queen Suhaimat kam,ba wata matsala,dan kallon juna sukayi ita da mijinta cike da jin dadi,suna murmushi.

Abie ma abun yayi masa daÉ—i,saidai dole abawa yarinyar da iyayenta dama,idan sun amince da batun auren shikenan,sannan itama yarinyar sai sunji ta bakinta idan ta amince shikenan.
Amma ma taji daÉ—in maganar Adeeb sosai,domin ta jima tana fatan ace,inama Adeeb zai auri fattu,dan ta yaba da hankali da kuma nutsuwar fattu,saidai awancan lokacin ba damar fadin abinda ke cikin ranta.

Abie ne yayi murmushi cike da jin daÉ—i,kafin ya kalli Sultan Habeeb,ya fara magana"Sultan kaji abinda É—an nata ya faÉ—a ko,ina fatan dai zuciyarka tana irin tunani da fatan da nakeyi, dan haka ina jiran jin ta bakinka,kaida mai dakinka"

Murmushi uncle Habeeb yayi kafin yace "ai ranka shi dade,wannan abun yayi min daÉ—i fiye da yadda kake tsammani,dan haka mudai ba abinda zamuce, sai Allah ya haÉ—a kansu,ya basu zaman lafiya, sannan ya karesu daga dukkan sharrin abin ki"ya kai zancen sa fuskarsa É—auke da murmushi.
Wani irin sanyin daÉ—i ne ya ratsa zuciyar Adeeb, Alhamdullah shikenan iyayen fattu ma sun amince da aurensu, shikenan bashi da wata matsala.
Kallonshi ya kai ga fattu,amma bai sami damar hada ido da itaba,dan kanta na duke,murmushi yayi wato fattu irin matan nan ne masu,kunyar ,hmmm zama ta ware ne ,dan shikam wllh zagewa zaiyi ya koyar da ita salon soyayya kala -kala,dan shi mutum ne mai son soyayya daga matarsa.

Hamdala abie yayi kafin yace "tunda yanzu mu Dukansu mun amince da wannan auren,yana da kyau muji ta bakin yarinyar,dan kar'ashiga hakkinta,tunda bada saninta akayi auren ba.dan haka Ƴata karki cuci kanki,ki sanar dani shin kin amince da wannan auren ko kuwa?"abie ya faɗa yana mai kallon fattu,da fatan Allah yasa itama tace ta amince.

Fattu kuwa kunyar duniya ta gama cika mata ciki,ji take kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki,yanzu ta yaya zata amsa muce cewar tana son Hamma?tab !wllh bazata iyaba.
Gaba É—aya dakin yayi shiru,amsar fattu kawai ake jira,saidai ba alamun fattu zatace wani abu.
Ƙuri !!Adeeb ya kure fattu da ido,karfa Hulwa ta ki amincewa da aurensa?kai baya wannan tunanin, domin yasan Hulwa na sonsa sosai bazata taba kin zama dashi ba.dan haka kallonta yake danjin mezatace.

Ganin fattu ta kasa magana sai kara sunkuyar da kanta take,yasa ammi dafa kafadunta cikin murmushi tace "karki ji tsoro yata,ba wanda zaiyi miki dole,amsarki kawai ake bukata"nan ma dai shiru fattu tayi bata ce komai ba.kunya take ji sosai.
Ajiyar zuciya abie yayi kafin yace "to alamu dai sun nuna Fatima bata amince da wannan auren ba,dan haka habeebee dole kayi hakuri ka sawwake mata"abie ya faÉ—a yana kallon fattu dan ganin yanayinta.
Aikuwa da sauri ta É—ago kai tana zaro ido waje,cikin muryarta mai kama da shagwaba tace "a'a Abie nifa bance bana sonshi ba,dan Allah karkasa ya sakeni,na amince Nima Ina sonshi"fattu ta faÉ—a cike da kuruciyarta, idonta akan Adeeb.
Gaba daya saida ta basu dariya,dan dai kawai suna cikin alhinin rashin Zulaihat ne, ya hana su darawa.amma saida suka murmusa.
Ajiyar zuciya Adeeb yayi yana mai kafeta da ido,sosai yake jin tana kara shiga cikin zuciyarsa.

Koda su Sultan zasu koma Ghana,sun bukaci tafiya da fattu, domin ta gana da yan uwanta,sannan ta dan saba dasu,amma ba jimawa zatayi ba tunda da aurenta.

Adeeb ji yayi kamar ya kwalla ihu, dan yasan zai sha wahala zama ba tare da fattu ba,amma ba yadda ya iya dole ya amince,akan idan komai yayi daidai, zaizo sai su wuce Nigeria wajen baffa.
Queen suhaimat kuwa tayi hakanne,dan tana son ta gyara yarta sosai,yadda zata kara martaba agurin Adeeb.
Cikin yanayi na gajiyar jiki da zuciya,ga tarin kewar fattu da Adeeb ya fara tun yanzu,ya mike tare da cewa"Anty bari muje dan ta shirya kayanta"ya faÉ—a yana kallon fattu,fuska amarairaice.

Kallonsa fattu ma keyi,cike da tausayinsa,dakuma kewarsa,amma dole tabi iyayenta,dan kuwa tana bukatar jin duminsu ajikinta,sannan tana son ta san yan uwanta.

Queen suhaimat ce ta kalli fattu tace "Zara kije ki shirya kayanki maza "ta fada tana shafa kan diyar Tata cike da so da ƙauna.

Mikewa fattu tayi,cike da kunya,tabi bayan Adeeb dan tuni yayi gaba.

Tana fita ta ganshi ya jingina bayansa da jikin bango,idanunsa alumshe.tana zuwa ta tsaya akusa dashi,tare da sanya hannu ta rike hannunsa.ahanakli ya buÉ—e idonsa tare da saukewa akan kyakykyawar fuskarta.baice komai ba ya rike hannun nata suka nufi part dinsa.

Suna shiga ya janyota jikinsa ya rungume tsam.ahankali yake sauke ajiyar zuciya,idanunsa alumshe.fattu ma lumshe ido tayi cike da jin tsananin so da kaunar Adeeb cikin zuciyarta.

Ahankali ya fara magana"Hulwa komai yazo ƙarshe,Allah ya bayyana mana azzalumai,mun ganesu, yanzu lokacine da nake bukatar kulawar ki da soyayya,saidai kuma gashi zakiyi nisa dani, alokacin da nake tsananin bukatarki kusa dani,Hulwa zanyi kewarki sosai"Adeeb ya faɗa cike da jin kewar fattu sosai yana kara kankameta ajikinsa.

Cike da tausayi fattu tace"Hamma nima fa zanyi kewarka, amma ai ba dadewa zanyi ba,ina son zama tare da iyayena,dan inji dadin da ake ji idan ana tare da su.amma Hamma zanyi kewarka sosai"itama ta faɗa ahankali tana mai ƙara kwantar da kanta cikin faffadan kirjinsa.

Sun jima ahaka,rungume da juna,Adeeb yana ta saukewa fattuhadda, wanda har bata san lokacin da ta biye masa ba itama,duk abinda yayi mata, itama shi take masa.basu rabu da juna ba har saida Adeeb ya samu nutsuwa sosai.kafin suka daure suka rabu da jikin juna,sai lokacin fattu ta fahimci ko kaya babu ajikinsu.kunya ce ta kamata,da sauri ta janyo bargo ta rufe jikinta tare da lumshe idonta.

Murmushi Adeeb yayi yana mai gyara mata gashin kanta daya barbaje,kafin yace "Hulwa meye kuma na rufe ido?nifa bana son wanna kunyar taki,Please ki buÉ—e ido ki kalleni,kinji?"ya faÉ—a yana hura mata iska akan idanunta.
Cikin wani irin salon murya mai cike da nishadin soyayya tace "Hamma Ni wllh kunya nakeji,kayi ta gane min jiki"ta faÉ—a ahankali tana rungumeshi.

Rungumeta shima yayi cike da soyayya kafin yace "hulwata idan ban kalli jikin ba,jikin wa zan kalla?jikinki mallakina ne,shine abinda zan kalla ya debemin kewa dan Allah karki hanani kallon abinda ke sani nutsuwa" ya faÉ—a cikin salon sa na shagwaba yana É—an turo baki.

Murmushi fattu tayi tana mai kara cusa kanta akirjinsa,cike da kaunarsa.
Gaba daya sun shagala da nunawa juna soyayya,sun manta da su, Sultan Habib dake jiran fattu,saida wayar Adeeb tayi kara sannan suka farga,kiran Abie ne dan haka cike da kasala ya mika hannu ya daga wayar,
"To Abie gamunan "kawai ya faÉ—a tare da kallon fattu yace "Hulwa su anty na jiranmu"ya fada kamar zaiyi kuka.

Da sauri fattu ta mike tana zaro ido,wllh sam ta ma manta da batun tafiya Ghana,gaba É—aya Hamma ya mantar da ita komai da soyayyarsa.
Shagwabe fuska tayi tana mai faÉ—in"Hamma kaga kasa na manta da su inna suna jirana ko?"ta fada tana nufar toilet da sauri tana tafe tana bubbuga kafa,ciki da tabara.
Lumshe ido Adeeb yayi yana mai faÉ—in "wayyo hulwata,zaki kasheni da salonki"kafin ya bita toilet din,wanka sukayi tare sannan suka fito,da kansa ya shirya fattu,kafin ya haÉ—a mata kayan da yasan zata bukata,sannan suka fito.

Haka Adeeb da Hulwa suka rabu cike da kewar juna,Adeeb ji yake kamar yayi kuka.

Tunda fattu ta tafi Ghana,kullum sai su wuni suna waya da Adeeb,sosai yake nuna mata yadda yayi kewarta,ita kuwa tausayinsa duk ya gama kamata,ba abinda yake son ji da gani sama dashi.saidai tayi tararrashinsa,tun tana kunyar fada masa kalamai harta zo ta daina,take zagewa tana nuna masa soyayya.

Ba irin gatan da fattu bata ganiba,agurin iyaye da danginta,kowa sonta yake,yana riritata,gyara kuwa tunda suka zo innarta ke fama,an tsuma fattu sosai,ta yadda da kanta wataran take jin tana bukatar Adeeb akusa da ita.
Tayi kyau jikinta ya kara gogewa,kallo É—aya zaka mata kasan tana cikin jin dadi da annashuwa,komai yaji ajikinta.

Satinta biyu a ghana Adeeb ya kasa daurewa ya shirya kayansa yace ya tafi Ghana.
Amagarkama kuwa,lamarin ammi ya gwabe sosai,dan kuwa zuwa yanzu bai zama lallai ka gane ta ba,wasu abubuwa take tamkar na mahaukata,tayi ta ihu kenan tana faɗin irin abubuwan da ta aikata,ƙafarta ɗaya ta lalace sakamakon ciwon da taji,banda wasu irin kuraje da suke fito mata masu tsananin karni da doyi.haka zatayi ta ihu tana yagunin jikinta.duk wanda yazo inda take,da gyar yake iya tserewa dan kuwa hauka take sosai,tana dukan mutane.hakan yasa aka kulle gurinta,saidai atura mata abinci ta kasan kofa.

Waziri kuwa,an yanke masa hukumcin daurin shekaru arba'in agidan yari, yayi nadama sosai kullum cikin kuka yake da neman gafara.

Rashad kuwa zuwa yanzu jiki alhamdullah,dan sosai yaji sauki walwalarsa ta dawo, Amma ma hankalinta ya kwanta sosai take kula da abie,abin sai godiyar Allah.

Ranar da Adeeb ya sanar da zuwansa Ghana,ba ƙaramin farin ciki fattu tayi ba,murna sosai takeyi har saida innarta ta fahimta,shiri akayi mata na musamman,cikin shiga irin ta ya'yan sarakuna, tayi matukar kyau kamar kasace ta ka gudu,sai ƙamshi take zubawa,gashi tadanyi kina kwanin sha'awa.

Wani kayataccen daki aka sauki Adeeb,ko ina yayi fes sai ƙamshi ke tashi,an jere masa kayan ciye- ciye,amma ko ruwa ya kasa sha,burinsa kawai yayi tozali da hulwarsa.

Wani sihirtaccen kamshine ya bugi hancinsa,wanda ya sanya shi saurin É—ago kai,cikin hanzari ya mike tsaye tare da kafe fattu da lumsassun idanunsa,wadanda ke cike da tarin gajiya da bukatar fattun tare da kewarta.

Murmushi take sakar masa cike da shaukin ganinsa.tana takawa kamar wata tarwada.

Cikin wani irin salo da zaƙuwa Adeeb ya bude mata hannayensa,alamun ta taho gareshi,da sauri ta ƙaraso tare da fadawa jikinsa,shikuma ya mayar da hannunsa ya rungumeta tsammm.


Muje zuwa masu karatu.

Mrs babi ce💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment
More typing.
29/08/2022, 11:11 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJI NE🪱🪱🪱


Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚



Free book

Page 91/92






_____________Cikin wani irin salo wanda ke nuna tsantsar farin ciki da zaƙuwa,Adeeb ya bude hannayensa,alamun fattu ta taho gareshi.
Da sauri fattu ta ƙaraso gareshi,cikin takunta mai jan hankali,tare da fadawa jikinsa tana murmushi.
Maida hannunsa yayi ya kulle tare da rungume fattu tsamm,ajikinsa.

Atare suka sauke ajiyar zuciya,wacce ke nuna tsantsar kewar juna da sukayi.
Banda ajiyar zuciya ba abinda Adeeb ke saukewa,kamar wanda yayi wasan tsere.
Ahankali cikin murya mai tattare da shauki yace "I miss You so much Hulwa"ya faÉ—a yana kare matseta akirjinsa,kamar zai maidata cikinsa.
Kusan minti biyar suka dauka ahaka,kafin Adeeb yayi karfin halin ɗago da fattu daga jikinsa yana kallon kyakykyawar fuskarta.gani yake kamar ba fattunsa ba,kamar wanda aka sauya masa ita,tayi kyau matuka,ta kara gogewa kai kace acikin ƙanƙara tare rayuwa.

Fattu ma kallonsa take cike da jin zazzafar kaunarsa na ratsa jini da tsokarta,dan gani tayi yayi mata kyau sosai,ya ɗanyi kiba kaɗan ya kara fari,ga sajen da ya kara ajiye wa yayi matuƙar ƙawata fuskarsa.

Ahankali ta kai hannunta tare da shafa gefen fuskarsa,lumshe ido yayi yana mai jin sanyi cikin ransa.cike da son nunawa Adeeb yadda tayi kewarsa ta kai bakinta kan nashi,ta fara kissing dinsa,kawai sai jin bakin fattu yayi cikin nashi.

Ai kamar mayen karfe haka Adeeb ya karbe lips din fattu ya fara sha kamar ya sami lollipop.
Tun abun yana karami har yazama babba,dan sun kasa rabuwa da juna,ganin suna neman faduwa ne yasa su zubewa akan lafiyayyar kujerar dake kusa dasu.adeeb bai bar wannan dama ba ,saida ya kara angoncewa, sosai ya shiga ruÉ—u da gigita,É—an jin fattu yayi kamar bai taba ma saninta matsayin ya mace ba,sosai ya nishadantu da ni'imarta,ya rikice mata sosai haka yayi ta sunbatu yana hawaye.albarka kuwa fattu ta shata ba adadi da kyaututtuka kala kala.
Saida suka sami nutsuwa kafin Adeeb ya samu yaci abinci.anan dakin sukayi wanka tare,gaba É—aya Adeeb ya kara kwarewa fattu,ko yaya tayi motsi hankalinsa na kanta,wani irin so yake mata marar misaltuwa.fattu duk da taji zafi amma haka ta daure bata nunawa Adeeb raki ba.nan suka shantake suna nunawa juna so da kauna,dama tuni Adeeb ya mika gaisuwa ga Sultan Habib da innar fattu.
Dan haka salla ma acikin dakin nan yakeyinta. Fattu kuwa ranar ta yabawa aya zaƙinta,dan ta tabbatar da cewar Adeeb yayi kewarta,kuma shidin jarumi ne na gaske.

Washe gari suka tashi daga Ghana zuwa Nigeria,da tareeÆ™ akayi tafiyar,dan dama tare suka zo da Adeeb,shiya sauka a masauki na daban.
Kai tsaye a Jos suka sauka,kafin suka nufi kauyen su fattu cikin dalla dallan motocinsu.
fattu da Adeeb cikin mota daya suke,yana rungume da ita ajikinsa,motar su ce agaba,ko kaÉ—an fattu bata manta hanyar kauyen nasu ba,dan haka tana lura da inda suke nufa.

Sai motar Sultan Habib shida innar fattu dasu zayyad.

Kauyen yana nan inda fattu ta sanshi, ba abinda ya sauya.gidansu ta fara hangowa,cike da doki take nunawa Adeeb gidan"Hamma ga gidanmu can,yanzu zanga baffana,Hamma bazan iya kwatanta irin farin cikin da nake ciki ba"fattu ta faÉ—a tana rike hannun Adeeb cike da murna idanunta ya cika da kwalla.
Murmushi yayi,dan shima saiya tsinci kansa cikin farin ciki, ganin yadda Hulwarsa ke farin ciki.
"Nima ina farin ciki Hulwa zataga baffanta,saidai anya kuwa zai gane ki?Adeeb ya faÉ—a yana kallonta da murmushi.
Cikin doki da dariya fattu tace "wllh zai ganeni,ko me nazama na tabbata baffana zai ganeni kuma zaka gani"ta fada daidai lokacin da sukayi facking akofar gidansu fattu.

Da hanzari fattu ta buÉ—e kofar motar ta fito,bata ko tsaya sauraron Adeeb ba,burinta kawai tayi tozali da baffa.da sallama ta shiga cikin gidan tana rarraba ido dan ganin ta inda zataga baffanta.
Ba kowa cikin tsakar gidan,gaba É—aya gidan yayi datti,ko ina kazantace cikinsa.jin sallama yasa gwogwgo hansai fitowa daga cikin dakinta,tana ta soshe soshen kwarkwata.
"Waye yau agidan nan nawa?rabon da naji wani yazo gidan nan,harna manta,kodai Hau......maganar gwogwgo hansai ta makale sakamakon ganin wata balarabiyar yarinya da tayi tsaye fuskarta É—auke da murmushi.
Cikin rawar jiki gwogwgo hansai ta fara fadin"maraba lalle baiwar Allah,daga ina?wa kike nema kodai gidan mai gari kike nema?"gwogwgo hansai ta fada cikin rawar jiki tana kallon fattu.

Dariya fattu tayi tana kallon gwogwgo Hansai,duk ta rame tayi baki sosai gashi ta tsufa,kallo É—aya zakayi mata kasan tana cikin wahalar rayuwa.
"Gwogwgo,baki ganeni ba ?nice fa,nice fattun baffa"fattu ta faÉ—a tana kama hannun gwogwgo Hansai ba tare da gyama ba.
Galala gwogwgo tayi tana kallon fattu,cike da ƙaryata abinda fattun ta fada,saidai kuma wa yasan fattun awani guri?bare yazo yayi mata wasa.cikin rawar murya tace "fa....t.t.tu,kece haka ?kece kika zama kamar balarabi?ina kika je kika zama mai kudi haka?ta fada tana shashshafa fattu.
Dariya fattu tayi kafin tace" nice gwogwgo tare muke da iyayena fa da hammana,suna waje bari nace su shigo,wai ina baffana ne tunda na shigo nake nemansa"fattu ta faÉ—a cike da doki tana nufar waje.

Lokacin da ta fita atsaye ta tarar da itayenta da Adeeb,mutanen garin sun zagayesu suna kallonsu da shafa motar da suka fito daga ciki.
Bata damu da mutanen gurinba tacewa su Adeeb su shigo.
Murna take sosai kamar wacce akayiwa bushara da gidan aljanna.

Gwogwgo Hansai jiki na rawa ta shimfida musu wata rubabbiyar tabarmar kaba.ko kaÉ—an basu nuna mata gyamaba suka zauna.
Bayan gaishe gaishene, gwogwgo tayi ta kuka tana bawa fattu hakuri,itadai fattu burinta daya taji ina baffanta yake.
Nan gwogwgo Hansai ta sanar da ita duk abinda ya faru da baffa,ranar da suka bar garin.
Kuka sosai fattu ta sanya,tana jin wani irin kunci cikin zuciyarta,ina zata ga baffa?mutumin daya tallafi rayuwarta ,ya bata kulawa,wayyo Allah.haka fattu tayi ta kuka,ajikin Adeeb yana rarrashinta.
Gwogwgo Hansai cikin nadama take faÉ—in"bayan tafiyar malam,gaba É—aya lamari ya lalace garin nan,kowa abinda yake so shi yakeyi,haka inaji ina gani,yarana mata sukayi cikin shege,yanzu haka bansan duniyar da suka shiga ba,shima namijin tuni ya zama rikakken barawo,yayiwa yar mutane fyade shine ya gudu,ya bar rugar nan.mai gari yana nan ya zama gurgu,jauro kuwa abarsa ta lalace har yanzu bata da amfani,haka haroji yana na da fuska kamar ta dodo,saidai yaje Bara cikin gari,dan Allah fattu ki yafe mana ,nasan hakkinkine ke bibiyarmu"gwogwgo Hansai ta fada cikin kuka.
Haushin ta sosai Adeeb yakeji,dan yasan kadan daga cikin mugayen halayenta.
Tashi sukayi domin barin rugar,dan bawani amfanin zamansu,tunda wanda suka zo gurinsa baya nan.

Kudi mai yawa sultan habib ya bawa gwogwgo hansai,sai murna take tana godiya,haka ya tabawa mutanen kauyen ma kafin suka bar garin.

Kuka sosai fattu keyi ajikin Adeeb,ta shiga damuwa mai tarin yawa,haka yayi ta rarrashinta,har suka iso cikin garin jos.

Wata babbar motace tayi faci akan tsakiyar kwalta,hakan ya haddasa go slow agurin,suna tsaye cikin mota,masu bara sai zuwa suke suna Bara.
Wani dattijone cikin shiga ta almajirai,kallo É—aya zakayi masa kasan yana shan wahala yazo jikin motar su fattu yana Bara,kasancewar gilas din motar irin mai duhun nan ne,yasa na waje baya ganin na ciki.

Fattu ce tayi firgigit tatashi daga jikin Adeeb tana kallon tsohon dake barar.
Wani dan ihu ta sanya tana mai ƙoƙarin buɗe kofar motar.kira take
"Hamma baffana,baffana"tana faÉ—a cikin rawar jiki tana kokarin buÉ—e motar.
Da sauri shima Adeeb ya kai kallonsa inda fattun ke nuna masa.
Tabbas baffa ne kuwa.gana É—aya fattu ta rikice tana kici kici buÉ—e kofar Amma tsabar farin ciki tama kasa,budewar sai kira take"baffana,baffana"
Hannunta Adeeb ya riko yace "ki nutsu hulwa,karkije kiki ciwo kinji bari muje gurin baffan"ya faÉ—a yana bude kofar motar.
Da sauri fattu ta fito daga cikin motar ta nufi gurin mutumin da yayi dan gaba dan zuwa wajen wata motar ya sami sadaka.
Da sauri ta kamo hannunsa tana faÉ—in "baffana kaine,haka ?"cikin azama baffa ya juyo sakamakon jin Muryar da akullum saiyayi kukan rashin ta,kuma duk kuÉ—in da yake samu na bara tarawa yake,dan yayi ta zaga garuruwa yana neman fattu,yasan watarana zasu hadu.
Jifa yayi da dan buhun dake hannunsa,wanda yake tara kudin barartasa ciki.
"Fattu,kece"baffa ya faÉ—a cike da shauki.
Kuka fattu keyi tana kallon baffa,kafin ta rungumeshi ajikinta tana kuka.shima baffa kuka yake cike da godewa Allah,yau gashi ga fattunsa,shikenan burinsa ya cika.
Sultan habib,da innar fatyu ma,fitowa sukayi,dan kobasu tambaya ba,sunsan wanna shine baffan fattunsu.
Adeeb kansa saida yaji kwalla ta cika masa ido,dan tausayin tsohon da yadda ya koma.

Horn din da motoci ke musu ne ya dawo dasu cikin hayyacinsu,dan tuni an janye motar data haddasa go slow É—in,dan haka cikin hanzari suka shige mota dan ba mutane hanya.
Motar su fattu baffa ya shiga,su Sultan ma suka koma cikin tasu ,sannan suka bar gurin.

Kai tsaye gidan da suka sauka suka koma,dan yau suke don komawa Ghana,
Fattu sai murna take daga ga baffanta.
Wanka kawai suka bari baffa yayi,aka bashi wasu kayan ya sanya,kafin suka daga sai Ghana....

Masu karatu bari muyi musu rakiya zuwa ghanar muma.



Ina kuke
Masoya anty mammy?

Albishirinku,ina mai farin cikin sanar daku,sabon littafina mai suna RAINON DAWA,yana nan akan hanya,da zarar mun kammala MACIJINE,hmmmm
Daga jin sunan kinsan ba magana.

Karku bari abaku labari.
Ga mai bukata ,zai iya biyan kudinsa tun yanzu,domin nan da kwana uku zaku fara samun wannan kayataccen labarin na RAINON DAWA.

akan fashi mai sauki,

Normal group 300

Special group 500

Sannan akwai manyan mata dake son atura musu private to kuma ga naku farashi,1000
Dan haka saina jiku,

Acc. No.
Saratu kabir
A.u.b
2215749011


Saiku nuna shadar biya ta wannan no.
08148360851


Saina jiku,masoya.

Show ne your love akan novel É—i Nan,
ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°ðŸ¥°

Mrs babi ce💘💘
29/08/2022, 11:11 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJI NE🪱🪱🪱


Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚


Free book

Page 93/94





_______________Ko a cikin jirgi fattu na kusa da baffanta,wanda yayi tsuru cike da tsoron jirgin,dan kuwa wannan shine karon farko daya hau jirgi.amma haka fattu ke kwantar masa da hankali har suka ƙarasa Ghana.
Part guda aka warewa baffa wanda ke dauke da duk wani kayan more rayuwa.baffa ya cika da farin cikin ganin irin rayuwar jin dadin da fattunsa keyi.abinci kala kala aka ajiye masa,har yama rasa wanda zaici.haka fattu keta zuba masa abincin tana tura masa.

Saida ya huta sosai nutsuwarta ta dawo jikinsa, sannan aka taru apart din da aka saukeshi, har Sultan Habib.godiya suka farayiwa baffa,bisa irin taimakon da yayiwa rayuwar yarsu,sannan suka ce suna bukatar yayi zamansa anan gurinsu,tunda bashi da kowa acan Nigeria.
Kuka kawai baffa keyi na gani yadda bayin Allah nan ke karramashi, suna son ya kasance tare dasu,amma wadanda ya taso cikinsu,haka suka koreshi korar kare bayan sun karbe masa dukiya.
Fattu ce ta dan turo baki tana kallon innarta da mahaifinta,kafin tace "Ni gaskiya ban yarda baffana ya zauna anan ba,tare zamu tafi dashi can gida,bana son yayi nesa dani,kuma shima yafi son zama kusa da fattunsa ko baffa"fattu ta faÉ—a cikin salon shagwabarta.

Murmushi baffa yayi,yace kwarai kuwa fattun baffa,duk inda kike to Nima Ina can koda kuwa cikin dokar dajine"baffa ya faÉ—a cikin murmushi.
Dariya sukayi suma,kafin mahaifin fattu yace "wato dai zara kin kwace mana baffanki ko?"ya faÉ—a da murmushi akan fuskarsa.
Dariya fattu tayi kafin tace "Allah ba haka bane daddy nayi kewar baffana,kuma nima inason in kula dashi,kamar yadda ya kula da rayuwata abaya"
Jinjina kai sukayi gaba É—aya,suna ayyana irin kaunar dake tsakanin fattu da baffanta.

Kafin su bar kasar Ghana saida mahaifin fattu ya mallaka wa baffa kanfaninsa na ƙera takalma da jakunkuna,ya maida sunan sa akan takardun kamfanin,sannan ya bashi gida,wanda idan yazo zai rinka sauka aciki sannan ya damkawa fattu takardun gida dana kamfanin,harda mukullin sabuwar mota yar yayi.
Kuka sosai baffa yayi yana godiya,fattu ma tayi matukar murna sosai.adeeb kam godiya yayiwa Sultan habeeb,haka innar fattuma ba'a barta abaya ba,dinkuna ta sanya aka yiwa baffa,na gani na faÉ—a, masu kyau da tsada.sosai baffa ke yaba karamcin iyayen fattu,ba abinda zaice saidai Allah ya saka musu da aljanna.

Washe gari kuwa jirginsu ya daga zuwa Misra,fattu harda kukan rabuwa da yan uwanta,haka innarta ta cika ta da kayan gyara kala kala.
Wani ƙayataccen bangare su fattu suka sauka,wanda bayan tafiyarta Ghana ,Adeeb sanya aka kera musu.tsyawa fadar irin tsaruwar da bangaren yayi abune mai matukar wahala.kallo daya zakayiwa gurin kasan an kashe kudade makudai.

Baffama bangare guda aka ware masa inda zai zauna.haka yasha kyaututtukan gurin iyalan Adeeb,sannan shima Adeeb ya ba baffa kanfaninsa na motoci,baffa neman zaucewa yayi da irin wannan kyautukan da ake ta bashi.
Sosai ake girmama baffa cikin fadar,dan kowa yasan shidin waye.
Cikin lokaci kalilan baffa ya wanke yayi fes dashi,masha Allah kyakykyawan bafillatani,yayi kiba ya koma Alhaji sosai.ba jimawa suka shirya shida Adeeb da fattu dasu nanny sukaje suka sauke farali.
Sun dawo da kwana uku aka shirya gagarumin taron nadin Adeeb matsayin sarki.sannan ranar za'a gudanar da bikinsu shida fattu.
Anyi taro na ban mamaki wanda saida ya girgiza duniya,taron daya hada sarakunan hasashe daban daban,daga turawa,larabawa zuwa hausawa,ba kalar mutanen da babu agurin.
Taro yayi taro,an nada Adeeb matsayin sarkin misra,SULTAN ADEEB MUHAMMAD ASHRAF.
haka aka kammala taro ya tashi lafiya,kuma ranar Adeeb ya mallaka fattu dankareriyar mota mai shegen tsada da kyau,sannan ya mallaka mata kamfaninsa wanda ake hada mayukan shafawa na mata da kayan kwalliya.
Murna dai agurin fattu ba'a cewa komai.

Sati biyu da nada Adeeb matsayin Sarki,fattu ta kama laulayi, wayyo kuzo kuga murna gurin bayin Allah nan,haka nanny ta zage tana kula da fattu,ita da amma,suna bata gata da kulawa sosai,haka uban gayya,dan har kuka yayi lokacin da labarin cikin fattu ya sameshi.kuma yayi mata alƙawarin idan ta haihu ta zabi inda take son zuwa yin karatu.

Cikin fattu nada wata biyar aka yi auren tareeÆ™ da wata yar uwarsa,rana daya aka daura auren dana Rashad,anyi biki na kece raini,su fattu sune akan komai na biki, zakuyi mamaki yadda fattu ta zama babbar mace,tayi mugun kyau har ta gaji,suna nunawa juna soyayya mai tsafta ita da Adeeb,yayin da suke rainon cikinsu cike da so da kauna.saidai fattu tana da girman ciki,dan yanzu haka inka ganta zaki tunanin cikin yakai wajen watanni bakwai, dan girmansa.

Komai yana tafiya daidai arayuwarsu fattu,basu da wata matsala yanzu,domin suna cikin aminci da kulawar yan uwa,sarauniya suhaimat da Sultan habeeb,sunyi matukar murna da samun cikin fattu,addu'oi kuwa,ba irin wanda fattu bata samu,domin takanas ake biyawamutane makka,dan suke suyi mata addu'a.

Lokacin da cikin fattu ya cika wata tara,ko tashi bata iyayi da kanta,saidai idan Adeeb ya tasheta idan tana zaune ko kwance,amma kasancewarta mai hakuri da kawaici,haka take daurewa tana nuna bata jin wahalar ciki,shikuwa Adeeb tausaya mata yake sosai.
Wata rana da safe suna barci nakuda ta kama fattu,aikuwa,nan da nan likitoci kwarraru,wadanda ke mata awo suka rufu akanta,cikin hikimar ubangiji,fattu ta haifi yaranta takwaye, mace dana miji masu matuƙar kama da Adeeb, kyakykyawa na ban mamaki.

Irin murnar da ahalin nan suka nuna abin ba'a cewa komai,ta ko ina zuwa ake ganin jarirai,ranar suna aka sanya musu sunan baffa dana Nazli,Abubakar,amma ana kiransu da Ameer da ameera.
Fattu ta sami alkairi sosai haihuwar yaran nan.dan motoci ma sun sami sama da guda sha biyar,banda gidaje da

Please Login or Register in order to submit comment