Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu kama da kadangaru sukayo kanta sukayi gutsigutsi da namarta...Gaskiya tayi mutuwar wulakanci....


😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

@*Abdul Alhaji Musa comment*
"Ahmed Da Nina Allah Ya jikanku da Rahama"


*_Mu Hadu a Episode 11_*

_@Abdul Alhaji Musa *Return*_


πŸ’€πŸ’€πŸ’€
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
πŸ’€πŸ’€πŸ’€

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________


*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________


*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*



*FREE BOOK*πŸ’―βœ…
*EPISODE 1️⃣1️⃣*
*THE CONFUSION*



#Tina da Mufydah ko suka hadakai guri guda cikin rad'a Tina tace da mufy..
"Ko meye dalilinsa nayin hakane oho"

Atif,mu'azz duk sunyi sanyi da sukajiyo wannan magana ta Samra....

*"Meye Al-Hussien ke Shirin boyewa gaskiya da lauje cikin nad'i,"*
Haka Atif ya furta cikin kasar zuciyar sa.....

Zuciyoyinsu Bugun uku uku take yayinda suka kasance a Ankare domin kuwa saura kiris wannan Garkuwa ta Rezar wuta ta kafe.
yadda suka kasance a ankaren hakama Scopions din suka kasance... Domin kuwa har sun soma matsowa wajen garkuwar.

Aiko daukewar wannan Garkuwa ta Rezar wuta tazo daidai da Tsinkewar wata siririyar murya Mai fasa dokin kunne...
Wannan Kara na bada sautin "Aaaaaaaaaaaaaaaaaaa!!" Cikin firgici da naiman kare kunnuwa su daga fashewar yasa suka toshe da hannayensu biyu..
Wannan Kara dai ya dauki lokaci kafin ya tsaya,bayan tsayawarta sai suka tsinci kansu cikin wani yanayi Mai wuyar sha'ani.

Kallon Abubuwa uku uku suke ta sanadiyar mugun jiri data kamasu dukka,ga kuma rashin jiyo sauti ta dalilin jini dake zubowa daga kunnuwan su...
Dukkan ninsu sun kasance cikin wannan yanayi illa Al-Hussien da ko daya daga cikin hakan bai samesa ba...

*ATIF*
Sai faramar Rintsa Idanu yake yanata Girgiza Kai da niyar ya samu waraka daga jirin dayake ji da Kuma rashin jiyo sauti.
Haka yayita fama Amma Babu alamar kaiga ci,hala bai daina wannan aba tasa ba daga karshe ya dago hannun sa ya daidaita setin kunnuwansa ya soma tafi dan yajiyo sautin Amma shiru kake ji....



*Noor*
Zaune take ta mansher da hannunta tamkar laita tana ta kunna wuta tana kashewa yayinda Forzy ke zaune gefe guda

"Noor! Zamafa bai same muba ya kamata mu Kara gaba ko Allah yasa mu dace...."
Fadar #Forzy kenan inda #Noor din ta Bata ansar cewa.

"Ni Kuma Ina ganin Nanne daidai gurin da ya dace mu yada zango,Ya kamata muhuta Domin Duk jiki na Rad'adi."

"Alright na amince Miki bawai Dan inaso ba dan ya zaman mini dole ne,Amma bayan Nan karki sake naiman agaji irin wannan"
Haka Forzy ta ce da ita...inda tayi Gajeriyar murmushi Hadi da cewa
"Cikin sauri haka kin amince da bukata ta kamar yadda Y'an Kungiya guda keyi, gaskiya kedin ta Daban ce"
Forzy ko tayi Gyaran Murya sa'annan tace da ita...

"Kina nufin Dangan taka kenan irin ta mutanen Team daya,Hm banason mu hada Dangan taka ta wannan sigar nafison mu zauna tare a matsayin Two sister Har izuwa karshen Rayuwan mu Dukda bansan goben mu ya zata kasance ba,ko mutuwa ko Kuma Rai Amma inason mu kasance sister Har ranar da daya daga cikin wayen Nan abubuwan Dana lissafa zata riske mu."
Haka tayi ta zazzaga bayani yayinda ta sauke idanun ta kasa...bayan ta karashe bayanin nata ko ta dago Idanu da niyar da kalli fuskar Noor ta Kuma cigaba da bayanin...Amma sai tayi kicabus da #Noor na sheka bacci hade da mishari..

"Noor!!.......Seriously?"
Haka ta furta bayan tayi arba da Noor din Hadi da dafa goshi bayan ta furta hakan ta dauki wata y'ar mitsitsiyar dutse ta jefi Noor din da ita.

Aiko cikin abinda bai wuci dakiku Goma ba itama ta fada duniyar bacci....Dukda surutan da take ita kadai.


"Atif,mu'azz,Simon,samra wai Bakwa jina ne ku kalleni anan gurin..."
Haka Al-Hussien ke furtawa yayinda yake ta d'aga musu hannu Aiko saidaga bisani suka Soma jiyo muryarsa yadda kasan ana Kara sauti na'ura haka suka soma jiyosa.

Bayan wasu Dakiku Jinsu ta dawo daidai....Nan da Nan sai Atif yace da Al-Hussien

"Maye yake faruwa?"

Al-Hussien nuni yayi musu da yatsa,suko cikin sauri suka juya ganinsu izuwa wurin da yake yimusu nuni....
Aikuwa bai wuci taku Ashirin bane tsakanin su da kunamun yayinda kuma suke karasowa cikin zafin nama....
Kansuce Kobo sai suka ji Kofar Nan dake bayansu taja kanta da karfin tsiya ta bude...

Wata irin zafine ya fito ta cikin wannan dakin,suko da suka kasance taku gomane kacel tsakanin su da kofar duk suka jike shakab Dan zunzurutun zafi ga muka wani hayaki dake bulbullowa ta ciki...Mai warin gaske.

Dakin ya kasance Babu haske ko kadan Danko bayan sunji kofar ta bude suka juyo ganinsu izuwa wurin haka zalika Scopions din suka take biriki...

Aiko cikin abinda bai Kaiga dakika guda ba suka Kara a guje da niyar shigewa Dakin....sabida basu da zabin da ya wuce shiga cikin dukda Basu san meye zasu tarar a gaba ba.
Aiko Saida sukayi gaf da shiga gurin sai Al-Hussien yace dasu.... *"Ku dakata"*
Tamkar daukewar Ruwan sama haka suka tsaya cek,Babu Mai motsawa,gurin sai yayi shiru domin sune Dama suke kokarin guduwa Dan tuntuni Scopions din sun tsaya guri guda.

Shuri kakeji ganin haka yasa Samra ta juya Hadi da yimusu alamar tambaya domin itace ja gabansu a guduwan....
Mu'azz cikin sauri yayi mata alamar *waya sani* nanfa ta juyo da niyar ta fuskanci kofar Aiko Bata sami damar yin haka ba,Ihun tayi Hadi da zura idanu ganin haka yasa mu'azz yayi sauri ya tureta suka zube kasa,haka ko duk sukayi cikin abinda bai wuci dakika guda ba duk suka kwakkwanta kasa ganin Al-Hussien shi bayi hakan ba yasa Atif Yaje a Guje da niyar yasa shi yayi hakan Aiko sai dayaje gab da tabashi sai ya gauce gefe guda nanfa Atif yasha kasa....


Dalilina Samra na yin wannan ihu ko shine Damin JemaguneπŸ¦‡πŸ¦‡ tayi arba dasu wayenda sukasha babban da ta duniya, domin girman su da Kuma yanayi su yayi Kama data horror films....
Sun Kai girman katon ZakaraπŸ“ gasu da manya hakwara....da Kuma jajayen Idanuwa.

Bayan sun gama fitowa ko suka fara kaiwa Scopions dinnan Hari ta yadda idan sun kama daya sai sun kacelcela nama sa haka suma idan kunama ya saresu sai naman jikin su ya zagwanye su koma kwarangwal.
Haka suketa kakkashe junan su..Aiko Basu tsaya kallon wannan yaki nasufa shigewa cikin dakin sukayi bayan Al-Hussien ya tabbatar musu da cewa daga zaran sun daya daga cikin wayennan halittu sunyi Nasara kansu zasu koma ta dalilin haka yasa suka shige wannan kofa....

Aiko da shigarsu kofar taja kanta ta rufe.....Duhu kake iyya gani ta ko'ina
Kasancewar su a wannan guri tayi daidai da kasance a duniyar Mars ba tare da abin tallafawa mutum gurin Nunfashi ba,domin da shigarsu kofar suka sume.

Tsawon lokaci sukayi a sumen kafin suka dawo bacci....cenfa Atif Ya farka inda ya Mike tsaye hadi da yin hamma da Kuma mika,bayansa ko Samra ce ta Mike tsaye itama...
Cike da mamaki suke suna ta kallon yanayin Gurin domin kuwa basuyi zaton haka zasu yadda guri ba aikuwa Jin Tina Ta tsinke da ihu yasa suka Razana Hadi da juyawa gurin da suke tsammani zasu tadda ita...

Haka ko akayi tadda ita a gurin sukayi yayinda ta yunkura a fusace....Zura Idanu Samra da Atif sukayi bayan sun tadda abinda yasa Tina Ihun.

"Subbuhanallahi Aikuwa a Tsakiyar kaburbura muka kwana"
Haka Atif ya furta inda sauran matafiyan nasu suka Mike a gurguje domin kuwa tuntuni suna sauraran su kasala ce kurun ta hanasu mikewa...tsayen.

Aikuwa kamar yadda ya furta haka al'amarin ta kasance domin Kuma a tsakankanin Kaburbura suke tsaye...

"Oh My God, wannan wace irin Almara ce?"
Fadar #Muzzaffar inda #Ali yace

"Ban Tabba Halattar irin wannan gurin nayi 30minutes ba Amma sai gashi yau na kwanta nayi bacci a tsakankanin su, gaskiya ya kamata mu gaggauta barin wannan guri.

"Wayyo Ni, Gaskiya ya kamata mu gaggauta barin wannan guri."
Fadar Mufydah inda mu'azz yace da su....

"Guys Hold it,Ina Al-Hussien da Kuma Harun?."

Cikin mamaki Samra tare da Atif sukayi furucin...
"Al-Hussien?"

"Eh Ko kungansu a Nan gurin?"
Tambayan da ya jefesu dashi kenan a madadin ansa,suko maimakon suce a'a juyawa kawai sukayi suka soma naimansu Hadi da kiraye kirayen sunayensu cikin Kara....

Aikuwa barin su wannan guri keda wuya sai hannun mutum ya baiyana a cikin kasan tamkar yadda tsirrai ke fitowa.

Al'amarin Forzy ko farkawa tayi daga bacci inda taga kanta kwance jikin Noor takumayi follow da kafadar Noor... hakan ko bai Bata wani mamaki ba har sai datayi arba Da motar su fake bakin hanya,shewa tayi Hadi da tasar Noor daga bacci,Budar idanunta keda wuya tamike cikin sauri Hadi da Rungumar Forzy..

Bayan tayi hakanne ta tuno abinda ya faru da ita a lokacin da ta fire da niyar ta lulluka cikin gajimare....Aiko Tino haka keda wuya ta saki jikin Forzy Nan da Nan ko gurin ya sauya...
Sararin samaniya ya dawo jajir kamar jini,ganin haka yasa ta rude Hadi da cewa

"Forzy wannan bad sing ne, wannan gurin Chakwalwalin bakaken Aljanu be ya kamata mubar gurin Nan da sauri."

Riko hannun Forzy tayi Amma ko Forzy tayi kamar hakan bai dameta ba...
Hakan yasa tace da ita "Muje ko" fadar hakan yasa Forzy ta shureta da hannu... Ai kuwa cen guri guda ta fadi.

Noor a firgice ta d'aga Kai inda tayi ido hudu da jajayen Idanun Forzy....
Aiko Forzy ca tayi kanta inda ta Danko sawunta,yadda ake kakkabe daud'a a jikin katuwar barko haka Forzy tayiwa Noor tana ta bubbugata da kasa.

"Noor! Noor! Noor!!"
Haka Forzy ke furtawa yayinda ta kasance tayiwa Noor din filo da cinyarta tana Kuma jijjigata Hadi da cewa *Ki tashi*
Aiko hakan bai samu yuwa ga Noor ba Danko taso ta farka daga mafarkin da take Amma haka baiyu ba sabida hadarin da take fuskanta a mafarkin nata...

Idan muka koma cikin mafarkin nata ko zamu ga hallau tana a hannun Forzy wacce take gallaza mata bakar azabar...
A zahirance Kuma tana kwance ne a hannun Forzy gaske,gumi ko ya jikata shekaf sai famar shureshure take kamar Wanda ake Zara Ransa...

Forzy ta rasa maike damun Noor,dukda tasan Jensin su ba daya ba Amma sai take kokarin tallafa mata...
Kuma Bata Razana ba har sai dataga Noor na Aman jini,hakan kuma ta farune ta sanadiyar mugun naushi data Sha acikin ta,ta cikin wannan mafarki nata Mai wuyar sha'ani...yasata wannan Amai na jini.

Bude Idanu tayi inda tayi arba da Forzy dake kokarin dawo da ita a duniyar gaske Amma haka kwata kwata baiyu ba Danko tuni ta sake lumshe Idanu haka ta sake tsintar kanta a gaban waccen aljanar Mai kama da Forzy,Yun kurin Tayi danta Mike inda bakar aljanar ta take kanta da zabgegiyar kafarta haka yasa ta bude fukafukanta inda wannan wings nata ya bude Forzy dake kokarin tasarta daga mafarkin ta Fadi gefe guda...

Ganin tana kokarin tashi ta fire Kuma idan ta tashi saman zata iyya jin rauni yasa Forzy ta sake yunkurawa a guje ta haye kanta Hadi da riko goshinta da yatsa uku,Aiko duk Shure shuren ta a hannun Forzy takeyi domin kuwa riko goshin nata da Forzy tayi yayi matukar hanata sakat....

Haka zalika cikin mafarkin nata ma ta gagara mikewa su Kara da waccen aljanar....
Fashewa aljanar tayi da dariya Hadi da kyakyatawa sa'annan tace da ita...

"Ke bakiga hakan ba,Aiko Ajalin Duk aljanar data shige wannan guri na rataye ne a wuyar Y'an Adam,kamar Kuma yadda take Shirin faruwa yanzun a kanki Danko Zaki bakunci Lahira Hade Kuma da tallafawar Forzy wajen danne mini ke yanzu"

Aiko bayan ta furta haka ta bangare hannu saiga wata zabgegen takobi ya bayyana a tafin hannun ta Noor naji Kuma tana gani Amma ta gagara komi har ta taka a hankali tazo kusa da ita.....

Murmushi tayi Hadi da d'aga takobin sama da niyar sare mata Kai.

Idan muka Laika bangaren Guda na wannan katafaren guri kuwa zamu jiyo muryoyin Su Atif na Ihun Kiran #Al-Hussien da Kuma #Harun inda ko suke ta waige waige...

Aiko Al-Hussien da Harun na tsaye guri guda Jin wannan kiraye kirayen nasu yasa suka baiyana cikin sauri.

"What's Wrong Guys?,are You alright?"
Tambayan da Harun yayi kenan inda Samra tayi sauri basa ansa..

"Aww Har kana da bakin Tambayan haka,bayan ku biyun Kun d'aga Mana hankali Mai zai faru kenan idan kuka dawo kuka tarar bamu Nan."

Tarar bakinta mu'azz yayi da cewa...
"Samra ya kamata mu Basu damar fadar dalilin su na tafiya ai"

Itako tayi tsawa Hadi da cewa
"No!!, wannan bayi bane Taya zai yadda ya kebance da wannan din"
Haka ta furta Hadi da nuna Al-Hussien da yatsa

"Ya kike fadar haka Samra,what got into you didn't you see what he did to us?"
Fadar #muzaffar kenan inda Tina ta karashe maganar da cewa.

"He saved our lives,ya kamata Koda ta dakika guda kiji kin yadda dashi domin rashin yadda Babu abinda zata haifarwa illa gurkushewar al'amura."

"No She's right, I'm a stranger tana da damarta nakin yadda Dani ko rashin haka Amma kafin tayi hakan ya kamata ta naimi dalilai kwarara da zata tsaya akai"
Haka ya furta yayinda yake kallonta cikin ido,ganin haka yasa Harun yayi sauri shiga tsakanin su Danko daga irin wannan kallo sai fada Domin kuwa Kama sukayi masa da zakarun dake yunkurin fada.

"A lokacin da muka farka mun tadda kuna cikin giyar bacci Dan ko munyi kokarin tasar ku hakan bazata saka ku farka ba,shine dalilin mu na barinku a wannan guri sa'annan Zuwan mu Nan gurin kuwa Nine Wanda na bukaci haka Kuma badan wani abuba saidan mu naimo Mana mafita daga wannan had'ari da muka kasance ciki."

"Mafita? Kudin wai Haha Taya zakuyi hakan?"
Haka Samra ta furta inda Atif yayi mata tsawa...

"You had Enough,Ya kamata ki daina wannan shasahncin."

"But Atif" haka tasoma da niyar fadar wani Abu Amma mu'azz yayi saurin cewa.

"No but,kawai kiyi shiru we have had Enough of this kinji just stay silent."

Hmm haka tayi Hadi da juyawa ta karasa wajen Simon da Mufydah ta tsaya,Aiko ganin tabar gurin Al-Hussien da Harun suka dubi juna...Bayan Nan Harun yace dasu

"Guys Alhamdulillah bincike mu Bata Fadi kas banza ba Dan mun Sami taswirar wannan gini Kuma dashi zamu iyya fita daga wannan guri."

Cikin mamaki Samra ta zuro Idanu haka zalika Atif shima Amma duk sauran basuyi mamakin hakan ba.

"Taya haka zata faru, gaskiya wannan abin da Almara take"
Haka Samra ta furta a kasar zuciyar ta inda Atif shima ya furta cewa.

"Sai wuya takai wuya ake iyya bada satar ansa,Domi inda kaga ance daku kuyi open Examination a makaranta to ana da tabbacin Babu Mai samun ansa ne"

Shiru yayi na wasu Dakiku kafin yasake da cewa

"Wannan taswirar sabon hadarine a gare mu baki daya ya kamata nasan meye abinyi gashi Samra dake kokarin korafi akan tafiyar Harun tare da Al-Hussien tayi shiru sabida mun Mara musu Baya Amma ko Babu komi saina binciko maike kasar wannan taswira"

Haka yayi ta sumbato shi kadai inda sauran abokan tafiyar tasa sukayi can kan taswirar suna dubawa,aikuwa bayan sun kammala dubawa suka dau haramin tafiya Amma hallau tsaye Samra da Atif suke.

Saifa da suka ga kan abokan tafiyar tasu ta suka bace musu kafinnan suka juyo suka dubi juna.
Babu Wanda yace da Dan uwansa uffan haka suma suka biyo sahu,dakin nada matukar girma domin kuwa bazaka iyya kure dakin da kallo daya Tak ba.


*#Forzy*
"Taya Zan taimaka Miki na dawo dake duniyar gaske sister kibar duniyar ta mafarki,gaskiya kaina ya d'aure matuka Amma gaskiya ya kamata na taimaka"
Haka Forzy ta furta cikin siririyar murya idan Kuma muka Laika cikin mafarkin nata ko zamu tarar Aljanan Nan Mai kama da Forzy tana rike da takobin yayinda ta d'aga Tama kamar Mai faskaren itace,tana kokarin dire takobi a makoshin Noor.

Aiko takobin na kaiwa gab da kan Noor sai ta tarwatse ba tare da Takobin ya sare mata kai ba...
Nanfa ta dawo duniyar gaske inda ta tadda Forzy na zaune kanta,tashita ta rugumi Forzy Hadi da cewa

"Bacci matsifane a wannan guri Forzy, gaskiya Ina cikin had'ari kasance wata Anan,na gode Miki da Kika dawo Dani wannan duniyar"
Cikin shesshekar kuka take furta hakan inda Forzy tace da ita.

"Gaskiya #Allah da girma yake,baya marawa karya g**di koda tazo a hannu kafiri ko Kuma musulmi,haka zalika Yana goyon bayan gaskiya akowace hannun daya fito,Koda kuwa a hannun kafirine ko Kuma Mai addini,Noor da ayoyin #Uban-Giji Mai girma na naimo Miki masaluha dukda cewa tana konaki kema domin kin kasance daya daga cikin bakaken Aljanu,Amma abin mamakin Dana tarar game da yanayin da Kika shige kuwa shine kwata kwata wayennan ayoyi Basu konaki ba hassalima dai baki karfin farkawa tayi, gaskiya nayi mamaki."

Aiko sake Rungumar Forzy tayi inda tace da ita
"gaskiya nayi dace abokiyar tafiya."

"Hmm Kin jiki wai,Y'ar uwa ko abokiyar tafiya."

Fashewa sukayi da dariya inda suka Mike suka Kara gaba dadd'i da bode wata kofa suka shige ciki...

Aiko wannan kofa dasuka kasance cikinta ta kasance tamkar a doron kasa take domin imba rashin Ganin Rana da sukeyi ba da sai suce suna a cikin Dajine kawai...

"Wow Kinga abin mamaki"

"Eh Naga hakan Forzy".

Ruwane kwance a gurin ga Kuma bishiyoyi dake gurin saman ruwanko Fararen furanni ne koto ina..masu Jan hankali

"Kinga Fararen fure, gaskiya gurin gwanin ban sha'awa,ya kamata na Ciro guda."
Haka Forzy ta furta....Hadi da rugawa a guje ta nufi gurin.

Idan na dauke ku ko mukayi taku Dubu tare daku a wannan guri zamu riske Taron su Atif a bangare guda na wannan Rafi inda Samra ke cewa...

"Wannan itace Aikin Taswirar? meye wannan to?"
Haka ta furta yayinda take nuna ruwan da hannu ta...

Atif cewa yayi
"Fararen furanni irin wannan,Kuma duk sun mamaye saman ruwan hakan na nufin ruwan Babu zurfi."

"Karkuce ta cikin ruwan zamubi mu wuce"
Tambayan da Simon yayi kenan inda Tina tace Aiko kasar wayennan furanni na matukar sa mutumin kaikayi....

"Aiko Babu Daman tabasu domin kuwa daga zarar mun taba guda daga ciki tofa mun afka cikin chakwakiyar bala'i da Bamu San iyakarta ba"😳...
Fadar Al-Hussien kenan....


_*Readers kamar fa naji Forzy tace zata Ciro daya tofa Allah yayi Mana maikyau*_


*Cigaban labari*
Daga cen inda suka baro wato Kaburburan da suka farka a tsakankanin su,mutane dake cikin Kaburburan ne ke fitowa yadda Iiri ke tsaga kasa ya fito haka suma sukayi ta fitowa...
Kowani daya daga cikinsu idan ya fito sai yayi girgiza Nan sai namar jikinsa ya zagwanye ya zube kasa kwarangwal nasa ko sai ya ruga a guje. Haka sukayi ta fitowa suna nufan inda Su Atif suke.


😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳
*_Mu Hadu a Episode 12_*

_@Abdul Alhaji Musa *Return*_
_1st September 2021_

Sai hakuri nayi late update litin kwana dayaπŸ˜‚πŸ€£πŸ˜


πŸ’€πŸ’€πŸ’€
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
πŸ’€πŸ’€πŸ’€

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________


*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________


*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*



*FREE BOOK*πŸ’―βœ…
*EPISODE 1️⃣2️⃣*




πŸ¦‡πŸ¦‡πŸ¦‡
"Aiko Babu Daman tabasu domin kuwa daga zarar mun taba guda daga ciki tofa mun afka cikin chakwakiyar bala'i da Bamu San iyakarta ba"😳...
Fadar Al-Hussien kenan....

Da juyo hakan ko Harun ya saukar da idanu alamar nazari,bayan Nan ya juya izuwa ga #Samra ya Mika Mata taswirar dake hannun sa.

"What?" Cikin salon Tambaya Samra ta furta hakan inda yace da ita..
"Ina son ki jagorance mu"

"What!!"
Cike da mamaki Tina ta furta hakan hade da zuwa idanu, sa'annan ta sake da cewa

"But why?"

"Wallahi Babu komi cikin Raina,kawai Naga jajircewar ta,Kuma inaga tafiyar tamu zata kayatar idan ita ke jagorantarmu."

"Hmm" hade da murtuke baki Samra tayi ganin yanayi da Samra ke ciki yasa Mufydah tayi sauri cewa.

"Guys shin kunsan ana binmu sallah na yini guda kuwa? Robonmu da sallah fa tun asuba'in jiya"

"Kuma hakane Fa ya kamata ku Sami guri da Kuma lokaci domin biyan sallolin da ake binku."
Haka #Simon ya furta shida ya kasance Kirista a cikin su.

Al-Hussien ko ya furta cewa
"Hm maiyasa kuke sakaci ne da yawa,Ashe bayan rashin tuno addu'o'i harda salloli ciki."

Aiko dukkan ninsu shiru sukayi inda Harun ya ce da Al-Hussien.

"Gaskiya mun sha'afa ne,domin wannan Guri na cike da Almara iri Daban daban,Amma duk laifina ne domin lokaci Dana farka daga sumar da mukayi na Tino cewa bamuyo sallah ba na yini guda,shiyasa nayi taimama na idar da sallar Amma lokacin da sauran abokan tafiyar na suka farka ban Tino musu da hakan ba,kuskure nane wannan."

"Tunda yanzu mun tuna hakan maizai Hana muyi ta yanzu."
Fadar Mufydah kenan inda Mu'azz yace dasu

"Uhm.. gaskiya Ya kamata Kam muyi yanzu,tunda yau shine karshen wahalar mu,kamar yadda Harun ya tabbatar Mana kunga kenan Babu bukatar mu buya sallah bayan mun fita daga Nan."

"Kwarai kuwa."
Hakan Tina ta mayar masa da martani, Harun shiru yayi Yana ta sauraron su...
Aiko saiga wata kudan zuman na kokarin shige masa Idanu cikin sauri ya soma korarsa da hannu Aiko Yana cikin haka ya hango taron korangwal dinnan na tunkaro su,Ganin haka yasa yayi furucin *Oh no*

"Ya dai?."
Tambayan da Ali yayi masa kenan shida ya fahimci yanayin Harun din ya sauya,ganin bai basa ansa ba ne yasa shi yunkurin juya Idanu izuwa inda Harun din ke fuskanta Amma sai Harun yayi saurin mayar masa da ganin sa hade da cewa...

"We have to leave this place... Now"

"What!,why?, sallar da muke kokarin Yi Kuma fa?"
Fadar Mufydah kenan inda mu'azz yayi saurin cewa...

"Ya kamata mu girmama fadan nasa domin bamu San dalilin sa na fadar hakan ba."

"Girmamawa sabida meye wai,munafa cikin had'ari Koda yaushe Mai zaka sanar da Uban Giji kenan idan iftila'i ta afka da Kai ka mutu?."
Tambayan da Tina tayi kenan Wanda yasa duk jikinsu tayi sanyi but Banda Harun da Kuma Al-Hussien,su sun kasance sun hada fuska domin basuji dadin hakan ba.

Samra Ganin kan abokan tafiyar tasu zata rabe gida biyu yasa tayi wub ta karbo taswirar dake hannu Harun ta bude,gani tayi taswirar na nuna Mata hanya a inda suke tsayen wacce ta cikin ruwan tabi ta wuce..

Bata ce dasu komi ba kawai tasa kafa ta shige ruwa,Aiko Babu Wanda ya sake fadar komi haka kowa yabi bayanta da dukkan alamu ta anshi tayin Harun..

*Al'amarin Forzy da Noor*

"Wow Kinga abin mamaki"

"Eh Naga hakan Forzy".

"Kinga Fararen fure, gaskiya gurin gwanin ban sha'awa,ya kamata na Ciro guda."
Haka Forzy ta furta....Hadi da rugawa a guje ta nufi gurin.

Zuwanta gurin keda wuya sai Noor ta kwala Mata Kira,Aiko cek ta tsaya inda ta juyo,fuskarta cike da annashuwa.

"Mai kike ci na baka na zuba,Aiko ta cikin furannin zamubi mu wuce Kinga kenan har Zaki koshi dasu Dan haka ki bar maganan cirewa kawai mu wuce."
Fadar Noor kenan inda Forzy tayi Gajeriyar murmushi Hadi da cewa.

"To ni banga kwale kwale ba Taya zamu bi cikin ruwan?."

"Fararen furanni na hayayyafa ne a gabar ruwa inda Babu zurfi sosai,to gashi sun mamaye kan wannan Ruwa haka na tabbatar Mana da cewa wannan ruwan Babu zurfi Dan haka muje,ta ciki zamubi mu wuce."

Aiko Babu Bata lokaci suka shige cikin wannan Ruwa wacce ta kasance daidai kugunsu suna tafiya cikin fira hade da Raha kamar tagwaye...

Kimanin Mintuna talatin both side din suka kasance suna tafiya Ruwan wato bangaren Su Atif da kuma tasu Noor, yayinda suka kasance sunyi matukar kusanci da juna Danko dabadan Hazon daya mamaye gurin bane da zasu hango juna.


Take biriki Samra tayi inda dukkannin abokan tafiyar nata suma suka tsaya..

"Impossible."

Zura idanu Tina tayi tun kafin taji dalilin Samra na furta hakan, Mufydah ko cikin sauri tace

"What's wrong?."

"Taswirar Bogi ce mukayi anfanin dashi,Kuma hakan na tabbatar min da cewa mun fada cikin iftila'i."
Ansar da Samra ta bayar kenan bayan taji tambayar da Mufydah tayi.

Aiko Atif cikin sauri ya anshi taswirar yasa Idanu inda Mu'azz shima yayi hakan...

Bayan mu'azz da Atif sunyi hakan ko suka dubi juna cikin mamaki shiko Atif yayi furucin cewa
"Taya taswirar ke nuna Nan itace hanyar fita?"
Haka ya furta a kasar zuciyar sa inda Mu'azz shima ya furta cewa..

"Shin

Please Login or Register in order to submit comment