Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abin farinciki ne. Tun da shuri ya saki sarewa na tabbata a yau za mu iya samun ƙaruwa a gidan nan." Faɗaɗa murmushinsa ya yi, ya janyo Fulani Umaima jikinsa ya furta. "Wannan haka ne yanzu me kike ganin ya kamata a yi?"

"Ina ganin zai fi kyau a yi dakan ɗaka shiƙar ɗaka... sai a kira Jakadiya ta zauna a wurinta koda ciwon zai tashi tana kusa da ita, a madadin a kira Ungozoma. Amma sai yadda kace ranka shi daɗe farin jakada." Fulani Umaima ta ƙarasa magana tana sunkuyar da kai ƙasa. Ajiyar zuciya Mai martaba ya yi, "Na baki wuƙa da nama mai farar zuciya Allah ya yi miki albarka." Fulani Umaima ta amsa sannan hirar tasu ta fara sauya salon faranta ran ma'aurata. Zuciyar Fulani Umaima ƙal ta je ta samu Jakadiya da zancan Takawa, Jakadiya na gama sauraronta ta yi ƙasa da murya tana ɗan waige sannan ta ce. "Wani ma ya yi rawa ma ballantana ɗan makaɗi? Ai wallahi sai mun ga abin da ya ture wa buzu naɗi. Ina mai yi miki albishi tauraruwar Mai martaba gobe war haka Fulani Babba na nan cunkushe da baƙin ciki fal ƙirjinta, idan an isa a yi Yarima ba a ɗakinki ba shegiya nake." Fulani Umaima ta saki dariyar ƙeta. "Jakadiya tamkar zuma haka kike ga zaƙi ga harbi. Na aminta da ke fiye da haka ma za ki iya aikatawa."

"Ai shi abin kasuwa na mai ciniki ne, ni ta ki ce Fulani har abada ina bayanki. Fulani kin manta ɗayan kirarin nawa kaska rabi mai jini ki bar shi da gashi." Fulani Umaima ta jinjina kai alamun gamsuwa. Jakadiya ta sake ƙasa da murya.

"Allah ya taimake ki ni zan ƙarasa zan biya na taso Baiwa Maimuna da zarar haihuwa ta taho gadan-gadan zan turo miki ita." Murmushi Fulani Umaima ta yi har Jakadiya ta yi gaba ta sha gabanta da sauri ta furta. "Jakadiya a kawo mini kayan Bayi sashena, sannan a tabbatar an bawa Maimuna ta kawo mini cikin hanzari." Shiru Jakadiya ta yi tana nazaratar Fulani. Cikin zuciyarta tana ayyana ƙwarewarta a mugun makirci da ƙuduri.

Da sauri Jakadiya ta wuce ɓangaren Fulani Babba a lokacin da ta ƙarasa dare ya tsala sosai, sai da ta yi sallama sannan ta shiga har cikin ɗakinta. Shigar Jakadiya ya yi daidai da farkawar Fulani babba, ƙarasawa ta yi gabanta ta ce. "Allah ya taimaki uwar ɗakina ya ƙarawa Fulani lafiya. Yanzu haka Mai martaba ne ya turo ni a kan na kwana da ke saboda yanayin da kike ciki, domin tuni shuri ya saki sarewa." Murmushi Fulani ta yi don ko ba komai ta ji daɗin yadda Takawa ya ba ta kulawa, hannu ta miƙa wa Jakadiya alamar ta taimaka mata. Wani abu ta ji ya tsira wa mararta haɗe da bayanta. Cije baki ta yi jin ciwon na ƙara tsanani gadan-gadan. A haka ta miƙe ta ƙarasa banɗaki da ƙyar don ta gyara jikinta, a lokacin da ta tashi ta sake lura da fitsarin da ya jiƙe makwancinta sharkaf, na wannan lokacin har ya fi na baya yawa da wari. Fulani na dawowa kafin ta shiga ɗakin ta ci karo da wata mata baƙiƙƙirin a tsaye a dokin ƙofa. Hannu ta miƙa mata cikin wata irin murya ta furta. "Ba ni cikin jikinki!" Da Mamaki Fulani ke kallonta har lokacin ciwo na cin ta, "Wace ce ke? Me ya sa zan baki cikin jikina?" Tana rufe baki ta ga matar ta miƙa hannuwanta masu ɗauke da waɗansu irin baƙaƙen farata da zaƙwa-zaƙwan yatsu, ta miƙa hannun da niyyar shafa saman cikinta, Fulani da sauri ta ja baya haɗe da furta. "A'uzubillahi, Innalillahi..." Da gudu ta ga matar ta shige cikin sashenta, wata uwar ƙara ta ƙwalla nan take sai ga Jakadiya ta nufo wurin da gudu. Jiki na karkarwa Fulani ta ce, "Jakadiya baki ganta ba?" Jakadiya ta waiga hagu da dama ta ce, "Wa kenan ranki shi daɗe?" Dum! Fulani ta ji kanta ya yi nauyi tana son tuna a kan abin da Jakadiya take tambayarta amma ta manta, gumin da ke tsattsafo mata ta share ta ce, "Ba komai mu je Jakadiya marata ciwo take. Wash! Bayana zai ɓalle." Jakadiya ta taimaka mata suka ƙarasa ciki, kafin fitowar Fulani daga banɗaki tuni Jakadiya ta gyara wurin ta haɗa gabaɗaya kayan karɓar haihuwa. Ganin zaƙi haɗe da jini ya fara bin ƙafar Fulani ya sa Jakadiya ta shimfiɗa mata ƙatuwar leɗa, Fulani da ƙyar ta yunƙura ta hau kai tana jin ƙasanta tamkar ɗa zai faɗo. Fulani Umaima ce ta yi sallama daga bayanta Baiwa Maimuna na biye da ita, yadda Fulani Umaima ta marairaice tana yi wa Fulani babba sannu sai ka rantse zuciyarta cike take fal da tsoron Allah. Wani jan ƙoƙo ta miƙa mata ta furta, "Mai martaba na cikin tsananin damuwa da jin halin da kike ciki, musamman da ya tuna da mutuwar Marigayya Fulani Samira. (Matar Sarki Abdul'aziz ta uku ce da ta rasu wurin haihuwa.) Ya umarci da a kawo miki wannan yanzu na karɓa a hannun Shamaki." Ɗago kan Fulani babba ta ga Fulani Umaima ta sauya mata a kammani, har take ganin kamar ta taɓa sanin kamannin, sai dai kuma ba ta jin za ta tuna kalar fuskar. Baiwa Maimuna da ke tsaye jikinta ya yi sanyi don ta san garin maganin ba ya wuce na wurin Bamaguje. Fulani Babba ta karɓe za ta kai baki ta ji wani irin nishi ya taso mata, cikin tsananin azaba ta wurgar da ƙwaryar gefe ta riƙe Jakadiya da ke gefenta, take jaririn ya faɗo ya fara mutsu-mutsu yana tsanyarewa da kuka. Wani irin baƙin ciki ya turniƙe ta Jakadiya ta waiga tana kallon Fulani don sanin irin hukuncin da za su yanke, da sauri Fulani Umaima ta fita sakamakon manta kunamar da Bamaguje ya bata. Jakadiya ta tsugunna ta sa reza ta yanke masa cibiya, a tunaninta ko Fulani Umaima ta zubda makamanta ne tun da jaririn ya riga da ya zo duniya. Ta gama yanke masa cibiya kenan Fulani Umaima ta faɗo ɗakin hannunta ɗauke da wata ƙatuwar kunama, a daidai lokacin Fulanin ta sake wani yunƙurin babu jimawa wani jaririn ya faɗo. Kusan mutuwar tsaye gabaɗaya suka yi, fuska babu walwala Fulani Umaima ta ƙarasa ta ɗora kunamar a kan jinin da ke zuba daga ƙasan Fulani Babba, kunamar na fara zuƙar jinin Fulani babba ta yanke jiki ta faɗi jikinta na wani irin karkarwa. Fulani Umaima ta saki shu'umin murmushi, sai dai kuma ganin jariran biyu ya sa ta samu shakkun wanda za ta aiwatar da mugun ƙudurin a kansa, na farkon da jakadiya ta yankewa cibi ta naɗe a zani ta ɗauka, take zuciyarta ta ƙwaɗaita mata wata shawara. Kiran Baiwa Maimuna ta yi ta damƙa mata shi, sannan ta ƙarasa gaban ɗayan jaririn da ko cibiya ba a yanke masa ba. Wutsul-wutsul yake yana kuka ta ɗauki kunamar da ke cikin jinin ta buɗe bakinsa da ƙarfin tsiya ta matse kunamar a cikin bakinsa. Take wani irin ruwa mai yauƙi haɗe da jini ya fara ɗiga a bakinsa. Kamar yadda yaro yake kama mama haka jaririn ya riƙa tsotsar jini da ruwa mai yauƙin. Ya jima yana sha sannan jaririn ya fara wani irin kakari wani farin ruwa mai haɗe da jini na fita daga hanci da bakinsa. Fulani ta waiga wurin Baiwa Maimuna ta furta, "Ina buƙatar ki fita ta ƙofar baya a sirrince, ki samu ƙaton kogi ki jefa shi ko kuma ki samu wani ƙaton ramin ki binne mini shi. Duk rintsi kada ki bar shi da sauran numfashi, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci." Baiwa Maimuna da jikinta ya gama sanyi ta ce, "An gama ranki shi daɗe." Har Maimuna ta yi gaba Fulani Umaima ta katse ta, "Iya ruwa fida kai. Kowa ya biya allonsa ya wanke. Ki tabbatar ba a samu matsala ba, wallahi matuƙar asiri ya tonu sai kin gayyaci mutuwarki da bakinki. Ni da kika ganni ba na ƙwaina sai da zakara don haka ki bi sannu, shawara ce na baki don kar ki bari kwaɓarki ta yi ruwa." Baiwa Maimuna ta russuna rungume da jaririn ta furta, "Tuba nake ragamar damisa a ja ki da nisa. Na yi tsammanin kin fahimci somu-somun hauka zubda yawu. Mai ƙafa ɗaya ma ya yi rawa ballantana mai biyu? Indai ni ce har gaban abadan ba zan taɓa baki matsala ba." Fulani Umaima ta saki malalacin murmushi ta furta, "Na aminta da ke Maimunatu, idan kin kammala komai ki samu Jakadiya akwai kyakkyawar kyauta. Amma ina buƙatar ganinki da zarar kin kammala." Cike da girmamawa Baiwa Maimuna ta ce. "Godiya nake giwar Takawa fara mai farar aniya, sikari baki yi farin banza..."

"Ba mu da isasshen lokaci ki hanzarta ki fita." Fulani Umaima ta katse ta a taƙaice. Daga haka Baiwa Maimuna ta fita daga sashen Fulani ta ƙofar baya, cikin duhu haka ta ci gaba da tafiya tana ratsa bishiyoyi da ƙayoyi har ta samu ta fita ta can bayan Masarauta.

Ganin har lokacin jaririn bai daina kakarin da yake yi ba ya sa Jakadiya ta dubi Fulani Umaima. "Ranki shi daɗe me zai hana mu ƙarasa shi tun da har yanzu bai ƙarasa mutuwa ba?" Da ido Fulani ta kafe jaririn.

"Bamaguje bai ba ni damar haka ba, ki tsaya kawai mu zura wa sarautar Allah ido. Kuma ni kaina ba na son ya mutu yanzu, na fi son na dasa wa Fulani Babba ɓacin ran da har ta mutu ba za ta manta da shi ba."

Jakadiya ta jinjina kai a daidai lokacin da jaririn ya tsagaita da wannan kakarin, a lokacin Fulani Babba ta farfaɗo. Ta yunƙura a hankali da niyyar tashi da yake jikinta babu ƙwari sai Jakadiya da Fulani ne suka taimaka mata. "Sannu Yaya, barkanmu da arziƙi Allah dai ya kawo mana Yarima lafiya." Fulani Umaima ta furta tana sakar mata murmushi, wani irin yammm take ji a jikinta kamar tafiyar kiyashi, jiki babu ƙwari ta sakar wa Fulani Umaima murmushi. Idonta ne ya kai kan jaririn da ke kwance ta kafe shi da idanu, wani abu take son tunawa amma kanta ya yi nauyi ta gagara tunawa. Jakadiya ta saki guɗa da ƙarfi tana ɗaukan jaririn da ilahirin jikinsa ya haɗe da gumi, ga wani irin zafi zam a kan fatar jikinsa. Guɗar da Jakadiya ta yi ce ta alamta wa Dogaran da ke kewaye da sashen saukar Fulani babba, kafin wani lokaci tuni labari ya isa wurin Mai martaba. Fulani da Jakadiya tuni suka gyara jariri da mai jego, an turare ɗakin da turaren wuta ko ina sai buga ƙamshi yake yi. Sai dai Fulani babba tana ƙare wa yaron kallo ta fahimci kamar idanunsa ba daidai suke ba, ga yawu da yake ɗan ziraro masa ta gefen bakinsa hancinsa na yoyon majina. Ƙura masa ido ta yi tana son tuna wani abu da ya shafi lokacin da take naƙuda har zuwa haihuwarta, sai dai nauyin da kanta ya yi ne ya haddasa mata ciwon kai ɓari ɗaya take jin kamar zai tarwatse mata. A hankali ta kalli Fulani Umaima cike da murmushi, "Na gode sosai da kulawarki ƙanwata." Fulani Umaima ta saki murmushin yaƙe don saboda rufewar ido har gani take babu abin da maganin Bamaguje ya yi wa jaririn, amma saboda kissa sai ta furta. "Haba Fulani babba me ye abin godiya ina ce da kai da kaya duka mallakar wuya ne?" Fulani babba ta jinjina kai cike da jin daɗi ta ce. "Amma kuma yaba kyauta tukwici in ji masu iya magana."

"Ai lamarin tuwona maina aka yi, ni dai bari na wuce Fulani na ji asuba ta fara ƙaratowa."

Fulani Umaima na zuwa sashenta ta faɗa gado cike da tashin hankali. "Ya zame mini dole na ziyarci Bamaguje kuma a yau ba sai gobe ba sai ya hallaka mini Fulani da abin da ta haifa, idan ba haka ba zuciyata bugawa za ta yi." Ta ƙarasa maganar tana shiga cikin uwar ɗakinta.

Tafiya mai nisa Baiwa Maimuna ta yi har sai da ta yi nisa da masarauta, ta shiga cikin wani daji mai duhun bishiyoyi. Kuka jaririn ya fara yana wutsul-wutsul, bankaɗa zanin ta yi ta ji tausayinsa ya mamaye zuciyarta. Da yake asuba ta yi haske ya fara mamaye cikin dajin, wani ɗan rami ta hango da ke gefen wata murgujejiyar bishiyar kuka, kallon bishiyar kukar kaɗai ya isa ya tsoratar da gangar jikin mammallakiyar ƙwayar idon. Da sauri ta ƙarasa wurin ta tsugunna sai a lokacin ta lura da zagayyan gidan tururuwar da ke wurin, taku ta fara jiyowa a ɗan nesa da ita da sauri ta saka shi a ciki ta bar wurin ta ɓoye a bayan wata bishiya, amma ga mamakinta sai ta ji shiru babu kowa. Gudun kada asirinta ya tonu ya sa ta fara zabga gudu ta nufi hanyar gida, a yadda take ji ba ta jin za ta iya kashe jaririn da bai ji ba bai gani ba, don rashin imaninta bai kai nan ba. Tana cikin gudun ta ji ta yi karo da wani abu garam! Har sai da ta faɗi ƙasa. Tsoro, firgici da matsanancin tashin hankali ya mamaye ta, take jikinta ya hau karkarwa sakamakon ganin bishiyar kukar da ta kwantar da jaririn a gabanta ta tsaya dass kamar yadda ta baro ta a baya.

_Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚
07062062624.
[10/4, 11:45 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA*


©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba. Ban yi shi don cin zarafin kowacce ƙabila da Masarautunsu ba.

SHAFI NA UKU

Fulani Umaima har ta zura hannu za ta ɗauko ƙahon ta busa sai kuma ta ayyana ta bari idan Maimuna ta dawo ta ji yadda ta ƙarke idan ya so sai ta ziyarci Bamaguje, saman gadonta ta faɗa ta kwanta babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita.

Sannu a hankali ta fara jin dariya sama-sama, sai dai kuma yanayin dariyar ya tababtar mata da dariyar ƙaramin yaro ce. Ba ta tsinke zaren tunaninta ba ta hango wani jariri tube tamkar a lokacin ya zo duniya, tunkaro ta yake yana ci gaba da ƙyaƙyata dariya hannunsa da wata murtukekiyar igiya yana jan waɗansu murtuka-murtukan shanu, hannunsa ɗaya ɗauke da kwari da baka. A tsorace ta miƙe tana ja da baya ganin jaririn na saita ta da niyyar harba mata, jin bango ya tokare ta ta baya ya sa hankalinta ya sake kai wa matuƙar ƙololuwar tashi. Sai da yaron ya zo gabanta ya furta, "Ba yanzu ba! Zan ƙara miki lokaci." Yana gama maganar ta ga ya juya yana ci gaba da ƙyaƙyata dariya.

Firgigit Fulani Umaima ta tashi daga nannauyan baccin da ya ɗauke ta har ya gayyato mata mafarkin da ke neman wargaza kwanyarta. Ajiyar zuciya take saukewa akai-akai sannan ta jingina da bango, da ta ga zaman ba zai kai ta ba ta faɗa banɗaki ta yi wanka ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar asuba, a lokacin da tuni rana ta jima da fitowa.

Kamar a mafarki haka ta ga bishiyar na sake tunkaro ta, a yadda take a zaune a ƙasa ta fara ja baya ilahirin jikinta na karkarwa. Wata irin iska mai haɗe da guguwa ce ta taso, Baiwa Maimuna ta sa hannuwa biyu ta rufe idanunta jin ƙura na shigar mata ido. Kamar an yi ruwa an ɗauke haka Maimuna ta ji wurin shiru tana buɗe idanunta ta nemi bishiyar ta rasa, a zabure ta tashi ta ci gaba da gudu kamar wacce ake bi a baya za a zare ranta. Ta jima tana abu ɗaya sannan ta ƙarasa ta bayan masarautar, a lokacin tuni gari ya waye. Sai da ta fakaici idon Dogarawan da ke gefen hanya sannan ta yi sauri ta shiga cikin gidan, tafiya take kamar za ta tashi sama don kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci kwanciyar hankali ya yi ƙaura daga gangar jiki da ruhinta. A haka da samu ta ƙarasa sashen matan sarki tana gab da shiga sashen Fulani Umaima ta ci karo da Uwar bayi, ƙare mata kallo ta yi sama da ƙasa sannan ta ce. "Maimuna daga ina kike haka?" Marar gaskiya ko a ruwa gumi yake, take Maimuna ta yi fiƙi-fiƙi baki na rawa ta furta. "Amm da ma... Yanzu..." Daga can baya Jakadiya ta katse ta, "Uwar Bayi tare muka kwana da ita a sashen Fulani babba yanzu haka gyare-gyare ta gama yi mana." Jinjina kai Uwar bayi ta yi sannan ta wuce, Jakadiya ta ƙarasa wurin Maimuna ta ce. "Ya kamata ki riƙa sara kina duban gatarinki, ki riƙa gayyato nutsu kina yafa wa a gangar jikinki. Kin san sarai wace ce Fulani Umaima." Ajiyar zuciya Maimuna ta sauke ta amsa wa Jakadiya sannan ta wuce sashen Fulani Umaima jiki a saɓule. Tun da ta doshi sashen take jin gabanta na faɗuwa ta rasa dalili, gani take kallo ɗaya idan Fulani ta yi mata asirinta zai iya tonuwa. A haka ta lulluɓa mayafin jarumta ta shiga cikin gidan tana karkaɗe jikinta da ya yi butu-butu da ƙasa.

"Barka da hutawa ranki shi daɗe." Ƙuri Fulani Umaima ta yi wa Maimuna tana karantar yanayinta. "Binne jariri tamkar wacce ta yi dambe da jarumai biyar, Maimuna me yake faruwa na ga jikinki kamar wacce aka tono daga rami?" Ras! Gaban Maimuna ya faɗi, murya na rawa ta ce. "Ranki... Shi daɗe... Dama... zuwa na yi na sanar da ke an aiwatar da komai... Cikin nasara." Shekararta kusan hudu da Maimuna, ta karanci halaye da ɗabi'unta sarai. Take ranta ya yi mummunan ɓaci don ta fahimci zallar ƙarya a saman harshenta. "Me ya sa na amince za ki iya yi mini komai ban aiwatar da kaina ba?" Fulani Umaima ta yi maganar cike da murmushin yaƙe. Ɗakinta ta faɗa ta ɗauko ƙaho cikin shigar ziyarar Boka Bamaguje, ba ta tanka wa Maimuna komai ba ta miƙa mata hannu, zaro idanu Maimuna ta yi ta ji wani abu yana tsarga mata. Babu yadda za ta yi ta ɗora hannunta a kan nata, ba su jima ba sai ga su a fadar Boka Bamaguje. A wurin da ta saba zama koyaushe yanzun ma a nan ta zaune, gumi ya jiƙe jikinta sharkaf zuciyarta na dakan lugude kamar za ta hudo ƙirjinta.

Fulani Umaima ta ce, "Bamaguje ina zargin Maimuna da cin amanata." Bamaguje ya saki murmushi. "Ba zargi ba ne domin yanzu haka duka jariran Sarki Abdul'aziz suna raye a doron ƙasar nan. Ba ta kashe shi ba kamar yadda kika buƙata." Wani yawu mai ɗaci Fulani Umaima ta haɗiya, ta wurgawa Maimuna kallon tsana. A firgice Maimuna ta zube bisa gwiwoyinta hawaye bibbiyu na zuba, "Ki gafarce ni uwar ɗakina wallahi..." Daga wurin da Fulani take ta ɗaga mata hannu. "Kin wargaza mini shirina Maimuna. Na yi rantsuwa da abin da ya busa numfashina sai na shayar da ke ruwan uƙuba mai tsanani."

"Faɗuwa ce ta yi daidai da zama."

"Ban fahimci kalamanka ba Bamaguje."

"Ina nufi sarane za a yi a kan gaɓa. Kin san akwai muhimmin aikin da na alƙawarta miki kwanaki, zan sadaukar da shi a kan baiwarki. Idan kuma za ki samo wata sai a aiwatar a kanta." Jin kalaman Bamaguje ya sa Fulani Umaima dariya ta sauya fuska cikin damuwa. "Amma kafin aikin Bamaguje ya aka yi aka haihu a ragaya? Na yi tsammanin kunamar da ka ba ni za ta hallaka jaririn Fulani? Ina fa tsoron kada wankin hula ya kai ni dare." Wata baƙar mujiya Bamaguje ya ɗauka ya sa hannu ya fige fukafukanta da ranta, ta saki wani kuka cike da azaba sannan ya jefa ta cikin wani daskararran jini. Ya shiga gudanar da al'amuran tsubbunsa, yana cikin yi ya ga tukwanen gabansa sun rushe. A razane ya ɗago yana ɗan ja da baya, ya sake kai hannun da niyyar sake aiwatarwa kamar saukar aradu ya ga wata baƙar kwari da baka ta faɗo tsakiyar tukwanen. Tashin hankalinsa ne ya tsananta, ya ɗago yana sharce gumin fuskarsa da ke cike da gashi. Garin wata farar ƙasa mai walwali da ɗaukan ido ya ɗebo ya watsa, nan take wata narkekekiyar baƙar saniya ta bayyana jingine da kwari da bakar nan. Da bayyanarta babu jimawa duka wutar wurin ta ɗauke, ƙirjin Bamaguje ya buga ya ɗago ya dube ta. "Tabbas wanzuwarsa a doron ƙasa akwai sanadi, ban san wacce kalar baiwa da matsayi ruhinsa ke ɗauke da shi ba. Sai dai a duk bincikena na garara gano taƙamaimai wane ne shi? Abu ɗaya shafin ƙaddararsa ya buɗe mini shi mai nasara ne, sai kuma samun goyon baya da taimakon ruhi da ke lulluɓe da fatarsa..." Cikin rashin fahimta Fulani Umaima ta katse shi, "Ban fahimci gurbin da kalmanka suke neman samun zama ba, wane ne shi wanda kake magana a kansa?"

"Jinin Sarki Abdul'aziz wato jaririn da kika sa aka fitar da shi, tabbas akwai ɓoyayyan al'amari a tattare da wannan yaron. Babban kuskuren da kika tafka kenan, da kika sa aka fitar da shi daga masarautar ba tare da shawara da ni ba. Zancan da nake yi miki yanzu ruhinsa ya yi nisan kiwon da babu hallitar da ta isa ta kawar da shi daga doron ƙasa. Ba zan ɓoye miki ba, daga ni har sauran matsafan da ke doron ƙasa ba na jin akwai wanda zai iya bankaɗa miki labuben sirrinsa, ba ina miki magana a kan masakin ɗan'uwansa ba domin wannan da shi da gawa marabarsu sauka da hawan numfashi. A yadda kika gan shi a haka zai ƙare rayuwarsa a nannaɗe, hatta ruwa da abinci idan ba a ba shi ba sai dai ya dauwama da yunwa. Shi kuwa wance ingarma ne mai ɗauke da rikitattun al'amura, amma ba zan yi miki iyaka ba Umaima idan har kina ganin za ki jarraba wani masanin fiye da ni ga fili ga mai doki." Wata gwauruwar ajiyar zuciya ta sauke fuska ɗauke da damuwa ta ba shi amsa, "Ba zan ja da kai ba Bamaguje domin na tabbata zaɓenka da mahaifiyata ta yi a matsayin madogara ba za ta yi zaɓen tumun dare ba, a halin da nake ciki babban burina bai wuce masarautar Huddam ɗin nan ta dawo ƙarƙashin ikon abin da zan haifa ba wala Takawa yana raye ko baya raye." Bamaguje na ƙarasa jin kalamanta ta ɗauko wani baƙin ƙaho ya kai shi saitin idonsa na hagu ya haske wani allon farin ƙarfe mai ɗauke da rubutun jini, ƙahon da ke hannunsa na fesar da wani tartsatsin jini a jikin kaskon. Ƙuri ya yi yana kallo yana sake fahimtar al'amuran da ke wanzuwa a kwarmin ƙwayar idonsa, kamar kazar da aka jefa da gishiri haka Bamaguje ya ajiye ƙahon ya dube ta. "Za ki haifi gawurtacce kuma ingarman matashin saurayi, mai cike da isa ƙasaita da izzar mulki. Kuma zai kasance sarki wato magajin karagar sarki Abdul'aziz..." Murmushi da murnar Fulani ya katse kalaman Bamaguje ta ce. "Tabbas da kuwa mun shimfiɗa mulkin da wani mai numfashi bai taɓa aiwatar da makamancinsa ba. Sai na shayar da Fulani babba ruwa mamaki domin sai na gasa mata tsakuwa a tsakiyar tafin hannunta." Bamaguje ya kafe ta da idanu yana faɗin, "Haba Umaima me kike ci na baka ma zuba, ai duk gaggawar ungozoma ta bari a haihu. Kuma duk gaggawar asara ta jira yi samu. Kamar yadda na gaya miki jininki zai kasance sarkin ƙasar Zazzau ne kaɗai bisa taimakon jini da ruhin wata hallita, ban san ya zan fasalta miki ita ba amma ta kasance mai ɗauke da rikitattun al'amura. Wanzuwarta a doron ƙasa sanadi ne, kuma ta kasance abar farautar al'umma da dama ciki kuwa har da mahaifina wanda ya shafe shekara da shekaru cikin halwar tsafinsa yana dakon zuwanta. Ban gama tabbatar da abin da nake zargi ba amma tabbas na ga walƙiyarta a cikin masarautar Sarki Abdul'aziz, wannan zai sauƙaƙa miki cim ma muradinki..." Da sauri Fulani ta katse shi cikin ƙagauta.

"Wacce irin hallita ce?

4 Comments On SHU'UMAR MASARAUTA
avatar
zainab-8-2

1 year ago

Reply

Tnx

avatar
asiya-mashi

1 year ago

Reply

Allah ya kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to asiya-mashi

Ameen

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Ameen

Please Login or Register in order to submit comment