Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kammala fadin hakaba sai suka jiyo wata kara mai kamada rushewar tarkace......a bangare guda na wannan daki da shike dakin nada girma basuma kula da bangaren dakin ba har sai da suka jiyo wannan sauti.

Cikin mamaki suka juyo ganin su zuwa bangaren,haka kuma suka soma taku a Hankali suna mai riskar wuri.....

"Hello! Da wanine anan gurin?"
Haka Ahmad din yake furtawa yayinda suka kasance suna nufar inda suka juyo wannan kara kuma sa'annan wannan bangaren ba wani haske bane da ita sa'annan kuma ba duhun cen ciki bane.

Wannan guri dai dasuka kasance ciki tayi kama da ma'ajiya
Danko dogayen *kabot kabot* ne a gurin,cikin kowani kabot kuma cike fal da Kwalaban magunguna irin ta mutanen da ga kuma ganyayyaki da dama duk suma dan hada magunguna suka kasance a gurin.

Forzy rike take da hannu Ahmad kem yayinda suke tafiya cikin sanda danko still wannan kara bata tsayaba kamardai ana using na kayukan ciki.....

Yayinda suka soma jiyo karan na dadd'a karuwa kuwa sai Ahmad ya juya ya kalli fuskar Forzy a wannan lokacin kuwa labe suke jikin daya daga cikin wayennan manyan kabut kuma suna kyautata zaton bayan wannan kabot dai zasu gane ma idanun su ko meye wannan abinda ke kokarin tsoratar dasu.

Cikin tsoro da kuma Rashin tunani Ahmad ya dauko wani yar itacen daya gani a wuri ya rike a hannu alamar duka zai dashi......

Nan ko ya kalli cikin idanun Forzy sa'annan ya daga y'an yatsar sa....
Alamar dai daga ya dungule hannun nasa zasu shiga a guje....

Hakan kuma sukayi danko yana gungule hannu suka sa kai.....

Abika dasu Atif ko,tafiye suke cikin jerin wayennan mutane,Dukda cewar an lullube su da kelle hakan bata hana nuna hasken da idanun nasu keda shi ba..
Hasken ya matukar haske wannan farar kellen....πŸ§Ÿβ™‚οΈ

Kicabus sukayi da saurar tawagar,danko wayenda suka shigo kofar da fari sune Atif Harun Tina Samra mu'azz.....

Cikin tafiyar tasu ko sukayi karo da sauran abokan tafiyan nasu wato....
Muzzafar,Simon,mufyda,Nina da kuma Ali.....

Cike da mamaki suka Rurrungume juya......
Inda Ali ya soma cewa...

"Ina labarin Ahmad da kuma Forzy?"
Haka ya furta cikin salon tambaya indako babu wanda ya iyya basa ansa...

Nan sai Mu'zzaffar yace dasu.....
"Wait a minute karkuce daga cen karshen dakin kuka tashi?"

"Eh hakane" inji mu'azz Samra ko tace dashi

"Mayyasa kace Haka?"

"Ai kuwa Tun dazu muke ta zagawa cikin wayennan kuma mun gagara samin hanyar fita.....
A tunanina zagayen Zobe kawai muke"

Da jiyo haka ko Samra,Atif,Harun da kuma Tina suka dubi juna cike da mamaki.....

Suna kan wannan tattaunawar yayin da suka tsaya guri guda....
Nan sai Nina tajiyo kara a bayan ta ba tare da tace da abokan tafiyan nata komi ba ta taka izuwa wajen daya daga cikin wayennan sangararrun mutane....

Kura masa na mazurai tayi ko kiftawa batayi nanfa sai ta kula shi wanda take tsayen gabanshi yana da banbanci da saura.....

Dan kuwa sanye yake da wata sarka wacce idan ba babban subane toh yana da matsayi cikin su.....

Nanfa Nina ta d'ale kan kafar sa ta ciro wannan sarka.....
Ta rike tana mai kallo cike da mamaki....
Kai kasa ganewa tayi wannan sarka na lu'ulu'une ko kuma harda Gold ciki dan yadda wannan sarka ke sheki kasan tana da matukar daraja.

Maye ko zai biyo bayan hakan........Hmm

Wani siririyar kara mai fasa dokin kunne ne ya tsahi awannan gurin inda suka toshe kunnuwan su ta sanadiyar wannan kara.... har dauke warta kafin suka sauke hannu....

Abin mamaki kuwa anan guri shine wannan karan bata fitini Nina ba kokadan danko bata sanma anyi ba......itadai kokarinta ta boye wannan sarka dan kar abokan tafiyan nata su gani.....shine abinda ta kasance tanayi.

Sa sarkan cikin jaka keda wuya sai wayennan Mutane masu kama da gumaka suka fara furta wani kalma da kaf cikin Zugar su Atif babu wanda yasan meye suke fada.....Danko bazaka iyya banbanta Kalman da Chinanci ba.

Bagaren aljanan nan kuwa tura wannan kofa tayi sa'annan tayi wani surutan tsafi dan naiman tsari kawai sai tasa kai cikin dakin...
da shigarta guri yadau haske,nan ta iyya gano cewa dakin da take ma'adanar kundine da kuma taswirori da duk jansin Littattafai.

Takasance kamar y'ar kauye yayinda ta kasance cikin wannan guri....
Sai famar kalle kalle take ta daga kai sama.....

Takun da tayi bazaikai goma ba sai taji kofan taja kanta ta rufe....
Wajen kofan kuwa wani kalma ya bayyana a jiki wanda tayi kama da karfe da yaji wuta...domin bai wani jima sosai ba kalmar ta bace wacce kalmar itace..
*MATATTARAR AJALI*


Taku take Cikin salon mamaki inda bata damu da kofan nan daya rufe a kanta ba,kawai ta kai hankalinta wajen kallekallen abubuwan mamaki.

Nan fa sai tayi arba da wani kundi a tsakiyar wannan daki wacce ita kundin a iska take yawo yayinda akayi mata ado ta musamman da ganin sa kasan bata banza bace...

Hakan ko yasa wannan aljana ta nufi wajen zuciyarta cike fal da burin dauko kundin....

Bai wuci daku ashirin bane tsakanin ta da wannan kundi kawai sai taji ta taka wani guri ya sauka kasan nan da nan ta tabbatar da akwai tarko a gurin amma Kafin ta ankare sai taji parat kibiya ya shigeta ta kafad'a ya fice ta baya....

Zubewa tayi a kasa yayinda jini ya mamaye gurin......
Nan sai wutar dake wannan guri suka soma kafewa har saida gurin ya dawo baki wuluk....

*Gaskiya banda shedar ta mutu* πŸ€”

Haka bangaren forzy da Ahmad kuma buga ihu sukayi ahhhhhhhhh yayinda suke kai wannan farmakin but tarar da gurin sukayi babu kowa nan sai suka zubi idanun juna....Hade da murmusawa.

Amma kuma yin hakan keda wuya suka kwarma bagidajiyar kara danko damin jemagu ne suka fito awannan guri....alamar makwancin sune nan.

Yayinda Ahmad ya rufe idanun sa,dan gudun kar su shigemar ido kuwa sai yayi arba da wata y'ar karamar yarinya cikin idanun nasa tana mikamar hannu alamar yazo gare ta.

Bude idanu yayi cikin sauri inda ya tarar da Forzy na sheka dariya danko ta razana matuka amma kuma sai taga bats ne.....
Shiko sam hakan bata basa dariya ba domin burinsa shine yaga wannan yarinya azahiri....but bai iyya ganin hakan ba.

"Akwai hanyar da zamu iyyabi mu fice daga wannan gurin"

"What are you talking about?"
Haka forzy ta ansa masa yayinda take ganin babu wata mafita da suke dashi wacce ya wuce su cigaba da zama a wannan guri....

"A nan gurin naga wata yarinya tana mikamin hannu tana kuma cewa nazo muje.....
Amma kuma bata fadamin inda zata kaini ba"...
Haka ya furta inda forzy tace dashi

"Ahmad wai yaushe kaga hakan?"

"Yanzun Nan"
Ansar daya bata kenan ita kuma ta sake jefo masa da wata tambayar....

"A ina, kuma tayaya?"

"Cikin kwakwalwana,kuma hakan shine kadai hanya dazamubi mu sami mafita daga Nan guri"...
Haka ya bata ansa.....

Itako ta sake da cewa
"But we are safe here"

Bai kula taba kawai ya juya ya fuskanci inda yaga wannan yarinya....
Nanfa ya sake lumshe idanu....yin hakan keda wuya sai ya sake arba da wannan yarinya...tana kuma cewa...

"Come to me.....come to me"
Cikin siririyar murya,forzy kuwa babu abinda bata fadiba wajen ganin ta dawo da tunanin Ahmad baya but inaa kwatakwata baya jin hakan....

Wannan yarinyar ko na kokarin kaiwa jikin bango yayinda take taku da baya kuma ta mika masa hannu.... bayan takai jikin bangon sai ta tsaya yayinda shi Ahmad ya nufota....

Kaiwa gurinta yayi sa'annan suka hade tafukan hannu yayinda yarinyar ke tayimar musmushi y'ar karama da ita....kuma kyakkyawa.

"Nuna mana hanyar fita".
Haka Ahmad ya furta,Kawai sai yaji forzy ta tsinkamar mari......
Bude idanunsa yayi arba da hannayensa na lumewa cikin wannan bango.....zura idanu yayi...cike da mamaki hade kuma da firgita

Ashe kuwa jawosa cikin bango take,haka forzy ta kasance tana mai zubarda kwalla tana mai cewa karsu rabata da Ahmad but ina wannan bango sai dad'a zugoshi ciki take nan sai ya sake lumshe idanu da niyyar sake magana da wannan y'a but maimakon yayi arba da kyakkyawan fuskar nata sai yayi da mugan fuskoki masu matukar tsoratarwa kuma sunkai sama da Hamsin suna rike da hannayen nasa suna kokarin jawosa ciki.

Forzy na kokarin janyesa daga jikin wannan bango sai ga wannan yarinya ta bayyana a fili tace da forzy.....

*"KI KYALESHI KIBAR GURIN NAN"*
cikin murya marar dadin ji ta furta hakan......
Biris Forzy tayi da fad'ar tata itako ta sake maimaitawa har bakin ta uku....
Kafin ta 'bace sautin muryar tako ya ratsa gurin tana mai cewa.

"Karkice manyi miki kashedi ba"......

Haka forzy taji na gani Ahmad ya nitse cikin wannan gurin....itako sai gata jikin bangon dan kuwa sun kasance a rungume suke da juna....

Zaune jikin bangon take tana mai cewa.....

"Mayyasa kuka rabani da masoyina"
Haka tayi ta nanatawa..... But then sai taga anyi mata rubutu ajikin bako da jini...

*"Leave Now"*

"Bazan taba fita ba"
Furta hakan take yayinda ranta a bace amma bata san su mutanen boye ba'a musu galaje ....

Sake rubuta mata sukayi a karo na biyu......

"Leave now....."

Amma sai ta ki cewa komi kuma taki tashi tabar guri....
Shesshekar kuka kawai take tayi.


Nan sai taga an jawo hannun ta na hagu an soma zazzana rubutu jiki yayinda naman jikinta ke tsastsagewa.....jini kuma yana kwararowa kasa.
Itako sai famar ihu take amma ina zata iyya kwato hannun nata...

Bayan an gama zana rubutun ne ta iyya karance abinda aka rubuta wacce itace.....

*Mutuwa ce makomar Ki*

Ganin haka yasa ta zura idanu cikin sauri ta d'aga ganinta izuwa jikin bangon inda taga duk rubutun da akayi naacewa tabar gurin ya dawo *DIE* Cikin tsoro ta zura idanu nan sai taji kofon wannan daki taja kanta ta rufe......

Hasken dake ciki kuma ta dauke.........yayinda itan kuma ta buga ihu
*AHHHHHHHHHHHHHHHH*πŸ€ͺπŸ€ͺ




*SORRY FOR LATE UPDATE*πŸ™πŸΌ



*THANKS FOR READING*


*COMMENT COMMENT COMMENT*
Ku kasance masu comment idan har kunason cigaba comment naku kwarin gwiwarmu,saina jiku comment more typing always.

✍🏻...........Abdul10k Naku a kullum.


πŸ’€πŸ’€πŸ’€
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
πŸ’€πŸ’€πŸ’€

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________


*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________


*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*πŸ’―βœ…
*EPISODE 0⃣6️⃣*


*"Leave Now"*

"Bazan taba fita ba"
Furta hakan take yayinda ranta a bace amma ita bata san mutanen boye ba'a yimusu galaje ....ba

Sake rubuta mata sukayi a karo na biyu......

"Leave now....."

Amma sai ta ki cewa komi kuma taki tashi tabar guri....
Shesshekar kuka kawai take tayi.


Nan sai taga an jawo hannun ta na hagu an soma zazzana rubutu jiki yayinda naman jikinta ke tsastsagewa.....jini kuma yana kwararowa kasa.
Itako sai famar ihu take amma ina zata iyya kwato hannun nata...

Bayan an gama zana rubutun ne ta iyya karance abinda aka rubuta wacce itace.....

*Mutuwa ce makomar Ki*

Ganin haka yasa ta zura idanu cikin sauri ta d'aga ganinta izuwa jikin bangon inda taga duk rubutun da akayi naacewa tabar gurin ya dawo *DIE* Cikin tsoro ta zura idanu nan sai taji kofon wannan daki taja kanta ta rufe......

Hasken dake ciki kuma ta dauke.........yayinda itan kuma ta buga ihu
*AHHHHHHHHHHHHHHHH*πŸ€ͺπŸ€ͺ

_*6DAYS EARLIER*_
_*KWANAKI SHIDA DA SUKA GABATA*_

Tsakiyar farfajiyar Ma'aikata zugar Mu'azz ne ke tafe yayin da suke daukar feelings....Hade da batsewa da nuna issa,basuko tsaya ko Ina ba Sai ofishin shugabar wannan ma'aikatar....
Shigarsu ko suka tsaya cirkwa cikwar Kamar wasu masu tallar magani....
Ganin su cikin wanna yanayi yasa shugabar tace dasu....

"Da'alamun Kunga sunayen ku a Marne ko....?Tafiyar zatayi taking place Next week da fatan bazaku bamu matsala ba....
Domin Munyi tajin kofare korafe tuntuni daga gareku tsakanin ku da dayar kungiyar da muka hada ku wannan Tafiya."

Gajeriyar murmushi Mu'azz yayi hade da cewa....
"Ko kadan Baza'ayi hakan ba Inshallah....."
Ma'anar sako shine Baza'a Sami matsala daga garesu ba.

Babu Bata lokaci suka Sa kai suka fice daga ofishin izuwa ofishin su wacce take makotaka data su *Atif*
A daidai wannan lokacin ko Atif da sauran mabiyan sa suna wani project Mai matukar anfani....

Amma Bayan sun gane hakan sai suka naimi hanyar da zasu durkushe wannan harkallah tasu....haka ko sukayi nasarar lalata komi ta sanadiyar hanasu sakat da saukin presentation nasu...dariyan su Atif suka tayi a karshe yayinda suka gane aikin ta lalace Kuma shugaban gurin na musu surutu......Hade da barazanar Basu suspended.πŸ™„


*CIGABAN LABARI*


Cikin Kasala Take bude idanu yayinda hasken Rana ta haskake idanun Nata....
Cikin sauri tasa hannu ta Kare idanun Nata daga wannan haske....but then Bayan Tayi hakan ne tukun ta gane inda take,domin kuwa ido biyu Tayi da blue sky yayi da tsintsaye ke ta shawagi a sararin samaniya ga Kuma iska Mai daddad'ar yanayi na kadawa.....

Ido biyu tare da koren ganyaye ta ko'ina, Gajeriyar murmushi tayi hade da Kuma yunkurawa ta mike tsaye,nan Sai ta duba kafafun ta da Kuma kayan dake Jikin ta.....
Sake murmushi tayi a karau na biyu Bayan taga komi na jikinta normal...nan tayi Yar Gajeriyar shewa hade da tsalle fuskarta na cike da annashuwa but then ta tuno dalilin suman Nata......nan da nan annashuwan dake fuskarta ta koma bacin Rai Danko hada fuska tayi.

*Idan Kuna biye da wannan labarin sau da kafa zakusan wa nake nufi*πŸ™„πŸ˜œ
Ba kowa bace wannan illa aljanan nan Wanda ta tsinci kanta a *MATATTARAR AJALI* wato ma'ajiyar muhimman taswirori da Kuma kunduna.....bayan ta Sami Rauni a wannan gurin ta sanadiyar taka tarkon datayi Kuma ta Fadi kasa ta sume saita tsinci kanta anan Gurin,Mai abin al'ajabi.

Cike da mamaki take yayi data tuno abinda ya faru a baya,nan Sai ta Soma kokonto kodai mutuwane tayi....?
Sake bawa kanta ansa tayi cewa"ai idan mutuwace bazana iyya anfani da baiwar tawa ba...but I still feeling I'm normal"....

Sa'anan ta sake Yiwa kanta tambaya a karo na biyu .......Kodai mafarki nake ne??
Amma a wannan karo maimakon ta bawa kanta ansa Sai tayi anfani da faratunta wajen yamusar kafadar ta Sai taga jini na kwararowa....

Nan ta sake tsalle hade da shewa Tana fadin na *tsira* _I'm safe_ daga wannan had'ari Dana shige ciki....
Bayan ta gama fadin haka Sai ta wani tsunkuya kasa ta wani yiwa gadon Bayan ta doroo....
Nan Sai Fuka fukan ta suka bayyana cikin abinda bai wuce Yan daki ku ba.......
Nanfa ta tashi sama ta Soma shawagi a sararin samaniya...πŸ™„πŸ˜²Wai shin Ta tsirane??Hmm😏 *who knows*

Al'amari su Atif da Mu'azz da sauran tawagar tasu ko tsayen suke yayin da wayen nan sangaranrun mutane na anbata... Wani batu Cikin wata yare da Basu taba jiyowa ba....
Amma da dukkan alamu furucin mutuwa suke Danko bbu abinda ya fimusu Dadin fada a wannan Guri Data wuce ta mutuwa....

Samra cewa tayi "Maiyake Shirin faruwa da mune??"
Kowa dake wannan gurin yaji wannan tambaya Amma Kuma sun kasance Basu da ansar da zasu Bata.....

Nanfa Sai sukayi yunkurin Guduwa but kwatsam Sai suka ga daya da Cikin sangaranrun mutanen nan ya sauko daga kan layin da suke ya shige gaban su...

Nanko suka take biriki shiko Cikin zafin nama ya Soma karasowa gunsu.....
Da ganin haka suka juwa da nufin komawa baya,shiko Cikin abinda bai wuci dakika guda ba Sai gashi a tsakiyar tawagar tasu....

Da hannu Daya ya shako wuyar Harun yayi jifa Dashi gefe guda haka zalika Ali.... samra ko ya sharara mata Tafi....
Da Dukkannin tunani wannan abin baso jimusu ciwo yayi ba Dan Bayan ya gama jifan dasu Sai ya tsaya gaban Nina ya kura mata ido....Yana wanu gwauron Nishi....

*Nina* a rikice take Sai famar karkarwar tsiya take yayinda wannan halitta na tunkarar ta,Bayan ya karasa wajen ta ya dago hannu zai taba fuskar ta kawai Sai yaji anhausa da duka dukan nin tawagar haka sukayi kaca kaca dashi....
Amma Cikin dakiku dakan ya sake lillikewa ya Dawo normal....
Murmushi yayi sa'anan ya furta *Let Fight*

Haka Atif da sauran abokan tafiyan nasa ke tsaye...
Sai suka Soma juyo sauran sangaranrun mutanen na maimaita fadin Dan uwan nasu wato *let's fight*

Haka duk suka sassauka suka yukura kansu....inda *Nina* Tayi wani Dan karan Ihu,Wanda da yin wannan ihu Sai wata haske ta tashi a kansu yadda kasan spark na utar lantarki haka ta tashi a kansu....Domin kuwa tuntuni da ganin yadda sangaranrun mutanen nan na furta let's fight suka Marne Guri guda.

Wannan wutar daukewa tayi daidai da bacewar tawagar....
Inda sangaranrun mutanen nan da sukayi caa gurin Sai suka Tara Babu kowa,nan fa sukayi takaici hade da juyawa izuwa wajen wannan da Nina ta cire sarka a wuyan shi....

Yimasa zobe sukayi yayinda suka daddafe shi da hannu Wanda Kuma Bayi da damar dafashi zai dafa Wanda ke gabanshi haka sukayi inda suka taru Guri guda....

Yayinda shi Wanda aka cire sarkar a wuyan sa na kokarin tarwatsewa....
Haka suka Soma wasu surutai yayinda duk jikinsu ke bada haske....
Bayan yin hadan da sukayi nadan wasu dakiku sai suka dago fuskokin su sama hade da kwarma ihu da alamar sunajin radadin yin hakan.....

Bayan sunyi hakanne Sai Mayafan dake fuskokin su suka zuzzube kasa.....
Nanne Muninsu ta bayyana a sararin,Domin ko da makaranci zaiyi ido hudu da fuskar wannan halitta,toh da zai iyya Suma dan tsantsar Muni da Kuma firgita.........

*Bangaren wannan Aljana* kuwa Bayan Tayi ta shawagi a sararin samaniya Sai tayi niyar nitsewa Cikin gajimare.... _but guess what happened_
Ji tayi,tayi karo da rufin daki Wanda Kuma kaurinta Kamar ta dutse....ji kawai ta sauka kasa yadda kasan laida haka ta Fadi kasa.....

Nanfa ta daga idanun ta karewa wannan gurin kallo....yin hakan keda wuya sai wannan Guri ta Soma durkakewa Tana komawa ainihin yadda take da alamun wani salone ta sirihi ta fada ciki.....
Cikin abinda bai wuci dakika guda ba ta tsinci kanta a jerin wannan kabot kabot na taswirori....

Nan Sai tayi sukum ta kasa cewa komi, matukar tsora Tayi a zuci...har idanun ta ya cike da kwalla....saura kiris ya zubo but then Sai taji ihu mutum ba kowa ne ya Fara zuwa mata a kwakwalwa ba illa Atif......

Sai tayi wani magana a kasar zuciyar ta..... "Idan ni Aljana ina da kuka inaga Dan'adam Mai Rauni,yakama ta nayi iyyakan kokarina wajen kareshi domin na sakashi Cikin wannan matsifa"....

Wannan ihu data jiyo kuwa Bata kowa bace illa ta *Forzy* dake gudu Cikin high speed.....
Yayin da wata Bakar hayaki Mai duhu ke biye da ita abaya...
Wannan Bakar hayakiko ta kasance Koda karfene ta ratsa wannan karfe saita narke bare itatuwa ko Kuma Naman mutum....

Aljanan ko ganin ta Cikin wannan hali yasa taa bude fuka fukan ta tayi cep da ita suka tashi sama yayin da wannan hayakin ta mamaye ilahirin Gurin.... Wato Cikin Ma'ajiyar.

Forzy Lumshe idanu tayi yayinda wannan Aljana ta fire da ita Amma daga bisani ta bude idanun Cikin yanayin tsoro... Bayan Ta hada ido da Aljanan ko Sai ta kwarma bagidajiyar ihu hade da sumewa....
Yin Hakanne yasa Tayiwa Aljanan nawi ta kasa Rike ta dako Tana fama da Raunin dake kafadar ta....

Haka ta sadaukar suka fada Cikin wannan hayaki.....
Yayin fadowar suko Sai ta rungume Forzy hade da yimata Makari da Fukafukan nata....saukowa suke Cikin high speed hade da bagidajiyar ihu Mai Kada Hanjin Cikin Dan'adam.

Al'amarin Su Nina Ko baiyana sukayi wajen wata Gabjejiyar kofa yayin da sukayi arba da Wani Dan gini da akayi a gaban Kofan Mai kama da *standard table* saman sako shatin tafukan Hannu ne.....

Cikin mamaki suka gubi juna hade da karasawa wajen Kofan da niyar bude wa but Sai sukaga Tana da banbanci da wayenda suka baro abaya.....
Danko wayenda suka wuce a baya daga sun taba Jikin kofar saita bude kanta Amma wannan maimakon ta bude Sai ta tsaya kallon su.

Bayan sungane basuda karfin bude wannan kofa Sai suka juyo hade da gamawa gurin nan da suke kallo....suka duba lungu da sako ba tare da sun motsaba illa jujjuya idanu dasukayi tayi.

Hanyoyi sukayi abar dasu har uku wance suke Kama da Cikin kogo....
A Cikin kowace hanya dayako bala'in da suka baro a bayane ke zuwan musu ta ciki......

Hanyar farko Ruwan utane ke zuwa ta ciki yayin da take anbaliya.....
Ta biyun ko wayennan halittu masu Kama da kadangaru suke zuwa ta ciki....
Last one ko wannan Bakar hayaki Mai narkar da duwasu,itatuwa dadai sauransu ne...ke zuwa ta ciki.....

Ganin haka yasa suka buga ihu hade da rugawa izuwa Jikin kofar suna Mai bugawa hade da raukon kofar ta bude kanta.....

#Nina ko tsayen take Sai ta Soma jiyo wata siririyar murya nayi Mata Rad'a Cikin kunnuwan ta.....
Abinda take jiyowa ko shine.... *The Key* !! *Makullan* suna ina find it..... find the key.....

Haka take jiyowa Cikin kunnuwan nata,haka ta saki jiki ta karasa wajen wannan Abin Mai dauke da shatin hannun mutum a sama.....

Bayan ta haye Guri Sai tayi murmushi hade da cewa.... "Tafukan Hannu sune makullan Kofan nan I'm sure"
Nina batasan yayinda ta furta hakan Cikin karaba..... sauran abokan tafiyan nata dajiyo haka suka juyo izuwa gareta Atif yayi furucin "What do you mean??"

Maimakon ta basa ansa ko Sai ta Daura tafukan Hannu Nata kan wannan shatii.....nan da nan gurin ta nitse da tafukan hannayen Nata,iyya wuyan hannu....ne ta nitse.

Ganin haka yasa suka cika da mamaki Kamar suna da tabbaci hasashen Nina gaskia ce.....
Ji sukayi Kofan na kokarin bude kanta haka suka juya suka kura masa ido harta gama budewa....

Aikuwa kan Kace Kobo tuni sun shege ciki..... Juyawar dasukayi suna murna Sai suka tarar Nina Bata Cikin sahun nasu....
Cikin mamaki suka yiwa kawunan su tambaya ina Nina... Juyawar da zasuyi Sai sukayi arba da ita tsayen hallau wannan Abin dai na rike da hannun Nata...

Mu'azz yukurin Zuwa yayi Amma Bayan Atif yayi arba da wayennan muggan abubuwa dake kokarin karasowa garesu Kuma sunyi kusanci da ita nina sosai ta yadda Babu Wanda zaije gurin ya iyya ceko rayuwan ta su dawo tare... batare da muggan abubuwan sunyi kacala dasu ba.
Yasa Atif yaja Kofan da karfin tsiya ya rufeta..... wannan dalili yasa Atif yaja kofar ya rufe ba tare da Mu'azz ya fita domin ceto Nina ba.πŸ™„


*TIRKASHI ANCE LAIFIN DADI KAREWA.*

*FANZ INA MAI MIKO SAKON GAISUWA GARE KU HADE DA BAKU HAKURI AKAN LATE UPDATE DANAYI NA WASU MONTHS INA FATAN MY FOLLOWERS KUNSAN DALILINA NA TSAYAWAN.....DAN HAKA BA SAINA SAKE DOGON BAYANI BA NA GODE DA SOYAYYAR KU FANS*

MUHADU A NEXT PAGE AMMA KU SANI COMMENT NAKE BUKATA MASU ZAFI DAN SAMUN KWARIN GWIWA😜

πŸ’€πŸ’€πŸ’€
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
πŸ’€πŸ’€πŸ’€

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________


*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________


*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*πŸ’―βœ…
*EPISODE 0⃣7️⃣*


"Forzy!! Forzy!! Forzy!!"....

Cikin Sanyayyiyar murya takejiyo hakan,muryar maishi ko na Fita Cikin Rad'a alamar Mai Kiran wannan suna bai bukatar wani ko wata na daban ya jiyo hakan....Forzy ko cikin salon kasala ta bude idanun.....nata inda tayi Arba da abin daya matukar bata mamaki wanda wannan abun ko shine,hada Ido tayi da Ahmed a zaune gefen ta wanda shine Mai Kiran nan nata,Cikin farin ciki hade da murna ta yunkura hade da rungume sa.... zubar kwalla ta soma Tana mai cewa.

"Banyi Zaton Zan sake saa kwayan idona a naka ba *Ahmed* ,A tunani na Narasa Kane Har Abada.....Amma mayyasa ka zabi ka kyaleni a baya? Mai yasa kakijin shawarar Dana Baka??,Koda shike mubar wannan magana a gefe guda tunda gashi kaddara ta sake hadamu,Dan haka Ahmed Dan Allah karka sake barina Cikin kadaici.... domin kuwa Nayi kewarka sosai."

Hakan ta furta yayin da suke a rungumen da juna....Tana Kuma shesshekar kuka
*Guess what* Budar bakin Ahmed ko yace da ita.

"Yanzu atunanin ki tare muke ne Forzy??"
Tambayar Daya matukar razana Forzy Kenan hade da dagula tunanin ta,kasa sakar jinin nasa tayi danko still rungumen suke da juna...........

Zuciyar tako bugun uku uku ta Soma,Cikin yanayin tsoro ta saukar da idanun ta kan gadon Bayan Ahmed....
Cikashi tayi Cikin sauri hade dajan jikinta gefe guda Bayan tayi arba da gadon Bayan nasa Wanda jinine ke zubowa ta sanadiyar manya manyar Raunin dake gadon Bayan nasa,Wanda suka Kuma rube

Please Login or Register in order to submit comment