Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*ASP ZARAH*👩‍✈️

*BOOK 2*

*Page 1*

_Federal Lowcost Gombe State._
_Monday 6:15am._

......Kwance yake a kan tamfatsetsen gadon shi hannunshi biyu dafe da cikin shi, kallo ɗaya zaka yi masa ka gane yana fama da matsananciyar rashin lafiya, banda gumk babu abinda yake haɗawa. Tsaki yaja a karo na ba adadi ganin ya kasa mirginawa ya isa ga wayarsa dake kan bedside drawer domin ya kira Abdallah yazo ya taimaka mishi.
Hamdala yayi bayan ya isa ga wayar lokacin da ciwon ya lafa, cikin sauri ya danna kiran wayar Abdallah ringing biyu kuwa ya ɗauka ya fara magana cikin zolaya kamar yadda ya saba.

"Ango na Zara'u ya da kiran sassafe haka."

Shiru yayi cikin son yayiwa Abdallah masifa amma tunawa da yayi cewa taimako yake nema ya sashi sassauta murya yace.
"Guy ka taimaka kazo ka kaini asibiti bani da lafiya ne."
Salati Abdallah yayi cikin tashin hankali yace.
"Meya same ka haka?."

"Wallahi yau da ciwon mara na kwana har yanzu yaƙi sakeni dakyar nayi sallar asuba."

Mamaki ne ya kamashi jin yaja tsaki tamkar wanda yaji mugun abu, shiru ya kuma jin Abdallah ya fara magana cikin fushi.
"Wai kai M J wane irin mutum ne haka da sam baka tsoron Allah, kanada iyali a gida amma kullum kana hanyar asibiti ciwon sha'awa na damunka, watan ku biyu da aure amma ka kasa sauke haƙƙin daya rataya a wuyanka, me zaka cewa Allah idan ka mutu da haƙƙin yarinyar nan, sanin kanka ne cewa zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya amma bazaka daina zargin yarinyar nan da aikata mugun abu ba."

Cigaba yayi da mishi faɗa tamkar ɗa da uba, shikuwa M.J bai ce komai ba har saida yaji Abdallah yayi shiru kafin yace
"Ka gama.??"

"Zan gama dai."

"Taimako na nema tunda bazaka taimakamin ba toh zan kashe waya."

"Wallahi Jawwad kaji na rantse koh, idan naji labarin ka kira wani likita saina gayawa su Daddy abinda kake aikatawa ga yarinyar nan."

''So kake na zauna da ciwo a jikina.??"

"Kana da magani a gida ai, wallahi na baka minti talatin naji sakamako mai kyau idan ba haka ba yanzu zaka amsa kiran Daddy."
Daga haka ya kashe wayar ya barshi sororo riƙe da waya a hannu cike da takaici, yana da tabbacin duk abinda Abdallah ya faɗa zai aikata kuma shi bayason iyayensa su san abinda ke faruwa tsakaninshi da yarinyar da yake tunanin mahaifansa zasu iya bada ransu a kanta, wannan dalilin ne yasa ya yanke yin amfani da shawarar Abdallah amma ta ina zai fara? Jim! Yayi kafin daga bisani ya saki wani shu'umin murmushi duk da ciwon dake nuƙurƙusarshi. Tabbas dole ya ƙara aure, hakan ne kaɗai masalaha a gareshi domin shi bai kasance mazinaci kamar ita ba, duk da yasan idan ya tado maganar ƙara aure yanzu za'a iya samun matsala amma dole hakan ne kaɗai mafita a gareshi domin bazai iya dinga haɗa jiki da rijiyar gari ba.
Agogon hannunshi ya kalla yaga 6:45am, yana da tabbacin yanzu bata fita aiki ba, a hankali ya miƙe hannu dafe da ciki ya saka bedroom slipper ɗinshi ya nufi sashin nata cike da zullumi.
Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka yake tafiya har ya iso side ɗin nata, falon a kimtse yake ko ina ƙal tamkar ba'a rayuwa a jikinshi ga wani ƙamshi mai sanyaya rai dake tashi a falon.
"Tana da tsabta." ya faɗa a ƙasan maƙoshi domin yadda yaga falon abin ya burgeshi, daidai nan kuma ya iso gaban ƙofar bedroom ɗinta, shiru yayi na wani lokaci yana nazari kafin ya yanke shawarar buɗe ƙofar ya shiga da sallama a can ciki domin ba lallai wanda akayiwa sallamar taji ba.

A tsaye ya hangota gaban madubi tana ƙoƙarin rolling veil akanta jikinta sanye da kayan aiki, cikin sakanni ya ƙarewa ɗakin kallo ganin komai neat tamkar mutum bai kwana a ciki ba, maida kallonshi yayi gareta yana daɗa ƙare mata kallon cikin shigartata, sai yau ya iya yi mata kallon da zai iya zaƙolota a ko'ina ya ganta, tayi mishi kyau sosai zubinta ya mishi kama da wata jarumar Bollywood Deepika Padukone musamman yanzu da take sanye da riga da wando na aiki zubinsu yayi mishi kamanni a wani tallen fim ɗin jarumar daya gani( Fighter ft Hritik Roshan and Deepika Padukone. World wide release on september 2023).
Tun shigowarsa ɗakin ta hangeshi saidai tayi mamaki ƙwarai data ganshi a ɗakinta, watansu biyu kenan da aure amma zata iya ƙirga sau nawa ta ganshi a cikin wata2 domin tun ranar da aka kawota gidan yayi mata sharaɗim kada ta kuskura taje inda yake baya buƙatar komai daga gareta saidai duk sanda zasu haɗu sai yayi mata rashin mutuncin da take daɗewa tana mata ciwo. Tasan hakanan bazai shigo mata ɗaki ba dole akwai abinda ya kawoshi, batason abinda zai ɓata ranta a wannan safiyar domin tana da aiki sosai a office kwananta huɗu bata fita aiki ba saboda menstrual pain dake damunta baya ga haka kuma yau tana da ganawa da sabon commissioner da aka ce mata an naɗa bayan mutuwar wanda tazo ta tarar a garin, bata bibiyi labarin ba domin a zatonta mataimakinshi aka rantsar a madadinshi.

"Nazo karɓar haƙƙina ne."

Tunaninta ya katse lokacin dataji abinda ya faɗa, mamaki ne ya kamata wanda har yasata juyowa ta kalleshi lokacin da yake zama a gefen gadonta domin ta tabbatarwa idonta shi ɗin ne ke magana, batace dashi uffan ba ta nufi gaban wardrobe ɗinta ta zaro abayar da zata ɗaura akan kayan tana ƙoƙarin warwarewa da nufin sakawa.
"Nasan kinji abinda nace dan haka bani da bukatar maimaitawa." ya kuma faɗa cikin tsare gira.

"Zaka iya dawowa wani lokacin amma yanzu ba samu zakayi ba." ta faɗa bayan ta ɗauki handbag ɗinta zata bar ɗakin.
Cikin bazata taji yasa hannu ya fincikota ta faɗa cikin, matseta yayi sosai kafin ya fara warware veil ɗin nata, mutsu-mutsun kwacewa takeyi amma sam yaƙi bata damar hakan.

"Ki bar ganin kina ƴar sanda ba iya kwacewa zakiyi ba, gara ma ki nutsu ki barnj nayi abinda zanyi nagama. Kika baiwa wasu na waje ma bare nida nake mijinki."
Daidai nan ya ƙarasa warware veil din wanda hakan ya bama dogon gashinta mai kyau da sheƙi zubewa a gadon bayanta, da fari yayi tunanin wig ne ta saka amma sai ya gane gashinta ne yayi mamaki duk da yasan cewa suna da gashi irin na fulani amma na Zarah ya zarce irin nasu a tsayi da santsi. A hankali ya fara shafawa yana tusa kanshi a ciki _Mai neman kuka an jefeshi da kashin awaki_ , nan da nan ya fice a hayyacinsa.
Taso yimai turjiya amma tunawa da tayi bata sallah yasa ta daina ƙoƙarin kwacewa ta barshi ya cigaba da abinda yakeyi.
Takaici ne ya turniƙeshi lokacin da ya gane dalilin dayasa ta nutso ta daina ƙoƙarin kwacewa, cike da takaici ya sauka a gadon ya fice daga ɗakin batare da ya tattara kayansa dayayi watsi dasu ba.

Cikin sanyi jiki ta miƙe ta nufi banɗaki, bata daɗe ba ta fito cikin hanzari ta ɗauko ɗayan uniform ɗin ta saka ganin har ƙarfe takwas ta kusa kuma ganawarsu da kwamishina 7:30ne. A hanzarce ta gama komai ta fice daga gidan ta wuce office ɗin.
Tun daga harabar gurin take ganin kamar tasan wasu daga cikin jami'an dake shawagi a farfajiyar wajen bata kula ba ganin tayi latti ya sa kai tsaye ta nufi office ɗin commissioner kai tsaye ko kula da sunan dake manne a jikin ƙofar batayi ba ta kutsa kai ciki bakinta ɗauke da siririyar sallama. Tashin hankali _ba'a saka masa rana_, zuciyarta ce ta cunkushe _damuwa tayi adabo a fuskarta_. Jikin tsantsar baƙin ciki ta riƙe handle ɗin ta nufi ficewa a office ɗin......✍️

*BY*
*JASMINE*🌸🌸

_Fans Mi😜😜😜 Meerah, Zee Bassa, Nab baby, Hussy, Mrs. Mukhtar, Miss Japanese and others da kuka hana kanku bacci jiya toh gashi nan kusha karatu😅😅 A daina hana kai bacci hilis dan nima bana hana kaina 🤦‍♀️._
_Su Ummu Huzaifah a sakar mini mara nayi fitsari, kada masoyiyata ta fara nata itama JJLuV😘😘_

Luv y'all.

*ASP ZARAH*👩‍✈️

*BOOK 2*

*Page 2*

...Dariya yayi mai cike da ma'anoni kafin yace.
"Barka da zuwa Zarah, ya zaki koma tun baki yimin maraba da samun sauyin gurin aiki ba?."
A hankali ta juyo ta kalleshi cikin tsana tace.
"Abinda ya kawoni kenan na taya wanda aka naɗa murna saidai wanda na tarar bai cancanci hakan ba, hmm so kake na tayaka murna kabar garin Bauchi a matsayin commissioner ka dawo Gombe a matsayi iri ɗaya? Wani cigaba kenan?. Zuwa na ya ƙaramin aiki domin kuwa ganinka da nayi anan ya tabbatarmin da cewa akwai hannunka a kisan tsohon commissioner saboda kanaso ka dawo inda nake aiki. Allah ya baka sa'a."

"Dakata ai baki karɓi saƙon naki ba." ya faɗa yana miƙewa a kan kujerar ganin tana ƙoƙarin barin offishin, tsayawa tayi harya iso inda take tsaye ya miƙa mata farar takarda yace.
"Wannan takarda ce ta dakatar dake daga aiki har na tsawon lokacin da za'a gama ƙaddamar da bincike akanki, an kamaki da laifi biyu, na farko ana zargin sa hannunki a ɓatan ƴar aikin dake muku aiki a gida wacce ta ɓata watanni biyu da suka wuce an rasata, na biyu kuma akan mutuwar ɗan jaridar da kukayi ganawar sirri dashi a ranar litinin wanda shima a daren aka kashe shi."

Tsaye tayi tana kallonshi har ya gama magana kafin ta sa hannu ta karɓi takardar tace
"Kamar yadda muka saba a kowani lokaci mai girma commissioner.." tana gama faɗin haka ta saka hannu ta yaga takardar ta kuma cewa.
"Ya fuskanceni, gaba da gaba mu gwabza dashi. Kai harka manta da sharaɗina, ba kallon shugaba nake maka ba kallon abokin gaba nake maka dan haka baka da hurumin da zaka dakatar da Zarah a aiki ko da na second ɗaya ne. Idan ya cika jarumi ya fuskanceni, na barka lafiya." daga haka ta fice a office ɗin ta barshi a tsaye sororo kamar wawan da yaga mace na wanka.

Bata ko tsaya amsa gaisuwar da ake mata ba lokacin data isa gurin aikinsu, kai tsaye office ɗinta ta wuce saboda sarawa da kanta yake yi yana mata masifar ciwo, kanta ta kifa a teburin ta fashe da kukan da batasan dalilin yin shi ba.
Tsagaitawa tayi da kukan batare da ta share hawayen dake zubo mata ba jin alamun za'a shigo office ɗinta batare da an nemi izini ba, tasan ɗaya daga cikin mutum biyu ne ke shigowa ko su duka biyun wato Saleem ko Jidda.
Hannunsu sarƙe dana juna suka shigo bakinsu ɗauke da sallama, cike da mamaki suke kallon fuskarta da ta jiƙe da hawaye, tuni hankalin Jidda ya tashi ta nufeta gadan gadan tana tambayarta abinda ke damunta.
"Babu komai fa Habibaty, kawai kaina ke min ciwo."

Murmushin daya tsaya iya baki Jiddan tayi kafin da zauna shima Saleem ya zauna akan kujerun dake fuskantarta, shiru Jidda tayi ta ƙura mata ido tanason gano abinda ke damunta kafin tace.
"Kinje Office ɗin commissioner da nufin taya shi murna sai akayi rashin sa'a kika tarar da Muttaka wato tsohon commissioner na jihar Bauchi a matsayin Commissioner a garin Gombe, hakan ne ya haddasa miki damuwa kike tunanin taya zaki shawo kan matsalolin dake damunki. Shin zance na haka yake ko akwai gyara.?"
Bata koyi mamakin jin batun Jiddah ba saboda sabo da tayi da hakan, shikuwa Saleem ganin Zarah ta gyaɗa kai alamun hakane yasa shi mamakin a ina Jiddah ta samu wannan labarin suna tare amma shi bai sani ba.

"Jeki ɗauraye fuskarki kizo muyi magana." Ta kuma faɗa.
Wannan karon Zarah abin na Jiddah ya bata dariya domin dai ta fahimci Jiddah ta gane fitsari ya cika mata mara ne shiyasa tace taje ta ɗauraye fuska gudun kada Saleem ya fahimci zance. Babu musu ta miƙe ta shige banɗakin dake manne a office ɗin.

Saleem kuwa maida kallonshi yayi ga Jiddah cikin zaƙuwa yace.
"Sa-Jid a ina kika samu labarin abinda ya faru bayan muna tare banga wani ya kiraki ya faɗa miki ba."
Shiru tayi na wani lokaci kafin tace

"Nima bansan ya akeyi nake gane abinda ke ran Zarah ba, wani lokacin sai naji kamar anayi min raɗa a kunne na tuhumeta kuma na bata shawara. Abinda yake ƙara ɗauremin kai kuma shine idan mukayi amfani da shawarar sai muga ribar abin. Nima na rasa gane me hakan ke nufi."
Jinjina kai Saleem yayi cike da gamsuwa, yana ƙara tabbatar da cewa ƙaunar dake tsakanin Jiddah da Zarah daga Allah ne, babu yadda za'ayi ɗayansu ta ɓoye damuwarta batare da ƴar uwar ta fahimci haka ba.

A wannan yanayin Zarah ta fito ta samesu, zama tayi suka cigaba da tattauna abinda da ya shafi binciken da Saleem yake gabatarwa akan mutuwar ɗan Jaridar.

"Ni fa inaga lokaci yayi daya kamata mu tunkari inda azzalumin nan yake tunda yaranshi biyu na hannu, mu tursasa sai sun faɗa mana inda yake." Inji Saleem

"A'a dear lokaci baiyi ba amma saura ƙiris domin muna gab da sanin inda yake." Cewar Jiddah.

"Hakane Barrister akwai sauran lokaci, baya ga haka har yanzu Raliya taƙi mana bayani akan komai daya shafe shi duk kuwa da irin azabar da ake gana mata."- Zarah

"Shikenan amma ya kamata muje ki ƙara yiwa mutumin nan barazana domin shima bashi da alamar yin bayani."

"Inada niyyar hakan dama tunda kunzo sai muje gaba ɗaya daganan na sake yiwa Raliya tambayoyi".

"Ok muje ɗin"
Daga haka suka miƙe tare da barin offishin.


Babu wani da zaiyi tunanin mutane na rayuwa a inda su Zarah suka je, domin wani tsohon kwango ne da ya ji jiki ginin gaba ɗaya ya fara rugujewa. A haka suka shiga tare da kutsa kai a wani babban ɗaki, Saleem ne ya isa daidai inda wasu shukoki suke ya kauda ƙasar dake gurin gefe sai ga wani murfi kamar na rijiya ya bayyana a gurin. Key Zarah ta miƙo mishi ya saka ya buɗe babban kwaɗon dake wajen tare ɗage murfin sai ga matattakala ta bayyana. Juyowa yayi ya kallesu yace
"Muje ko."
Kamar ko yaushe sune ke fara shiga sai ya biyo bayansu, yauma hakan ce ta faru saida suka shige kafin shima ya bisu bayan ya dudduba baiga kowa ba.
Tana ɗaure a jikin kujera sai wata mata dake gefe a zaune tana daddana waya, ganin shigowarsu Zarah ne yasata miƙewa tana musu barka da zuwa tare da gaishesu, amsawa sukayi cike da fara'a kafin Zarah tace
"Babu wata matsala ko Jummai.?"

"Babu ranki ya daɗe, sai dai jiya tayi ƙoƙarin guduwa bayan na kwance ta zatayi amfani da toilet, amma ta rasa hanya ina kitchen naji ta shine nazo na ɗaure ta."

"A tunaninta zata iya guduwa daga nan.?" -Jiddah

"Haka take gani." wacce aka kira da Jummai ta bada amsa.

Gabanta Zarah ta isa ta ɗago fuskarta da ta nuna alamun galabaita tace.
"Kinga wannan Raliya acid ne a yau idan baki mana bayanin inda Alpha yake ba zamu kona fuskarki ta yadda ko kin kuɓuta babu yadda za'ayi ya aure ki kamar yadda kike da buri."

A razane Raliya ta ɗago ta kalli Zarah tana mamakin yanda akayi tasan wannan zancen domin bayan ƙawayenta dake gidan da Alpha yake ajiyesu babu wanda yasan wannan zance, yanzu ta sadaƙar cewa ko bata gaya musu ba zasuyi amfani da asiri su karanci abinda ke ranta. Hawaye ne ya wanke mata fuska cike da takaicin yau zata faɗi wani sirri na masoyinta tace.
"Zan faɗa miki."

"Muna jinki." Saleem ya faɗa.

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

Malam Surajo Mai Idon Naira shine sunan da mutane kw kiranshi saboda tsantsar son kuɗi da yake da shi daga shi har Matar sa mai suna Lauratu. Malam Surajo da Lauratu ma'auratane da aka sansu da masifar son kuɗi da roƙo tare da bibiyar masu kuɗi suna musu fadanci, ƴaƴansu biyu kacal a duniya. Hajara itace ta farko wacce a yanzu take da shekaru 22 sai ƙanwarta Na'ima dake shekaru na 17. Duk wani buri sun ɗaurashi akan ƴaƴansu domin suna mishi kallon kadara wacce zasu dinga zamun kuɗi dasu.
Saidai a cikinsu Hajara ce kaɗai tayi gadon iyayen nata domin tana da buri sosai, a cewarta ma bazata yi aure ba idan ba mai hannu da shuni ta samu ba, saidai a ɓangaren Na'ima abin ba domin yarinya ce mai nutsuwa da sanin ya kamata sam bata yi halin iyayen nata ba shiyasa basa shiri sam dasu.

A daren ranar lahadi ne wanj abin farin ciki ya samesu a cewarsu, domin wani baƙo ne ya zo musu da wata kwangila mai tsoka. So yake su yi sanadin da ƴarsu Hajara zata auri ɗan shahararren mai kuɗin nan wato Eng. Muhammad Jawwad Sulaiman, batare da tunanin komai ba suka amince saboda zunzurutun kuɗin da za'a basu bayan haka kuma zasu samu kuɗi sosai idan ƴarsu tayi nasarar auren shi. Ya tsara musu komai da yadda Hajara zata haɗu da M.J tare da kalan aikin da yake so tayi mishi idan taje gidanshi, a haka suka rabu bayan ya ajiye musu makuɗan kuɗi domin yin hidima tare da faɗa musu cewa ta kasance cikin shiri domin a kowani lokaci zai iya kiranta domin su haɗu da M.J ɗin.
Wannan abu ya matuƙar faranta musu rai, domin a ganinsu fa kakarsu ta yanke saƙa.

Washegari kuwa kamar yadda yace, ya kirasu tare da yin magana da Hajara bayan ya gama gaya mata abinda zatayi idan ta fita.

A ɓangaren M.J kuwa bayan ya sha magani ya ɗan samu sauƙin abinda ke damunshi, shiryawa yayi ya fita zuwa gurin aiki domin bazai iya zama a gidan ba. Yana tafe zuciyarsa cike da tunani kala-kala, bai ankara ba hannu motar ta kwace mishi cikin rashin sa'a kuwa ya bige budurwar dake ƙoƙarin tsalleke titin tana sanye ta dogon hijabi har ƙasa milk colour, da hanzari ya taka birki ya kashe motar cikin tashi hankali ya fito ya sameta a zaune tana ƙoƙarin miƙewa alamun motar bata taɓata sosai ba.

"Sannu kinji baiwar Allah, kiyi haƙuri, daure ki mike na kaiki asibiti a duba ki."

Cikin sanyin murya tace

"A'a banji ciwo ba ka barshi kawai." tana mikewa da kyar tamkar saniyar dake naƙuda.

"Kar muyi haka dake dan Allah muje na kaiki ko da Pharmacy ne a duba ki."

Babu musu ta bishi tana takawa dakyar har ta ƙarasa inda yake tsaye ya buɗe mata ƙofar motar yana jera mata sannu babu adadi. Bayan shigarta ne shima ya shiga motar ya tada ta suka bar gurin zuwa asibiti.....✍️

_Kai na na mini ciwo_.🥺


*BY*
*JASMINE*🌸🌸

*ASP ZARAH*👩‍✈️

*BOOK 2*

*Page 3*

Da kwatance take nuna masa hanya ya Isa har ƙofar gidansu bayan ya kaita Pharmacy an duba lafiyarta duk da ba wani rauni sosai ta ji ba, ita ta fara shiga cikin gidan jim kaɗan kuma Na'ima ta fito ta gaidashi tare da faɗin ance ya shiga daga ciki, babu musu kuwa ya bita har cikin gidan inda aka shimfiɗa masa tabarma a tsakar gurin Inda su Malam ke zaune tare tare da Hajara.
Bayan gaishe gaishe ne M.J ya kuma basu hakuri akan abinda ya faru, nan suka nuna babu wata matsala, miƙewa sukayi duka inda aka barshi da Hajara bayan ta kawo mishi sihirtaccen zoɓon da Ummansu ta haɗa mishi, duk da yake mutum ne mai ƙyanƙyami amma haka bai hanashi shan zoɓon ba ganin kamar yanayin mutanen baiyi kama da ƙazamai ba.
Sun daɗe suna hira kamar da ma can sun saba duk da shi ba mutum bane mai yawan magana amma ya sake sosai yana hira da ita, ya jima kafin ya musu sallama ya tafi bayan yayi musu ɓarin naira tare da alƙawarin zai dawo ya duba jikin Hajara, haka sukayi sallama zuciyar wannan ahali cike taf da farin cikin samun wannan arziki da sukayi.

Yana tafe amma zuciyarshi fal tunanin mutanen da yau ne ya fara haɗuwa dasu musamma ƴar su da ta riƙe mishi zuciya lokaci ɗaya yaji kamar sonta na barazanar kamashi, lokaci guda kuma zuciyarshi ta aminta cewa ya samu kalar matar da yake nema a fannin tarbiyya duk da yanason mace wacce tayi karatun boko, fata yake a cikin ranshi Allah yasa babu wanda ya riga shi domin kam bazai yarda yayi rashin wannan kamilar mace ba. Da wannan tunanin ya isa office amma ya kasa taɓuka komai tunanin yadda zai ɓullowa su Daddy da zancen ƙara aure ne ya dameshi musamman da bayaso auran ya wuce nan da wata ɗaya ko biyu.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Cike da ƙosawa Jiddah ta kalli Raliya dake faman zubda hawaye tace
"Kina daɗa ɓata mana lokaci fa idan ba zakiyi magana bane ki faɗa tun wuri mu samawa kanmu masalaha."

"Bansan ta yaya bane zaku isa ga inda Alpha yake domin nima bansan hanyar inda yake ba bare nayi muku jagora." ta faɗa gami da sunkuyar da kanta ƙasa.

Cikin ɓacin rai Jummai ta kawo mata duka saidai bata kai ga isarta ba Zarah ta tare ta tana faɗin.
"Sassauta Jummai abinda ta faɗa gaskiya ne amma tsaya muji ƙarashan zancen" komawa baya Jummai tayi tana huci kamar wani firgitaccen zaki.
"Ke muke saurare Raliya bamu da lokacin da zamu cigaba da zama anan."
Shiru tayi na wani lokaci kafin tace
"An haifeni ne a garin Jos, ni kaɗai ce ƴar da iyayena suka haifa kuma mahaifina hamshakin mai kuɗi ne na ban mamaki yana da dukiyar da shi kanshi bai san adadinta ba, watarana sai harƙalla ta haɗasu da Alpha batare da yasan ko shi waye ba. A zahiri Alpha dukiyar mahaifina kaɗai yaso karɓa amma ganin mahaifin nawa yasan wasu daga

1 Comments On ASP ZARAH book 2
avatar
ibrahim-8-7

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment