Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki. Wata ƙasar ya ci wata kuma ya burtune jikinsa da ita, tana ji tana gani bayan ta gama kallonsa ta fice daga ɗakin. Abin ka da gidan masarauta take labarin kai Abubakar gidan yari ya gama zagaye gidan kowa da abin da yake tofawa, sai dai mafi yawa daga cikin shakkun Fulani Umaima ya hana su faɗar gaskiyar abin da yake cikin zuciyoyinsu.

"Allah ya taimake ki ni fa don kada a ce na saki linzamin harshena amma Allah ya sani na fara ɗora zargi a kan Fulani Umaima. Lamarin zamantakewar da ke tsakaninki da Takawa akwai fa ayar tambaya." Jakadiya ta yi wa Fulani babba maganar tana yin ƙasa da murya. "Jakadiya tafi kanki tsaye ba mu fahimce ki ba." Jakadiya ta sake yin ƙasa da murya.

"Bari na fito miki a mutum Fulani, an ya kuwa Fulani Umaima ba ta bi ta ƙarƙashin ƙasa a kan Takawa ba, duba da yadda take cin karen ta babu babbaka a gidan nan kamar wacce ta wanke masa hannu aka. Yanzu musakin yaron nan Bukari me ya yi da zai fuskanci zama a sashen gidan ajiya da gyaran hali." Jin haka ya sa hawaye ya zubo wa Fulani Babba. A fakaice Jakadiya ta saki murmushin cin nasara, don babban burinta ita ma bai wuce ta samu sanadin dandalar arziƙin da su Fulani suke ci ba a matsayinsu na matan Sarki. "Jakadiya al'amurana a yanzu haka na miƙa su a wurin Ubangiji, duk ma wanda ya nemi ya ƙuntata wa rayuwata Allah ba ya bacci yana sane da abin da yake faruwa." Jakadiya ta taɓe baki a fakaice.

"Amma ya kamata ke ma ki tashi tsaye domin kin san da sanyin safiya ake kama fara." Fulani babba ta ɗan sauya fuska don haka kawai ta ji ba ta aminta da waɗannan shawarwarin na Jakadiya ba.

"Ni fa hatta ciwon yaron nan wallahi na jima da ɗora zargina a kan Umaima, saboda Allah yaro shi ba aljanu ba amma an mayar da shi wani iri. Kwanaki fa har barbaɗe na ga tana yi a turakar Mai martaba wai don ya daina jin ɗanɗanonki." A ɗan razane Fulani babba ta dubi Jakadiya sai kuma ta haɗe fuska. "Jakadiya muna buƙatar hutawa a ba mu wuri." Ganin babu fuska ya sa Jakadiya ta fice tana wurgawa Fulani babba mugun kallo.

"Sakarai da ba ta gaji arziƙi ba kya ƙare a wahale cikin warin jiki da fitsari." Jadiya ta faɗa cikin jin haushin rashin samun nasara a kan Fulani Babba bayan ta fita waje.



Wacce ta shirya biyan kuɗin karatun ci gaban littafin *SHU'UMAR MASARAUTA* Ƙofa buɗe take, za ta iya turowa ta wannan Acc ɗin da ke ƙasa domin free pages na gab da ƙarewa. Waɗanda suka fara biya su min afuwa zuwa lokacin da zan buɗe group bayan na kammala free pages.

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
[10/4, 11:49 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA*


©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.

*Masu ƙorafe-ƙorafe ta pc da groups zan rage 100 daga yau zuwa ranar da zan gama free pages. Free pages za su ƙare a page a 10 daga yanzu zuwa ranar duk mai son karanta littafin za ta turo 400*

SHAFI NA TAKWAS

RIGAR ARƊO

A gajiye tuɓus suka dawo gida sakamakon yawon kiwon da suka je cikin dokar daji, zamansu babu wuya wata farar dattijuwa ta ɗauko ƙorai guda biyu sai da ta fara zuba nono a cikinsu ta miƙa wa mai gidanta Baffajo. Ta jima a tsugunne tana jiran ya karɓa tana ɗagowa ta lura da yadda ya dulmiya cikin kogin tunani, a sanyaye ta kai hannu ta taɓa shi.

"Yanzu Baffajo ba za ka daina wannan tunanin ba? Idan kai kana yi ni kuma sai ƙaƙa?" Ajiyar zuciya ya sauke. "Inna wuro aradun Allah lamarin yaron nan ƙara ci mini tuwo a ƙwarya yake, yanzu a ce ɗan mutum ba shi da abokan rayuwa sai gidan tururuwa da dokar daji? An ya Inna wuro ba za mu kai Kamalu wurin Malamijon farar riga ba?" Inna wuro ta yi jim cike da damuwa sanna ta furta, "Eh to hakan ma wani abu ne amma ni sai na ga kamar har da sabon shiga dawa..."

"Kayya mu ba a dawa muka yi rayuwa tun daga ƙuruciya ba? Kin manta a lokacin baya tsakiyar dare nake tsintoshi a bayan rumfar can wurin shurin da ke gabas da shi." Kamalu ya ɗago fuska a haɗe don jin abin da Iyayensa suke furtawa, motsa baki yake kamar wanda zai yi magana, amma sai ya gimtse ya kawar da kai gefe. "Kamalu kai fa ba yaro ba ne a ƙalla shekarunka sun haure goma, mahaifinku girma ya kama shi ba ka ganin sauran 'yan uwanka ba haka suke ba." Kamalu ya sunkuyar da kai ƙasa ba tare da ya kalle su ba, A'iru da ke gefe ta furta.

"Kwarankwasa dubu rannan har gani na yi yana ɗibar wani abu a kan gidan tururuwa yana sha, dubi wancan zobe." A'iru ta yi maganar tana nuna hannun Kamalu mai ɗauke da wani zoben azurfa mai ɗauke da wani irin zane.

"Da bakinsa ya ce mini tsintarsa ya yi a kan shuri wai gadon Masarautarsu ne." A razane su Inna wuro suka dube shi, Baffajo ya ce. "Kamalu wa ya ba ka wannan zoben?"

"Tsintarsa na yi." Kamalu ya furta kai tsaye ba tare da ɗago ya kalle su ba. Haushi ya fara kama Baffajo don haka ya ce, "Kai Kamalu hai ka shiga taitayinka, ba ka san dawa ba ko?" Kafin Kamalu ta ya ba shi amsa daga sama suka fara jin gudun dawakai da iface-ifacen mutane, kafin su yi wani yunƙuri tuni waɗansu Dogarai da sojojin masarauta suka farmusu cikin shammata suka riƙa taɗe su suna ɗaure su da wasu murtuka-murtukan igiyoyi a jikin manyan itatuwa. Lokaci ɗaya garin ya hautsine ban da ƙura babu abin da yake tashi, waɗanda suke da rabon tsira tuni suka shuɗa daji. Waɗanda aka riga da aka rubuta zanen ƙaddararsu kuma tuni aka damƙe su, a cikin waɗanda suka tsira har da Salele ɗan gida Baffajo. Shi kuwa Kamalu ko da ya ga abin da yake faruwa ko gezau bai yi ba, yana nan zaune wani Dogari ya isa gare shi ya fisgo shi da niyyar taɗe shi, ɗayan hannun nasa ya sa ya bigi gefen hannun Dogari, wata irin azaba ya ji tamkar an zuba masa ruwan dalma. Da kansa ya ƙarasa wurin wasu Dogarawa da ke tsaitsaye suna ɗaure ragowar mutanen da aka kama wanda ko tantama babu sun riga da sun zama bayi. Sai da aka ɗaure Baffajo da waɗansu mutane biyu sannan aka ɗaure Kamalu, a ɓangaren mata kuma tuni aka ɗaure Inna wuro da sauran mutanen da ke cikin rigar. Kafin wani lokaci rigar ta yi fayau sai kukan dabbobi da ƙananan tsuntsaye da ke tashi.

ƘAUYEN GANGARE

Jiki a matuƙar sanyaye suka ƙarasa cikin ƙauyen gangare hannun Mai gado ɗauke da jaririya, tun daga ƙofar gari aka fara jefa musu tambayoyin inda suka samu jaririya sabuwar haihuwa. Sai dai amsa ɗaya suke bayarwa tsintarta suka yi a cikin gona, da haka suka samu suka ƙarasa gida. Da zuwansu babu jimawa gidansu ya cika maƙil da mutane, wasu na taya su murna ya yin da wasu suka fara tsegungumi da ƙananan maganganu. Wani tunani Umaru ya yi take ya sa Mai gado ta ɗauki jaririya har ta ɗora ruwan da za ta yi mata wanka ya dakatar da ita kai tsaye suka wuce gabaɗaya wurin Mai gari. Umaru yana zuwa fadar Mai gari ya zube ya kwashi gaisuwa sannan ya gabatar da jaririyar hannunsu da mahaifiyarta ta yi mata laƙabi da Jawahir, bayan ya tsahirta ya karɓe ta daga hannun Mai gado ya miƙa wa Mai gari, sanƙira yana raɓe a gefensa. Tun da aka ɗago jaririyar Malam Malmo ya zura mata idanu ko ƙiftawa ba ya ni, wannan ya haddasa fargaba da tashin hankali a zuciyoyin Mai gado da Umaru, sakamakon sanin Malam Malmo sarai da mugun aikinsa. A sakaye Umaru ya ɗan yi gyaran murya ya furta.

"Allah shi ba ka yawan rai yanzu haka Mai gado ta ɗora mata ruwan wankan da za a yi mata wanka da shi." Mai gari ya jinjina kai tare da yi musu nasiha a kan su riƙe ta da riƙon amana. Su Umaru har sun miƙe bayan mutane sun watse yana waigawa ya ga Malam Malmo yana yi wa Mai gari raɗa a kunne, haka kawai ya ji zuciyarsa ba ta aminta da wannan raɗar da yake yi wa Mai gari ba. Tsawar da sanƙira ya yi masa ce ta sa shi zura takalman fatarsa ya yi gaba jiki a sanyaye kamar kazar da aka watsawa gishiri.

"Mai gado ina tsoron Malam Malmo a kan yarinyar nan kada fa a ce ya gano wani al'amari game da ita." Umaru ya faɗa bayan Mai gado ta yi wa Jawahir wanka tana shafe mata jiki da mai. "Ni kaina ina tsoro amma In shaa Allah babu abin da zai faru sai alkhairi." Wannan ƙawarin gwiwar da ya samu daga wurin Mai gado ya sa ya tashi ya fita don tatso wa Jawahir nonon akuyar da za a shayar da ita. Sannu a hankali suka ci gaba da rainon ta, tun suna ɗari-ɗari da ita har suka saki jikinsu sakamakon babu wani abu da suke gani na ban tsoro a tattare da ita. A ɓangare ɗaya kuma wata irin soyayya suke nuna mata, ga shi sai ta wuni ba a ji kukanta ba idan ba yunwa take ji ba.

Abu ɗaya ne ya fara damun Mai gado da yake faruwa da Jawahir cikin dare, duk lokacin da ta farka don ta ba ta nonon akuya da dare sai ta ga wani baƙin jini ya tsattsafo a goshinta, idan kamar bacci ya ɗauke ta har asuba ta yi, sai da ga goshin na ta ya yi ɗan duhu amma babu jinin a jiki, zuwa wayewar gari kuma sai ta nemi komai ta rasa jinin ya washe. Tun tana barin maganar a ranta har ta taɓa tashin Umaru ta sanar da shi, shi kansa ya yi mamaki amma gudun kada ƙilu ta ja bau! Ya ce su zuba wa sarautar Allan ido tun da ba ta kuka wataƙila abin ya mata ciwo. Kwanan Jawahir goma Mai gari ya aika a kira masa Umaru, tun da Umaru ya ji kiran Mai gari gabansa ya faɗi har sai da Mai gado ta ƙarfafa masa gwiwa sannan ya nufi gidan Mai gari cikin wasuwasi.

Yana zuwa aka yi masa iso har cikin shagonsa da yake hutawa a soro, ganin Malam Malmo ya sake tsinka zuciyarsa. Dole ƙanwar na ƙi ya zuba wa fuskarsa murmushin yaƙe cike da girmamawa ya gaishe su. "Umaru ka sani a gaban Mai gari kake don haka muke son duk maganar da muka tambaye ka ta zama gaskiyarka za ka faɗa. Wace ce yarinyar da ka zo da ita kuma a ina ka same ta?" Malam Malmo ya jefa masa tambaya. "Allah ya baka yawan rai wallahi tsintarta muka yi..."

"Idan tsintarta kuka yi ina mahaifiyarta? Ko kuna nufin jaririya ɗanyar haihuwa za ta kawo kanta ne?" Mai gari ya katse Umaru. Shiru Umaru ya yi yana tsoron kada ya ba da kai bori ya hau, yana cikin nazari ya tsinci kalaman Malam Malmo.

"Sanin kanka ne Umaru duk yankin nan babu wanda ya kai ni sanin sirrin tsafi da sihiri, na bincika kuma na gano waɗansu bayanai tun ranar da na ɗora ƙwayar idona a kan yarinyar nan. A zahiri ne kuke ganinta ƙanƙanuwa amma a baɗini basarakiya ce, shu'uma ce kuma tana ɗauke da rikitattun al'amura. Ita ba kamar kowa ba ce dalilin da ya sa mahafiyarta ta yo gudun fanfalaki da ita kenan daga cikin danginta, mukuma a ɓangarenmu na masu aikin tsubbace-tsubbace wannan yarinyar ta kasance tamkar taki ce da ke farfaɗo da shukar da ke cikin gona. Ya zama wajibi ka mallaka mana ita domin cikar muradinmu, a zahiri Mai gari zai karɓi riƙonta ta koma gidansa da zama. A baɗini kuma zan aiwatar da aikin da za ta kasance a ƙarƙashin ikona. Sharaɗi na biyu ya zama dole ka nuna mini daidai wurin da gawar mahaifiyar yarinyar nan take, idan ba haka ba wallahi sai na shayar da kai ruwan mamaki."

Gumin da ya shiga keto wa Umaru ne ya bankaɗa sirrin da ke cikin zuciyarsa, cikin matsanancin tsoro ya ɗago jiki na rawa ya furta. "Duk abin da kuka buƙata haka za a yi ranka shi daɗe, da kai da kaya duka mallakar wuya ne." Malam Malmo ya saki murmushi cikin jin daɗi don ya ga tsoro malale a saman fuskar Umaru don haka ya furta.

"Ba zan barka haka ba Umaru dole za mu aiwatar maka da naka tukwici mai tsoka." Umaru ya saki murmushin yaƙe yana godiya, sannan Mai gari ya sallame shi.

Kamar zai tashi sama haka ya ƙarasa gidan yana alla-alla ya ɗauko Jawahir ya kai musu ko ya yarda ƙwallon magwaro ya huta da ƙuda.

Masarautar Huddam

A ranar da aka kai Abubakar ɗakin da ke ɓangaren gidan ajiya da gyaran hali ko runtse Fulani babba ba ta runtse ba, baƙinciki da ɓacin rai ya mamaye zuciyarta. Sai gabannin asuba sannan ta samu hawaye ya zubo mata, zuciyarta cunkushe da ɓacin rai. Wani abu da ya so ɗaure mata kai ganin ta wayi gari lafiya ƙamas babu fitsari a shimfiɗarta, ba ta ankara da haka ba sai da aka kira sallar asuba da za ta yi wanka kamar yadda ta saba duk asuba sai ta wanke fitsarin jikinta. Amma wannan ranar da ta kwana idonta biyu sai ta ga babu komai a jiki, mamaki cike da zuciyarta ta yi alwala bayan ta gabatar da sallah a gurguje ta nufi sashen da Abubakar yake kwance ɗauke da kayan sawar da za ta sake masa kamar yadda ta saba tsaftace shi.

"Waye nan?" Aka furta mata cike da tsawa a lokacin da ta ƙarasa jikin babban ƙauren ƙofar. Baƙin ciki ya kama ta jin ƙasƙantaccan bawa na buga mata tsawa, da ace a sashen ta yake babu wanda ya... "Ina magana waye nan?" Kamalan Dogarin suka katse mata tunani. Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta furta. "Fulani ce na zo wurin Abubakar." Cikin girmamawa Dogarawan suka zube. "A gafarce mu uwar gijiyarmu, muna neman afuwar saƙon da zai fito daga bakunanmu." Zuciyar Fulani ta fara azalzala kamar za ta hudo ƙirjinta, fargabarta ɗaya kada su ce mata wani abu game da Abubakar. "Allah ya taimake ki, ki yafe mu amma Takawa ya ja kunne da kada a sake buɗe ƙofar nan har sai hantsi ya ɗaga wurin ƙarfe tara." Da sauri ta dube su. "Yaushe ya bada wannan umarnin?"

"Ranki shi daɗe jiya da dare."

Sai da ta haɗiyi yawu mai ɗaci sannan ta miƙa musu kayan hannunta da akushin abincin da ta taho da shi.

"A gyara Abubakar da shi a tabbatar da an yi masa wanka, wannan abincinsa ne." Jim suka yi sannan ɗaya daga cikinsu ya furta. "Allah ya taimake ki koda mun karɓi kayan nan sai lokacin da Takawa ya zartar za mu buɗe ƙofar, amma a gafarce ni ranki shi daɗe." Wani irin kukan takaici ne ya taso mata, gudun kada ta bar abin faɗa ya sa ta juya da sauri ba tare da ta amsa musu ba. Fulani babba na zuwa sashenta ta fashe da matsanancin kuka, tana tsaka da kuka ta ji Khadija mai kimanin shekara goma sha shida ta dafa kafaɗarta. "Ummi me ya sa kullin cikin kuka kike? Ummi kin san idanun masarautar yana ko ina a lungu da saƙo don Allah kada ki bari a samu a bin faɗe, komai ya yi tsanani maganinsa Allah kamar yadda na ji kina faɗa. Wuya ba ta kisa na san a kan Sadiq kike wannan kukan don Allah ki kwantar da hankalinki na tabbata babu abin da zai faru da shi." Khadija yarinya ce mai nutsuwa da sanin ya kamata, idan tana magana kamar babbar mace, a hankali ta goge wa mahaifiyarta hawaye ta ci gaba da tausarta har damuwar da
take ciki ta yaye. Haka ta haƙurƙurtar da zuciyarta har lokacin da ya dace, sannan ta ɗauki kayan da kanta ita da Khadija suka nufi wurin Abubakar. Tun tasowar Abubakar ko da wasa Fulani ba ta taɓa yunƙurin ba wa wata baiwa hidimarsa ba, haka ta sawa ranta har zuwar ƙarshen rayuwarta za ta ci gaba da kulawa da shi ba tare da ta sare ba. A lokacin da suka ƙarasa ɗakin duk da kasancar safiya ce ƙudaje ne suka fara yi musu maraba, a kwance suka same shi kamar yadda Fulani ta bar shi da dare sai dai ya fitsari da kasaye duka kayan jikinsa. Ƙudajen da ke kai-kawo a kansa yake ɗaga kai yana cafko duk wanda ya zo hannunsa ya kai bakinsa ya cinye. A fakaice Khadija ta share hawayenta, sannan suka gyara masa jikinsa. Khadija ta kira Baiwa Salamatu ta damƙa mata kayan Abubakar don a wanke su, sannu a hankali Fulani babba take ba shi abinci wani ya karɓa wani ya zubar bayan sun gama suka tashi suka rufo shi suka fito daga sashen zuciyoyinsu babu daɗi.

Tsaye take hannunta ɗauke da wata irin sharɓeɓen tsafaffiyar takobin da Boka Bamaguje ya bata don kare kanta da shi, ta hango ƙurar ɗan matashin yaron ya tunkaro ta da bai fi sa'an Muhsin ɗin ta a shekaru ba, duk yadda ta so hana shi shiga cikin ƙofar Masarautar Huddan sai abu ya gagara. Ganin haka ya sa ta zaburo da sauri kafin ta aiwatar da abin da yake ranta ya sa hannuwansa biyu ya mauje ta, ta faɗi ƙasa warwasa. Ɗagowar da za ta yi ta hangi Baiwa Maimuna a bayansa tana sakar mata murmushin mugunta, sai wata inuwa da ta gagara tantance wace ce ita. "Ban yafe miki abin da kika yi mini ba kuma sai na ɗauki fansa a kanki." Rufe bakin Baiwa Maimuna ta sa hannu ta fara jan Fulani Umaina a ƙasa kanta sai kurjewa yake jini na zuba, ko da ta hango Bamaguje yana tsaye a gefe yana kallonsu cikin magiya da tashin hankali ta fara roƙonsa. "Da kai kaɗai na dogara Bamaguje ka taimaka mini za su kashe ni." Wata irin mahaukaciyar dariya ta ga ya bushe da ita, ya juya mata baya ya fara tafiya yana faɗin. "Na riga na gaya miki kin yi sake wannan yaron ba kamar ɗan uwansa yake ba."

Firgigit Fulani Umaima ta farka daga mummunan mafarkin da ta yi, a 'yan kwanakin nan ta rasa dalilin waɗannan miyagun mafarkai nata. Kusan kullin sai ta yi mafarkin wannan yaron yana barazana da rayuwarta. "Waye wannan da yake ƙoƙarin kutsowa cikin rayuwata har yake neman dagula lissafina?" Ta tambayi kanta ba tare da ta san amsar tambayarta ba. Ƙirjinta ya buga a lokacin da ta tuna jaririn da baiwa Maimuna ta fitar da shi yana nan a doron ƙasa, "Ƙarya ne ba shi ba ne! Ba zai taɓa razanar da ni ba." Fulani Umaima ta furta tana kai wa da kawowa.


*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
[10/4, 11:49 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA*


©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.

*Masu ƙorafe-ƙorafe ta pc da groups zan rage 100 daga yau zuwa ranar da zan gama free pages. Free pages za su ƙare a page a 10 daga yanzu zuwa ranar duk mai son karanta littafin za ta turo 400*

SHAFI NA TARA

Ayarin dakarun masarautar da ke tafe da su Baffajo tafe suke cikin gajiya sakamakon doguwar tafiyar da suka yi, a farfajiyar wata bishiya suka yada zango suna hutawa sai bayan sun huta sannan suka ci gaba da tafiya, cikin zuciyarsu kowa da abin da yake ayyanawa. Ganin magriba ta fara dosowa ya sa suka yanke shawarar kwana a cikin dajin washegari da asuba sai su ɗora daga inda suke tsaya.

Ƙauyen Gangare

Ganin yanayin da Umaru ya koma gida da shi ya sa Mai gado shan jinin jikinta.

"Mai gida ya kuka yi da Mai gari na ganka duk a sanyaye." Ƙasa ya yi da murya ya furta. "Ina yarinyar nan take? Zan kai ta gidan Mai gari" Kallon rashin yarda ta bi shi da shi ta sake gyara goyon Jawahir da ke bayanta. "Me za ta yi a gidan."

Kamar zai yi kuka Umaru ya ce, "Malam Malmo Mai gado ban san ya za mu yi ba, sun buƙaci na mallaka wa Mai gari ita." Rass! Ta ji gabanta ya faɗi, sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta yi ƙasa da murya. "Ba zan iya rabuwa da Jawahir ba Mai gida, na san Malam Malmo sarai ba zai wuce tsubace-tsubbace zai yi da ita ba." Umaru ya waiga kamar wanda ake kallo duk a tsorace ya ce. "Ya zamu yi yanzu? Mene ne mafita?"

Masarautar Huddam

Wuni guda haka Fulani Umaima ta yi shi cikin rashin ƙwarin jiki, ba ta san dalili ba amma haka kawai za ta ji gabanta na faɗuwa. Har ta so dannewa ta ji zuciyarta na azalzala ba za ta iya jure rashin zuwa wurin Bamaguje ba.

Tsufansa ya sake fitowa sosai don jiki da hannuwansa har karkarwa suke yi.

"Ta zo duniya da ƙarfin iko, shi kuma yana gab da dawowa gidansu na gado."

Bamaguje ya furta bayan ya gama sauraron ƙorafin Fulani Umaima. Ta ɗago a hargitse bakinta na rawa, ƙirjinta na dakan lugude. "Su waye? Kuma daga ina suke."

"Garaje ga dami, daɗina da ke gaggawa Umaima. Na ɗauka za ki tambayi alaƙar shi da masarauta da ita kanta yarinyar." Ajiyar zuciya ta sauke. "Tamkar tagwaye haka suka kasance tsakaninta da Hidaya, sai dai waccan ruwan sanyi ce salam a kan wannan. Ban san a wanne muhalli zan tirke ta ba, abu ɗaya na sani ita ta kasance daga cikin wata irin zuri'a masu matuƙar hatsarin gaske. Na ga takobi a cikin jininta sannan wuta na gewaye sashenta, takaicina ɗaya Mahaifiyarta ta riga da ta binne duk wani al'amari da sirrin da ke ƙunshe a cikin rayuwarta. Daga ni har sauran matsafan duniya duk wani bincike da za mu yi ba za mu tantance takamaiman ainihin tushenta ba. Sai dai kuskure guda mahaifiyarta ta tafka wanda da shi kaɗai za mu iya cin galaba a kan wannan yarinyar."

Cike da zumuɗi Fulani Umaima ta furta. "Mene ne shi? Duk wuya duk tsaninsa zan nemo shi..."

"Bincike ya bayyana mini tana da matuƙar tasiri a rayuwarsa. Ina nufin jaririn da kika sa Maimuna ta fitar da shi shekara goma sha ɗaya baya, shi yake gab da shigowa gidan sarautarku. Sai dai kuma ita da shi za su kasance tamkar wuta da ruwa a fannin gaba, kowannensu ba zai ƙaunaci ɗan'uwansa ba. Shigarsa tamkar dasa nakiyar da ke tashin zamani da alƙaryarki ne, ba tun yau ba; na gaya miki shi ba kamar ɗan uwansa ba ne. Ruhinsa ɗauke yake da zaratan dakarun da ke sarrafa zuciya da tunaninsa, tun ranar haihuwarsa na fahimci zanen ƙaddararsa ya wanzu dalilin da ya sa na baki shawarar matse kunamar nan a cikin bakinsa, ashe tagwaye ne halwar tsafina ya gagara nuna mini. Tun yana jariri ya sauka a fadar Sarkin fararen aljanun doron ƙasa, da ke tsakiyar dajin Wuruju a daidai wurin da Baiwa Maimuna ta dire shi. Sun naɗa masa kambun da babu mai iya sauke shi sai mutum ɗaya

4 Comments On SHU'UMAR MASARAUTA
avatar
zainab-8-2

1 year ago

Reply

Tnx

avatar
asiya-mashi

1 year ago

Reply

Allah ya kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to asiya-mashi

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Ameen

Please Login or Register in order to submit comment