Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta na ciki ya Dauke a'a Sai hoton nata ya bita da kallo suna Mai dariya hade da nunata da yatsa.

Rashin Sani tafi Dare Duhu,Forzy da tasan Meye take barowa a baya data gaggauta komawa Domin ko wannan bala'i data tsinci kanta a ciki yafi waccen data baro abaya.


_CIGABAN LABARI_


*"Barkan Ku da shigowa kofar ajali, Yayinda kuka Riske wannan wasika kuka Kuma kasance Kuna karanta wannan sako,Toh Ku saurari zuciyoyin ku sa'annan kuyi aiki da kwakwalan ku..... Makullai ko nace Halin da zaku kasance ciki na jikin Takobin Da zaku bude wannan kofar dake gaban Ku.......dashi,Takubba shida Zakuyi anfani dasu wayenda suke dauke da Harufa Kamar Haka"*

*Ma*
*Uu*
*Ta*
*Uu*
*Wa*
*Aa*

Zura idanu Samra tayi Muzzaffar ko yace da ita "meye hakan ke nufi....??"

Mufyda Tace *"Mutuwa"*

*Mu'azz* alamar mamaki yayi hade da Furta "what" Cikin siririyar murya ba tare da na kusa dashi ma yaji hakan ba....
Ansar Wasikar yayi daga Hannun *samra* ya Soma dubawa inda *Atif* Shima yasa Ido suka karanta tare,Bayan sun kammala Haka ko Sai suka dubi idanun juna.

Suna Kan hakan kuwa Sai suka Soma juyo sawun Scorpions din..... yadda kasan girgizan kasa haka gurin ta Soma dauka Dan zunzurutun yawan su, Dukkannin su kuwa suka Daga kallon su izuwa saman wannan gini ma'ana inda sukabi yayin fadowa wannan Guri....

"What are we going to do??,I really don't want to died down here...."
Haka Mufyda ta furta Amma Babu Wanda ya kulata,Duk sunji hakan but they keep silent.

"Ya kamata Mu naimo Takubban" haka Harun ya furta,Cikin hadin baki kuwa Samra Simon Ali suka bashi Ansa "Mu naimo meye?" Hade da Kuma yin tsaki alamar hankali su Bata dauki shawaran nasa ba

"Have you lost it?"
Cewar Mufyda,inda Harun din ya Bata ansa irin ta yen Nigeria wato ansa tambaya da tambaya....
"What?" Itako Bayan Tajiyo tambayar tasa Tace dashi "Kwakwalwar ka,Kai Dama baka ga hakan a tattare da Kai ba....... Taya zakace mu naimo makullan Halakanmu da Kai mu,ai koba komi ya kamata ace mutuwar tamuce ta riskemu da ace mu muka risketa"

"Kwarai kuwa"Haka Tina da Simon suka Bata kwarin gwiwa...

Atif da Mu'azz suka dubi Tina da Simon Nan da Nan suka kame baki sukayi shiru.....

Al'amarin Nina Da Kuma Noor Cikin murya Mai matukar razanarwa sukaji Ahmed yace "What the heck is going on with you??" Cike da Mamaki hade da razana Nina ta zuro idanu ta Kuma kasa motsawa dankuwa Ahmed din na rike da Hannayen ta.

Jiyo Hakan da Noor tayi keda wuya Sai ta bude tafin hannun ta,ta shuri Ahmed da ita....

Cen Guri guda ya Fadi mikewar dazaiyi ko saiya Dawo ainahin halittarsa Mai matukar munu.....da Kuma bantsoro.
Yayi Kama da ababen tsoratarwa har kala uku na farko shine yayi Kama da dodo👹na biyu yayi Kama da horor🧟nna karshen ko shine fatalwa..

Ganin Haka Yasa Noor ta riko Hannun Nina suka Ruga a guje,Basu tsaya ko'ina ba har sai dakin Nan da Forzy ta kasance a ciki wannan daki Mai cike da dubban Madubi.

Take biriki Noor tayi bayan tayi Arba da wannan daki,fuskar tako cike da mamaki ta sanadiyar tayi Arba da wani abun Daya Bata mamaki ya Kuma tsoratata....

Cikin Sauri ta saki Hannu *Nina* hade da zura idanu...ta tsaya kallon fuskar Nina,juyawa Nina tayi ta kalli fuskar Noor.

"Nina who are you Really??"
Haka Noor ta furta Cikin mamaki....hade Kuma Naiman Sani.

Nina cewa tayi "what?" Hade da yunkurin riko Hannun Noor but tayi saurin ja da baya.....

Bakomi bane Dalilin Noor na taka birikin illa Arba da tayi da wayennan mirrors dake wannan daki.....
Abinda yasa ta saki Hannu Nina kuwa shine Cikin madubin da suke tsaye gaban sa kuwa Babu hoton ko mutum daya daga cikin su,hakan Kuma na faruwane da aljanu,ko Kuma fatalwa kadai.

Duk Wanda ya tsaya gaban mirror Dole yaga reflection nashi ciki Amma aljan ko hakan Bata faruwa dasu.

"Karki karaso kusa dani,wacece ke??"
Haka Noor ta sake fada,ganin yadda Noor ta matsa wajen ganin Sai ta binciko ko wacece ita...ya hassala Nina shiru tayi wup!!

Gashin kanta suka mike tsaye, ya Kuma kitsa kansa da kansa Nan da Nan ta koma ainahin halittarta..... Ba kowa bace wannan illa Yarinya Nan data nitsar da Ahmed Jikin bango...
Hada ido sukayi Sai hasken dake wannan dakin ta Dauke gurin tayi matukar duhu sosai....

"No no no no!!!"
Haka nake jiyo muryar Noor na furtawa Cikin murya Naiman tsari Haka Kuma na sake jiyo kofar ta ja kanta ta Rufe..

"Bazasu sake dawowa ba domin kuwa sun ziyarci lahira,sa'anan daya bayan daya sai Kun sheka izuwa barzahu".
Haka wannan Aljana ta furta inda nake kyautata zaton akan Ahmed da Nina take magana...

Bayan ta furta hakan da wasu dakiku na iyya jiyo muryar Noor ta buga ihu na fitar hankali.

Ihun Aljana Noor ce ta ratsa cikin wannan katafaren ginin inda karan ta ratsa ko'ina a fadin gurin ta Kuma kaiga riske *Forzy*, a firgice ta take biriki bayan ta duba ko'ina batare da taga komiba sai ta soma sauri danta hango wata hanya wacce take kyautata zaton Mai billewace.....



Bangaren Su Atif ko tsaye suke sun kasa tsaida magana daya kowa na fadar San ransa akan su tsaya ko su ƙara gaba,suna kan Haka ko sai sukayi arba da scopions🦂🦂dinnan masu girman gaske sun shige wannan guri inda Atif da sauran tawagar ke tsaye....


Aikuwa tuni cikinsu tadau ruwa a Karon da sukaga wayennan halittu na tinkarosu gashi Kuma babu mafaka Kuma Basu da ishesshen lokaci dazasu naimo wayennan takubba dasuka kasance sune makullen wannan kofan da suke tsaye gabanta.

Rashin wayennan abubuwa guda biyu wato hanyar tsira da Kuma ishesshen lokacin naimo makullan kofar ne yasa suka fara ja da baya...
Ai kuwa wayennan halittu Baku rage gudun da suke ba har Saida #Simon yasa kafarsa a wani guri data nitse da kafan tasa ta dama kafin Nan suka take biriki.....

Ganin haka yayi matukar bawa tawagar nasu mamaki Danko dukkannin scopions 🦂 din sunki motsawa....
Haka su Atif suma sukayi babu Wanda ya motsa sai Simon din da kafar tasa ta makale yake kokarin cirota....

Bayan shirun na Dan dakiku kuwa sai wata rezar wuta Mai kaifin tsiya ta tsaga katanga tsakanin su Atif din da wayennan halittu.
Yayin baiyanar wannan garkuwar rezar utar ko sai data sheke sama da scopions 🦂 dari da suka kasance suna setin inda ya bayyanar,Haka zalika tayi daidai da cirewar yatsan Simon biyu....

Buga ihu yayi na fitar hankali hade da dafe hannun nasa... Aiko jiyo Haka da sauran tawagar tasa sukayi hade da...Gani garkuwar rezar utan ta mamaye ilahirin gurin,yasa suka soma ammatar sunan Simon suna komawa a guje...

Aiko mantawa sukayi da scopions din zuwansu gurinsa keda wuya suka fara basa tallafi gaggawa #Mufyda ko tsayawa tayi kallon wannan rezar utan yayinda ta ciki zaka iyya hango abinda ke bayan wannan Rezar.

Juyawar ta tace Dasu "wannan garkuwar bazata wani Jima sosai ba,Ya kamata mu Kara gaba"

"Mai kike nufi #Mufy,Taya Kika San hakan?"
Fadar #Tina kenan inda #Samra tace Dasu..

"Ya kamata ku bar wannan maganar ku aje ta gefe guda...
Ku kawo abinda kuke dauke dashi mu samu mu tsayar da jinin dake zubo masa yafi surutun da kuke...."

#Simon kuwa sai ihu yake yayinda #Atif ke kokari tsayar da jinin dake zubo masa...
#Mu'azz da Kuma Harun kokarin Ciro kafarsa suke daga Ramin....

Wayennan Halittu na kallon duk abinda ke faruwa... Amma sunki motsawa Haka zalika sunki barin guri....

#Mufyda Hallau sa musu ido tayi sa'annan ta sake cewa...

"Tina tambayar da kikayi na cewa Taya nasan hakan shine ban sani ba Amma idan kuka dubi wayennan Halittu Kamar suna zaman jiran garkuwar ta balle su samemu...."

Jiyo Haka yasa #Samra ta d'ago idanu inda tayi arba da Nina tsaye cikin jerin kunamun...
Bayan sun hada Idanu kuwa ta juya ta koma... #Samra kuwa zura Idanu tayi hade da ambatar sunan ta.

#Atif #Mu'azz da sauran abokan tafiyar nasu suka jiyo ganin su izuwa kan #Samra...
Bayan sunyi Haka kuwa sai suka tarar da ita Tana kallon kunamun...
Haka suma suka d'aga ganin su izuwa bangaren da take dubawa... Suko Basu tarar da kowaba...Danko tuni ta bace cikin scorpions din..

Mikewa tayi hade da cewa "I saw her, wallahi I saw her Tana cikin hadari ya kamata mu taimaka mata".

Dukkannin su a tsaye suke inda Atif yadan dafe hannun Simon suka Mike tare...
Tsayawa kallon ta sukayi yayinda ta gigice Tana ta safa da marwa Kamar Mai naiman wani Abu...

Ganin Haka yasa Atif ya dafe ta inda ta tsaya cek juyawar ta ta soma cewa.....

"Y'ar Uwa Nina Tana cikin hadari"
"Nasani" Haka Atif din ya Bata ansa,Inda ta sake da cewa....
"Yah kamata muyi wani Abu akai Atif,mu ceto rayuwar ta"
Cikin muryar kuka take furta hakan...

Rungume juna sukayi inda ta soma shesshekar kuka Atif ko hada Idanu sukayi da mu'azz inda da faruwar Haka ya gyada kai....

Nan ya juya inda ya fuskaci katangar dake tsakanin su da wayennan Halittu...Amma sai ya tarar ba ko daya daga cikin kunamun ko sahun su babu....

"Abun mamaki Ina ne suka shige" haka ya furta inda dukkanin su,suka juya suka fuskanci gurin.....

"Oh no,This is a very bad sing" haka #mufyda ta furta inda da fadin hada sukaji wata Kara Mai kamada tashin nakiya a wannan guri da suke....tsaye

Guri tadau kura sai data dauki wasu dakiku kafin kurar ta yaye...
Cen suka hango gurin Nan data fashe kaikace fasata akayi da nakiya...Kuma a bangaren da suke ma'ana Ramin ta baro garkuwar a baya.

Tsit sukayi Babu Mai motsawa cen sai Atif yace da mu'azz...

"Find the key"

Gyada Kai yayi alamar ok inda Samra ta Soma cewa...

"Hakan bazai taba yuwa ba,bazamu sake barin Nina abaya ba..."
Haka tayi ta furtawa yayinda Atif da sauran mutanen ke kokarin shawo kanta Amma daga karshe ta kwace kanta daga hannun su ta ruga tana Mai dotsawa izuwa wannan Ramin daya fashe aikuwa sai daya saura taku talatin ta kaiga Ramin kawai sai taga wannan macijiya Mai girman bishiyar dafino ta billo ta wannan Rami....

Bayan tayi ido hudu da wannan macijiya ko tayi furucin "Oh no" cikin siririyar murya.


*_Mu Hadu a Episode 10_*

_@Abdul Alhaji Musa *Return*_

https://www.wattpad.com/1116988953?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Abdul10k&wp_originator=b2LZ7blrJjHg%2FvOfGZxWJ3AYIE8qslxtU9ClU2M%2FTT%2BSVKWX%2BlyffYS%2BvoISj0i81Vheq3cNh4IprLmP6xM79L36yrnAUAfinzWZ8S%2BGHI7tsPKxxPin1oz31xIOhKwE



💀💀💀
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________


*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________


*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*



*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 1️⃣0️⃣*
*THE DEATH*




Ihun Aljana Noor ce ta ratsa cikin wannan katafaren ginin inda karan ta ratsa ko'ina a fadin gurin ta Kuma kaiga riske *Forzy*, a firgice ta take biriki bayan ta duba ko'ina batare da taga komiba sai ta soma sauri danta hango wata hanya wacce take kyautata zaton Mai billewace.....

Cikin sauri ta Soma tafiya tana kokarin kaiwa ga kofar,Amma Kuma sai ta Soma jiyo wata murya Mai kama da nata sak nayi mata dariya..abaya,Aikuwa cikin razana ta juyo inda ta tarar da bayan nata Babu alamar kowa,nanfa kirjinta ya soma bugun uku uku...ta Kuma soma magana a kasar zuciyar ta.

"Shin kodai kunnuwa na ba daidai suka jiyo bane....? Kamar naji anayimin dariya"
Aiko Bata kammala fadar haka ba taji tafin hannun mutane sunkai goma a kan kafadar ta....


*#Samrah*

"Hakan bazai taba yuwa ba,bazamu sake barin Nina abaya ba..."
Haka tayi ta furtawa yayinda Atif da sauran mutanen ke kokarin shawo kanta Amma daga karshe ta kwace kanta daga hannun su ta ruga tana Mai dotsawa izuwa wannan Ramin daya fashe aikuwa sai daya saura taku talatin ta kaiga Ramin kawai sai taga wannan macijiya Mai girman bishiyar dafino ta billo ta wannan Rami....

Bayan tayi ido hudu da wannan macijiya ko tayi furucin "Oh no" cikin siririyar murya.

Aikuwa macijiyar batayi Wasa da damar taba,dankuwa ta wani shure ta kaikace Shirin film....
Haka ta tashi sama kamar kwad'o Kuma Babu abunda ya tokare ta illa kofan ga dake bayansu domin kuwa sun bawa kofar baya....

Aiko Sumewa #Samrah tayi Atif, mu'azz da sauran mutanen suko zura idanu sukayi Dan mamaki...

Macijiyar ko ta Soma wani jujjuyawa cikin salo Mai matukar tsoratar tana ta bubbude wuya kamar wata jegariya nanfa ta kurama taron nasu ido....
Can tayi kansu sulululu ta yadda idan ta kaiga su wub daya zatayi musu ta hadesu Dan kuwa a tsaye suke guri guda sunki motsawa sai ihun tsiya da suke....

Kamar walkiya sai ga wani santalelen saurayi ya diro gaban wannan macijiyar, saurayi Mai cikar Kamala da Kuma kwar jini,ga faffadar kirji irin ta jaruman kwarai.

Bayyanarsa a wannan guri yayi daidai da budewar bakin macijiyar da niyar hade taron su Atif... Amma Allah bai Bata damar haka ba ta sanadiyar bayyanar wannan saurayi,kabbara yayi hade da dafe saman kan wannan macijiya aiko cikin kankanin lokaci ta koma baya da karfin tsiya Danko karfin kabbaran yafi karfin ta ba kusa ba.

Zuru zuru mu'azz,Atif da sauran mutanen gurin sukayi domin kuwa abin yayi matukar Basu mamaki,ko kibta ido basuyi...
Wannan saurayin ko tsaye yake yayin da wannan macijiyar ke kururuwa tana komawa baya.... Fadiwa kasa wannan macijiyar tayi cikin sauri da Kuma zafin nama ta Mike hade da yunkurin sake farmakar su...

Aiko wannan saurayin bai Bata damar yin haka ba Dan kuwa soma karanta *Suratul Jin* yayi bayan ya karanta Aya goma na wannan Sura sai wannan macijiyar ta Soma ihu cikin kankanin lokaci ta rikide ta dawo Suffan mutum... Atif da mabiyansa ko mamaki takai makura domin kuwa sun rasa ta cewa sai kallon ikon Allah.

"Meye naka ciki,idan na hallaka su?"
Haka tayi masa tambaya yayinda ta nunashi da hannu sa'annan ta kuma sake da cewa.

"Zaka iyya dakatar Dani daga hallakasu yanzu Amma Ina Mai tabbatar maka bazasu Kai labari ba,Domin matsifun dake tinkaro su ya wuce karfin tunani...Zanga iyya gudun ruwan ka Dan nasan bazaka iyya Basu kariya na har abada ba"

Aiko cikin kasaita saurayin yace da ita....

"Zaku iyya fin karfin Yan Adam Amma bazaku iyya da Allah ba...
Yafi karfin ku,Kuma shi zai bamu damar kare kanmu daga muggan halittu irin ku,masu hukunta mutane ba tare da sunyi laifi ba"

Kelkelewa tayi da dariya sa'annan tace dashi.....
"Mayyasa kake alfahari da karfin da ba taka bace...ita
Karfin da kake ikirari dashi kowa zai iyya mallakar ta... Sa'annan inaso in sanar maka Yau ka Kona ni Amma inaso kasani wannan kuskure da kayi sai dukkanin ku kunyi nadama haka, dukka saikun biya bashin da kuka dauka".

Aiko kafin saurayin ya sake bude baki tuni ta bace tamkar warkiya a tsakiyar dare..
Muryar ta suka soma jiyowa tana ikirarin sai sunyi nadamar konata da sukayi,cen sai tayi shiru hakan ya bawa saurayin damar juyawa ya kurama taron su Atif din Idanu.


*Forzy*

#Forzy #Forzyy cikin Rad'a take jiyo muryar maishi na Kiran sunan ta,juyawa tayi inda ta sake guba lungu da sako na dakin Bata ga kowa ba....

"Wai maike Shirin faruwa da nine?,gaba daya na kimauce.. Hm"
Haka ta furta sa'annan ta girgiza Kai alamar takaici Hadi da tsaki.. bayan tayi hakan ko ta juya da niyar cigaba da tafiyar Tata.

Ihu tayi bayan tayi arba da Tarun Y'an mata maru kama da ita sak saidai banbancin su shine fuskar wayennan y'an matan nada abin tsoro domin wata iriyar dariya suke Mai sa gashin jikin mutum ta Mike tsaye...

Aiko bayan #Forzy tayi ido hudu da wannan matsifar sai ta lumshe Idanu Hadi da hada tafin hannayen ta guri guda Dan zunzurutun tsoro ta Soma karanta *Suratull-Baqara* a cikin ranta....takeyi Dukda cewar tana sauyawa ayoyin gurare haka baisa ta daina karantawa ba haka tayi ta karantawa bakinta na raga haka zalika jikin ta na 'bari.

Dukda karatun da take Bata daina jiyo sautin muryoyin nasu ba...Bayanta ko sai ga wani hannu yazo cikin sauri ya dafe ta aiko yadda kasan Danko haka tajita a yashe gefe guda.
Bude Idanu Forzy tayi cikin sauri bayan taji karan fadiwan mutum Hadi da son sanin waya dafe tan.

Bude ido tayi ta tarar da gurin Babu kowa Babu y'an matan ko daya,cen ko guri guda ta tarar da wani a kwance maishi na kokarin tashi...Aiko yadda kasan barbela haka ta ruga izuwa ga wannan mutumin.

"Karki Tabanin karki Tabanin"
Haka ta furta cikin siririyar murya inda #Forzy ta dakata da niyarta na tallafa mata ta Mike..

Dago fuska tayi suka hada ido inda #Forzy tayi furucin "You?" Cikin mamaki Hadi da zura idanu...

"Yes me"
Haka ta Bata ansa aiko Babu abinda Forzy ta Soma tunowa illa bakar hayakin daya biyota a guje dazun da Kuma yarinyar Nan data taimaka mata Mai fuka fukai a gadon baya wacce ba kowa bace illa budurwar Nan dake zaune gaban ta.

Sake shiga yanayi ta Sumewa tayi sai yarinyar tayi ceb ta cebko ta Hadi da girgiza ta Amma ko bayan tayi haka ta buga ihu ta fitar hankali dan jikin Forzy na d'aye mata fatar jiki yadda Kanan kunar wuta har gurin na hayaki.....

Bude Idanu Forzy tayi yayinda yarinyar tayi saurin cika mata hannu ta bada rata a tsakanin ta da Forzy.
"Maike faruwa?" Tambayan da Forzy tayi kenan inda ta Bata ansa da cewa

"Kina matukar Kona ni Yar uwa, kinada tsari a tartare dake,Kuma Zaki cigaba da tarwatsani idan na tsaya tare dake"

Cikin mamaki hade da daurewar Kai ta wangale baki tana kallon *#Noor*

Bagaren su Atif da wannan jajirceccen saurayin ko.... kafin saurayin ya budi baki tuni ta bace tamkar warkiya a tsakiyar dare..
Muryarta ko ya ratsa cikin ginin tana mai ikirarin sai sunyi nadamar konata da sukayi,cen sai tayi shiru hakan ya bawa saurayin damar juyawa ya kurama taron su Atif din Idanu.

"Gaskiya muna Mai Godiya Dan uwa"
Haka mu'azz ya furta inda Atif shima yace dashi mun gode matuka Amma shiko hada Rai yayi ya kura musu ido...

Y'an matan dake guri tuni sukayi caa kan Samra dake kwance...
Zuwansu suka soma yimata fifita hade da yayyafa mata ruwa haka a hankali ta farka budewar idanun ta ko tayi Karo da mitar wannan saurayin yayinda yace cewa.

"Wai wace irin mutane ne ku?,Mai yasa kuke manta mahalacci a lokacin da kuka tsinci kanku cikin had'ari,Mai yasa kuka manta koyarwar da addinin mu tayi Mana game da naiman tsari a lokacin da muka shiga sabgar mutanen boye maiyasa bakwa naiman tsari daga uban giji sai ihun banza....da bazata kareku da komi ba"

Haka ya jera musu tambayoyi Babu kakkautawa,suko saukar da idanun su kasa sukayi bayan yayi shiru Sai Harun yace dashi
"Gaskiya munyi kuskure na rashin Mikawa mahaliccin mu damuwar mu,Amma insha Allah zamu gyara"

Hm yayi hade da juya baya da niyar tafiya Nan sai Atif yace dashi
"Gaskiya Dan Uwa munyi mantuwar da Bata da amfani... Mun sha'afa ne"

Aiko #samra cikin naiman sani tace da y'an matan dake kusa da ita
"Wai waye wannan? Ya sunan sa Kuma Mai yake a Nan gurin"

Juyawar sa yayi gajeriyar murmushi hade da cewa...
"Shin wai har mun saba da zaku iyya yimin irin wayen Nan tambayoyin?, Yar uwa ba keba dukkan ku anan gurin zuciyar ku cike fal da burin sanin koni waye"
Haka ya bata ansa sa'annan ya sake da cewa....

"Amma Matsifu Sama da dubu dari suna birne a kasan wannan guri.....
Tsayawar ku anan gurin Babu abinda zata tsinana muku illa ta karashe ku baki daya domin wannan garkuwa ta Rezar uta tana gab da dauke wa"

Aiko bayan ya furta haka Harun ya jefesa da tambaya kamar haka.
"Kana magana tamkar ka haddace wannan matsifeffen guri Taya kasan duk wannan malam?"

Gajeriyar murmushi yayi hade da cewa
"da zakubi ta nawa da Kun gaggauta naimo takubba Nan da suka kasance sune makullen kofar domin tsiratar da rayuwar ku,domin kowace dakika sake shiga hadari kuke ya kamata ku fahimci haka"


Shiru sukayi Babu Wanda yace dashi kala domin yama fara Basu tsoro domin tunaninsu ba bil'adam bane
Shiko dayaga alamun haka a tattare dasu sai ya Soma cewa...

"Al-Hussien sunana na kasance Dan bincikena tarini ne sa'annan iftila'i ne yasana shigo Nan gurin,ku yadda Dani ku naimo takubban".

"Maiyasa zamu yadda dashi??"
Fadar #Samra kenan inda Atif yace da Al-Hussien..

"Taya kashigo wannan guri, sa'annan tsowon wani lokaci ka dauka anan gurin"?

"Labari ne Mai tsawo Baku da lokacin sauraron haka"
Haka ya basa ansa shiko yasake da cewa..

"Kana nufin idan mun samu lokaci zaka sanar damu kenan?"
Dajin wannan tambaya ko ya kyalkyale da dariya....

"Don't tag me in,we are not us sabida bana cikin tawagar taku".

"Amma Aiko kaji abinda waccen aljanar tace,Dukda ta nuna bazaka iyya bamu tsaro ba ai ya kamata ka jarraba"
Abinda Simon ya fada kenan shiko ya girgiza ka sa'annan yace dashi.

"Aiko gaskiya ta fada,domin nida kaina bani nake kare kaina ba Allah ne ke kareni kamar yadda nake kyautata zaton zai kareku"
Aikuwa bayan ya furta hakan Samra ta Mike tsaye hadi da furta cewa...

"Hold on Guys,What did I miss??"

Dukkan ninsu ko suka juya idannun su izuwa kanta....cike da mamaki

#Mufydah gajeriyar murmushi tayi sa'annan tace da ita

"Alot"

Al'amarin Forzy da Kuma Noor ko zaune suke yayinda suke nesa da juna...Nan Forzy tace da ita..

"Taya kike tunanin kwakwalwata zata dauki abinda kike fadane,tayaya"

"Forzy nasan bazaki amince ba Amma gaskiyar kenan, waccen da Kika ganmu tare ba Nina bace"
Haka Noor ta furta inda Forzy tace da ita...

"Bama wannan ba Noor,Taya kike tunanin Zan yadda dake bayan ke da bakinki kikace kin koro daya daga cikin mu izuwa wannan guri Kuma nasan ba kowa bane wannan illa Atif.. toh nasani ko kece kike shirya komi ma'ana shirya nitsewar Ahmed da Kuma bacewar Nina da sauran tawagar mu hmm, wannan guri ba gurin yarda da mutun bane Noor cikin kalaman ki na dauki wannan darasin domin kin yadda da wata wacce tazo Miki a suffar Yar uwata daga karshe taso tarwatsa ki,Ina ganin ba kuskure bane nima idan naki amincewa dake".

Gajeriyar murmushi tayi sa'annan tace da ita....
"Bada mugun nufi nazo gareki ba Forzy, Amma kina da damarki nakin amincewa da batuna domin nayi kuskure Dana kasance Ina tsutarwa domin nasan idan da badan Ina tsutarwa ba da tsarin da kike tattare dashi bazata konani ba....
Amma inaso ki fahimci wani abu da da mugun nufi nake bazan iyya tinkaro inda kike ba Forzy ki amince Dani"

Shiru Forzy tayi tana ta nazari Noor ko ta kura mata Idanu....


*ATIF*

Tsaye suke gaban wannan gabjejiyar kofa inda sukasa takubban jikin kofar kamar yadda wasikar da suka karanta ta nuna....
Takubban dake da kalmomin mutuwa suka naimo suka Kuma makalata a jikin kofar a inda suke tunani mazaunin takubban ne....

Shiru kakeji Babu alamar budewar wannan kofa... Nan Tina tace dasu

"Anya kuwa daidaine mukayi hakan"

"Wata kila ba haka suke son muyi ba" fadar Samra inda Al-Hussien yace da ita "ya kamata mudan jingirta...

Aiko Samra tayi salati Hadi cewa....
Garkuwar na karyewa Kuma gashi kunamun sun sake bayana...

Al-Hussien ko ya juya ya duba Hadi da cewa...
"Dama rufe Mana Idanu tayi da karfin tsafi,kunamun sun kasance na gaskene ba Aljanu bane suka rikide....shiyasa suka kasance har yanzu suna gurin Ya kamata mu gaggauta barin nan"

"Tayaya Al-Hussien kanafa ganin abinda ke Shirin samun mu Amma ka gindaya Mana sharud'a idan munaso mu tafi tare da kai...kace Babu Mai taba ka Kuma Babu aikin da za'a saka kayi sannan komi saidai ka fada Mana da baki bawai ka tayamu yiba... Taya kake ganin haka zaiyi"
Samra ce ta furta hakan shigo ko shiru yayi Hadi da dauke idanunsa kasa...

#Tina da Mufydah ko suka hadakai guri guda cikin rad'a Tina tace da mufy..
"Ko meye dalilinsa nayin hakane oho"

Atif,mu'azz duk sunyi sanyi da sukajiyo wannan magana ta Samra....

*"Meye Al-Hussien ke Shirin boyewa gaskiya da lauje cikin nadi,"*
Haka Atif ya furta cikin kasar zuciyar sa.....


*2Hour Ago*
*Awanni biyu dasuka wuce*


"Tafukan Hannu sune makullan Kofan nan I'm sure"
Taimakon da Nina tayi abaya kenan ta sadaukar da rayuwarta wajen ganin ta tsiratar da abokan tafiyar ta abinda ya faru da itako bayan Atif yaja kofar ya rufe shine....

Gani tayi kowani lungu da sako wasu irin halittune ke bullowa ta ciki...Hadi da wayenda tayi musu sata wato sangaranrun mutanen Nan masu kama da gumaka....

Aiko Nan tasan nata yazo karshe...ajiyar zuci tayi dan Babu yadda ta iyya domin hannunta na makale hallau a wannan guri data saka....su

Jitayi hannuwata sun guntule nanfa ta buga ihu na fitar hankali jini ko ta soma kwararowa.... Izuwa kasan gurin,caa halittun Nan

Please Login or Register in order to submit comment