Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nata ya san ba na lafiya ba ne. Jikina ne ya ɗauki tsuma sakamakon ganin halin da take ciki kace-kace da jini, a gefe ɗaya mutane daga jinsin maza da mata sun yi carko-carko a kanta suna kallon halin da take ciki. A gabanta na tsugunna raina ya kai ƙololuwar ɓaci, na dube ta fuska babu walwala na furta "Waye ya yi miki haka Kadala?" Ilahirin jikinta rawa ya ke don haka na kama hannunta na haɗa su da nawa na sake furta, "Babu abin da zai faru da ke ki gaya min waye ya yi miki haka?" Cikin yanayin azaba ta furta, "Ban san sunansa ba amma na ji wasu suna ce masa Barde." Ban jira ragowar maganar ta ba saboda tun farkon ganin halin da take ciki shi ne mutum ba farko da ya fara faɗo min a rai, saboda sanin hali ya fi sanin kama. Barde riƙaƙƙen ɗan akuya ne baya iya kwana biyu ba tare da ya kusanci wala macen bil'adam ko dabba ba. 

Ina miƙe wa na riski muryar Goga ya fara fito yana busa ƙaho wanda yake alamtawa sauran ƴan uwa na nesa da na kusa akwai fita ta gaggawa. Kafin ya gama busar da yake tuni gidanmu ya cika damƙam da sauran ƴan uwa maharba da mafarauta kowanne yana tafe cikin shirin dawa, ɗaya bayan ɗaya na kalle su kowannen su yana jiran umarnin da zan bayar. Jin na yi shiru ya sa Goje  ya ɗaga gorarsa sama da hannun ɗaya, ɗayan hannun mai riƙe da kwari da baka ya sauke ya fara zabga mini kirari. "Burugu ce da kanta ba aike ba mace mai kamar maza ko cikin maza sai an tona. Cau cau cau cau ƙurungu mugun kifi sa'a a dawa sa'a a cikin gari wani aiki sai jan wuya makutsa daji, a lafiya uwar gidan kere amanar kura kyaci da gashi. Dawa dai, dawa gidan maza tsanani yana dajin Gurɓu ku bar faɗa musu wahalar sanar da su daɗin maza na cikin dawa mata na gida suna yin girki, wuya a dajin gwiɓau wuya a dajin fatalaki wuya ta ƙare a kan Barde yau ya taɓo ajalinsa." Ilahirin jikina ban da rawa babu abin da yake yi saboda tsumin da ya tayar min har nake jin da ace Barde na gabana babu abin da zai hana ban tsarge ruhinsa gida biyu ba, duk da kowa ya san Barde a cikin garinmu ba kanwar lasa ba ne.

  Da sauri na faɗa bukkarmu na ɗabo gurun damatsan hannuwana da wuya, na kunce fatar mesar da ke ɗaure a ƙuguna na ɗaura ta damisa sannan na ɗauko kwari da baka haɗe da zabgegiyar adda na fito wurin da su Goga suke tsaitsaye. Suna ganina suka yi yunƙurin saka kai a hanzarce na dakatar da cewar, "Wannan fitar ba taku ba ce saboda Barde gidanmu ya taɓo ba ku ba, na yi rantsuwa da abar bauta ba zan dawo gida ba sai na sauke kan Barde daga gangar jikinsa, weeeehuuuuhuuuuu sai ni sarauniyar baka jikar marigayi Baushe amanar kura kawanciyarka ka huta muna tafe idan dabbobi sun ƙare. Sai ni yaƙi ban san wasa ba Abar bauta ta buɗa mana matuƙar na saka kai ko yau ko yanzu ban san namiji ba sai na ga tabo a jikinsa, wahala a hanyar tugu wuya a hanyar badake wuya ko da magani babu daɗi ko ana ha maza ha mata sai na dawo da kan Barde a hannuna." Ina gama zabga kirari cikin haɗin baki tawagar da ke wurin suka furta, "Dawa dai Sarauniyar kwari da baka, Abar bauta ta buɗa miki a dajin Gurɓu." Har na saka kai zan fita na dawo wurin Mahaifiyata na russuna saitin kunnenta ina faɗin, "Ki roƙar mini abar bauta da ta rinjayi ɗayan ruhin kar ya ziyarce ni ina tsoron kada Barde ya yi nasara akaina." Cike da ƙwarin gwiwa ta furta min, "Sa'a dai Sarauniya abar bauta ta buɗa miki ɓoyayyan ruhi ba zai ƙara ziyartar ki ba." Ina gama sauraronta na fice daga cikin gidan cike da ƙwarin gwiwa na nufi wurin da na tabbatar Barde na zama da ƴan koronsa.

Daular Sarki Damina.

   Daga kogon boka mai zamani ya so kai ziyara bukkar babban dodo amma sai ya ga mafi dacewa ya fara zuwa wurin al'ummarsa ya umarci rundunar mayaƙansa da su fita yi masa farautar duk wata halitar bil'adam, musamman daga tsagin maharba da mafarauta kamar yadda suka saba yi a baya. A tsaitsaye suke dubbanin mutanen daular don a zatonsu maganin warakar annobar da ke damunsu aka kawo musu, Waziri ne ya yi gyaran murya sannan ya furta, "Ya ku waɗannan jama'a ya kamata kowa ya nutsu don jin saƙon da Sarauniya sha-kundum ta aiko." Tamkar ɗaukewar ruwan sama haka wurin ya yi tsit, Sarki Damina ya yi gyaran murya sannan ya dube su ɗaya bayan ɗaya  ya sanar da su duk yadda suka yi da boka Mai zamani sannan ya ɗora da cewa, "Ina umartar manyan mayaƙan dakarun daular nan da su hanzarta fita cikin gaggauwa don yi mana farautar bayi kamar yadda suka saba a baya, kuma su yi sani cewa ya zama wajibi su farmako mana La'anannun hallitar can ta maharba da mafarauta a ko ina suke a faɗin duniya. Wannan umarni ne daga Sarauniya sha-kundum idan ba haka ba bala'in da muka shiga da wanda muke ciki a yanzu shafar mai ne akan abin da zai faru da mu a gaba." Yana rufe baki zaratan dakarun mayaƙan suka fara fita a guje zuwa mahallansu kowanne na fito wa da manyan makamai, runduna guda suka yi tsaya a gaban sarki Damina. Sai da ya ƙare musu kallo sannan ya kasa su gida huɗu, manyan zaratan mayaƙan ya ce su bi gabas hanyar da za ta sada su da ƙasar Dabur. Runduna ta biyu ya ce su bi Yamma hanyar da za ta sada su da ƙasar Baƙasud, runduna ta uku ya ce su bi kudu hanyar da za ta sada su da ƙasar Mubali sai tawaga ta huɗu da ya umarce su da Arewa wacce za su isa da Ƙasar Surima. Lokaci ɗaya suka bazama a yunwace da farauto kowanne irin bil'adam kamar yadda Sarkin da yake mulkarsu ya ba su umarni.

*KU MATSO KU TAHO*💃🏼

Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananjn ban tausayi😰  ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.

Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼

Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera 'yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰
Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na'isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba'a nuna masa hanya, sa'a dai 'yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER'S* Amanar Marubuta La'ilaha'illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚

*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
[8/20, 7:26 PM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*

      ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
 
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

                  2

Fita ta ke da wuya na ci karo da Mahaifina da ya sawo kai ciki kafaɗarsa maƙale da barewa da ingarman zaki, ganin yanayina ya tabbatarsa masa akwai wani abu da yake faruwa don ya san fitarsa ban yi da shi zan shiga dawa ba. Cike da ladabi na miƙa masa gaisuwa irin tamu ta maharba ina faɗin, "Dawa dai Sarkin sarakuna uban dawa ga tsini ga mashi, ina gwanin wani ga nawa gamji kake ka fi ƙarfin saran maƙiya ɗan butar uban nan. A lafiya garnaƙaƙi uƙubar Gabatarawa, Abar bauta ta buɗa maka ka ci gaba da maganin munafukan mafarauta, sha zamanka ka ci gaba da kai dabbobi ƙasa wallahi ko yau ko gobe ko baka nan muna yi maka yaƙi." Cikin jin daɗi Mahaifina ya jingina gorar hannunsa da tawa sannan ya furta, "Dawa dai Sarauniya Abar bauta ta buɗa miki ko dare ko rana a dokar daji. Cau cau cau amanar Baushe wata wuyar sai a tsakiyar tsaunin Mani." Ɗora kokarata na yi a wuya na saɓi hanya tare da furta, "Sa'a dai ruwan saman mai dukan basarake da faƙiri, shawarar Duba amanar Duna." Kai tsaye mazaunin Barde na tunkara da ke cikin ƙasurgumin dajin Gurɓu, duhun almuru har ya fara karaɗe gari don haka na ƙara ƙaimi domin na cin musu don ba na son Barde ya sake shaƙar doguwar iskar numfashi. 

Ganin dajin na sake yi min nisa kuma ina gudun rasa Barde a yammacin, ya sa na lalubi ramin bushiya cikin nasara na fisgota da ƙarfi tsiya, ƴar ƙaramar aska na ciro ya tsaga bayanta sannan lalubi ganyan tunfafiya na murje a bayanta, na damƙi ƙayoyi na soka a tsakiyar kanta. Sai da na kalli kusurwa huɗu da ita a hannuna sannan na saita hanyar da za ta sada ta da mazaunin su Barde na dire ta a ƙasa tare da furta, "Bisa ga Barde amanar Lado, ko tsuntsu kika gani kar ki bar shi ya kubce."

  Tun ban rufe baki ba ta zabura da matsanancin gudu sannan na rufa wa sawunta baya. A lokacin da na ƙarasa wurinsu tuni na riski zaren carbin rayuwarsu ya kusa tsinkewa, ilahirin jikinsu ƙayoyi ne kwatankwacin yadda suke lulluɓe a jikin bushiyar da na aika musu, ganina ya harzuƙa Barde ya dube ni cikin huci yana cewa, "Uwar dawa me ye haɗina da ke da za ki aikata min haka ina cikin shaƙatawata? Ba don ina ganin mutumcinki ba da tuni na roki Abar bauta ta la'anci ruhinki kamar yadda kullin muke yi wa Baƙar Daula wannan addu'ar..." Tun bai rufe baki ba na ƙarasa wurinsa haɗe da yi masa mahangurɓar da ta kusa gigita lissafin rayuwarsa, a fusace na sake kai masa duka a maƙoshi ina faɗin, "Barde yau akuyancinka ya kai ka wurin da ba za ka sake sanin wata ƴa mace ba sai a rayuwarka ta gaba idan ka na da rabo, ka roƙi Abar bauta da ta yafe maka zunubinka wataƙila ka samu sauyi a rayuwar da za ka dawo nan gaba." Wata sakaran dariya Barde ya saki sannan ya ce, "Wai kina nufin ƴar shilar da na latsa ta gidan ku ce? Ya aka yi haka bayan na san ke kaɗai kika wanzu a cikin gidanku?" Ban ba shi amsa ba sai wani mahaukacin duka da riƙa kai masa ta ko ina, ganin haka ya sa ya damƙi ƙasar gabansa haɗe da ɗaukan cinnaka ya ɗora a kai ya dunƙule su wuri ɗaya sannan ya ɗaga hannunsa sama ban yi aune ba na ji ya watso min ƙasar da ta rikiɗe zuwa jinsin cinnaku. Nan take muka fara sabon artabu kowanne yana son nuna ƙwarewarsa da ƙarfin jarumta da na tsatsuba, ganin hanyar da ya ɓullo da ita ba mai ɓille wa ba ce ya sa ya dube ni cikin hakki yana faɗin, "Kin cika zabuwa mai tsoro don na tabbata da ace ƙarfin damtse za mu gwada babu abin da zai hana ban yi nasara a kan ki ba, ya ke ƙasƙantacciya la'ananniya marar rabo, ya ke gajiyayyiya watsatssiya ƴar taka hayen maharba ba ƴat na koya ba. Wallahi ko giwa ta yi mushe ta fi ƙarfin bakin karnuka, dawa dai  dawa ga mazaje ba mata ba Aradu mai tarwatsa ƙananan la'anannu ni Barde kabari nake duk daren daɗewa ina sauraronka." Wata irin kuɗa na ji har tsakiyar kaina yayin da maganganun Barde suka fara amsa-amo a majiyar sautina, daga bayana na fara jiyo sautin haniniyar dawakai tare da ƙarar ƙarafa da miyagun makamai, sannu a hankali na waiga don ko kaɗan na ƙi jinin wannan yanayin da nake riskar rayuwata a ciki. A duk lokacin da wannan yanayin ya riske ni na kan gaza sarrafa gangar jiki da ruhina don na banzatar da abin da nake gani a zahiri ba tare da wanda nake mu'amala da su sun riski abin da nake tozali da shi ba. Kamar wacce guguwa take fisga haka na riƙa jin ana fisgar gangar jikin da ke jingine da ruhina zuwa ga mayaƙan da nake riska suna tunkaro ni gadan-gadan, a koyaushe ina jin baƙincikin yadda nake yaƙar ƴan uwana wato jinsin Maharba da Mafarauta waɗanda su ne nake ganin rundunarsu cikin ƙwayar idona.

Ƙaddara wata abada ce da take sarƙe da gangar jiki da ruhi! Ni tawa ƙaddarar salonta mai tafiyar kura ne, ko a tarihi ban taɓa riskar makamanciyar irin tawa ƙaddarar ba.
  Na fito daga cikin jinsin Maharba da Mafaruta, don haka na fi jin daɗin rayuwar cikin dabbobin daji akan mutane. Sai dai kash! Na tsinci ruhina a jikin wani gangar jikin da ba ta ahalina na Maharba ba, na rasa yadda aka yi nake iya rayuwa cikin jinsi biyu. Ko na aikata wani mummunan zunubin a rayuwata ta baya ban sani ba? Idan haka ne na cancanci hukunci irin wannan tun da gangar jikin da nake rayuwa da ita bata ji ba bata gani ba? Ban gama zayyana wa kaina jerun gwanon tambayoyin ba na hangi yadda suka zagaye ni tamkar yadda ale zagaye bakin rijiya, kamar yadda kullin nake ji a wannan karon haka gangar jikina ta riƙa ingiza ruhina ba don na so ba tafi da gudu na riƙa kai sara ina kare kaina. Da alama Barde mamakin abin da nake aikatawa yake don duk wanda yake tare da ni ba ya gani ko fuskantar abin da nake gani a maganaina. Ganin ya samu wannan damar ya sa ya biyo ta bayana a zabga min sara a kafaɗata, wanda fitar jini daga jikina ya haddasa wata irin gigitacciyar tsawa a dajin kamar yadda yake faruwa a duk lokacin da jini ya fita daga jikina. Abin sai ya haɗe min hagu da dama don na rasa wanne daga ciki zan kare duba da rundunar dake kawo min sara ga Barde da yake niyyar yin galaba a kaina. Ban yi aune ba wata irin juya ta fara katantawa da ni tun iya daga tsaye har na gagara mallakar kaina, wani saran na sake riska a gadon bayana wanda silar haka ya sa na durƙushe a wurin ga rundunar da ke gabana na son hallaka ni nan take.

Daular Sarki Damina.

   Bayan watsewar tawagar rundunar mayaƙan Sarki Damina, daga harabar wurin kai tsaye keɓaɓɓan gida ya nufa wurin da Yarima yake rayuwarsa a ciki. Gidan an keɓe shi ga Yarima kaɗai saboda gata da kulawar da ake bashi sakamakon mummunar larurar da yake fama da ita, idan kuka zauna kuna ma'amala da shi ba za ka taɓa tsammanin yana da wannan ciwon ba har sai ya motsa za ka tabbatar da haka. Tun daga bakin ƙofar gidan har zuwa ƙofar ɗakin Yarima Maza ne suke gadinsa sakamakon mummunar lalurar da yake tare da ita, wannan dalilin ya sa hatta masu yi masa hidima maza ne don gudun abin da kaje-ya-zo. Saboda kafin a farga da lulararsa a baya mata ne suke yi masa hidima wani abin mamaki duk ranar da aka wayi gari sai an samu gawarwakin ƴanmata waɗanda ya yi musu fyaɗe, waɗansu su galabaita gudun ƙarin wahala Sarki ya sa a ƙonne su ko a binne su da ransu. Ba wannan ne dalilin da ya sa Sarki Damina ya kwashe mata ya sa aka zuba masa maza ba, saboda duk wani abu da zai faranta ran Yarima shi ya ke so bai da mu ba ko da matan yankin za su ƙare. A lokaci wata jarabta ce ta same su matan daular suka daina haihuwar ƴaƴa mata sai maza, wannan ne ya fargar da Sarki Damina ya taka tsibirin Boka mai zamani ya tuntuɓe shi game da haka, nan take ya sanar masa da matuƙar Yarima zai ci gaba da salwantar da rayuwar ƙanana yara mata tabbas za su wayi da ƙarewar ƴaƴa mata a gabaɗaya yankin. Idan kuwa haka ta kasance Sha-kundum za ta yi fushi da su fushi mai tsanani. Wannan dalilin ya sa Sarki yake saka ake zaɓar cikakkun mata da ƴan matan da suka isa ake kaiwa Yarima duk lokacin da larurarsa ta motsa.

  Shigar Sarki ɗakin ya tarar da Yarima na ta wani irin kakari tamkar wanda yake gargarar mutuwa, hakan ce take faruwa a duk lokacin da larurar Yarima ta tashi idan ka ga yana wannan halin sai ka rantse ba zai ƙara rayuwa ba. Cike da tausayawa Mahaifinsa ya ƙarasa gabansa yana zura masa ido, duk dakiya irinta Sarki Damina sai da ya zubda masa ƙwallah. A haukace Yarima ya cakumo Mahaifinsa cikin fitar hayyaci da ɗimauta yana yunƙurin haike masa, da sauri Sarki Damina ya fara yunƙurin ƙwatar kansa amma tsananin ƙarfi irin na Yarima ya sa ya kasa, a kan dole dogarawan da ke kewaye da ɗakin suka runƙuro suka taimaka wa Mai martaba. A wahalce Sarki ya ke sauke ajiyar zuciya sannan ya furta, "Ku ɗebo masa ƴan mata biyar don ba na son na rasa yarima, shi kaɗai na mallaka ko matan garin nan za su ƙare sai an nemo masa wasu a faɗin duniyar nan." Tun bai kai ga rufe baki ba wata gihitacciyar tsawa ta ratsa ciki da wajen ma'adanar sautinsu. A razane Yarima ya rungume mahaifinsa don wannan ita ce tsawa karo ta biyar da suka sake riskar irinta. A baya duk ranar da aka yi musu tsawa irin wannan lokaci ɗayamatan Daular suka riskar kansu cikin ɓallewar jinin Al'ada har tsofaffi waɗanda lokacin yin su ya gushe musu, a gaggauce ya fita don isa ga bukkar babban Dodo don ya sanar musu wannan tsawar da wacce irin masifa ta zo musu. A daidai ƙofar keɓantaccan gidan Yarima ya tsaya ya ɗaga kansa yana kallon sararin samaniya, kururuwar dattijuwar ce ta dawo da shi daga duniyar harsashen da yake yi. Waɗansu manyan barada ne riƙe da gashin wata mai tsohon ciki da alama naƙuda take jini na bin ƙafarta, ɗayan yana riƙe da wani matashin saurayi da fuskarsa ke fidda habbon jini daga hancinsa. Tsohuwar na riƙe da su ana jan su tare tana kururuwa da roƙon Dogaran akan kar su aiwatar da abin da Sarki ya umarce su, gyaran murya ya yi lokaci ɗaya Dogarawan suka tsaya cak kamar waɗanda suka haɗiyi taɓare nan take. Bawan da ke tsugunne a gabansa ne ya lura da inkiyar da Sarki ya yi don haka ya furta musu, "Sarki na buƙatar ganin ku a gabansa." A gaggauce suka ƙarasa gabansa bisa lura da yanayinsa suka fahimci ƙarin haske yake nema game da busasshiyar tsohuwar da take riƙe da mutanen da ya bayar da umarni a binne su. Wani narkeken Dogari mai ƙirar samudawa ne ya kwanta a gaban Sarki Damina, sai da ya lashi saman ƙafarsa sau bakwai sannan ya yi sujjada a gabansa yana faɗin.

  "Abar bauta ta ja da zamanin adalin Sarki mai cikakken iko. Wannan tsohuwar mahaifiyar baiwarcen ce, muna ƙoƙarin cika umarninka ta nemi..." Bai ƙarasa maganarsa ba Sarki Damina ya ɗaga masa hannu tare da faɗin, "A kawo min ita." Tun Sarki bai gama maganar ba Tsohuwar ta yunƙura cikin tsananin firgici, ganyen da ke maƙale a ƙugunta wanda ya kasance shi ne tufafin da suke rufe al'aurar su, tuni ya samu matsuguni a ƙasa. Tun daga sama har ƙasa gudawa ce take bin ƙafafuwanta, jan ciki ta fara yi cike da tashin hankali da nadama tana cewa. "Ya Abar bauta ki yi gaggawar kawo min mafita daga wannan baƙin zalincin azzalumin bawan na ki." Da ƙarfin gaske Dogarin ya ƙarasa ya fisgi ƙafarta ɗaya wacce nan take ta yi ƙara ƙaras! Da alama ya karya ta ya fara ja bai dire ta ko ina ba sai a gaban Sarki Damina. Sandar da ke hannunsa ya saka ya dokare wuyanta nan take ta fara kakari sannan ya miƙa hannu zuwa idanunta, zaƙwa-zaƙwan faratansa ya saka ya zaro ƙwayar idanunta nan take ta ƙwalla wata gigitacciyar ƙara jini ya wanke fuskarta. A cikin wani ƙanƙanin ƙoƙo ya jefa ƙwayar idon sannan ya yi gaba, Fadawan da ke take masa baya ne suka bi shi sannan ya juyo ya ce, "Kada a binne ta a kaina ɗakin zuma ta ƙarasa tsokar jikinta." Daga haka kai tsaye ya wuce Bukkar babban dodo don lamarin tsawar da ta saba haddasa musu tashin hankali ba ƙaramin tsinka hantar cikinsa ta yi ba.

   Tattakawa ya yi har ya shige gidan ƙasa wanda a nan ne bukkar babban dodo ta samu matsuguni, sai da ya yi sujjada sau bakwai a gaban bukkar sannan ya zura idanun tsohuwar a wata ƙanƙanuwar ƙoramar da ke gefen bukkar. Ta gefen tagar ya fara zayyane buƙatar da ke tafe da shi, sai da ya gama bayanin matsalolinsa daga cikin bukkar aka fara magana da wani irin yare cikin murya mai matuƙar ban tsoro. Ga wanda zuwansa ne na farko a lokacin da ya saurari muryar za ta iya kurumta sauraronsa, sai da aka yi yare sama da goma sannan aka fara maganar cikin harshen hausa.

  "Tabbas jinin sarauniya Sha-kundum ne yake zuba a daidai wannan lokacin, hasalima rayuwarta tana cikin wani hali. Rasa rayuwarta a karo na biyu tamkar rushewar daular na ne gabaɗaya, na yi rantsuwa da tsabbun da na gada a wurin iyaye da kakannina matuƙar sakacinku ya sa kuka sake rasa Sha-kundum shakka babu kun rinƙa ganin masifu kala-kala kenan har ƙarshen rayuwarku." Hankalin Sarki Damuna ya fi na kowanne lokaci tashi, ga rabuwar shawarwari da ya samu daga wurin Boka mai zamani da babban dodo. Cikin damuwa ya furta, "Ya babban Dodo mai share mana hawaye kai ne mai ciyar da mu da shayar da mu a wane yanki wannan Sarauniya tamu take saboda na..." A tsawace aka furta, "Idan za ka zagaye faɗin duniya babu wanda zai tabbatar maka a nahiyar da take. Hasali ko da za ka yi tozali da ita ba za tantance fa ba sai dai alamu su nuna mana da isowarta ga mahaifarta, a kaf faɗin duniyar nan Boka Mai zamani ne kaɗai ya san kalar surar Sarauniya Sha-kundum kasamakon abin da ya faru a shekara ɗari biyar baya da suka shuɗe, kuma ko da ta ƙaraso daular nan ba na jin jinin da ta sake wanzuwa a ciki na Maharba da Mafarauta zai bar jinin daular nan ya yi tasiri a jikinta. Sarainiyarku ta sake wanzuwa a cikin jinsin Maharba da Mafarauta, haka kundin ƙaddarar yake don haka ba mu da damar ninke babin ƙaddararta. Game da lalurar matan Daular nan ka ɗauki Mahaifiyarka mai babbar turaka kai ta wurin Yarima ya mu'amalanceta ni nake gaya maka ciwonsa zai daɗe bai sake tashi ba kuma munanan al'amura za su jima ba su sake faruwa ba. Idan ya gama ka kawo min dattin al'aurarsu zan taimaka muku na yi wani aiki da shi amma idan na gama haɗa shi wajibinka ne ka sadu da Mahaifiyarka domin kammalar aikin bakiɗaya."

  Ajiyar zuciya Sarki ya sauke sannan ya furta, "A duk lokacin

4 Comments On SHU'UMAR MASARAUTA
avatar
zainab-8-2

1 year ago

Reply

Tnx

avatar
asiya-mashi

1 year ago

Reply

Allah ya kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to asiya-mashi

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Ameen

Please Login or Register in order to submit comment