Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

!hulwa!!amma bata ko motsaba,ajiye ta yayi tare da bude fridge ya dauko ruwa mai sanyi yana yayyafa mata.amma bata ko motsaba ,wai wannan suman na menene haka?duka duka yaushema ta dawo hayyacinta ne ?gashi yanzu ta ƙara suka.
Huci kawai yake yana kallon fuskarta,zuciyarsa kamar zata fasa ƙirjinsa ta fito,sam baya ƙaunar ganin fattu cikin wani mugun yanayi,waima menene yayi silar wannan suman nata ne?kallon dakin yayi yana mai jinjina kai ,ba shakka tayi arba da yadda dakin nan ke sauyawa ne,wani irin runtse idanunsa yayi tare da dafe kansa,duk laifinane dana fita da ita da duk haka bata faru ba.bude idanunsa yayi wanda suka juye zuwa na macizai sak, ahankali jikinsa ya kama wata irin girgiza yana hayaƙi,kan kace me saiga ɗakin ya turnuƙe da hayaƙi, kusan minti biyar dakin yana wanann yanayi hayaƙi da wata irin ƙara,kafin hayaƙi ya baje, saiga wani murtukeken maciji mai girman gaske ya fasa kai yana huci.
Cikin tafiyar macizai macijin nan ya fara sauƙa daga kan gadon ,bangon dakin ya kama tare da fara lauye jikin wanan haɗaɗdun labulayen yana nannadesu tare da fesa musu wani irin ruwa daga bakinsa,da zaran ya fesa ruwan sai kaga labulen yana hayaƙi tare da murmushewa, haka yayi tayi saida ya bata gaba dayan labulayenan sannan ya fara bugun kwayayen dakin dake bada hasken nan mai ban sha'awa da jelarsa.tas saida ya gama fashesu, sannan ya nufi kan gadon,yana zuwa ya hau kan cikin fattu dake kwance ,cikin halin suma,zagayeta ya farayi tare da shigewa ciki rigarta sosai,yana goga mata sanyin dake jikinsa.

Aikuwa sanyin yana fara ratsa fattu ,ta fara bude idanunta ahankali,tana mai dafe kanta tare da yamutse fuska.
Abu taji yana fitowa sululu daga cikin rigarta,da sauri ta tashi zaune tana mai daga rigarta sama,daidai lokacin shikuwa macijin ya gama fitowa daga jikin nata.
Saƙare fattu tayi tana kallon macijin cike da tsantsar mamaki,shima macijin kallonta yake ido cikin ido.

Masu karatu meke faruwa ne?
Wannan macijin kuma waye?

Shin Adeeb dama bai daina zama macijin ba?

Muje zuwa takuce anty mammy

Mrs babi💘💘💘

Share and comment
Fisabilillah.

More comments
More typing.
29/08/2022, 10:53 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJI NE🪱🪱🪱



Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚
https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din👆ðŸ½

Free book

Page 31/32





_________________Saƙare,fattu tayi tana kallon macijin cike da tsantsar mamaki, kamar yadda macijin ke kallon fattu shima ido cikin ido.

Ahankali fattu ta lumshe idonta,tana mai ambaton sunan Allah,abin da ya bata mamaki shine,sam bataji tsoroba, saima bin jikin macijin da tayi da kallo,tabbas wannan macijin ta ne na yar ruga, kenan hakan na nufin Hammanta ne ya ƙara zama maciji? innalillahi ,yanzu yazatayi kenan?awane matsayin take idan bai dawo mutum ba?
Ahankali ta furta "Hammana" hawaye na zubowa daga cikin idanunta.

Shikuwa macijin yana ganin hawayen nan nata,ya taho zuwa gareta,yana zuwa ya hau kan cinyarta tare da nannaÉ—e jikinsa ya É—ora kansa akan kafaÉ—unta.

Lumshe ido fattu tayi cikin kuka tace " dan Allah HAMMA karka zauna cikin wannan yanayin,bazan iya rayuwa Ni kadai cikin wannan gidan mai aljanu ba, dazuma saida Hulwarka tazo ta tsoratani, gaba daya ta sanja duniyar wannan dakin ,ya koma wata kala,kalli kagani yanzu yadda ya koma,Hamma inajin tsoro"fattu ta faÉ—a tare da É—ora hannunta akan macijin tana shafawa.
Dagowa macijin yayi tare da zuba mata idanu,itama kallonsa take hawaye na zubowa daga idanunta. Jikinta ya fara zagayewa yana yana nannaÉ—eta,kafin kuma yayi baya da ita akan gadon,kwanciya fattu tayi tare da runtse idanunta .
Ita kam tariga ta gama sallama wa rayuwa, tasan idan har macijinta bai dawo mutum ba to mutuwa zatayi, ahalin da ake ciki yanzu tana jinsa ne har cikin ranta,kome takeyi shi take gani,ba abinda take bukata akullum kamar tajita kusa dashi,ta san duk ransa wani ya ganshi matsayin maciji ,to za'ayi ƙoƙarin kashe mata shine,wanda tayi imanin duk randa aka kashe Hamma, to tabbas da gawarsa za'a binnesu.

Shikuwa maciji bayan ya kwantar da fattu saiya zare jikinsa daga nannaɗetan da yayi,sannan ya kamo bargon dake kan gadon ya lullaba ajikin fattu,duk abinda yake kallonsa fattu keyi cike da tausayawa,ace mutum yana komawa wata da bar daban?kuma mai haɗari wacce kowa ke gudunta.saukowa yayi daga kan gadon tare da tsayawa daga can gefenta yana kallonta, itama kallonsa take ,kusan minti uku suna kallon juna,yayin da fattu ke zubda hawaye,juyawa yayi tare da nufar ƙofar dakin.
"Dan Allah Hamma ka dawo mutum,kada ka tafi ka barni,ina don kasancewa tare da kai,bani da kowa awannan sabuwar duniyar saikai"abinda fattu ta faɗa kenan lokacin da taga yana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin.

Aikuwa tsayawa yayi kamar wanda yake sauraron me take faÉ—i .saida ta kai aya azancenta,kafin ya kalleta da idanunsa masu naunuka daban daban,sannan ya fice daga É—akin.

Kuka sosai fattu ta fashe dashi,tana daga kwancen nan,shikenan komai yazo mata ƙarshe,idan Hamma ya tafi ya barta,ita ahalin yanzu ma, ta fara tunanin kodai duniyar aljanu ya kawo ta?
Haka tayi ta kukanta tana daga kwance har barcine wahala yayi gaba da ita.

Shikuwa Adeeb yana fita kai tsaye dakin daya baro ya nufa ,ahankali yake jan jikinsa , harya kai kan gadon ,hawa yayi tare da kwantawa lamo kamar baya nunfashi,rufe idanunsa yayi yana nishi da gyar, kafin kuma jikinsa ya kama girgiza sosai yana hayaƙi, sosai dakin ya turnuƙe da hayaƙi kafin ya washe.

Ikon Allah Adeeb na hanga kwance akan gadon nan,ya duƙunƙune jikinsa,sai rawa yake kamar mai jin sanyi,ahankali ya ɗaya hannunsa dake ta faman rawa ya dage kansa,yana mai yamutse fuska ,da alama kan ke masa ciwo,kusan minti goma ya ɗauka cikin wanan halin kafin naga ya miƙe jiki ba kwari,ya nufi toilet ,wanka yayi tare da sake kaya,ya fito cikin fara tass ɗin jallabiyya.
Zama yayi akan wata kujera dake gaban gadon,kujerar tsabar kyanta ,kai kace da zallar kwal akayita.sai ƙamshi yake bugawa, kallon ɗakin yake yana mai mamakin shidai yasan ya fita zuwa kitchen kuma har yayi girki,bayan nan kuma ya nufi dakin Hulwa, kuma...

Da sauri ya mike yana mai zafi ido,tabbas asume ya ganta aÉ—akin ,amma kuma me yasa shi yaganshi ana ?me ya dawo dashi É—akinsa.
Da sauri ya nufi ƙofa yana ficewa daga dakin,saidai yana fita kafin ya kai dakin nata,yaji sanarwar zuwan tareeƙ,kallon kofar Tata yayi sannan ya nufi bakin ƙofar shigowa falon, yana ɓudewa ya ga tareeƙ da kaya riƙi-riƙi ahannunsa.
Kallonsa tareeƙ yayi yace "yallaɓai lafiya kuwa?
Ahankali Adeeb ya lumshe idanunsa kafin ya jinjinawa tareek din kai,alamu lafiya ba komai.

Shigowa tareeƙ yayi da kayan ya ajiye yana mai cewa"yallaɓai idan an duba sai afadamin abinda babu aciki." Nan ma dai kai kawai Adeeb ya daga sannan ya kalli kayan ,ledojine kusan guda goma manya-manya.
Kallon TareeÆ™ yayi na dan wani lokaci kafin yace "an shirya komai na zuwan gurin mai Abie"?
" Eh yallaɓai komai ya kammala ,lokaci kawai muke jira" cewar tareeƙ kenan cikin girmamawa .
Jinjina kai Adeeb yayi kafin yace " U can go"

"Ok yallabai"
TareeÆ™ ya faÉ—a yana mai barin falon .
Kayan da tareeƙ ya ajiye Adeeb yayi da kallo kafin ya ɗauki leda ɗaya yana ɗan leƙawa, idanunsa ne suka sauka kan inner wear masu bala'in kyau da tsada,da sauri ya rufe ledar yana ɗan kallon ƙofa, dan sosa kansa yayi kafin ya dauko bra guda ɗaya da hannunsa yana mai kallonta,shiru yayi yana tunanin lallai zatayiwa fattu daidai,dan ahalin yanzu yana kallon abubuwan ta daya taɓa gani a toilet,murmushin yay tare da dan sosa kansa kafin ya ɗauki ledojin duka ahannunsa yayi dakin fattun.

Yana tura ƙofar kuwa ya jiyo ƙinkishin kukanta,tana zaune a tsakiyar gadon ta haɗa kai da gwuiwa tana kuka.dan bata wani jima tana barcin ba ta farka kuma ita tsoro takeji taje ta taɓa kofar wannan hulwar ta kuma tsoratata.

Da sauri ya ƙarasa cikin dakin yana kallonta,tsayawa yayi akanta bayan ya ajiye ledojin dake hannunsa,sosai yake jin tausayin fattu cikin zuciyarsa,sam baya kyaunar ganinta cikin damuwa,yanzu zaiji zuciyarsa tayi masa zafi sosai.

"Hulwa " Adeeb ya furta cikin muryarsa mai sanyi da nutsuwa.
Da sauri fattu ta É—ago kanta ,sakamakon jin Muryar Adeeb da tayi,
Ai bata san lokacin data diro daga kan gadon nan ba ta wani ƙanƙame Adeeb da iya ƙarfinta tana kuka,
"Hammana dama nasan bazaka gudu ka barni ba, Hamma na shiga damuwa sosai lokacin danaga ka koma macijin nan,nayi tunanin guduwa zakayi ka barni Hammana dan Allah karka rabu dani"fattu ta faÉ—a cikin matsanancin kuka,wanda zamu iya cewa na farin cikine.

ahankali Adeeb ya lumshe idanunsa,tare da sakin ajiyar zuciya"har abada bazan taba rabuwa dake ba,ina tare dake komai rintsi komai wuya hulwatee" abinda Adeeb ya faÉ—a kenan , cikin zuciyarsa,amma azahiri kawai rungume fattu yayi shima ,yana mai shafa bayanta ahankali.
Kuka sosai fattu keyi tana kara rungume Adeeb,bazata iya faÉ—in irin farin cikin da take cikiba,
" Ya isa haka kukan " Adeeb ya faɗa yana mai ɗago kanta.komar da kan nata tayi tare da kara kwanciya akan faffaɗan ƙirjinsa.

Murmushi kawai Adeeb ya tsinci kansa dayi,yana mai shafa bayan fattu,sosai yake jin wani nishadi idan fattu ta ruƙunkume shi nan ,ji yake kamar su tabbata ahaka.
Bangaren Fattuna dai hakan ne ,ji tayi bata don rabuwa da jikin Adeeb ɗin,dan ba ƙaramin nutsuwa take samu akan wannan ƙirjin nashiba.
Kusan minti goma suna rungume da juna ,kafin Adeeb yayi karfin halin cire ta daga jikinsa yana mai cewa" waike bazai sakeni ba saikin karyani?kin fiye son jiki fa" ya faÉ—a yana É—an harararta .

Kai ta duniyar ƙasa kafin tace "Hamma yunwa nakeji" kallon inda ya ajiye abincin dazu yayi kafin ya janyo table ɗin zuwa gaban gadon,
" Zauna "yace mata.
Zama tayi abakin gadon tana kallonsa,farin ciki fal cikin ranta.

Tea ya haÉ—a mata sannan ya mika mata flate É—in kwan da bread zuwa gabanta.wani bowl ya mika mata ta wanke hannunta,kafin ta fara cin abincin,lallai fattu na jin yunwa ,dan kuwa tass ta kawar da abincin nan,shidai kallonta kawai yake,azuciyarsa yace "wannan badai ciba" tana gamawa tayi hamdala tana mai lashe lips É—inta,É—ago kai tayi suka haÉ—a ido da Adeeb ,saikuma kunya ta kamata,ganin yadda ta kawar da uban abincin nan.
Shikuwa Adeeb cewa yayi " kin koshi ko zaki ƙara dan naga kedin akwai ci kamar Gara"
Dan shagwabe fuska tayi kafin tace "Allah Hamma abincinne ke wuce silik -silik,ba dan ma na cinyeba.ta faÉ—a tana kallon farantin.

Ƙureta kawai yayi da ido yana kallonta baice komaiba,dagowa tayi suka haɗa ido ,harararta yayi yace "zaki fara kallonsa ko" girgiza kai tayi tare da maida kanta ƙasa."zanyi sallah Hamma"ta faɗa kanta a ƙasa.

Nuna mata toilet yayi da hannunsa ,ba tare da yace komai ba.

Mikewa tayi yake bakin ƙofar ta tsaya tare da juyowa.
Yana kallonta baice komai ba,dan yasan me take nufi,ita komai bata iyaba
Saida yayi jimmm!kafin ya mike ya ƙarasa jinkin ƙofar, ya murda handle ɗin yace "kin gani haka ake yi"jinjina kai tayi tare da mamakin wai ƙifama sai anwani murɗata kamar kan fanfo"
Maida ƙurar yayi ya kulle sanan yace "buɗe"kallonsa tayi kafin ta kalli ƙofar, hannunta ta sanya tayi kamar yadda yayi aikuwa saiga ƙofa ta bude.wata dariya ce ta kwacewa fattu ganin tayi nasarar buɗe kofar tace " hahhahhh laaaah Hamma dan Allah kaga abin sauƙi wllh kuma budewa daɗi"ta faɗa tana kara sanya dariya cikin farin ciki.
Shikansa Adeeb dariyar tayi har saida fararen haƙoransa suka bayyana.jijjiga kai yayi kafin ya wuce ciki yana faɗin"Allah ya shiryeki"

Komai saida ya nuna mata ,sanan yasa ta kunna da kanta,aikuwa fattu gaba É—aya yau ta zama kamar wata shasha ,data kunna abu yayi zata kama dariya,wataran harda É—an tsallenta takeyi.
Shidai fitowa yayi ya barta dan tayi wanka da alwala.

Bude kayan da tareeÆ™ ya kawo yayi ,wata doguwar pink É—in riga ya dauko da mahaifinta ya ajiye mata,sannan ya dauko wani fant da bra ya ajiye akan gadon,sannan fice.

Bayan fattu tayi sallah ne taga kaya akan gado,ɗauka tayi tana kallon kayan,sunyi mata kyau a ido sosai ,amma saita ajiye da sauri tace "ƙilama na hulwar tasane ,Ni wllh na tsani wannan hulwar" ta faɗa tana hararar kayan.
Adeeb me ya shigo cikin dakin da sallama can ƙasan maƙoshinsa.
Tsayawa yayi yana kallon fattu ganin bata sake kayan daya ajiye mata ba.

" Baki Ga kaya bane kika maida wannan. Dan ƙazanta" Adeeb ya faɗa tana hararar fattu.

"Kayi hakuri Hamma nayi tunanin a hulwar taka ne ai" fattu ta faÉ—a tana daga kayan,
"Hamma wannan fa " ta faÉ—a tana daga bra É—in nan.

" Baki san me ake yi da itaba maza ki shirya ina jiranki" ya faÉ—a harararta tare da ficewa daga É—akin.

Fattu kuwa data rasa ya zatayi da bra É—in na sai kawai ta sanya kayanta haka tayi waje .
Tana fitowa Adeeb ya biya da kallo ganin bata sanya bra dinba ,yace ........


Mu hade next page banda cajine.


Mrs babi ce💘💘💘
29/08/2022, 10:55 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJI NE🪱🪱🪱


Na mammy kabeer
(Anty mammy)




Elegant online writers📚📚



Free book

Page 33/34






________________Fattu kuwa data rasa inda zata maƙala wannan abun ,sai kawai ta sanya kayanta haka ta yi waje gurin Adeeb, kafin ta fita daga ƙofar saida ta buɗe ta rufe kusan sau biyar,idan buɗe saitayi dariya ta ƙara rifewa, sannan ta buɗe,murna take sosai itama yanzu ta iya buɗe kofar yan wata duniyat.

Tana fitowa kuwa Adeeb ya bita da kallo, so yake yaga ko tasaka wannan abun,saidai kamar yadda ya tsammata ,bata saka ɗin ba kuwa,dan haka kallonta yayi tare da dalla mata harara yace " kingama shiryawa kenan?" Kai fattu ta daga masa tana gyara lullubin da tayiwa matakin kamar wata amarya,ta rufe kusan rabin fuskarta ,sannan ta kama wuyan ta rike ƙam da hannunta.

Shiru yayi yana É—an wani tunani,shi baisan ta yaya zai faÉ—a mata cewar tasaka bra É—in ba,dan haka sai yace" ina wannan abun da kika tambayeni na menene?"ya faÉ—a yana kallonta.
Itama kallonsa tayi kafin tace " na barshi agurin ne ,dan bansan a ina ake sakawa ba" ta faɗa tana ƙara riƙe wuyanta, dan kar mayafin ya faɗi.

Kallonta yayi har zaiyo magana sai kuma ya fasa ,wayoyin da tareeÆ™ ya taho masa da su ya É—auki daya daga ciki , ya daga tare da kiran tareeÆ™ .
Yana dagawa yace "ka tahomin da make up artist yanzu ta shirya yarinyar nan"

"Ok sir " tareeÆ™ ya faÉ—a yana mai kiran wata number.
"Koma daki" Adeeb ya faɗa yana mai mikewa shima ya bar gurin.juyawa tayi ta koma tana mai tunanin kodai tayi masa wani abunne ? Taji yace ta koma ɗauki?zama tayi bakin gado tana mai cire mayafin nan ,dama duk ya isheta.gashin kanta ta shafa,tun wannan daurin dake kanta ,shine har yanzu,kuma kan nata ƙaiƙayi yake mata amma Indai ta zata ƙaramin wanka saita nemi omo ta wanke kan dashi .

Ba komawa saiga tarin ya shigo gidan,waya ya kira Adeeb yake sanar dashi sun karaso.
Cewa Adeeb yayi ya nuna mata É—akin farko shikuma yashigo É—akin hutu.
Kasancewar ba inda tareeÆ™ bai sani ba acikin gidan,dan haka ya nunawa matar wacce take balarabiya ce dakin yace tayiwa yarinyar ciki duk abinda ya dace .
Shikuma ya shiga dakin da Adeeb ke ciki.
Da sallama ya shiga dakin,Adeeb na kwance akan gado, ba barci yake ba ,amma idanunsa alumshe suke .zama tareeƙ yayi yana mai cewa" yallaɓai fatan dai kana cikin ƙoshin lafiya"

Ahankali Adeeb ya yunƙura ya tashi zaune,kallon tareeƙ yayi kafin ya sauke ajiyar zuciya yace " tareeƙ ina tunanin abinda nayi ne ,kada yarinyar nan taga kamar na cutar da itane"Adeeb ya faɗa yana kallon tareeƙ da yanayin damuwa akan fuskarsa.

"Ko kaɗan yallaɓai,idan har tayi tunani zata gane baka cutar da itaba, kuma Allah yaga niyyarka, kayi hakan ne dan kare martabarta da kiyaye hakkin Allah, amma yallaɓai mai zai hana kasanar da ita abinda ke faruwa ,dan gudun samun matsala nan gaba"tareeƙ ya faɗa yana mai kallon ogan nashi .

Shiru Adeeb yayi na kusan minti biyu kafin yace" no tareeÆ™ ,she's too young ace munyi wannan maganar da ita,is better mubar maganar atsaninmu har zuwa lokacin da Allah zai bayyana iyayenta,inyaso saina basu ita ahannunsa,sannan kaga tayi free .

"Shikenan yallaɓai amma yanzu kana ganin ,zaka kaita can gidane,ko kuma zata zauna anan?"tareeƙ ya faɗa yana kallon Adeeb da jiran jin me zaice.

Kusan minti biyu Adeeb ya É—auka kafin yace" ko zamanta anan tare dani akwai matsala tareeÆ™ bana so wataran zuciya ta Kani ga aikata wani abun da zai zamo na cutar da ita,zan kaita can gida gurin ammi ne tunda nima mafi zama can din" ya faÉ—a yana mai lumshe idanunsa.

" Hakan yayi yallaɓai, Allah ya baka nasara akan kudirinka na alkairi" tareeƙ ya faɗa cike da ƙaunar ogannasa.

"Ameen "Adeeb ya amsa ahankali tare da kwanciya.

Ita kuwa wannan matar mai make up,kasancewar tareeÆ™ yayi mata bayanin komai tun kafin su zo gidan,dan haka da sallama tashi ga cikin dakin,juyowa fattu tayi da sauri tana kallon matar.

Murmushi matar tayi tare da kama hannun fattu ta miƙar da ita tsaye tana murmushi,
Kallonta kawai fattu keyi cikin tsoro da rashin sanin ko itaÉ—in wacece?
Cikin harshen larabci matar ke cewa" kai masha Allah yarinya mai kyau da daukar hankali,gaskiya kina da sihirtaccen kyau,Æ´ata, zanyi Mali kwalliya mai kyau kamar ke" ta kai karshen magannarta tana murmushi. ita dai fattu kallon matar take tana tunanin wannan É—in kuma daga ina ?wacece?kodai itace hulwar?

Ahankali matar ta kama fattu ta zaunar da ita bakin gadon,gashin fattu ta fara warwarewa, " kai masha Allah,kina da gashi mai tsananin kyau,samun irin gashinki ba kowacce mace ba,larabawan ma" matar ta faÉ—a cikin harshen labarci,

Ita dai fattu tayi gurum cike da tsoron matar,gashi kuma ta kasa koda yunƙurin gudawa ne bare ta tsere.haka matar ta kama fattu sukaje toilet ta wanke mata kanta tass,sanann suka fito.

Gaban madubi ta kai fattu tare da ɗauki handryer ta busar da kan na fattu,mayuka kala-kala ta shafawa fattu akanta,kan kame tuni kan fattu ya ɗauki wani sheki da ƙamshi, ita kanta fattu wani sawai takejin kan nata.
Gyara mata kan tayi sosai sannan ta ɗaure mata shi da wani ƙaton ribom mai kyau.
Kwalliya tayiwa fattu cikin nutsuwa ba mai yawa ba,daga powder sai lips da kwalli ta sawa fattu a idonta,irin sakun nan da larabawa keyi,kusan rabin ido.
Kai fattu fa tayi mugun kyau fuskar nan Tata kamar farin wata dan haske,kwalliyar ta karbi fuskarta sosai,kodan ba tabayin kwalliyar tayi ba oho?
Ledojin nan mata ta buÉ—e tare da É—auko wata bakar doguwar riga,dama kuma kayan duk dogayen riguna ne masu kyau da sutura jiki.
Har zata dauko su bra,sai taga wata akan gadon ,dan haka sai bata daukoba.

Wani ƙaton towel ta ɗauko ,dake gefen kofar bandakin asaƙale ,mikawa fattu tayi tare da cewa ta cire kayan jikinta ,saita sanya bra ɗin sannan tasa kayan nan.cikin harshen larabci matar ke magana.dan bata san cewa fattu bata jin larabci ba,dan kuwa ita tayi tunanin fattun ƴar Misran ce itama.

Kallon fattu tayi gurum! Kamar kurma,dan bata san me matar ke faɗi ba.ganin fattu bata karɓi towel ɗin ba tana zaune kawai yasa matar tunanin kodai kurmace?
Kwatance ta farayiwa fattu da hannu,cikin ikon Allah kuwa fattu ta gane wai rigar zata cire ta ɗaura towel din .karɓa fattu tayi tare da daura towel din asaman ƙirjinta.murmushi matar tayi tare da ɗaukar bra ɗin ta mikawa fattu.kallon brar fattu tayi tare da kallon matar" tab Ni nasan me zanyi da wannan abun da kina wani mikomin" fattu ta faɗa cikin ranta tana mai turo baki tare da kauda kanta.

Murmushin matar tayi tana mai rayawa aranta ,kodai fattun kunyar saka bra É—in take?dan ga dukkan alamu wannan ne karonta na farko asaka bra É—in.

Cikin hikima da dabara matar ta sakawa fattu bra bayan sun sha artabu,dan fattu sam ƙin yarda tayi da farko, aganinta wannan hulwar so take ta gane mata abubuwa,amma cikin hikima matar tayiwa fattu munin ba ganin jikinta zatayi ba tana son rufe mata jikinta ne,sannan ta dagawa fattu rigar jikinta tare da nuna mata itama ta saka irinta.sai lokacin fattu ta fahimci inda ake saka bra ɗin.ikon Allah wato suma waɗannan abubuwan harda jakar da ake boyewa?lallai zakaga abu da yawa idan baka mutuba.

Aikuwa tsif bra din tayiwa fattu ajikinta,Dan dama koda tareeÆ™ yaje karbowa cewa yayi budurwa yar kimanin 16 za'a haÉ—awa kayan,
Saidai fanties É—in duk sun mata kaÉ—an sosai,da gyar matar ta samo mata wani mai kama da gajeren wando sannan tasaka.

Da kanta ta sanya rigar ajikinta,masha Allah masu karatu duk wanda yaga fattu awannan lokacin zaiyi tunani wata fattun aka sake,dan tayi kyau har ta gaji da yin kyan.
Tauraruwa matar ta fadawa fattu ajikinta masu daɗin ƙamshi,sannan tayi mata rolling ta ɓame da wani kyakykyawan abinda ake riƙe mayafi dashi dan gudun zamewa.

Sosai matar ke yaba kyan da Fattun tayi , ga sarƙarta sai walwala take,matar sai kallon sakar take cike da jinjina irin kuɗin da aka batar wajen siyanta,kafin ta kama hannun fattun ta juya da ita gaban madubi.saida gaban fattu ya faɗilokacin datayi arba da kyakyakywar fuskarta jikin madubi,hannu tasa tare da shafa fuskartata,dan tabbatarwa itaɗince kuwa.
Ƙuri!! Fattu ta kure kanta da kallo ta jikin madubi,wai dama haka take ko kuma dai ba ita bace wannan ɗin?anya matar nan ba sake mata fuska tayi ba ?dan dan ita bataga tsohuwar fuskarta ta da ajikin madubin ba.
Murmushin tayi lokacin data É—an mintsini hannunta kadan,kuma taji zafi.
Wllh nice ,nice fattun baffa, gaba daya na zama Æ´ar gayu aradu zan tsula tsiya, wayyo Allah na ,ina Hamma yazo ya ganni ,yaga yadda na koma fattu Æ´ar gayu.
Juyowa fattu tayi tana kallon matar nan, fuskarta dauke da murmushi, itama matar murmushin tayi tana yaba kyau da Allah ya ba faytu.
Wayar matar ce tayi ƙara hakan yasa ta dauka ba tare da tace komai ba ta kara akunnenta,
"To yallaɓai ganin nan"
Shine abinda matar ta faÉ—a tana mai haÉ—a jakarta ,sallama tayi fattu bayan ta rungume fattun.

Koda matar ta fita tsayawa fattu tayi jikin madubin nan tana ƙara kallon kanta,tajita nan ta juya can tana dariya ƙasa -ƙasa.

Adeeb ne ya shigo ɗakin sanye da farar jallabiya mai tsananin kyau da ɗaukar ido,kansa kuma hiramine sai wannan baƙin abun da suke ɗorawa asaman hiramin, ba ƙaramin kyau yayi ba sai sheƙi fuskarsa keyi.

Tsak !ya tsaya abakin ƙofar yana mai faɗin "masha Allah,watabarakallahu fi ahsanil kaliƙin" lokacin da yayi arba da ƴar gayu fattu,wacce Bama tasan yana gurin ba,kallon kanta kawai take ,ta taɓa nan ta taɓa can.
Saida yayi gama ƙureta da kallo,yaga dai idan ya biye ta kallonta to zasu kwana anan ba tare da ya gaji da kallon nata ba,dan haka sai yayi ɗan gyaran murya kafin yace " idan kin gama kalle madubin zo mutafi.

Sai lokacin fattu ta an kare da Hammana nata na gurin" cikin jin daÉ—i ta nufeshi tana murmushi," Hamma kalli yadda matar nan ta sauya min fuska? Wllh gani nake kamar bani ba "fattu ta faÉ—a tana dariyarta mai burge wa da ban sha'awa.

Kallonta kawai Adeeb yake ,dan shikam ya rasa bakin magana ma,gaba É—aya fattu ta sanya shi cikin wani yanayi na ruÉ—ewa da zallar kyanta.
Ita kuwa tana tsaye gabansa sai rangaji take ,jinta take kamar sarauniya yau É—in nan.

Ahankali Adeeb ya kai kallonsa kan waÉ—an nan abubuwan na fattu, ajiyar zuciya ya sauke ganin yanzu kam ta saka wannan abar.dan haka hannunta kawai ya kamo sukayi waje.

Sai lokacin fattu ta sami damar kallon tsarin falon,sama gidan baki É—aya .
Suna tafe amma fattu na waige waige,ikon Allah Allah garin daɗi na nesa,ashe su amaƙabarta suke,anya kuwa wannan gidan ba aljannar duniya bane.ahankali tace " kaikuwa Hamma dan Allah wannan gidan na waye?"ta faɗa tana kallon yadda yake danna nonbibin bude ƙofar.


Kallonta yayi bayan sun fito farfajiyar gidan,kafin ahankali yace "nawa ne"
Baki fattu ta buÉ—e cike da mamaki kafin tace " ikon Allah, to Hamma a ina ka sami kudin gina wannan gidan, dan nasan aradu zai kai kusan dubu saba'in ko tamanin " ta faÉ—a tana irin jinjina kan nan na ta kwaso kudi da yawa.
Dariya ce ma ta kama Adeeb ,saidai kasancewarsa ba mai yawan dariya ba yasa yayi murmushi kawai ,kafin yace " ki tara kuÉ—in da kika faÉ—a kibani na baki gidan" ya faÉ—a cikin nishadi,haka kawai yake jinsa cikin wani irin nishaÉ—i dajin daÉ—i

Kama baki fattu tayi cikin zato ido tace"woooooh Ni ɗiyar baffa,ina zanga wannan uban kuɗaɗen? saidai idan kaina san siyar insamu, Ni wllh bazan gina gida irin wannan ba ma,haba saikace wanda zan zauna da aljanun duniya acikin" ta faɗa tana wani dan taɓe baki irinna rufamin ashirin nan.

Kallonta Adeeb ya É—anyi, yadda take ta zuba

Please Login or Register in order to submit comment