Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»Ώhttps://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe

πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺



Story & Written by (MRS 🌹 ISHAM 🌹)



Da sunan Allah me rahama mejinkai πŸ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen πŸ₯°πŸ€Ž






Masha Allah mundawo hutu da izinin Allah.






Book two πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š







꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂




&_____________________________________&




Page 3️⃣1️⃣





Dagowa fanan tayi dasauri tana kallon me martaba dan San gasgata wani azaad din yake nufi, gyada mata kai me martaba yayi domin tabbatarwa tunani tafarayi taya hakan ze kasance Mr azaad din da bawai sona yakeyi ba zasuce sun mana aure innalillahi wainna ilaijiraji unnn yah Allah Ina rokon ka daka bani iKon cinye wannan jarabawan. Ummi tarasa farin ciki zatayi ko akasin hakan tayi matukar jin dadin wannan labarin domin dama burinta bewuce fanan tazamo surkantan taba gashi Allah ya amsa adduah ta, amma abin tambayan anan shin fanan zata amince da wannan auren kuwa . Mama kam ji takeyi lamarin kamar amafarki cikin awowin dabasu wuce uku zuwa biyu ba har an tabbatar da fanan amatsayin matar aure lallai baa mamaki da iKon Allah me kowa me komai mai tsara komai ayanda yaso kallon fanan kawai takeyi tana tuna zata koma wani gida tayi rayuwa nan take taji wani irin kewarta yakamata, ganin tayi shuru kanta akasa tana wasa da yatsun hannunta ne yasa baba cewa " Fatima nasani ke yace me biyayya ga iyayenta bakya taba sabama umarninmu shisa akoda yaushe nake matukar alfahari na kasancewarki ya agaremu , wannan auren da akayi bawai anyishi bane dan kuntatawa daya daga cikinku bane ah ah! Anyi wannan auren ne domin kare mutunci da martabanku dakuma namu gaba daya, zaku iya fitowa duniya kununa musu kudin ma'aurata ne hakan shikadai ne ze wanke sunanku a idon duniya! Kuma iname tabbatar muku da sesun nemi afuwarku, auren nan da akayi yana daga cikin kaddarar rayuwarku Allah yariga daya kaddara azaad shine mijinki kema kece matarsa kiyi hakuri ki rungumi wannan auren in sha Allah zakiga alkharin dake cikinsa Allah yamuku albarka "
She's speechless gaba daya kalaman baba sun gama kashe mata jiki tama rasa takamemmen mezatace innalillahi wainna ilaijiraji unnn kawai take iya furtawa acikin ranta ahankali tafara samun nutsuwa.
Gaba daya tausayinta yakamasu Abba ne yace " Fatima kifada mana shin kin amince da hakan dan bazaa taba miki dole ba munsan dole zakiji wannan lamarin awani iri amma munyi hakan ne saboda wanke sunanku" kanta akasa tana wasa da kyawawan yatsunta dasuka kasance chocolate color with her sweet voice tace " na amince " basuyi tsammanin hakan ba amma dasukayi laakari da fanan yarinya ce me biyayya ko da batasan abu bazata taba musawa ba kokuma taki bin umarninsu ba, alhamdulillah sukace atare yaseer ne yace " yanzu abinda zefaru asamu ashawo kan azaad inyaso zuwa gobe se ashirya hira dasu agidan tv " jinjina kai sukayi alamar gamsuwa da maganarshi , cigaba da magana yaseer yayi yana kallon faisal" kashirya appointment da BBC news dakuma NTA domin sun dade sunason hira dashi Allah beyi ba seyanzu da dalili yazo nasan zasuji dadin wannan maganar " " to shikenan zanyi hakan yanzu base anjuma ba " aikuwa yana gama magana ya lalubo wayarsa yayi dialing number customer service na BBC news macece ta daga tace " hi, am Jenifer thank you for contacting BBC news how can I help you?" Maida mata da amsa yayi " by the way my name is Faisal adamu I am azaad the billionaire official secretary luckily I want to inform you that your appointment has been approved " wani irin ihun farin ciki tasa tana " heyyy thank you jesus " bama ita kadai ba hatta sauran ma'aikatan dasukaji labarin murna kawai sukeyi dan abinda suka dade suna jira kenan yin hira dashi bakaramin daraja zedagawa gidan tv suba domin he's the most famous person da kowan ne suke bukatar tattaunawa dashi. Haka faisal yakara kiran NTA yasanar dasu kafin yakashe wayarsa. Duk shuru sukayi suna jiran suji abinda me martaba zece

____ " alhamdulillah abu nagaba danakeso infada duk da kunsani kuma shine! duk yarinyar da aka daura aurenta tana tarewane agidan mijinta a ranar inbawai akwai wani kwakwaran dalili bane zehanata tarewa" yajuwa ga su ummi yacigaba" Aysha yau base gobe ba ku fara shirin daukan amarya banyan sallah isha " daf!daf!daf gaban fanan yatsinke ta shiga uku yanzu ana nufin bazata kwana agidansu ba wani irin rayuwa zatayi atare da Mr azaad. Abinda baba yake tunani yazo daya da abinda mama da su ya Usman suke tunani taya zaayi amarya ta tare batare da iyayenta sun mata kayan daki daduk wani abinda ake bukata ba, suna bukatar abasu ko nan da gobe ne saboda bawai basu dashi bane Allah ya hore musu abinda zasu mata irin na yar gata ma kuwa.
Baba ne ya nisa kafin yace " me martaba agafarceni, banqi ta taka ba domin kai amarya aranar da aka daura aurenta izuwa dakin mijinta bakaramin lada zata samu ba da albarkan aure saboda hakan shine ka'ida ! amma abamu daga yau zuwa gobe wannan auren yazo mana baa kan shiri ba bamu tanadi komai ba in sha Allah daga yau zuwa gobe inyaso se azo adauketa" murmushi irin tasu ta manya me martaba yayi yana kallon yan falon gaba dayansu sannan yace " shin awani ayah ko hadisi kukaji ance kayan dakin mace dakuma duk wani abinda zata bukata agidan aurenta yarataya aka wuyan iyayenta ? To bari kuji abinda kuka manta a musulunce muddin mutum ya auro mata komai yanakanshi daga abinda yakama gida wato muhalli, kayan amfanin gida, tufafinta, shanta da ciyar da ita duk ya tattara akan wuyanka amatsayinka na shugaba agareta! Yanzu ne da zamani yake juyawa yakoma juyi_juyi iyaye suka fara kai yayansu da kayan su gado su setin daki dasauransu amma badole bane wannan kuma yin hakan shike Kara sangarta mazan sukeyin duk abinda suka gadama gadaransu yanzu shine kawai sadaki zasu bada da kayan lefe se gida shikenan amma da su sukeyin komai da komai dakansu bazasu taba kuskuren sakin matansu ba dan haka babu abinda fatima zata tafi dashi gidan mijinta koda kuwa cokali ne " babu yanda su baba suka iya tabbas maganar me martaba gaskiya yafada amma yanzu anawa mata hakane domin gudun reni ko kana nan maganganu.
Abba da ummi kuwa sunji dadin maganar da me martaba yafada domin suma abinda zasu fada kenan yarigasu domin sune da matukar godiya da baba yabasu auren fanan yarinya me hankali da tarbiya babu gidan da bazaayi farin cikin samun yah Kamar taba .
Karfe 5:00 saura Adduah me martaba yayi sosai taro yakare, mikewa yayi rike da sandar shi yana musu sallama su fulani da galadima suma sukabi bayanshi suka tafi, su abba ma fitowa sukayi zasu tafi suka rako su har bakin gate suna musu se anjuma insunzo daukan amarya tare da musu godiya sosai ahaka sukayi sallama . Komawa cikin gida sukayi suna jinjina iKon Allah babu wanda yayi zaton haka awannan lokacin zama sukayi suna dan maida magana mikewa fanan tayi tabarsu afalon bin bayanta sukayi da kallo gaba daya jikinsu babu laka bin bayanta suhaima da amira sukayi dakin akwance suka sameta kanta na kallon saman celling kamar wata me tunani zama sukayi akusa da ita.
Baba ma dakinshi yashiga bayanshi mama tabi dan tanason jin yanda sukayi dangane da fanan.


via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺



Story & Written by..
MRS 🌹 ISHAM 🌹


Page 3️⃣2️⃣





_____ " babansu yakamata kafada musu komai dangane da fanan kar azo daga baya abu yazo yacabe " cewar mama dake zaune tana facing din baba , Maida hankali baba yayi gunta yace " haba sumayya ta taya kike tunanin zan boye musu wani abu dangane da yarmu nafada musu komai domin me martaba Shima ashe yanada labarin amma besan wacece takamemmen sarauniya ba " yafadi hakan ayayin da yake bude wata locker dake jikin wardrobe dinshi kudi yafito dasu akalla sun kai dubu dari hudu " Kinga wannan kudin ki kira firdausi kibatasu taje kasuwa tasiyowa fanan kayan sawa dakuma akwatin da zaa sasu amma banda atamfa shi innaje shago zabayar wa tela yamata dinki " yamika matasu ahannunta karba tayi tana jujjuya kudin ahannunta hawayen dake kokarin zubowa a idonta ta mayar dasu tana fadin " yanzu kenan fanan ayau zatabar gidan nan tun kafin ta tafi nafara kewarta bansan wace irin rayuwa yata zatayi atare da wanda bayason taba " shikanshi baba abin yadameshi amma hakan shine ze samo musu sauki , girgiza kai yayi kafin yace " karki fadi haka aure anriga da anyishi amatsayinki ta mahaifiyarta adduah kawai zaki mata na zaman lafiya agidanta " jiki asanyaye mama tace" hakane Allah yabasu zaman lafiya " ameen.

____ " haba azaad sekace baka da tausayi dan saboda kaine fah wannan abun yafaru da yarinyar nan Yakamata da akayi maganar auren nan kabada goyon bayanka dari bisa dari amma ko kunyar iyayenta bakaji ba afili kace bakason yarsu " cewar yaseer da dawuwansu kenan yashigo part din Azaad, duk wannan maganganu dayakeyi azaad najinshi kalla bece mishi ba shikadai yasan abinda yake damunshi duk bazasu fahimmce shi bane, tashi yayi yazauna yana kwabe fuska yace " yaseer nasani nasan saboda nine sunan yarinyar yabaci kuma am willing to do anything daduk karfina wajan ganin nawanke sunanta amma aiba dole seta hanyar aurenta ba ! Can you imagine wai kamar ni azaad muhammad mainasara the billionaire nizaawa auren dole unbelievable, bana sonta kwata_kwata kuma banajin zan iya sonta saboda she's still kid to me akwai sauran yarinta akanta and tamin karama , duk inda aka ambaci aure yashiga tsakani to andauki amanarta ne anbaka kulawa da ita, lafiyanta rashin lafiyanta dakuma tarbiyanta se adalci nikuma yanda banasanta banajin zan iyayin daya daka cikin wayan nan abubuwan shisa bazan iya zama da ita ba " tabbas abinda azaad yafada haka shin ze iya kula da fanan ne ko baze iyaba mutumin da ko kadan mata basa gabanshi be masan tayanda zekula dasu ba wani irin tausayin fanan ne yakamashi amma yasa aranshi in sha Allah seyayi iyayinshi naganin ya dedeta tsakaninsu da iKon Allah.
_____ " to yanzu de ba wannan ba kashirya ayau zaa kawo maka amaryaka kazama cikin shiri dan acikin daren nan Yakamata ka angonce " cike da shakiyanci yaseer yake maganar dan yasan yanzu ze fusata azaad, uhmmm kawai azaad yafada yana aiyanawa aranshi inya kusanci wannan jaririyar aiseta kusan mutuwa, Yaseer de tashi yayi yabarshi adakin dan yaga azaad inya fusata zasuyi dauki ba dadi.

Anty firdausi ce da mama, suhaima,Amira,auta afalon suna zaune sunata bubbude kayan da anty firdausi tasiyo da kudin da baba yabada kayane nagani nafada akwati biyu masu kyau abaya ne da akalla zasu kai guda ashirin se wasu fitinan nun kana nan kaya nahutawa dakuma liffaya suma sunkai 20 da takalma da jaka se jewelries nagani nafada kaya de masu matukar kyau suna zaune suna kallon kaya ya usman da ya al ameen suka shigo suma hannunsu niki_niki rike da manyan ledoji na kayan cosmetics daga abinda yayi kan turare, kayan make up, lotion,soaps shower gel, shower perfume etc. Shirya kayan akayi duka a akwatu nan se aka fitar mata da wanda zatasa yau suka gama shiryasu tsaf. Ana kiraye_kirayen sallah mangrib mama tace " firdausi yakamata kitashi kuje ki shiryata kinga lokaci natafiya kar babansu yashigo yasamu baa kammala ba" Daukan kayan dazata sa anty firdausi tayi takai dakin tasameta tana kwance tabawa kofa baya zagayowa tayi gabanta idonta biyu ba bacci takeyi ba , hannu anty firdausi tasa tadagota tazauna murya asanyaye tace kitashi kije kiyi wanka tare da alwala inkikayi sallah sena shiryaki " babu musu tamike tashiga wanka, tayi wankan tadauro alwala tafito daure da towel amma ta rame fuskanta fayau dogon rigar jallabiyarta tasa tadau hijab ta tada sallah seda tayi adduah sosai kamin tadan jabaya tajinginu da jikin gadon . Matsowa kusa da ita anty firdausi tayi tarike kafadarta sannan tace " fanan kidena sawa kanki wasu irin tunani ki karbi komai ayanda yazo miki kuma kikara da godewa Ubangiji yasa hakan shine mafi alkhari domin duk abinda kikaga yasamu bawa to muqaddarine daga Allah , nasan tunaninki ya karkata akan wani irin zama zakiyi da mijinki da bayasonki to kisani wannan abu ne me sauki inkika kara mika lamuranki ga Allah sannan ahankali hankali zakike cusawa mijinki sonki azuciyarshi mu mata inde mukaso babu tayanda bama bi da namiji duk yanda kikaso zaki iya lankwasashi domin namiji zumane seda wuta kisa aranki zakuyi rayuwar farin ciki kedashi ko bakuyi ayanzu ba zakuyi nan gaba zanyi duk iya kokarina wajan tallafa miki kina dani kidenajin wani kunya kinji ko " gyada mata kai tayi domin kalamanta sun kwantar mata da hankali tadanji relief, karajin kwarin guiwa tayi.

Jin datayi anshiga sallan isha ne yasa ta tashi ta tada kabbarah bayan ta idar ne anty firdausi tace mata tazauna agaban mirror zama tayi kamar yanda tabukata miko mata wasu mayuka masu bala'in dadi tayi dan tashafa shafawa tayi tana jin kamshin har tsakiyar kanta light make up anty firdausi tamata karkuso kuga fanan yanda tayi kyau da make up din nan, Mika mata wando na jeans dakuma yellow din body hook me dogon hannu tayi karba tayi tasa bakaramin kamata sukayi ba tab sukamata sunzauna ajikinta sosai hips din nan kamar zasu faso wandon sufito , liffaya anty firdausi tadauko fari sol medan touch din yellow ajiki nada matashi tayi mekyau ajikinta ta mata dauri da dolface yellow gashin kanta kuwa dauresu tayi seya zama kamar gammo dan kunne da sarka tasa mata se awarwaro da abin hanci me dan karamin stone rufa mata liffayan tayi ajikinta tako Ina harda fuskanta sannan tafesheta da wasu mayun turare masu kamshi sosai tabata takalmi white color se hand bag dinta,shiryata tsaff tayi wani irin kyau da fanan tayi mara misaltuwa tafito sakk amarya , rikota anty firdausi tayi tazauna akan gadon tana kokarin rufe mata fuska kenan segasu amira, suhaima sunshigo suma sun gama shiryawa cikin atamfa sunyi kyau sosai zama sukayi akusa da ita suna yaba irin kyaun datayi kamar su saceta sugudu duk yanda takai da basar dasu seda suka dan sata dariya, dan dazunma dasuka shigo dakin dataga zasu dameta kawai tasharesu tajuya musu baya.

Anty amina, anty shayida anty Zainab se zeenat ne zasuje dauko amarya su yaseer da fawwaz ne zasu kaisu duk sunci ado abunsu suka nufi anguwarsu fanan motar uku kawai suka dauka dan baason ayi yawanda zaa gane,bayan su isone suka shigo falon mama suka zauna suna Kara gaisawa mikewa anty firdausi tayi tashige dakin tariko hannun fanan da fuskanta yake arufe dakin baba sukayi domin yamata nasiha

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DDπŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺



Story Written by...
MRS 🌹 ISHAM 🌹










Page 3️⃣3️⃣ & 3️⃣4️⃣



Dakin baba suka shiga tazauna akan sallaya fuskanto ta baba yayi kafin yafara magana " Fatima ni nafi kowa sanin halinki kin kasance me hakuri da juriya dakuma sadaukarwa , to ayanzu ne wayan nan halayen zemiki amfani ke yanzu ke bakamar sauran yan mata bace karki dinga hada kanki dasu domin ke yanzu kinzama babba tunda kika zama matar aure kikama mutuncinki amatsayinki ta matar aure , wani shiga shirgin daba naki ba babu ruwanki! Sannan aure yar hakuri ce duk wasu ma'aurata dakika gani dukkansu hakuri suke da juna domin anriga da anzama daya, yazama dolene se anyi hakuri da juna kiga misali da mahaifiyarki yau shekara ashirin da biyar da aurenmu amma dede da musu wannan bata tabamin ba balle bakar magana mara dadi hakurinta yazarce misali itadin matace tagari to zanso kiyi koyi da ita kiyi hakuri da mijinki ako wani irin hali kikasance meyi mishi biyayya kibishi sau da kafa nan ne zakiga ribar auren dakuma hakuri rashin kunya ba naki bane, inyace kiyi , kiyi inyace bari kibari karki tsaya yana fada kina maida masa magana , sannan mudin kika fita zuwa wani wajen batare da izinin mijinki ba duk taku daya mala'ikun Allah tsine miki zasu dingayi ! Wannan gidan bekai gidan mijinki ba domin mace da gidan mijinta take tunkaho duk abinda ze hadaki da mijinki kizama mace me sirri karki yarda sirrin mijinki yafita sede in abinda yakeyi yazarce ka'idan addinin musulunci nan ne zaki kai kara domin neman solution, Karki manta aljannarki na karkashin kafarsa seya daga zaki shiga dan haka kiwa mijinki biyayya karki saba mishi Allah yamuku albarka yabaku zaman lfy zaku iya tafiya" tunda baba yafara magana taketa sheshekar kuka gaba daya maganganunshi ya ratsata sosai rarrafawa tayi har gabanshi tarungumeshi tana kuka bubbuga bayanta yakeyi yana shafa kanta tare da samata albarka . Haka anty firdausi tafito da ita falo tana kuka mikewa su anty Amina sukayi da niyyar tafiya fitowa mama tayi hannunta rike da wata yar karamar box riko hannayen fanan tayi tabude box din awarwaro ne guda hudu aciki na zinari alamun sundade ba design din zamanin nan bane se sheki sukeyi zurawa fanan tayi ahannun kafin tace " wannan awarwaron dakike gani gadon alhalinmu ne kakar kakatace tabawa kakata lokacin datayi aure itakuma kakata tabawa mama na dazatayi aure nima sanda zanyi aure mamana tabani kinsan metace min " dago manyan idonta dasukayi jaa tayi takalli mama ta girgiza Kai, yar murmushin yake mama tayi tacigaba" cemin tayi duk sanda nahaifi yata tayi aure itama inbatasu, ki kula dasu sosai kinji? Kizauna da mijinki lafiya fanan kimishi biyayya kizauna dashi da akwai da babu Allah yamiki albarka yabaku zaman lafiya " fashewa da kuka fanan tayi ta rungume mama kam_kam kamar zata koma cikinta kuka takeyi kamar ranta zefita, na mijin kokari mama tayi bata bari hawaye yafita a idonta ba sosai sukaji tausayin fanan amma dolene wannan akan kowace ya mace dole tabar gidan iyayenta , kokarin raba jikinsu takeyi amma fanan taki saketa ganin takine yasa su anty shayida sukazo suna kokarin rabasu suna bata hakuri Abu kamar wasa sunfi 30mint ahaka karasowa gunsu ya usman yayi yamata magana akunnenta sake maman tayi tarungumeshi shida kanshi yafara tafiya da ita zuwa motar bayansu sukabi zama mama tayi hawayen rabuwa da yarta dakuma farin ciki na kwarara daga idonta. Motarshi yashigar da ita back seat anty firdausi da anty amina suma suka shiga tana kuka suna rarrashinta su amira dasu anty shayida suka shiga motar suhaima natsaye tama rasa ina zata shiga fawwaz lura da hakan ne yabude matar gaban motarshi yamata alama da hannu yace " princess let's go" cike da kunya tashiga anty zainab dake motar dariya tayi kasa_kasa aranta tana fadin "ohhh wato su fawwaz ma ankamu kenan " tada motocin sukayi sukahau titi tafiya sukeyi ahankali harsuka iso gidan wangale musu tangamemen gate din akayi suka shigo fitowa sukayi dukansu suka tsaya suna jiran afito da fanan rungume da ita anty Amina tafito suka nufi part din ummi abakin kofa anty Amina tatsaya tace mata tayi adduah sannan tashiga da kafar dama haka kuwa akayi afalo suka samu abba, ummi da areef mikewa ummi tayi tazo ta rungumeta tana mata lale marhaban zaunar da ita tayi akan lutsa_lutsan kujerun falon abba se murmushi yakeyi yaso ace azaad na gida daya mishi tsiya dazun yafita da car key ahannunshi ko inazeje oho . Budewa fanan fuska ummi tana Masha Allah dukda tabata kwalliyar da kukan datasha fuskan nan yadan kumbura zama sukayi afalon gaba daya suna hira duk dan susamu fanan tasaki jikinta ya usman ne yashigo falon yana rike da akwatin kayan fanan dayan kuma wani security narike dashi anty Amina ce tamike tacewa security yabiyota da akwatu nan part din Azaad tanufa security nabiye da ita abaya shiga tayi falon nashi dakuna ne manya guda biyu banda na azaad se babban falonshi da dinner table da kitchen komai akwai a part din se corridor sunji furnitures dakin dake manne dana azaad painting dakin fari ne se makeken gado da wardrobe me girman gaske ga mirror da aka cikashi da kayan shafa and kayan make up,dade sauransu , bude wardrobe tayi wanda yake shake da kaya nagani nafada babu abinda babu komai ansaka matasu aciki kaya kala_kala bangaren takalma da jaka daban bangaren kana nan kayama haka se bangaren dogayen ruguna su hijab pants and bra sleeping dress, atamfofi, waje tasamu ta ajiye akwatu nan tarufe wardrobe din layin ummi takira tace su anty firdausi da suhaima suzo da fanan part din Azaad aikuwa haka akayi shigowa sukayi dakin datake toilet ta nunawa fanan tashiga tayi wanka tana mika mata doguwar rigar abaya da gyalensa karba tayi tashiga toilet din tayi wanka tasa abayar milk color ta yafa gyalen tafito tasamu anty Amina da anty firdausi basa dakin zeenat tashigo tana masu suhaima masifa " wato shine zaku taho bazaku kirani bako" hararan wasa suhaima tamata " to aigaki kinzo " magana zeenat zata kara fanan dake gaban mirror tana shafa lotion tace " to anty masifatu Allah karku dameni tam"
Zama zeenat tayi tace " wace ni rufamin asiri amaryar yaya guda nina isa indameki matarmu" dariya sukayi kara bata fuska fanan tayi tacigaba da abinda takeyi tana gamawa kuwa

1 Comments On NI DA PATIENT DINA book 2
avatar
aisha-9-6-3

1 year ago

Reply

I like this book

Please Login or Register in order to submit comment