Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wato wannan yarinyar." Bamaguje ya ƙarasa maganar yana haska wa Fulani Umaima inuwar wata yarinyar. Ta tsinci muryarsa ya ci gaba da faɗin.

"Mu koma maganarmu ta baya na kuskuren da mahaifiyar Fargi ta tafka. Ta bar tauraron 'yarta a sake wanda duk wani matsafi kallo ɗaya ko bincike ɗaya idan ya yi a kanta zai fahimci muhimmancinta gare sa. Duk wanda ya mallaki ruhinta shi zai kasance mafi shahara a faɗin yankin nan a ɓangaren gawurtar tsafi da sihiri, runduna ce guda a tare da ita domin mahaifiyarta kafin ta mutu ta riga da ta juye mata nata jinin a jikinta."

"Mene ne mafita, don ta ni gabaɗaya a mutu har liman a rasa mai jan sallah." Cewar Fulani Umaima da zuciyarta ta gama ƙeƙashewa.

"A baya na fid da rai da samun wannan ɗaukakar, amma idan kin yadda me zai hana mu jefi tsuntau biyu da dutse ɗaya?"

Mai Gado

"Guduwa ita ce mafita, sai dai mu bar garin nan amma ka san muddin muna cikin ƙauyen nan Malmo ba zai bar mu da sauran numfashi ba." Shiru ya yi yana tunanin shawarar da ta kawo, ganin ya tsaya yana nazari ya sa Mai gado ta faɗa ɗaki ta ɗaura kayansu a cikin ɗankwali ta fito.

"Allah ya sani na ɗauki aniyar kula da yarinyar nan, Malmo azzalumin mutum ne, na san halinsa sarai tun da ya ƙallafa rai a kan yarinyar nan ko mun damƙa musu ita sai sun hallaka mu don gudun tonuwar asirinsu." Mai gado ta faɗa tana miƙa wa Umaru ƙullin kayansu, sai da ya karɓa sannan ya furta. "Na gode wa Allah ya sa kika fahimtar da ni da tuni na sa mun yi tsalle mun afka cikin rijiya gaba dubu. Yanzu dai babu sauran lokaci mu bi ta ƙofar baya." Cikin sauri Mai gado da Umaru suka hankaɗe katangar karan da ke gewaye da gidan, kamar masu shirin tashi sama haka suka dinga sauri suna kutsawa ta ciki bishiyu duk da a lokacin magriba ta kawo kai. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske sannan suka ƙarasa wani ƙaramin gari a lokacin dare ya tsala sosai babu haske sai na farin wata, a gajiye suka zube a gefen ganuwar garin suna sauke ajiyar zuciya. Cike da galabaita Jawahir ta fara mutsu-mutsu sai a lokacin suka shiga damuwar abin da za su sama mata ta sha. Gorar ruwa Mai gado ta kunto ta ba ta sannan suka yi jigum-jigum, har sun zauna da sunan hutawa Umaru ya furta.

"Mai gado an ya wurin nan yana da kyau kuwa? Me zai hana mu ƙarasa cikin garin nan mu nemi alfarma?"

Mai gado ta yi murmushin takaici, "Duk in da za mu je matuƙar za su fahimci ba na shayar da yarinyar nan dole za su harbo jirginmu, kuma su ɗora mana zargi da tambayoyi a kanmu. Abin da muke gudu kuma ya faru ka ga an ƙi cin biri an ci dila." Umaru ya yi jum sannan ya furta. "Ina ganin mu ƙarasa bakin kasuwa mu kwana asubar fari sai mu bar garin, mu ɗora daga inda muka tsaya." Ta gamsu da shawararsa don haka suka yi gaba suna tambayar kasuwar garin har Allah ya datar da su, suna gab da shiga kasuwa suka ga wata mai fura da nono suka siya nono sannan suka ƙarasa. A bayan rumfunan kasuwar suka yada zango bayan sun take wa Jawahir cikinta da nono, babu jimawa baccin gajiya mai nauyi ya yi awon gaba da su.

Sanyin asuba ne ya bige su suka farka don haka kamar marasa gaskiya suka sake nufar doguwar hanyar suka ci gaba da tafiya. Ba su yi tafiya mai nisa ba suka tsaya suka gabatar da sallah sannan suka ɗora daga inda suka tsaya. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske sannan suka tarad da wani ayarin mutane, yara, manya, maza da mata. Sai kuma Dogarawan da ke kai kawo a kansu, kallo ɗaya Umaru ya yi musu ya fahimci bayi ne aka kama. Da yake suna ɗan nesa da su da sauri Umaru ya ja hannun Mai gado ya furta, "Maza zo mu gudu idan Dogaran nan suka gan mu na tabbata kashinmu ya bushe don mun zama Bayi na har abada." Yana rufe baki suka juya da sauri. Cak! Suka tsaya cikin faɗuwar gaba, Mai gado ta riƙo hannun Umaru jiki na karkarwa.

"Gidan uban wa za ku gudu?" Kalaman Sojan masarautar mai ƙirar samudawa ya ratsa su, gabaɗayansu aka rasa mai bakin magana. Ganin haka ya sa Dogarin tsula wa Umaru bulala a baya, cikin azaba ya hau susar baya yana faɗin. "Tuba nake ranka shi daɗe ba guduwa za mu yi don Allah ku yi mana rai." Da hannu Dogarin ya nuna musu hanyar da sauran mutanen da ke zaune a ƙasa suke, babu musu Mai gado da Umaru suka bi hanyar ba tare da sun furta komai ba. Tun da suka tunkari wurin mutanen wurin suka zuba musu na mujiya suna kallonsu.

Bai san dalili ba haka kawai yake jin ƙirjinsa na bugawa, zuciyarsa kamar za ta yi tsalle ta hudo ƙirjinsa. Duk taku ɗaya da Mai gado take yi tana kusanto shi ji yake kamar ana ɗana wa zuciyarsa ruwan dalma, da wata irin ƙuda da wani surutai da ya gagare tantance harafi ɗaya ballantana ya yi wa kalaman nasu hisabi. Da yake hannunwansa biyu a ɗaure suke a jikin itace, kansa ya tura cikin ƙafafuwansa yana runtse ido. Bai yi aune ba ya fara jin sautin kukanta a tsakar kansa, yana yunƙurin buɗe idonsa kamar a mafarki ya ji an furta. "Ita daban ce don haka ta fito daga cikin wani irin ahali, tarayyarku alheri ce mai samar da taimakon juna a koyaushe. Sai dai zuciyoyinku za su gagara ba ku haɗin kan da za ku cimma manufarku ta alheri. " Firgigit ya ɗago kansa cikin mamaki, ba yau ce rana ta farko da ya fara jin waɗansu irin surutai a kansa ba. Amma na yau sun matuƙar dagula lissafinsa. "Wace ce ita?" Ya furta a fili. A daidai lokacin aka kama Umaru aka ɗaure ita kuma Mai gado aka kama ƙafarta ɗaya aka ɗaure, ta ci albarkacin jaririyar da ke bayanta.

"Idan muka kama hanya a yanzu babu wani sauran hutu da za mu ƙara yi a hanya, domin mun kusa shiga cikin ƙasar Zazzau." Wani turɓunannan mutum ya furta fuskarsa a murtuke babu fara'a. A galabaice cikin yunwa, ƙishirwa da wahalar tafiya suka ɗauki hanyar da za ta sada su da ƙasar Huddam. Sai da suka yi tafiya ta kusan sa'o'i shida sannan suka ƙarasa cikin masarautar ta Huddam.

A lokacin da suka je daidai ƙofar shiga Jawahir da ke a bayan Mai gado ta fara wata irin jijjiga idanuwanta suka fara yunƙurin kakkafewa, cike da tashin hankali Mai gado ta sauko ta, ganin halin da take ciki ya sa ta ƙwallah kururuwa cikin neman agaji. Da sauri Dogaran da ke wurin suka buga mata tsawa. "Hattara dai muna gab da shiga masarauta..." Ganin Jawahir na ci gaba da shiɗewa ga wani irin jini da ke tsiyaya daga hanci da kunnenta ya sa Mai gado ta furta.

"Ku taimaka mini ɗiyata za ta mutu." A fusace wani Dogari ya ƙarasa da niyyar zubga mata bulalar da ke hannunsa, gannin halin da Jawahir ke ciki ya sanyaya jikinsa, yana shirin yayyafa mata ruwa suka ji gijif alamun faɗuwar abu. Suna waigawa suka hangi Kamalu ya faɗi ƙafarsa ɗaya na jijjiga, daga ƙugunsa zuwa tafin ƙafarsa take ya sauya launi zuwa jawur, jini ya fara zuba daga cikin kunnuwansa. Ganin haka ya sa Dogarawan suka sa aka ɗauke shi aka shiga da shi ciki, jiki a sanyaye Mai gado ta rufa musu baya hannunta rungume da Jawahir da har lokacin ba ta daina kakkafewa ba.

Fulani Umaima

Da yanayin damuwa ta dube shi, "Ban fahimci kalamanka ba Bamaguje." Bamaguje ya tattara nutsuwarsa wuri ɗaya ya furta. "A lokacin da nake ƙarami burin mahaifina kenan ya mallaki ruhin wannan yarinyar, sai dai kash binciken farko da ya yi ya bayyana masa lokacin da yarinyar za ta zo duniya ba ya raye. Ni kaina na yi tsammanin a farkon rayuwata za ta wanzu, amma sai ga shi sai da tsufa ya make gangar jikina. Ina son ko ba yanzu ba idan kun haɗu da yarinyar nan ki ribace ta har zuwa wannan tsibirin nawa. Domin ba za mu iya kamata da alƙaluman tsafi da sihiri ba, idan kika yi haka tamkar kin kawo ƙarshen rayuwar yaron da kika sa aka fitar da shi daga cikin masarautar ne. Wannan kaɗai za ki aiwatar mini sauran bayanan zan yi miki su daga baya." Fuska ɗauke da damuwa ta furta. "Ban santa ba ban taɓa ganinta ba ta yaya kake tunanin zan gane ta har na ribace ta na kawo maka ita?" Murmushi Bamaguje ya yi ya furta. "Daga shi har ita ba su kasance kamar kowa ba, kuma shigarsu cikin masarautarku zai ƙara tayar da rikitattun al'amuran da ke cikinta. Masarautarku shu'umar masarauta ce da ke raye a ƙarƙashin ikon waɗansu ɓoyayyun hallitu. Ko ban faɗa miki ba shurin da ke cikin turakar Takawa akwai dalilin wanzuwarsa, tun da kin san banza ba ta kai zomo kasuwa. Zan sake bincike game da wasu al'amuran ko za mu da ce a wannan karon." Bamaguje yana rufe baki ya watsa wani baƙin jini a cikin wata tukunyar ƙasa take wuta ta fara ci gangan-ganga, shiru ya yi yana nazartar abin da yake faruwa zuwa can ya saki wata irin dariya. Shiru Fulani Umaima ta yi tana kallonsa cike da ƙosawa. "Wani abin farinciki da ban za ta ba, kusan gabaɗayansu ruhinsu na da kusanci da juna..." Kalamasa suka katse sakamakon ganin wutar gabansa ta ɗauke yo kansa kamar za ta ƙone shi sai kuna ta ɗauke ɗif, bai so haka ba amma ko babu komai ya tsinci waɗansu abubuwa da za su ba shi narasa a game da yarinyar.

"Ki sa ido sosai a wurin da kika binne jariran da kika taɓa binnewa a bayan ɗakin Sarki Abdul'aziz. Matuƙar kika ga an tone ta ba kowa ba ne face jininsa, ina nufin jininsa da kika fitar da shi. Idan har kika ga kan tinkiyar da kika rataye a ɗakinki wanda a kullin jini yake ɗiga a kan zanin kishiyarki ya fara tsutsa ta tabbata gabaɗaya su biyun suna da kusanci da ke, wato suna rayuwa a cikin masarutarku. Idan ba ki manta binciken da na yi miki a baya na gaya miki akwai wanzuwar rayuwar waɗansu ruhi masu ɗauke da rikitattun al'amura a cikin masarautarku waɗanda suke yunƙurin shiga al'amuran masarautarku. Lokacin ganawata da sarkin baƙaƙen aljanin ƙarƙashin ƙasa ya yi, zan ba shi aikin matar wani attajiri akan kishiyarta, ki ba ni wuri sai wani lokacin idan kin sake dawowa." Fulani Umaima guntun tsaki ta saki cike da takaici, ta yi masa bankwana ta koma ɗakinta.

Lokacin da aka shigar da su Baffajo sashen Bayi aka wuce da su, kusan gabaɗaya jikinsu a sanyaye yake sakamakon ganin halin da Kamalu da Jawahir suke ciki don a tsammanin mutane da yawa mutuwa za su yi. A hankali Kamalu ya fara buɗe idanuwansa yana ganin mutane dishi-dishi, ajiyar zuciya ya sauke ya yunƙura da ƙyar; da sauri Baffajo ya ɗago shi yana zubda ƙwallah. Mutanen da ke wurin suke bi su da kallo cike da mamaki, Inna wuro ta share ƙwallah tana faɗin, "Na faɗa maka Kamalu ba zai mutu ba." Baffajo ya jinjina kai yana tallafo haɓarsa, "Amma har yanzu jikina yana ba ni za su iya halaka mini shi, wataƙila ba za su bar mana shi ba." Kamalu da ke zaune bai tanka musu komai ba sakamakon wata irin juwa da ke ɗibansa, waani dattijo tsoho ya gani a gabansa ya sakar masa murmushi tare da faɗin. "Muna ta ya ka murnar dawowa cikin ahalinka, ka tashi ka ƙarasa bakin rafin can ka ɗebi ruwan cikinsa ka ɗura a kunnenka, ka damƙi ƙasar cikinsa za mu yi maka iso har bayan turakar Mai martaba yanzu, aikin da za ka zartar sai kai domin abin salsala yake bi." Kamar wanda aka ƙara wa ƙarfi haka Kamalu ya miƙe daƙau, Dattijon ya kama hannunsa ya fara tafiya Baffajo da Inna wuro suna ƙwala masa kira, ko waiwayensu bai yi ballantana su saka ran zai tanka musu.


*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
[10/4, 11:50 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA*


©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

*Masu ƙorafe-ƙorafe ta pc da groups zan rage 100 daga yau zuwa ranar da zan gama free pages. Free pages za su ƙare a page a 10 daga yanzu zuwa ranar duk mai son karanta littafin za ta turo 400*

LAST FREE PAGES

SHAFI NA GOMA

*🤔WAI NA CE KINA DA WAƊANNAN MATSALOLIN AMMA KIKE ZAUNE DA TARUN TUNANI FAL KWANYA?*

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Da duk wasu nau'in supplement da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*



Ba iya su Baffajo ba hatta sauran Bayin da ke wurin sai da suka rufa musu baya, sakamakon ganin wurin da Kamalu yake ƙoƙarin kai kansa. A tarihin masarautar babban kuskure zuwa rafin tsamiya da doshin magriba, hasali ma a ranar juma'a akwai abubuwa biyu da suka haramta ga mazauna cikin masarautar. Na farko, duk ranar juma'a haramun ne shan nonon shanu, awaki ko na raƙumi. Duk wanda ya yi gangancin karya wannan ƙa'idar kuma zai iya tsintar talatarsa a laraba, domin a labarin da yake yawo a cikin masarautar an ce shekara sama da ɗari an taɓa samun turka-turka tsakanin Sarkin da ke mulki da Bafulatanar Aljana kafin daga baya aka sasanta, amma wannan labarin kusan na kunne ya girmi kaka ne don babu wanda kai tsaye zai ce maka ga daga wurin wanda ainihin labarin ya fito. Shi kuma wannan rafin ana kiransa da rafin tsamiya sakamakon wata narkekiyar bishiyar tsamiya da ke girke a tsakiyar rafin, shi wannan rafin yana daga can gefen sashen bayi kuma rafi ne mai hatsarin gaske. Ba a taɓa ganin ya ci mutum ba, sai dai duk wanda ya yi gangancin shiga cikinsa ranar juma'a, zai fito lafiya ƙalau daga cikinsa amma a ranar za a neme shi sama ko ƙasa a rasa. Wasu daga cikin mutanen gidan masarautar sun ce faɗan Bafulatana ne ya shafi rafin yayin da wasu suka ce alƙwarin babban sarkin Aljanin ruwa ne yake cika dalilin wata yarjejeniya da ke tsakaninsa da Sarki Muhammad Safwan wato Kakan Sarki Abdul'aziz na uku. Sarki Muhammad Safwan ya yi mulki kafin hawan Sarki Abdul'aziz da shekara ɗari da biyar, har zuwa wannan lokacin babu tsayayyiyar wannan magana. Sai dai duk mazaunin cikin masarauta ya kwana da sanin masarautarsu ta sha bambam da sauran masarautun da ke wannan nahiyar musamman a kan al'amura masu rikitarwa da ban mamaki.

Da sauri Baffajo ya sha gaban Kamalu cike da damuwa ya furta, "Kamalu hai ina za ka je ne, can ba ka ganin kududdufi ne?" Tsohon da ke riƙe da hannun Kamalu ya sakar masa murmushi haɗe da faɗin. "Tabbas sun kasance iyaye masu baka kulawa amma ka sani dakatarwarsu tamkar komawar cigabanka baya ne." Jin Kamalu ya yi shiru ya sa Inna wuro ta furta, "Kamalu ko wani abu yana damunka ne?" Girgiza kansa ya yi ya furta, "Inna wani ne ya ce na je cikin ƙoramar can." Ras! Gaban Inna wuro ya faɗi, tana shirin yin magana daga bayansu suka ji an furta.

"Tun wuri ku kama ɗanku idan ba haka ba wallahi matuƙar ya shiga cikin wancan rafin a yau sai dai nan gaba ki haifi wani." Uwar Bayi ta yi maganar cikin halin ko-in-kula. Take jikinsu ya ɗauki karkarwa, Kamalu na kai dubansa wurin tsohon ya ga ya tsuke fuska rai a ɓace ya furta. "Kai ba kamar kowa ba ne, jininka yana da bambamci da nasu don haka ba koma ne za ka riƙa bankaɗa musu sirrinka ba." Yana gama faɗar haka ya ɓace masa. A lokacin tuni Baffajo sun riƙe hannuwansa bibbiyu sun koma da shi cike da tsoro. Komawarsa babu jimawa Jawahir ta farfaɗo tana yin wata irin shaƙuwa mai ƙarfi, duk wanda yake wurin sai da jikinsa ya yi sanyi ganin halin da ƙanƙanuwar yarinya take ciki. A hankali take sauke numfashi, Mai gado ta sa ruwa da ɗankwalin kanta ta goge mata jinin fuskarta. Buɗe baki ta fara yi alamar tana buƙatar abinci, a nan ne kuma hankalin mai yankan kaba ya koma ga rina domin Mai gado ta manta sam da batun nonon da za ta bai wa Jawahir. Cikin damuwa ta kalli wata Dattijuwa.

"Baba don Allah ku taimaka mini ko da nonon akuya ne yarinyar nan shi nake bata." Kusan lokaci ɗaya suka kalli juna a firgice, Uwar soro ta ce. "Baiwar Allah sai dai kam ki bata wani abin ba nono ba domin yau juma'a kuma duk ranar juma'a ba a shan nono a gidan duk wanda ya sha ya dinga aman nono har a zare ransa." Mai gado na jin haka ta rushe da kuka, don ɗan kwanakin da ta yi da Jawahir ta shiga ranta sosai.

"To ke me ya sa bakya ba ta nono?" Mai soron baƙi ta sake wurga mata tambaya." Mai gado har za ta fallasa alaƙar da ke tsakaninsu da Jawahir sai kuma ta tuna da kalaman mahaifiyarta a lokacin da ta haife ta. "Tun lokacin da na haife ta babu ruwan nono a jikina, kafin zuwanmu nan har magani mun nema amma a banza kare ya sha tsamiya." Waɗannan kalaman na Mai gado suka ƙara dasa tausayin Jawahir a zuciyoyin mutanen da ke wurin, "Bakin da Allah ya tsaga na tabbata ba zai hana shi abinci ba, akwai baiwa Zinaru da ke shayarwa mai zai hana a roƙi alfarmar yau ɗaya ta shayar da ita?" Uwar tuwo ta furta. Zuciyar Mai gado ta yi ƙal ta ƙarasa wurin Baiwa Zinaru da ke goyon ɗanta mai kimanin shekara guda. Take Zinaru ta amsa ba ta musa ba, sai dai tana ɗaukar Jawahir ɗanta da ke gefenta ya ƙanƙame mahaifiyarsa yana tsanyare wa da matsanancin kuka haɗe da cusa kansa cikin jikin mahaifiyarsa. A lokacin babu wanda ya kawo komai a ransa don a tunaninsu ma kishine irin na yara yake yi don ya ga an ɗauki wata yarinyar, kai tsaye Zinaru ta rungume Jawahir ta fara shayar da ita, wani irin zuuu! Zinaru ta ji tamkar wacce aka kafa wa shocking har tsakiyar kanta. Ga wata irin zuƙa da take ji Jawahir na yi kamar za ta fige maman jikinta, suna nan tsaitsaye ruwan nono ya fara dawo wa Jawahir ta hanci da kunnuwanta. Wannan yanayin da ta shiga ya sake faɗar da gaban mutanen wurin, cikin masifa Jakadiya ta fara magana. "Wannan wacce irin masifa aka kawo mana saboda Allah, yarinyar tun da aka kawo ku sai faɗar mana da gaba kike yi." Mai gado jiki a sabule ta karɓi Jawahir ta fita zuwa bakin wata bishiya ta zauna cikin sarewa ta fara zubar da ƙwallah. Jawahir ta jima a haka sannan nonon da ke fita daga jikinta ya dakata da zuba, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta sake goge mata haɗe da saka ta a baya ta goya ta. A ranar kusan kwanan zaune mai gado ta yi cike da rashin sabo da zaman baƙunta, uwa-uba rashin kyakkayawan makwancin saɓanin wanda suka saɓa kwana a ciki.

Cikin Dare.

Wata doguwar hanyar ya bi samɓal yana tafiya wacce babu komai sai dogayan bishiyu, tsawo da girmansu ya haddasa wa wurin duhu mai ban tsoro. Daga bayansa ya ji kamar ana bibiyarsa don haka ya yi saurin waigawa cikin tsoro da tashin hankali, wata baƙar mage mai ratsin fari ya gani tana tafe tana shinshina sawunsa. Tun bai yi wayo ba yake ƙaunar kyanwa don haka ya tsugunna da niyyar kai hannu kanta, da sauri ya ji an fisge shi gefe waɗansu surutai na tashi sama-sama a cikin kunnuwansa. Waigawa ya yi bai sake ganinta ba, ya ci gaba da tafiya. A jikin wata murgujejiyar bishiyar kuka ya hangi wata rantsatstsiyar karaga, "Je ka ƙarasa kan karagarka." Ya ji an furta masa. Wani irin sanyi ya ji yana ratsa shi, jiki a sanyaye ya fara takawa da niyyar hawa kan shimfiɗar da ke ɗauke da karagar, ga mamakinsa sai ji ya yi wannan baƙar magen ta hankaɗa shi gefe ɗaya. Ta ɗora wani mulmulallan abu mai kama da ƙawai a kan karagar, sannan ta fara zagaye karagar cikin ƙasaita. A can ƙasa ya faɗi kansa ya bugu da wani farin dutse take jini ya fara ɗiga, dafa wurin ya yi cikin azaba sai gani ya yi magen ta ƙaraso tana lasar jinin da ke zuba daga goshinsa. Ta fara ɗaga kanta tana da alamar tana son kai wa kansa farmaki wurin da ragowar jinin yake ɗiga. Ganin ta dumfaro shi ya sa ya ci gaba da ja baya zuciyarsa na dakan luguje, ganin haka ya sa magen ta fara wata irin dariya fiƙoƙinta na zubowa ƙasa ɗaya bayan ɗaya. Duk wurin

4 Comments On SHU'UMAR MASARAUTA
avatar
zainab-8-2

1 year ago

Reply

Tnx

avatar
asiya-mashi

1 year ago

Reply

Allah ya kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to asiya-mashi

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Ameen

Please Login or Register in order to submit comment