Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[9/29, 9:19 AM] Kawata: °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
*JALILA...*
_'yar bariki ce_
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_(Short story)_
*_by SaNaz deeyah_*


_°~°~°~dedicated to Anty Maijidda Musa°~°~°~_


«BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM»

_Dis novel is an imaginative writing(fiction)ban yarda wani ko wata ya juya min shi ta wata siga ba,musamman masu d'auka su kai website d'insu so ban yarda ba a canza ma littafina salo ba tare da iznina ba, so a kiyaye please_

_Wadda ta san zata zageni karta karanta novel d'ina😡_



*_~«Episode 1»~_*

Da gudu ta fito k'ofar d'akin ta fara kilkila amai kamar zata juye hanjin cikinta,duk abinda taci sai da yayo waje.

Nishi takeyi a hankali tare da dafe kanta,samari da 'yammata dake whot a gefe suka k'yalk'yale da dariya tare da fad'i
"Wata sabuwa inji 'yan caca" suka sake saka dariya.

'Daya daga cikinsu ta taso tare da fad'in "lallai zaman bariki iyawa ne idan ka iya takunka babu mai raina maka aji"

A dai dai lokacin jalila ta shigo cikin gidan.
"Jar uba"
Ta fad'a tare da k'arasowa inda suke.

"Me nake gani?"
"Abinda kike gani mana"

"Dakata dakata Zuby ba dake nake ba da deejah nake magana"

Deejah ta d'ago kai tare da yatsina fuska "me kike gani kuwa amai nayi,please kawo min ruwa na kuskure bakina"

"Dalla dakata malama ruwan uban me zan kawo miki,ke wace irin jaka ce deejah? haba ko akuya tana fin wata shidda kafin ta haihu ta samu wani cikin amma ke a akuyoyin ma jaka ce tunda duk bayan wata biyu sai kinyi ciki"

"Ya isheki jalila,kada ki takura min domin duk wanda kika gani a bariki shi ya kawo kanshi dan haka ke baki isa ki juyani ba yadda kike wa 'yan gidan nan isa da mulki ni bazaki min ba"

Tuni 'yan gidan suka fara hayaniya ran jalila ya b'aci sosai ta juyo ta kallesu tare da fad'in "kaaiii ya isa haka duk tsinanniya ko tsinnan daya k'ara magana sai naci ubanshi babu d'an iskan daya isa yaja da jalila,da khadija nake magana bada ku ba k'ananan karuwai matsiyata kawai"

Duk sukayi shiru ko wacce ta cigaba da abinda take wasu kuwa suka shige d'akunansu suna gunguni.

Ta juyo ta kalli deejah tace "ke kuma na juyo kanki wallahi ni ba jaka bace da zan ta yawon kaiki asibiti a zubar da ciki,kinga kamar yadda kikazo da ikram wadda ban sani ba ko itama a yawan barikin kika sameta Allah zaki sake haife wata ni ba baiwarki bace"

"Dakata jalila karki nemi ki fad'a min magana,ikram dai ke kikace zaki rik'eta a matsayin 'ya amma da tuni na yarda ta dan sanadinta aka koreni daga gidanmu mijina ya sake ni saboda yana tunanin ikram shegiya ce amma 'yar shi ce,kuma zan d'oketa in yarda ta duniya ta d'auka dan bazan iya bariki da 'ya ba"

"Amma kike kwaso ciki duk bayan wata biyu da an zubar sai ki samu wani haba sai kace akuya ke kowa kika sadu dashi sai kin d'auki ciki"

"Ai ba abin kunya bane"
"Abin kunya ne kuwa saboda kinsan bariki iyawa ne duk wanda ta kwab'ewa shi yaso"

"Masha Allah tunda iyayena basu haifeni shegiya ba kuma na san ni dai ban tab'a haifar shegiya ba saboda ko ikram 'yar halak ce na tsaneta kawai saboda ta sanadinta na shiga bariki kuma karki sake dangantani da ikram dan kece kika maidata 'ya"

Tsaki taja ta wuce Jalila ta bita da ido cike da jin haushinta.

"Ni kika gorantawa ko?wallahi sai na rama" da sauri ta juya ta fita rai a b'ace.

«««««»»»»»

Cikin dank'areriyar motarshi ta alfarma k'irar(Corrolla S) a hankali yake driving cikin nutsuwa.

Paradise Hotel naga an rubuta a saman dank'areren ginin,horn yayi aka bud'e masa gate d'in ya shiga,parking space yaje yayi parking.

Wani matashin saurayi wanda bai wuce sa'anshi ba yayi saurin zuwa ya bud'e k'ofar motar.

A hankali mamallakin motar ya fito,bak'ine wanda bak'in nashi yayi masa kyau hakan yayi katari ne da hutu.

Dogone matsakaici sanye yake da farin glass wanda zamu iya cewa medicated glass ne...
He's beautiful, awesome beauty,black beauty nd wise enough.

'Yallab'ai barka da zuwa.
Matashin saurayin wanda bai wuce shekara 23 a duniya ba yayi maganar.

Mujahid ya fito daga motar cikin tak'ama da alfarma,ya kalli saurayin tare da fad'in "Bashir are you still alive?"

Dariya yayi sosai sannan yace "ko bakayi murnar ganina bane?"

"No ba haka bane am very surprise dana ganka anan dan naji kamar ance ka mutu"

"Oh no!ba yanzu ba sai na zama kamarka"

"God!ina so ka fini ma"

"A'a idan na fika kuma ai da matsala,nafiso in zama kamar kai a kud'i,matata d'aya da 'ya'yana biyu kuma inyi aure a age d'inka 29"

"Hahahah u ar very funny my bros,in kanaso ka zama mai kud'i kamar ni sai ka nutsu kayi karatu amma bashir yanzu ka gudu kabar mamanka bakason karatu sai yawo a haka zaka zama n?your mother is always crying because of your bad characters bashir you have to change your life from bad to good"

'Bata rai yayi sannan yace "mamana ita taso na zama haka saboda tana nuna min k'iyayya"

"Karkace haka duka tana sonku please ka koma gareta bashir almost five months baka tare da ita anata nemanka"

"Eh a hotel d'innan nake aiki"
"Aikin me?"
Sosa kai yayi yace "yallab'ai"
"What?"
"Nothing"
munzo National conference amma dana gama zan d'aukeka mu koma gida ta ganka hankalinta ya kwanta".

"To"
"Kada ka gudu fa ka zauna anan zan fito nan da 2hours"
"To uncle Mujahid ina nan"

Brief case d'inshi ya d'auka ya shiga ciki.

Yana ganin ya shiga yace "tab munyi babban kamu aini na manta da kai uncle Mujahid wallahi kazo hannu kuma bazaka sake ganina ba sai dai muk'arrabaina.



_Sadeey S Adam_💅
[9/29, 9:19 AM] Kawata: °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
*JALILA...*
_'yar bariki ce_
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

_(Short Story)_
_*by SaNaz deeyah*_


_°~°~°~dedicated to Anty Maijidda Musa°~°~°~_


*_~«Episode 2»~_*

Yana zaune ya gama labarta mata komai tayi dariya tace "kasan kuwa munyi fad'a da Kabir guy d'in daka had'ani dashi"

Bashir yayi dariya sosai sannan yace "akan me?guy d'in yana kashe miki kud'i deejah gashi kuma kullum kuna tare ko hanta da jini bazasu nuna maku mannewa juna ba keda kabir"

"Shege bashir dad'ina dakai akwai tsari,amma ni yanzu na daina tsayawa da guy d'aya kasan hausawa sunce zama guri d'aya tsautsayi"

"Hahha kinbi layin jalila kenan"

Hmmmm "kasan yau ma sai da mukayi fad'a da ita?"

"Hahhahh jalila sarkin tsari meya had'aku da ita kuma?"

"Wallahi bashir ciki na sake kwasowa kasan ita jalila bata iya tayima mutum abu cikin rarrashi sai tayi ta min tsawa kamar ita ta kawoni bariki"

"Ai jalila oga ce duk gidannan tsoronta kuke saboda me?"

"Hmmm tsoronta suke dai amma banda ni,wai saboda shugabar gidannan ita ta rik'eta kuma mai gidannan saurayinta ne yarinyarshi ce idan kayi misbehave ko ka b'ata mata rai yanzu za'ayi dismissing d'inka daga gidan nan"

"Kina nufin jalila a bariki ta girma?"
"Cab wai kana maganar a bariki ta girma to inyi maka kat jalila a bariki aka haifeta bata san uwarta ba bare ubanta"

"Tab na tausaya mata"
"Saura ka fad'a mata"
"Ni asuwa na fad'a mata"

"Yawwa nawan yanzu yaushe zamuje na sameshi nifa har na k'agu na gamu a gado d'aya ni dashi"

"Hahahhh baki da sanya deejah ki bari zan kaiki har office d'in shi"

"A ina yake aiki?"
kamfanin sayar da motoci na A.S.

"A.S MOTOR'S dake Sharad'a?"
"Eh"
"Cabb da matsala"
"Tame?"
"Kasan akwai dadiron jalila dake aiki anan shine director na kamfanin"
"Meye sunanshi"
"Alhaji yakubu zaka ganshi babbane daga ganinshi magidanci ne"
"Bashi bane wannan idan ance miki yayi aure bazaki yarda ba dan bashi da wani shekaru kuma d'an caras tamkar saurayi"
"Kana nufin da matarshi?"
"Eh amma ai babu wata matsala"
"Are you sure?"
"Am very sure"
"Alright! yaushe kake tunanin zanje?"
"Ki bari sai monday amma kuma ya zakiyi da cikin jikinki?"
"Karka damu cikin zai taimakamin wajen samunshi a hannu"
"Okay kabir fa?"
"Dalla share shi tunda ga wani na samu dama mun gaji da juna kasan ni ba kamar jalila bace idan ta nacewa saurayi har sai sun fara gajiya da juna"
"Ai jalila da ban ce,ko banza ta fiki wayo da iya wankar maza"
"Hmmm ainima bak'in ciki take min cox taga na fara samu shine take danganani da ikram wallahi sai na koyawa jalila hankali"
"Ya dai kamata".

Haka suka cigaba da hira yana tsara mata yadda zata shawo kan Mujahid.


«««««»»»»»
Mujahid na fitowa ya nemi bashir ya rasa.

Ya tambayi securities d'in gurin ko sun ganshi?suka sanar masa yanzu ya fita kuma suka tabbatar masa k'arya yake babu wani bashir dake aiki a hotel d'in.

Ranshi a b'ace ya tafi gida,tun daya shiga layin gidan yake horn,kafin ya iso tuni maigadi ya bud'e masa k'aton gate d'in gidan.

Yana shiga yayi parking ya fito da sauri,maigadi yayi masa barka da zuwa ya amsa cikin sakin fuska.

Yana shiga falon 'ya'yanshi suka rugo da gudu sukayi hugging d'inshi.

Dukansu ya d'aga sama sannan ya sauke chuchu ya shafa kanshi suka k'arasa cikin falon.

Lailah ce ta fito daga kitchen,fara ce matsakaiciya,kyakkyawace ajin farko
Hannunta d'auke da robar ruwa da cup.

Da sauri ta k'araso tayima mujahid kiss a goshi tare da fad'in "u ar welcome my dear"
Ya d'anyi murmushi sannan yace "barka da gida gimbiya"
Itama murmushin ta maida mashi sannan ta janyo Fad'ima tana bata ruwan.

"Yau malamin su fad'ima bazai zo ba?"
"Zaizo ai lokaci baiyi ba"
"Oh hakane fa"

Tsayawa tayi tana karantar damuwar fuskarshi kafin tace "amma wani abu ya faru ne a meeting d'in"
"No!me kika gani?"
"Na karanto damuwa a fuskarka"
"Hmm kinsan yau na had'u da bashir?"

Sai da ta d'an tsaya cak kafin tace "Bashir d'an gidan malam habu?"
"Eh shi"
"Ka kaishi gidan nasu dai ko?"
"Ina fa ya gudu shiyasa abin yake damuna,har yau idan naje gida gaida su Abba indai na shiga gidansu wallahi sai Mama bilki tayi kuka amma bashir ko a jikinshi tana bani tausayi matarnan"

"My dear yanzu baka san inda yake ba kenan?"
"Wallahi kuwa dama anan paradise hotel inda mukayi meeting d'in na ganshi yace min anan yake aiki kuma dana fito ban ganshi ba na tambayi securities d'in gurin sunce gaskiya babu wani bashir dake aiki anan dan sunga fitarshi ma"

"Dama taya zaice anan yake aiki ka yarda mutumin da ko secondary certificate baya dashi,Allah dai ya bayyana shi yasa karya janyowa iyayenshi zagi"

"Hmmm zagi na nawa kuma sai dai kar a kuma"

"To Allah ya kyauta"
"Ameen"

Tashi tayi zata tafi ya janyota da hannu ta dawo jikinshi,ta d'an yi masa signing akan cewar su chuchu na gurin,ya mak'e kafad'a.

"My dear zan had'a maka ruwan wanka kayi wanka kaci abinci ka huta"
"Nak'i wayon"
"Am serious fa"
"Okay"

Tashi tayi tana 'yar dariya tayi bedroom.






_Sadeey S Adam_💅
[9/29, 9:20 AM] Kawata: °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
*JALILA*
_'yar bariki ce_
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

_(Short Story)_
*_by SaNaz deeyah_*


_°~°~°~dedicated to Anty Maijidda Musa°~°~°~_


_Masoyana wanda na sani da wanda ban sani ba,wannan page d'in sadaukarwa ce gareku,tabbas da bazarku nake taka rawa a fagen rubutuna,duk lokacin da raina ya b'aci kuna k'ok'arin sanyaya min shi,nagode sosai kamar yadda Allah ya had'amu daku a online Allah ya had'ani da ku a gaske ya kuma had'ani daku a aljannah nagode da nuna min so da k'auna da kukeyi ina sonku sosai Allah ya bar mu tare🙏🏻._



~_*«Episode 3»*_~

Toilet ta shiga ta had'a masa ruwan wanka ta zuba duk wasu turaruka na wanka sannan ta fito.

A gefen gado ta ganshi zaune yana jiran fitowarta,murmushi tayi tace "ruwan wankan ka is ready"

"Oyaa muje ko"
"Ina?"
"Bathroom"
Smiling tayi had'e da lumshe idonta sannan ta bud'e ta sauke k'wayar idonta akan kyakkyawar fuskarshi.
"Nayi wanka already but muje na taimaka maka"
"No no no just leave it,I"ll do it by my self"
Ta d'an b'ata rai tace
"Are you angry with me?"
Girgiza kai yayi sannan yace"No! But why do you said so?"
"naga kamar you are not in the mood"
"Yeah hakane amma ai ba kece sanadin b'acin raina ba"

Hmmm tayi ajiyar zuciya tare da komawa kan stool d'in mirror ta zauna.

Ya matso kusa da ita ya d'ora hannunshi kan kafad'unta yace "baby am sorry ba akanki nake damuwa ba ki gane hakan"

"I understand but I feet upset"
"Why"
'Dago kai tayi ta kalleshi tace "ya kamata ace koda an b'ata maka rai a waje ni in sanyaya maka amma wannan karon na kasa, mijina idan yana fushi inajin tamkar nice da laifi please my dear ka saki ranka"
"Okay na daina baby ayimin afuwa this most be the last time"

Murmushi tayi sannan tace "ya wuce"
"Okay! Come and help me please"
"Nak'i kace zakayi da kanka just go and take your bath"

Murmushi yayi ya shige toilet tare da fad'in "Allah huci ran gimbiya"

Kafin ya fito ta fito masa da kayan da zai saka.

Ita ta taimaka mashi ya shirya sannan suka nufi dining sukayi lunch.

Wasan jefa-jefe da cushions suka fara abin gwanin ban shawa'a,har zuwa k'arfe uku da rabi na yamma lokacin malamin su chuchu na islam yazo suka fita farfajiyar gidan inda yake masu karatu da koya larabci.


Chuchu shekaranshi 6 ita kuma fad'ima shekaranta 3,yarane da suka taso cikin so da k'una da kulawar iyayensu ta both side d'in.

Dan da sun dawo cikin gida k'arfe biyar da rabi Laila zata ce suyi mata bitar karatun da akayi masu idan da gyara tayi masu haka Majahid ma yana kulawa sosai wajen ilminsu na addini da boko.

Chuchu yana nursery2 ita kuma fad'ima pre nursery take.

«««««»»»»»

A buge ta shigo gidan tana tangad'i,tare da zage zagen data saba yiwa deejah da sauran 'yan gidan duk ranar da ranta ya b'aci ta bugu.

"To fa abu ba sabo ba amma akwai wuyar sha'ani" Zuby ta fad'a tana kallon sauran mata dake zaune suna ludo.

Hafsy tace "cabd'ijam lallai hausawa sunyi gaskiya da sukace raina kama kaga gayya,in ba dan haka ba wai ace waccan yarinyar ce ke ruling d'inmu sai abinda tace a gidan nan"

"Hmmm haba hafsy ai kinsan babu yadda za'ayi kura tayi gudu d'anta yayi rarrafe,karki manta jalila a bariki aka haifeta anan ta girma tayi wayo anan ta bud'e ido ta ganta kinga kuwa dole ta fimu gogewa ina nan dake wata rana ita zata zama magajiyar gidannan"

A daidai lokacin jalila ta k'araso inda suke cikin maye ta d'aga robar lemon dake hannunta ta juyeshi a tsakiyarsu.

Da sauri duk suka mik'e tsaye,
"Kan uban can,abin naki kuma yayi yawa" Zuby ta fad'a cikin b'acin rai.

Hannu jalila ta yarfa tare da fad'in "gulmata kuke kuma wallahi sai nayi maganinku d'aya bayan d'aya"

Hafsy ta marairaice tace "haba jalila kin b'ata mana ludo da lemo dubi yadda ruwa ya shiga ciki haba dan Allah"

Tana tangad'i ta k'arasa gabanta tare da shak'o wuyanta cikin maganar maye tace "ke zaki fara barin gidan nan karuwar banza kawai"

Ta saketa tana tangad'i ta juya tayi d'akinsu tana maganganu cikin maye.

Tana shiga ta zube a k'asa,deejah ta kalleta tayi tsaki.

Ikram ta k'araso inda take ta durk'usa ganin yadda kan jalila yak'i tsayawa sai layi take yasa ikram tace "mommy what's wrong with you?please meye sameki ko baki da lafiya"

A maye tace "lafiya ta k'alau amma sai nayi maganin 'yan gidan nan harke deejah"

Deejah ta tab'e baki tare da fad'in "sai dai 'yan gidan amma ni deejah nafi k'arfin ki wallahi kema kin san wutsiyar rak'umi tayi nesa da k'asa"

Ikram ta tashi cikin kuka ta kalli deejah tace "Aunty please meya sami mommyna dan Allah ki fad'a min?"

"Shaye-shaye takeyi ikram ba wani abinda ya sameta"

Kuka ta farayi sosai ta rungume jalila tana kuka.
Matsar da ita tayi gefe sannan ta mik'e tsaye tana maye ta shak'o wuyan Deejah sosai tace "k'arya kike matsiyaciya wallahi baki isa ki jada abinda na fad'a ba,me akai akayi ki deejah,hmmm wallahi k'aryar mage tace zata tunkari fad'a da muzuru"

"Sakarni jalila please"
"Bazan saki ba sai kin fad'amin yaushe kikayi bakin fad'a min duk maganar da kika ga dama,a gidan nan na ganki kina garari baki da ko d'akin kwana na kawo ki d'akina na mayar dake mutum amma kina neman watsamin k'asa a ido"

"Amma sorry jalila na yarda you are my mistress please sakarni"

Cikin kuka ikram ta k'araso gurin tace "mommy dan Allah kiyi hak'uri"

Kallon ikram tayi sannan ta kalli deejah,ta saketa ta fad'a kan gado,tana ta maganganu irin wanda 'yan maye keyi.

A haka bacci ya d'auketa.






_Sadeey S Adam_💅

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
*JALILA...*
_'yar bariki ce_
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

_(Short Story)_
_*by SaNaz deeyah*_


_°~°~°~dedicated to Anty Maijidda Musa~°~°~°_


_*~«Episode 4»~*_

Kamar daga sama takejin kiran sallah a kunnenta,a hankali ta bud'e ido ta kalli inda take.

Ikram na gefenta tana bacci bata ma ga deejah ba hakan ya tabbatar mata ba a gidan ta kwana ba.

A hankali ta tashi ta fita toilet ta shiga tayi wanka sannan ta d'oro alwallah ta fito.

Tashin Ikram tayi ta sakata tayi alwallah itama sannan ta dawo,lokacin har ta tayar da sallah,ikram ma ta d'akko hijab taje kan sallayar ta tada sallah.

Bayan sun idar ikram ta janyo al-qur'ani tace "mommy nayi tilawar na baya ki d'ora min wani?"
"Eh kiyi muji wanda mukayi jiya da asuba,suratul Noon aya ta shidda da ta bakwai"
"To mommy"

Fara karantowa tayi Jalila nayi mata gyara har ta idar sannan ta d'ora mata.

Sai da gari ya fara haske sannan suka rufe al'qur'anin.

Ikram ta kalleta jikinta a sanyaye tace "mommy wai da gaske shaye shaye kike?"

Kallonta jalila ta tsaya yi ta rasa me zatace mata,ikram yarinya ce 'yar shekara 6 a duniya amma tana mata irin wannan tambayoyin.

"Ikram ba shaye-shaye nake ba kada ki k'ara yarda ana fad'a miki wannan maganar kinji"

"Mommy nagani da kaina,kuma kawayena sunata min gorin mamana karuwa ce ni shegiyace mommy wai ina daddyna?meyasa muke zaune a gidan nan?mommy please mu bar gidan nan kuma dan Allah ki daina shaye-shaye kuma ki daina fad'a da Aunty bana son ranki yayi ta b'aci"

Wasu zafafan hawayene suka fito daga idon jalila,ta rungume ikram tana fad'in "tunaninki yafi k'arfin shekarunki ikram,bana son ki dunga yawan surutu,bana shaye-shaye har sai idan raina ya b'aci"

Hannu ikram tasa tana goge ma jalila hawaye tana fad'in "mommy baran sake ba am sorry"

Cak jalila ta tsaya tana kallonta,a zuciyarta ta furta.

_ikram ina tausayin ranar da zaki san deejah ce mahaifiyarki bani ba,deejah ta fini shed'anci,bana wasa da sallah,sannan ban tab'a kawo namiji gidan nan ba sai dai naje na same shi domin bana son tarbiyyarki ta gurb'ace kamar yadda uwata tayi min,kina da banbanci dani domin ke tsabtatacciyar 'ya ce wadda aka sameta ta hanyar aure ni kuwa ban san ubana ba haka kuma ban rayu da uwata ba,na d'auki alk'awarin zan kareki daga duk kan sharrin ma sharranta._

"Mommy lokaci tafiya school ya kusa"
"Okay bara na d'ebo miki ruwan wanka ki cire kayanki ki d'ora towel"
"Okay" ta fad'a ita kuma jalila ta fita.


Ta taho da bucket d'in cike da ruwa tana hango yadda mutane ke hayaniya a k'ofar toilet d'in ko wacce so take ta shiga tayi wanka.

Murmushi jalila tayi lokacin data k'arasa ta ajje bucket d'in.

"Jalila please karkiyi mana datse kinganni nan inajin na fiki uzuri"

"Ahhh dakata malama,ikram zata fito tayi wanka wallahi babu wacce ta isa ta hanani datsar layi saboda skul zata tafi bana son ta makara"

"Wannan ikram d'in ko uwarta bataji da ita kamar ke"

"Zuby me kika ce?"
"Ni bance komai ba"
"Uhmm kima fad'a dai"

Duk kansu ransu ya b'aci haka sukayi ta gunguni tana jinsu sai dai tayi smiling dan idan bata so hayaniya ba ko me za'ai bata tankawa.

Haka ikram tazo zata shiga wanka sai da tad'an zuba izal sannan ikram ta shiga tayi wanka tana tsaye tana jiran fitowarta.

Aikuwa tana barin gurin suka hau surutu da bak'ak'en maganganu,tayi banza kamar bata jin me suke fad'a ma.

Bayan ta gama shirya ikram ta fito kenan zataga ko mai mashin d'in dake d'aukarta yazo kawai sukaci karo da deejah a bakin k'ofa.

Kallon juna sukayi sannan deejah ta wuce ba tare da tace masu komai ba.

"Ikram meyasa kina ganin Aunty baki gaida ta ba?"

Ta d'an b'ata rai sannan tace "mommy jiya tayi ta zaginki"

"Komai tayi miki ki rik'a gaidata kinyi saboda kinga itama mamanki ce"

"A'a mommy ke kad'aice mamana"

Kallonta kawai tayi cike da tausayinta.

««««««»»»»»

Tana ta makeup a fuskarta ta shafa wannan ta fenta wannan.

Jalila kawai kallon ta take cike da mamaki,har ta gama ta janyo wasu riga da wando zata saka jalila tayi saurin cewa "deejah ban gane ba?"

Juyowa tayi ta kalleta tace "kamarya?"
"Wai dagaske wannan kayan zaki saka?"
"Eh mene?"
"Deejah abinda kike is not fair,kin ajje 'ya kamar ikram amma kina irin wannan abun haba deejah?"

"Oh my god! Jalila dan Allah ki k'yaleni inyi rayuwar danaga dama"

"Gaskiya deejah wallahi abinda kike ya fara damuna,ki duba ki gani ikram ta fara girma wallahi duk ranar da tasan kece mahaifiyarta bazata yafe miki ba"

"To sai mai idan bata yafe ba?kinga wallahi ki daina sako ikram a al'amurana raina na k'ara b'aci bani son saka ikram a tsarin rayuwata"

"Dole na saka ikram dan wannan lokacin ne ya kamata ace ta san wace mahaifiyarta ta san danginta deejah ni ki fad'amin garinku zan kai ikram da kaina bana son ta tashi a gidan karuwai ta koyi d'abi'a mara kyau"

"Aikuwa baki isa ba,ko ki yarda ta,koki rik'eta ko kuma ki barta itama ta tashi a bariki kamar ke,amma ki manta da cewa zan tab'a fad'a miki iyayenta dan gudun kar wata rana kiyi tsautsayin tunkararsu"

"Cabb aikuwa dole ikram ta san wace uwarta dan wallahi dole ki canza hali dan naga iskancin naki k'aruwa yake,ni kuma ikram ta fara karya min zuciya duk da a bariki aka haifeni na girma anan nasan bazan canza ba dan haka dole ki zauna ki bawa ikram kyakkyawar tarbiyya a matsayinki na uwa,khadija kefa babbace bai kamata kina irin wannan ba a matsayinki na wadda ta ajje ikram,shekarar ikram 6 fa ke ba yarinya bace deejah kiji tsoron Allah"

"Hahahh lallai kuwa wai yau karuwa ce ke fad'awa 'yar uwarta karuwa taji tsoron Allah hahh kin bani dariya jalila,ya kamata ki zauna kiyi wa kanki fad'a kafin

Please Login or Register in order to submit comment