Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakan yasa har Mayan tsutsotsi ke ta shagalin su aciki.

Forzy ko datasan Abinda zata tarar a fuskar nashi dako tayi hakuri su kasance a rungumen har *illa Masha Allah*

Bayan ta cikashin ne taja kanta da baya tayi Nesa dashi ba kadan ba,nanfa ta Sami damar duba hannayen nata......
Hmm Mai zaifaru kuwa??atunanin ku

Tsutsotsin ne suka mamaye hannayen nata biyu,yadda kasan Kudan Zuma haka suka mamaye ko'ina a hannun nata....

Forzy Ihu take tafitar hankali yayinda zazzafar kwalla take zubowa a fuskar,haka zalika ta kasance Tana kokarin sharesu daga Jikin nata Amma ta gagara hakan Domin Kuma kokari sune su shiga Cikin Naman Jikin ta.....

Dago idanun ta datayi kuwa Sai tayi arba da fuskar Ahmed din Wanda yin hakan yasa ta sake buga ihu hade da sumewa.....Hmm
Munnin Fuskar Ahmed tayi tsanani ta yadda ba mutum ba ko bakin aljanine zaiyi arba da Shi saiya razana.....

Ihu hade da yunkurawa tayi ta yadda saidata Mike tsaye kafin ta take biriki,Nishi tasoma nafitar hankali Kai Kace dutsen Uhud aka daura mata...a gadon baya.
Bayannan sai ta d'ago Hannayenta ta Dubai,shasshafawa tayi daga gwiwar Hannu zuwa wuyan sa kafin nan tayi ajiyar zuciya sa'anan tayi wata magana kasar zuci cewar ta shine.

"Allah Nogode da wannan bala'i ta kasance cikin mafarki ne.....Ba'a zahiran ce ba
Yah Allah ka kareni da kariyar ka,ka kuma gafartawa Ahmed idan nashi tariga ta riskeshi" ....

Bayan Tayi wannan addu'a Sai ta Duba hagun ta da muka dama.....iyya ganin ta duhu take iyya gani.... Nanfa Sai ta sake yin wata magana a kasar zuciyar ta akaro na biyu.

"Hmm Shin Yanzu zan kasance Cikin kadaici awannan Guri Mai matukar had'ari........."
Tana kan furta hakan kuwa Sai tajiyo muryar Atif juyawar dazatayi Sai taga gasu cen suna tafia Cikin wannan duhu....

Da faruwar haka bai wuci dakiku goma ba fitulun gurin suka kama kunno kanwunan su,Nanko Su Atif suka iyya ganin ta haka sukazo a guje suka rurrugume juna,Cikin Farin ciki da Kuma murna tayi ta hamdala...

Suko suka sakata a tsakiyar su,suna me cikata da tambayoyi akan yadda Tafiyar tasu ta Kaya sa'annan ina labarin Ahmed...

Babu bata lokaci ta kwashi labarin komi ta Basu hade da tabbatar musu da cewa Ahmed ya rigada ya mutu tuntuni.....
Budar makin Atif ko Sai yace da ita *"Kamar Yadda duk Nan muka mutu Kenan"* dajiyo wannan batu na Atif Sai Forzy tayi tsit na Yan dakiku kafin tace dashi....

"Atif kana Tsorata ni fa"
Dajiyo haka kuwa samra ta juyo kanta ta baya....ma'ana fuskar ta ta koma baya keyar takuma ta Dawo gaba Sai tace da ita...

"Kamar Haka??"

Haka Forzy ta sake shiga halin tsoro Wanda ya ninka wancen data Fita daga Cikin sau dari.....

*Al'amarin Su Mu'azz kuwa* yukurin Mu'azz yayi Domin zuwa ya ceto *Nina* Amma Bayan *Atif* ya tuno da wayennan muggan abubuwa dake kokarin karasowa gurisu Kuwa sai Yasa Hannu yaja Kofar da karfin tsiya ya rufeta.....

Mu'azz ko karasawa wajen nasa keda wuya ya shako kwalar Atif hade Kuma da cewa..

"Why do you do that?? You kill her"
Furta hakanne Yayi Cikin fushi yayinda ya shako kwalar Atif....

"Nayi Hakan ne Domin na ceto rayukan mu,You get it?"
Ansar da Atif din ya basa kenan....shiko Cikin sauri ya cika kwalar nashi hade da furucin *Oh shet*

"Shin kasan Mai ka aikata kuwa Yanzu?? Answer me

Haka ya sake mayarwa da Atif Samra ko tace dashi....

"Ai Ni kokadan Banga laifin da Atif yayi ba...
Domin Dukkannin mu Sabon rayuwa ya bamu Kuma Ina kyautata zaton koshi ya kasance a wannan yanayi zai so muyi hakan Domin mu tsira daga halakar da zamu shige ciki....
Kuma Bayan Nan Ina kyautata zaton Nina itama zatayi alfahari da haka Domin ita ta bamu damar tsira daga wannan hali."

Haka saura tawagar sukace Kwarai ckin hadin baki sa'annan Ali ya daura da cewa....

"Samra kinyi gaskiya Domin koni bazan so wannan taro tamu ta salwanta ta dalili na ba...."

Tina ko tace dasu
"Gaskiya I'm so scared.....Sai nakeji Kamar bazamu Fita daga Nan gurin ba...
Domin Tun d'azu sauka kasa muke tayi"

"What are you talking about??"
Haha samra ta jefo mata tambaya itako ta Bata ansar cewa...

"Shin Wai Baku ga hakan Ba,Tun dazo Sai sauka muke akan manyan matattakalu bacin munsan kofar daki Daya muka shiga Wanda girmar sa bai wuce misali ba Amma har Yanzu sai kwancecciyar hanya muke ta gani marar iyyaka"

Mufyda ko Shesshekar kuka ta Soma inda Simon ko yace da ita *meye hakan??*
Alamar ta bashi kunya itako Sai tayi musu Nuni hade da cewa...
"Gaskiyar ki Tina kudubi cen ku gani".....

Haka Dukkannin su suka juyo ganin su izuwa wannan Guri datake nuna musu....
Gani sukayi still sabuwar hanyace marar iyaka....
Da shike wannan daki da suka shige ciki ba wani duhun kirki bane gareta,shiyasa suka iyya ganin haka...

Hanyan Kuma ta kasance mamaye take da kasusuwan Mutane....

"Oh my!! we are all going to die down here!!"
Hala mufyda ce ta furta hakan Cikin muryar kuka yayinda *Muzzaffar* yace da su....

"Wait a minute guys shin gaskiya ne zancen Tina na cewa sauka kasan Gurin mukeyi....if yes Taya zamu kubuta daga wannan bala'i Kenan??".....

Harun Yace "Who knows.....Oiii gaskiya Tuntuni mukayi Kuskure Kuma I'm pretty sure bazamu iyya Gyara wannan Kuskuren ba"

"Hold it,what do you mean??"
Haka Atif ya furta nanfa suka fara cacan baki Kamar zasuyi fada..

Samra ko Kwarma bagidajiyar ihu tayi cewar ta shine *Ya issa* tsit sukayi Danko sunyi matukar razana Domin kuwa Guri ya anshi muryar nata....

"Yakamata mu dukufa Cikin Naiman Hanyar tsira daga wannan Gurin da muka kasance cikin bawai mu tsaya rigima a tsakanin mu ba"...

"I'm with you πŸ’―%"
Cewa Ali Kenan Harun ko yace

"Maganar ki haka take, Dan ko masu iyya magana na cewa zama Guri daya Tsautsayi".....

"But am about to ce muku mu naimi Guri muya da zango Dan kuwa wallahi a gaje nake tilis...."

Cewar Mufyda inda Tina tayi sauri Bata ansa.....

"Ehye toh an Sami bakin magana harda cewa a huta....
Keda Kika cika Mana kunnuwa da Shesshekar kuka Amma Yanzu harda cewa muhuta Kamar Hutu ne ya kawomu Nan....."

"Hmm Kyale ta Tina....." Haka Samra ta furta yayinda take kallon Tina sa'annan ta juyo kan mufyda dake zaune tace da ita ..

"Kinga Yadda muke a tsayen Nan ko minti guda bazamu Kara a Nan gurin ba tunda kowa ya amince da aje a naimi mafita so idan Zaki iyya zama ki huta kibi Bayan mu anji toh wannan Kuma shawarar kine tarage Miki Amma mu a'a wallahi"....

Haka Suka Dauki zuga suka shige wannan hanya inda suka kyaleta a zaune but then ta mike Cikin sauri tace kujira ni....Haka tabi Bayan su...aguje

Bayan sun bar wannan Guri ko Lakanin wannan kofa ta baiyana wacce itace.....
*MAFARAR BALA'I*


Al'amarin Forzy kuwa Toshe kunnuwan ta tayi niyarta ya hanata jiyo dariyar da su Atif suke yimata Mai matukar Razanawa Amma hakan Bata hanatajin komi ba.....

Gangar Jikin Taki na kwance a Cinyar Aljanan Nan Yayinda Jikinta tayi matukar zafi ga Kuma birgima da takeyi....
Hakan ne ya tabbatar mini da cewa mummubar mafarki mai hadarin tsiya Forzy takeyi.....
Wacce ta gagara farkawa dukda cewa Aljanan Nan na iyya kokari ta tashe ta Amma hakan Babu abinta ta haifar....

Ganin haka yasa Aljanan tayi tunanin Mai zai hana tayi anfani da Karfin baiwar da take dashi wajen gano halinda Forzy tace ciki....

*Bad Idea*

Daura tafukan hannunta tayi a goshin Forzy hade da Lumshe idanu....Amma Bayan Haka Sai ta Soma kakkarwa kaikace sanyi takeji Tana Kuma kokarin bare hannunta a goshin Forzy but Ina saida jini ya Soma zubowa a hancinta daga bisani Taji iska Mai Karfin tsiya Yayi jifa da ita gefe guda....

Cikin Kasala ta d'ago Kai ta kalli inda Forzy ke kwance....


Nanfa Sai taga Forzy ta farka a fisace....yadda dai Ake farkawa idan akayi mummunar mafarki,Koda shike natan ba mafarki bane Danko Bayan ta farka Sai taga shatin Hannu Atif Daya matse Mata Hannu.. Amma Kuma abinda ya Bata mamaki shine Babu na wayennan tsutsa....

Nanfa Aljanan ta yunkura Cikin murna hade da ambatar sunan Forzy.....
Abinda ya matukar dagula tunanin Forzy Kenan har yasa ta Soma ja baya Tana *Karki cutar Dani,Taya kikasan Sunana??*

Aljanan ko Bayan taje gareta Sai tace.....
"Cutarwa kuma??"....

Shiru Forzy tayi ta Soma tunanin Ina taga fuskar wannan yarinya......
Aiko Bata tuno ba har sai da Aljanan ta taba ta duk da cewar tanawa Aljanan kashedi da kartayi hakan Amma sai datayi......

Nanfa Sai ta tuno yayinda wannan bakin hayaki yabiyo ta aguje,da Kuma lokacin da Tayi Ido hudu da Aljanan....a lokacin da suka fire sanan.

Nan Sai ta Soma cewa *kece wallahi kece.....kece wacce na gani!!* Tana ja da baya..... Daga karshe kuwa ta sume Dan ta razana.....da Kuma mamakin datayi.....

Kamar kiftawar idon sai Aljanan ta dire a gefen Forzy tace.....

"Oh Poor girl maiya kawoki wannan Gurin Mai wuyar sha'ani"....

Bata Gama Fadar Haka ba sai Taji sawun kafa na Guduwa a Bayan ta....
Nanfa sai ta tarwatse Kamar hayaki ta bayyana a gaban Mai guduwan....

Ganin haka yasa sake juyowa da niyar guduwa....but still ya sake shiga gaban sa.... Kamar walkiya

Bude tafin Hannu tayi Sai Wuta ya Soma ci a hannun nata.... sa'annan ta Soma cewa

"Who are you? and Why are you doing this to us"

Shiru kakeji babu ansa ganin Haka yasa ta karasa wajen maishi da niyar ganin fuskar sa amma kuwa sa Hannun da zatayi sai Taji ya Fadi kasa...

Saida ta tsunkuya kuwa ta fahimshi Suma maishi Yayi ta dalilin razana da maishi Yayi.....

Shin kokunsan Waye wannan ba kowa bane illa Nina....Wanda Tawagar ta suka kyaleta a baya.....

*_How possible_ ?? Gaskiya jikina bai dauka ba Amma muje zuwa*

Aljanan hadasu tayi Guri guda da Forzy inda ta zauna gefen su....
Nan Sai tayi magana kasar zuci cewar ta shine....

"Taya Mutum Daya na Koro izuwa wannan daki Amma Kuma sai hayayyafa suke??"

Idan muka leka bangaren su Atif kuwa zakuga Tafiya suke Cikin tsoro yayinda suke zaton a kowace lokaci mutuwa zata iyya riskar su....

Kuma Basu tsaya da hakanba har saida sukaji Samra tayi salati....
Nan Dukkannin su suka juyo hade da cewa.....

"What Again? Samra"

Cewa tayi Don't move.....Amma suka cikata da tambaya maiya sa....

Cewa tayi dasu....
"Muna saman Rijiya"

Atif ko shiru Yayi Danko tuni yaga hakan.....

Bakin wannan Rijiya ko Tayi Girman Roundabout guda na babbar jaha....
Wacce suka kasance suna tsakiyar saman wannan rujiyan......
Ask me how.....Rijiyar Rufe take da kankara ta yadda bazaka gane Rijiya bace saika hau tsakiya.....
Bayan kahau tsakiya ka kalli kasa to zakaga Rijiyane Mai matukar duhu a kasar Kuma duk wanda ya fada ciki Hmm *Bana Ce ba*

A tsastsaye suke suna ta kallon idanun juna kowa na tambaya meye nayi ne yanzu.....
Sabida motsin da sukayi akai tasa Gurin ta Soma tsagewa....

_*Kadan Daga Labarin wannan Rijiya Kuwa*_


Rijiyar ta kasance Gaba Dubu Wacce fadinta ta wuce misali.....Kasar tako manya manya macizaine masu Girman gaske ne a kasa.....
Kuma Duhun kasan wannan Rijiya takai makura ta yadda Koda Fitula ka fada ciki dashi bazakaga na gabanka ba...Balle ka fada Hannu Rabbana.


*CIGABAN LABARI*

Tsastsaye suke sun kasa tayi.....
Mufyda ko tuni ta kigicewa Tana ta rawar jiki.....Tana kuma waige waige ta hakan sai ta sake hango musu wani Bala'in na daban.....Meye wannan Kuma??

*Kunamu* Tagan su Zagaye dasu ta ko'ina ma'ana sunyi musu zobe....kuma ko wacce daya daga Cikin kunamun Girman sa takai Girman Akuya..... πŸ¦‚πŸ¦‚

*Tirkashi Duniya nada Abin Al'ajabi* Kasan rijiya gaba Dubu macizai nee marasa iyyaka da Kuma girma,sama Kuma manyan kunamu Hmmm.....


HMM KUDAI KASANCE DANI RANAR WEDNESDAY DOMIN GANIN YA TAFIYAR TASU ZATA KAYA......

KUGA RASHIN COMMENTS TAJA MUKU HUTU KO DAN HAKA A KIYAYE IDAN ANA BUKATAR LITTAFIN YA CIGABA.

πŸ’€πŸ’€πŸ’€
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
πŸ’€πŸ’€πŸ’€

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________


*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________


*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*πŸ’―βœ…
*EPISODE 0️⃣8️⃣*



Tsastsaye suke sun rasa tayi.....
Mufyda ko tuni ta kigice Tana ta rawar jiki.....hade kuma da waige waige ta hakan ne ta hango musu wani Bala'in na daban.....Meye wannan Kuma??
*Kunamu* Tagan su Zagaye dasu ta ko'ina ma'ana sunyi musu zobe....kuma ko wacce daya daga Cikin kunamun Girman ta takai Girman Akuya..... πŸ¦‚πŸ¦‚
Cikin zafin Nama suka yiyo kansu Ganin Haka Yasa Duk suka Rikice, *Atif da Mu'azz* ko suka kalli idanun juna,kamar hadin baki sukayi tsalle suka dira da kafafun su Kan Wannan shunfudeddiyar kankarar da suke.. nan da nan suka tsunduma Cikin wannan makeken Rijiya......Ta sanadiyar tsastsagewa da wannan Kankara tayi,Ihu suke Ahhhh!! Yayinda suke fadawa cikin wannan Guri,A tunanin Atif da Mu'azz ko yin hakan zaisa Kunamun su koma inda suka fito but hakan Kara musu hazaka tayi Domin Kara sauri sukayi suna Kuma shiga Rijiyar yadda kasan taron kud'an Zuma.

β–ͺ️β–ͺ️β–ͺ️β–ͺ️β–ͺ️

"Gaskiya Nayi matukar mamaki, Domin banyi Zaton zanga hakan da idanuna ba.....Gaskiya Nayi mamaki sosai da sosai"

*Reply*

"Ah kina nufin bakya Jin tsoro na??,Nifa Gaskiya Jikina bai dauka ba"...

"Hmm Maizai saka naji Tsoron ki,Aiko Babu Abin tsoro a tattare dake Noor"

Haka Forzy ke jiyo Wannan Tattaunawa Nasu Nina Yayinda ta kasance kwance take gefe duga suko zaune Guri daya wato Nina da Noor....sun Kuma kasance sun Bawa Forzyn Baya.
Haka *Forzy* ta tashi Cikin Sand'a ta Dauki jakar ta ba tare da sun sani ba ta Ruga A Guje,Nina Da Aljanan Nan Kuwa Ko iyya juyo sawun Kafrnta Basu yiba har ta bar gurin..

Cikin Sauri hade da kuma Gudu Forzy ke Tafiya yadda kasan biyo ta akayi baya,Tana Wannan Sauri hade da Nishi Yayinda Take tunkarar Kofar wannan Daki data kasance a ciki Wanda a Halin Yanzu Bata wuci Taku Talatin Bane kacel tsakanin ta da Kofar....

Tuni Takai ga wannan kofa tasa hannu da Karfin tsiya ta bude....shiga ciki tayi sa'annan ta mayar da Kofar ta Rufe.

Al'amarin Nina da wannan Aljanar ko Fira Tayi Fira suka Soma Sako Forzy Ciki inda Nina Tace Da ita..... "Kawa tace ita,Kuma Ina......"
Bata karashe maganar nata ba ta sanadiyar ta juyo da niyar nuna inda Forzy ke kwance Amma Sai ta tarar da gurin Babu kowa...
Cikin mamaki ta Furta cewar "Ina Kuma Gangar Jikin Forzyn Ta shiga"...

Aljanan ko Tayi saurin cewa da ita "what are you talking about" Amma Bayan tayi Arba da shunfudar Forzy sai Ta cika da mamaki ta Kuma kasa cewa komi....

Nina kuwa ta ce da ita......

"Anan Take Kwance fa,Amma Ina ta shige"

"Kodai maiya dauke ta ba,Ina ko zataje Bayan Tuntuni anan take kwance Kuna ma a tsorace"
Cewar Aljanan Kenan wacce Nina keyi Mata lakani da *Noor*

"Badai Dauke taba... Da Kafanta ta bar gurin nan"

"Tayaya??" Tambayar da Noor din Tayima Nina Kenan inda nina'n ta tabbatar Mata da Haka yayinda ta nuna Satin kafafunta ma'ana inda tabi yayin guduwar.....
Cikin Mamaki Noor ta sake jefo Mata tambaya....."Amma Meye dalilin ta nayin Haka??"

"Allah ne kadai yasan Wannan,Kinga karmu Bata wani lokaci mubi bayanta watakila ko zamu tadda ita a hanya."

Haka suka kwashi summarsu suka Biyo Sahun..... Forzy,Idan mun leka Cikin Rijiyar Nan Mai gaba Dubu,Tare daku iyya Duhu zamu iyya gani Yayinda Ko zaka juyo sahun kafafun Kunamun nan na shiga yadda kasan Sahun dawakai.....

Dukda cewar Cikin nada matukar Duhu sosai ta yadda ko kaje da Fitular ka zata dauke hakan Bata hanasu shiga ciki ba....Duk tsawon lokacin nan da aka dauka Su Atif Basu kaiga kasar wannan Rijiya ba....Ihun kawai kake iyyajiyowa badai gani ba....
Amma Cikin Lokaci kalilan sukaji *tsit* Nayi iyya kokarin na Domin na jiyo karar Dirar su Amma hakan Bata yiwu ba....

An Dauki Dan Lokaci Cikin wannan yanayi Kafin Damin Butterfly *malam bude littafi* suka ratso saman Rijiyar suna ta shawagi cen sai suka Zurma Cikin rijiyar....
Wannan butterfly dai sunsha banban da sauran Butterfly sabida su tamkar fitula suke yayinda suka kifta wani Guri hasken su saita haskake ko'ina gurin,Ta sanadiyar sune na iyya gano Halin da Su Atif din ke ciki Danko sun mammakale Jikin wasu igiyoyi masu kama data bishiya....
Nan suke dukkan ninsu a mammakale suke sun rirrike,Da dukkan alamu hanya wayennan Damin Butterfly sukazo Domin su nuna musu Danko wani kogo sukayi ta shiga ciki Wanda yake kasar inda suke a makalen saidai ba Nan gizo take sakar ba..Bayan Ganin Hanyar Nan da sukayi Sai Kuma suka sake Arba da dubunnen macizai, nanfa suka sake rikivewa Danko saman πŸ¦‚πŸ¦‚πŸ¦‚πŸ¦‚ kasan ko macizai........ saidai sa'ar da sukayi macizan na sheka bacci....


Haka Sukayi ta sauka Cikin Sauri,gudun kar Damin butterfly din su wuce su kyalesu agurin Haka Kuma akayi saida suka Gama sauka Dukkannin su illa Samra dake rataye a wannan igiya Taki saukowa Ihu suke Yi Mata datayi saurin ta saukowa but inaaa Taki yin haka,aikuwa Bata tashiyin ba har saida ta hada Ido da Scorpions dinnan dake zuwa,nan tayi Ihu hade da sake Igiyar......

Cepko hannunta Ali tare da Atif Sukayi suna kokarin jawota Cikin wannan hanya ko nace cikin wannan Yar kogon da wayennan butterfly ke shiga....nanfa garin jawota ta Dalewa Sai ta ballo katotuwar dutse ta sauka a Rijiyar....Dimm!! Haka Ta bada sauti.... Suko sukayi shiru.

Shiru gurin Yayi Nay'an wasu dakiku... Kawai Sai sukayi Arba Da wata katotuwar macijiya.....Wanda Girman ta,kaurin ta da Kuma tsayinta takai Bishiyar dafino....ta tashi Daga kasar Rijiyar ta Kuma Kura musu Ido Tana ta wani Huci.... Mufyda ko kasa rikewa tayi Ta buga Ihu....

Al'amarin Forzy Bayan ta shige kofar kuwa,tadda wannan daki tayi yadda kasan *Moscow* πŸ”οΈπŸ”οΈ domin kuwa komai na wannan Daki A daskare yake....Tuni Ta Soma 'bari Tana Kuna jujjuya idanu.....

Tuni Kwakwalwar ta ya Soma Raya Mata *Forzy ki koma inda Kika fito Domin gara cen danan* ... Yayinda Kuma zuciyar ta ke Raya Mata *Karki kuskura kiyi hakan Domin Kuwa wancen Bakar Aljanar cinye ki zatayi*

Haka tayi ta Tafiya Cikin wannan hali Daga karshe sai Tace "Kai inaa I must go back"
Haka ta Dawo da baya Domin kuwa ta gwammace Gara ta koma ga wancen Aljanan data tsaya nan *sanyi* Mai karya garkuwar jiki ya kasheta.. kuma hakan tayi Domin ta koma wannan kofa data shigo ta ciki Dan ba wani Nina tayi da kofar ba...But *it's too late*

Wangale baki Forzy tayi ta sanadiyar taga dakin ya sauya Bayan ta bude kofar.... Komai dake Cikin dakin ta banbanta...
Dukda sauye sauyen da Forzy ta ganin hakan baisaka ta koma baya ba...Hala tasa kafa ta shige ciki.

Wannan dakin data shiga ko Tasha banban da sauran Danko Duk Inga ka Duba Jikin wannan daki zakaga hoton kanka yadda kasan *Mirror* "Madubi" Haka dakin yake.....

Bangaren Noor da Nina ko Cikin Sauri suka karasa kofar Nan da Forzy ta Shiga sai Nina Ta juyo fuska ta kalli Noor....

Batare da Noor din Tace wani Abu ba tasa Hannu ta bude kofar...nanfa na cike da mamaki matuka Danko Dakin Da suka tsinci kansu ciki Tasha banban da Wanda Forzy ta Shiga... Domin kuwa Forzy dusar Kankara ta gani cike da dakin yayinda su ko suka tarar da dakin wani iri....

Dakin nada abun ban tsoro matuka yadda kasan tafkin matattu,Kuma tayi Kama da *masarautar mayu* Domin kuwa komi na wannan Daki anyi sane da kasusuwan Mutane....
Kama Daga Kan kujeru zuwa Kan kabot kabot har fitulun gurin Duk da kasusuwan Mutane akayi.

Kan suce kobo....iskar Wannan daki ta zugosu ciki suka zube kasa....kofar taja kanta ta Rufe zanen Jikin kofar ko ta bada haske Wanda wannan hasken harufan rubutu ne suka bayyana wacce itace.... *FARFAJIYAR MUTUWA*

Haka suka mike suna waige waige hade da Tafiya Cikin Sand'a Dukkannin su biyu har zaka kasa gane wacece Aljanan a Cikin su Danko Duk a tsorace suke.

Karar Rushewar Tarkace suka jiyo Nan da Nan sai suka fiskanci wurin Cikin tsoro Noor Tace "waye??" Sake furta hakan tayi "waye? Wai waye anan gurin??" Amma Babu Wanda ya ansa Mata nanfa saita juya ta kalli idanun Nina.....
Nan Sai suka saki jiki suka Soma Tafiya Kamar Babu komi but then Sai Nina Taji an kamo Hannun ta....cewa tayi

"Haba Noor Yanzu tsoron naki harta Kai ki rike mini Hannu?,Domin karkiji Kamar ke Daya ce anan gun""
Haka tafurta yayinda suke Tafiya Cikin kwanciyar hankali... Noor ko Tace da ita

"Rike Hannu Kuma,Taya zanyi Haka baya ga hannayen nawa biyu kina kallo"
Haka tabata ansa hade da Daga hannayen nata Nina ganin Haka yasa ta kwarma Ihu hade da juyawa taga waya rike Mata Hannu....

Juyawar da zatayi kawai Sai ta tarar da *Ahmed* tsaye gefen ta.....
Cikin Mamaki hade da shewa ta kirawo sunan sa nanfa suka rungume juya.. ganin Haka Yasa Noor taje wajen su da sauri ta rabasu....

"What Got into You Noor? Abokina nefa Shi Kuma mun rabu dashi tun Lokacin da muka Shiga wannan Guri,Amma Mai yasa kike son hanani murna ko nace magana dashine"
Batare da Noor din Tace da ita komi ba ta sake riko Hannun Ahmed nanma Noor ta Raba Hannun,ta hanasu sakan da Ran Ahmed ya baci sai yace.....

"What the heck is going on with you??"
Cikin wata murya Mai matukar razana mutum...
Cikin Mamaki hade da razana Nina ta zuro idanu....

Idan Muka koma Bangaren su Atif kuwa zamu tarar dasu atsaye....yayinda sukayi Shiru Nay'an wasu dakiku... Kawai Sai sukayi Arba Da wata katotuwar macijiya.....Wanda Girman ta,kaurin ta da Kuma tsayinta takai Bishiyar dapino....Kura musu Ido wannan macijiya tayi Tana ta wani Huci.... Mufyda ko kasa rikewa tayi Ta buga Ihu....

Nanfa Suka Ruga a guje yayinda Macijiyar ta biyosu cikin wannan kogon da suka Shiga.... Haka zalika butterfly din Suma tsill suna ta Shiga.

Cikin gudun da suke kawai Sai sukaji sun taka wani Guri ya nutse dasu,ihu hade da shureshure suke tayi kafin sukai kasan wannan Guri.....

Zubewa sukayi a kasar wannan Guri.....yin hakan ko keda wuya suka mimmike tsaye suka Kuma Daga ganin su sama Domin sunga wannan Macijiyar.....
Katotuwar idonta suka gani ta laiko su...Danko wannan Guri da suka fada bazata isheta shigaba Haka tayi ta bugawa harta gaji ta koma...

Fitarta ko ScorpionsπŸ¦‚πŸ¦‚πŸ¦‚πŸ¦‚ suka shige ciki......da dukkan alamu Gurin Suma zasuje Kuma inamai kyautata zaton idanko sukaje wannan Guri sai sun shige da zamin zatayi daidai dasu.....

Al'amarin su Atif ko tsintar kansu sukayi a tsakankanin zabga zabgan takubba wacce tayi Kama da irin ta samudawa.....
Cikin Mamaki suka bude baki suna kallon ikon Allah Domin kuwa Duk wayennan takubba sun kasance ta zinari ne...

Samra tsintar wasika tayi Cikin Mamaki hade kuma da Naiman sanin maike Cikin wannan wasika saita bude...
Rubutun Cikin wasikar da jini akayi ganin Haka Yasa ta zuro idanu...sanar dasu tayi inda suka naimi data karanta musu....nanko tayi gyarar murya ta Soma Kamar Haka.


*"Barkan Ku da shigowa kofar ajali, Yayinda kuka Riske wannan wasika kuka Kuma kasance Kuna karanta wannan sako,Toh Ku saurari zuciyoyin ku sa'annan kuyi aiki da kwakwalan ku..... Makullai ko nace Halin da zaku kasance ciki na jikin Takobin Da zaku bude wannan kofar dake gaban Ku.......dashi,Takubba shida Zakuyi anfani dasu wayenda suke dauke da Harufa Kamar Haka"*

*Ma*
*Uu*
*Ta*
*Uu*
*Wa*
*Aa*

Zura idanu Samra tayi Muzzaffar ko yace da ita "meye hakan ke nufi....??"

Mufyda Tace *"Mutuwa"*
..........................😲😲😲


πŸ’€πŸ’€πŸ’€
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
πŸ’€πŸ’€πŸ’€

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________


*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________


*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*



*FREE BOOK*πŸ’―βœ…
*EPISODE 0️⃣9️⃣*




Wangale baki Forzy tayi ta sanadiyar taga dakin ya sauya Bayan ta bude kofar.... Komai dake Cikin dakin ta banbanta...
Dukda sauye sauyen da Forzy ta ganin hakan baisaka ta koma baya ba...Hala tasa kafa ta shige ciki.

Wannan dakin data shiga ko Tasha banban da sauran Danko Duk Inga ka Duba lungu da sako na wannan daki zakaga hoton kanka yadda kasan *Mirror* "Madubi" Haka dakin yake.....

Forzy Babu Bata Lokaci ta Soma taku Cikin sanyin jiki,Amma kuwa Abinda Bata sani ba shine Duk madubin da Ta wuce maimakon hoton

Please Login or Register in order to submit comment