Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ciki kuma yanzu zanje in gayawa Abba da Ammi jirani yanzu zanje in dawo sai mu kirata".
Murmushi ta k'arayi tace,
"nagode ya Usman". Shiko mik'ewa yayi ya nufu cikin gida Kai tsaye part d'in Abba ya wuce inda ya sameshi shida Daddy da Ammi da Nenne suna maganar batun auren nasu,
A nan ya zauna yayi musu bayanin yadda sukayi da Ummul batun rubuta labarin ta,
murmushi Abba yayi shida Daddy da Ammi sukace sun yarda Allah ya sanya al'khairi rubutun Allah Kuwa yayiwa marubuciyar albarka komai za'ayi da yardarsu sun yarda a rubuta labarin ko suna yensu a saka kuma kar a canza labarin,
sosai Usman yaji dad'i cikin happy ya juya ya fita kai tsaye part ensu ya koma,
yana shiga ya zauna gefen Ummul nashi
sannan ya
d'anyi baya ya jingina da kujera yace,
"amma fa gaskiya Ummul auren mu shine cikar burina da kuma k'arshen littafin Ummu na ina sonki ina sonki kusa dani ina da buk'atarki kusa dani".
kauda kai tayi cikin sanyi tace,
"Toh yanzu mu kira Aunty Aysha Garkuwa kayi mata magana da kanka".
"To" yace sannan ya Karb'i woyartata yasa Hf cikin sanyi ta fara magana a hankali tace,
"Anuty Aysha kiyi hak'uri na matsa miki Ummul ce wanda kukayi magana jiya dama ya Usman ne yake son kuyi maga".
cikin tausayawa GARKUWAR FULANI ta fara magana dan yahaya hayat ya tura mata labarin ta karanta cikin tausayawa rayuwarsu tace,
"Ayyah Ummu sannu Allah ya jik'an Hamma Umar Allah yasa ya huta rabbi ya karb'i shahadarsa Allah yasa Al'jannace makomarsa muko in tamu tazo Allah yasa mu cika da imani da kalmar shahada,
Allah ya bawa Ya Usman lafiya da nisan kwana Allah ya raya Farouq k'arami".
"Amin Amin Ameeeeeeeeeeeeeeeen ya rabbil izzati".
suka amsa a tare ita kuwa garkuwa tuni take kuka cur-cur tunda ta karanta labarin nasu ta kasa tsaida hawayen ta,
cikin sanyi ya Usman yace,
"Mun gode da Addu'arki ga d'an uwanmu Aysha Ummul tace min kince baza ki amshi aikin labarin namu ba gashi yanzu tana kuka kuma mun gayawa iyayen mu sun yarda Insha Allah anjima zan had'aki da Ammin mu ta gaya miki da kanta".
cikin sanyi da rauni tace,
"Ba komai ya Usman na yarda in dai naji daga bakin Ammi na yarda zan rubuta labarinku ina gama *Bandirawo* kafin Sallan layyah bayan sallah zan fara labarin ku,
zan ajiye duk labaraina sai na gama rubuta labarin ku dan tabbas labarin Ummul akwai izinah a ciki darasi mai girma a ciki".
Godiya suka rink'ayi ita kuwa Ummul sai kuka takeyi,
bayan sun katse kiran ne Usman yasa hannu a hankali cikin wani irin salo ya j.........




*SADAUKARWA GA DR UMAR IBRAHIM UMAR SHUWA (HAMMA UMAR)*





*By*
*GARKUWAR FULANI*
[07:03, 12/9/2017] 😄😄💲ⓂℹL£®😀😀: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 3⃣5⃣

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*Kin kid'i kankad'a, damuni na damoni, gid'd'omo fina laramo, gaid'omo fina sukoyo, ladde Allah yamad'u, ki b'ib'b'e samme te, ki d'oidi yalete, b'end'uki yamete, yoriki tenets,*





*Ina mik'o sak'on ta aziyata ga yan uwana Fulani ma zauna Numan dake jihar Adamawa Yola Allah ya isan mana ya saka mana cikin gagga bisa kisan gillan da k'abilar B'acamawa sukeyi mana, Allah ya jik'an wadanda suka kashe Allah ya karb'i shahadarsu Allah ya saka mana yadda suke tozarta mu Fulani ma zauna cikin rigogi suma Allah ya tozarta su Allah ya isa Allah ya isa Allah ya isar mana kuma shi zai saka mana zalumin ci da ake mana, ina kuma kira ga ugiyar TABITAL FULAKU ta jihar Adamawa tare da Ugiyar MI YETTI ALLAH da su hamzarta shiga cikin wannan Al'amari domin kawo k'arshen wannan zalumcin da akayi mana shekaran jiya da jiya a kwana biyu ace an kashe mutun kusan arba'in wannan zalumcin dame yayi kama😭😭😭😭*







*A* hankali ya janwo ta jikin shi ya d'ora kanta a kan kijinshi sannan yasa hannun shi ya ruggume ta sai wani irin numfashi yake fitarwa a hankali yana lumshe ido da sauk'e ajiyan zuciya yana mai jin k'aunar ta da wani irin sonta,
itako sai lafe tayi a jikin shi tana kuka mai cin zuciya dan tuno Hamma Umar d'inta da tayi,
yayinda shikuma yakejin kukan ta har cikin ranshi gaba d'aya ta hargitsa shi yana jin tausayi kanshi da kanta cikin lallashi yace, "wayyo Allah ba Ummu na dan Allah ki rufamin asiri kidena kukan nan zuciya ta tana harbawa da k'arfi".
Sake cusa fuskar shi yayi a wuyanta yasa bakin shi a saitin kunnen ta cikin sigar rarrashi da rad'a ya hura mata iska mai sanyi cikin kunnen nata murya a narke yace,
"Ki taimakawa zuciyar data dad'e tana muradin samunki, ki tausayawa ran daya dad'e yana kwad'ayin ganin farin cikinki ki jik'aina kidena zubda hawayen ki,
kiyi min son da ako yaushe kika tuna Hamma na kiyi mishi Addu'a,
Wallahi Allah Ummul kece burin raina,
kece zab'ina,
Kece farin cikin ruhina kuma muradina,
zanso kiban dama in gwada miki yadda nake azab tuwa da cuter k'aunar ki da rad'ad'in rashin d'an uwana kece kad'an zaki samamin farin ciki,
ina kaunar ki k'auna mai tarin yawa,
wallahi Ummul idona baya gani sai ko wacce mace da sigar aure sai ke,
kunnuwa na basa jin zak'in muryar ko wacce mace sai muryarki,
Noor qalbee wallahi idan nace ina ganin sauran mata kamar maza kar kiyi mamaki wallahi bazan iya rayuwa babu keba".
ya k'arishe maganar tare da sa hannun shi ya shafo wuyanta numfashin shi na fita da kyar muryar shi na rawa yace,
"Ummuna kaunar ki zatamin illah in dai ban same kiba,
dake nake kwana dake nake tashi numfashi na da bugun zuciyata duka nakine,
bazan iya jure rashin kiba, ki taimakeni ki yarda da aurena wallahi hakanne kawai mafita guna kinji ka'nwata abar k'aunata".
Zuwa lokacin Ummul tafa ra tsorata da Usman gaba d'aya yanason b'atar mata da hankali,
sai wani irin fesa numfashi yake yana lumshe ido da laso lips enshi kamar wanda yake cikin maye,
ganin yadda yake ta k'ara matsowa jikin ta yasa ta d'an juya kai ta fuskarta ta fuskanci tashi hakan yasa hancinsu ya had'u guri guda sannan ta sauke ajiyar zuciya da hakan yasa iska fitowa daga bakinta kamar da gangan tayi,
aiko Usman najin iskar kasala ta sauka mai jikin shi ya mutu hakan yasa shi sassauta rik'on dayayi mata ya koma jikin kujerar ya jingina yana lumshe ido yana bud'esu da kyer gaba d'aya ya sake sai wani irin shu'umin kallo yake mata,
Ita kuwa hakan yasa tasami dama ta fusge jikinta daga rikon dayayi mata da k'arfi cikin sassarfa tafice daga parlor tana kuka cikin sanyin sauti.

Kai tsaye d'akin su ta nufa tana shiga tafad'a kan gado tacigaba da rairo kukan ta,
dakyar Ammi dake gefenta ta rarrasheta cikin kukan da tuno Hamman ta tayi lamo akan gadon kamar mai bacci,
ganin tayi shirune Ammin ta fita ta barta.

A parlour kuwa dakyar shima ya yunk'ura a daddafe yashige bedroom din ya fad'a kan gado hannun shi rik'e da marar shi yayita mirginawa yana juyi hawaye na bin fuskarshi pillow ya jawo Ya rungume da k'arfi yanajin wani irin yanayi na shigar shi,
yad'au lokaci a haka sannan ya tashi dak'yar yafad'a bathroom yasakarwa kanshi ruwa sannan yafito ya shirya tsaf ya d'au mukullin mota yayi b'angaren Nanne .


Kwance yasami Ummul kan gado kamar me bacci Ammi kuma da shigowarta d'akin kenan tana ajiye kayan data shigo dasu ya rusuna k'asa yasake gaida ta amsa tayi sannan tasami bakin gadon ta zauna saida yayi kamar zai tashi sai kuma ya zauna yace,
"Yauwa Ammi akan maganar rubuta littafin da Ummul takeso d'azu munkira ita marubuciyar munyi magana shine nace mata zan had'aku da ita tasake ji daga bakin ki saboda tad'au abin da muhimmanci duk da dai daga yanayin yanda mukai magana da ita baza a samu wata matsalaba kuma bisa ga dukkan alamu Ummul ta k'ara samun Aunty dan bakiga yadda tayita rarrashinta d'azuba".
Nan da nan Ammi taji k'aunar marubuciyar na ratsata kasancewar a yanzu bata da burin daya wuce ganin samun kwanciyar hankalin Ummul d'in ta da murna tace,
" To madallah kirata muyi magana kaga sai nasake mata godiya". D'an d'agowa yayi ya lek'o kan gadon yace, "Khairi mik'omin wayar ki".
Dana sauri Ammin tace, "Haba Usman kace in mik'omaka mana saika tayarmin da ita daga baccin tun d'azufa kuka take yi da kyer na samu tayi shiru".
A hankali ta d'an d'ago kanta wadda daman tana jin duk zancen nasu ta d'auko wayar tayi ta mik'o mai,
Kanshi a sunkuye yasa hannun zai karb'i woyar cikin hikima ya had'e wayar da hannun ta ya rik'e yana murza yatsunshi biyu kan yatsunta cikin salon lallashi da so,
da sauri ta zame hannun ta tana kallon Ammi,
Itako Ammo batama ga abinda suka yiba, Dialling number yayi bata jima tana ringing ba ta d'auka sannan ya mik'awa Ammi ta karb'a tasa a kunnen ta sannan tace,
"Assalamu alaikum". Cikin muryarta mai sanyi da saisaita zuciya ta amsa sallamar sannan tace,
"Wa alaikissalam ina kwana".
gyara zama Ammin tayi tana fara a tace,
"lafiya lau d'iyar albarka, ya yaranki ? da mai gidan ? ya kuma gurin manya?".
Cikin ladabi ta amsa da, "lafya lau Alhamdulillah".
cikin girma Ammi taci gaba da cewa,
"Y'an nan Ammin Ummul ce".
jin hakan Garkuwar cikin tausayawa tace, "Ayyah Ammi kece ya hakurin mu na rashin Hamma Umar? Allah ya jik'an shi yamai rahama yasa can yafi masa nan ku kuma Allah ya k'ara maku juriya da hak'urin rashin shi".
Cikin sanyi Ammi ta amsa mata da,
"Ameen nagode Allah ya bada lada".
sannan tayi ajiyan zuciya tare da ci gaba da cewa,
"Usman ya sanar dani yadda duk kuka yi akan rubutun littafin kuma yace kinaso ki k'ara tabbatar da sahihancin labarin shiyasa nasa baki kuma nake fatan zaki karb'i abun dan taimakawa".
Shiru tayi dan sauraren amsarta inda cikin girmamawa tace,
"Insha Allah Ammi babu matsala zanyi iya k'ok'arina inga munbada sak'on da labarin yake d'auke dashi, duk da ina da wasu ayyukan banda wanda nakeyi a yanzu amma da yardar Allah zan aje komai idan na k'arasa wanda nake aiki akai yanzu Insha Allah shi zan fara."
Cikin jin dad'i tace,
"To y'ar nan Allah yamiki albarka ya jib'anci dukkan lamuranki yakuma biyaki da gidan aljannah".
Daga ita har Usman da Ummul da,
" Amin Amin Ameeeeeeeeeeeeeeeen ya rabbil izzati ".
suka amsa cikin sakin fuska Ammi tasake cewa,
"To sai hakuri da k'anwar taki gatanan kuka koyaushe takasa daina shi sai ki cigaba da d'orata kan hanya dan tabbas had'uwar ta dake ya kawo canji a yanayin ta da".
"Insha Allahu" Garkuwa tace sannan Ammi taciga da cewa,
"Yauwa Aisha nagode sosai Allah ya bada sa a Allah yabaki ikon aikin alkhairin da kikayi niyya Allah ya miki al'barka".
"Ameeen". da haka sukayi sallama Ammi ta mik'awa Ummul wayar ta mik'e tana kallon Usman cikin k'aunar d'an nata tace,
"Fita zakayi ko?".
yana inda yake zaune yace,
"eh me kike buk'ata? in kawo miki?".
tana tafiya tace, "bakomai Allah ya kiyaye ka ya dawo dakai lafiya".
Yana sosa kai kamar mara gaskiya yace,
"Amin".
Tashi yayi yakoma bakin gadon ya zauna ya k'ura mata mayan idauwan shi sannan cikin rad'a yace,
"Wai ina yarona ne?". Kanta a k'asa tana wasa da yatsunta tace, "Yabi Daddy tunda yazo gaida Hajjajo".
K'ara sunkuyowa kanta yayi cikin lumshe ido yace,
"To amma dai bawata matsala ko?".
Murya na rawa tace, "bakomai".
hannu shi yasa ya ruk'o nata yana d'an murza yatsunta a hankali yace, "To aimin rakiya mana irinta masoya".
nan da nan ta kwab'e fuska ta tayi rau-rau da ido alamar zatayi mishi kuka,
Ganin haka ya sake daburcewa jiki na tsuma mik'ewa yayi sannan ya sunkuyo dai-dai kunnen ta ya tsurawa k'irjin ta ido murya a cushe yace,
"Kiyi baccin ki mai dad'i tare da mafarki na ina lasar wad'an nan lips en na ki masu taushi Ummu na ina begen randa zaki zamo mallaki na".
Fusge hannun ta tayi ta rufe idonta cikin kinda da mamakin ya Usman d'in,
shiko ko ajikinshi dan daman haka yake baya b'oye abinda yakeji,
juyawa yayi har yaje bakin k'ofa yace,
"please ki ajiye wayarki a kusa".
Sannan yasa yatsunshi biyu a kan lips d'in shi yai kissing d'insu ya hura mata da bakin shi sannan ya fice.

Kai tsaye yawuce FCE(T) inda yake koyar da masu koyan computer duk juma a da asabar.

Office d'in Mallam Bashir Bala abokin aikin shi yashige kai tsaye kasan cewar nan yake zama in yaje saboda yakan jene sabida nemanshi da sukai yarink'a taimakawa,
bayan sun gaisa Malam Bashir yace,
"To bari inje kafin ka huta".
Yana fita shiko ya d'aga kafafuwan shi ya d'ora akan kujerar dake kallon wadda yake zaune ya ciro waya yakira number Ummul ya saka a kunne,
saida ta kusan katsewa sannan ta amsa murya can k'asa tai mashi sallama,
"wa alaikissalam Hubby, ykk".
Jin abin tai wani iri sabida ganinta yanzun nan yafita amma yana tambayar ya take,
shiya dawo da ita daga tunanin da take da cewa,
"Allah yasa ba bacci kika fara na tasheki ba, kiyi hak'uri wallahi soyayyar ki ce take d'ibana nake kasa jurewa shiyasa zakiga ina irin wannan abu buwan".
baki ta tura tare da cewa
"hmmm". Kawai shikuma yaci gaba,
"Gaskiya Baby ki dena min rowar muryarki dan Allah ki karb'eni kiban dama nashigo rayuwarki na cika zuciyar ki da farin ciki pls".
Yasan da wuya tabashi amsa dan haka yaci gaba da cewa,
"Kice wani abu dan Allah, indai kinaso nayi aikin danazo yi".
shiru dayajin ne yasa d'an sauke k'afar shi k'asa yazura takalmin shi ya mik'e yana mak'ale da wayar yafara tafiya yana cewa,
"Ganinan dawowa tunda bazaki min magana ba nima babu abinda zan iya yi gwara indawo inta zamana a gida". Dai-dai nan yabud'e murfi motar shi yashiga ya rufe kofar,
k'arar rufe motar yasa ta tabbatar dagaske zai dawo da sauri cikin sanyin murya tace,
"Ya Usman dan Allah karka dawo". Komawa yayi ya jingina da jikin kujerar motar yayi murmushin jin dad'i yace,
"kin barni na fito bakimin addu'a ba kuma yanzu nakira kink'i kimin magana gashi duk a matsa nake wane irin aiki kikeso nayi a hakan?".
Katseshi tai da,
"Kayi hakuri Allah yabada sa'a ya kiyaye ka".
Wani irin sanyi yaji a zuciyar shi yasa hannu yabud'e motar ya fita ya maida murfin ya rufe sannan yace,
"Amin, to ko kefa, yanzu ne zanyi aiki ki kulamin da kanki saina fito".
"Adawo lfy".
tace sannan ta katse kiran tabi wayar da kallo tana jinjina hali irin na ya Usman shi sam ya fiye zalama daga dukkan alamu shi ba irin Hammanta bane mai hak'uri.


Shak'uwa mai k'arfice take shiga tsakanin Ummul da sabuwar Auntyn ta Aysha Aliyu Garkuwa, wanda sukan yi waya sannan suna dadewa suna chat, hakan na debewa Ummul kewa kuma tasami nutsuwa saboda irin rarrashi da shawarwari datake samu daga gareta saidai kusan koda yaushe dukkansu da kuka hirar tasu take k'arewa musamman idan GARKUWAR tayi mata wata tambaya game da rayuwarta ta baya,
ranar wata asabar Ummul ke fad'awa Auntyn nata zasu tafi Saudi dan gudanar da aikin Hajji ita da Ammi da Ya Sadiq kuma zasu tafine ta international air dan haka Dubai zasu wuce sannan daga can su dawo k'asa mai tsarki. Addu'a tayi mata sannan suka rabu.

Kamar yau aikin hajji ya k'are dan haka suka d'unguma sai Dubai inda zasu kwana kafin da safe suwuto gida Nigeria,
Wannan yaba Ummul damar bud'e data ta tayi sa a Auntyn ta tana online taji dad'in ganin ta saboda hakanan taji tana buk'atar su tattauna akan abunda yake damunta,
sallama ta yimata bayan su gaisa sosai ne Ummul tafara tambaya kamar haka, " Aunty dan Allah dagaske ne yanzu idan nasake aure
DOWNLOAD
DOWNLOAD

4 Comments On RUBUTACCEN ALAMARI
avatar
shukra-sulaiman

7 months ago

Reply

Thanks

avatar
shuraihu

7 months ago

Reply

Replying to shukra-sulaiman

Tnx too

avatar
fatima-idris

7 months ago

Reply

Nice novel

avatar
taskar

7 months ago

Reply

Replying to fatima-idris

Aha tnx

Please Login or Register in order to submit comment