Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗauro Alwala ya fito ɗaure da Towel a kugunsa

Wajan Mirror ya wace yana zuwa ya shafa Mai masu kamshi ya feshe jikinsa da turare masu kamshi kafin ya nufi wajan Wardrobe
Kayan baccin sa ya sanya kafin ya fice daga dakin


"Kya nima yunwa naƙe ji Wllhy" cewar Mima tana riƙe cikin ta

Kallonta Mary tayi tace"to nikuma maye zanyi miki kenan"

Cikin matsifa Mima tace"Nace wani abu zakiyi min ne to, kya'asu wa wai kare da gudun layya, kinga fita zanyi Wllhy kada kirufen daki ina zuwa"


Gyara kwanciya Mary tayi tana fadin"kinga kwanciya ta sai kinzo kawai"

Tsaki taja ta fice tana sanɗa

Kitchen ta nufa , tana zuwa taga baki kirin cikin Kitchen ɗin, hannu tasa da niyar kunna wutar Kitchen ɗin sai kuma komayi ta tuna ta bari

Wajan frige ta nufa tana zuwa ta buɗe nan idon ta ya sauka kan Cake daƙe ciki

Murmushi tayi tasa hannu ta ciro tare da Spoon kafin ta rufe frige ɗin

Hawa tayi kan frige ɗin ta zauna nan ta fara cin Cake tana lumshe ido


Zaif da tunɗa ta shigo yaƙe kallonta girgiza kansa yayi yana miƙe wa tsaye ya ajiye Tea Cup daƙe hannun sa ya nufi wajan frige


Mima cak ta da katar da cin Cake ɗin ta tana sauraron tafiyar da taji
A jiye Cake ɗin tayi gyafen ta kafin ta fara rarraba ido ko zataga Mai shi
Ji tayi an daga ta cak , aiko cikin razana ta buɗe baki zata kwalla kara Zaif yayi saurin sanya Bakinsa cikin nata

Tsayawa tayi tana kallon fuskan sa amma saboda duhu bata iya ganin fuskan mai shi

Zaif bayyi yin kurin Shucking Tongue ɗin ta ba amma haryanzu Bakin sa na cikin nata

Sundau lokaci a haka kafin ya zare bakin sa ya fice daga Kitchen ɗin yana ɗafe kansa daƙe masa barazanar tarwatse


Yana fita ta sauƙe numfashi kafin cikin tsoro ta nufi hanyar fita
Tsayawa tayi tana kallon Cake ɗin aiko komawa tayi ta ɗauke Cake ɗin ta fice tana sauri ta haura Step
Tana zuwa bakin dakin ta buɗe kofar da ƙarfi ta shige ciki tana numfashi kamar wacce tayi gudu

Mary tashi tayi tana kallon Mima tace" ƙekuma lafiya ya nagan ki haka fa"

Mima zama tayi bakin bed tana kallon kofar ta kalli Mary tace"Wllhy akwai matsala Mary"

"Matsala fa Kika ce na maye kuma?"

Mima hannu tasa tana shafa Lips ɗin ta,ta kalli Mary tace"yayi kissing ɗina"


Cikin dagawar murya Mary tace"What Waye?"

Tana turo baki tace"nima bansan shiba kawai dai ina cin cake ɗina naji ya ɗaga ni daga zaunen da naƙe zan kwalla kara ya sanya bakinsa cikin nawa"

Zaro ido Mary tayi tace"Bakinsa cikin naki kika ce fa Mima?"

Wani irin kallo Mima tayi wa Mary kafin tace"a a karya nake miki kinji"

"Ok yi hakuri Ni kiban naci Cake ɗin Wllhy ya shiga raina da kika shigo dashi"


Dariyar mugunta Mima tayi tana kallon Mary tace"Ki mutu dan wannan karya ne kice zakici Yasin, da kin rakani ai babu yadda za'ayi wani kato ya shamin baki amma dan bakin ciki ai kwanciyar ki kikayi nayi tafiya ta ɗan haka ban badawa aha"


Mary shiru tayi tana kallon Mima can kuma sai tace " Please Sis"

Idanu Mima ta juya kafin ta mikawa Mary plat ɗin tace"Take it kadda ki cinyan"

Tashi tayi ta haura saman bed ta kwanta

Mary kuwa cin Cake ɗin ta tafara yi


Yana koma Bedroom ɗin sa ya faɗa kan Bed ya Kwanta yana lumshe idonsa
Zakin bakinta ne yaƙe ta mamaye cikin nasa bakin ɗuk da bayyi hakan da wata manufa ba ɗan kawai saboda kadda tasa musu ihu ta tayar da kowa daga bacci ne yasa yayi hakan

Ganin abin kara daɗuwa yaƙe yasa shi jan tsaki ya tashi ya shige Toilet ya wanke bakinsa ya fito ya kwanta nan bacci yayi Wuff da shi....



*Wacece MIMA*
*Waye ne ZAIF* Kubiyoni Next page dan ji yadda zata kaya


More Comment
More Typing
Share Fisabidillah


👩‍🔬 *Dr. ZAHRA* 👩‍🔬

_*Funny, love story*_


*By Asmeety Ce*




*ELEGANT ONLINE WRITER'S*




*Free Book*



*Page-7&8*



**WATTPAD LINK**Asma'u Aji Ibrahim

https://www.wattpad.com/story/302746450?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=ASMAUAJIIBRAHIM&wp_originator=mpzyPESu8LQOti9aB44TSAWdBLMfYyHXI2bTd%2F4xBGBoopEqZJVmZEtpYTjP3JfXV6X2Fj2EaDLHFWpku7oEsQX5xGWGb330DhtPLZnKCqh%2FAM7%2FAqJMgKjgMLG%2FeIY9


**Short Story**


*_Bismillah Rahman Rahim_*

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai._


**Alhmdllhi Ala kulli Hamid**

*Wacece MIMA da Zaif*

Alhaji Mamman Mustapha shine asalin sunan Mahaifin Mima
Dan uwa ga Alhaji Abubakar Mustapha Mahaifin Zaif

Alhaji Abubakar Mustapha da Alhaji Mamman Mustapha wa da kanine inɗa tun suna ƙanana iyayen su Allah yayi musu rantsuwa

Kafin Mahaifin su Alhaji Abubakar Mustapha ya ratsu yana da babban Private hospital wadda yaƙe a garin Abuja

Alhaji Abubakar Mustapha(Abbeiy) bayan ya gama karatun sa a kasar London yana zuwa garin Abuja nan Mahaifin su yace a fara aiki a Hospital ɗin sa
Alhaji Abubakar Mustapha(Abbeiy) yayi matuƙar farin ciki da hakan
Babu ɓata lokaci ya fara aiki anan

Bayan wasu shekaru uku Alhaji Mamman Mustapha shima ya kammala karatun sa a garin Kano shima bangaren Likita ya karanta
Yana zuwa Abokin Mahaifin su yace yana bukatar Alhaji Mamman Mustapha ya fara aiki a Hospital ɗin sa daƙe farin Maiduguri

Haka Mahaifin su ya amince da hakan saboda akwai babban abota a tsakanin su sosai

Ana cikin haka Alhaji Abubakar Mustapha(Abbeiy) ya kamu da Son ƴar Abokin Mahaifin sa wato Bilkisu (Ammeiy) basu wani ɗauki lokaci ba akai auran su

Anyi auran su da Wata goma ta haifi ɗanta kyakkyawa fari, ranar suna aka raɗa masa sunan Mahaifin su Alhaji Abubakar Mustapha (Abbeiy) wato
Alhaji Mustapha Zaifudden inɗa aƙe kiran yaron da sunan Zaifudden


Bayan shekaru goma sha biyar Alhaji Mamman Mustapha yazo Abuja yana zuwa ya sami yayan sa da Maganan Auren sa, nan Abbeiy yaƙe tambayan sa a ina yasa mu mata
Alhaji Mamman Mustapha yace "A Maiduguri Yarinyar shuwa ce kuma tana da hankali sosai amma matsalan shine iyayen ta sunce baza su iya bawa Wani yare ɗiyar su ba sai KANURI ko SHUWA kuma gaskiya yaya muna son junan mu sosai" kallon sa Abbeiy yayi yace"Ok gobe sai muje garin ko?"
Cikin jin daɗi Alhaji Mamman Mustapha ya amsa da "To"

Da washe gari kamar yadda Abbeiy yace haka suka tafi Maiduguri suna zuwa kuwa sun sami zama da iyayen Yarinyar nan ma Mahaifinta yace shi bazai bada auren ƴar sa ga Fulani ba

Abbeiy babu yadda bayyi dasu ba amma sunki haka suka hakura suka koma Abuja, Alhaji Mamman Mustapha yaci gaba da aikin sa

Tunɗa Alhaji Mamman Mustapha suka rabu da Abbeiy a ranar bai saƙe zuwa Abuja hutu ba gashi Abbeiy idan ya kirasa a waya ya tambaye sa yaushe zaizo sai yace sai wani Weekend haka har shekara biyu

Wata rana ranar Sunday Abbeiy Zaune yaƙe a babban falon gidan sa Alhaji Mamman Mustapha ya shigo da Sallama jin Muryan dan uwan sa yasa Abbeiy juyowa yana kallon sa, rike yake da wata karamar yarinya wacce baza ta wuce shekara ɗaya da watanni biyu ba
Karitso wa yayi yana sakar wa Abbeiy Murmushi
Yana zuwa ya sami waje kan kujera ya zauna
Abbeiy ma Murmushi yayi yana kallon ɗan uwan nasa kuma yana kallon Yarinyar yace"Wannan fa Mamman?"
Murmushi yayi yana kallon Kyakkyawar fuskarta yace"Jeki wajan Abbeiy ki"
Mikawa Abbeiy yayi
Yarinya kamar tasan abinɗa yace ta fara mikawa Abbeiy hannu tana Dariya
Bayan Abbeiy ya karɓe ta yana yi mata wasa yace"Beautiful Baby, Mamman a Ina kasamo wannan Kyakkyawar Yarinyar nan?"
"Ƴata ce yaya"
"Ƴar ka kuma Mamman taya?"
Gyara zama Mamman yayi yana kallon yayan nasa yace"Eh ƴa ta ce sunan ta ZAHRA Mai sunan Mahaifiyar mu, nasan yaya zakayi Mamakin jin hakan, bayan dawowar ka daga wajan nemamin auren KOSHSHE iyayen ta suka fitar mata da Miji, banji labarin haka ba sai aure sauran kwanan biyu KOSHSHE ta sameni taƙe sanar min cewa ita Ni take so dan haka ko na aure ta ko ta shiga ɗuniya ta lalace, babu yadda na iya haka mukaje wajan limamin unguwar su ranar Juma'a aka ɗaura mana aure, ahalin KOSHSHE najin haka suna ce basu babu ita, haka na ɗauke ta na ajiye ta a gida na daƙe can muka ci gaba da zama, tunɗa KOSHSHE ta sami ciki bata da Lafiya kullum babu dare ba rana haka muƙe yini mu kwana cikin rashin lafiyar ta, ranar da cikin KOSHSHE ya cika wata tara da kwana goma sha ɗaya da Daddare misalin ƙarfe 9 ta fara na kuda, cikin gaggawa na kaita Hospital nan muka shiga bata taimakon gaggawa, bata wani shan wahala ba ta haifi ƴar ta, bayan ta haihu aka gyarata likitoci suka Kaita ɗakin hutu nan ko minti biyar bata cika ba Allah yayi mata ratsuwa "
Shiru yayi yana share hawayen sa yaci gaba da faɗin"Yaya nayi kukan rashin Matata, Mata ta gari, bayan kwana uku na ɗauki Zahra na kaita wajan dangin Mahaifiyar ta nan suka ce su basu karban ta ɗan haka na fita da ita daga gidan,nan na ɗauki Zahra na kaita gidan marayu Ni kuma naci gaba da yin aiki na"

Numfashi Abbeiy yaja kafin yace"Than Why ka ɗauko ta yanzun ka kawo ta?"

Har kasa Mamman ya ɗuka yace"nasan zakayi fushi dani akan ban kawo ta tun farko ba amma kayafe min Please yaya, ga Zahra na baka ita har a bada ƴar kace ka haɗa ta da Zaifudden matsayin yara a gunka ina neman wannan alfarmar yaya"
Ɗafe kafadan sa Abbeiy yayi yace"Zahra da Zaifudden duka abu guda ne a waje na kaji insha Allahu yadda na ɗauki Zaifudden matsayin ɗa haka Zahra ma taƙe matsayin ƴa a guna"

"ai nima hakan ne kadda ku manta dani mana" suka jiyo Muryan Ammeiy daga bayan su

Murmushi Abbeiy yayi yace"wato laɓe kikayi mana kenan?"

Tana Dariya ta karitso ta zauna kan kujera tana kallon Mamman tace" kadda ka samu damuwa kanina Insha Allahu Zahra zan ɗauke ta tamkar Ni na haifeta kaji?"

Cikin jin daɗi Mamman yace"Nagode da wannan Auntie na"

Murmushi Ammeiy tayi tace wa Abbeiy"Kawo ta Alhaji"

Tana karban ta Zahra ta farayin Dariya tana kallon Ammeiy
Itama Ammeiy dariya tayi tana wasa da ita

Mamman kallon Abbeiy yayi yace"Ina Babana yaƙe banganshin ba?"

"Ai yana Makaranta a London"

Cikin jin daɗi Mamman yace"Alhamdulillah Allah ya bada Sa'a"
Da Amin suka amsa

Akwatin da Mamman ya shigo dashi yaja ya buɗe nan ya ciro da wata farar ta karda ya mikawa Abbeiy yace wasikar Mahaifiyar Zahra ce tace idan ta ratsu na baka ka karanta"

Abbeiy karɓa yayi yana buɗe paper ɗin

Nan ya fara karanta wa kamar haka

*Assalamun Alaikum, yayan mu ina maka Barka da warhaka, na rubuta wannan sakon saboda kai kuma ina neman wata alfarma a gunka, yaya koda bayan raina ne inason ka aurawa Zaifudden Zahra a matsayin Matar sa ta sunnah ko taki ko taso amma shi Zaifudden kada kayi masa dole sai ita Zahra kadai zai zauna da ita a a koda yana da wacce yaƙe so to kabarshi ya aura bayan haka sai ka aura Masa Zahra Dan Allah wannan alfarmar nake nema a gare ka yaya Ma'assalam Allah ya saɗamu da Alkairi Amen*

Abbeiy numfashi yaja kafin ya kalli Ammeiy sannan ya mika mata da paper'n nan Ammeiy ma ta karanta

Abbeiy kallon Zahra daƙe wasa a jikin Ammeiy yayi yace"Insha Allahu Baba na Mijin kine Mama ta Allah ya raya mana ku"

Murmushin jin daɗi Ammeiy tayi haka Mamman ma

Tashi yayi yana kallon su yace"Bara na wuce kadda dare yayi min gashi gobe inada aiki sosai a Hospital"

Abbeiy ganin har ƙarfe 3:39pm yayi ya kalli Mamman yace"yamma tayi ai kabari gobe ka fita da safe yanzu kam ko ka fita baza ka samu shiga gari ba ai tunɗa ƙarfe 5:00pm suke rufe gate"

"A a zan tafi ko a BENISHEKH (My local government area 🥰) zan kwana"

"To a can ɗin akwai gidan da zaka kwana ne?" Cewar Ammeiy

Murmushi yayi yace"Matar yaya ai zan kwana a Locust H4 ( our 🏠 Number Miss you 😢) gidan wani babban likita wadda muƙe aiki dashi a Hospital ɗin tamu"


Abbeiy kallon sa yayi yace"Wani Mutum ne wannan wadda har zaka je gidan sa ka kwana kana ganin ba matsala?"

"Eh yaya Mutumin gaskiya bayi da matsala harta iyalin sa bata da matsala suna karban baki sosai wallahi gashi yana da yara kuma dukka mata ne su 7 da maza 2 yaya"

Numfashi Abbeiy yaja kafin yace"To Allah ya kiyaye hanya sai ka kula kaji abuda gida dukka mata wannan Akwai bin rai"

Yana tashi yace"Babu komai yaya yaran ma suna da karki babu ma kamar ɗayan ƴar tasa wacce taƙe karatun likita a yanzun haka gaskiya tana da hankali Wllhy"


Abbeiy na tashi yayi dariya yace"kodai zaka auro ta ne irrin yabo haka?"

Tsosa kyaya yayi yana kallon sa yace"Tab na isa itama fa anyi Saven Date ɗin ta fa"

"Wow hakan yayi ka gaishe su to "

"To yaya Bara na yuce" Kallon Zahra yayi kafin yayi mata Kiss a goshi yace"Miss You Sweetheart Bye"

Ammeiy bataso tafiyan nasa ba haka ta hakura tayi masa Fatan Alkairi

Abbeiy ma badan yaso ba Mamman ya tafi

Da washe gari kamar daga sama aka kira shi a waya yana Office bayan ya amsa aƙe sanar masa da Motan dan uwansa Alhaji Mamman Mustapha yayi hatsari kuma Allah yayi masa ratsuwa

Abbeiy cikin tashin hankali ya nufa gida bai jima da zuwa ba sai gashi an shigo da gawar Mamman
Tsosai Abbeiy yayi kukan rashin ɗan uwan sa tilo tak

A haka rayuwa tai ta tafiya cikin jin daɗi wani sayin Abbeiy yayi ta kukan sa haka Ammeiy zata sashi gaba tana rarrashin sa kamar jariri
Abbeiy ya ɗauki son ɗuniya ya aza akan Zahra Komai ya samu Zahra baya tuna kowa sai Zahra
Bayan Shekara ɗaya Ammeiy ta haifu ta haifi ƴar ta kyakkyawa
Ranar suna taci sunan yayar Ammeiy wato Maryam
Ammeiy ɗuk Son da taƙe wa Maryam bai kai na Zahra ba saboda Yarinyar duk wadda ya kalle ta so ɗaya to sai ta shiga ranka

Bayan shekaru 20
Zaif ya gama karatun sa a London
Zaif bangaren likita ya karanta
Tunɗa Zaif yazo yaga Zahra yaji baya kaunar ta kwatakwata
Zahra Bata jin magana amma Allah ya dora Mata Son Zaif
Kullum tana jikinsa shi kuma baya Son hakan saboda ya tsane ta shiyasa baswa shiri kullum

Zaif yana da shekaru 25 ita kuwa Zahra tana da Shekaru 10

Zahra tana Makaranta ne a Abuja
Tunɗa Zahra ta fara zuwa School kullum ana cikin kawo karar ta na dukan yaran Mutane, kuma ita bata da wani aiki sai wasan CRICKET shine tafi so a rayuwar ta
Zahra ta kasan ce tana da ƙoƙari wajan karatu ɗuk jarabawar da aƙe yi to ba'a barin Zahra a baya saboda cikin ɗubban nin ɗalibai Zahra ita taƙe zuwa farko

Ranar da Zahra ta cika shekaru goma sha biyar ta kammala Secondary School ɗin ta inɗa Abbeiy yace ɓangaren likita zata karanta, aiko Zahra kwana tayi tana kuka idan akwai abinɗa tafi tsana sama da likita to babu ita a ra'ayin ta kawai ta zama jarumar Wasan CRICKET Amma Abbeiy ya hana
Inɗa Zaif yana jin labarin hakan ranar haka yayi wa Zahra ɗuka akan hakan

Tun daga wannan lokacin ne Zahra ta tsani Zaif har cikin ranta

Haka zata ringa kusantar jikinsa saboda baya Son hakan ita kuwa dan taga ta sanya ransa ya ɓaci yasa taƙe hakan

Zaif yana da shekaru 36 inɗa kullum yaƙe kwana da ciwon mara
Tun abin baya damin sa har ya fara damin sa, a haka ko wanni dare sai yasha Tea da lemon kafin ya kwanta

Babban Abokin Abbeiy ne yasa mi Abbeiy yaƙe sanar masa cewa yana So ya bawa Zaif auran ƴar sa
Abbeiy tunɗa Abokin sa yayi masa wannan Maganan yaƙe tunani, idan ta shine babu macan da Zaif zai aura bayan Zahra ita kaɗai ce matar sa amma kuma idan yace wa abokin nasa hakan bazayiyu ba abotan su na shekara da shekaru zai bace haka Abbeiy ya amince da zancen......


More Comment
More Typing
Share Fisabidillah

👩‍🔬 *Dr. ZAHRA* 👩‍🔬

_*Funny, love story*_


*By Asmeety Ce*




*ELEGANT ONLINE WRITER'S*




*Free Book*



*Page-9&10*



**WATTPAD LINK**Asma'u Aji Ibrahim

https://www.wattpad.com/story/302746450?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=ASMAUAJIIBRAHIM&wp_originator=mpzyPESu8LQOti9aB44TSAWdBLMfYyHXI2bTd%2F4xBGBoopEqZJVmZEtpYTjP3JfXV6X2Fj2EaDLHFWpku7oEsQX5xGWGb330DhtPLZnKCqh%2FAM7%2FAqJMgKjgMLG%2FeIY9


**Short Story**


*_Bismillah Rahman Rahim_*

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai._


**Alhmdllhi Ala kulli Hamid**

*Wacece MIMA da Zaif*


Abbeiy tunɗa Abokin sa yace ya bawa Zaif ƴar sa ya aura ya kasa Faɗawa koda Ammeiy ce haka har ya mance da zancan

Zahra ta gama Makarantar inɗa Abbeiy yace zata fara yin aiki a Hospital ɗin sa tun daga wannan ranar Zahra taƙe cewa ita batason aikin sai wasan CRICKET

Tun a wannan lokacin Abbeiy ya haɗa ta da Zaif inɗa ya hana ta fita ko ina daga gida sai gida, tunɗa Zaif ya kafa wa Zahra wannan dokan taƙe kara tsarar sa har cikin ranta

Haɗa baki sukayi ita da kawarta da suƙe wasan CRICKET tare Kan idan tana wucewa zuwa wajan wasa sai ta biyo mata su ringa tafiya tare, Zahra sanarwa Mary tayi nan Mary ma ba'abarta a baya ba taji daɗin Haka

Kullum haka Zahra taƙe fita da asuba sai ta dawo dai dain kafin kowa na gidan su farka

Zaif tunɗa ya tafi wani aiki a London ya kai wani mara majinyace bai kara zuwa ba sanda yayi shekara ɗaya

*Cigaban labari*

Fitowa tayi daga wanka ɗaure da Towel, gaban Mirror taje
Duban ta takai kan Mima wacce taƙe kwance tana Game na CRICKET a wayan Mary

Girgiza kai Mary tayi tace"Wato dai Uncle Yana gari ma baza ki daina yin wasan nan bako Mima?"

"Idan naki fa?" Ta bata amsa tana yin Game ɗin ta

"Sai na faɗa masa cewa kina fita da asuba kije sai ki dawo gidan kafin kowa ya tashi"

A jiye wayan hannun ta Mima tayi tana kallon Mary tace"to bismillah malama jeki fada masa"

Taɓe baki Mary tayi tana nufar wajan Wardrobe tace"Nidai babu ruwa matsifaffiya kawai"

Murguda masa baki Mima tayi kafin tayi cilli da wayan Mary tana tashi

Kallonta Mary tayi tace"dan bakida shi shiyasa kike jin haushin nawa?"

Ran Mima ne ya ɓace ta nufi hanyar fita

Murmushi Mary tayi tana kallon Mima tace"Madam yau fa zakiyi bako Yakamata ki shirya sab kafin yazo angon naki"

Mima manna mata tayi ta fice tana tunanin abinɗa zatayi wa Mary ta huta

Bata tsaya ko inaba sai Side ɗinsa tana zuwa ta tura kofar falon nasa
Da Sallama a bakin ta, ta shiga
Kallon falon ta tsaya yi ganin ko ina sab yaƙe a gyare ga kamshi yana tashi
Taɓe baki tayi tana nufar Bedroom ɗin sa

Tana zuwa ta buɗe kofar nan ma baya nan, jin karar ruwa da tayi a Bathroom yasa ta faɗin "hmm wanka kamar kifi"

Duban ta takai wajan da Wayoyin sa yaƙe da Laptop ɗin sa, Murmushi tayi ta nufi inɗa wayan yaƙe tana zuwa ta ɗauki wayan nasa kafin ta haura saman bed tayi rub da ciki ta daga kafafunta ta fara latsa wayan

"Mtshwwwww ko Game bakada ita bara na saukar ma"ta faɗi hakan tana shiga play store nan ta saukar da Game ɗin CRICKET


Zaif Yana fitowa daga Toilet idon sa ya sauka kan ta, waro ido yayi yana kallon ta, gani yayi game ma taƙe yi amma baisan wacce game taƙe bugawa ba

Ɗauke idanun sa yayi daga kallonta ya nufi gaban Mirror
Mai masu kamshi ya shafa sai kuma ya feshe jikinsa da turare masu kamshi

Mima kallonsa tayi tace"Laaa Hero zaje ganin amarya kenan?"
Sai kuma tayi dariya tana tashi

Kana ta nufi inɗa yaƙe daga tsaye a gaban Mirror yana taje kansa

"Ummm Herooo" tayi Maganan ne a shagwabe tana turo baki

Banza yayi da ita yaci gaba da gyara suman ƙansa

Jin yayi shiru yasa ta kamo hannun sa da yaƙe gyara gashin kansa
Kallonta yayi yace"Leave"
Shagwaɓar da fuska tayi tace"Umm Umm naki"
Zaro Ido yayi cikin faɗa yace"What!!!?"

Ta tsorata sosai hakan yasa ta fashe da kuka mai sauki, janta yayi ta faɗa kirjinsa, rungume ta yayi yana bubbuga bayan ta

Lamo tayi a jikinsa tana shaƙar daddadin turaren sa masu sanya zuciyan Mutum yaji sanyi
Bakinsa yakai kunnen ta yace"Wato har kinsan daɗin jikin na miji ko?"
Dagowa tayi ta kallesa taga kamar bashi yayi Maganan ba ya wani zoge

Cire ta yayi a jikinsa yana kallon ta yace"What?"

Tana turo baki tace"Ka zauna na gyara maka tsuman kanka"
"Am I ur made?" Ya faɗa yana Mata wani irrin kallo
Tsoro taji amma a haka ta daƙe tace"gyara maka tsuman kanka Zanyi"
Badan yaso ba ya zauna dan yasan yanzu idan yaki zata sa masa kuka shikuma abinɗa yafi tsana kenan kukan mace
Tana Dariya ta ɗauki man gashi ta shafa masa kafin ta dauki Kum ta fara taje masa cikin kankanin lokaci ta gama gyara masa tana Murmushi cikin jin daɗi tace"Hero juya kaga Mirror"

Lumsassun idanun sa ya ware su akanta yana kallon ta, kafin ya juya ya fuskanci mirror ɗin waro ido yayi yana kallon kansa harga Allah ta iya gyaran gashin kuma yayi matuƙar yi masa kyau
Murmushi ne ya kubuce masa yana kara kallon kannasa daga cikin mirror

Mima na ganin haka ta kwantar da kanta kan Kafadar sa ta sanya hannayen ta, ta zagi kirjinsa tana Murmushi cikin sanyi Murya tace"You so Handsome Hero "

Zaif lumshe idon sa yayi yana jin yadda tsigar jikinsa na washi, yadda tayi Maganan ba karamin kasala ta sanya shiba,

Ganin ko magana yaki ne yasa ta fara shafan kirjinsa tana hura masa iskar bakinta cikin kunnen sa cikin Cool Voice ɗin ta tace"Herooo say Something naaahh"
Haba Yaya lafiyar kura taƙe balle antabo ta, aiko Zaif bai san lokacin da ta sanya hannu ya ɗauke ta cak sai kan.......


More Comment
More Typing
Share Fisabidillah 🤲

👩‍🔬 *Dr. ZAHRA* 👩‍🔬

_*Funny, love story*_


*By Asmeety Ce*




*ELEGANT ONLINE WRITER'S*




*Free Book*



*Page-11&12*



**WATTPAD LINK**Asma'u Aji Ibrahim

https://www.wattpad.com/story/302746450?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=ASMAUAJIIBRAHIM&wp_originator=mpzyPESu8LQOti9aB44TSAWdBLMfYyHXI2bTd%2F4xBGBoopEqZJVmZEtpYTjP3JfXV6X2Fj2EaDLHFWpku7oEsQX5xGWGb330DhtPLZnKCqh%2FAM7%2FAqJMgKjgMLG%2FeIY9


**Short Story**


*_Bismillah Rahman Rahim_*

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai._


**Alhmdllhi Ala kulli Hamid**


Dagota yayi cak sai kan cinyar sa
Mima tsoro ne ya Kamata runtse idon ta tayi tana fadin"wayyo Hero Sorry Please"
Kallon fuskarta yaƙe
Can kuma sai ya saki Murmushi ya dire ta ɗaga jikinsa ya miƙe ya nufi wajan Wardrobe

Yana zuwa ya buɗe ya cire da kayan sa ya nufi Bathroom

Mima ta kallonsa har ya shige ciki, ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta zaune bakin bed tana jiran fitowar sa

Buɗe War kofa da taji ne yasa ta ɗagowa tana kallon fitowar sa

"Woww Hero u look so nicely" ta faɗa tana tashi

Zaif kauɗa ƙansa yayi baice komai ba sai ma Mamaki da yaƙe yadda Mima ta raina sa gata sai shegen tsoro da saurin yin kuka, shi kuma bayason abinɗa zai sata kuka sam

Kamo hannun sa tayi suka nufi wajan Wardrobe
Tana Murmushi tace"Hero Site"
Shi dai Zaif kallonta kawai yaƙe yana Son yaga gudun ruwan ta
Zama yayi bakin bed ɗin

Mima wajan takalman sa taje ta ɗauko masa takalmin sa Mai kyau baki takalmin mai yatsa ne
Tana kawowa ta sungunna a gabansa ta sanya masa shi kafin ta ciro dankwalin kanta ta goge masa shi tas ɗuk da ba wani kura gare sa ba

Tashi tayi ta buɗe Wardrobe ta ciro masa da hulan sa Zanna bukar ta ajiye a gyafen sa tace"Hero Up"

Zaif kamar sololo haka ya tashi tsaye yana kallonta

Hannu tasa ta rufe masa da butul din wuyan rigan sannan ta kamo hannun sa ta sanya masa linke ɗin hannun rigan ɗuka biyu kafin ta ɗauki hulan ta fara ƙoƙarin sanya masa shi amma ta ƙasa saboda ya fita sayi
Turo baki tayi tace"Uhmmm Hero"

Murmushin da bai shirya ba ta kuɓuce masa girgiza kai yayi ya jayo stool ɗin gaban Mirror kafin ya kalleta amma baice komai ba

Mima na ganin haka ta haura kan stool ɗin ta tsaya kafin ta sanya masa hulan tana shafa gyafen kyakkyawan sajan sa da taƙe kwance lub lub da shi

Kuri tayi wa wajan tana kallon sa ita Sometime Mamaki ma taƙe irrin kyau na Zaif kamar mace ga nuna Izza da kamala

Da gowa yayi yana kallon ta
Sundau lokaci suna kurawa junan su ido kafin a hankali ta motsa bakin ta tace"Hero"
"Uhmm" yace yana kurawa ɗan karamin bakinta ido ganin yadda ta jikasu da silver ɗin ta tana motsa su a Hankali

Tana shafa sajan sa tace"Inason na fita"
"Kije ina" ya jefa mata tambaya yana kallonta
Ƙasa tayi da kanta cikin sanyin Murya tace"Sarlun wanke kaina "
Kallon kan nata yayi da yaƙe ɗaure da dankwali yace"let me see"
Hannu tasa ta zame ɗan kwalin

Kurawa gashin kannata ido yayi ganin baki kir sai yalki yaƙe gonin burgewa, hannu

Please Login or Register in order to submit comment