Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wajan khadijan tace,

"Kinga yaron nan bazai yi wani barcin kirki ba in bajin nono yayi abakin shi ba kallifa yanda ya keta wawure-wawure kiba shi yaja hakanan ai nonon yazo yanzu."

Cikin shagwab'a khadijan tace,

"Mama kaddafa yayi min da zafi?!"

"Keni ban san shirme bashi yasha ni zai kashemin dodon kunne."

Ita dai Maman khadija na gefe tana dariya, Maman ta samu ta nuna mata yanda zata bashi aiko da sauri caraf ya cafke da karfin shi ya fara zuka ihu khadijan ta saka tare da furta.

"Wayyo Allah nono na Mama."

Saida ya saki sannan Maman ta amshe shi tuni yayi bacci itako khadija hadda hawayenta wai da zafi. mutane nata shigo musu barka domin tuni Aminu ya gama zagaye mutune da suma sunyi sabon baby.

Da la'asar ya nufo gidan yanajin ya gaji sosai sai dai har yanzu farin cikin da khadijar ta shayar dashi da sanyin safiyar yau be sake shiba dan haka nan yake murmushi shi kadai tun a cikin asibiti.

Yana faka motar ya kwaso ledojin daya taho dasu ya nufi cikin gidan, yayi mamaki da yaji mata nata mishi barka da arziki, kayan ya zube cikin kitchen ya nufi d'akin khadijan,
aiko zaune ya taddata da k'aton jariri ahannu tana kukan bashi nono shi kuma yana kukan sai yasha.

Da sassarfa ya isa garesu sam be lura da matan dake cikin d'akin ba ciki kuwa hadda Maman tashi. d'aya bayan d'aya suka bar d'akin ganin yanda malam Amadu ya rungume iyalin shi yana jin wani farin ciki na ratsa zuciyar shi,

"Allah yayi miki albarka babyna Allah yayi miki sakayya da Aljanna yanda kike faranta min kema Allah yafaran tamiki ashe kinajin ciwo da safe amma kika sani dole na dameki ko?gashinan kinja na zunguro shi, nagode sosai yanzu kukan me kike yi shima yana taya ki ha?"

"Amin honey yaya na wai dole sai yasha nono kuma ko d'azu saida naba shi wallahi akwai zafi."

Bin yaron da kallo yayi yaga sai lasar bakin shi yake yana son saka hannu abaki, murmushi yayi kamin ya share mata hawayen yace,

"Kin gafa kina kuka yana kallonki kadda kisa ya raina kifa bashi kad'an yasha saimu gaisa dashi dan kar ya min kuka."

*💗DR.AHMAD💗*

41

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)



*H*ararar yaron tayi kamin ta saka mishi nonon cikin bakin shi, dafe kafad'unta Ahmad yayi ganin yanda take kankame jikinta kamar ma so take ta kwace abinta.

Yaron yaci gaba dajan abincin shi har sai da ya saki dan kanshi sannan Ahmad d'in ya d'auke shi daga jikin ta ya rungumeshi yana ta sakin murmushi, kallon yaron ya keyi sosai ganin irin kamar da yaron yayi dashi, Allah nagode maka da kamin wannan kyautar, Allah nagode maka da arzikin da kamin ka bani dama in cigaba da gode maka."

Rungumo khadijan yayi tare da shafar kirjinta wa inda suke cike taf da alama ruwan nonon yariga ya samu, kwab'e mishi hannu tayi tana hararar shi.

"Allah ya baki aljanna matata ina fatan Allah ya barmun ke babyna kin isheni zaman duniya dana kiyama wallahi nagode nana khadijana..."

Murmushi kawai tayi tare da jawo ledar balangun da babanta ya aiko mata dashi d'azu sai faman kamshi yake.

Kusan tare suka cinye naman har lokacin yaron na hannun abban shi, shiko Ahmad tuni ya sami abin kallo gani ya keyi kamar banashi bane jiyake kamar za'a ce bani ba naka bane, ko yaji ana tashinshi daga bacci yasan mafarki ne amma yaji shiru sai mamakin kanshi yake wai shike da wannan zuk'ek'en yaron.

"Oh ikon Allah babana ka fita mana mutane nason shigowa amma sabida Allah kazo kayi zamanka a ciki ko kunya."

Kallonta yayi da kyawawana idanun shi kamin yace,

"Mama ganin su fa na keyi, kuma so nake muje asibiti yanzu a duba su."

"Amma dai ai ka bari suyi wanka ko? tunda shi yaron ance so d'aya ya wadatar dashi."

Cikin shagwab'a khadija tace,

"Mama waini bake zakimin wankan ba to waye zai min?"

"Haba khadija nace miki gwaggonki zatayi miki amma sai tambayata kike yi tun d'azu."

Idanun shi awaje yake kallonsu kamin yace,

"Haba Mama wai kina nufin baby tubewa zata yi wata taga jikin ta bayan ni?!"

Harararshi tayi sam idanunshi sun rufe kamin tace,

"Kai tafi can, nifa ban san hauka gwaggonta ta tace wata? to eh ita zata yi mata."

Grgiza kanshi yayi kamin yace,

"Ahh no gaskiya Mama gaskiya ban yarda ba wallahi kuma ban amince ba indai ke baza kiyi mata ba to gaskiya sai dai kibari ni nayi mata ko kuma a hakura da wankan, ya za ayi kowa sai yaga jikinta dan Allah haba-haba.."

Batai mamakiba domin tuni tagane irin masifar kishin shi akan khadijan amma batai tunanin abin ya kai haka ba. Kai ta girgiza kamin tace,

"Allah ya shiryaka to."

Sannan tabar musu d'akin.

Shi kam juyawa yayi wajan khadija yana tambayarta,

"Babyna babu inda kemiki ciwo ko?!"

Kallonshi tayi sannan ta kalli yaron dake hannun shi tace,

"Laah ya Ahmad wallahi da kai yake kama ka gani kuwa?"

Murmushi yayi tare da kashemata ido d'aya yace,

"Yoo yarinya angaya miki ni d'in na wasa ne ko matsalata ai tasa yaron yayo kama dani, tambayarki nayi fa ina kemiki ciwo?"

"Jikina be min ciwo amma dai ina jin zafi awajan abuna."

Kwantar da yaron yayi kamin yajata can karshen d'akin saman gado yace,

"Kwanta in gani ko kinsami kari ne."

Bata yi mishi gadda maba domin tana jin zafin wajen sosai daurewa kawai take yi. cikin nutsuwa ya dubata yaga tasamu amma dai beda yawa befi aimata d'inki d'aya ba kuma daga waje ne, shafarta ya fara yi bayan ya gama dubawa musamman kirjinta da sun riga sun gama tsokane mishi idanu, ganin yana neman fita hayyacin shi ne ya sata fara tureshi daga jikinta sabida tasan bata da abin bashi sannan tasan shi wasan ninnan bawani yi mishi suke ba shi dai kawai yajishi in.

"Nashiga uku ni Habi babana uban me kuke yi cikin kuryar d'aki kuma daga haihuwa yau sakaran wofi kawai...? zaka fito ko saina ci maka mutunci yanzun nan?"

Zaro idanuwa yayi yana kallon khadija saida ya dai data nutsuwar shi sannan ya fito yanata murmushi tare da shafar sumarshi yace,

"Kai Mama bafa wani abu zanyi ba dubata kawai nayi yanzuma idan kin yi mata wankan zanje da ita sai nayi mata d'inki tukunna ta denaji ciwon."

Harararshi tayi kamin tace,

"To naji zoka fice waje dan Allah kabarta ta huta haba mana kadai. san yanda haihuwa take yarinya nason hutu amma ka like da wanne kakeso taji?"

Hakuri ya bata tare da sumbatar yaron shi agoshi sannan ya bar d'akin bako kunya shi yanzu har wata fitsara-fitsara yakeji sabida ya girna ya zama Abba.

***

Kullum gidan nan cike yake da mutane Ahmad sam be cikin sukuni domin idan yabar gidan tun safe to be kuma dawowa sai dare sabida mutane. sosai yayi kokarin ganin yayima khadija da yaron shi bajinta domin akwati uku yayima khadijan sannan yayi ma yaron akwati d'aya sabida shi yaron kullum cikin samun kaya ya keyi daga abokanan shi da dangi kowa ya naso yaga yayima Ahmad din wani abu da zaiji dad'i.

Sun bawa mutane mamaki domin kuwa kowa yayi tunanin zai sakama yaron sunan mahaifin shi ranar sunan sai kawai sukaji an sakama yaro suna MAHMOUD, wato sunan malam Mamuda mahaifin khadija sai dai sun saka mishi suna na alkunya wato Abba.

Har hawayen dad'i malam Mamuda yayi lokacin daya ji sunan yaron yayi farin ciki tare da godema Allah, sannan ya shiga har gidan yayima Mama godiya sai dai itama godiya take mishi hadda hawaye yayinda ta tuna irin halaccin dayayi musu a cikin rayuwar su.


BAYAN SUNA:-

"Mama inaga abarta anan kawai d'akinta zaifi tunda baba yak'i yadda ta koma can d'in kuma mani sai naga dama nan da can d'in ai duk d'aya ne ko?!"

Wani kallon banza tai mishi kamin tace,

"Babana ban san meyasa yanzu ka rainani ba wallahi, so kake yi in bar maka yarinyar mutane kasani jin kunya wataran? kaddafa ka kamanta nice mahaifiyarka na sanka ciki dabai dan haka bazan bar khadija a d'akin taba zata dawo nan d'akina kai kuma ka zauna ana kun data gama wanka saita dawo d'akinta idan tagama zaga dangi amma gaskiya bazan yadda da zamanku tare ba sabida inajin tsoran halinka babana..."

Hakuri ya bata tare da barin d'akin cikin sanyin jiki. zaune ya taddata tana bawa yaron nono shima jikinta ya shige har wani ajiyar zuciya ya sauke kamin ya fara d'an shafarta sama-sama yana jin wata irin masifar kewarta jiyake kamar yayita tsala ihu ko za afahimci abinda ya keji cikin jikinshi.

Daga shi har ita nisa suka yi,sai dai sukaji ihun yaron ashe Ahmad dinne ya kwace nonon daga bakin shi ba tare da sanin lokacin da yayi hakan ba wato shi ya maye gurbin yaron, dariya suka saka tare bayan yai saurin maidama yaron nonon cikin bakin shi.

Dariya suke yi sosai musamman khadija da harwani nuna Ahmad din ta keyi da yatsa, saida Mama ta leko sannan sukai fargai-fargai dasu tace,

"Kukan me abba keyi haka?!"

Shiru su kayi kowan ne ya sadda kanshi k'asa, hararar Ahmad d'in tayi kamin tace hala yau ba zaka fita ba ne ko?!"

Mikewa yayi ya shige ciki saida ya shirya ya fito, Maman tabashi hanya ya fice sannan taje ta amshi yaron ta goyeshi ta fara had'a kayan da zasu bukata ta dinga kaiwa d'akinta ita dai khadija nata ido kawai.

Saida ta gama kintsa komai sannan ta tasa khadijan zuwa d'akinta,

"Ke naga alamar bawani hankalin kirki gare kiba inba haka ba duka yaushe kika haihu da zaki fara biye mishi tunda kin san ba hakuri ne da shiba? koda yake bazan yi mamakiba tunda shine ya raineki babu abinda be koya mikiba ke ma kin zama shi."

Kunya tasa khadijan rufe kanta akan gado tun tanajin motsin Maman har barci ya d'auketa a haka.












*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[3/11, 10:04 PM] 0mmer Farouk: *💗DR.AHMAD💗*

42

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)


*B*ayan kwana biyu masu jego sunyi shar abinsu basu da wata damuwa sabida irin kulawar da suke samu daga gurin duka side din, abba sai k'ara washewa ya keyi da wayau tubarkalla Mama bata da aiki saina kallon abba tare dayi mishi rawa ita dai Allah ya jarabce ta dason yaron wanda har bata iya boyewa.

AMINU kam kullum sai anyi daga dashi domin soya keyi ya dinga goyashi itako Mama taki yarda khadija ko babu ruwanta daya ce bani take mika mishi haka Maman zatai tamata fad'a amma bazai hana gobema taba shiba dan tana ganin bayan uban yaron to Aminu ne na biyu.

Malam Amadu kuwa tuni ya fara tsanewa atsaye duk da cewa kullum yanzu azumi yake yini dashi amma dakyar yake barci sabida kewar matar shi.

Zaune yake cikin ofis d'inshi yau tun safe babu abinda ya tsinana gashi yanzu har anfara kiran sallar azahar a wasu masallatan, wayar shi ya lalubo kamin ya dan na mata kira, cikin shagwab'a ya furta,

"Babyna..!"

Murmushi tayi kamin tace "uhumm yayana ya aikin?"

"Na kasa baby wallahi yau jinake kamar zan halaka Mama ta daina jin tausayina wai har yanzu baki fara sallah ba?"

Tunowa tayi da fad'an Mama dan haka da sauri tace mai,

"Eh ban fara ba, amma dai yau baka azumin ne?!"

"Inayi baby ya zanyi."

"Ayya toh shike nan dama cewa zanyi kai sauri ka dawo yanzu kamin Mama ta dawo ko ragewa sai kayi, tunda kuma kana azumin shike nan.."

Ai tuni ya mike tsaye tare da furta,

"Ashe batanan amma kikaki gayamin tun safe? bari inzo ganinan."

Dariya ta fara yi mai bayan ta ajiye wayar, zuwa yanzu mijin nata ya daina bata mamaki sai dai tausayi, sannan kullum adduarta gareshi shine Allah ya dauwamar da hankalin shi a kanta ya kauda idanunshi daga kallon matan banza ballema harya kaiga ta yawa.

Jikinta ta gyara da turaruka sannan ta tsaya jiran shi tana addu'ar Allah yasa kar Mama ta dawo da wuri. aiko sai gashi yau ko takan abba bebiba wata irin wawar runguma yayi mata akirjin shi kamin ya fara sunsunarta da lasarta, jikinshi harwata tsuma ya keyi yana cewa,

"Babyna yaushe rabon da ko rungumarki nayi Mama ta hana komai wallahi na kusa mutuwa da kyar nake daurewa, dan Allah da abun ya d'auke kimin magana ko sau d'aya ne nayi batare da sanin maman ba kinji matata?!"

Sumarshi take shafa ahankali cikin lallashi kamin tace,

"Kayi hakuri kaji kayiwa Mama biyaya nima ka tayani yi mata abinda take so."

Bak'aramar murza ta shaba a hannunshi ba sannan ya samu ya rage damuwar shi, Allah ya temaketa harya gama bired'ed'en shi hankalin shi be kai wajan abinba dan tasan da saiya gane ta sami tsarki ita kuma tana tsoran kar Mama ta gane tayi mata kallon wani abun.

kwance yayi agadon yana sauke nunfashi, har lokacin idanunshi alumshe yake kuma hannunshi na saman kirjinta yana cigaba da shafarta,

"Uhm! honey ya Ahmad to ka tashi ka shirya jikinka kamin Mama ta dawo ta taddaka kasan fad'a zatayi kuma sai ta gane sannan ya maganar azuminka yana nan?!"

Dariya yayi kamin yace,

"Ai kema kin san yabi ruwa na yau babyna amma dai zanyi gobe insha Allahu ai na rage zafi."

Itama dariyar tayi kamin tace,

"To yaza kai da girkin da zatayi maa anjima?"

Janta yayi jikin shi yaci gaba da tsotsar lips d'inta idanunshi arufe tsawon lokaci domin harta farajin zafi sai dai batasan ta katse shi domin samun nustwarshi itace tata.

Motsin yaron ya kwaceta dan haka da sauri ya tashi ya fara goge jikin shi ita kuma ta nufi abba dake son fara kuka.

Wucewa yayi d'akinsu yana fad'in,

"Sorry bari inyo wanka yaron baban shi sai nazo in d'aukeka kajiko?"

Tana bawa yaron nono shi kuma ya shigo ya canza kaya sai kamshi ya keyi, ganin irin kallon da take mishi yasa shi zama gefenta yace,

"Baby na can zamiki ne?!"

"A'a dadyn abba kawai dai naga kaimin kyaune sosai ina fatan zaka kauda idanunka daga kallon haramun?!"

Abba ya amsa a hannunta kamin yace,

"Ki tayani addu'a babyna insha Allah zan kiyaye nagode da kulawarki gareni Allah yayi miki albarka."

"Amin."

Wasa ya fara yima yaron kamar wani babba shiko yaro ya zubama fuskar baban shi ido.

"Kaga nidai kawoshi ka tafi kadda Mama ta dawo tayi tunanin ko wani abun kadawo mawa."

Yana mika mata yaron Mama na shigowa domin tunda ta hango motarshi taji hankalinta ya tashi, sannu da zuwa sukai mata ciki-ciki ta amsa tare da jefama Ahmad din wani kallon tuhuma,
kauda kashi yayi ga barin kallonta kamin yace,

"Mama ashe unguwa kikaje yanzu na shigo khadija ke gayamin gidan hassan naje shine nace bari na biyo daga nan in gaya miki hadda d'an-wake zakimin na bud'a baki sabida na rabu dacin shi wallahi."

Washe baki Maman tayi kamin tace,

"Au to shike nan yasu hassan d'in ai tun safe nafita dawowata kenan."

"Toh sannu rikeshi baby in wuce sai na dawo."


Kallon tausayi Maman tabishi dashi kamin ta maido kallonta gun khadija tana murmushi tace,

"Ashe yanzu shima ya dawo?!"

"Eh Mama shigowar shi kenan sai ya dauki abba toh kema sai gashi kin shigo kamar tafiyar ku d'aya."

"A'a ni yanzu na shigo Allah ya dawo dashi lafiya."

"Amin Mama."


Irin gyaran da Mama takema khadija ya sanya tuni itama tafara adduar Allah yasa Mama taje unguwa kosun samu su sake da juna dan ta tsumu iya tsumuwa, sai dai ina Mama ta tsare ta rantse sai anyi arba'in cas.

"Please Mama na kiji tausayi na tunda tayi kwanaki 40 din kibarni da ita wallahi kamar zan mutu nakeji ki tausaya min Mama dan Allah ki cetoni daga fad'awa halaka kamar yadda kika cetoni tun kafin nakai haka girma.."

"Oh ni na bani babana nadai koma abokiyar wasanka kawai, yo in ba haka ba niza ka samu da wannan maganar?!"

"To Mama ya zanyi kefa mahaifiya tace amma kin hanani ganin khadija bani da nutswa idan na gaza hakuri na dauko wani zunubin wallahi hadda laifinki ciki Mama please, yanzu bakya sona kin daina damuwa dani baki san ya nake kwana ba haba Mama ni nefa Ahmad d'inki babanki d'anki wanda kikafi so a duniya."

Tashi tayi tabar mishi d'akin cike da jin nauyin maganar shi, aiko shima afusace ya bar gidan yana cewa,

"Yaukam bazai yiwu ba wannan wahalallen barcin da nake yi ba dani ba, babu wani lemon tsamin da zanshi...."












*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[3/11, 10:04 PM] 0mmer Farouk: *💗DR.AHMAD💗*

43

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO.....*💡
(Home of expert & perfect writer's)



*K*usan duk taji abinda ya faru tsakanin Ahmad da Mama dan haka agigice ta fara lalubar wayarta tana sharar hawaye daga kwancen da take, tajima tana ringing sannan ya d'aga wayar muryarshi tayi matukar yin sanyi da kaji kasan yana cikin damuwa.

Cikin muryar kuka ta fara magana,

"Ya Ahmad kadda kai min haka dan Allah ka rufamin asiri ka dawo gida kadda ka aikata wani zunubin wanda zamu samu kamasho muma, ka dawo gida wallahi zan kwana a wajanka ko Mama bata so amma kadda kaje wani wuri kaji dan Allah?!"

A kai-akai yake sauke ajiyar zuciya kamin yace,

"To ki daina kukan yanzu zan dawo."

"Nidai ban yadda ba ka dawo in ba haka ba wallahi bazan iya zama dakai ba sabida zanfara zarginka gara ka dawo yanzu nasan ko nisa ba kaiba."

"Toh shikenan ganinan amma in taddake a d'akin mu kinji ko?!"

"Toh..."

Ta furta tare da ajiye wayar, idanu suka had'a da Maman wacce tuni tagama jin duk wata magana da suka yi.

Idanun tane suka kuma kawo ruwa kamin tace,

"Mama kiyi hakuri tsoro na keji, wallahi tsoronake Yaya Ahmad bashi da hakuri ya riga yaje makura kiyi hakuri.."

"A'a toh nikuma menene nawa khadija? ai kunfi kusa Allah ya baku zaman lafiya da hakuri da juna, amma dai sai gobe zaki koma d'akin naku ko? sabida a d'an k'ara gyara shi.

Ba yadda zatayi tace,

"Toh Mama."

Goma saura ta sulale zuwa wajan mijinta domin tuni ya isheta da kira, lallab'awa tayi ta ajiye yaron kusa da Mama tayi tafiyarta wajan Ahmad, kusan cin karo suka yi a hanya harya gaji da jira zaizo ayi yanda za ayi, tana rungume jikin shi har gado ko kofar basu tsaya sakayawa ba suka fara shagalinsu domin ba k'aramin hakuri Ahmad d'in yayi ba shi kanshi beyi tunanin zai iya hakurin ba amma dai yasha wahala fiye da yanda masu karatu zasu fahimta....

Lokacin da tafiya tayi tafiya tuni malam Amadu aka fara sambatu da kiraye-kirayen sunaye sabida ba karamin gigitashi babyn tashi tayi ba, sosai ta temaka mishi har wajan asuba suna nanike da juna koya ta motsa saiya mai da ita jikinshi, sun manta da batun jaririn su abba da yake dama yaron bawani damuwa da tsotsan dare yayi ba hakan yasa suka manta dashi.

Kasa fita sallar asuba yayi sabida wani irin matsiyacin zazzabi daya sakko mishi, koda sukai sallah kuma nad'eta yayi ajikin shi yana kyarma itako tuni tafara mishi hawaye sabida tausayin shi takeji dan har ta fara tunanin ko yanada shafar aljanu.


MAMA kam jin kamar motsi kusa da ita ya sata tashi zaune tare da haskawa,

"Lahaula wala kuwwata illabillahir aliyulazim ni Habiba nan ta kwangarar dakai kenan ta tafi wajan mijinta, oh ni yaran zamani to banda shirme aida dashi ta tafi idan da ya tashi ni zan bashi Nono ko kuwa..."

Kuma haska yaron tayi idanunshi biyu yatsa kawai yake tsotsa, hab'arta ta kama kamin tace,

"Ikon Allah zamani..."

Koda tayi sallar asuba rungumar yaron tayi jikinta tana mutmushi idan ta tuna shirmen iyayen shi.

Koda gari yayi shaaa tuni Ahmad ya fara galabaita sabida aman daya keta shek'awa dan haka arud'e khadijan ta nufi d'akin Mama tana hawaye.

A tsorace Maman ta mik'e dan dama bawani barcin kirkine ya d'auketa ba sabida tana gudun kadda yaron yai kuka,

"Lafiya khadija?"

"Mama bashi da lafiya tun dare yanzu kuma amai yake tayi harya gaji."

"Innalillahi muje na ganshi."

Saida ta goya yaron sannan suka nufi d'akin yana kudundu ne a cikin bargo ya rufe har fuskarshi, sannu Maman tayi mishi kamin tace,

"Ina wayarka akira maka ko Hassan ne ya duba ka?"

Muryarshi tai sanyi sosai yace,

"Mama tana falo."

Khadija ta kira dr. hassan da yake abokin aikin Ahmad d'in ne kuma suna abotaka sosai sannan unguwarsu d'aya, saida tayi mishi bayani sannan yace gashinan zuwa.

"K'arb'eshi kibashi nono inje inrage ayyukan kamin yazo ya dubashin."

Zama tai kusa da Ahmad domin bawa yaron nono bayan fitar Maman d'akin Ahmad ya rungumota jikin shi yana kallon yaron kamin yai murmushi yace,

"Kinga be kuka ba da dadaddare gunta zai dinga kwana ma kawai ko?!"

"Eh..!"

Ta furta a hankali kamin tace,

"Ya jikinka?!"

Kirjinta ya matsa da karfi har saida yaron ya kware da nonon kamin yace,

Koma dai menene ai kune kuka jamin tunda da kika biyema Mama akaita jamin rai."

Shiru tayi mai tak'i yin magana dan tasan tsiya yake yi mata,


"DR. ya haka?"

Cewar dr. Hassan dake dariya, shima Ahmad d'in dariya yayi kamin yace,

"Kai nifa bana san iskanci kaje kakawo min magani kawai insha."

Ficewa yayi yana dariya itama dai Maman bata kuma bi ta kan shiba dan tasan ciwon berasa nasaba da tasowar kwantacciyar jarabarshi ba.

Sai wajan sha-biyu sannan ya warware nan da nan ya fara lalubar khadija, saima lokacin ne ta tuna da zafin dataji jiya da daren domin bakaramar wahala yaba taba.

Marairaicewa tayi tace,

"Kai yayana daga warkewar ka?!"

Ko kulata beyi ba sai da ya sami nutsuwa sannan ya rungumeta jikin shi yana sauke numfashi murya k'asa-k'asa tace,

"Khadija kin sauya da yawa wallahi jinake kamar in makale ajikinki na daina fita, ashe idan mace ta haihu k'ara canzawa take yi?"

Murmushi kawai tayi aranta tana cewa inda gyara ko, ai wannan aikin Mama ne.

Aminu ne ya zabga sallama d'akin da sauri suka rufe jikinsu da bargo kamin Ahmad din yace,

"Kai Aminu ya akayi?!"

"Mama ce tace akawo shi kuka ya keyi kuma a cire mishi kayan sanyin rana ta fara zafi..."

"To kawoshi nan."

Ganinsu cikin bargo yasa aminun cogewa saida Ahmad din yace,

"Kawoshi mana a'a Maman shi barci take yi."

Daga kwancen ya karbi yaron Aminu ya fita yana waka shi kuma ya gyara mai kwanciya ajikinta yace,

"Bashi yasha sai muje muyi wankan."

*****

Babu sauran wata b'araka tsakanin ma'auratan domin Mama ta tsaya musu tsayin daka wajan ganin zaman nasu ya d'ore amataki na adalci da kyautatawa juna, haka rainon yaron kusan awajanta yake indai ka ganshi hannun khadija to nono zai sha ya saba da Mama sosai sabida yanda take kulawa dashi kullum wajata yake kwana idan ya motsa tabashi ruwa, be tab'a yi mata kuka ba.

Ahmad ya fara cuku-cukun neman karatun khadija ya sami karin girma da transfer zuwa katsina dan haka cikin farin ciki ya gayama Mama tare da shawarar komawarsu gaba d'aya can, domin Maman taso kin zuwa sai dai tun alokacin khadija ta saka kuka tare da rantsuwar itama ba zata bishiba matukar Maman baza taje ba.

_Kunjifa surukai ko masu shirin zama surukan ya kamata musan irin zaman da zamu yi da matayen 'ya'yan mu tunkamin sufara mana adduar mutuwa sabida bak'in halin da muke nunawa a garesu."_


Ckin sati uku suka koma cikin garin katsina da zama sai dai sunbar Aminu a gidan malam Mamuda sabida makaranta idan ya kammala J.s sai ya k'arasa acan. satin su biyu da tarewa khadija ta fara zuwa makaranta inda ta samu Omar musa 'yar aduwa, bata da matsala da abba domin ya fara shan kamu wanda Mama ke had'a mishi na waken suya da madara har taje ta dawo be kosawa da jiranta shima d'an albarkar....










*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[3/11, 10:05 PM] 0mmer Farouk: *💗DR.AHMAD💗*

44

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO...*💡
(Home of expert & perfect writer's)



*K*ullum shike sauketa a makarantar sannan shi kuma ya wuce wajan aikin shi, yana matukar girmama khadija da duk abinda ya shafeta bejin kiwar yi mata duk abinda take so sabida bata rageshi da komai ba musamman wajan bukatarshi koda bata so takan jure tak'i nuna mai hakan har sai ya barta dan kanshi. kullun cikim gyaran jikinta take da kayan marmari da kamshi sam bata yarda yajita da wani tashi wanda ba kamshi ba, tana matukar amfani da shawarwarin surukar tata domin wasu lokutan ma ita da kanta take murzamata kankana da madara ko kuma kwakwa da jikakken dabino ko kuma had'in kanunfari da zuma, had'i ne masu matukar k'arama d'iya mace lafiya da kuzari tare da d'and'ano mara algush shi yasa kullum mijinta yake like da ita bata

Please Login or Register in order to submit comment