Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai-dai shi duk ya zuba musu kayan amfani dai-dai matsayin aljihun shi.

Sai d'akin su ciki biyu ne sai falo a tsakiya sannan toilet mai had'e da bathroom, gaskiya anyi komai cikin tsari dan kuwa ginin yayi kyau sosai haka kuma labulaye sai da aka sakama kowan ne d'aki, kujerun khadija masu matukar kyau ne Ahmad ya zuba mata, amma d'akin Mama babu abinda aka saka mata sai cafet wanda ya mamaye d'akin.

Sai d'akin Aminu daga gadon shi sai wajan ajiyar kayan shi.

Gyara ya kammalu harma ya fad'i randa zasu tare.

*****

Zaune yake akan kujerar shi dake cikin ofis d'in shi, waya ce a hannun shi sai murmushi kawai yake zab gawa har wani lumshe idanun shi ya keyi da alama ba k'aramin jin dad'in wayar ya keba.

"Please babyna kibar kukan haka nan in dai ba so kike in kasa duba marasa lafiya ba, yanzu zan duba wani amma idan na gama zan kiraki kinji ko?"

"Ok bye-bye.."

Yanke wayar tayi tare da murmushi duk da cewa ba wani dad'in jikinta take jiba domin kuwa wani irin murd'awa takeji cikin ta na mata kamar za tayo amai.

**

Ba tare da yayi mishi kallon sani ba ya fara tambayar shi abinda ke da munshi, mamaki ya hana mutumin magana kamin ya d'ore yace,

"Oh nikam gani na keyi kamar yaron k'anina wanda yarasu IRO?!"

Wani kallon zama kai bayani Ahmad d'in yayi mishi kamin yace,

"Allah ko?!"

Cigaba yayi da rubutun shi kamin yace,

"Zaka iya tafiya wasu su shigo idan baka da abunda ke damun ka."

Da sauri mutumin ya fara bashi hakuri kamin yayi mai baya nin damuwar shi, magunguna ya rubuta mishi kamin yace.

"Insun k'are zaka iya dawowa domin muga yana yin jikin naka, zaka iya tafiya."

Tsabar kallon daya kema Ahmad din ne yasa shi cin karo da kofar office d'in, cikin tashin hankali ya fice har wani sassarfa ya keyi ya kosa ya k'arasa wajan babban yaronshi daya rako shi,

"Rikeni zubairu rikeni zubairu ashe wannan yaron me sunan baba na wajan marigayi ne likitan wallahi shine..."

Shi kan shi wanda aka kira da zubairun sai da yayi mamaki kuma ya tab'a zuwa ganin likita yaga Ahmad d'in amma sam be gane shi ba domin rabon Ahmad d'in da garinsu tun rasuwar mahaifinshi da yaje so d'aya suka yi mishi wulakanci be kuma komawa ba.

Hannun uban ya kama kamin yace,

"Allah ya kyauta to kawuce muje wajan maganin inga idan kud'ina zasu isa na siya maka."

Wani murmishin takaici yayi bayan tsohon ya b'acema ganin shi tabbas ada ya manta yanada wasu dangi daga mahaifinshi sai dai ayau da yaga tsohon nan ya tuno komai daya manta yayi kuma kokarin ganin ya sharesu aran shi.

*****

Sukuku haka ya koma gida, damuwa fal cikin ranshi sama-sama suka gaisa da Maman ya wuce d'akin da yake nasu shida khadijan, sai dai yana shiga ya taddata tana ta amai tuni ta gama galabaita.

"Innalillahi."

Ya furta da karfi kamin ya rungumeta jikin shi be damu da aman dake jikin taba.

Shigar da ita yayi ban d'akin dake d'akin ya gyara mata jikinta kamin ya kwantar da ita ya fara gyaran wajan, sannan ya shiga yayi wanka. koda ya fito tuni tai barci dan haka jikinta kawai ya tab'a sannan ya bar d'akin ta wuce d'akin Mama.

"Mama naga baba salisu yau yaje asibiti."

"Allah sarki ya suke suna lafiya ko?"

Beyi mamakin jin hakan daga gare taba domin tuni ya san cewa mahaifiyar shi macece me kawaici da kauda kai tare da yafiya. haushi yaji dan haka be kuma maganar ba sai ma maganar khadija daya sako mata,

"Mama baby fa amai ta keyi dana shiga d'akin amma dai yanzu tayi barci."

A rud'e ta kalleshi kamin tace,

"Subhanillahi dama naga yau kamar bata jin dad'i girkin ma ni nayi, Allah ya bata lafiya amma dan Allah babana ka dubata idan ciki ne sai kafara hakuri kadda amai-maita irin wancan karan."

Sauke kanshi k'asa yayi yana cin abinin shi sabida kunya, ya jima bece komai ba kamin yace,

"Kun gama had'a kayan ko? sabida daga dare zuwa safiyar gobe nake so mukoma can sabida an kusa bikin yusuf d'in bana so in takura shi sai insa ai mishi gyare-gyaren inda muka b'ata duk da dai naga babu abinda gidan yayi."

"Eh hakan yayi aima ya kyauta wallahi Allah ya saka da alkhairi ni tun jiyama na gama kintsa komai harna Aminu, sai dai ko d'akin ku."

"A'a canma yanzu zan shirya kamin ta tashi daga barcin tace ita zata yi.."

"To Allah yayi albarka ya kara bud'i me amfani."

"Amin Mama na gode."

******

"Wallahi da gaske nake muku yaron Habiba na gani yayi kud'i ya zama babban mutun daga gani ya tara abin duniya yaron nan."

D'alha wanda ke zaune abin duniya yada meshi yace musu,

"Yanda za ayi kawai mu shirya ranar asabar muje gidan nasu sai muce kawai dama zumunci muka zoyi kunga sai mugani idan arzikin nasu ne."

Innarsu wacce girma ya kama sosai tace,

"lallai baku da kunya har kai wannan yaron yanxu nan har kuna da idanun da zaku kalli iyalin iro da sunan zumunci? lallai kuna tare da dana sani."

Banza suka yi mata da kudirin zasuje su gani kota halin k'ak'ane.

****

Motsin shi taji ya ta sheta saida ta wanko bakinta sannan ya tema kamata ta zauna kamin yace,

"Babyna ya jikin naki? Tashi muje in ga fitsarinki kinji ko? yi hakuri me kike so kici? gaya mun na shirya mana kayan mu zuwa gobe zamu koma namu gidan angama komai sai naje na samo miki abinda kike so bayan kinyi fitsari na aunaki."











*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[3/8, 10:40 PM] ‪+234 816 846 7910‬: *💗DR.AHMAD💗*

39

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by Dota *Hajja ce*👈


*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)



*I*nnalillahi haba khadijatu toh kuma menene na kuka? kiyi hakuri kinji dama haka ne kowa ce mace da kalar yadda take yin natq laulayin, kiyi shiru kinji ina ke miki ciwo yanzu?"

"Mama babu inda kemin ciwo, kawai dai banijin dad'i ne."

"Toh Allah ya baki lafiya ai kuma yanzu ke dajin dai-dai sai dai idan Allah ya saukeki lafiya sannu."

A bincin su aminu ya jera musu kamin ya fice gidan su khadija sabida sam be san zaman gidan sabida babu abokan wasa amma gidan su khadija akwai.

Cin karo ya kusa yi da ita tafito daga toilet daga ita sai karamin tawul wanda iyakar shi cinyoyinta had'iyar miyau yayi jikake k'uttt kamin ya nufeta yana murmushi mai cike da ma'anoni daban-daban ya sakalata jikin shi tare da cewa,

"Babyna kin k'ara kyau da cika wallahi cikin nan yayi matukar yi miki kyau."

k'okarin zame jikinta ta keyi daga jikin shi shi kuma tuni ya fara sunsunarta yana lumshe idanuwa sabida kamshin sabulun da tayi amfani dashi, daurewa tayi ta biye mishi sabida tasan yayi hakurima sabida yanda yake da zalama tasan sam beda hakuri amma gashi yayi wajan kwana biyar sabida rashin lafiyar da tayi.

Kusan babu kalar shirmen da bemata ba sabida tsabar gigicewar da yayi, jiyayi kamar ranar ya fara saninta sabida irin samun nutsuwar da yayi akanta jikinta yayi zam-zam ta k'ara armashi har ya kasa gane farkon yinshi da na yanzu.

Cikin sanyin murya ya fara mata magana yayin da hannun shi ke cigaba da yawo ajikinta,

"Babyna kin gaji ko?"

"Uhumm..!"

Kawai ta iya cewa sabida gajiyar da tayi.

Ganin tayi shiru yasa shi cigaba da lalubarta da alama sake yi zai yi sabida ba karamin dad'i yajiba yanzu saima ji yayi kamar ya tsokano ma kanshi buk'atarta.

Cigaba da murzarta yayi har saida yaji ta sakar mishi kukan ta gaji sannan ya saura mata tare da rungumeta ajikin shi yana d'an jijjigata jikin shi saida yaga tayi lamo tana sauke nunfashi sannan ya tashi a hankali yana cewa,

"Bari in had'a mana ruwan wanka kinji ko..?!"

Tare suka yo wankan su har lokacin bebar lakud'ar jikinta ba ita ko kasala sai dai kawai tabishi da manyan idanuwan ta farare kal.

****

Sun jima tsaye kofar gidan suna jiran ganin yaron da zasu aika cikin gidan domin sam basu yadda da cewa wai wannan gidan nasu Ahmad bane, domin cikin suma akwai wa in da basu yarda da cewa Ahmad d'in likita bane.

Cikin ikon Allah saiga malam Mamuda zai shiga gidan domin tunda suka tare bezo yayi musu Allah ya sanya alkhairi ba, shine yaga yau tunda asabar ce yasan duk suna gida bari yaje.

Saida sukai kallon-kallon tsakaninsu kamin malam Mamudan ya mika musu hannu sukai musabaha domin shi yaga basu da niyyar bashi hannun da alama dai mamaki ne ya kusa kashe su.

"Kushigo mana kuzo mushiga ai sunanan ciki yau hutun karshen mako har Dr d'in ma nasan yana nan ciki."

Cikin sanyin jiki suka bi bayan shi, yayin da idanunsu keta yawo acikin gidan domin ba wata k'arya aka tsaraba agidan ammafa bak'aramin kyau yayi ba musamman da har yanzu yake kamshin sabon fenti.

Zaune suka taddasu d'akin Maman Ahmad na kusa da Maman shi yayin da khadija ke kwance acinyar Maman Ahmad d'in na mata matsar kafafu ita kuma Maman nata shafar gashin kanta tuni ita tayi barcinta sukuma hira kawai suke abunsu bazaka tab'a gane cewar suruka akewa wannan gatan ba.

"Sannu da zuwa Ahmad d'in da Maman kema malam Mamuda kamin idanun su ya sauka akan wa inda ke bayan shi.

Fuskar Maman babu wata damuwa sai dai tuni ta Ahmad ta canza dan haka komawa yayi kawai ya zauna tare da gyarama khadijan kafafunta wa inda ya sauke daga jikin shi yanzu.

Malam salisu ne ya fara magana cikin alhini da karayar zuciya yace,

"Dama mun zone domin muyi zumunci tunda kun yaddar damu sai kace ba jinin kuba."

Wani mugun kallon takaici Ahmad yayi mishi kamin yace cikin gadara,

"Ahh zumuncifa kace malam? kanaso kuyi shari'a da zumunci a gaban Allah kenan tunda har zaka iya zuwa wajan mu da sunan wai zumunci, koda yake kila ka manta irin korar dabbobin da kukai mana tare da yanke duk wata alaka datake tsakanin mu? kamanta ranar da ka dinga kiranmu da shegu karnuka kuma lalatattu dan kawai munje sada zumunci daku? ka manta ranar da kace mu d'auka bamu da sauran dangi acikin garin charanci sabida kun ruga kun ya femu? kun manta ranar da kuka tasani nida kanina kuka dinga tsine mana albarka da zagin cin mutunci ga mahafiyar mu kuma a gaban idanun mu?

Kamanta ranar da kake furta cewa kune kuka kashe mana mahaifi kuma kani agareku sabida kawai beyi muku d'in kunan daya saba mukuba?

Kun manta kace duk ranar da muka sake waiwayar charanci lallai sai kunyi sanadin ajalina musamman ni danake babba?
a hakan kuke tunanin zamu kuma waiwayarku harmu sada zumuncin?"

Ckin matukar sanyin murya ya furta,

"Ina yawan zuwa charanci ba tare da sanin kuba haka ma Mama sabida inaso inga ko zuciyarku ta sauya kunfara son mu, sai dai kash! kullum baku da aiki saina binmu da mugun kalaima na b'atanci da lalacewa, idan ban manta ba ko wata hudu da suka shige ankama yaronku musa yayima wata yarinya ciki, me kace a ranar? cewa kayi inama me sunan babane aka samu da laifin nan.
sabida haka kunga wannan ya nuna musu malam Mamuda wanda ya zabga tagumin mamaki da tsoran halin mutanen ya hanashi ko motsin kirki, Ahmad yaci gaba, to wannan shine uba agaremu nida k'anina bamu da kowa saishi shine ya tsaya mana haihuwar mune kawai beyi ba sannan daga karshe kun san gatan da yayi min wanda Ku kuka kekashe kuka kasa yimin? nasan baku saniba to wannan d'iyarshi ce ya aura min kamar yadda kukemin fatan inyima yaran mutane ciki to hakan be faruba sabida ya bani d'iyar shi tun kamin ta mallaki hankalin kanta, yanzu haka cikina ne na halal a cikin jikinta kuma ban tab'a shaye-shaye ba kamar yadda kuke min fata, ni _AHMAD BANI DA SAURAN WATA ALAKA DAKU_, dan haka kuyi gaggawar barin gidan nan kamin in had'aku da hukuma."

"Kai Ahmad gidan ku, nace kajiko gidan ku, nace iyayen naka zaka kai ga hukuma dan iya shege to inji kafara kaga yanda zanyi dakai..."

Cewar malam Mamuda da yayi karfin halin yin maganar, itako Mama ai kuka kawai take yi sabida jitai komai ya dawo mata sabo sannan bata tab'a tunanin shi Ahmad d'in ya rike abubuwan da suka faruba a baya ba.

Ahmad da takaici ya kusa kashewa share kwallar idanunshi yayi kamin d'auki khadija cak! daketa barcinta yasab'ata akafad'a yabar d'akin, gaba d"aya suka bishi da idanu domin har yanzu anrasa wanda zai kuma tankawa cikin su, saima sheshshekar kukan Maman dake tashi kadan-kadan cikin dakin.

Sunjima cikin shiru kamin sufara bata hakuri daya-bayan daya, tare da neman gafararta data yaranta duk da cewa sunga rashin sauki dagashi gurin *DR.AHMAD* d'in amma dai suna so ta yafe musu.

Malam salisu ne ya d'ora da cewa,

"Tabbas muncika azzalumai Habiba domin tun tasowar iro muke cutar dashi sai gashi duk da abinda muke mushi hakan besa Allah ya tabar da shiba sai ma yayi mishi d'aukaka sama damu, muna cikin wani hali munsan cewa alhakin kune yake bibiyarmu kuduba irin gidan da kuke ciki babu abunda kuka rasa, muko kullum cikin tashin hankali muke sabida yanzu tun a duniya Allah kefara sakayya dan Allah kuya femana kuyi mana afuwa tabbas masu hali irin namu nanan sunada yawa a duniya, munafatan Allah ya shirya su tunkamin lokaci ya kuremusu kamar yadda muka sami kanmu aciki kuyi hakuri Habiba muntub'a wallahi harga Allah kuma bazamu kuma aikata wani abuba makamancin wannan domin munga ishara."

Saida malam Mamuda yasa baki sannan tace ta yafe, aiko sukai ta godiya tare da cewa zasu kawo iyalansu domin suka waje.


MALAM Mamuda ne ya fara magana cikin farin ciki domin tabbas yajima yana fatan zuwan wannan ranar yacce,

"Tabbas mun godewa Allah daya nuna mana wannan lokaci munafatan Allah ya kuma kare zumuncin shi, gaskiya nayi farin ciki sosai wallahi na tabbata malam ibrahim shima zai yi farin ciki duk da yake kwance cikin k'abari Allah yaji kanshi yayi mai rahma."

Gaba d'aya suka amsa amin cikin jimami.

Malam Mamuda ya d'ora da cewa,

"Tabbas mutane da dama sukan aikata kuskure batare da tunanin kuskurene ba misali zaka sami yaron wani kaita zagi tare da aibatashi da munanan kalamai sai-dai sani ne da ba muyi ba amma a duk lokacin da kai hakan to tabbas mala'iku sukan maido da wa'innan muyagun kalaman ne akan iyalinka, shi yasa sai kaga kaima acikin iyalinka kasami me irin wannan halin koma fiye,

Haka kuma idan kayima iyalan wani kyakykyawan addu'a to tabbas saita sami naka iyalin sabida haka yaka mata mu kula sannan mudaina kullatar marayu domin dayawansu Allah baya tabar dasu kuma tabbas wataran sai kaci arzikinsu Allah yasa mugane.

Sannan ina iyaye masu tsatstsauran ra'ayi akan yaran su? kanada yaro namiji kuma baligi cikakken mabukaci amma ku hanashi aure harsai ya gama karatu ya sami aiki kuma ya gina gida yasai mota tsawon wannan lokacin kasan iyakar zunubin daya kwasarma kanshi? to karka manta kuma iyayenshi akwai naku kason na zunubin domin laifin kune duk wani abu da zai aikata
.
Yima yara k'ana nu fyad'e ya yawaita sabida haka aure da iyaye suke yi sabida wani buri nasu nada ban, yarinya zata nuna tana son aure amma iyaye suk'i yi mata sai tasami me kud'i ko kuma sai tayi zurfin karatu wannan kuskureni domin sha'awa babu abinda baza tasa mutun ya aika taba, misali yanzu shi Ahmad me yarasa?
Babu, itace amsar anyi mishi aure alokacin da ya bukata kuma gashi yayi karatun shi hankali kwance, yanzu inda ba ayi mishi ba mun san iyakar yaran da zai lalata? bamu saniba dan haka yaka mata mu iyaye mu kula tunkamin ranar da Allah zai tirkemu da tambayar yaya muka tafiyar da amanar daya bamu.

Bari muje sallah Habiba a sama musu abinda za suci kamin mu dawo zan shawo kan shi Ahmad d'in insha Allah."

Godiya suka yima malam Mamuda kamar zasu yi mai sujjada sabida farin ciki, a haka duk suka yi alwala suka fice, itako Maman kitchen ta shige domin ganin ta dafa abu me sauki wanda zasu ci......










*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[3/8, 10:41 PM] ‪+234 816 846 7910‬: *💗DR.AHMAD💗*

40

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO...*💡
(Home of expert & perfect writer's)



*D*uk iyakar lallashin malam Mamuda gurin Ahmad daya yiyafiyar amma ta gagara domin, bayan dawowar su daga masallaci sunci sun koshi kowan ne baki awashe Ahmad ya yunkura zai tashi malam Mamuda ya hanashi tare da bashi hakurin da suketa fama dashi, idanun shi sunyi jawur sosai yake kallon yayyen mahaifin nashi da kannenshi d'aya bayan d'aya kamin yace da kyar.

"Na yafe musu duk abinda sukai min ammafa babu ruwana da huld'a dasu domin ina jin tsoran in sake dasu su cutar damu kamar yadda sukai sanadin d'an uwansu."

Ganin ya bar d'akin yasa malam Mamuda kallonsu tare da cewa,

"Kuyi hakuri insh Allah zai sakko kunsan yaro da rikon abu dole sai a hankali zai manta."

Itama matma hakurin dai ta basu tare da musu alkawarin zuwa su su duka garin domin sada zumunci.

***

"Ya Ahmad gaskiya be kamata kai musu haka ba naji baba nata fad'a dan Allah kai musu hakuri su duka ka yafe musu, kaga sun tuba zaka sami ladan yafiya kaji kaji..?!"

Murmishi yayi tare da rungumota jikin shi ya fara shafar cikinta wanda yake ashafe kamin yace,

"Nima na yafe musu baby kawai dai haushin su na keji wallahi na kasa manta abinda suka yi mana, oya haa bakin ki amshi abincin idan kinci da yawa to zan fita yawo dake anjima da yamma."

Baki ta bud'e da sauri a hankali ya dinga bata yana janta da hira hartaci da yawa ba tare da tasani ba, sai da ta kammala sannan ya kwashe kayan ya mayar kitchen ya dawo kusa da ita ya zauna.

"Sannu kaji mijin Khadija, Allah yabar mu tare ya k'ara mana hakurin juna.."

"Amin Dijama ta 'yar albarka ke kad'ai kike iyawa dani Allah yayi miki albarka."

"Amin my Dr ai kaine duk ka koya min ka raineni akan duk yadda kake so na kasan ce Khadija love you so much."

Da sauri ya kankameta a jikinshi tare da furta,

"Ahmad love's you so so very much..."

***

Ahmad da kanshi yayi tunanin fara azumi domin samun sauk'in rayuwar shi data khadijan shi, sai dai lokuta da dama adaddafe yake kai azumin sabida dama yunwa takan kwantar da sha'awa ammafa da kaci ka koshi zata iya tasowa.

Hakan yasa idan yana yi baya zuwa gida sai gaf da magriba sabida ko kwalliyarta ya gani sai taji abu ya fito mai amma idan gaf da magriba be zai koma yayi sallah a masallacin kofar gida sannan ta shiga ciki da haka yake samu ya saurarawa Khadija dama Zainab tunda ta tafi ba'a biyo sahuba shima bebiba tunda ta nuna mai bazata iya maiba.

*Bayan wata bakwai*
Cikin ikon Allah rayuwa ke juyawa wataran da dad'i wataran asami aka sin hakan. a bangaren su Ahmad sun cigaba da zumunci da 'yan uwansu suna matukar girmama Ahmad d'in domin yana kokarin ganin ya manta da komai daya faru abaya dan ya kyautata musu, sannan sukan ziyar ce su akai-akai domin temakon su shi yasa suke mishi kallon babban mutun ballantana da Allah yayi mishi arziki dai-dai bakin gwargwado.

A bangarenshi da khadija kuwa sai dai ace alhamdulillah domin cikinta harya shiga watan na haihuwa tana matukar samun kulawa fiye da duk yanda zan misalta muku musamman wajan mijinta ya d'auketa da matukar muhimmanci arayuwar shi ko washh ta furta to yanzu hankalin shi zai tashi, kullum cikin lallashi da bata labarin kaunar shi gareta ya keyi abinda ranta keso shi suke mata, domin samun surkai irinsu Mama zai yi wahala bata tab'a cewa babana meyasa kaima khadija abu kazaba ni bakai min ba? A'a sai dai kullun cikin tuna mishi take khadija taimaka halacci babana kadda kai mata butulci tayima iyayenta biyayyar zama dakai tunbaka da hankali sabida haka kadda ka cutar da ita, sannan ka dinga saurara mata da bukatarka sabida cikin jikinta kadda ka yadda ka koya mata gudunka kadinga tausaya mata domin tana bukatar hakan. kullun Mama bata barcin kirki kusan kwana take yi akan sallaya tana rokama khadija saukin haihuwa da zuri'a d'ayyaba.

Shin iyaye mata surukai munayin hakan kuwa?
nasan da yawa amsar itace a'a sabida haka kadda mu manta duk abinda kaima d'an wani to tabbas yananan zuwa kan naka. in kai me kyau zaka gani haka in kai sab'anin hakan shima zaka gani Allah yasa Mu dace, idan mun dace Mu dafe abunmu....

****

"Babyna zan fita babu abinda kike bukata?"

Tulelen cikinta ta shafa kamin tace,

"Honey yayana kadan d'ebe min kewa mana kota minti talatin ce ina bukace da kai naga kwana biyu baka san yi kuma ni wallahi ina..ina so."

Zama yayi gefenta tare da damke hannayenta cikin nashi yanajin wani irin mugun sonta na ratsa sassan jikinshi murya can k'asa kamin yace,

"Ayy sorry babyna ina jin tausayin kine shi yasa nake hakura amma tunda kinaso bari muyi sannan na tafi asibiti but babu inda kemiki ciwo yanzu ko..?!"

"Ni dai babu sai ciwon buk'atar mijina itace kawai take damuna."

Yana jin haka yayi saurin zame takalmin k'afarshi dama me neman yin kuka ne sai aka jefeshi da kashin awaki kunga kuwa sai yi.

Kusan da dabara ya samu biyan bukata sabida girman cikin yau kwana uku kenan ta lura ko bacci baya yi sosai kuma abinda ke damun shi kenan shi yasa tayi mishi wannan dabarar dan yasamu sakewa koda kuwa ita da babyn zasu takura.

Saida ya temaka mata tayi wanka sannan shima yayi ya sake kintsa jikin shi yayi mata sallama yana ta faman sa mata albarka zuciyar shi wasai a haka ya fita.

****

"Wayyo Allah na...!"

Cewa khadija wadda taji mararta ta isheta da tsinkulawa. da kyar ta kai hannu kan wayarta ta kira Maman kamin ta ajiye wayar Maman ta shigo.

"Sannu..sannu khadija oh ikon Allah kamar ana jiran babana ya bar gidan? kodai shine ya dameki?"

Banza tayiwa Manan ita dai hannu kawai take yarfewa ganin haihuwar tariga tazone yasa Maman gyara mata wajan zama cikin yardar Allah ko minti arba'in ba tayi ba saiga yaronta d'irkeke gundumeme kato tabarkalla Masha Allah, kuma daga ganin shi lafiyayye ne ko dan ihun daya cika musu kunne dashi.

Nan da nan jikin Mama ko ina rawa yake sabida murna ta rungume jaririn da jinin shi a jikinta da komai tana addu'a kamin tafara gyara shi ta na d'eshi ta koma kan khadija wacce tuni barcin dad'i ya fara d'ibarta.

Goge mata jikinta tayi sannan ta kamata ta maida ita gado sabida tasamu isasshen hutu sabida anaso idan kika haihu akalla kisami awa hud'u a kwance kamin wanka ya biyo baya sabida yin wankan da wuri shine ya kan kawo bugun jini da sauran su.

Zama tayi ta goge yaron nan tas! sannan tasa ka mishi kayan sanyi ta zuba mishi ido babu inda yaron ya baro uban shi sai bud'e idanun shi yake yi yana rufewa jitayi wasu hawaye sun zubo mata tace,

"Oh yanzu da basu yi mishi aure ba kila can za'a tsiyayar da yaron nan kila ma a kawo mata shi ya zamto itace zata raini d'an da bana halak ba da hannunta, amma yanzu murna take ji take tamkar ta suma danjin dad'i.

Godiya ta dinga jerama lillahi kamin ta rab'ashi gefen Maman shi wacce tuni tai barci, tashi tayi tafara gyaran wurin cikin kanknin lokaci d'akin ya d'auki kamshi kamin tayi waje da kanta ta d'auraye kayan ta shanya sannan ta d'orama khadijan ruwan tea wanda yaji kayan yaji saida ta had'a komai har kunun waken soya tayi mata sabida ruwan nono yazo sannan ta d'ora musu ruwan wanka domin daga mejego har jaririn ba aso daga haihuwa asamusu ruwan zafi ajiki hutunsu akafi bukata bawai wankan ba.

*****

kiranshi na hud'u kenan sannan yaji an d'aga sallama tayi mishi kamin tace,

"Honey yayana ya aikin naka?"

"Lafiya lau babyna ya kike ya ajiyata?ina fatan duk lafiya kuke ko?!"

"Lafiya lau muke wallahi ga Mama zaku yi waya."

Maman ta mik'awa saida ya gaishe ta sannan tace mai,

"Dama zance idan zaka taho gida kad'an taho da kaji zan bama khadijan sabida jikinta."

"Ok toh Mama zan taho dasu ai yau karfe hudu zan dawo insha Allahu."

"Allah yasa toh."

"Amin Mama bye."


Maman khadija ce da Maman Ahmad zaune sunata hirarsu ko wanne fuska awashe anyi jika, jariri ya fara kuka Mama tayi saurin d'aukar shi ta koma

Please Login or Register in order to submit comment