Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka zauna

Ɗafe kansa Zaif yayi yana fesar da numfashi
Kallonsa Umar yayi yace"Dr. Tell Me maike damin ka Please duk ka canza ka rame "

Idanun sa da tayi jazir ya ware su kan Umar yayi kallonsa cikin raunin murya yace"I'm feel in love"
Zaro Ido Umar yayi yace"What!!"

Fesar da numfashi Zaif yayi nan ya bawa Umar labarin abinɗa ya shiga tsakaninsu da Mima da kuma yadda yanzu yaƙe Son ta

Umar Murmushi yayi yana kallon Zaif yace"Your Rong Dr"
Wani kallo Zaif yayi masa

"Yes Your Rong, Dr Why ka aikata hakan tun yanzu ai dole ta raina ka, kuma fa kace ada baka kaunar ta baka Son ta saida Ka amshi budurcin ta kafin kafara Son ta aiko nine dole nace ba sona kaƙe ba sha'awata kaƙe"

Cikin damuwa Zaif yace"Than What Shall I do?"

Umar gyara zama yayi kafin yace"Zaka share ta, ka fita daga harkan ta kuma ka daina nuna kana damuwa da ita batun Son ta kuma kayi kamar baka Son ta kai dai Abinda zakayi kayi kamar baka taba sanin Mai suna Zahra ba a rayuwar ka, kaga daga nan Ni nafada maka da ƙanta Zahra zata zo tace tana Son ka, kuma batun kwanciyar Aure kuma ka hakura nadan lokuta kadan ita da kanta zatazo ta naimeka da kanta tana buƙatar ka, Kuma da Son samune ma idan tazo kaja mata aji kayi kamar kaima baka buƙatar hakan sai kaga tana shan wahala sannan ka biya mata buƙata kaga daga nan ma zakayi yadda kaƙe so da ita, nidai shine shawarar da zan baka idan yayi maka fa"

Murmushin da bayyi zato ba ya kuɓuce wa Zaif yana shafa kansa yace"That Good Solution"




Mima tana shiga Direct Office ɗin Abdullah ta nufa tana zuwa ta same shi kuwa yana saka da aiki
Jiransa tayi ya gama kafin ya fito da ita nan yabi ko ina na cikin Asibitin ya nuna mata da kuma aikin su
Office dinta ya nuna mata nan tayi godiya ta shiga

Tana zama kan kujera tace"Aiki banason ta amma sai nayi?"

Wata Nurse ce ta shigo hannunta riƙe da wasu Files
"Barka da zuwa Sister"

"Yawwa"tace tana kallon Nurse ɗin
Murmushi Nurse ɗin tayi kafin tace"Are You DR. ZAHRA ?"

"Yes I Am, Any problem Sis?"
Tace tana bin Nurse ɗin da Kallo

Miƙa mata Files ɗin tayi tace"Dr. Abdullah yace na kawo miki kiduba sai kisa hannu"

Kamar ba tayi tana yatsuna fuska
Ko karanta Files ɗin batayi ba ta sanya hannu ta miƙa wa Nurse ɗin

Kallonta Nurse tayi tace"Dr. Zahra Baki karanta bafa"
Harara Mima ta dalla mata kafin tace"Anywhere"

"Ok Thank" fita Nurse ɗin tayi


Misalin ƙarfe 2:00pm

Tana zaune a Office tana Game a wayan ta aka turo kofar Office ɗin aka shigo
Ɗagowa tayi
Murmushi tayi kafin ta miƙe tsaye tace"Dr. Abdullah "
Shima Murmushin yayi yace"Dr. Zahra kya muƙe jira fa"

Cikin rashin ganewa Mima tace"Like How?"
Yana Murmushi yace"Aiki We start now"
Mima batasan Kan Komai ba tace"Okayy"
Fita sukayi Abdullah yana gaba Mima na baye dashi suka nufi ɗakin tiyata
Suna shiga nan wata Nurse ta mikawa Mima kaya irrinta Likitoci wadda idan zasu shaga yin aiki a ɗakin tiyata
Kayan rigane da wando Blue da hula sai face mark da hanglop da takalmi
Suna shiga ciki Mima ta zaro ido waje
A zuciyar ta tace"Wai daman irrin wannan aikin ne ta sanya hannu?"
Tana fesar da numfashi tace"Akwai Matsala Wllhy"
Aiko aiki aka farayi na cire wa wani Soldier Bulet a kirjinsa
Inɗa Mima ta tsoro ta da hakan jikinta na kirma haka aka gama aikin suka fito
Direct Office ɗin ta ta wuce tana zuwa ta wuce Toilet nan ta fara korara amai babu gaggauta wa
Sanda tayi mai isar ta kafin ta wanke fuskar ta da bakinta ta fito tana sauke numfashi

Zama tayi kan kujera tana sauke numfashi
"Gaskiya akwai Matsala idan har wannan ne aikin"


Misalin ƙarfe 3:30pm
Dai dai Mima ta fito domin zuwa gida , tana tsaye daga gun parking space Motan Zaif ya turo kai
Tun daga nisa yaƙe kallonta yana Murmushin mugunta
Tunowa yayi da Maganan Umar sosai yaji daɗin shawarar da abokinsa ya bashi
A gaban ta yayi Parking
Mima na ganin sa ta turo baki tana ta kawa a hankali har ta isa inda Motan yaƙe
Tana zuwa ta buɗe kofar ta shige tana Sallama ƙasa ƙasa
Amsa yayi fuska babu yabo ba fallasa

"Ina wuni" tace tana kauda kanta
"Lafiya ya aiki?"
Tana fesar da numfashi tace"Alhmdllhi"
Daga haka babu wanda ya kara ce komai har Zaif yaja Motan suka bar asibitin



Ta fiya mai dan nisa sukayi kafin suka isa gida
Bayan yayi Parking ya fito
Itama ta fito
Ko kallon inɗa taƙe bai ba ya wuce part ɗin sa
Taɓe baki Mima tayi itama ta wuce ciki


Mima nashiga ta sami Ammeiy da Mary zaune a falo
Ammeiy na ganin ta tace"Wow My Daughter andawo daga gun aiki kenan?"
Mima tana Murmushi ta zauna gyafen Ammeiy tace"Ammeiy na gaji sosai"

Shafa kanta Tayi tace"Yakamata kije kiyi wanka ki kwanta ki huta kinji?"

Tana kallo Mary tace"Bab ya aiki?"
Mary na Murmushi tace"ai ke Yakamata na tambaya ya aiki tunda yau ne first"
Itama Murmushin tayi tace"gaskiya kam Wllhy aikin akwai wuya"
Dariya Mary tayi tace"Go and Rest first Sis"
Tashi tayi ta haura Bedroom


Zaif Yana shiga Part ɗin sa ya wuce Bedroom
Bayan ya cire kayan jikinsa ya faɗa Toilet yayo wanka kafin ya fito

Cikin riga da wando mara nauyi ya shirya kafin ya fito
Direct part ɗin cikin gidan ya nufa
Yana zuwa ya sami Ammeiy zaune ita kadai
Zama yayi yana kwantar da kansa bisa kafadar ta
Shafa kansa Ammeiy tayi tace"Ya aikin Son?"
Yana lumshe idon sa yace"Ammeiy Hungry"
Dagoda kansa tayi tana kallonsa tace"Ohhh Sorry Bara nasa a hado maka abinci"
Mima ta kwalawa kira

Lokacin Mima tana zaune tana danna lapton dinta itama ta sauya kayan jikinta zuwa doguwar riga ta Material sai bakin Hulan ta
Jin Ammeiy na kiranta yasa ta miƙe ta fice

"Ki haɗa wa Son abinci "

Tana yi masa wani irrin kallo tace"Ok Ammeiy"
Murmushi Zaif yayi ƙasa ƙasa kafin ya ɗago fuskar sa a Murtuke yana ya mutse fuska yace"Ammeiy Mary Bata nan ne?"
"Tana nan"
"To Ammeiy kice ta haɗo min"
Wani irin kallo Ammeiy tayi masa kafin tace"ga Matar ka sannan kace Mary ta haɗo ma abinci ita kuma Mima maye amfanin ta"
Yana shafa kansa yace"Ammeiy saina auro Babban Mace kafin na fara cin abincin Matata"
Aiko Mima zuciyarta ta bada sauti rasssss da sauri ta juya tana kallonsa

Zaif yana Mata wani irin kallo yana ya mutse fuska yace"Ammeiy gaskiya wannan baza tamin abinɗa raina ke so ba shiyasa na yanke shawarar na auro wacce zatana iya yimin Komai"

Ammeiy kasa yin Magana tayi tana kallon Zaif kafin tace"Son amma..... Ammeiy gaskiya kubari nayi abinɗa raina ke so tunɗa an tilasta ni na aure waccan kam nima kubari na aure wacce naƙe so"
Yana gama faɗin haka ya miƙe ya fice
Cikin fushi
Ammeiy da take masa tayin abincin yana fita yace"No Ammeiy"

Mima ji a sanyaye ta koma Bedroom
Zama tayi bakin bed tayi ta gumi
Mary tana fitowa daga wanka ta kalleta tace"Lafiya Sis Naga kinyi ta gumi"
Mima tana tara hawaye tace"Hero wai zayyi aure"
"Mtshwwwww shine kakai tagumi sai kace anyi miki mutuwa, ta sai maye dan zan kara Aure ai Nagadai ba Son sa kikeyi ba ai kinga abin nema ta samu"
Tana gama faɗin haka ta nufi wajan Wardrobe


Zaif Yana fata ta fashe da Dariya yana ciro da wayan sa a aljuhu
Umar ya kira bugu daya Umar ya Daga
Zaif yana Murmushi yace"Please zaka iya zuwa bayan Sallah Magarib?"
Umar da yasan komai yace"Hmmm ka fara kulla abin kenan, Eh zanzo"
Kashe wayan Zaif yayi yana zama kan kujerar daƙe Guarding
Kwantar da kansa yayi da jikin kujerar yana lumshe idonsa wani irrin sanyi yaƙe ji yana ratsa ta ko ina na jikinsa


Da Daddare misalin ƙarfe 9pm
Zaif ne zaune a babban falon gidan shida Umar suna sanye cikin Shadda masu kyau
Sai Ammeiy daƙe zaune gyafen su
Suna hira da Umar
Shiko Zaif hankalin sa yana wani wajan Allah Allah yaƙe Mima ta fito
Aiko sai gata ta fito riƙe da Plat
Yana ganin fitowar ta ya miƙe tsaye yana kallon Umar yace "Muje ko tayimin Text yanzu tana jiran dawowar mu"

Umar yana Murmushi yace"Ok, Ammeiy bara mu wuce"
Ammeiy ɗuk kanta ya kulle tana kallon Umar tace"Ina zaku haka?"
Umar yana Murmushi yace"Ammeiy rakasa zanyi daman wajan.."
Sai kuma yayi shiru yana Murmushi irrin yana jin kunya haka

Mima ɗuk abinɗa suƙe fadi tana tsaye jikinta sai rawa taƙe tana kallonsu

Umar suna nufar hanyar fita ya kalli Mima yace"a a Uwar gida an fito kenan"
Kasa yin Magana Mima tayi sai hawayen da ya taru a idanun ta

Zaif kam tuntuni ma ya fice daga Falon
Zuciyan sa fas ko babu komai ya kutun ta mata rai

Umar yana fita suka sa Dariya
Kallonsa Umar yayi yace"gaskiya fa Mutuniyar ka jikinta yayi sanyi "
"Hakan shine kadai hanyar da zan bi na san Zahra tana Sona Ko kuwa bata Sona"

Ɗariya Umar yasa yace"To Bara Ni na wuce kadda Madam ta jiran tajini shiru "
"Ok Saida safe"
Sallama sukayi kafin Umar yaja Motan ya fice
Shi kuwa Zaif yayo Part ɗin sa


Mima suna fita ta haura Bedroom tana zuwa ta faɗa kan bed ta saki kuka


Kallonta Mary tayi tace"Lafiya?"
Cikin kuka tace"Wllhy sister Hero aure zai kara da gaske gashi yanzu sun tafi hira wajan Budurwar sa shida Yaya Umar fa"

Mamaki sosai Mary tayi kafin tace"Mima You Love Uncle right?"
Tana turo Baki tace"niba Son sa naƙe yi ba"
"Hmmm?"
Ta tambaye ta tana kallon ta
Shiru Mima tayi tana share hawayen ta
Murmushi Mary tayi tana ɗafe kafadar ta tace"Mima da kinki da kinso wllhy kina son Uncle tunɗa har kina Kishin sa"
Batace komai ba ta miƙe ta shige Toilet
Girgiza kai Mary tayi tana ci gaba da wasa da wayan ta


Da asuba kuwa Mima jiki babu kwari ta tafi wajan wasan CRICKET
Bata dawo ba sai kusan karfe 9am
Tana zuwa a waje suka haɗu da Zaif

Zaif kuwa yana ganin ta ya ɗaura waya a kunnen sa ya fara faɗin"Eh Honey a shirye naƙe mana"
Shiru yayi kafin yace"Alhmdllhi kice yanzu naje na sami Abbeiy mana aje ayi Maganan auren mu"

Mima kasa Control din kanta tayi ta nufi Wajan sa
lokacin Zaif yana ƙoƙarin buɗe kofar Motan sa yaji ta kama hannun sa
Ɗagowa yayi yana Binta da wani irrin kallo kafin yace"Honey Ina zuwa please Bye I love you"
Zaro Ido Mima tayi tana kallon sa
Shima kallonta yaƙe
Ganin batada niyar sakin hannun sa yasa shi faɗin"Excuse Me Dr. Zahra"

Kuka Mima tasa tana Faɗawa jikin sa
Lumshe idonsa yayi yana jin kukan ta har cikin ransa
Hannu yasa ya rabata da jikinsa kafin yace"Stop Cry banason kukan nan"
Tana turo baki tace"Bakai ne ba"
Waro ido yayi yace"maye nayi Ni kuma?"
Tana shashshekar kuka tace"Aure zakayi"
Murmushi yayi yace"Kishi kiƙe Zahra"
Ɗagowa tayi ta kallesa tace"Niba kishi naƙe ba kawai dai" sai kuma tayi shiru
Murmushi yayi yace"Hmmm gwara kin daina yin kukan nan yafi dan Aure Ni Zaifudden babu fashi kuma nan da 1 Month insha Allahu zan zama Angon Shamsiyya, kinga na sami wacce zatana kula dani ta ringa bin umarni na, ke kuma kije Kiyi ta wasan CRICKET yafi komai Allah ya bada Sa'a"
Yana gama faɗin haka ya shige Motan sa yaja yabar gidan ransa ɗuk a ɓace

Mima jiki a sanyaye ta shige cikin giɗan

Bayan 3weeks
Mima tunɗa wannan abin ya haɗa ta da Zaif bata saƙe sanya shi a idanun taba
Tana zuwa aikin ta
Batun wasan CRICKET kuwa tun a wannan lokacin ta daina zuwa

Tana zaune a falo ita da Mary wayan ta ya ɗau Kara
Ɗuba tayi taga New Number ne
Tsaki taja taki dagawa
Kallonta Mary tayi tace"Kiyi Picking Mana ko Mijin kine tunɗa baya kasar kinga ɗole ya nemi Matar sa"
Ɗagowa tayi ta kalli Mary tace"Baya kasar kuma?"
Gira Mary ta ɗaga mata kafin tace"Yaje London daga nan idan zaizo sai tsaye a Dubai ya hado kayan lefen Matar "

Mima batasan sanɗa ta miƙe tsaye ba nan taƙe jiri ya fara ɗiban ta
Mary ganin haka yasa ta tashi ta kamo hannun ta cikin ruɗewa tace"Sis lafiya"
Mima wani irrin Amai ne yazo mata aiko ta fara kokara amai babu ko gaggauta wa
Mary kwalawa Ammeiy Kira tayi
Ammeiy fita tayi cikin tashin hankali tana kallon Mima na amai ta nufi wajan su
Kafin kace Maye Mima jiri ya ɗibe ta ta faɗi tsumammi ya

Cikin tashin hankali Ammeiy ta ɗauki waya ta kira Abbeiy ta sanar masa komai
"Gani nima ina kan shiga gida"cewan Abbeiy kit ya kashe wayan
Hijabin ta suka sanya mata kafin Abbeiy ya ɗauke ta suka sanya ta cikin Mota
Nan Abbeiy ya bawa Motan wuta suka bar gidan

A babban Hospital ɗin sa ya nufi da ita
Yana zuwa da kansa Abbeiy ya duba ta

Bayan sun sanya mata Drip Abbeiy ya fito jiki a sanyaye
Ammeiy na ganin sa ta nufi wajan sa tace"Alhaji yaya jikin nata"
Abbeiy kallon Ammeiy yayi yace"Muje Office"
Nan suka nufi Office ɗin Abbeiy
Bayan sun zauna Abbeiy ya kalli Ammeiy yace"She Have a pregnant"
Zaro Ido Ammeiy tayi tace"Alhaji Ciki fa kace Innadillahi wa'inna ilaihi raju'un......



More Comment
More Typing
Share Fisabidillah


👩‍🔬 *Dr. ZAHRA* 👩‍🔬

_*Funny, love story*_


*By Asmeety Ce*




*ELEGANT ONLINE WRITER'S*




*Free Book*



*Page-31&32*


*_Assalamun Alaikum Masoya ɗuk Mai buƙatar Book ɗin SARAUNIYA SADDIKA Document Naira 500 kacal. Gamai buƙata yayi min Magana ta wannan layin or WhatsApp 07089540330_****




**Short Story**


*_Bismillah Rahman Rahim_*

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai._


**Alhmdllhi Ala kulli Hamid**



"Innadillahi wa'inna ilaihi raju'un" Haka Ammeiy take ta maimaita wa
Abbeiy kam kasa yin koda matsin kirki yayi yana kallon Ammeiy
Can sai yace"Tunɗa mukayi musu aure sun taba ƙyaɓe wa ne ita da Son?"
Ammeiy tana kallon Abbeiy tace"A a gaskiya ban taba gani ba, kuma ba Son junan su suƙe ba kaga baza su taba aikata hakan ba tare da sun tare ba"
Numfashi Abbeiy yaja kafin yace"To ki gwada tuntubar Yayata mana May be ita zatasan komai tunɗa ƴar uwar tane "

"Gaskiya kam Alhaji dan bana tunanin Mima zata iya aikata haramtacciyar abin nan ba"cewar Ammeiy

Tashi tayi ta fice
A waje ta sami Mary tsaye
Mary na Kallon Ammeiy ta miƙe tace"Ammeiy Maye Abbeiy yace?"
Numfashi Ammeiy taja tana kallon Mary tace" Zauna na tambaye ki"
Zama sukayi kafin Ammeiy tace" akwai Abinda ya taba shiga tsakanin Mima da Son ne?"
"A a Ammeiy babu gaskiya"cewar Mary tana kallon Ammeiy

Ammeiy zufa ce ta fara keto Mata ta ko ina, hawaye ne ya fara zubo mata daga idanun ta
Cikin ruɗewa Mary tace"Ammeiy Mai ke faruwa ne, kodai Mima ta mutu Ammeiy"?"
"Ba gwara mutuwar ba da abin kunyar da Mima tajayo mana "
"Ammeiy maye Mima ta jayo kuma?"
"Maryam Ƴar uwar ki Zahra tana ɗauke da juna biyu harna wata ɗaya da sati biyu"
Mary batasan sanɗa ta rungume Ammeiy ba tana farin ciki

Ammeiy tana kallon ta tace"Farin ciki kiƙe bayan cikin bamusan ko na waye ba"
Mary tana Murmushi tace"Ammeiy ki kwantar da hankalin ki wannan cikin daƙe jikin Sis na Uncle ne"
Nan Mary ta bawa Ammeiy labarin komai
Ammeiy batasan sanɗa ta fashe da kukan daɗi ba
Tana godiya ga Allah

Abbeiy yana fita ya hangosu suna cikin wannan halin
Nufar wajan su yayi yana zuwa Ammeiy na ganin sa tace"Alhmdllhi Alhaji cikin na Son ne"
Abbeiy da Mamaki a fuskar sa yaƙe kallon Ammeiy shi abinma ya bashi Mamaki sai kuma yace"Yaran zamani kenan abinɗa bakai tunani ba shike faruwa Allah ya raya mana su ya Albarka ce rayuwar su"
Da Amen suka amsa kafin Abbeiy yayi musu iso zuwa dakin da aka kwantar da Mima

Turo kofan dakin sukayi
Kwance taƙe idanun ta a lumshe suƙe, jin an turo kofa yasa ta buɗe idanun ta
Tana ganin su Ammeiy ta miƙe zaune tana taro hawaye

Ammeiy cikin Murmushi ta karitso ta riko hannun ta tana kallon ta tace"Sorry Dear yaya jikin naki yanzu kike ji?"

"Da sauki Ammeiy yanzu bana jin komai"
Tace tana kwantar da kanta bisa kafadar Ammeiy

Abbeiy daƙe tsaye yana kallonta yace"Mamata babu abinɗa kike buƙata ne?"

Girgiza ƙanta tayi

Murmushi Mary tayi tana kallon Mima tace"Sis Sannu fa"
Harara Mima ta dalla mata kafin ta lumshe idonta


Misalin ƙarfe 2pm aka sallame su
Nan suka dawo gida

Bayan Mima tayi wanka ta kwanta kan bed nan ta lula duniyar Tunani

Mary ce ta shigo riƙe da Plat wadda yaƙe ɗauke da fruit salad da Glass Cup wadda shima yaƙe ɗauke da Banana juice
Zama tayi bakin bed kafin ta kalli Mima tace"Taso inji Ammeiy kici wannan Fruit da juice zakiji Daɗin sa"

Tashi tayi daman yunwa taƙe ji
Kallon Fruit ɗin tayi tana kwaɓe fuska kamar mai son yin kuka tace"Amai naƙe ji kuma Ni ba wannan naƙe so ba"
Mary tana Murmushi tace"ahh lalle sai yanzu na tabbatar da cewa gaskiya ne mata masu laulayi haka suƙe da zaban abin ci"
Kallon rashin fahimta Mima tayi wa Mary kafin tace"Maye kiƙe nufi da hakan?"
Mary tana ajiye Plat ɗin hannun ta tace"Eh Sis Ina nufin irrin ku masu karamin ciki haka kuke"
Tashi tsaye Mima tayi tana taro hawaye tace"Ciki fa kika ce? Kina nufin Ina ɗauke da Cikin Hero a jikina?"
"Eh mana Sis ai ba haramun ba ko?"
Mima fashewa tayi da kuka tana shafa cikin nata sai kuma ta saki Murmushi tace"Alhmdllhi komai na Allah ne dole na gode masa, koda banason Mahaifin wannan abinɗa ƙe cikin nawa ba to dole zanso yaron da zan haifa"

Tausayi sosai Mima ta bawa Mary
Tashi tayi ta kamo hannun ta suka zauna kafin ta kalleta tace"Sis Uncle Yana matuƙar Son ki amma ƙe kuma baki Son sa shiyasa ya nisanta kansa daƙe saboda kadda ya takura miki, kuma a halin yanzu haka ƙema kina matuƙar Son Uncle Hero please Dan Allah ki Kwantar da hankalin ki kinga ba lafiya gare ki ba kinji"
Rungume ta Tayi tana kuka tace"Sis gaskiya ina Son Hero Wllhy inason Mijina"
Bubbuga bayan ta Mary tayi kafin ta samu tayi shiru



After 2 month

Ammeiy ce zaune a falo tana kallo
Mima ta sauko
Riƙe taƙe da Laptop ɗin ta tana sanye da ƙatuwar hijabinta da ya sauka har ƙasa yana ja sai ɗan karamin cikinta da ya fito dagwas abinsa gwanin sha'awa


Zama tayi kan kujera tana faɗin"Ashhhhhhh!!"
Kallonta Ammeiy tayi tace"Yakamata kina hutawa Daughter Kinga yanzu kin fara nauyi wannan kina buƙatar hutu sosai"
Turo baki tayi tana kallon Ammeiy tace"Ammeiy nifa bana nauyi "
Dariya Ammeiy tayi
Suna cikin hira ta shigo da Sallama
Juyowa suka yi Ammeiy da Mima
Sanye yaƙe da ƙananun kaya riga ja sai Blue Black jens riƙe da Wayoyin sa a hannu

Mima tsayawa tayi tana kallon sa
Shima kallonta yaƙe
Kafin ya ɗauke ganin sa gare ta ya karitso cikin Falon
Zama yayi yana gaida Ammeiy
Murmushi Ammeiy tayi tace"sai yau ka tuna damu Son"
Murmushi yayi yace"Ammeiy aiki ne yayimin yawa"
"To Allah ya taimaka "
"Amen " yace

"Sannu da zuwa Uncle Hero"
"Sannu" yace kafin ya miƙe ya fice
Da kallo Mima ta bisa harya fice
Ajiyar zuciya ta sauƙe

Ammeiy na lura da ita tace"je ki kai masa abinci Daughter"
Tashi tayi ta nufi Kitchen
Bayan ta haɗo Masa ta jera su kan tiry ta fito tayo hanyar part ɗin sa


Zaif yana fita Direct Side ɗinsa ya nufa
Bedroom ya shiga ya rage kayan jikinsa ya faɗa Toilet
Wanka yayi ya fito
Cikin 3coter fari da blue ɗin riga mai karamin hannu ya shirya
Fita yayi falo ya sami waje ya zauna kan kujera yana kallon Tv


Turo kofar tayi a hankali bakinta ɗauke da Sallama
Zaif yana ganin itace ya ɗauki wayan sa ya sanya a kunne ta fara wayan ƙarya

Mima cikin sanyin jiki ta nufi wajan Daining ta ajiye tiry kafin ta nufi inɗa yaƙe
Tana zuwa ta sami waje ta zauna ƙasan kapet tana zama daƙer
Ko kallon inɗa taƙe bai ba yaci gaba da wayan sa

Zaman 30mint Mima tayi haryanzu Zaif bai daina yin wayan ba
Hakan yasa ta miƙe daƙer tayo hanyar fita
Tausayin ta yaji kafin yace"Come"
Komawa tayi jiki a sanyaye ta zauna daƙer
Ajiye wayan yayi yana ƙare mata kallo daga sama har zuwa ƙasa yaga ɗuk ta rame tayi baƙi ga ko kwalli babu a idanun ta balle kwalliya
Zama ya gyara kafin yace"Baki iya gaisuwa bane?"

Cikin sanyin Murya tace"Ina wuni Hero?"
Dauƙe kai yayi yace"Sanda na roka bazan amsa ba"

Tana zub da hawaye cikin rawar murya tace"Kayi hakuri dan Allah kaji"
Zaif jikinsa ne yayi sanyi tunani ya shiga yi yana faɗin "Why tayi sanyi haka kodai bata da Lafiya ne?"
Tambayan kan sa yaƙe amma babu amsa
"Taso nan" ya faɗa yana nuna mata gyafen sa
Tashi tayi ta zauna tana sunna kanta ƙasa
Kamo hannun ta yayi aiko da sauri ya saki hannu yana kallon ta cikin ruɗewa yace"Zahra mai yaƙe damin ki kodai baki da lafiya ne?"
Shiru tayi tana hawaye
Zaif hannu yasa ya zame hijabin daƙe jikinta
Zaro ido yayi saboda tozali da yayi da kashin wuyan ta ɗuk sun fito raɗa raɗa
Hannu yasa ya ɗago haɓar ta yana kallon ta yace"Tell Me What Rong with you?"
Fashewa tayi da kuka tana Faɗawa jikin sa
Sosai taƙe kukan ta kasa Control kanta
Zaif runtse Idanun sa yayi yana jin kukan nata kamar ana datsa masa wuta a cikin zuciyan sa
Mima cikin kuka tace"HERO I LOVE YOU"
Waro idonun sa daƙe lumshe yayi yana sanya hannunsa ya ɗago fuskar ta

Idanun ta ta buɗe kafin tace"Yes I LOVE YOU HERO please kadda ka saƙe Ni santa kanka dani Wllhy mutuwa zanyi idan ka saƙe"

Murmushi yayi yace"Zahra I'm sorry I can't loving you yanzu ma da shirin baki takardar sakin ki nazo, banason abinɗa zai saƙe ta kura miki a rayuwar ki"

Jirine yaso ɗiban ta tashi tayi tsaye tana kallon sa kafin ta sanya hannu kan dan karamin cikin ta wacce ta fito
Bakin ta na rawa tace"He....Hero No please don't leave Me please Wllhy Mutuwa zanyi"
Duk maganan da Mima ƙeyi idonun Zaif yana kan Cikin ta yana kallo
Hannu yasa ya shafi cikin kafin ya ɗago da kansa yana kallonta yace"Zahra isn't True?"
Gyaɗa Masa kai tayi tana sanya hannun ta kan nasa daƙe cikin ta

Zaif baisan sanda yaja ta zuwa jikinsa ba
Fashewa yayi da kuka kamar karamin yaro
Itama haka kukan ta fashe tana shige kirjinsa

Sun ɗau lokaci kafin a hankali ya zame jikinsa daga nata yana kallon fuskarta yace"Zahra Why Baki sanar min kina da ciki ba? ina ƙoƙari sanya ki cikin wani hali"
Tana shashshekar kuka tace"Hero I'm sorry please" tana riko hannun sa
Girgiza mata kai yayi yace"Banason ganin wannan hawayen,yana sani cikin tashin hankali"
Da sauri ta sanya hannu tana goge hawayen ta cikin ƙasa da Murya tace"Na daina to kagani ko"
Murmushi yayi yana kallon ta cikin wani irrin tsalo yace"Yaushe cikin ya bayyana?"
Nan taba shi labarin komai yadda Mary ta faɗa mata na Uncle zayyi Aure
Murmushi yayi yace"bakison na karo miki abokiyar zama ne Sunshine?"
Zame wa tayi ƙasa tana kamo hannun sa cikin kuka tace"Dan Allah kadda kayimin Kishiya Wllhy idan ka aure wata kashe kaina zanyi"
Dagota yayi yana faɗin"Muje naci abinci yunwa naƙe ji"
Wajan Daining Table suka nufi
Zama sukayi nan Mima ta zuba masa kafin ta ajiye masa
Kallonta yayi yace"And you?"
Girgiza kai tayi tana wasa da yatsun hannunta tace"Ni naci nawa na koshi"
Baice komai ba ya fara cikin abincin
Shiru wajan bakajin karar komai saina Spoon
Time to Time Zaif Yana ɗago Yana kallonta
Itako Mima ƙanta a katsa tana wasa da zoben hannun ta
Bayan ya gama ci ya kalleta yace"rakani na wanke bakina"
Hannun ta ya kamo suka nufi Bedroom ɗin sa
Direct Toilet suka shiga
Bayan ya wanke bakinsa suka fito
Riƙe yaƙe da hannun ta har suka nufi part ɗin cikin gidan
A falo suka sami Abbeiy da Ammeiy zaune
Zama sukayi a kasan Capet inɗa Mima daƙer ta zauna Abbeiy na yi mata sannu
Bayan sun zauna ya gaida Abbeiy
Kallon sa Abbeiy yayi yace"Ya aikin kuma?"
"Abbeiy Alhamdulillah aiki yana tafiya yadda Yakamata"
Yace yana kallon Mima da cikin ta
Abbeiy yana kallon Zaif yace"To Allah ya bada Sa'a,kuma daman inason Magana daku dukan ku biyun"
Hankalin su suka baiwa Abbeiy nan Abbeiy yaci gaba da faɗin"Tunɗa Allah yasa kazo daman kai muƙe jira idan kazo zaku tare da Matar ka cikin daya daga gidajen ka kafin Allah ya sauƙe ta Lafiya kuma"
Yana ɗukar da kai yace"Abbeiy hakan ma yayi amma naga anan zatafi samin kulawar Ammeiy Mai zai hana ta zauna anan ɗin?"
Jingina kai Abbeiy yayi yana kallon Ɗan nasa Lalle Allah ya bashi Ɗa mai hankali dakuma wasan ya kamata
Numfashi Abbeiy yaja kafin yace"Shikenan babu komai, amma sai ku tare ko a bangaren ka kafin nan"
"To Abbeiy"yace yana jin daɗi

Ammeiy kallon su tayi tace"Muɗai ba'a neman shawarar mu ko kunyi abinku kai da ɗan ka"
Dariya Abbeiy yayi yace"Eh ƙyama kuje kuyi taku da ƴar ki mana"
Murmushi Ammeiy tayi tace"ai tamu

Please Login or Register in order to submit comment