Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ƙuna a zuciya ta nuna fuskokin da ake nunawa a tv tace ,
"Ya Usman kallesu sune suka yankamin Hamma na a gabana sune suka kasheshi wallahi har abadan bazan manta waɗan nan fuskokin ba bazan manta fuskokin suba wallahi sune".
Gaba ɗaya jikinta na rawa,
sosai Usman yasake matsota ya tare mata fuskar ta daga kallon tv shima yana rumtse idanun shi da ƙarfi dan har abada bazai so ƙara kallon waɗannan mutanen da suka kashe mai Hamman shiba,
Adam dayake tsaye jikin shi yana rawa yafara musu bayani,
"Hakane cikin azumi wani azumi daya wuce ankama waɗanda suka kai harin bomb a Jos! Kano da Zaria a gurin da ake verification na malaman makaranta, an kamasu ne a hanyar komawar su a Daɗin Kowa ta jahir Gombe, wannan da take nunawa yanzu dashi a cikin su yanzu kuma dasune akayi musaya suka bada y'anmatan Chibok da aka sace sukuma aka badasu wa uƙiyar tasu".
Sadiq ne yakar ɓi zancen da cewa,
"Ammi waɗannan dukkansu y'an asalin nan potiskum ne fa wata ƙil".
Usman da tunda aka fara maganar baice komaiba sai addu'a da yaketa tofa mata,
ganin har yanzu bata dawo hayyacin taba yasa yamiƙe hankali itama ya ɗagota duk jikinta na rawa suka fita yanufi ɓangaren shi da ita tana makale dashi tana rawar jiki da zazzaro idanuwa,
Suko su Ammi da su Adam ɗin gaba ɗaya haka suka zauna sunata jajantawa da yiwa Hamma Umar ɗin addu'a.


A ɓangaren su Ummul kuwa kukan taketa yi a kiɗime,
ganin haka yasa Usman ya wuce da ita part nasu kan kujera ya jawota suka zauna
rarrashin ta ya rinƙayi amman ina ya rigada Ummu ta buɗe shafin kuku dan ganin fuskokin waɗanda suka kashe mata ɗan uwanta kuma mijin ta,
jawota jikin shi yayi a hankali ya tallabo haɓarta cikin sanyi da zubda ƙollah ya haɗe bakin shi da nata wuri ɗaya kissing ɗinta ya rinƙayi cikin salon son tsaida kukan nata daga nan ya gama rikitata da salon soyayyar shi mai tsanani duk da kuwa shima yanayi yana zubda hawaye,
haka suka kwana ranar ma yanata ririta ta da son sama mata nitsuwa,
sai dai duk yanda yaso daya samu damar raɓarta bata bashi damar kusantar taba shikuma baida niyyar takurata haka dole ya haƙura kamar yadda ya haƙura jiya,
Asubar fari ta tashi ta gudu kamar yadda tayi jiyan.




Usman ne yasami Abba da Daddy a safiyar litinin a palour Hajjajo yake sanar dasu cewa tafiyar shi zata kama cikin satin nan zuwa ranar juma a, kuma zaitafi da matar shi dakuma yaronshi Farouq duk da ba daɗewa zaiyi ba aiki ne kawai zaije na watanni uku yadawo,
Addu'a sukayi mashi cikin jin daɗi sannan Abba yace,
"Usman bazan hanaka ɗaukar matar ka da yaron kuba amma inaso ka fahimci hakan zai iya taɓamai karatu shi kada kayi tunanin dan yanzu yafara bazai sami matsala ba amma kaga ko zuwa kayi ka sakashi makaranta acan watanni 3 kawai zaiyi kasake ɗaukoshi kudawo kaga canje-canjen makaranta baida daɗi ga yaro dan haka kayi hakuri kutafi kubarshi anan yana zuwa makaran tar shi har kudawo ku sameshi ina ganin baza a sami wata matsalaba tunda daman yasaba da iyayen ku gakuma Adam da Sadiq sannan ga abokinshi Aliyu".

Kanshi a kasa idonshi yafara ƙollah ya daure ya danne halin da yake ciki gudun kada su Abba su gane a hankali yace,
"To Abba shikenan saimu barshi".
sai ya kuma ɗan gyara zama cikin sanyi yace,
"Abba dama Ummu tace min tana son zuwa gun AYSHA ALIYU GARKUWA marubuciyar dake rubuta labarin tannan to dama mun gama shiri kafin mu tafi Malesia sai munje garin su Garkuwar toh shine nake so in zamuje can ɗin kam a barmu mu tafi da Farouq dan itama Aysha tana son ganin Farouq ɗin".
Daddy ne ya ɗan kalleshi cikin murmushi yace,
" ba damuwa Usman Allah yayi muku albarka yasa ayi tafiyar a sa'a Allah ya kuma dawo daku lafiya".
Da "Ameeen duka suka amsa sannan sukayi ta tattaunawa kafin suka watse.


Ɗaki Usman ya koma yafaɗa kan gado yanajin wani irin zafi a zuciyar shi idanuwan shi na zubar da kollah a hankali yajanyo wayar shi yakira Ummul tana ɗagawa yace,
"Kisameni a ɗaki".
yana faɗin haka ya katse kiran,
jin muryarshi yasa jikinta yin sanyi dan ta fahimci akwai damuwa tattare dashi dan haka ba ɓata lokaci ta fita ta nufi ɗakin nashi.

Sallama tayi a parlour taji babu motsin shi dan haka ta murɗa kofar bedroom ɗin a hankali da sallama ta shiga,
kwance yake yana kife a haka ya amsa sallamar ta yaɗago hannu ya kamota sannan ya juyo ya janyota jikin shi zamewa tayi ganin ƙollah a idanun shi tasa hannu ta goge mai a hankali tace,
"Menene kuma?".
Shima tashi yayi ys zaune ya ɗora kanshi akan kafaɗarta duk ya narke a jikin ta cikin shogoɓa yace,

"ba komai Ummuna".

hannu tasa ta shafa sajen fuskarshi tare da cusa hanun ta cikin suman kanshi tana ɗan murza yatsunta a ciki murya can ƙasa cikin raɗa tace,
"Da komai kam ya Usman,
daman tunda naji Abba yaje yana faɗama Ammi da Nanne yanda kukayi akan tafiyar nan kuma naga kiranka sannan naji muryarka nasan abunda kake wa kukan".
Hannu tasa tashafi gefen fuskarshi tare da shafa wuyanshi zuwa ƙeyan shi ta ƙara manna kanshi a ƙirjinta cikin tattausan lafazi tare da sanyin murya tace,
"Yanzu saboda sunce kabar Farouq ne kake kuka?
Baka yarda da kulawar da zasu bashi bane? dan Allah ya Usman ka rege son da kakewa Farouq dan Allah kada kabari wani daga cikin iyayenmu yaga raunin zuciyarka akan wannan abun,
domin baza suji daɗi ba,
ni dakai zamuyi ƙoƙari mu danne damuwar mu musawa zuciyoyin mu haƙuri tunda ba rabamu dashi akayi gaba ɗayaba watanni 3 kamar yaune kadaure kaji ko? ya Usman na ko sokake nima nakasa jurewa nayi kuka har su gani?".
Ɗago kanshi yayi yana juya mata kai alamar a,a duk ya wani maraice mata tamkar yaro sai fama nuƙurƙusanta yake da salon sakalcin sa da Hamma Umar ya sakal tashi,
a hankali yasa hannu yakamo fuskarta ya zuba mata idanu sannan cikin karya murya yace,
"Nabari Noor ƙalbee na nadena zan jure badan raina yaso hakan ba Ummu bana son duk wani abu da zai nisan tani da Farouq".
ganin zai sake tada rigimar tasa yasa ta ɗan tureshi ya konta sannan ta ɗan kifa ƙirjinta kan nashi a hankali ta ɗan murza haɓarta a kan sajen shi cikin salon kawar mai da damuwar tace,
"Naji ka gayawa Abba zamuje garin su Anty Aysha ko?".
kai kawai ya iya gyaɗa mata dan tuni ta rikatashi ta yadda ko maganar zata bashi wuyan yi,
ita kuwa lips enshi ta kalla sannan tasa yar yatsarta tana zagaye lips en nashi cikin happy ta lumshe ido tare da cewa,
"To yaushe zamu tafi? in munje kwana nawa zamuyi?".
hannu yasa yana shafa bayan ta a hankali cikin cushewar voice yace,
"Hmmmm hahhhh gobe zamu tafi kuma kwana biyu zamuyi,
in muna dawowa zamu biya Yankari muyi kwana ɗaya in mun dawo da kwana ɗaya zamu wuce malesia".
murmushi tayi tare da subbatar lips enshi sai kuma tayi maza zata janye jikin ta,
amman ina tuni Usman ya samu damar yi mata tsotsar Lolly pop a
haka sukaita lallashin juna sannan suka rabu ta koma cikin gida ta fara shirin zuwa garin Fulɓe gun Antyn ta Garkuwa.

Washe gari da safe suka kama hanya dan tafiya ce mai nisa a tsakani,
inda Garkuwa kuwa take ta farin ciki da zuwansu tana ta shirya musu tarba ta musamman,
Alhamdulillah sun zo lafiya ga Garkuwa ga Ummul ga Usman ga Farouq ɗan Hamma Umar,
sunsha hira sosai
Inda sukayi kwanakin su cikin jin daɗi sannan suka shirya suka koma jiharsu ta Yobe sun koma lafiya sun bar Garkuwa cikin kewar Ummu da Farouq da Usman Allah ya ɗaiyiba.


Shirye-shirye suke dan tafiyar su kasancewa zasu tafi ranar juma a su tashi zuwa kasar malesia.

Ranar juma a misalin 12:00 am jirginsu ya tashi zuwa Dubai inda dagacan kuma suka hau jirgin Qatar air ways zuwa kasar malesia, sun sauka a filin sauka da tashin jirage na jalah sultan isma'il, kuala lumpur. daga nan suka ɗauki hanya da jagoran cin wasu abokan aikin ya Usman dake can da zama zuwa jalal pentaling tafiyace mai nisa sukayi saida suka wuce masjid Jamet da flea market sannan suka ɗauki hanyar pentaling street, anan ne suka tsaya a fest shin kee beef noodles suka sai abinci sannan suka wuce soho city inda duka sauƙa a ɗan madaidaicin gidan da aka basu,
wanda yake da 2 bedroom sai parlour su mai d'an girma sai kitching da dinning area gida dai ɗan dai-dai buƙatar su kuma akwai komai na kayan more rayuwa,
da duk wani kayan bukata a gidan,
a gajiye suke dan haka sukayi wanka suka ɗanci abincin da bai musu daɗiba suncine dan yunwa suka kwanta bacci.


Haka suka kwana cikin ɗan gajiya sai asuba suka tashi sukayi wonka sannan sukayi sallah suna idarwa suka ɗanyi karatu har zuwa 7:30 nasu na can wanda yayi dai-dai da kusan ƙarfe biyu kenan a ƙasarmu nan,
a hankali Ummu ta ɗanyi miƙa tare da yin hamma a hankali ta yuƙura zata tashi,
da sauri Usman dake kallon ta cikin wani irin salo ya ɗan jawota jikin shi sannan ya kuma miƙewa yana ruggume da ita ya koma kan gado da ita yana kontar da ita,
shima ya raɓa gefen ta ya konta a hankali y............






*By*
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 3⃣8⃣

*Na*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇




*Wai-wai na kusa nayi tuya na manta da albasa Amman na tuno takwarancy tawa AISHA ALIYU TSAMIYA sa ranki a inuwa bazanyi littafi har na gama ban baki kyautar shafiba Insha Allah haka bazata tab'a faruwa ba dan ke tawace dan haka wannan shafi gaba d'ayanshi naki ne kiyi yadda kikaga dama dashi ana tare🤝☺😉😍😘*





*A* hankali ya kontar da ita sannan yasa mata pillows a bayanta ta yadda ta d'an taso sama kad'an kamar ya jingina nata,
A/C ya kuma k'arawa gudu sannan ya zare jallabiyar jikin shi ya ajiye gefe,
sai kuma ya haura kan gadon cikin wani irin salo ya rab'a jikin ta
kanshi ya manna a tsakiyar k'irjin ta sannan yasa hannun shi duka biyu ya zagayo k'ugunta ido ya lumshe tare da sauk'e ajiyan zuciya yana mai fidda numfashi a hankali idon a lumshe ya rink'a murza fuskarshi a kan dukiyar fulaninta yana mai k'ara k'wak'wumota joking shi tamkar zai had'iyeta,
janyota jikinshi ya k'arayi ya fara yi mata wani irin salon shafa da kissing ɗinta tako ina sai shushunar wuyanta yakeyi yana murza kanshi a k'irjinta zuwa k'asan wuyanta,
tuni yafara rikitata gaba d'aya ya kaita tsakiyar duniyar masoya a hankali ta fara mik'a tana d'an lumshe ido sai kuma ta cusa yatsunta cikin tarin sumar kanshi tana d'an murza yatsunta tare da d'an kame jikin ta,
ganin zai zautar da ita tasa hannun ta manna k'irjinta tana d'an tureshi,
yayin da shiko take hakan kamar wani salon romancing take mai gaba d'aya yagama susucewa duk ya daburce ya d'imauce ya zama tamkar zaucecce,
cikin rawan jiki yasa hannu yana zame rigar jikinta kanshi kuwa ya kife a k'irjin ta,
nanfa jikin shi yafara rawa yana shafa k'irjinta a hankali cikin wani irin bak'on yanayi da bai taɓa jiba sai jan numfashi yake da k'arfi yana murzata a jikin shi yana mai sauk'e ajiyan zuciya.

Ita Kuwa Ummul ganin yana neman wuce gona da irin yasa ta fara zubda k'ollah cikin rauni a zahiri take ganin kamar amanar Hamman ta take son ci a ranta take ganin sam auren Usman bai dace da itaba yau gashi ya Usman yana shirin kasan cewa a matsayi da Hamma Umar ya kasance a gareta a shekaru 3 da suka wuce cikin sanyi,
tasaka hannun ta duka biyu a k'irjin shi tana ɗan tureshi da janye jikin ta daga rilkon da yamata,
shi kuwa sai k'ara mak'aleta yake yana k'ara manna kanshi a k'irjin ta yana isar da sak'onnin shi masu wuyar fad'uwa,
Jiki na rawa tak'ara tureshi da k'arfi tana jujjuya kai ido cike da k'ollah,
Da kyer tasamu ta zame jikinta daga gareshi jiki a mace ta mirgina tayi juyi ta d'an zame k'asan gadon ta dunk'ule jikin ta a guri ɗaya ta manna kanta a jikin gadon ta d'an kifa guiwowinta k'asa gaba d'aya jikinta sai rawa yake tana faman zubda k'ollah tana k'ok'arin jawo blanket d'in ta rufe jikin ta,
Jiki na tsunami shima ya mirgino k'asan kusa da ita jiki babu kwari idanuwan shi duk sun canja sunyi jazir sun cicciko da k'ollah sai shek'i sukeyi alamar a ko wanne lokacin zai iya zubda k'ollah,
k'irjin shi na bugawa da sauri da sauri duk tsikar jikin shi ta mimmik'e,
Idanun shi da suke cike da k'ollah ya zuba mata naɗan wani lokaci sannan cikin disashiwar murya mai cike da rauni murya na rawa yace,
"Ummu na kiyi hak'uri ki taimaka min,
wallahi ina wahala sosai a duk lokacin da kika gujeni ina cikin wani yanayi please ki Jik'aina,
Wallahi a yanda nake ji yanzu zan cutu in baki matso gareni ba,
kinsani namiki uzuri a gida saboda a tunanin kunyace tasa kike guduna kinaga a gida muke,
Sannan haka kika yimin a yola wanda nayi zaton in munyi nesa da gida zaki tausaya min,
amman har muka dawo kin kasa amsata a matsayi mijinki duk da hakan nayi miki uzuri nace duk kunya ce,
to yanzu munyi nesa da duk wanda zakiji kunyar gaba d'ayama bama k'asar tamu amman kuma kalli yadda kike min,
haba Ummu na kiyi hak'uri kibani hak'k'ina mana please wallahi a takure nake".
Ya k'arashe maganar cikin sigar lallashi,
Itako Ummu wacce tunda ya sauk'o k'asa ta rumtse idonta da k'arfi ganin yadda ya matsota ba komai a jikin shi sai blanket da ya jawo ya rufesu,
Kuma duk maganar da yake hannun shi na kan k'irjinta,
jin yayi shirune ya k'ara matsota ya manna bakinshi a k'irjinta,
yasa ta bud'e ido cikin rauni da muryar kuka tace,
"Hamma na,
ya Usman bazan iya amincewa da kowanne namiji a duniya bayan inba shiba,
Ya Usman inajin kunyar hakan,
bazan ci amanar shiba". Ta k'arashe maganar cikin kuka mai tsanani.

A hankali yasa hannun shi ya rungumo ta tsam a k'irjinshi,
cikin tsananin mutuwar jiki yafara shafa bayanta zuwa wuyanta yana d'an murza k'irjinta a nashi k'irjin yana d'an hura mata iska a kunne tare da d'an bubbuga bayan ta har saida yaji ta sassauta kukan,
sannan ya ɗagota ya maidata kan gado ya kwantar da ita yaja mata bargo sannan ya manna mata kiss a goshinta,
Sannan yajuya jiki babu k'arfi ya shine bathroom ruwa ya sakarwa kanshi yana yi yana zubda k'ollah a haka yayi rink'a tsayuwa cikin ruwan har saida yaji hankalin shi ya dawo jikin shi sannan ya fito ya shiga kitchen ya had'a musu breakfast.

Bacci take sosai har yagama abinda zaiyi ya shirya tsab,
Sannan yaje yasake manna mata kiss a goshi ya gyara mata lulluɓin bargon yafita wurin aikin da yazo yin.

Sai wajen 12:00 pm agogon kuala lampur ta tashi daga baccin,
wanka tayi sannan tayi break,
tana gamawa ta shiga kitching tadafa musu abinci,
Sannan tadawo palour ta kunna Tv ta kwanta kan 3 seater tabuɗe data wayarta tafara chat da yan uwa,
har k'arfe 3:00 pm tana ta chat salla ke tada ita duk da kuwa da Aliyu ne kad'ai take chart d'in sai kuma Aunty Aisha Garkuwa,
Dawowar Usman yasa tayi musu sallama ta tashi ta nufi inda yake tsaye ya buɗe mata hannuyen shi,
a kunyace taje ta d'an faɗa jikin shi tana mai rumtse ido,
rungumeta yayi da k'auna yana kissin wuyanta tare da tallabo kanta yana d'an lasan lips enta,
A haka suka ɗauki lokaci mai d'an tsawo sannan tazame jikinta ta kama hannun shi suka shige bedroom,
Wanka yayi sannan sukaci abinci suka cigaba da hirarsu har lokacin sallah magrib, basu tashi daga sallayar ba har saida sukayi sallah isha'i sukayi addu'o'in su sannan cikin lumshe ido Ummul ta d'an kalleshi murya can k'asa tace,
"Ya Usman zanyi bacci yanzu dan Allah ka tasheni anjima inason ganin posting ɗin Aunty Garkuwa yau har yanzu batayi posting ba wata k'il sai anjima zatayi".

Ido ya zuba mata cikin tsananin begin ta sannan yace,
"Yanzu duk baccin da kikayi ɗazu bai ishekiba?
to zonan muyi wata magana kafin kiyi baccin".
Matsowa tayi tashige jikin shi tana mak'ale wuyan shi,
Shima hannnshi yasa ya daɗa rungumeta yana mai cusa hannun shi cikin rigar ta kamar mai raɗa yace,
"Ummu na dan Allah ki saurareni kuma inaso ki fahimceni
duk da k'issar nan ta kasance ne a tsakanin yan uwa mata amman zata wakilci yan uwa maza,
Annabi mohammad (S A W) ya aurawa sahabin shi Usman bin affan y'arshi sayyada Ruqayyat (r a) tayi wafati sannan yasake ɗaukar k'anwarta Sayyada Ummulkhursum ya aura mashi haka itama Allah ya karb'i rayuwarta sannan a hakan Annabin mu abun koyinmu yace,
"Da inada wata y'ar dana k'ara aura mishi".
Kinga idan muka duba wannan babu wani haramci ko abun kunya cikin aurena dake madadi baya da wani aibu a musulunce".
Sake tura fuskarta tayi a kirjin shi,
Da k'arfi yayi wani irin gwauron numfa
DOWNLOAD
DOWNLOAD

4 Comments On RUBUTACCEN ALAMARI
avatar
shukra-sulaiman

8 months ago

Reply

Thanks

avatar
shuraihu

8 months ago

Reply

Replying to shukra-sulaiman

Tnx too

avatar
fatima-idris

8 months ago

Reply

Nice novel

avatar
taskar

8 months ago

Reply

Replying to fatima-idris

Aha tnx

Please Login or Register in order to submit comment