Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wacce bala'i ne yanzun muke kokarin Fadawa ciki?, gaskiya ya kamata mu gaggauta komawa baya."
Haka shima ya furta a kasar Ransa.

Daga inda Forzy da Noor ke tsaye suna iyya jiyo motsin mutum ta ruwan yayinda Forzy ta gano haka sai tayi saurin cewa..

"Da wasu anan gurin."
Fadar haka Forzy tayi inda Noor tayi sauri Bata ansar cewa.

"Haka ne,I can smell Humans watakila abokan tafiyar kine."

Aiko da jiyo haka sai tayi murmushi Hadi da yunkurin zuwa gurin Amma sai Noor ta riko hannunta sa'annan tace da ita.

"Gudun Fadawa matsifa,bai zama lailai sai munje gurin ba Zan iyya Gwada warware wannan kafin da Karfin Baiwata,na Gwada yaye wannan Hazo Dan mu hanko abinda ke nesa."

"But.." haka Forzy ta soma furtawa Amma dashike tasan abinda take niyar fada sai ta tari bakinta da cewa.

"Karkiyi kokarin dakatar Dani domin hakan shine mafita."

Shiru Forzy tayi wacce hakan ne ya bawa Noor karfin gwiwan amfani da baiwarta,Aiko hada tafin hannayen ta tayi inda ta soma surutan tsafi, Bayan ta karashe surutan nata ta raba tafin hannayen nata.

Aiko Nan da Nan sai wannan Hazo ta yaye gurin tadau haske,ganin gurin yayi haske yasa Forzy murmushi yayinda Noor ko d'igon jini ya fado daga hancin ta,ya Fadi Cikin ruwan.
Tana cikin yanayin na kasala da Kuma Jin jiri,kwatsam sai tayi arba da jinin dake kan ruwan na rubuta Mata wasu harrufa wacce sune...

"Idan Kika kasance kina anfani da baiwar da kike gadara da ita,toh wata Rana ba hancinki ne kadai zata zubar da jini ba har kwakwalwarki saita buga."

Dafa goshi tayi yayinda jirin ke kokarin daukan ranta Danko idanun ta sun kusan rufewa dan zazzafar jirin dake damunta.

Forzy ko ido hudu tayi da Tina inda tayi shewa Hadi da juyawa tana furta cewa.

"Wallahi sune,abokan ta.......
Aiko shiru tayi Bata karashe maganar nata ba Domin ta tarar da Babu kowa a tsaye inda Noor take dazun, ma'ana Bata sami Noor din ba.

"Noor! Noor! Noor!!!."
Haka Forzy ke furtawa yayinda take waige waige.
Tina ko kwarma ihu tayi yayin Kiran sunan Forzy Aiko karau daya sauran tawagar suka daga idanun su inda sukayi arba da Forzy,dukda cewa abin farin cikine haduwarta da sauran y'an uwan nata Amma sai ta kasance cikin takaicin rasa Noor datayi.


a zahirance Kuma Noor ta kasance tana tsaye gefenta yayinda take ta Kiran sunan ta harma tana cewa..
"Forzy gani Nan fa banje ko Ina ba" ,haka tayi ta furtawa Amma ganin Forzy ta wuce ta jikintane ya tabbatar Mata dacewa Forzy Bata iyya ganin ta.

Samra fuskar ta cike da annashuwa yayinda tayi tauzali da Forzy Domin kuwa Bayan kyewarta da suka tayi,sunji takaici da suka gagara tallafa Mata waccen karon Kuma hakan duk suka kasance a gurin,Harun ko ganin suna kokarin zuwa wajenta ne yasa shi cire daya daga cikin furannin dake gurin,ya murkushe ta Hadi da yasar da ita cikin ruwan.

Bayan ya gama wannan aika aikar ko ya daga kallonsa nanfa sai ya tarar da Al-Hussien na kallon sa..Basarwa yayi ya maida ganinsa gefe guda Hadi da gofe hannayensa

Aiko Cikin sauri su Atif sukaso su kaiga Forzy Domin kuwa guduwa bazatayo ba a cikin ruwa Amma sai suka gagara yin hakan Danko cire furen da Harun yayi shine sababin shigarsu cikin matsifar da basuyi zaton ba..

Aiko Cikin kankanin lokaci gurin ta sake hadewa Hazo ta mamaye ko'ina sa'annan saman gurin tayi baki Kai kace hadiri Danko har walkiya na faruwa a saman gurin...
Komi na gurin ya sauya cikin kankanin lokaci yayinda Samra da saura mutane suka tsaya domin kuwa sun daina ganin Forzy..

Juyawar da zatayi Dan sanar da sauran hakan ko sai ta tarar da Babu kowa aikuwa cikin sauri ta Soma furta cewa.

"Guys! Guys guys!!!"
Aiko abinda Bata sani ba shine dukkan ninsu a cikin wannan Hali suka kasance domin Babu wani daga cikinsu daya kasance tare yake da mutum kowa a gurin daya ya kasance.

Atif shima ya kasance sai kiraye kirayen sunayensu yake haka zalika mu'azz da sauran abokan tafiyar tasu....

Dukda cewar ba wani nitsa sukayi da junan suba Amma wanna hudu da kuwa tsawa Hadi da walkiyar ta hanasu ganin ko jiyo muryar y'an uwan su.

"Forzy Ina tare dake,gani Nan kusa dake Forzy."
Jiyo haka da Forzy tayi yasa bakin cikinta ya gushe Nan da Nan fuskar ya cike da annashuwa,wata y'ar murmushi ta saki Hadi da Soma tafiya da niyar takaiga Noor din.

Haka kowace bangaren suka Sami abokan tafiyar kamar yadda ya faru da Forzy haka ya faru dasu Kuma kowa na kokarin zuwa ga mutanen da suka tarar.

Atif ko Mu'azz ya ganin hakan ya Soma tafiya cikin sauri Dan ya kaiga iso sa, Samra ko Tina ta gani tare da muzzaffar...

Al'amarin Forzy ko sa hannu ta tayi cikin na Noor Nan sai wata ciyawa ya rike Mata kaya ta juya da niyar cirewa aikuwa ta cikin ruwan tayi arba da hoton Noor na kokarin fahimtar da ita cewa waccen din ba ita bace..

Ganin hoton Noor din ta cikin ruwanne yasa ranta yayi matukar tsinkewa domin kuwa da ganin fuskar wannan ta cikin ruwan tasan waccen data kasance a boyen itace Noor din asali toh Amma wacece wannan da ta riko hannun ta..Abinda take da burin sani kenan Aiko d'angowa tayi inda ta hada Ido da Noor din dake rike da hannun nata.

Hadewar idanunsu keda wuya taso su rungume juna Amma Forzy taki yin hakan sai wannan dake cikin suffar Noor ta rikede ta dawo mermaidπŸ§œβ™€οΈπŸ§œβ™€οΈ aikuwa rudewa Forzy tayi ta kwarma bagidajiyar ihu wacce kowannen su sai da ya jiyo wannan ihu na Forzy.

Kama daga kan Atif,samra,Simon mu'azz da sauran abokan tafiyar nata ko suka jiyo haka cikin kankanin lokaci mu'azz da ke tare da Atif shima ya rikide ya dawo mermaidπŸ§œβ™€οΈπŸ§œβ™€οΈ haka zalika Tina da muzzaffar wanda Samra ta hadu da suma suka rikide suka koma wannan suffar.

Aikuwa cikin mamaki dukkan ninsu suka zura idanu domin kuwa y'an matan kan ruwan sun kasance suna da manya hakwara...
Mufydah ko data kasance rungume take da daya daga cikin Wayennan halittu a tunaninta daya daga cikin abokan tafiyar na tane,ihun Forzy nakaiwa garesu ko sai wannan aba ta buga Mata hakwara a wuya Aiko tuni jini ya Soma kwararowa daga wuyarta..

Sai famar Shure Shure take ita Mufydah kamar wata karsanar da aka da'ba ma wuka a wuya,nanfa sai taji an duki mermaid din da karfin tsiya Nan ta cika Mata wuya ta fada cikin ruwan ta gudu...
Aiko ba kowa bane Wanda ya cece ta illa Harun.

Forzy ko juya bindi abar tayi ta bugeta dashi Inda ta Fadi kusa da Atif Amma sai suka kasa ganin juna...
Ganin abin na karasowa wajenta da karfin tsiyako yasa Noor ta shige gaba dukda tasan bazata iyya kareta daga hakan ba..

Dukkan ninsu fa dakyar sukasha a hannun wayennan halittu Amma bayan duk sun taru guri guda sai wayennan halittu suka kasa karasawa garesu..

Sa'annan Kuma sukaki kai mata Forzy farmaki dukda ta kasance tsaye take ita daya....


Shiru kakeji Babu mai motsi Dan zunzurutun tsoro da suke...
Bayan Shirun Nan ko sai suka Soma wata irin Kara Mai kamadata 🐝 kudan zuma.

"Car'uba."
Abinda ya fara fitowa daga bakin Tina kena inda Mufydah ta Soma cewa.

"I don't want to die"

Fadar hakan keda wuya sai Tina ta jiyo ta kalle ta da niyar tace da ita wani Abu but then kawai sai taji sulub an janye Tina ta saka kasar Ruwan.

Dukda katuwar rauni dake wuyarta tako bai Hana ta kwarma bagidajiyar ihu ba....

Aiko yin hakan keda wuya sai taron kudan zuma suka sauko akan Ali yadda kasan taron safa da marwa haka sukayi masa Babu abinda suka Bari a jikin sa,har firewa sukayi dashi suna ta kaimasa farmaki.

Aiko da zaka d'aga idanu ka kalli sararin samaniya tofa ko haske kadan bazaka gani ba Dan yawan wayennan zuma dake addabarsu.

bayan bala'in kud'an zuman Nanfa sai wayennan Fararen furanni suka Soma mikewa suna Kai Sara kamar macizai.

Aiko gurin ya dawo tambar filin yaki domin kowa na kare kansa al'amarin Tina ko Damin furanni ne suka nannade ta itama Babu abinda zaka iyya gani a sassar jikinta...πŸ‰πŸ§œβ™€οΈπŸhaka ta kasance a kasan ruwan na iyya lokaci da suka dauka suka wannan fada.

Forzy ko takasance karfinta yasha Dan ko furanni sun nannade hannayen ta hagu da kuma Dama, sa'annan Kuma zuman sunayowa kanta ganin haka da Noor tayi yasa ta shige gabanta tayi kururuwa.

Aiko sai ta baiyana cikin haske Yadda kasan Bob na utar lantarki tana Mai shiki,abinda ta fada ko shine ki Kulla da kanki Y'ar uwa..
Nanfa sai hasken nata yafi kaifin ganin Forzy ta wannan dalilin ne yasa ta lumshe Idanu Noor ko tarwatsewa tayi yayinda hasken nata ya tsistsinke furannin Hadi da tarwatsa taron kudan zuman sa'annan Kuma duhun gurin ta yaye...

Cikin abinda bai wuci dakiku uku ba ruwan dake gurin ta tsotse guri yayi fili Aiko saiga Ali tare da Tina na kwance Rai a hannun Allah.
Tina tayi kore Shar kaikace green girl🧟hatta gashin kanta ya cenza Kama ganin haka yasa Samra ta soma zubar hawaye...

Ali shiko jikinsa ta dawo tamkar Rariya Dan yawan hujin dake jikinsa ga Kuma rasa ganin da yayi domin Kudan zuman sun rabasa da ganin sa...

Mufydah ko Nan take zaune ta rike wuyan nata da hannu biyu, muzzaffar ko ganin haka yasashi kama bakin rigarsa ya yage cikin sauri ya d'aurewa Mufydah wuyarta,domin Dakar da kwararowar jini.

"Wannan bala'i da meye tayi kama."
Fadar Samra inda Simon ya Mike hade da takawa izuwa inda Harun ke tsaye,bayan sun hada Idanu ko ya wanka masa tafi.

"Kai ka haddasa hakan,kasan komi Kai kake kokarin cutar damu."
Hakan Simon ke furtawa yayinda kwalla ke zubo masa a fuska.

Ganin haka yasa Mu'azz da Kuma Atif sukayi saurin shigewa tsakanin su,suna Kuma kokarin basa hakuri Aiko dajin kallamar hakuri yayin ihu yiyin fadar abarsa ya koyawa Harun din hankali.

Karar ya ratsa gurin har ya kaiga inda Forzy ke shesshekar kuka tana Kuma rike da Noor a hannu..
Bata iyya cewa komi ba Domin tana cikin yanayine na babbar Rashi..

Tofa *Wasa farin girki* Ni a tuna Nina komi yazo karshe Amma ko wannan shine soma tabi Danko bayan wasu Dakiku sai gurin tadau girgiza yayinda kasar ke tsagewa dad'in dad'awa Kuma saiga wayennan kwarangwal da suka baro a baya sunsa Kai...

Ganin haka yasa Samra Sallati Aiko jiyo haka da Mufydah tayi yasa ta Mike tsaye,arba tayi da taron korangwal dinnan Aiko batasan lokacin data soma kuka ba.

Amma kafin su karaso garesu sai wannan guri ta saura kasa dasu Nan take gurin yayi Rami Kai kace rijiya ce,yayin saukar su ko sai da suka ciyu Danko sunsha azabebbiyar wahala domin duwasu na Fado Musa aka.

Hakan wannan guri ta rabasu da Forzy domin Basu sake samun damar ganin taba.

Aiko nitsewar da gurin yayi dasu ba ko'ina ya kaisu ba illa inda suke da burin zuwa wato inda wannan taswirar keson kaisu..

Dukkan ninsu suna a gurin daya daga su har wayenda suka jikkatan wato Ali da Tina,Wanda mu'azz da Atif ne Basu kulawa.


Ganin gurin yasa suka Mike tsaye dashike da kwai rata tsakanin su sai it's,sai suka daga ganinsu sama suna kannon ikon Allah domin Basu taba ganin irin wannan abar ba.

Domin kuwa gadar da suka hango zakace *door of heaven* ne Danko wata doguwar gata me wacce Bata da madafa ga Kuma tsayi Danko da za'a daura wani a karshen gadan ta sama da zai kalli mutanen kasan gurin tamkar kiyashi,Dan zunzurutun tsayin wannan gada.

Gadar ta somane daga inda suke tsaye, matattakalu ne aka jera har izuwa karshen gurin,Kuma Babu abinda ya tokare ta atsakiya.

Aiko ganin hakan yasa Samra tasa Hannu ta Ciro taswirar inda taga taswirar na tabbatar Mata da Nanne gurin da suke naima,Nan sai tayi murmushi Hadi da Soma taku Aiko step biyu da tayi sai wata katuwar keji ta fado kan sauran tawagar nata ta kulle su a ciki.

Wanda wannan girman kejin da Kuma nawinta sai samudawa ne zasu iyya d'aga ta,da jiyo karar fadowar wannan abinko tajuya da niyar ganin mai ke faruwa Amma kawai sai ta jita a sume Dan ko naushi Tasha wacce ya sumar da ita,Karo daya.

Bayan ta Fadi kasan ko aka Ciro taswirar dake hannun ta.


_*TIRKASHI NA ZAUNE BAIGA GARI BA*_

*_Mu Hadu a Episode 13_*

_@Abdul Alhaji Musa *Return*_


πŸ’€πŸ’€πŸ’€
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
πŸ’€πŸ’€πŸ’€

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________


*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________


*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*



*FREE BOOK*πŸ’―βœ…
*TRAILER EPISODE 13*



*_UPCOMING EPISODE OF KOFAR AJALI_*


"This is the only way out, and it's made for one person only... so Taya kuke tsammanin Zan tsaya kallo har na hallaka kaina."
Aiko bayan fadar hakan ya kyalkyalewa da dariya sa'annan ya cidaba da cewa.

"Wannan hanyace da aika yita Dan mutum daya Kuma wannan mutumin ba kowa bane illa ni."

πŸ‰πŸ¦‡πŸ§Ÿ
πŸ‰πŸ¦‡πŸ§Ÿ
πŸ‰πŸ¦‡πŸ§Ÿ

"It's all your fault Atif."
Fadar Mu'azz

"Why are you blaming me?, bayan a idon kowa akayi haka."
Ansar da ya bayar kenan

Inda Samra ta furta cewa....

"Yeah laifin Kane Atif,idan da badan Kai ba da duk haka bazata faru ba,And now komi ya tabarbare."

"This is the final, sa'annan ita ake Kira da Hard way and the only way, wannan Guri tayi gaskiya duk Wanda ya shigeta ba lallai bane ya fita."

"Hakane sister Amma Ina ganin na Samo Mana mafita."

Cikin bacin Rai suke wannan tattaunawar............


*EPISODE 13 ZATA ZO MUKU RANAR JUMMA'A DA MISALIN KARFE TAKWAS NA DARE KUDAI KU KASANCE DA NI DOMIN WARWARE KILLIN.*



πŸ’€πŸ’€πŸ’€
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
πŸ’€πŸ’€πŸ’€

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________


*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________


*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*



*FREE BOOK*πŸ’―βœ…
* EPISODE 1️⃣3️⃣*
_FINAL EPISODE_
πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š




Cikin Kasala Samra ta soma bude Idanu,inda ta tarar da an daure Mata hannaye jikin Kejin da su Atif suka kasance a ciki,Aiko sai data duba ko'ina dake gurin kafin ta Ankare hannayen nata a daure.
Nanfa ta soma kokarin kunce hannayen nata daga jikin karfe but sai ta Soma jiyo tafi daga cen nesa shiru tayi tana sauraron abinda zai biyo Bayan wannan tafi,kalmar da mai wannan tafin keyi ne ya ratsa ilahirin guri wadda wannan kalma ko itace *well well well*

Cikin kasaita da nuna kwaraiwa wannan Mai tafin ke karasowa gare ta,Aiko sai daya baiyana gabanta be ta shige mamaki ba iyaka Hadi da wangale baki tana kallon sa.

"Harun?!!"
Abinda ya fara fitowa daga bakin Samra Kennan inda Harun din ya Bata ansar cewa

"Yeah it's me."

Kasa cewa komi Samra tayi tana ta iy'ina kamar dacen haka take magana,Aiko ganin Harun na rike da taswirar a hannu ne ya tabbatar Mata shine wanda ya buga mata naushi ta suma,Kuma shine Mai alhakin daure Mata hannaye.

"What are you doing Harun,Mai yasa kake yin hakan?."

Gajeriyar murmushi yayi Hadi da cewa..

"Sarauniyar Nuna kulawa ga wasu,yau Kuma bazaki duba halin da y'an uwan naki suke ciki ba kenan."
Haka ya furta cikin kasaita Hadi da yimata nuni da yatsa bayanta.

Zura idanu Samra tayi Hadi da waigawa cikin sauri,inda tayi arba da sauran abokan tafiyar nata na kokarin bawa Tina da Ali tallafi Hadi Kuma da Karin wani kwance gefe guda Yana Shure Shure..mutuwa

Samra na iyya kokarin ta wajen ganin fuskar wannan mai Shure shuren Amma Ina hakan baiyuba,tana kan hakan kuwa sai ta jiyo muryar Harun na cewa.

"Karki wahalar da kanki wajen naiman ganin fuskar wannan,Zan sanar dake ko waye wannan."

Jiyo hakan yasa Samra ta juyo cikin 'bacin Rai yayinda ta hade fuska idanuwanta jajir.

"Harun what got into You?."
Haka ta furta yayinda ta kasance cikin bacin Rai shiko ya sake cewa da ita.

"Ah Ah ya hakan? Kin fara nuna tausayi tun kafin na sanar miki cewa nine silar shigarsa wannan halin?."

Da jiyo hakan ta zuwa idanu,shi Kuma kyalkyale dariya hadi cewa.

"Kai ka haddasa hakan,kasan komi Kai kake kokarin cutar damu Harun,shin Zaki iyya Tino Wanda ya furta hakan bayan ya wanka min tafi idan Zaki iyya tunawa to shine wancen dake gabar mutuwa."

Sauke Idanu Samra tayi inda ta tuno lokacinda suka kasance cikin ruwan Nan dake kwance,hala lokacin da suke cacan baki...
Aiko bayan tayi hakan sai ta zura idanu Hadi ta furta cewar

"It must be him,Simon."


"This is the only way out Samra, and it's made for one person only... so Taya kuke tsammanin Zan tsaya kallo har na hallaka kaina."
Aiko bayan fadar hakan ya kyalkyalewa da dariya sa'annan ya cidaba da cewa.

"Wannan hanyace da aika yita Dan mutum daya Kuma wannan mutumin ba kowa bane illa ni."



_*Readers Bari Mu dawo baya da labarin*_



_Gwabzawar da akayi tsakanin Scopions da Jemagu_ ne Yasa Tawagar tasu ta tsira daga bala'i Scopions din but duk da hakan a guje suka shige kofarnan da suka bude ta da Takubba dake da Harafin Mutuwa a jiki.

Aiko da shigarsu kofar taja kanta ta rufe.....Duhu kake iyya gani ta ko'ina
Kasancewar su a wannan guri tayi daidai da kasance a duniyar Mars ba tare da abin tallafawa gurin Nunfashi ba,domin da shigarsu kofar suka sume,Tsawon lokaci sukayi a sumen kafin suka dawo bacci.


"Harun! Harun! Harun!."
Kusa da kunnuwarsa yake jiyo hakan,Aiko lullukawa cikin duniyar mafarki a yayinda kake jiyo sauti a kunnuwa ka abune Mai sauki..
Nanfa sai ya fada duniyar mafarki yayinda yayi mafarkin Mahaifiyarsa tilo,wannan mafarki dai tamkar tarihi ne domin abinda ya faru dashi ne yake sake gani.

Wannan mafarki ta soma da lokutan nishadi tsakanin sa da Mahaifiyarsa daga cen sai labrin ta dawo abin tausayi yayinda Mahaifiyarsa ke mummunar jinya Wanda Kuma shi kadai ne Mai kula da ita Aiko Yana ta ganin haka sai yaga wata katanga ta ginu tsakanin sa da Mahaifiyar tasa wacce take wanciyar jinya,Babu Mai dagata ya Bata abinci Babu Mai yimata komi gashi bazata iyya yiwa kanta komi ba.

A firgice ya farka idanuwan sa cike da kwalla, tarar da Al-Hussien a gefensa ne yasa shi Tino wannan kiraye kirayen sunan nasa da akeyi.

"Why don't you just wek me up? instead of calling my name's."
Bayan ya furta hakan ne yasa hannayen a fuska ya Kuma sauke Kai.

Al-Hussien Shiru nay'an wasu dakiku kafin Nan yayi wasu maganganu a kasar zuciyar sa Wanda yake cewa.

"Your mother will be alright,Amma farko let's help me with my plans."

Gajeriyar murmushi yayi bayan ya furta hakan a kasar Ransa Nan sai yabawa Harun ansar tambayan da yayi masa wato.

"Why don't you just wek me up? instead of calling my name's."

"Ina Mai baka hakuri,Kuma dalilina na tasarka ta wannan hanyar shine,we promise not to touch each other that's all."
Bayan Al-Hussien ya furta hakan ne yasa Harun dago Idanu izuwa kan da.

"Akwai abinda ya kamata ka sani Harun."

Dajiyo haka Harun ya murtuke fuska alamar rudewa... Al-Hussien ko ya sake da cewa

"Just follow me." Hadi da mikewa, Harun baida ta cewa kawai sai ya Mike ya bisa a baya dukda yasan Sauran tawagar tasa suna yanayi na nannauyar bacci.

*_Readers shin Taya Al-Hussien yasan da Mahaifiyar Harun? Naga a mafarki Harun din yaga Mahaifiyar tasa kuma bai sanar dashi ba, Amma Taya ya sani?_*

Tafiya sukayi wacce Bata da nisa sosai sai suka kaiga wata kogo Aiko sa Kai Al-Hussien yayi Hurun shima ya bisa a baya.

Tsintar kansu sukayi a ma'ajiyar littattafai wacce take da haske sosai ganin haka yasa Harun mamaki Hadi da wangale baki.

"Inane Nan guri?."
Tambayan da ta soma kubuta daga bakin Harun kenan inda da diyo haka Al-Hussien ya kame Kam Hadi da juya ganinsa izuwa kan Harun.

"Wannan Guri na dauke da d'inbun Tarihin,Wanda zasu anfane mu domin idan ka duba zakaga ababen anfani su ake adanawa a store to anan gurin Kuma ababen masu anfani su ake Tarawa a Ma'ajiya irin wannan,Dan hakan zamu iyya samun taswira ko Kuma tahirin gidan wance hakan zata matukar taimaka Mana Dan hakan ka duba wannan bangaren Ni Zan duba cen duk abinda kaga ba daidai ba karsanar dani."


"Okay."
haka Harun din ya furta Hadi da yunkurin juyawa Amma sai yayi arba da mirror *madubin* wacce ta ciki Hotonsa kadai yake iyya hangowa Babu ta Al-Hussien dukda Al-Hussien Yana gurin.
😳😳

Kasa motsawa daga gurin yayi yanata wasi wasi cewa.
"Anya wannan shine Al-Hussien da muka Sani Kuwa? Anya wannan ba tarko aka 'Danan na hayeba."
Yana kan fadar hakan sai wata kundi ta fado masa a gaba sa'annan ta bude kanta da kanta.

Wasu harrufa rubutu be suka baiyana inda ya karancesu cikin sauri,nanfa suka bace,Aiko jiyo muryar Al-Hussien ne yasa shi rawar d'ari...cewar Al-Hussien.

"Shin Ka Sami wani abinne?."

"A'a Babu komi."
Ansar daya bayar kenan inda Al-Hussien din ya cigaba da aikin gabansa shiko ya tsunkuya cikin sauri ya dauko kundin Hadi da lullube madubin da wani farin kelle daya tarar a gurin.

Juyawar sa sai yaji an yafe Kellen da karfin tsiya,Aiko zura idanu yayi cikin sanyin jiki ya jiyo inda ya tarar da wani rubutu a jikin madubin...

Zura Idanu yayi cikin tsoro ya kasa motsi sai Nishi yake Nan sai ya jiyo muryar Al-Hussien na cewa.

"I found something Harun."

Cikin sauri ya juya Hadi da karasawa wajen Al-Hussien din karasawar sa Al-Hussien din yace dashi

"Taswira na Samo wacce nake kyautata zaton zai kaimu ga kofar fita daga wannan matsifa."

Aiko jiyo hakan da yayi sai ya Soma waige waige Yana Kai idanun sa lungu da sako,abinda yayi matukar basa mamaki ko shine gani yayi taswirar an bajeta a kasaπŸ“œ ganin haka yasashi cikin zurfin tunani,Yana kokonto shin abinda ya tarar gaskiya ko kuwa.

Abinda ya tunoko shine rubutun da ya gani jikin madubin wacce itace.

"Maraba da Kasancewa cikin Dakin gaskiya,dakin zata bayyana kowace karyar da aka lullube da mayafan gaskiya."

Bayannan sai ya tuno da abinda kundin yace da shi sai yace da Al-Hussien din

"Ka cigaba da duba wannan gurin Ina dawowa"

Aiko cikin sauri ya koma ga madubin Hadi da zubewa gaban madubin ya Ciro kundin daya boye a jikin sa ya bude.

Taswirar, zaku tsinci taswirar da zata kaiku ga wata katafariyar gada saidai gadar ta mutum daya ce Tak daga zarar mutum sama da daya suka haye tuni zata zube...

Gajeriyar bayani daya Samu daga kudin kenan game da taswirar dake hannun Al-Hussien Nan sai ya gaskata maganan kudin haka ya sake amincewa da rubutun da kundin ta nuna Masa tunkan ya dauketa wato "idan kana son tabbatar da gaskiya sai ka yadda da kanka kafin ka gane gaskiya sa'annan,karka yadda da kowa idan ba kaiba....kowa ba abun yadda bane idan ya kasance cikin wannan gidi."

Komawa yayi wajen Al-Hussien yayinda Al-Hussien yake kokarin nuna mishi taswirar shiko Daban abinda yake shukawa domin sai daya Gwada taba gadon bayan Al-Hussien sai yaji sulub hannu sa tashige ciki Nan ya tabbatar Al-Hussien ba mutum bane.

*Cigaban labari*

Sauke Idanu Samra tayi inda ta tuno lokacinda suka kasance cikin ruwan Nan dake kwance,hala lokacin da suke cacan baki...
Aiko bayan tayi hakan sai ta zura idanu Hadi ta furta cewar

"It must be him,Simon."

"Yeah yeah shinefa."

Cikin bacin Rai Atif ya yunkura Hadi da furta cewa.

"Harun yaushe zaka bar wannan haukar taka, ka dakatar da abin Nan da ka jefawa simon"
Cikin tsawa ya furta hakan inda Mu'azz shima ya furta cewa

"Idan Yana tunanin ya Sami wani karfin zai ci Mana fuska da ita toh yayi tayi Allah na bayan Mai gaskiya."

Hahaha kyalkyalewa yayi da dariya Hadi da cewa

"Karkuyi tsammanin Ni na jefaku cikin wannan halin no,ku kuka jefa kanku domin Kun yadda da junan ku Kuma kun yadda da kowa, kowa kuka gani zaku yadda dashi kamar yadda kuka yadda da Al-Hussien Wanda ya kasance Yana son ganin bayanmu gaba daya."

Zura Idanu Al-Hussien yayi Hadi da cewa "what

Please Login or Register in order to submit comment