Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zaro idanu cikin fargaba har sai da ya fahimci ruɗewar da take ciki.

"Lafiyarki Umaima?" Cikin kissa ta daidaita nutsuwarta ta ce, "Dama na yi mamaki ne ganinka shiru, kar dai ka jima kana jirana." Murmushi ya sakar mata haɗe da girgiza kai. Ta ƙarasa wurinsa asirtaccan ƙamshinta ya ratse hancinsa, ya lumshe ido cike da jin daɗin ƙamshinta.

"Ki tabbata kin sa shi ya shiga bayan gida kafin ki saka wa Maimuna turare a gabanta."
Kalaman Boka Bamaguje ya dawo mata raɗau a cikin kunnuwanta. Miƙe wa ta yi ta furta. "Sarkina bari na haɗa mana ruwa mu ɗan watsa ko?" Ba ta jira cewarsa ba ta nufi banɗaki ta haɗa komai da kanta sannan ta zuba turaren da Bamaguje ya bata, bayan dawowarta ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa sannan suka wuce banɗaki. Da kanta ta ɗebi ruwan ta watsa masa cikin sigar tsokana, sai kuma ta yi farat ta furta. "Na yi mantuwa."

Kallon da ya yi mata ne ya alamta mata yana buƙatar ƙarin bayani daga gare ta.

"Ina zuwa." Kawai ta furta ta fice a gaggauce. Sai da ta tabbatar da ta rufe ƙofar ta baya sannan ta koma turakarsa cikin sauri ta ɗaga doguwar rigar Maimuna ta kwara mata turaren a ƙasanta sannan ta shafa mata a fuskarta, ita ma ta murtsuke jikinta da shi ta rage kayan jikinta ta sake komawa cikin banɗakin. Tana shiga ƙamshinta ya daki hancinsa, take ya ji wani irin yanayi ya tsarga masa. Buƙatar ya kusance ta ta yunƙuro masa, ganin saƙwannin da yake aika mata ya tabbatar mata da haƙonta zai cim ma ruwa, don haka ta fara neman shawarar da za ta yanke wa kanta. A hankali ta yakice shi tana faɗin, "Sarkina a banɗaki muke mu ƙarasa turaka." Bai musa mata ba, ta ƙarasa sheƙa musu ragowar ruwan sannan suka fito hannunta na riƙe da shi, idanuwansa a rufe suka ƙarasa don haka ko da ta zaunar da shi a gefen gado ta ga ya rarumo Baiwa Maimuna da ke zaune kamar gawa. Fulani Umaima ta koma gefe ta zuba masa ido zuciyarta ƙal, tana nan tsaye Takawa ya gama mu'amalarsa da Maimuna ya koma gefe ɗaya sai gani ta yi numfashinsa ya ɗauke. Da sauri ta ƙarasa ta ɗebi najasar jikinsu ta isa bakin rijiyar da tun da take shiga cikin turakar ba ta taɓa taka wurin ba, wata irin kuɗa ta fara ji a cikin kunnuwanta ga wata 'yar juwa-juwa da take ji sama-sama. A haka ta samu ta zuba najasar a kan rijiyar take murfinta ya buɗe, wata baƙar ƙura ta turnuƙe ta. Sai daga baya komai ya washe, ganin haka ya sa Fulani Umaima ta koma ta janyo hannun Baiwa Maimuna sai da suka je bakin rijiyar Fulani Umaima ta furta.

"Maza ki shiga rijiyar nan da ƙafar hagu."

Ba musu Maimuna ta ɗaga ƙafarta ta zura cikin rijiyar ta zauna a kan wani mulmulallan baƙin dutse. Kamar yadda Bamaguje ya gaya mata Maimuna na gama shiga murfin ya taso da kansa ya rufe ruf. Ta koma can gefen Sarki Abdul'aziz ta kwanta tamkar da ita Takawa ya gama mu'amala. Bayan ɗan wani lokaci Mai martaba ya fara motsawa, jin haka ya sa Fulani Umaima ta fara sauke ajiyar zuciyata tana rarumo shi cikin kissa da kisisina. Wani irin nauyi dum! Kansa yake yi masa don haka ya gagara tunano abin da ya faru a baya, ganin yanayin da suke ciki ya sa ya sakar mata ajiyar zuciya ya yunƙura suka wuce banɗaki don tsaface jikinsu. Irin rawar jikin da yake yi a kanta ne ya sake tabbata mata da tabbas alƙaluman tsafin Bamaguje ba su zube a ƙasa banza ba, ta ci gaba da narke masa tana cin karenta babu babbaka. Daren ranar a sashen Sarki Abdul'aziz ta ƙarashe shi har zuwa wayewar gari.

Cikin abin da bai fi wuni biyu ba, maganar haihuwar Fulani ta yaɗu cikin da wajen Masarautar Huddam, musamman da ya kasance an san Takawa ba shi da ɗa namiji sai a wannan lokacin. Manyan mutane da masu kuɗi haka suka dinga zuwa suna bada gaisuwa haɗe da yi masa barka da samun ƙaruwa, mafi yawa daga cikinsu har da sha tara ta arziƙi suke kawowa. Duk da Fulani Umaima ta san jaririn a nakashe yake hakan bai hana ta jin ƙyashi, baƙin ciki da ƙunci a kan kyaututtukan da Fulani Babba take samu ba. A lokacin sai ta tsiri kwanciya da tsirfar ciye-ciye wani lokacin har amai take ƙaƙalowa a turakar Mai martaba, duk da cikin jikinta babu abin da yake saka ta. Ganin haka ya ɗaga hankalin Takawa har ya aikata sashen magunguna aka kira masa Ungozoma da jikar Baushe don su duba ta su ba ta magani. Tashin farko aka sanar wa da Sarki cikin da ke jikin Fulani Umaima, farin ciki kamar zai zuba ruwa a ƙasa ya sha. Ita kuwa Fulani Umaima ko kaɗan ba ta nuna wa Takawa ta san da cikin jikinta ba, nan ta shiga gwalangwaso da feleƙe wani lokaci hatta ƙamshin Turakarsa ce wa take ba ta so.

Cikin wannan yanayin aka ɗebi kwanaki mai jego tana ɓangarenta tana jego ita kuma Fulani Umaima tana rainon cikinta, gabaɗaya gidan sarautar ya zagaye da ƙananan maganganu. Jin labarin cikin Fulani Umaima da Fulani Babba ta yi ba ƙaramin faranta ranta ya yi ba, kuma rashin ganinta kwana biyu a ɓangarenta ko kaɗan bai dame ta ba don ta san yadda laulayin ciki yake ba shi da daɗi. A ɓangare ɗaya Fulani Babba na cikin matsanancin tashin hankali sakamakon yadda fitsarin da yake zuba daga jikinta yake sake ta'azzara, tun tana ɓoyewa har ya zamana sai da Baiwa Zainaba ta fahimci halin da take ciki, ga shi abin kullin gaba yake yi da ta kwanta ko bacci minti biyar ba ta yi tana farkawa sai dai ta ji ta sharkaf da fitsari, ga kuma jinin biƙi duk shimfiɗarta ta haɗu ta dagule. Ana gobe suna da asuba bayan ta tashi ta sake ganin wurin ya yi sharkaf da wani irin zarnin da ke tashi har ya wuce misali. A wannan lokacin take zuciyarta ta karye ganin lalurar tata a kullin gaba take yi ba baya ba, a daidai lokacin yayarta da suka zo daga Masarautar Bassar ta shiga ɗakin, ganin ta a zaune ya sa ta ɗan yamutsa fuska.

"Fatima wai mene ne yake wari ne?"

Da yake mai shirin kuka ne aka jefe shi da kashi awaki take Fulani Babba ta fashe da matsanancin kuka, da mamaki Halima ta furta, "Fatima me yake faruwa ne?" Sai da ta yi mai isarta sannan ta miƙe tana nuna wa yayarta ta ce.

"Ki duba ki gani Yaya Halima wai ni ce yau nake malala fitsarin kwance. Ni dai na fi zargin tun ranar na haihu na haɗu da wannan iftila'in, duk yadda zan yi takatsantsan ina runtse idona duk gajarta bacci sai dai na tsinci kaina a cikin fitsari." Jakadiya da ta zuro kanta da niyyar sanar da Fulani Babba ruwan wankanta ya yi zafi ta yi fakare tana sauraronsu. Yaya Halima cike da damuwa ta jinjina kai.

"Kin sanar da Mai martaba?"

Girgiza mata kai kawai ta yi don ba ta son ta buɗe baki har ta iya sanar da danginta zaman doya da manjar da ke tsakaninta da Takawa. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta furta, "Ya zama wajibi na sanar da Yakumbo a nemar miki magani, domin wannan fitsarin ba na lafiya ba ne. Ni fa dama zuciyata da hankalina ba su taɓa aminta da wannan kishiyar taki ba..." Da sauri Fulani Babba ta katse ta. "Yaya kada ki zargi Umaima domin ban taɓa zarginta a kan wani mugun abu ba, zamana da ita babu wata matsala ni dai a yi mini magani amma Allah ya sani babu sa hannun Umaima a lalurata." Inuwar da Yaya Halima ta hango a wurin labule ya sa ta furta.

"Waye a wurin nan?" Jikina na rawa Jakadiya ta faɗa ɗakin tana faɗin, "Allah ya taimaki Fulanin Takawa, uwar yariman gobe da yardar Allah. Dama ruwan wanka na kwashe na zo sanar da uwar gijiyata." Daga cikin ɗakin Fulani Babba ta furta.

"Saƙonki ya isa Jakadiya."

"Godiya nake zinariya fara mai farar aniya bangon talakawa da marasa gata, Allah ya raya mana yarima ya gaji karagar da babu kamarta a faɗin nahiyar nan." Yaya Halima ta amsa tana bin Jakadiya ta kallon tuhuma. Sai da ta ga Jakadiya ta fita sannan ta furta.

"Da alama wannan farar zuciya taki na iya kai wankin hula ya kai ki dare, jikina yana ba ni idon masarautar nan yana kanki."

"Yaya Halima shi zato zunubi ne! Don haka..." Da sauri ta katse ta. "Dama ki ajiye zurfin cikinki kin amayar mini da abin da yake cikinki domin abokin kuka ba a ɓoye masa mutuwa." Idanun Fulani Babba ya ciko da ƙwalla don ita kaɗai ta san zafin da zuciyarta take yi mata, amma sanin Yaya Halima na daga cikin irin marasa haƙuri ya sa ta danne damuwarta ta furta. "Babu wani abu da yake damuna Yaya Halima, idan ma akwai na fauwala wa Allah saboda saniyar da ba ta da jela Ubangiji ne ke kore mata ƙuda." Yaya Halima ta taɓe baki ta fice ba tare da tanka mata ba, Fulani Babba da ta yi shirin wanka tana kai idanunta kan jaririnta. A kullin ta kalle shi zuciyarta na wasu-wasi a kan ingancin lafiyarsa, sai dai babu yadda za ta yi tun da ba fada gare ta a wurin Takawa ba balle ta yi masa bayanin halin da jaririn yake ciki.

Kamar za ta tashi sama haka Jakadiya ta yi sashen Fulani Umaima a lokacin Fulani na shaƙar bacci ko sallar asuba ba ta yi ba duk da gari ya waye garau, da farko Bayin da ke kula da ita sun sanar da Jakadiya Fulani na bacci. Amma da yake bakinta cike yake fal da tsegumi a dole haka ta shiga tana ta rangaɗa sallama. Kamar a mafarki Fulani Umaima ta ji sallamar Jakadiya wanda hakan ne ya alamta mata akwai wani muhimmin abin da yake tafe da ita, tana daga kwance ta sa a yi wa Jakadiya iso har cikin turakarta. Jakadiya na shiga ta zube a ƙasa, "Hutawarki lafiya tauraruwar Mai martaba uwar yariman gobe da yardar Ubangiji. A yi mini aikin gafara na tashi uwar gijiyata a farar safiya..." Da hannu Fulani Umaima ta katse ta, kamar ba za ta yi magana ba sannan ta ce. "Akwai magana a bakinki Jakadiya don na tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa." Jakadiya ta yi mata jinjina da hannu. "Allah ya ƙara yawan rai wannan yarinyar da nake ganinta mai hankali ashe lumbu-lumbu ce wutar ƙaiƙayi?"

"Jakadiya tafi kanki tsaye. Fulani Umaima ta faɗa a gajarce.

"Halima yayar waccan ragowar fitsarin, ita na ji tana shirin ɓallo mana ruwa. Ni kuma na ce har gaban abada kwaɓarmu ba za ta yi ruwa tsululu ba, sai dai a mutu har liman kowa ya rasa sallah..." Jakadiya ta kwashe duk maganganun da ta ji Fulani Babba suna yi ita da Yaya Halima. Murmushi Fulani Umaima ta saki. "Daga kallon da na ga tana bi na da shi ya sa na fahimci ruwa ba zai taɓa tsami banza ba. Ta shi ki je Jakadiya idan hantsi ya fito ki dawo akwai kyautar samirar alkaki da nakiya, zan haɗa miki da fallan zani da gorar maɗi. Na rantse da Allah sai na tabbatar wa Halima ba a taka shuri kowanne iri a zauna lafiya." Jakadiya ta sake zubewa. "Godiya nake uwar ɗakina, godiya nake zinariyar Mai martaba uwar duka mazauna ƙasar Huddam da kewayenta. Allah ya buɗi ido lafiya ya kawo mana Yarima cikin ƙoshin lafiya." Fulani Umaima ba ta amsa ba, inkiya ta yi mata da ido. Ganin haka ya sa Jakadiya ta fice daga ɗakin don ta san ba za ta amsa mata ba.

Washegari ya kama suna jaririn Fulani Babba ya ci suna Abubukar Sadiq, haka kawai Sarki Abdul'aziz ya tsinci kansa cikin farin ciki duk ba ya iya nuna soyayyarsa game da yaron, ya so a gayyaci masu wasannin al'adar bahaushe amma wata irin fargaba yake ji da tsoron Fulani Umaima a zuciyarsa. Da ya yi wani yunƙuri sai ya ji kamar idan ya aikata bai kyauta wa Fulani Umaima ba. A haka aka ci taron suna sai dai hatta Bayin da ke cikin masarautar ranar sai ta zame musu daban sakamakon walwala da suka samu ta hanyar sauya abinci da sakewa. Fulani Umaima ta saki jiki sosai a ranar da kanta ta gayyaci 'yan wasan tauri aka gudanar da wasanni, tamkar babu wani mugun ƙuduri a zuciyarta. Bayan suna da kwana biyu 'yan uwan Fulani Babba suka tattara kayansu suka koma masarautarsu, ko a ranar da za su tafi sai da Yaya Halima ta jaddada wa Fulani Babba suna komawa za a aiko mata da magungunan da suka da ce. Ita ma kuma Fulani Umaima a ranar da suka tafi a ranar ta dira wurin Bamaguje ta shimfiɗe masa bukatunta, kuma take ya zartar mata da su, haɗe da jinjina mata bisa aikin Baiwa Maimuna da ta aiwatar ba tare da an samu matsala ba. Sai dai abu ɗaya da ya sanar mata ne ya nemi hargitsa kwanyarta har ta koma gida ta gagara runtsawa tana tunanin makomar abin da zai biyo baya.



*Masu ganin laifin Fulani Babba na rashin yin addu'a kada ku manta labarin an sanya ya faru a shekaru saba'in baya da suka wuce (1953) Kun ga a lokacin ilimin addini bai yawaita ba, ba kamar yanzu da ilimi ya zaman ruwan dare ba. A mafi yawan wancan lokacin, camfi da tsubbace-tsubbace sun fi ƙarfi a kan yawaitar addu'a, babu wayewar kan da idan abu ya same ka kace bari ka duƙufa ba dare ba rana ka kai wa Allah kukanka.*


_Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚
07062062624
[10/4, 11:48 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA*


©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.

SHAFI NA SHIDA

Ajiyar zuciya Fulani Umaima ta sauke ta zauna a gefen gado, wani irin gumi ya fara tsattsafo mata.

"Binciken da nake kan yi dangane da abin da kike ɗauke da shi a cikin cikinki, na shafe tsawon kwanaki ina bincike har yau na gagara sanin mene ne a ciki. Kullin duhu nake mai ɗauke da rashin alkairi, duhu ne mai ɗauke da tururi da ke ƙone duk wani makusancinsa. Ba ke kaɗai ba ni kaina ina da burin sanin me za ki haifa domin amfanar gobena. Ina buƙatar Magaji a halwar tsafina Umaima."

A razane ta ɗago tana kallonsa, "Ban gane kalamanka ba Bamaguje, me ye alaƙar abin da yake cikina da gadon halwar tsafinka?" Bamaguje ya saki murmushi. "Wannan sirrintaccan sirri ne tsakanina da mahaifiyarki, ba alaƙar abin cikinki ya kamata ki tamabaya ba. Amma mu jirayi lokacin kin san ko ba daɗe ko ba jima akwai lokacin da ya za ta ɗakin ƙanwa."

Sallamar Baiwa Salame ta katse Fulani Umaima daga duniyar taunanin abin da suka tattauna da Boka Bamaguje. Ba ta amsa mata ba don haka Baiwar ta koma, Fulani Umaima ta miƙe ta ci gaba da kaiwa da kawowa damuwa cunkushe a zuciyarta. Kamar wacce aka tsokara haka ta miƙe ta ƙarasa ta ɗauko akwatin sirrinta, ta ɗauko littafin da Bamaguje ya bata. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta buɗe shafin da ta tsaya da karatu.

Na jima a tsugunne gaban Uwar Bayi ina tsammanin kalamanta har sai da na fara yanke ƙauna da samun abin da nake buƙata, ba zato na ji muryarta a tsakiyar kaina.

"Hidaya labarinki cike yake da almara, al'ajabi da ban mamaki. A tsammanina ni ce mace ta farko da na fara tozali da ke a cikin masarautar nan, ban sani ba ke 'yar cikinta ce ko akasin haka. Abu ɗaya na sani watarana na tafi isar da saƙon Fulani Hauwa na gan ki tsaye a jikin bishiyar kukar da ke bayan ɗakunan Bayi kina rusa kuka, gudun kada na yi latti a aiken da aka yi mini ya sa sai da na kai na dawo har lokacin ba ki daina kuka ba. Da yake a ranar an shigo da sababbin Bayi sai na yi tsammanin 'yar ɗaya daga cikinsu ce yawo ya kawo ta nan take kuka ta gaza gane hanya wurin mahaifiyarta. Sai na riƙe miki hannu muka wuce sashen Bayi na ƙaraci cigiya babu wanda yace 'yarsa ce, to da yake a cikin Bayin da aka kawo akwai wasu mata biyu da suka rasu sai na yi tsammanin mahaifiyarki na ɗaya daga cikinsu. Amma daga baya sai na ga 'yan uwansu suna cewa sam ba tare da su aka kawo ki ba, wannan dalilin ya sa kika ci gaba da zama a sashen Bayi ba tare da iyaye ba."

Kalama Uwar Bayi suka zo ƙarshe a daidai lokacin da ni kuma bakin ƙomar idaniyata ta ɓalle, sai da na yi kukana mai isata na dube ta. "Haka zan ƙare rayuwata ba tare da sanin makomata ba."

Uwar Bayi ta wara hannuwa. "Abin da na sani kaɗai na sanar da ke, idan Allah ya sa akwai rabo sai ki gansu ko a nan gaba ne." Yau ita ce rana ta farko da na ji daddaɗan kalamai daga bakin wani daga cikin Bayin da nake mu'amala da su, don haka na ƙirƙiri murmushin da bai kai zuci ba na furta. "Shi kenan ina godiya Uwar Bayi da wannan bayanin naki." Babu wanda ya sake tanka mini haka na tashi jiki a sanyaye kamar kazar da aka jefa da wuƙa na koma mazaunina na farko na zauna ina jin zuciyata babu daɗi. Ina jin su suka ci gaba da hirarsu sai dai ko kaɗan ba na fuskantar koda kalma ɗaya, zuciyata ta yi nisan kiwo a fannin tunani da na gagara janyo ta balle ta gane in da hirarsu ta dosa.

Wani farin tsoho mai ɗauke da farin gemu na gani yana tunkaro ni, tsananin kammanin da muke yi da shi ya sa na tsaya cak ina kallonsa. Tun da na zo duniya ban taɓa ganin mai kamceceniya da ni ba, ban yi tsammanin ya kusance ni ba don haka na ji hannuwansa a cikin nawa.

"Kada ki damu da sai kin san wace ce ke, kina da kowa kuma wannan masarautarki ce gadonki ce halak malak, sai dai ina mai ta'ajibin sanar da ke har duniya ta tashi ba za ki ga mahaifiyarki ba. Ni ne mahaifinki! Ni ne mahafinki!! Ni ne mahaifinki!!!"

Firgigit na farka daga mafarkin da nake yi, na juya ina kallon yadda mutane ke baccinsu hankali kwance. Mamaki ya kama ni, cikin damuwa na furta.

"Ya aka yi ka zama mahaifina? Kuma me ya sa kuka guje ni." Kamar alamara na ji an furta mini.

"Ba mu guje ki ba, mun kawo ki karagarki ne don ki karɓi abarki."

Waige-waige na fara yi don ganin mai tanka mini a cikin tsohon daren nan, har na yunƙura zan tashi sai na ji tsoro ya mamaye ni, ba shiri na koma na zauna bacci ya ƙaurace mini. A lokacin da bacci ya fara fisga ta na ji Uwar bayi tana tashinmu cikin hargowa da masifa kamar yadda ta saba duk asubar fari.

A haka na ci gaba da gudanar da rayuwa cikin rashin daɗi, rashin 'yanci da ƙangin bauta. Mu Bayi ba mu da wani gata ba musan ci mai kyau da sha mai kyau ba, ana cikin haka watarana saƙo ya iso gare mu ana san Uwar bayi ta sake zaɓen Bayi ta kai sashen Fulani Hauwa kulu, haka kawai na ji gabana yana tsananin faɗuwa. Aka saka mu muka yi layi cikin tsautsayi ƙaddara ta yarfo mini hannunta, Uwar Bayi ta zaɓa har da ni a cikin mutane ukun da Fulani Hauwa take buƙatar ƙari.Tun da nake rayuwa a cikin Masarautar ban taɓa shiga sashen Fulani ba, hasali ma ban taɓa tozali da ita ba, sakamakon rashin imanin da nake jin ana faɗa game da ita. Wannan ta sa nake takatsantsan a kan abin da zai sa na kai kaina sashenta. Tun da muka dumfari hanyar sashen Fulani nake jin jikina yana yi mini wani irin zafi, hayaniya na fara ji sama-sama a kaina ga wani kiɗan tambura da nake ji yana tashi a tsakiyar kunnuwana. Sai dai yadda na lura ni kaɗai nake jin waɗannan baƙin al'amuran da ke yi wa duniyana dirar mikiya.

Take gumi ya fara keto mini sakamakon yadda nake jin zafin na ratsani kamar wacca aka tsire a tukubar tsire. A babban ƙofar rumfar (Falo) Fulani Hauwa na coge, sakamakon yadda nake jin ana fisgata. Hayaniyar da nake ji ta fara rikiɗa zuwa muryar da nake jin tamkar na taɓa sanin mamallakiyar muryar.

"Barka da zuwa Sarauniya."
Na ji an furta. Waige na fara yi amma ban ga kowa ba, na riƙa jin busar sarewa a tsakar kaina ba tare da na ga masu yi mini ba. Ina nan tsaye na ji Uwar Bayi na faɗin.

"Ku yi hanzari kada ku fusata Fulani kuke tafe laƙai-laƙai kamar marasa laka a jiki." Da sauri na ci gaba da tafiya har muka ƙarasa babban rufar Fulani da ta ƙayatu da kayan alatu kala-kala. Kaina na ji ya yi girma wata irin ƙasaita, isa da tsantsar izzar mulki na ratsa ni, da ƙyar nake taku cikin ƙasaita. Uwar Bayi da sauran Bayin da muka taho tare suka tsaya cak a bakin wata mashinfiɗa wacce bayi suke tsayawa idan sun shiga wurin Fulani Hauwa kulu. Ban kalle su ba na zarce kan ƙasaitacciyar karagar da ke cikin falon, na zauna ina kallon su Uwar Bayi ɗaiɗai. Da zamana na ji wani abu ɗau! Yana zagaye ƙoƙon kaina. Uwar Bayi kusan mutuwar tsaye ta yi ganin ɗanyan aikin da na aikata, bakinta na rawa ta furta mini.

"Hidaya...hankalinki ɗaya kuwa? Kin san a fadar wacce kike?"

"Ya kamata ki gyara linzamin harshenki, idan ba haka ba sai na sa an datse shi nan take. Wannan fadata ce..." Ashar ɗin da Fulani Hauwa kulu ta saki ya katse kalamaina, na dube ta cikin tsadaddiyar shigarta ina ƙare mata kallo.

"Uban waye ya halatta wa wannan ƙasƙantaciyyar zama a karagata?" Cikin isa da ƙasaita na ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, kamar ba zan amsa ba na ɗago ina kallonta a wulaƙance. "Wannan karagar iyaye da kakannina ce don haka ki gyara kalamanki."

Na lura da razani a saman fuskarta, ɗan yatsanta na rawa ta nuna ni. "Ta tabbata ke ce Hidaya ko?" Na jingina da jikin kujerar na furta. "Ba tsammani ba ne ni ce Gimbiya Hidaya." Wata gwauruwar ajiyar zuciya na ji ta sauke. "Tabbas da alama tarihi zai kuma maimaita kansa.

"Tarihi tuni ya sake maimaita kansa tun da gani na wanzu a gabanki."

Fulani Umaima ta rufe littafin tana jin kanta na sarawa don a kullin labarin Hidaya ƙara hargitsa kwanyarta yake. Ta wurga shi cikin akwatinta tana sakin tsaki a fili don ba ta jin za ta sake ci gaba da karanta wannan rikitaccan labarin.

Komawar su Yaya Halima Masarautarsu da kwana ɗaya labari ya dawo wa Fulani Babba na sabuwar lalurar da ta afka wa Yaya Halima na kurumcewa da makanta, hankalin Fulani Babba ba ƙaramim tashi ya yi ba. Da yake jego take yi babu damar ta tafi dubiya haka ta zauna ta ci kukanta a cikin ɗaki, ta sake ayyanawa zuciyarta ko da wasa ba za ta sanarwa da mahaifiyarta halin da take ciki ba don kar damuwa ta yi mata yawa.

BAYAN SHEKARA GOMA

Tafe suke a cikin wani baƙin ƙasurgumin daji mai matuƙar hatsarin gaske, su kansu sukan yi takatsantsan wurin shiga irin waɗannan dajijjikan sakamakon miyagun hallitu da iskokin da ke cikinsa.

"Mai gado wai ni kam kin taho mini da baƙar bakata?" Umaru ya faɗa yana sake leƙen wani koren maciji da ke saƙale da wata koriyar bishiya. "A'a Malam

4 Comments On SHU'UMAR MASARAUTA
avatar
zainab-8-2

1 year ago

Reply

Tnx

avatar
asiya-mashi

1 year ago

Reply

Allah ya kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to asiya-mashi

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Ameen

Please Login or Register in order to submit comment