Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa surutu,ashe dama tana da surutu haka?yanzu ta sake dashi sosai,kuma ya fuskanci idan suna tare sam bata fiye lura da wasu abubuwan da zata gani taji tsoroba.

Dai dai nan suka kawo wajen ajiye motoci,kafin su karasa saiga tareeƙ ya fito daga cikin wata rantsatstsiyar mota Black,mai baƙin gilasai,motace yar ubansu wacce kana gani kasan anyi barin kuɗin agurinta.
Bude musu motar yayi yana ɗan satar kallon fattu,wai zuƙi haka yarinyar take dama,gaskiya yana fatan Allah yasa wanan alherin da suka ƙalla karya kunce .

Harararta Adeeb yayi cikin jin haushi yadda ya kafawa fattu idanu yace " to yi da gaske ka cinyeta" ya faɗa cikin harshen larabci yana hararar tareeƙ .

Dan sosa kai tareeƙ yayi yana murmushi,azuciyarsa yana faɗin lallai yallaɓai irin wannan kishi haka kiri-ƙiri?hmmmmm .


Shiga motar sukayi fattu na ta kallon yadda motar take wani sukuf da ita ,kamar siffar wani kwaron,
Kallon Adeeb tayi wanda ya jingina kansa da jikin kujera as usual idanunsa alumshe.
"Hamma wai a wannan duniyar da mukazo, acikin kwarya ake yawo ne?"ta faɗa tana mai riƙe haɓa.

Idonsa daya ya buɗe tare da kallon ta ,yana rasa mai zai ce mata dan takaice wai motace ƙwaro,kai fattu sai gyaran Allah.
Ganin yayi shiru ta kuma cewa "Hamma yanzu kuma wace duniyar zamu?"
Kai Adeeb ya dafe cike da gajiya surutu yace " duniyar cinye mutane masu surutu" ya faɗa yana harararta.

Allah Sarki fattu dagalo!!tayi tana kallonsa cikin mutuwar jiki ,kafin ahankali ta ɗan matsa kusa dashi tare da kamo hannun rigarsa ta rike tayi kalar tausayi sosai ,ashe duk murnar da take dama duniyar cinye mutane zasu koma,?shikenan bazata ƙara ganin baffanta ba?
Ahankali tace "Hamma baffa....

"Hihhhhhhhh" Adeeb ya fada yana mai ɗora danyatsarsa akan bakin fattu,sannan ya kwanto da kanta zuwa kafaɗarsa.

Kwanciya tayi lamo cike da tunani kala kala aranta .

Tafiya sukayi mai ɗan nisa kafin naga sunzo gaban wani irin makeken gida mai matukar girma da ƙasa,girman gidan yayi haɗa anguwanni manya guda uku,get suka nufa ,suna idan akaga tareeƙ sai abude masa cikin girmamawa,ba wanda ya kula da Adeeb dake bayan motar,dan glass ɗin bakinsa sosai.

Saida suka wuce manyan get bakwai ,kafin suka nufi wani get mai matukar kyau da girma,wani irin walwali get ɗin keyi kai kace da zallar kwal akayishi.

Daga samansa kuma wasu danjojine masu ruwan kwal ke rubuta,

Well come to the King palace cikin manyan baki.

Ahankali get din ya buɗe bayan wata doguwar na'ura ta danno kai ta haske ko ina cikin motar .
"Yallaɓai mun karaso" tareeƙ ya faɗa yana ɗan juyowa kadan.

Shiru Adeeb yayi yana mai jin wani irin kewa da damuwa azuciyarsa." Tareeƙ how long na dauka ba'asan inda nake ba?Adeeb ya tambaya cikin sanyin murya.

"Yallaɓai 5 months 3days" tareeƙ ya faɗa cikin jimami.

Runtse idanu Adeeb yayi tare da budewa ,da sauri kuma ya yunƙura tare da dauke kan fattu daga kafaɗunsa,wacce tayi lamo kamar mai barci tsoro duk ya gama cika mata ciki.

Fitowa yayi daga motar kafin ya fara takawa cikin nutsuwa da jin kewar iyayensa.
Da sauri fattu ta fito daga mota ita ta riga da gudu tabi bayan Adeeb,Allah yasa flat shoe ne akafarta.saurin kamo gefen hiraminsa tayi ta riƙe gan cikin hannunta.yana jinta baice mata komai ba ,har suka kai bakin ƙofar.

Ahankali ya nuna fuskarsa jikin wani dan madubi,wani dogon layine naga yana zagaye fuskar tashi,kafin kofar ta buɗe da kanta,yana sanya kafa cikin wani tafkeken falo ,naji wata murya ta dauki
Magana," Well come home prince Adeeb Muhammad Ashraf ,your hinest you have a big surprise to see "

Masu karatu fattu fa gaba ɗaya ta tsure da ganin irin duniyar da suka shigo,wani irin mahaukacin falone ,wanda ta ko ina matsalar benece acikinsa, ga wani dan banzan sanyi da ƙamshi dake dukan hancin ta.nan da nan jikinta ya kama rawa.
Ta rike hannun Adeeb gam-gam cikin nata.

Kamo hannun nata yayi tare da kanta zuwa cikin tsakiyar falon,wanda da gyar fattu ke taka ƙafarta dan wani irin kaishi da taji a ƙasa dakin.
Zaunar da ita yayi yana mai kallonta,
"Ki zauna anan, za'a shigo dake yanzu."
Adeeb ya faɗa yana mai kallon yadda jikinta ke tsuma.

Hannunsa ta kara damkewa kafin tace "Hamma tsoro nakeji sosai" ta faɗa cikin rawar murya.

Hannun nata ya kama ahankali ya kai bakinsa ya sunbata, kafin ya shafa gefen fuskarta ,yace kijirani kinji " yana faɗin haka yabi matakalar dake tsakiyar falon yayi sama.
Kallo fattu tabishi dashi cike da tsantsar tsoron wannan guri.hawayene ya zubo mata sharrrrr!! Daga idanunta,ahankali ta sanya hannu ta share wahayen .

Shikuwa Adeeb wani haɗaɗden part ɗin naga ya nufa asaman,hadimaine birjik farfajiyar gurin kowa da abinda yake ,tafiya yake cikin sauri da sassafar,ba abinda yake so da buri illa yayi ido hudu da abinsa.wata baiwa ce ta ankare da Adeeb,cikin hanzari ta zube ƙasa tana faɗin
Takawarka lafiya ,dan sarki jikan sarki,yarima mai jiran gado,alherin Allah ya kai maka.
Da sauri duka suka ankare da abinda baiwar nanke fadi,cikin azama da tsantsar farin ciki sauran ma suka zube ƙasa suna kwasar gaisu da murnar ganin Adeeb,ba wanda Adeeb ya kula kai tsaye dakin mahaifinsa ya nufa.
Ahankali ya buɗe kofar cikin sanyin murya yayi sallama.
Wani farin Balarabe dattijone kwance akan wani lafiyayyen gado irin na sarakuna masu ji da kansu,gefensa kuma wani likita ne ke ƙoƙarin daura masa ruwa ahannunsa,
Sai wani mata guda biyu dattijai, sunsha ado da gwala-gwalai na alfarma ,ko wacce tana inbakiyi bani guri,
Sai wani farin matashi zaune kusa da dattijon nan,ya riƙe hannunsa.

Cikin azama dattijon ya wani zabura tare da sauƙowa daga kan gadon yana mai goge idanunsa,kafin cikin rawar murya yace " habeebee Adeeb "
Ya faɗa tana nuna gofar dakin ,inda Adeeb ke tsaye ,cikin shaukin ganin mahaifin nashi.

Gaba dayan yan dakin ne suka biyo suna kallon ƙofar dakin,aikuwa Adeeb ne ya dawo,prince Adeeb ya dawo gida.

Da gudu Adeeb ya karaso cikin dakin tare da rungume dattijon nan ajikinsa tsantsan yana mai faɗin," habeebe rurh cikin kuka"
Shima kuka kawai dattijon nan yasa tare da ƙanƙame Adeeb ajikinsa.

Matan nan kuwa kallon kallo naga sun fara cikin rudewa da shiga kokwanto.



Masu karatu muje zuwa yau dai ga fattu cikin gidan sarautar Masar,koya zata kasance?


Ga kuma Adeeb jikin mahaifinsa .
Sai mun hade next page.

Anty mammynku ce

Mrs babi💘💘💘

Share and comment fisabilillah

More comment
More typing.
29/08/2022, 10:56 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄


MACIJI NE🪱🪱🪱




Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚




Free book

Page 35/36





_______________Kallon- kallo naga matan nan nayi atsakaninsu, ko wacce tana jifar ƴar uwarta da mugun kallo, yayi da zuciyoyinsu ke buga cike da mamaki .

" Habeebee ina kashiga? Me yasami rayuwarka? Na shiga damu matuƙa lokacin da muka wayi gari an nemeka anrasa ba ƙasashen da bamu zagaye ba wajen nemanka, na sanya ƙudede, kadarori,dama kanfanunuwa na ga duk wanda ya kawo min koda labarin in da kake ne,amma bamu sami komai da ya shafeka ba,meke faruwa habeebee?"dattijon nan ya faɗa yana mai shafa fuskar Adeeb hawaye na zuba daga idanunsa.
Ahankali Adeeb ya kamo hannun mahaifin nashi ,tare da sumbatar hannunsa ,sannan yace " abie wasu abubuwan basu buƙatar afadesu,saidai kawai mubarsu cikin zuciyarmu, sannan muyi ta kallon azzaluman dake neman ganin bayanmu da bakin halinsu." Adeeb ya faɗa yana mai kallon daya daga cikin matan dake tsaye aɗakin.
Kallone irin na duk abinda kike aikatawa akaina, na sani kuma ki kiyaye ranar haduwarmu.

Ahankali naga matar cikin ruɗewa da irin kallon da Adeeb ke mata,ta sanya gefen mayafin dake kanta tana goge zufa daga goshinta ,kanta a ƙasa.

Ita kuwa ɗayar mata cikin sassarfa ta karaso gaban Adeeb ,hannu tasa akan kumatunsa tana shafawa, hawaye ya gama wanke mata fuska.
"Hayatee nayi kewarka fiye da yadda zan fadamaka, naji daɗi da Allah ya kuɓutar dakai daga sharrin mahassada" matar ta faɗa cikin kuka tana mai rungume Adeeb.

" Ammina" Adeeb ya faɗa cikin wata irin murya mai cike da kewa ,yana mai rungume matar daya kira da amminsa.

Matashinnan kuwa gaba daya ya haɗe fuska ,ba alamun fara'a ko murnar dawowar Adeeb gida atare dashi.zamu iya cewa ma bakin ciki yake da ganin Adeeb ɗin.

Zama sukayi abakin gadon ,shida mahaifin nashi,fuskokinsu dauke da mafificin farin ciki da ɗauki ganin juna.
" Habeebee ka bani labarin abinda ya faru" mahaifinsa ya faɗa yana mai kwantar da kan Adeeb ɗin akan cinyarsa.
Kwanciya Adeeb yayi tare da kamo hannun mahaifin nashi kafin yace " abie ,zan baka labarin komai daya sameni ,amma yanzu baka da lafiya ka huta kayi barci abie na" Adeeb ya faɗa yana sumbatar hannun mahaifin nashi.

Dariyar farin ciki abie yayi tare da shafa kan Adeeb yace " ai naji sauki yanzu kam ,wanda yayi silar kamuwa da cutar yazo ya bani magani,bana jin ciwon komai habeebee likita ,zaka iya tafiya" abie ya faɗa yana mai kallon likitan cikin fara'a .

Godiya likitan yayi cikin garmamawa ,yana mai taya sarki murnar dawowar Adeeb ɗin gida,dan kowa yasan da batun bacewar Adeeb ɗin.
Dubawa nayi cikin dakin naga ya rage daga sarki sai Adeeb da ammi,amma ɗayar matar da saurayin nan tuni sun bar ɗakin.

Fattu kuwa tana nan zaune afalon wannan matar ta sauko daga saman sarki cikin wani irin yanayi ,dan ko lura da fattu batayi ba, sai ƙoƙarin kiran waya take .

Ba jimawa kuma,saiga wannan kyakyakywan saurayin shima ya fito cikin fushi da bacin rai,kallonsa fattu keyi taba dan hango yanayin kama da sukayi da Adeeb,saidai ko kama ƙafar kyan Adeeb baiyi ba.

Harya gota inda fattu ke zaune ,sai kuma ya dawo da sauri ya tsaya akanta.
Fattu kuwa da sauri ta mike tsaye tana kallonsa.ganin irin yadda ya tsaya mata akai ƙerere.
Shikuwa saurayin nan mai suna,Rashad ,wani irin. Shegen kallo yake bin fattu dashi,tunda ga sama har kasa,wow wannan kayan fa ?daga ina haka?ya faɗa cikin zuciyarsa yana mai kashewa fattu idanu.
Haɗe fuska fattu tayi tana mai turo baki tare da kawar da kanta gefe.

"Hi babe !" Rashad ya faɗa yana mai ƙoƙarin kamo hannun fattu.
Da sauri fattu tayi baya tana mai turo baki tare da biye hannunta abayanta.
Murmushin gefen baki yayi tare da shafa gefen fuskar fattu yace " yanzu ina cikin hanzari amma zan nemeki,dan kin kwanta araina kuma yawuna ya tsinke" ya faɗa yana mai wucewa bayan ya sunbaci hannun daya taɓa fuskar fattu dashi.
Duk zancen da yake da larabci yake yinsa,dan haka ba abinda fattu ta fahimta cikin zancen nasa.taɓe baki tayi tare da binsa da harara , tana faɗin" Allah ya isa taɓa min fuska da kayi" ta faɗa afili tana mai murguda baki,sannan ta koma ta zauna.

Tana nan zaune shiru -shiru agurin nan ,tunanin take ko ina Hamma ya shiga ya barta anan?karfa taje tana zaune kawai taji anfara yankan naman jikinta,ga shegen sanyin falon duk ya isheta.

Wani irin ƙamshine ya doki hancin fattu,cikin sauri ta lumshe idanunta tare da budewa tana mai kallon ta inda tajiyo ƙamshin,
Masha Allah,wata kyakyakywar budurwace mai tsananin kyau da gayu,taci ado da wata doguwar riga baƙa ,mai tsayin gaske ,dan saida wasu yammata kusa su shida dake Binta abaya suka riƙe kasan rigar,gaba daya wuyanta da hannunta hatta gashin kanta anyi masa ado ne da kwal,tayi kyau matukar gaske,kallo daya zakayi mata kasan tana cikin farin ciki,dan kuwa sai murmushi take,tana tafiya ɗas-ɗas cikin salo da yanga.
Kallonta kawai fattu keyi cike da tunanin wannan ɗin ko wacece?amma gaskiya ƴar gayuce ta gaske,nima nan gaba irin wannan kwalliyar zan riƙayi inji ta yanga abina.fattu ta faɗa cike da murmushi tana kallon budurwar.

Ita kuwa budurwa tana karasowa tsakiyar falon ,idonta ya sauƙa akan fattu,dammmm !taji gabanta ya faɗi, wannan ɗin kuma wacece?daga ina haka?me takeyi acikin babban falo?budurwar ta faɗa cikin zuciyarta ,tana mai jin wani irin tsabar fattu cikin zuciyarta,dan saitaga duk yadda take taƙama da kyau wannan yarinyar tafita,saidai kawai tafi wannan wayewa da sanin duniya.

Kallon -kallo aka fara tsakanin fattu da wannan budurwa,ba abinda ya ƙara batawa budurwar nan rai irin yadda fattu ta tsareta da ido,wato ko shakkar ta ma batayi.

Cikin takunta na isa da rangwada ta ƙarasa gurin da Fattun ke zaune,
Kallon wulaƙanci take yiwa fattu tana wani yamutse fuska.

" Wacece ke?
Budurwar ta faɗa cikin harshen larabci.
Kallonta fattu tayi ba tare da tace komai ba,dan bata san me take cewa ba.

Ran budurwar ne ya ɓaci sosai,hannu tasa tare da fizgo fattu ta kama kwalar rigarta, cikin isa da gadara take faɗin" ke kinsan komi wacece ina miki magana kika shareni?ke ƴar uban waye marar kunya?"budurwar ta sake faɗa cikin fushi,
Fattu kuwa cikin jin zafin abinda budurwar tayi mata ta ballawa budurwar harara tare da ture hannun budurwar daga wuyanta,tana mai murguda baki.

Gaba daya hadiman da suka taki budurwar nan zato ido sukayi,cikin tsoro da tausaya wa fattu ,dan ta tabka babban kuskure.

Zato ido budurwar tayi itama tana mai kallon fattu ," kee!!! Ni kika turewa hannu?lallai minti babban kuskure.budurwar ta faɗa tana mai ɗauke fattu da wani lafiyayyen mari, kafin fattu da gama dawowa cikin hayyacinta ta sake jin wani zazzafan marin a dayan kumatunta.

Wani irin azabar raɗaɗine ya ziyarci fuskar fattu,cikin hanzari ta dafe duka kumatunta tana kallon budurwar nan,nan da nan zuciyar ƴaƴan Fulani ta motsowa fattu, ai batasan lokacin data ɗaga hannu itama ta shararawa budurwar nan matuka har biyu ba.......


Manage please my fans,
Wllh am seek.

Mrs babi ce💘💘💘
29/08/2022, 10:56 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJI NE🪱🪱🪱



Na mammy kabeer (anty mammy)



Elegant online writers📚📚



Free book

Page 37/38




https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




________________cike da zallar madarar mamaki budurwar nan ke kallon fattu,tunda take arayuwarta ba wani mahaluƙin daya taɓa daga hannu da sunann ya faɗa mata koda baƙar magana ne, amma wai yau itace tsaye gaban wata kucakar yarinya,sannan agaban bayinta ,dafe da kunci,wai da sunan an sharara mata maruka har biyu?
Lallai wannan yau ko ƴar gidan uban waye saita gane kurenta, zata san cewa ni Zulaihat nafi ƙarfin awulaƙantani ,kuma azauna lafiya.
Gaba ɗaya barorin gimbiya Zulaihat atsorace suke ,kuma kawunansu sunkuye a ƙasa, yayin da zuciyoyinsu ke bugawa cikin tsoro da fargabar abinda zai biyo baya.

Fattu kuwa tana tsaye riƙe da ƙugu,ta ƙurawa gimbiya Zulaihat idanu,kamar yadda itama ke kallon fattun,lokaci ɗaya fattu taji mugun tsabar Zulaihat cikin zuciyarta,haka kawai zata wani daga hannu ta dallamin uban mari?ai wllh saidai acinyeni agidan nan,amma idan wannan banzar tayi min abu saina rama dan ba tsoronta nakeji ba ehe.fattu ke wannan zancen ,cikin zuciyarta tare da murguda baki bayan ta kammala zancen zucinta.

H
Ahargitse gimbiya Zulaihat ta fara juye-juye ,can ta hango wani ƙarin flower vase na tangaran,da hanzari tayi gurin da tare da rarumoshi tayi kan fattu tana huci.
Tsorone ya gama kama fattu,yanzu idan ta jibga mata wannan ƙaton abun akai ,ai wllh sai kanta yayi raga-raga,tab yaseen bazata tsaya ba.baya fattu ta farayi cikin tsoro tana mai kallon gimbiya Zulaihat,
Ita kuwa gimbiya zulaihat ganin fattu na ƙoƙarin gudawa yasa ta dakawa hadimanta tsawa akan su riƙe mata fattu,wani irin zafi takeji cikin zuciyarta,wllh zata iya kashe fattu yadda takejin tsanar fattun cikin ranta,dan haka tayi rantsuwa yau saita illata fattu,ta yadda ko hannunta bazai ƙara moruwa ba,bare ta sake gigin marin wani.
Cikin azama kuwa suka tsakumi fattu suka riƙe ta,ihu fattu ta fara cike da tsoron abinda matar nan zata mata," wayyo Allah na Hamma kazo, zasu cinyeni danya da raina ,wayyo hammana!wayyo Hamma kana ina!! Fattu ta faɗa cikin ihu,lokacin da tajita ahannun waɗannan manyan yan matan masu shegen ƙarfi.

Zulaihat kuwa cikin rashin imani da tsana take faɗin,"wllh yau saikin komi wacece ,kin siya babban kuskuren taɓa Zulaihat,kuma yau zaki girbi abinda kika shuka" Zulaihat ta faɗa cikin fushi tana daga wannan flower vase ɗin da iya ƙarfi ta zata sakarwa fattu.

"Zulaihaaaatttttt!!!!" Aka kwalla kiran sunan gimbiya Zulaihat din ,cikin wani irin sauti mai ƙarfin gaske ,wanda saida dukansu suka tsorata .

Afirgice Zulaihat ta saki flower vase ɗin nan daga hannunta ya fadi ƙasa.
Ba kowa bane yayi mata wannan bahagon kiran face Adeeb ,wanda ya fito ne dan shigowa da fattu gurin mai martaba,lokacin ya gama basu labarin irin taimakon da fattu da baffanta sukayi masa ,da kuma dalilin tahowa da ita nan ɗin .shine mai martaba yace ya shigo da ita ciki.
Dama kuma yana zaune ne ,amma zuciyarsa tana can gurin fattu,dan yasan ta da shegen tsoro,abu kaɗan ne zai firgitata.
Dan haka cikin sauri yake tafi lokacin daya fito daga part ɗin sarki,
Yana doso babban farko kuwa ya fara jin ihuj fattu tana kiran sunansa.dan haka da gudunsa ya ƙaraso cikin falon,yana zuwa idanunsa sukayi masa mummunan gani,Zulaihat na ƙoƙarin illata masa Hulwa.

Cike da tsoro bayin nan suka saki fattu tare da zubewa kasa suna gaida Adeeb.
Wani shegen kallo da Adeeb ya watsa musune yasasu ficewa daga falon da gudu cike da tsantsar tsoro .

Fattu kuwa da gudu ta nufi Adeeb tana kuka,cikin sauri shima yake saukowa daga matakalar benen, uku -uku,hurhuɗu yake tsallake step din, atsakiya falon suka hade da fattu,tana zuwa ta faɗa ƙirjinsa tare da ƙanƙame shi tana kuka."Hamma mutafi daga gidan nan,tsoro nakeji,wannan matar muguwace daga zuwa ta ta mareni har sau biyu,kuma tasa wadancan doyoyin suka rikeni wai zata baremin kai" fattu ke faɗin haka cikin kuka tana kwance akan ƙirjin Adeeb.

Wani irin tausayin fattu ne yake mamaye ilahirin jikin Adeeb,tare da tsantsar jin haushin Zulaihat cikin ransa.
Ahankali yake shafa bayan fattu yana shiiiiiiiii da bakinsa alamun rarrashi.

Idanunsa sun kada sunyi mugun jaaaa ya kafesu akan fuskar Zulaihat,wacce tayi mutuwar tsaye tana kallon wannan yarinyar kwance akan ƙirjin Adeeb,wanda ita bata taɓa samun wannan damar ba.banda bugawa ba abinda zuciyarta keyi,lallai akwai gagarumar matsala,wacece wannan yarinyar?meye alaƙarta da Adeeb?
Cikin daukewar tunani da tsananin kishi daya rufewazulaihat idanu,kunsan matan larabawa da bakin kishi,Zulaihat ta nufi kansu Adeeb gadan -gadan.tana zuwa ta sanya hannu tare da ƙoƙarin fizge fattu daga jikin Adeeb.

Wasu zafafan marukane guda biyu suka sami gurbin zama akan fuskar Zulaihat ɗin,wanda sun fitowa daga hannun Adeeb.
Kusan minti biyu Zulaihat ta dauka kafin ji da ganinta sudawo daidai.

Ihu ta kurma cikin azaba tana mai dafe kumatunta" habeebee nika mara?akan wannan jakar?wacece ita?meye alaƙarka da ita ? Da har zata kwanta akan ƙirjinsa,kaikuwa kana rarrashinta?Zulaihat ta faɗa cikin kuka da rikicewa.

Wani matsiyacin kallo Adeeb yayi mata, yana mai gyarawa fattu kwanciyarta akan ƙirjinsa kafin yace " ita ɗin mutumce mai matukar muhimmanci arayuwata,mafi kusanci da zuciyata wacce zan iya aikata komai akanta,ki kiyaye nan gaba,hukuncin da zan miki bazaiyiwa kowa daɗi ba " Adeeb ya faɗa cikin wata iriyar murya mai kama da ta basasa,yana mai nuna Zulaihat da hannunsa.

Cikin karawa kukanta ƙarfi Zulaihat tace" kana nufin harni,tafini muhimmanci agareka?" Ta faɗa cikin ruɗu.
Wani banzan kallo Adeeb ya wurgawa Zulaihat kafin yace " ke wacece?wane matsayi kike dashi agareni,karki ƙara haɗa kanki da Hulwa banza shashasha marar zuciya da kamun kai " Adeeb ya fada yana mai juyawa da fattu suka fara tafiya zuwa sama.

Cikin kuka kamar zata shiɗe Zulaihat tace " wacece ita"

Saida sukayi taku kusan uku ,kafin Adeeb ya juyo cikin murtukakkiyar fuskarsa yace " MATA TACE ita" ya faɗa yana mai tsare Zulaihat da idanu.
Wani wasan ihu Zulaihat ta kwalla tare da ficewa da gudu ta nufi waje.

Harara Adeeb ya bita dashi kafin ya juya suka ci gaba da tafiya ,duk abinda suka faɗa fattu batasani ba, dan da Yaren larabci sukayi maganarsu.

Saida sukaje bakin ƙofar part ɗin sarki sannan Adeeb ya tsaya tare da gogewa fattu hawayenta.yace "kinga duk kin bata kwalliyarki da hawaye, kiyi shiru zamuje gurin abie ne yanzu kinji?karki damu bazata ƙara yi miki komai ba"ya faɗa yana mai riƙe kumatunta.
Kallonsa fattu keyi tare da shagwabe fuska tace " Hamma Ni tsoro nakeji"
"Ba abinda zai sameki ,bagani ba?" Ya faɗa yana kama hannunta suka shiga dakin abie.

Zulaihat kuwa tana ficewa daga falon,kai tsaye mota taje ta shiga tana kuka kamar ranta zai fice,da mugun gudu take tafiya hatta bar cikin masarautar ,kai tsaye wani hotel ta nufa tana zuwa dama akwai dakin dake amazaunin nata cikin hotel ɗin.

Fridge ta buɗe tare da ɗauko wata kwalba ta buɗe cikin sauri tare da kafa kai ,saida ta shanye abinda ke ciki tass kafin ta jefar da kwalbar. Waya ta dauka tare da kiran wata number tace tana jira.

Ko minti biyar ba'ayin saiga wani saurayi kyakyakywa ya shigo ɗakin ,yana zuwa lokacin harta fara fita daga hayyacinta ,tana surutai," saina kasheta ,saina ranta da yarimana ,nawa ne Ni kadai.
Rungume saurayin tayi suka fara aikata alfasharsu,subhanallah,Zulaihat Allah ya shirya.

Adeeb kuwa suna shiga dakin abie ,fattu ta kama gefen rigarsa ta rike gan! Cikin hannunta .ammi ce ta ƙaraso tare da kamo hannun fattu tana murmushi tace "ƴata yar albarka sannu kinji" ammi ta faɗa tana mai rungume fattu.
Abie ma murmushi taye yana mai kallon fattu ,lokaci ɗaya yaji yarinyar ta kwanta masa arai tana da hankali da nutsuwa.

Nan ammi tace agurinta fattu zata zauna ,ita zata kula da ita ,sannan zata taya Adeeb cigiyar mahaifan fattun.

Bayan sati guda Sarki ya hada wani gagarumin taro na farin cikin dawowar babban dansa magajin faɗa,wanda aka gayyato sarakuna daga kasashe daban -daban.

Kuma nan da kwana biyu taron zai gudana,dan haka gyara ake yiwa masarautar sosai.ko ina ka kalla an gyara shi yayi mugun kyau,

Adeeb kuwa shima yanzu ya shiga busy,yana ɗan bin kamfanoninsa na kasashe daban -daban yana duba yadda harkokin ke tafiya,dan haka yau kwana hudu baya gida .kuma basu hadu da fattu ba .
Gaba ɗaya fattu ta shiga damuwa,kullum tana cikin dakinta da aka bata mai shehun kyau,saidai akawo mata abinci taci ,tayi wanka ta kwanta.
Ko falo baya fita.itama ammi gaba ɗaya bata zama tana ta uzuri.
Gashi bata ita tare su ba,Gara ammi wataran takan dan yi mata Hausa kadan kadan.

Yau dai fattu tana zaune shiru ,tace bari ta fito falo dan yasan huta kuma ta duba Hammana.

Tana sanye da doguwar riga milk mai fadi kanta yanke da mayafin rigar,ba kwalliya akan fuskarta amma tayi kyau sosai.

Falon ta fito tana binsa da kallo,ya hadu iyakar hafuwa, sai ƙamshi ke tashi ta ko ina.
Tana ɗan zagayenta afalon ,taji anbude kofa.
Juyawa tayi ɗan ganin waye ya shigo,
Rashad ne ya shigo ɗakin shida zulaihat.suna tafe suna dan magana ,da alama kuma rarraba jin Zulaihat ɗin yake.
Turus suka tsaya suna kallon -kallo atsakaninsu su ukun.
Ita dai fattu kallonsu take tana tunanin,dama wannan matar agidan nan take ?tun ranar bata sake ganinta ba,sannan
Kuma ta gane wannan. Saurayin,shine wanda ya taba mata kumatu awancan ɗakin,dan haka da sauri fattu ta kawar da kanta gefe tare da hade fuska, nemar guri tayi ta zauna akan lumtsuma luntsuman kujerun da suka yiwa falon ƙawanya.

"Kai !!Rashad me wannan fitsararriyar keyi anan?aikuwa wllh saina koya mata hankali"Zulaihat ta faɗa tana ƙoƙarin ƙarasawa kusa da fattu.
Da sauri Rashad ya riko hannunta yana mai faɗin "haba -haba ke matsala ta dake gaggawa ,ba yanzu muka gama magana dake ba,zaki taimakeni,nima zan taimakeki, cikin sauƙin kowa ya sami abinda yake so.
Idan kika yi wani abu yanzu ,to shirin mu ga zai wargaje,kuma kinsan wancan horon bashi da sauƙi ko kaɗan.ba dai jini ne za'ayi taron nan ba? Rashad ya faɗa yana mai sakin wani shegen murmushi.
Jinjina kai Zulaihat tayi tana mai hararar fattu.

Cigaba Rashad yayi da maganarsa"to ki kwantar da hankalinki, ranar zamu aiwatar da ƙudirinmu akanta ,zamu tarwatsa koma menene ke tsakaninsu,Ni sam na kasa gane inda ammi ta dosa ,bata bamu goyon baya kamar yadda ya kamata,amma zamuiyi komai da kanmu.
Kedai kawai ki danne zuciyarki akan komai har zuwa jibin"

Rashad ya faɗa cike da ƙarfafawa Zulaihat gwuiwa.
Jinjina kai tayi cikin murmushi tace " nasanka nasan halinka,kuma zaka iya Allah ya nuna mana lokaci, amma wllh na tsani yarinyar nan sosai acikin raina" Zulaihat ta faɗa tana hararar fattu.

Fattu kuwa murguda mata baki tayi itama tana mai cewa cikin ranta" oho dai saidai kiyi ta hararata amma wllh baki isa ki doke in gyaleki ba ,ba ruwana da wani kin girmeni ehe" fattu ta faɗa tana mai dan dukan cinyarta har saida ƙaran ya fito sukaji.

Kallonta sukayi gaba dayansu ,Zulaihat tace ka "gani ko dukda batasan me muke cewa ba,amma kalli abinda take ?wllh daka barni na tattara yarinyar nan,ai Prince baya gida bare yace wani abu"Zulaihat ta faɗa cikin muryar bacin rai.
"No karki fara,ko baya gida yanzu ai kinsan zai dawo ko?kuma ma gaskiya bazan bari ki taba min kayana ba,dan gaskiya ina hango hutu agurin man sosai " Rashad ya faɗa yana wani kashe ido tare da kallon fattu.

" Wllh Ni haushi ma kake bani

Please Login or Register in order to submit comment