Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki, za ta shiga lamuranki ba za ta da mu kunya ba albarkacin tsafi da farauta." Jin daɗin kalamansa ya sa na sakar masa murmushi a daidai lokacin na ji Abar bauta ta sake cewa, "A daren yau zuwa gobe za a katange yankin nan daga baƙar guguwar da ta taso mana. Ya zama wajibi a zubar da jini ga rauhanai don su sake dafa mana akan sha'anin rayuwarmu, wannan shi ne abin da zan iya sanar da ku don na taimaka muku. Idan kuka bijirewa umarnina zan iya sauya sheƙa daga wannan yankin zuwa wani na kafa daulata, munanan abubuwa za su yi ta faruwa a kan ku haɗe da farmakai daga sauran ƙasashe musamman Baƙar Daular da kullin burinta ta shafe tarihin Maharba a faɗin duniya." Cikin aminta da kalaman abar bauta da ba ta yarda ya sa muka amsa mata da faɗin, "Uwar gijiya abar bauta ta dafa mana ta shafe matsalolinmu, mun dogara da ke don haka ke ce mai yaye mana damuwa da ba mu waraka a kowanne lokaci. Mun ji mun amince za mu yi abin da kika ce domin mu ma su bin umarninki ne, mun dogara da tsafi da sihiri sune madogarar abar bauta ita kuma ita ce madogararmu a koyaushe."

Fuskar abar bauta ce ta fasalta irin farincikin da ta yi da mu, don haka ta ɗaga hannunta sama ta wara ƴan yatsunta nan take wani mulmulallan haske ya dira a kai. Ta dube mu ta sake kallon haske sannan ta furta, "Albarkacin tsafi da sihiri, albarka da tabbata a gare ku ya ku wannan zuri'a ta mafarauta masu albarka. Shin akwai mai son a bincika gobensa don sanin abin da zai faru da shi? Akwai mai ciwo mu warkar da shi? Ko akwai mai son mu ninka nasara da tsaririn tsafinsa don ya gagari kowanne rauhani a dajin farauta?" Tun bata rufe baki ba mahaifina ya ɗaga hannu sama, kasancewar mahaifina sarkin Maharbin yankinmu ya sa mutanen garinmu suke matuƙar ba shi girma domin mutum ne mai adalci da son talakawansa. Ganin mahaifina ya yi magana ya sa alummar da ke wurin suka fara  kai masa gaisuwa cikin girmamawa, "Sarki ya zo mutuwa ta zo, mutuwa mai kai ƴan maza ƙasa ko da son rai ko babu. Abar bauta ta riga da ta buɗa maka kwarankwatsa dubu sai ka gama lafiya amanar ƙauran garin Dume, amana ta kai mana amana ta kai maka mun baka amana ka ba mu gaskiya ko sun ƙi ko sun so sai mun bar wuya a dajin Gagarar maza. Sa'a dai maza sa'a dai uban dawa wuya mai sa ƙarar kwana ga ƙananun maharba uban dawa sai ya kai labari ko da daɗi ko babu." Sunkuyar da kai Mahaifina ya yi alamar gaisuwar tana kai masa sannan ya ɗago ya amsa musu da cewar, "Dawa dai mazaje! Ba kyau ba daɗi, idan wuya ta yi wuya yaro ke guduwa ya bar babansa. Kwarankwatsa dubu ranar Talata mai zuwa sai na kai hallitun dawa dubu biyar da ɗoriya ɗan butar uwa, Abar bauta ta buɗe mana dai." A hankali muka riƙa takawa har kan tudun tsira sannan mahaifina ya tura ni daga gabansa kaɗan ya fara yi mata magana."Abar bauta ta yafe min kada ta yi fushi da ni a yau ma na sake dawowa da 'yata Kyauta domin ta shiga lamuranta. Ɓoyayyun al'amura na sake bayyana a tattare da ita, don haka na sake dawowa da ita don na ji ko akwai wani taimako da Abar bauta za ta yi domin Kyauta ta rinƙa rayuwa kamar kowa." Daga can duhu-duhun wurin da mutane ke tsaitsaye na hango wani matashin saurayi yana ƙara kutso kai sakamakon jin bayanin da Mahaifina ya yi, muna haɗa ido ya sakar mini murmushin da ban san dalilinsa ba, sai dai abin da ya ɗaure min kai ba kasafai na cika tozali da matashin ba sai a ranaku makamantan waɗannan da muke kai wa Abar bauta kukanmu.Hasali ko kaɗan ba ya daga cikin zuri'armu domin gabaɗaya mun san kanmu waɗanda suke rayuwa a yankin. Ina cikin wannan tunanin na riski muryarta tana faɗin, "Akwai ɓoyayyun lammura game da Kyauta don haka nake gagara bincika abin da yake damunta, a duk lokacin da na bincika gobenta ba na samun biyan buƙatata. A duk faɗin yankin nan babu wanda zan bincika rayuwarsa ta gaba na samu tangarda sai Kyauta, ina mai yi maka albishir da cewa ita ɗin ta musamman ce don haka waɗansu abubuwa suke baƙuntar rayuwarta. Babban abin da za mu saka a gaba shi ne, mu mayar da hankali wurin zagaye garin nan domin idan muka zagaye gari na yi ammana da tsafi da sihiri babu abin da za same mu." Wurin ne ya yi tsit muna sauraron ci gaban bayanin da abar bauta take. Sai da ta sake hawa can ƙololuwar samman tsauninta sannan ta ci gaba da cewa, "Albarkacin ranar talata da nasarorin da ke cikinta muna miƙa wuya ga alƙaluman tsafi akan zan sanar da talakawa su nemi waɗannan kayan tsarin su aiwatar da shi domin neman warakar su. Da farko za ku saro kan wani ƙasurgumin kumurcin maciji da ke Dajin Bawaya, sai ku kawo min na jiƙa shi da ruwan sihiri haɗe da tumfafiya, idan ya kwana ɗaya a jiƙe sai a dake kan macijin ku samo mana ruwan kogin haladu a wanke idon matasan makafi a haɗa da ƙasar kabarin Jarumi Baushe uban Yaɗiya, idan kuka yi haka ku kawo min na haɗa sauran mahaɗin da kaina. Zan baku shi ku je ku zagaye garin nan da shi kuma duk abin da za ku gani kada baki ya furta ko zuciya ta tsorata, duka waɗannan abubuwan za a same su ne a cikin ƙasa da kwana biyu." Duk da zuciyoyinmu sun fara karaya bai hana mun amsawa abar bauta ba, tana gama jawabin ta dafa raunin da ke jikina haɗe da ɗaura min wata baƙar fata wacce da alama ta baƙar wahainiya ce. Nan take raunin jikina ya warke wani ƙarfi ya ratsa ni tamkar wani abu bai taɓa faruwa da ni ba, daga haka ta sallame mu sannan kowa ya watse gidansa.  

Sannu a hankali na rinƙa waige-waige don ganin na lalaubo matashin da nake ɗora zargi a kansa, amma sai haƙana ya gagara cim ma ruwa. Na neme shi sama da ƙasa na rasa! Dama na san za a rina wai an saci zanin mahaukaciya. A duk lokacin da na yi tozali da shi haka ce take faruwa don haka nake tunanin yana tattare da mummunar manufa game da yankinmu. Saboda na tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa, kuma tamkar wanda yake wa rufa ido ban taɓa ji wani ya yi magana ko ƙorafi akansa ba. Kasancewar ba a ranar na saba ganin hallitun da ƴan uwana ba sa iya ganinsu ba ya sa na ja bakina na yi shiru, amma haka kawai jikina ya ba ni ziyararsa a gare mu ba alheri ba ce.

Matashin saurayin na barin wurin kai tsaye ya bi ta wata ɓarauniyar hanya da ke ƙarƙashin ƙasa, cike da fargaba ya rinƙa falfala gudu don yana tsoron tonuwar asirinsa musamman da ya tuna irin kallon zargin da Kyauta take yi masa. Sai da ya yi gudu mai nisa sannan ya isa wurin wasu rundunar dakarun mayaƙa, haki yake yi kamar ransa zai fita sannan ya sanar da su duk abin da ya ji game da yankin su Kyauta sannan ya ɗora da cewa, "Matsala dai ɗaya ce kamar yadda na gaya muku a baya, duk lokacin da na shiga yankin nan ba na iya ganin kowacce halita da idona face manyan dabbobi da ƙanana. Da taimkon Shugaba Usaina ta ba ni wani laƙani shi ne nake iya ganin yarinya ɗaya da idanuna kuma nake iya jin sautin abin bautarsu, ita ma a yadda na lura tana ganina sai dai ina tsoron kar asirinmu ya tonu." Shugaban Dakarun ne ya bushe da dariyar ƙeta sannan ya furta, "Ka gama aikinka don haka za ka iya tafiya ga Daularmu mai albarka, na tabbata idan muka kai wa Sarki wannan zuri'a ta Maharba sai ya yi mana ƙarin girma ya ɗaukaka darajarmu.

Runtse idonsa matashin ya yi tare da faɗin, "Shugaba Usaina! Shugaba Usaina." Nan take wani haske ya mamaye wurin babu jimawa ya ɓace ɓat. Gurfane yake a gabanta yana sauraron abin da za ta faɗa, sanin faɗin rai da izzarta ya sa ya ƙagara har ya ɗago don a tunaninsa ko ta bar wurin bai sani ba. Suna haɗa ido ya sauke kansa ƙa sa cikin girmamawa ya furta, "Sha kundum ta dafawa aikinki." Miƙewa ta yi ta fara taku ɗaiɗai ta rinƙa zagaye shi sannan ta furta, "Na saurari bayaninka don haka ina mai umartarka da ka iya bakinka idan ba haka ba sai na fisge rai daga gangar jikinka. Tabbas Boka mai zamani ya yi gaskiya Sha kundum ta sake bayyana a wannan yankin da kake min leƙen asiri sai dai babbar matsalar da har yau ya gagara bayyanar da suffar yarinyar. In dai ina numfashi Sarki Damina ba zai taɓa samun cikar burinsa na jininsa ya gaji karagar mulkinsa ba, na yi rantsuwa da abar bauta sai dai zuri'arsa ta ƙare a wahale yana ji yana gani zan gina Daular nan da jinin da ba na shi ba." Ta kai ƙarshen maganarta a tsawace kamar wacce aka ɓata wa rai, a razane matashin ya gyaɗa kai yana shirin sake magana ta katse shi da cewar, "Fitar da sirrina tamkar ka sanya takobi ka datse rayuwar da kake ciki ne, ka kiyaye idan ba haka ba wankin hula zai iya kai ka dare." Godiya ya yi mata sannan ya tashi zai fita ta sake katse shi da cewar, "Ka tabbatar da ka bawa yarima mugunyar ruwan sihiri a daren nan kafin wayewar gari." Amsa mata ya yi cikin ladabi sannan ya fice daga ɓangarenta.

Dare ne ya tsala sosai ban da kukan tsuntsaye da na ƙananan dabbobi babu abin da yake tashi, cikin sanɗa da ɓadda-bami take tafiya a hankali tana waige don kar wani ya ganta har ya fahimci abin da yake tafe da ita. Kamar yadda ta saba a duk daren da take neman biyan buƙatarta haka ta tunkari tsaunin Boka Mai zamani, kamar yadda ya ga zuwanta a cikin ƙoramar sihirinsa haka ya ji takunta zuwa kogon dutsensa. Tun daga bakin ƙofa Boka Mai zamani ya rungume ta a yunƙurinsa na son su fara aikata masha'arsu kamar yadda suka saba duk lokacin da ta ziyarce shi, a hankali ta zame shi daga jikinta tana faɗin, "Sha kundum ta ci gaba da rufa mana asiri dangane da ɓarnar da muke aikatawa Sarki Damina." Boka mai zamani ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan ya furta, "Wane mutum In ji mutuwa shalelena? Asirinmu ba zai taɓa tonuwa ba don ba na jin wancan sakaran zai iya kusanto da Sha kundum cikin wannan Daular, hasalima rashinta tare da mu shi ne mafi alheri domin na tabbata idan tana yankin nan asirinmu ya gama tonuwa. Yanzu dai ya kamata a baiwa kura ajiyarta." Takawa ta fara yi a hankali tana zame ganyen da ke jikinta daga wanda ya rufe al'aurarta har zuwa na ƙirjinta sannan ta furta, "Ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai ya ke ba mudubina. Indai wannan ne ai ta kwana gidan sauƙi jariri a ɗakin mayya. Amma abin da yake tafe da ni bai wuce kan maganar wancan sakaran Yariman ba, shin maganar da na ji Sarki ya faɗa gaskiya ne zai iya warkewa? Saboda ina ɗagawa Sarki Damina ƙafa ne don na san a halin da yarima yake ba zai iya mulkar Daular nan ba." Boka mai zamani ya ƙarasa wurinta yana yawo da hannunsa a sassan jikinta sannan ya furta, "Tabbas a bincikena matuƙar Sha kundum ta bayyana a Daular nan zai iya warke wa amma da sharaɗin sai an bankaɗo sirrin da ba kowa ne ya sani ba kuma ba kowa ne zai gan shi ba. Mai wannan ikon yanzu haka ta bar duniya, Mai babbar Turaka ita ce ta san da wannan ɓoyayyan sirrin wanda ko da Sha kundum ba ta dawo daular nan ba matuƙar aka bankaɗo shi Yarima zai warke, yanzu haka gawar Mai babbar turaka na ɗakin yarima na kashe ta ne a lokacin da take ƙoƙarin sanarwa da Yarima sirrin ɓoyen da bankaɗe shi ba alheri ba ne a game da ke, ni kuma duk abin da zai muzanta shi zan iya kawar da shi. Sarki Damina yana kallonki a matsayin mahaifiyar Yarima alhalin Hasana ita ce Mahaifiyarsa kece Usainarta, Ko kin san har gobe Mahaifiyar Yarima tana raye a faɗin duniyar nan? Ko kin san Yarima ba shi kaɗai ne Ɗan da Sarki Damina ya mallaka ba? Ko kin san ƴaƴan Sarki Damina Uku ne a faɗin duniya? Idan bacci kike ki farka domin a duk lokacin da Damina ya gano kece kika nemi salwantar da rayuwar yarima da mahaifiyarsa na tabbata kashinki ya bushe. Ki yi duk abin da za ki yi ki nemo tagwayen jarirai ki kawo min domin na cika miki wani aiki da su idan ba haka ba komai zai iya faruwa, kuma ki tabbata jariran sun fito daga cikin jinin Maharba domin har gobe jininsu na tasiri akanmu tun da sune suka yi galaba a kan mu a lokacin da mummunan al'amari ya faru da Sarauniya Shakundum." Jakadiya da tun shigar Mai ɗakin Sarkin Damuna take laɓe a ƙofa ta riƙe bakin cikin mamaki, a hankali ta furta, "Tabbas Usaina ta cika tattaciyar marar imani amma na yi rantsuwa da Sarauniya Sha kundum da mulkinta sai kwaɓarta ta yi ruwa, a kullin fata da burina bai wuce Sarki Damina ya auri Jummai don na tabbata ko da tsiya da azziki sai Jummai ta haihu a gidansa. Jakadiya bata ƙarasa wannan tunanin ba ta hango harshen wutar itace kafin ta yi wani yunƙuri Bayin Sarki Damina suka haske ta da shi, a tsawace babban bawansa ya furta, "Jakadiya Lami me kike yi a wurin Boka mai zamani a talatainin tsohon daren nan duba da kin san haramun ne matuƙar ba a sanar da Sarki Damina wannan ziyarar ba?" Daga cikin kogon dutsen cikin Boka mai zamani da Usaina mai ɗakinsa ne ya kaɗa, nan take zufa ta fara keto musu cikin faɗuwar gaba ta furta, "Halaka ta zo mini matuƙar Sarki Damina ya san da ni a kogon dutsen nan." Kafin boka mai zamani ya yi magana daga cikin rijiyar da gunkin Sarauniya Sha kundum take suka ji wata irin tsawa wacce ta haddasa razanar Jakadiya ta faɗo cikin kogon dutse a hargitse. Ganin haka ya sa Sarki Damina da Fadawansa suka rufa mata baya, don ya kawo ziyarar cikin dare ne sakamakon mummunan mafarkin da ya yi akan Yarima da wata matashiyar buduwa mai ɗauke da kwari da baka a hannunwanta."

*Ummou Aslam Bint Adam*🌚



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


4 Comments On SHU'UMAR MASARAUTA
avatar
zainab-8-2

1 year ago

Reply

Tnx

avatar
asiya-mashi

1 year ago

Reply

Allah ya kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to asiya-mashi

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Ameen

Please Login or Register in order to submit comment