Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

meye wannan halitta ya hango ba.

Bakin hayakin nan yayi ta tafiya cikin sararin samaniya yana naiman hanyar tsiratar da ransa.
Bayan yayi tafiya mai nisa cikin gajimaren sai ya rikide ya dawo mutum mai suffar jemage,wato yanada fukafukai a gadon bayansa irin ta jemagu.

Atif cike yake da mamaki dan ko da fari ya dauka shi ya razana wannan abar amma bayan yayi arba da wannan wuri nanko yasan inda yake fa ba karamin guri bane.

Mikewa yayi ya kurama wannan gini ido,tsakanin sa kuma da wannan kofa bata wuci taku ashirin ba kacal,haka ya kakkabe kurar dake jikinsa sa'annan ya daga kai ya gamawa wannan gini kallo..

"Ina dalilin tsoratan wannan halitta?ina kuma dalilin rugawar sa aguje? Bani da ansar way'anan tambayoyin."
Haka Atif ya furta cikin siririyar murya.

Bangaren direba kuma tsaye yake gefe guda inda wannan daya tsayar akan babur yake kokari wajen ganin yasa motar tasu tayi tafia,amma kuma duk da kokarin daya yake motar taki motsawa,suna kan hakan ne sai suka jiyo wata kara mai kama da Direwar *New clear* a sararin samaniya.

Dajiyo hakan kuwa suka kai ganin su sama, gani sukayi wata bakar hayaki ta wuce ta samansu,su atunanin su jirgi ce amma basu san wannan itace shatin guwar wannan bakin halitta daya biyo bayan atif bane.

Al'amarin Atif ko karasawa yayi wajen wannan kofa inda ya karanci wata kalma dake jikin wannan kofa ba tare da ya tada da hannu ba.
Karance wannan kalma keda wuya wannan guri tadau duhu sararin samaniya ta gauraya da haduri baki wuluk.

Ko'ina a wannan guri ta dau duhu ta fitar hankali haka zalika ida motar tasu ta lallace,tsawa aka soma wadda ke direwa kan manyar bishiyoyi tana kuma konasu.

Haka kasa ta soma girgiza kai kace sama zata fado,Atif kasa tsayuwa yayi da kafafunsa ta sanadiyar wannan azabebbeyar hali daya kasance ciki haka yake ta mikewa yana kuma fadiwa kasa kai kace d'an dake koyon tafiya ne.

Haka wata jar iska mai kamada hayaki ta fitowa ta wata fuji dake jikin wannan kofa,haka Atif yanaji yana kuma gani wannan iskar ta mamaye sassar jikinsa sa'annan ta jawosa cikin wannan fuji dabai wuce fadin karamin yasaba.

Da karfin tsiya wannan iskar ta zugoshi ciki,dukda nisan gudun da wannan halitta daya biyo Atif yayi saida wannan kofar ta jawosa ciki shima.


Dukda karfin da yake nunawa yana jan Kansa da niyar kubuta amma inaaaa saida ta jawosa ciki.

Yin hakan keda wuya iskar ta dauke wannan bakin hadirin ta yaye,komai ya bubbude rana ya fito ya haskake gurin.

Abin mamaki a wannan gurin kuwa shine,duk bishiyar data karye sanadiyar wannan guguwar kokuma ta kama da wuta ta sanadiyar tsawar ko girgizan kasa toh daga zaran wannan hasken rana ta ratsa kanta sai komai nata ya dawo freshOne.

*Wannan dajinko da bala'i take,gaskiya na tausaya wa Atif wallahi*

Duhune ta ko'ina acikin wannan wuri dasu Atif suka kasance ciki,a yashe yake a cikin wannan guri sa'annan ya wani santare kaikace gawa ne shi.
Ta dalilin haka muke kyautata zaton a sume yake.πŸ˜‚

Dukkannin su dake wannan gurinko a wannan yanayi suka kasance har na wasu Awanni.
Samra ce ta soma bude idanu,duhun wannan gurinne ta soma mata sannu da zuwa danko bata maa iyya ganin Tafin hannun ta ballan tana inda kafafunta suke....ganin haka yasata kokonto kota makance ne.

Haka ta mike daga kwanciyar da take,nan ta soma cewa "da wani a nan gurin ne?"
Tsoratata muryar tata tayi danko gurin na ansawa.
Haka yasa ta soma dafedafe kamar makauniya,ta daina cewa komi.

Ji tayi ta shuri wani Abu da kafa cikin sauri ta risuna tasa hannu ta dauka,sai bayan ta dauko ne tukun ta tabbarar da jakar tace ba wani abun bane na daban.

Cikin sauri tasa hannun ta Ciro wayarta,sa'annan kuma tayi sauri wajen kunna haske.

Tarar da kanta tayi a tsakiyar kasusuwan mutane,wasu suna sanye da kayan yakin su irin ta mutanen daa wasun kuma kogunan kawunansu ne kawai ta saura.

Kwarma bagidajiyar ihu tayi bayan tayi arba da hakan,wannan ihun nata ko shine silar tashin Atif daga dogon suman da yayi.

Bude idanu yayi yaga gurin babu alamar haske ko kalilan.....
Nan da nan yasa hannu cikin aljihu da niyar ciro waya....
But bayan yakai hannu cikin aljihu ya tuno aiko wayar tasa ta fadi a lokacin da yake gudun wancen halitta.....

Tsaki yayi hade da furta *Ohhhh shet* hakan ya furta yayin da yake mikewa......
Mikewar tasako keda wuya,sai yaga wata farar haske na tunkaroshi cikin salon guduwa.

Kafin ya ankara ko ganin kansa yayi a kasa ta sanadiyar garo da wannan haske da yayi......
Jiyo muryar *Samra* yayi ta buga ihu,nan ne yasan mutumne ke rike da wannan haske a hannu.

Daga kai yayi,yayinda Samra ta dago hasken fitilar tata ta haske fuskar *Atif*
Sake karma bagidajiyar ihu tayi a karo na biyu,danko bata tsammaci zata gansa a wannan gurin ba Danko a mota suka kyaleshi.

*Al'amarin sauran tawagar tasuko sun kasance suna guri guda,sa'annan haska toci hade da kiran sunan samra......

Daga cen nesa kana ina hango hasken fitulun nasu,Basu jima suna naiman nata ba sai suka tarar da ita tare kuma da Atif,sun cika da mamaki matuka danko basu san taya ya shigo wannan matsifar da suka fad'a ciki ba

Duk da Haske da suka haska a wayoyin su hakan batayi sanadiyar daukewar duhu ba,wannan duhu bata gusa ko'ina ba,hakan suka kasnce cikin tsoro..

Suna kuma tambayar kansu shin *ina suke* suna cikin wannan yanayin ko sai wayar *Mufyda* ta dauke uta....

"Muna cikin wannan yanayin mai na kashe utan toooo"
Furucin Simon kenan nan mufyda ta budi baki tace dashi.

"Taya Zan kace haske bayan kunsan nafi kowa tsorata anan guri...."
Kafin ta karashe furta hakan sai duk wayoyinsu ta dauke uta daya bayan daya.......

Samra ce nata ya dauke karshe.........nanfa duk suka soma waige waige dukda basu ganin komi......

Wani kara suka soma ji kamar ta motsin mutum nan sai Harun yace dasu....

"Dan Allah kowa ya kama inda yake,ku daina motsinnan dan kuna tsorata mu....
Atif and Samra nasan kune"

"Taya zakace mune baya....."
Haka Samra ta soma furtawa amma sai taji Atif yayi shiiiiiiiiiiiit alamar tayi shiru.

Hakan ko sukayi dikkansu suka kasance suna jiran mai zai biyo bayan shirun da sukayi......

Soma jiyo wata sauti sukayi *DIM DIM DIM* kaikace sawun samudawane.......

*COMMENT COMMENT COMMENT*
Ku kasance masu comment idan har kunason cigaba comment naku kwarin gwiwarmu,saina jiku comment more typing always.

✍🏻...........Abdul10k Naku a kullum.
πŸ’€πŸ’€πŸ’€
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
πŸ’€πŸ’€πŸ’€

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________


*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
https://www.facebo.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________


*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*πŸ’―βœ…
*EPISODE 0⃣4⃣*


Wani kara suka soma ji kamar ta motsin mutum nan sai Harun yace dasu....

"Dan Allah kowa ya kama inda yake,ku daina motsinnan dan kuna tsorata mu....
Atif and Samra nasan kune"

"Taya zakace mune bayan....."
Haka Samra ta soma furtawa amma sai taji Atif yayi shiiiiiiiiiiiit alamar tayi shiru.

Hakan ko sukayi suka kasance sunyi tsit suna jiran mai zata biyo bayan shirun da sukayi......

Soma jiyo wata sauti sukayi *DIM DIM DIM* kaikace sawun samudawane.......
⬇⬇
Wannan sautin bana komi bane illa wasu sanduna dake rarrataya a jikin bago bangaren ne,hagu da dama,suke kamawa da wuta.....domin bada haske.
Soma ci wayennan sanduna sukayi yayinda haskensu ta haskake farfajiyar gurin na y'an wasu dakiku kadan sa'annan suka sake kafewa,haka Suka sake tsintar kansu cikin wannan duhu a karo na biyu.

Sake jiyo wannan karar cen nesa na yowa ta gurin su inda suke iyya hango hasken ta daga cen nesan nanko suka yanke shawarar bin wannan haske da zarar ta karaso cewar mu'azz *wata kila hanya take son gwada musu.*

Haka ko suka laminci zancen suka kuma ankare suna jiran wannan haske ta karaso,kamar yadda suka tsara haka abin ya tafi ba sabani..... wannan haske na ratsowa inda suke suka bita a guje yayinda ta kasance tamkar fitulu dake haska musu hanya.....duk da cewar tana kunnuwa na bayanta na daukewa......

Haka suke guduwa yayinda duhun kebinsu a baya.....Basu kuma tsaya da gudunan ba har saida suka tsinci kansu a wani guri mai dan karen guhu ga kuma zafi har nunfashin mutum na yankewa ya kuma dawo....nanfa Mu'azz yayi danasanin shawarar daya bayar danko wutan nan ta dauke sa'annan basu da damar komawa inda suka fito,domin basuma gane inda suke ba....

Suna cikin wannan yanayi na kaka nakayi sai Samra ta soma cewa.....

"Zamu iyya kwana uku batare da munci ko munsha ba,mako guda batare da mun sami hutu ba amma bazamu iyya minti goma ba tare da shakar iska ba....dukkan mu mutuwa zamuyi"
Cikin muryar kuka ta furta hakan...

,Furta wannan kalma ta mutuwan da Samra tayi keda wuya sai gurin ta dau shecking [girgiza] kaikace tashin Duniya..
Ga bakin Duhu ga rashin Nunfashi ga kuma girgizar....sa'anan basu masan akanmeye suke tsaye ba.

Al'amarin Wannan halitta Mai Kama da jamage kuwa tsintar kansa yayi a wata kazamemmiyar guri......Gurin na d'oyi matuka gakuma kukan kananun kwari da suka cike gurin.
Nan da nan ya kime ganin kansa cikin duhune yasakashi bude tafin hannunsa nan sai wuta ta tashi cikin tafin hannun nasa.

Ganin hakan keda wiya yawani jujjuya tafin hanun nasa cikin salon burgewa nan wasu abubuwa suka soma fitowa tacikin tafin hannun nasa.... Suna kuma haske yayinda suka kasance cikin suffar malam bude littafi.....haka suka mamaye saman sa.
Nan da nan Guri tadau haske matuka,ganin haka yasashi komawa halittarsa ta ainihi wato wata kyakyawar y'a mai farar idanu ga kuma gashi har gadon baya...

Cikin farar kaya take wacce akayi mata ado dajan furan ni.....
Nan sai tayi kama da y'ar shekara 15...

*Cigaban labari*

Wannan guri da take kuwa takasance tamkar bolar matattune.....Danko gawarwakine birjik a gurin.....
(Hmm Harna tuno da wani sharerren littafi na marubuci king articles, *Gidan matattu* )

Gani kanta cikin wannan yanayi yasa ta saki fuska alamar takaici,jujuwa take tana ta ganin gawarwakin iri daban daban,na muggan halitu ne,na aljanu ciki harda na Bil'adama......
Mafiyaa yawa a gurin sune Bil'Adam saikuma
Jinnu,sannan wasu halittu na daban.
πŸ’€
Al'amarin su Atif kuwa sun kasance cikin wannan duhu hade da girgizan kasa sa'annan nunfashi na yankewa na wasu dakiku kafin suka soma ganin wata jar haske na fitowa ta kasa yayinda kasar ke tsage.
Wannan hasken ne tadan yaye musu duhu suka soma ganin idanun juna.

Haka sukayi ta gujema wannan tsagewar ta kasa har ta kai ga rabasu gida biyu,bayan takai ga rabasun ne wannan girgiza ta tsaya haske ta haskake koyina sa'annan kasar ta daina tsagewa,kamar daukewar ruwan sama cek haka ta tsaya.....Harun ko yace.....

"Kar kowa ya motsa,bamusan maike lullube akasan wannan guri da muke ba.....
Dan haka karmuyi saurin fadawa wata matsifar kuma"

Haka ya furta cikin salon shawara....inda yake tsaye kuwa sunkasance su Biyarne, dashi da Samra da kuma Atif sai kuma Nina da Simon...
Sauran mutane kuma suma suna guri guda mu'azz mufyda da sauran su.
Saidai kuma Forzy data kasance tsaye take ita kadai... danko kasa motsi tayi har wannan abu tayi mata zobe.....

Dukkan ninsu dakwai y'ar Rata a tsakani,wacce da wuya mutum ya iyya tsalle ya dira wajen dan uwansa....

"Gaskiya a tsorace nake"
Haka forzy ta furta inda Samra Da Atif sukayi sauri cewa da ita cikin hadin baki.

"Forzy take it easy we are coming for you"
Bayan taji hakan yasa ta soma zubar da hawaye,ganin hakan ya dugunzuma hankalin Samra da sauran mutanen guri.

Tsoransu karsu motsa wani abun ya faru dasu..
Amma duk da hakan suna mai nuna kula ga Forzy din haka suka kasance suna mai kwantar mata da hankali cen sai Ahmad yayi wup yace dasu.

"Wait shin wai How long are we going to stay like this...... kuna nufin zamu kare rayuwan mu anan gurin kenan,Ya kamata mu naimi mafita bawai mu tsaya muna jiran tamu tazo garemu ba?".
Bayan ya furta hakan ne mufydah tace dashi.....

"Ahmad mayya taushe maka kwakwalwane wai?,maiya saka baka ganewa ne?,we are in danger Bamusan meye muke tsaye a kaiba taya zamu naimi hanyar barin nan.....so kake mu kuma jefa kanmu cikin wata rikicin na daban?."

Haka mufyda ta basa ansar marne kuma da tambaya....nan suka soma sa'insa a tsakanin su har takai ga Ahmad ya fusata yace dole saiya motsa izuwa inda Forzy take tsaye.

Shugabar tawargar tasu wato *Mu'azz* shima yayi dashi karya motsa but ina Ahmad yaki sauraransa yasa kafa yayi tsalle izuwa gurinda Forzy ke tsaye....
Dirarsa gurin suka Rungume juna.....yayinda Forzy ke zubar kwalla tana kuma furta kalmar godiya ga Ahmad....
Kwatsam sai sukaga gurin nan ta soma sauka dasu,yana nitsewa dasu cikin kasa.

Haka zalika guraran nan da suka tsastsage suka soma sauka kasa....har suka nitse cen
Nanfa Ahmad yayi nadamar abinda ya aikata danko gani yayi sun daina hango kawunan sauran abokan tafiyan nasu....
Sannan hallau gurin bata daina sauka dasu kasa ba.

Ji yayi gurin ta tsaya cek.....yayinda suko tuni a rungume suke sun kuma rufe idanu suna jirar saukar su kasan gurin....
Basuyi zaton abin zai tsaya suna da Raiba amma gashi sai suka kasance suna mai nunfashi kamar sauran halittu.

Kasar su kuma wuta ne ke ambaliya.....cikin wannan wuta kuwa koda dungulellen Bakin karfe datakai girman zuma Rock ka jefa ciki tofa nan da nan zata narke....
Haka gurin tadau haske.... Al'amarin Mu'azz da sauran ko tsaye suke yayinda suka kasa ganin komi ta sanadiyar bakar hayakin dake kashe musu ido.....

Kin bude idanu sukayi har sai da suka jiyo muryar Tina da Simon na cewa....

"Gasu cen!!" Cikin kara hade da murna....
Yayin da suke kuma nuna Ahmad da Forzy.....da yatsa.
Ahmad da forzy dai sun kasance rungume suke da a tuna ninsu sun ruga da sun hallaka basu san wannan shine mafarin wahala ga mai taurinkai ba.

Da jiyo hakan kuwa suka saki jikin juna yayinda suka kai ganin su sama.....
Yan misti mitsi suke ganin su....danko akwai nisa tsakanin su.....

Inda badan hasken wutar nanba da saidai suce sun sheka.....

Tsintar kansu sukayi akan wata y'ar *Gada* wacce iyya ganin ka bazaka yiya kureta da kallo ba.....sanadiyar nisa da kuma wannan bakar hayaki data jaguda gurin.

Wannan Gada dai tayi kama da Gadar mayu dan kuwa babu madafa sa'annan wannan gada ba wata fadi bace da ita.

Idan ka leko kasan wannan gada.....ko tsoro kurun zatasa hanjin cikin ka kad'awa.....

Kasar gurin nan gaba daya ta nitse cikin wannan wuta illa gadodi ukun Nan ne suka rage....

Wato wacce take dauke da Atif da Samra sai kuma wacce take dauke da su mu'azz sannan na Forzy da Ahmad dake cen kasa.


*Al'amarin* wannan kyakkyawar y'a kuwa tafiya take cikin kasaita....
Bayan takaiga indasu Atif suka baro daga farko sai wannan haske data kunna da karfinta na tsafi ta soma daukewa daya bayan daya.

Haka ta zura idanu dan bata zaci haka ba......
Bayan duk sun kafe,sai ta sake busar iska ta kunna wacce kunnuwar wannan haske keda wiya suka sake dauke wa.

"Tirkashi.....wannan bala'i da mai tayi kama?"
Furucin ta kenan....nan ta soma tafia cikin duhun ba tare da tasan inda take sa jafafunta ba....

Wucewarta keda wuya sai wasu muggan halittu suka baiyana a gurin data tsaya.....
Yayinda suka bita da kallo hade da rugawa suka bi bayan ta.....

Bangaren Samra ko taku suke a kan wannan Gada yayin da sunayi nisa sosai......
Cen suka soma hango karshe gurin yayinda Samra taja gwauron nishi hade da cewa....

"Ga cen hanyar da zata 'bulle damu"
Haka ta furta yayin da take yimusu nuni da yatsa...

Kwatsam ba shiri saiga wasu halittu sun ciko wannan guri......
Ta haryar da suka shigone wayennan halittu ke shigowa....

Wayennan Halittu sun kasance suna kama kadangaru amma kuma girman su da suffar su na tsorone....
Danko sunkai girman jakuna ga kuma kwara awaje kai kace *Kada*

Haka suka lodu cikin wannan guri ganin haka yasa Tina ta buga dan karan ihu yayinda take nunawa sauran abokan nata ta bayansu.....

Yin hakanko yasa duk hankulan halittun ya dawo kansu......
Nanfa wayen nan halittu suka soma rige rige wajen hayewa kan wannan gada domin zuga ga Wayen nan mutane wato su Atif....

Yadda suke kokarin hayewa kan wannan gada ko kai kace sun shekara dubi ba tare da sun ci ba....

Kai kace kudan zuma haka suka taru suna nufar inda su Samra da sauran mutanen suke.....
Ganin haka yasa suka ruga a guje.......

*HmmmmπŸ™„ I pity does guys wallahi*

Hakafa suka kasance suna gudun ceton ransu.....
Wayen nan halittun kuwa sai faman hayewa kan wannan Gada....
Nan gadar ta soma tsagewa....yayinda kuma wayenan halittu still na kokarin hayewa....


Rushewa gadar ta soma ta sanadiyar nawi nasu.....
Cikin kankanin lokaci suka riske su yayinda daya yayi Wup da Harun....
Kucelcila shi wannan abin yake yayinda ya kamosa a jakar dake gadon bayansa ganin hakan yasashi cire kansa cikin jakar ya dire kasa....

Nan ya saki rugawa a dari....haka wayennan halittu suka taru kan jakar tasa bayan sun tabbatar ba nama bace suka yowa kansu but it too late already sunkai kofar nan da suke hangowa daga nesa.

Karasowar Harun suka ja kofar suka rufeta........
Hmm Masu iyya magana kance Rashin sani tafi dare duhu....
Kuma duk wanda yaki jin bari zaiji oho......

Da sunsan inda suka tsusa kansu da basuyi gaggawar kai kansu ba......
Zai fi musu idan jira sukayi wayen nan halittu su cinye su.

Amma ya suka iyya tunda kaddarar suce......
Bayan sunja kofar suka rufe na iyya ganin wani rubutu da akayi a saman kofar.
Wacce itace *Mashigar ajali*

Yayinda suka kasance cikin wannan daki kuwa tsaye suke jikin kofar sai famar haki suke nan sai suka soma ganin haske na kunnuwa cikin sauri suka waiga baya.....

Abar sukayi da wani abun dayasa suka wangale baki Tina ko ta....sumewa tayi lokaci guda.......


*Toh fa meye wannan abin?*




*THANKS FOR READING*


*COMMENT COMMENT COMMENT*
Ku kasance masu comment idan har kunason cigaba comment naku kwarin gwiwarmu,saina jiku comment more typing always.

✍🏻...........Abdul10k Naku a kullum.
πŸ’€πŸ’€πŸ’€
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
πŸ’€πŸ’€πŸ’€

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________


*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________


*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*


*FREE BOOK*πŸ’―βœ…
*EPISODE 0⃣5⃣*



Rike *Ahmad* yake da Hannun forzy,yayinda suke sheka gudu na fitar hankali.
Bayansu kuma wayannan halittu masu kama da kadangarune ke biye dasu,wayannan Halittun kuwa sunyi matukar kusanci dasu, danko acikin idan da wani yayi missing step to fa sai wanin shi Bade shi ba,danko Loma daya zasuyi dashi.

Cikin wannan Yanayin suka kasance Nayen wasu dakiku,Har saida suka kaiga Mabilla kamar yadda su Harun suma suka sami tasu mabillar.

Kofa suka hango daga cen nesa babu Bata lokaci suka dad'a himma sai da suka tsinci kansu cikin wannan daki kafin suka taka biriki,ta sanadiyar sun kai bangon karshe na wannan daki.

Abin Da yayi matukar Dagula lissafin Forzy tare da Ahmad ko shine,a guje suka shigo wannan daki yayinda tsoro ta hanasu tsayawa surufe wannan kofa bayan sun shige cikin. amma kuma sai suka tsinci kansu a wani faffadar guri kuma babu abinda ya kasance a bayansu yayinda suka kai bangon wannan daki.

Cikin mamaki suka Dubi juna yayinda zuciyoyin su ke cike da tambayoyi amma babu wanda ya furta hakan ga d'an uwansa dan kuwa ko sunyi babu mai ansawa a cikinsu.

*Al'amarin* Wannan aljana kuwa tafe take cikin duhu,yayinda take wannan tafiyar ko sai tajiyo sautin takun kafan mutum ya wuce ta bayanta cikin sauri.. Sa'anan kuma a razane ta waige baya..
Amma meye kuwa kuke Tunanin zata tarar abayan nata?

meye kuwa zata gani daya wuce empty place sai kuma shiru da gurin yakeda ga kuma dan karen duhu......

Batare datace komi ba ta jujjuya idanu zuwa kowani lungu da sako amma still babu wanda ke wannan guri.....
Ajiyar zuci tayi sa'annan ta waiga da niyar tafiya,amma kuwa koda taku guda batayi ba, ta sake jiyo wannan sauti a karo na biyu,amma kuma wannan karan akwai dan banbanci,dankuwa hade da dariya cikin siririyar murya tajiyo....muryar kaman na karamin yaro ko kuma yarinya.

Cikin sauri ta sake waigawa ta karewa wannan guri kallo ba tare data ga komi ba,hakanne ya sake tunzura ta,ta juyawa ta kuma soma tafiya cikin sauri but sai tasake jiyo hakan wanda wannan karon harji tayi karamin yaro ya ta'ba mata kayan jikin ta.


"Da wani anan gurine?"
Abinda wannan yarinya ta furta kenan,jin babu ansan data samu ne yasa tajuya.... kwarma bagidajiyar ihu tayi dan kuwa ba karamar razana tayi ba.

Abinda ya tsoratar da itan ko shine juyawar da zatayi sai wutan dace wannan guri suka kunna kansu yayi da suka bada wani sautin a yayin kunnuwar mai razana mutum wani *buUuu* yadda kasan Tukunyar gas ce ta kama da uta.


*TIRKASHI WAI ALJANI DA TSORON DUHU*

Aiko bata sake 'bata lokaci anan gurin ba,cikin sauri ta kara gaba....
Cikin wannan siririyar hanya mai kama da cikin kogon dutse take wannan tafiya....

Cikin Abida bai wuci dakiku Goma ba ta tsinci kanta gaban wani Zabgegen kofa.....
Mai matukar tsayi ga kuma duk sassar jikin kofar ta mamaya da zanen ababen ban tsoro....ga kuma yana data baje jikin kofar,da kaga kofar kasan tayi shekaru da dama ba tare da an bude ta ba.

Al'amarin su Atif ko yayinda suka kasance cikin kofan nan da akayi rubutu a samanta wato Mashigar Ajali....

Bakomai Yasa Tina suman nan ba illa tayi arba da wasu muggan abubuwa wanda a zaton ta sunfi wanda suka fito daga ciki hadari....
*(KUMAFA HAKANEπŸ€”)*.......

Ba komi bane wannan illa wasu sangararun mutane wanda aka nannadesu cikin farararen kelle,kamar wasu Ghost...
Girman dakin nan na mashigar ajali ta zarce misali sannan kuma tayi kama da ma'ajiya irin ta mutanen da.....

Wayen nan sangaranrun mutane dai sun kasance a jejjere suke layi layi kai kace taron *asambili* akayi musu,wayennan mutanen dai basa mosti sannan kuma dukkan su tsaye suke kem... Kamar Gumaka.

Iyyakar ganin ka baza iyya hango karshen layinnan nasu ba,hakan yasa suka matukar razana da farko but daga karshe cika sukayi da mamaki yayinda suka tambatar da mutanen basu mosti.

Dukkan tawagan ko sai suka shige layi guda suna mai tafiya ciki,yayinda suke cike da mamaki danko basu taba ganin irin wayennan halittun ba.....
Gasu da hannu da kuma kafafu kamar y'an'adam amma saidai kuma sunfi y'an adam girma da kuma tsawo....

A cikinsu kuma babu wanda ya zarce dan uwansa da koda misalin tsayin al'lura....kawunan su daya.
Dukda cewar basu ga fuskokin wayen nan halittu ba ta sanadiyar nadesun da akayi da kellen hakan bata sa sunji wani iri ba sakai sukayi cikin suna ta taku.

Yayinda suka kasance cikin tafiyan kuwa,bayan sun farfado da Tina daga sumar da tayi sai wayennan mutane suka koma binsu da kallo...
Ma'ana duk Layin da suka wuce na sangaranrun mutanen nan,sai kaga kawunan halittun nan na juyawa yana kuma binsu da kallo wanda wannan kollon abin tsorone matuka domin kuwa idanun su jajir kamar garwashi wuta...

Dukda kellen da suka kasance ciki hakan bata hana nuna hasken da idanun nasu keda shi ba..
Hasken ya matukar haske wannan farar kellen....πŸ§Ÿβ™‚οΈ

*bangaren Forzy Da Ahmad kuwa* cike da mamaki suke guri guda nan sai suka juyo ganin su zuwa wannan kofa da suka shigo ta ciki.....

Tarar da wayennan halittun sukayi yadda kasan Kudan zuma,amma kuma kaf cikinsu babu wanda ya iyya shigowa wannan daki....
Ganin Haka yasa Forzy tayi ajiyar zuci tace da *Ahmed*

"Meye ma'anar Haka?"

"It means that we are safe"
Haka *Ahmad* Din ya Bata ansa itako dajin haka ta naimi guri ta zauna kamar tana da tabbacin fadar *Ahmad* gaskiya ne.

"Ah Lafiya kuwa malama?"
Haka Ahmad din ya jefo mata tambaya inda ta ansa masa da....

"Ina kaga lafiya a nan gurin kuwa,Hmm Tunda mun kasa sanin inda muke bare mu iyya naimi hanyar fita"

"Karki sami Damuwa Y'ar uwa,ina tare dake duk tsanani duk wuya,ni mai kare ki ne dan haka ki kwantar da hankali daya bayan daya komi zai dawo daidai"

Bayan ya furta hakanne tayi gajeriyar murmushi hade kuma da cewa....

"Shin kana nufin Zamuyi ta zama a dakin nan kenan har sai tamu tazo garemu".....

Bata

Please Login or Register in order to submit comment