Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

min".
Yana kaiwa nan ya juya yafuce,
shiko Usman ganin haka yabi bayan shi da sauri a palour ya sameshi yana shirin fita,
da sauri ya kamo hannun Adam d'in kan kujere ya jawoshi suka zauna murya can k'asa yace,
Adam please karka gayawa kowa maganar nan".
ido Adam ya rumtse wasu hawaye masu zafi suka zubo a fuskarshi ranshi cike da tausayi Usman a hankali yace,
"Usman meyasa kake son b'oye min matsalar ka wacce kasan zan iya magan ceta".
shiru yayi cikin lumshe idanun shi murya can k'asa yace,
"Ina son Ummul Adam ina sonta ina son zama da ita da yaro na, bana son b'acin ranta bana son suyi nesa dani nafi son na renesu da kaina nafi son na kula da jinin Hammana da kaina bana son Farouq yayi agolanci bana kuma son rabashi da mahaifiyarshi bana son ya taso kamar yadda nida Hamma na muka taso ba Uba uwar kuma bata kusa damu bana so Farouq ya tashi a gida na kuma ace ba mahaifiya shi
bace ta reneshi,
kuma bana son b'acin ran Ummul ko abinda zai tayar mata da hankali gashi ta tsani aure bata son a mata maganar aure sai tayi ta kuka kukanta na sani cikin k'unci sai in rink'a ganin na gaza samawa iyalen Hammana farin ciki ne bana son b'acin ran ta ina jin ciwon biyu in tana kuka,
Adam kamin alkawarin zaka rik'e min wannan sirrin nawa muyita addu'a har muga abinda Allah zaiyi mana da ikon shi a hankali farin cikin Ummul zai dawo".
Juyowa Adam yayi cikin kuka ya rungumi d'an uwan nashi suka cigaba da kuka mai cin rai har zuwa d'an wani lokaci,
a haka sunata kuka babu mai rarrashin wani haka suka gaji suka kai shiru,
a hankali Adam ya kwantar da kanshi akan cinyar Usman d'in murya na rawa yace, "Ya Usman to haka zamuyi ta zama da wannan damuwar?
har sai yaushe farin cikin mu zai dawo?
shin fushi mukeyi da hukun cin mahaliccin mu kenan?
shin bazamu gane cewa wannan rubutaccen al'amari ne daga Allah ba ko so muke mu raunata imanin mune haka zamu rayu kullum ba walwala, addu'ar da muke yiwa Hamma itace so mu daure mu bar kuka,
ka auri Ummul ka reni Farouq da kanka tunda aure dai abin yine tunda da lafiyar ka?".
Cikin sanyi da rauni ido cike da k'ollah,
Usman ya shafa kanshi murya a raunane yace,
"A a Adam bazamu zauna cikin k'unci ba done wata rana zamuyi farin ciki ai ya rigada Allah ya sama bayinshi mantuwa a ransu ba dan mantuwar da Allah ya sa mana ba da ciwon mutuwar wani zai jawo na wani ba dan danganar da Allah ya samin ba da ciwon mutuwar Hammana ya kasheni Adam kalli rubutaccen al'amari yau ni Usman mai hujejjiyar zuciya ina raye nida kowa ke zatawa mutuwa amman bata d'aukeni ba sai ta d'auke Hamma na wanda ba'a tuna maiba kuma ta hanyar da ba zato ba tsammani,
Adam zamuyi ta addu a Allah zai mana maganin damuwar mu nagode naji dadi da samun d'an uwa mai rik'emin sirrina". Murmushi k'arfin hali Adam yayi sannan ya tashi yakoma bedroom ya fad'a bandaki ya sakarma kanshi ruwa,
shiko Usman tashi yayi ya d'auko qura'an ya fara karatu cikin rauni da halarto da kushi'i tun yana yi yana zubda k'ollah har yaji zuciyar shi ta fara sanyi a hankali yaji k'unshin ranshi na gushewa,
Qura'ani kenan mai girma maganin hawan jini maganin ciwon suga maganin jutar daji maganin Iblis da junnu da mugun bani Adam duk tsanani sauk'in shi nan cikin qura'ani sai dai in mutum bai lizamceshi ba.

A parlour bak'in Kuwa Mustapha yanata aikin rarrashi a hankali ya taso yamatso kuda da kujerar da Ummul ke zaune ya zama yayi a gaban ta ya tonk'oshe k'afafun shi a cikin sanyin murya da tausasawa yace,
"Ummul narok'eki kiyi hakuri kiji tausayi na ki sassautawa zuciyarki Khairi na kinfi kowa sanin yanda nake jinki a zuciya ta kukan ki yana k'onamin zuciya, kiyi hakuri kibani dama indawo miki da farin cikin ki Ummul ina sonki wallahi ina miki son da bana yiwa kaina Ummul rayuwa ta zata cikane kawai idan ina tare dake".
Yanda yaga Ummul ta d'ago kanta cikin razana ta zuba mai manyan idanuwan ta da suka canza kala zuwa jawur yasa yai shiru ya zuba mata nashi idanun.
Kalmar da Ummul taso fad'amai ta "bana sonka". ce ta kasa fito sakama kon tunawa da tayi da yanda taita furtawa Hamman ta kalmar wadda gashi yanzu tazamo mata sana diyyar b'acewar farin cikin ta a yanzu wanda bata tab'a yin nadamar wani abu a duniya kamar shiba,
wani irin abune yataso mata ya tokare mata zuciya dakyar ta samu ta fisgo wani irin nannauyan ajin zuciya wanda ya fito da kuka mai k'una da zafi,
ido a rufe ta rab'a gefen Mustapha da sassarfa tayi cikin gida,
shiko Mustapha binta yayi da kallo harta fita sannan ya juya jiki babu k'arfi ya koma yad'auki Umar Faruq daketa wasanshi ya rungume yanajin wani irin so da kaunar yaron da mahaifiyar shi Ummul a ranshi sannan ya fito,
Ita kuwa Ummul da gudu tafad'a cinyar Ammi tasaki kuka mai k'arfi jikinta duk na rawa,
a gigece Ammi take tabbayar ta,
"menene Mama na kiyi hakuri ki fad'amin mana meke faruwa?".
Aliyu daya biyo bayanta ya zuba gwiwa a k'asa shima hawaye na bin fuskarsa ganin yadda Ummul ke wani irin kuka kamar ranta zai fita ko ina jikinta rawa yake,
Nanne da ya sadiq suma da gudun suka shugo,
Nanne ma tuni jikinta yad'au rawa zuciyar ta na bugawa ganin yadda Ummul tafita hayyacin ta dan kuka,
ya Sadiq d'in ne ya matsota ya dago kafad'arta ya janyota jikin shi,
aiko shima tuni zuciyar shi tayi rauni dan jin zafin jikinta da yanda jikinta ke rawa cikin sassauta murya yace,
"Ummu na meya sameki ne?".
K'ara tusa kanta tayi a cikin cinyoyinta ta k'ara sakin kuka mai k'arfi,
Su Usman kuwa sai yanzu suka fito shi da Adam zasu shige part d'in Nanne,
a farfajiyar gidan sukaci karo da Mustapha wanda ke rik'e da Umar Farouq,
aiko yana ganin Abban shi Usman ya mik'o hannu shima Usman da murmushi yakai hannu ya karb'e shi sannan ya mik'ama Mustapha hannu suka gaisa cikin sakin fuska sannan suka gaisa da Adam yai musu sallama ya shafa kan Farouq tare da cewa,
"bye bye bobona".
Amman yajuya ya nufi motarshi cike da damuwa da kunar zuciya da jin zafin kukan da Ummul take yi.

Su kuwa da sauri suka k'arasa bangaren Nanne jiki na rawa dan jiyo kukan Ummul da sukayi
cikin k'unar rai da firgici Usman yake salati idanuwan shi sun rufe da kyar ya matsa jikin gini ya jingina yana sauke numfashi da kyar,
ya Adam ne ya k'arasa gurin ya dafa kafad'ar ya Sadiq yace,
"meke faruwa ne? meya sameta?".
Kai kawai Sadiq ke juyawa dan haka Adam ya tsuguna ya d'auko Ummul daga jikin Sadiq ya gyara zama ya kuma matsota jikin shi sannan yasa hannu ya kamo fuskarta cikin rarrashi yace,
"k'anwata kiyi hakuri ki sanar damu damuwar ki,
kinga dukkan mu hankalin mu ya tashi, kinga yaronki yana kallonki kada kisa mufara zargin kanmu da rashin cikawa Hamman mu al'kawarin rashi baki kulawa,
daure ki fad'a mana". sai kuma yasake sa hannu ya d'ago kanta yace,
"kallemu Ummul dukkanmu zamu iya jure duk wani abu dan mu samar maki farin ciki ki daure ki fad'a mana koma menene?".
Cikin kukan ta sauke nan nauyar ajiyar zuciya sannan tasake cusa kanta jikin Ammi murya na rawa tace,
"Ya Adam dan Allah ka hana Mustapha zuwa gidan nan,
wallahi bana sonshi, ba zan sake son kowaba bayan Hamma na bazan so kowaba bare ma Mustapha wanda soyayyar sace tasa na kasa ganin soyayyar da Hamma na yake min na tsani Mustapha dan shine sanadin bijirewa Abbana duk da bai zugani ba kuma ya nusar dani da inbi zabin iyayena amman taurin kai da zuqar shaid'an tasa nak'i masoyi na auren Hamma na ya isheni ni nagama aure bana son ganin shi bana son ganin fuskar shi,bazan aure shiba bazan auri kowaba a barni da auren Hamma na dan Allah".
Kafin kowa yayi magana Usman dake tsaye jikin bango ya sauke ajiyar zuciya ya mik'awa ya Sadiq dake kusa dashi Faruq sannan ya matsa kusa da ita ya tsugunna ya kamo hannun Ummul itama d'ago kai tayi tana kallon shi cike da rauni da tsantsar nadamar illar rashin bin umarnin iyaye tace,
"Ya Usman".
da sauri yasa yatsa akan lips d'inta dasu kayi jawur sabida kuka a hankali yace,
"Na sani Ummu na kiyi hakuri zamuyi duk yadda kike so amma saikin daina kukan nan sai na dena ganin hawayen ki".
Kai ta d'agamai sannan yayi murmushi yace,
"Yawwa k'anwata Allah miki albarka".
dukkan su suka amsa da "Amin".


Mustapha kuwa yakasa zaune yakasa tsaye zuciyarshi takasa samun sukuni yanajin bazai iya rayuwa inba Ummul haka nan yayita fama da tunani da damuwa kullum saiya kira wayar Aliyu yace yakai ma Ummul suyi magana,
amma idan Aliyu ya kawo sai tak'i karb'a shima wani lokacin baya kawowa sai yace tana bacci dan shima bayason damuwar ta.


Farouq nada watanni 17 ya k'ara wayo da kyau yana yawon shi ko ina sannan Ummul ta yayeshi,
Ummul da ya Usman kuwa kullum shakuwar su k'ara k'arfi take indai yana gida bai fitaba to suna tare a palour Nanne ko na Hajjajo, Ummul bata tab'a rasa wani abuba dan koda yaushe Usman na cikin tarairayar ta da tambayar me take buk'ata inko ya fita zai dawo to da tsara barta kala-kala yanzu Farouq ya cika shekara biyu har ya shiga na uku.


Wata ranar Jimmy'a da yamma Abba da Daddy suka shigo palour Hajjajo suka inda suka sami yaran nasu dukkan su suna ta hira suna shiga Farouq yaje gaban Abba da gudu ya taho yana oyoyo Abba,
cikin happy Abban ya bud'e hannu wan shi Farouq ya fad'a ya d'agashi sama yace, "sarkin wasa ya akayi".
Daddy ne yayi murmushi yasa hannu ya karb'e shi tare da yace,
"zo nan in tafi dakai gidana".
wuri suka samu suka zauna bayan sun zauna ya Usman ne yafara gaida su suka amsa sannan kowa ya mik'a tashi gaisuwar. saida suma suka gaida Hajjajo sannan Abba ya kalli Usman cikin kulawa yace,
"Usman naji d'azu wani abokina yana waya da yaranshi yana fad'a musu ankirashi ance anfara saida admission form na NCE a nan FCE(T) shine nace inna sameku zamuyi shawara tunda k'anwarku tak'i maganar aure ko zaku saya mata saita fara kara?".
gyara Zama Usman yayi sannan yace,
"to Abba zamuyi shawara insha Allahu zamu sanar daku duk abinda mukayi mungode".
Daddy ya jinjina kai yace,
"to Allah yayi maku al'barka".
Dukkansu suka amsa da "amin".
sannan suka d'an tab'a hira jimawa kad'an suka tashi suka fita,
suna fita Ummul da zuciyarta tafara bugawa tunda Abba yafara magana ta mike jiki ba kwari ta fita, Usman ma mik'ewa yayi yabi bayanta Adam kuwa ya zuba musu idanu cike da tausayin yadda Usman d'in yake fama da soyayyar k'anwar tashi.

Shiko Usman yana shiga yasame ta zaune kan kujera yasami gefenta ya zauna a hankali cikin tattausan lafazi
yace,
"Ummuna meyasa su Abba na fita kika taso kika baro gurin mutane kikazo nan ke kad'ai ? kinsan bana son damuwar ki kuma banaso ki b'oyemin komai".
d'ago kai tayi tare da yin rau-rau da ido alamar zatayi kuka murya na rawa tace,
"Ya Usman wlh bana son karatun na hakura da komai a rayuwa ta zan zauna in dauwama ina yiwa Hamma Umar addu'a,
banajin dad'in komai a rayuwa ta bani da wani sauran farin ci daya wuce inga ina yiwa Hamma na addu'a,
dan Allah kacewa Abba bana son kara tun wanda nayi a baya ya isheni, yayi hak'uri ya barni". tana gamawa ta kwab'e fuska zatai kuka,
Da sauri yasa hannu ya tallabo hab'arta cikin tattausan lafazi yace,
"farin cikin ki zai dawo bazamu dawwama cikin k'uncin rayuwa ba Ummuna ki bani dama ni Usman zan dawo da farin cikin ki ta yadda Hamma na zaiyi Al'fahari dani".
lallashinta ya rink'ayi da kalamai masu taushi da sanyaya zuciya,
itako Ummul sai cigaba da zubda k'ollah take tana d'an narkewa, dakyar yasamu ta hakura sannan yace,
"ba wanda zai kaiki makara tar anan zamuyi zaman mu ko har sai Allah ya dawo mana da farin cikin mu?".
Dakai ta amsamai sannan ta matsoshi ta kwantar da kanta a kafad'ar shi numfa shin ta na fita a hankali tuni Usman yafara zaucewa a hankali yakai hannu ya d'an tureta sannan ya rumtse ido yana shafa kanshi zuwa wuyan shi yanajin kaunar ta na tsuma ko ina na jikin shi,
cikin sanyi yace,
"Allah ya d'ayyiba".
kai ta d'ago ta zura mai ido cikin murmushi tace,
"Ya Usman ina son ka".
ido ya bud'e da sauri sannan ya k'ara matsowa kusa da ita a hankali yace,
"Da gaske kina sona?".
kai ta gyad'a mai tare da kad'a harce tace,
"ehh mana ina sonka".
kai ya juya cikin k'arfin hali yace,
"Allah ya d'aiyiba nima ina sonki so na hak'ik'a,
Ummu ina sonki zan aureki mu reni Farouq da hannun mu,
ina sonki ina shawa'awar rayuwa da ke a k'ark'ashin inuwar aure bisa sunna Ummu ina sonnnn ki zan dawo miki da farin cikin ki nima ki tallafawa rayuwa ta".
Ido ta zazzaro tare da fuska tsuke cikin zubda k'ollah murya a carke tace,
"Na shiga uku ya Usman".
sai kuma ta mik'e da sauri ta gudu d'akinta ita da Ammi,
a haka tasu hirar ta watsent a palour Nanne,
inda ita ko Nenne duk taji abin da suke cewa dan tana cikin kitchen,
shiko a nan ya zauna ya kasa tashi inda ya sametan,
sai lokacin sallah la'asar yatashi tafiya masallaci,
sai ya shiga d'akin nata dan yasan Ammi tana parlour Hajjajo,
yana shiga ya d'ago ta yasa hannu ya shafa fuskarta yakai yatsan shi kan lips d'inta ya lumshe idanuwan shi da suka canja launi sannan ya juya ya fice tare da cewa,
"Ina son ki Ummu so irin na aure ban saniba ko nima zaki tsanene kamar Hamma sai randa na mutu ki soni".
yana fita itema tashi tayi tashige toilet wonka takeyi tana kuka ta rasa matsayin Usman a gareta shike tayata batun kartayi aure yau kuma shike cewa zai aureta me sunanta inta aureshi ta auri yaya ta auri k'ani yau ya Usman ke mata zaurancen saida Hamman ta ya rasu take sonshi a haka tayi ta kokenta,
sannan ta fito dan yin Sallah.



Ranar wata lahadi Ummul na kwance a cinyar Aunty Halima datazo tun safe tanayi mata kitso,
Aliyu ne ya shigo ya zauna gaban Ummul yace,
"Aunty Ummul Dr Bashir yazo yana palour yana jiranki, kamar bazata amsaba saida ta d'au lokaci sannan ta ce,
"ina zuwa, ina Farouq fa?".
cikin jin dad'i Aliyu yayi y'ar dariya yace,
"ai muna ball yana ganin motar yatafi da gudu saida na rik'eshi motar ta tsaya yana fitowa na sakeshi yatafi da gudu gunshi".
Aunty Halima ce ta d'anyi murmushi tare da cewa,
"ya ganeshi kenan?".
Sadiq ne dake kwance kan kujera yana latsa wayar shi yace,
"ai Farouq ko sau biyu kazo gidan nan a na uku sai yanuna ya ganeka,
balle Hamma Bashir da duk sati sai yazo indai yana gari".
murmushi sukayi baki d'aya sannan ita kuma Ummul ta
d'auko hijabi tasaka tafita.

zaune tasame shi a k'asan carpet yabud'e ledar da yazo da ita yana b'arewa Farouq sweet din dayasaba kawo mishi,
sallama tai tasami guri ta zauna sannan cikin nutsuwa ta ca,
"ina wuni?".
da fara'a d'auke a fuskar shi ya d'ago kai yace,
"lafiya Ummul khair ya mutanen gida?".
Kanta a k'asa tace, "suna lafiya".
shiko Farouq cikin kici-kici yasa
DOWNLOAD
DOWNLOAD

4 Comments On RUBUTACCEN ALAMARI
avatar
shukra-sulaiman

8 months ago

Reply

Thanks

avatar
shuraihu

8 months ago

Reply

Replying to shukra-sulaiman

Tnx too

avatar
fatima-idris

8 months ago

Reply

Nice novel

avatar
taskar

8 months ago

Reply

Replying to fatima-idris

Aha tnx

Please Login or Register in order to submit comment