Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamin tace "Allah ciwo wajan keyi kabari har gobe nad'an k'ara warwarewa. Rungumeta yayi jikin shi kamin shima yace "kiyi hakuri amma bazan iya barinkiba nima nayi mamakin yanda na shige da kyar jiya kila sabida munjima bamu had'uba ne kiyi hakuri idan ina yi akai akai wajan zai saki kinji ko....?!"

Da zafi-zafi yake nemanta kaikace cinyeta zai yi da kyar ta samu ta temaka mishi yasami nutsuwa sannan ya barta tayi barci yana nanike da ita, tunanin yanda zai kawo zainab gidan ya fara baya jin zai sami matsala ta ko ina saita wajan mamanshi zai iya hakuri da khadija ita kadai amatsayin matarshi sai dai ba zai iya hakurin rashin haihuwar taba yana bukatar son yaga jinin shi zai jure komai matukar za,a barshi ya auri zainab sabida dalilin haihuwa kawai bawai dan khadija bata isarshi ba a'a yana samin nutsuwa fiye da duk yanda zai misalta, a haka har barci ya kwasheshi cike da tunanika kala kala.

Da asuba fitinar shice ta tasheta saida ya kuma samun nutsuwa sannan sukai wanka ya tafi masallaci, kokari tayi tafita domin shirya abin kari gabb'anta duk ciwo suke yi sai dai tasan dole ta d'auki juriya da hakuri tunda har ya riga ya dawo.

Sai da taci ta koshi sannan ta koma d'akinta har lokacin Ahmad be fitoba, dan haka wanka tayi ta shirya sannan ta haye kujera tayi kwanciyarta dan tasan tana shiga kai kanta gado to ya gama barcin kanta zai koma, kamin wani lokaci tayi barci itama.

Sai wajan sha d'aya na safe Ahmad ya tashi,murmushi kawai yayi daya ganta tana barci, sai da ya gama shirinshi sannan ya nufi d'akin Maman shi. bayan sun gaisa yayi breakfast d'in shi sannan ya fuskance ta duk da irin bugawar da zuciyar shi keyi mishi akan maganar da zai gaya mata.

"Ammh Mama dama akwai wata yarinya sunan ta zainab damu kayi karatu tare da ita 'yar funtuwace to mun dai-daita da ita zamu yi aure shine nace zan gaya miki..."

Zubami shi idanunta tayi tana yi mishi wani kallon kurilla amma sam takasa tankawa ma sabida tsananin mamaki da al'ajabi....!









*MAMAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€

[3/8, 11:16 PM] β€ͺ+234 805 777 9929‬: *πŸ’—DR.AHMADπŸ’—*

30

*NA MAMAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€

Edit by *Hajja ce*πŸ‘ˆ

*HASKE WRITER'S ASSO....*πŸ’‘
(Home of expert & perfect writer's)


*T*ajima tana kallon shi tare da mamakin furucin Ahmad d'in, can dai ta numfasa tare da cewa,

"Toh babana aini sam bamma fahimci inda ka dosaba balle in fahimci abinda kake nufi, ai saika fahimtar dani sosai ko ta yadda zan gane."

Cikin jin nauyi yace,

"Mama wata yarinya ce da muka yi karatu tare da ita shine..shine dama muka kulla soyayya yanzu so take yi in aureta Mama."

Wani mugun kallo tayi mishi wanda yasa shi gaggawar saukar da kanshi k'asa, kamin ta d'ora da cewa,

"Toh naji amma bada yawuna ba, kuma na gaya maka, yo ban dama kai d'in butulu ne babana me yayi maka zafi da har zaka k'ara aure haka? sabida Allah duk irin k'ok'arin da yarinyar take yi akanka baka gani yanzu da abinda zaka saka mata kenan wai kishiya?
To ba dai da amince wata ba domin nid'in ba butulu bace irinka domin ban mance da irin halaccin da iyayenta sukai mana ba kuma bana fatan na mance shi har abada, tashi kabani wuri tun kamin ranka ya b'aci ma."

Cikin sanyin jiki yabar gidan gaba d'aya, nan da nan ya shiga damuwa domin ba k'aramar takura yake shaba wajan ita zainab d'in akan yaje gidansu domin tuni itama ta dawo gida.

Abangaren maman kuwa kullun korar shi take yi domin yanzu ko zaman hirama ta daina yi dashi, itako khadija bata san me ake ciki bama domin ko afuska babu wanda ya nuna mata akwai wani abu.

Ganin fin sati biyu yana ta fama da Mama kuma ya kasa shawo kanta dan haka kai tsaye ya yanke shawarar tunkarar malam Mamuda da maganar domin bashi da wani uba bayan shi duk da yana tunanin be kyauta ba idan yaje mishi da maganar a matsayin shi na sirikin shi sai dai bashi da yanda zai yi dole shine zai iya shawo kan Maman shi d'in.

"Babyna kizo muje nayi miki wankan naga kamar kin gaji da yawa ko?"

Yak'en dole tayi mishi kamin tace,

"Eh ai kam na gaji amma dai kaje kayo wankan ka tunda kace fita zaka yi, ka gani banjima da dawowa daga makaranta ba kai kuma ina shigowa ka taramin wata gajiyar, yanzu barci na keji amma idan na tashi to zan kintsa kamin ayi la'asar sai ka dawo."

Cike da kauna ya sunbaci kuncinanta sannan yabar d'akin.

******

Daga masallaci suka dawo tare shida malam Mamuda suna tafe suna hira har suka iso gidan, azauren gidan suka zauna kamar yadda Ahmad d'in ya bukata.

Sunjima zaune shiru babu wanda ya tanka domin sai yanzu Ahmad d'in yake jin wani irin nauyi daya dabaibaye shi.

"Ahmad nifa babanka ne idan baka gayamin abunda ke tafe dakai ba wa zaka gaya mawa? karka damu zan fahim ceka insha Allah fad'i ina jinka."

Cikin nutsuwa Ahmad d'in yayi mishi bayanin komai, sunjima babu wanda ya kuma tankawa domin shikan shi malam Mamuda saida yaji babu dad'i domin har saida ya gaza hakuri ya tambaye shi, kodai akwai abinda khadijan kemishi amma yace babu komai kawai dai yanaso ya k'ara auren ne idan sunyi mishi izini.

Ajiyar zuciya malam Mamuda ya sauke kamin yace,

"Toh ai be kamata ai ita Maman taku ta hanaka yiba tunda har kana so, amma dai sai inga kamar daka bari aikin naka ya kankama kadda ka takura kanka kaji?"

Cikin jin nauyi da kunya Ahmad d'in yace,

"Baba dama ba yanzu ba ina so Maman ta amince ne tukunna, itakuma yarinyar agana da iyayenta sabida kadda tayi tunanin ko yaudarar ta zanyi, kuma ranar litinin zanfara zuwa aiki a babban asbt har ofis d'ina naje nagani kuma akwai albashi me tsoka sannan kuma ko yanzu akwai kud'i awajena Mama ce dama dai abin jin."

"Toh shike nan karka damu insha Allah da anyi sallar isha'i' zanzo gidan kaji ko?"

Cewar malam Mamuda.

****

kamar yadda ya gaya mishi kuwa haka aka yi domin daga masallacin ma kai tsaye gidan su Ahmad d'in ya nufa.

Khadija da murna ta d'a ne mahaifinta, shiko dariya kawai yake tare da furta

"zaki kayar da nifa khadija ke har yanzu baki san kin girma ba ne..?!"

kallonta yayi yana jin tausayinta kamin yace,

"Ina Maman taku take ne wajanta nazo."

"To baba kashiga tana ciki."

"Yauwa toh kiramin mijinki idan yana nan ya taddani wajan Maman taku."

Sam babu sakin fuska haka suka gaisa domin tasan dalilin zuwan shi wajanta. shi kanshi Ahmad d'in saida yasha jinin jikin shi balle da yaga sam babu walwala atare da ita hasalima ko kallon inda yake bata yi..

Hakuri sosai malam Mamuda yayi ma Maman tare da nasiha san nan ya d'ora da fad'in ta amince da auren domin babu wanda yasan me gobe zata yi.

"Haba malam yaushe ne zaka daina biyema shirman yaron nan?
toh nidai gaskiya ban amince ba sabida Allah duk irin kokarin da yarinyar nan take yi dashi shi begani shinema zai saka mata da kishiya? kishiyarma gogagga 'yar duniya tunda har waje tatafi karatu wama yasani ko iskancin su sukai tayi shida ita shine abin be ishe shiba zai aurenta, toni ban yadda ba in kuma yace dole sai yayi to sai dai ya saki khadijan domin bazan yadda ya tozar ta taba wallahi."

Cikin tashin hankali Ahmad d'in ya fara bata hakuri tare da gayamata cewar bazai iya rabuwa da khadijan ba kuma yana sonta.

Wata uwar tsawa ta daka mishi wadda ta tsoratashi da malam Mamuda kamin tace,

"Maza ka tashi ka ficemin a d'aki na kamin na illataka wallahi sakarai kawai shasha sha."

Jiyayi kamar yayi ta kurma ihu lokacin daya fita kuma sai yayi karo da khadija bakin kofa tanata zubar hawaye domin tajima da jin duk wata magana da suka yi.

Da sauri ya nufeta sai dai kamin ya k'arasa jikinta tayi waje sabida wani mugun takaicin shi takeji, tunaninta shine duk irin yanda take kyautata mishi amma shi tunanin shi naga wata kenan, kuka take yi sosai yana lallashinta, bayan shigarsu cikin d'akinsu sai dai ko sauraran shi ta kasa yi balle ta fahimci me yake cewa ma.

A bangaren Maman kuwa ba k'aramin aikin lallashi da nasiha malam Mamuda yayi ba kamin ya shawo kanta wanda har kuka sai da tayi sabida tsabar takaici, bata tab'a tunanin Ahmad d'in zai iya haka ba ta kunya ba, domin wannan abun kunya ne sosai sannan tasan yaja mata zagi wajan mutane kai ba itabama harta iyayen khadijan sai abin ya shafesu. koda ta amince sam kin yadda tayi ayi maganar yanda za agyra komai sai dai daga karshema cewa tayi sam babu ruwanta da hidimarshi yayi duk abinda yaga dama aishi ne ya d'aure mishi k'ugun yin auren.

Daga karshe dai dole malam Mamuda yabar gidan tare da tunanin yanda zai fara tsara hidimar fatan shi Allah ya bawa khadijan shi hakuri da juriya kodan tallafama maraya da yayi shima....







*MANAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€
[3/8, 11:20 PM] β€ͺ+234 805 777 9929‬: *πŸ’—DR.AHMADπŸ’—*

31

*NA MAMAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€

Edit by *Hajja ce*πŸ‘ˆ

*HASKE WRITER'S ASSO...*πŸ’‘



*S*am k'in yarda tayi ya rabi jikinta, dole ya koma gefenta ya kwanta batare da tunanin bacci zai d'auke shiba. sosai ya kejin tausayinta musamman yanzu da baccin wahala ya d'auketa amma ajiyar zuciya kawai take saukewa, gawani zazzabi-zazzabi daya keji kamar zai rufeta.

Tun asuba yaso ko magana ta hadasu amma ina kalma daya ce ta iya d'aurewa ta furta mishi, itace ina kwana daga ita bata k'ara ba.

kayan jikinta kawai ta canza tabar mishi d'akin gaba d'aya, wajan Mama taje suka gaisa sannan tace,

"Me za a d'ora Mama?"

Wani tausayin tane ya kama Maman dan haka ta rungumota jikinta kamin tace,

"kiyi hakuri kinji, insha Allah babu komai kibarshi yayi auren tunda ya nace muzuba mishi ido kawai, dama saida nace ban yadda da karatun sa a k'asar wajeba amma malam yazo ya matsa gashinan tun kamin aje ko ina ya fara zuwa mana da sabbin abubuwa kiyi hakuri dan Allah kidaina damun kanki kinji d'iyata..."

Hawaye tashare kamin tafara magana cikin kuka-kuka,

"Mama ya Ahmad be kyauta minba duk irin abinda nake mishi amma shine zaimin kishiya Mama kofa haihuwa banyiba?"

"Nace kiyi hakuri kirabu dashi tunda yanzu babu yanda zanyi mahaifinki yazo ya kasa ya tsare bani da wani abun yi domin ina jin nauyin mahafinki kiyi hakuri kawai."

Lallashinta taci gaba dayi har garin Allah ya waye kamin su shiga kitchen tare suka yi kunun tsayima da alalen leda.


Babu wanda ya kulashi ko wajan yin breakfast d'in dan haka sai yaji duk ya kasa sakewa ballema ya karya din dole ya tashi yabar gidan batare da sanin inda za shiba.

Dariya Maman tayi tare da mik'ama khadijan hannu suka kashe kamar wasu kawaye, ko abokanan wasa.

"Mama bari naje nayi shirin makaranta kinsan munata shirye-shiryen jarabawar fita."

"Toh madallah a dawo lafiya."

****

Cikin sati d'aya Ahmad ya fara fita hayyacin shi domin sam cikin gidan yadaina mishi dad'i sannan ga aiki daya fara zuwa duk zuciyar shi babu dad'i ga kuma shirye-shiryen biki domin tuni malam Mamuda yayi jagora zuwa funtuwa sungana da iyayen zainab kuma komai ya dai-daita ansa biki nan da wata biyu masu zuwa.

Tsakanin shi da khadija kuwa sai gaisuwa babu ruwanta da fitinar shi yanzu shi yasa harwani kumari tayi jikinta ya murje, sai dai tayi wanka ta shirya ta fice wajan Mama. to shima da yake yanzu be zaman gidan idan yafita takwas na safe sai biyar da rabi na yamma yake dawowa, burinshi yanzu ya sai mota kozai huta da wannan zirga-zirgar da yake fama da ita.

*****

A b'agaren amarya zainab kuwa burinta ya cika zata auri gwarzon namiji kamar Ahmad sam bata da damuwa, duk da cewa iyayenta sun raina arzikin shi Ahmad d'in da kuma kankantar shekarunsa da nata amma da yake diyar gatace shi yasa suka amince dashi domin suna sonta shi yasa suka amsa kuma suka bashi.
shirye-shirye suke yi sosai na bikin.


*****

Cikin ikon Allah su khadija suka fara jarabawa tafi daga secondary sosai tamanta da duk wata damuwa da take ciki, kuma dama shima Ahmad d'in ya samusu ido ita da Maman ta hidimar ginin shi kawai ya keyi domin gefen d'akin khadijan yasa ginin wani d'akin ciki da falo da toilet kamar dai na khadijan. Ana saura sati biyu biki suka gama jarabawan dan haka ana saura sati d'aya bikin Maman tace khadijan ta shirya zasu unguwa kuma ta d'ibi kaya, haka shima Aminu.

Charanci suka nufa batare da sanin shi Ahmad din ba sai dai kawai ya dawo gidan ya tadda babu kowa ga key din dakin khadija nan amma babu na kitchen balle na d'akin Maman.

Jiyai ranshi yayi mummunan b'aci musamman daya duba kayan khadijan yaga an d'iba da yawa, dama yana takaicin hanashi hakkinshi da take yi tun lokacin da taji batun auran shi wai yajira na amarya shine yanzu kuma zata fice bada saninshi ba.


*****

Komai da ake bukata na dangin amarya iyayen khadijane suka yishi duk da cewa ita mahaifiyar khadijan ba akan son ranta takeyin komaiba kawai dai tanabin umarnin shi mahaifin khadijan ne.


Ranar da aka d'aura auren, khadija kwana tayi kuka wanda daga karshe haddasu zazzabi da amaye-amaye ta dinga yi.

A bangaren amarya da ango kuwa burinsu ya cika dankuwa an d'aure aure lafiya kuma amarya ta tare a cikin d'akinta sai dai kamin danginta subar gidan saida rayukan su Ahmad din yayi mummunan b'aci dankuwa habaici da korafe korafe babu kalar wanda basu zubarba, atunanin su zainab ta wuce da ajin wannan gidan balle mutanen ciki.....










*MAMAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€
[3/8, 11:20 PM] β€ͺ+234 805 777 9929‬: *πŸ’—DR.AHMADπŸ’—*

32

*NA MAMAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€

Edit by *Hajja ce*πŸ‘ˆ

*HASKE WRITER'S ASSO...*πŸ’‘
(Home of expert & perfect writer's)


*πŸ€”Toh Ahmad ya bani gurin jama'@, Ashe haka ake bin novel din? To Maman Khady na gaishe da duk wani mai karanta DR AHMAD Allah yasa mu amfana da abinda ke cikin shi ya yafe mana kura-kuran cikin Amin*πŸ‘

INA 'YAN

HASKE FAN'S
HIKIMA WRITER'S
HUGUMA NOVEL
MUSHA KARATU na ybk2
HOME OF NOVEL na Xoxo
FEEDOHM Novell's
HAJJA CE novels grp?

*Duk ina mik'a gaisuwa a gareku naji comments d'inku Ahmad yace sai fa ya k'ara ahhee*πŸ˜…



*D*a kyar ya samu ya taushi zuciyar shi har ya samu nutsuwa, sannan ya shiga gidan bayan sawu ya d'auke.

Babu ko irin kunyar nan zainab ta rungumi mijinta tanajin farin cikin da bata tab'ajin irin shiba, sosai take kaunar Ahmad shiya sama ta yarda da auran shi a yanda yake duk da cewa tasan kwanannan shima zaiyi kud'in tunda ga aikinshi ya samu sannan da albashi me tsoka yana samu.

Rik'e k'ugunta yayi yana murmushi kamin yace,

"Amarya bakya laifi koda kin kashe angonki."

Bakinta ta hangame tare da fiddo da manyan idanunta tana dariya kamin tace,

"A'a bari fad'in hakan domin hakan ma bazai faruba."

Tana jikinshi ya zauna bakin gadon da ita kamin yabi d'akin da kallo gaskiya iyayenta sun narkamata dukiya domin ko kayan cikin falon abin kallone balle kuma na nan cikin bedroom d'in.

Kayan jikin shi ya rage itama haka sannan sukai alwala, kusan adaddafe ya samu sukai nafilar sabida yanda yake amatukar matse lallai bak'ara min hakuri yayi ba khadija ta azabtar dashi sai dai yasan ba laifinta bane laifin shine daya yimata kishiya alokacin da take tunanin zataji dad'in shi.

Bak'aramar wahala yaba zainab ba duk da cewa sam jikinta bekai rabin tsukewar na khadija ba amma yasan shine na farko daya fara saninta musamman yanda yaga tai gwale-gwale da ita har Allah ya isa tayi mishi kuka kam ai hadda majina lallai abin babbane, bata tashi k'ara gane kuren taba saida asuba dayakuma nemanta kusan da karfi yayi mata sabida gaddamar da tayi mishi shi kam ko ajikin shi domin har yanzu beji abin yakayi mishi yanda yake soba, ai saima ta godema Allah dayayi mata budaddan gaba domin sam ba irin na khadija bane khadija ta dabance duk lokacin da zai kusanceta sai sunsha wuya sannan zai sami hanya musamman idan sunjima basu had'u ba, itako zainab abud'e take domin inda zata hadu da jahilima zai iya cewa tasan wani namijin awaje to menene na damuwa? acewar Ahmad wanda ya fara gajiya da aikin lallashin zainab daya keyi, domin aranshima inda zata yarda toh kuwa da ya kuma.

*****

Da zazzabi ta tashi me zafin gaske Maman duk ta rud'e tunaninta ko duk dan auran da Ahmad d'in yayi ne.

"Sannu-sannu khadija muje ki gyara jikinki sai muje kiga likita kinji sannu nace ki daina sama kanki damuwa insha Allah komai zai wuce kinji?!"

Sai kusan Azahar sannan suka sami ganin likitan inda yayi ma khadijan tambayoyina gami da gwaje-gwaje inda daga karshe cikin ikon Allah saiga shi an tabbatar musu da cewar ciki na wata uku.

Mama tayi tsallen murna ta rungumi khadija ajikinta hadda hawayen farin ciki ashe da rabon taga jika itama,. Magunguna aka basu sannan suka yi gida cike da farin ciki da murna, Ammafa ab'angaren maman kawai, itakam khadija tsabar jin haushin Ahmad din data keyi yasa har cikin taji bata so.

Sosai Maman ta cigaba da kulawa da ita hakama tsoffin gidan abinda takeso shi suke mata, aiko nan da nan khadija tayi wani bul-bul da ita jikinta yayi laushi na musamman ga wani haske da tayi.

*****

Cikin kwanaki tara kadai zainab tafige ta lalace sabida tsabar jarabar Ahmad sam be barinta ta huta in dai yana gidan damma Allah yate maketa kullun yana zuwa aiki aida tuni tagama kad'ewa, abinda ke kuma bata ranta shine wani lokacin ko babu yaddarta da amincewarta yin abinshi ya keyi iyakaci dai taci wahala. sabida zullumi yasa duk ta rame gawani masifar tsoranshi da takeji kuma sai akayi rashin sa'a itasam bata da karfin sha'awa balle d'auriyar abin ita tunaninta tsabar zuba love kawai shine dan lashe lashe da tsotse-tsotse (romance) kawai na zamanin nan sai dagabaya tagane shirme ne kenan.


kwace yake saman gado amma ba barci yake yiba, ta shigo d'akin da sallama sai zuba kamshi ta keyi, wani mayataccen kallo yabita dashi, yayin da cikin zuciyar shi yake furta mace har mace amma babu dauriya, yanzu yanda taci gayun nan daya nuna yanaso zata fara kuka tare dajami shi Allah ya isa. idanun shi ya lumshe nan da nan wata kewar khadija ta lullubeshi jiya keyi kamar daya bud'e idanun shi kawai yaganta ajikin shi.

"Ahmad..!"

Zainab ta kirashi gyara kwamciyar shi yayi kamin yace mata,

"Uhumm ina jinki my zee."

Saida tayi d'an jim sannan tace,

"Cewa nayi dama ko wajan baban zakaje ko Allah zaisa asami su Maman su dawo hakanan gidan babu dad'i idan katafi aiki kuma kaga aikin ma yana min yawa dan Allah kace su dawo hakanan har yanzu bantab'a ganin Mama ba."

Murmushi yayi kamin yace,

"Zainabu abu me tagwayen suna kedai kawai kice kingaji dani ko?"

Sadda kanta k'asa kawai tayi amma aranta addu'a take yi Allah yasa ya amince inko ba hakaba gaskiya takusa tafiya gida domin jinsinta dana Ahmad dai baizo d'aya ba tabbas zai iya lahantata wataran.

Hannuwanta ya kamo ya rike yana kallon idanunta kamin yace,

"Nasan ina damunki zainab amma gaskiya sai dai kiyi hakuri domin tunkamin ki aureni saida na gaya miki wannan matsalar kuma kika amince daga khadija saike kune halal d'ina, ita khadijan ta gujeni kekuma kullum kuka da korafi ya kuke so inyi ne?
inje inbi na waje ko kuwa ya kikeso inyi? kusanfa daurewa na keyi zainab amma wallahi lokacin da kike bani naki sam be isata hasalima wani lokacin korafinki kesawa inji abin ya isheni alhalin bahaka bane, kid'an kara hakuri har khadija ta dawo nasan zaki sami sauki matsalata."

Wayar shi ya lalubo yauma kamar kullun number d'in arufe take besan meyasa khadija ta zabi ta azabtar dashi haka ba koda yake laifin Maman shine data d'orata akan hakan.


BAYAN WATA 'DAYA. khadija na zaune da Mama cikin kwanciyar hankali tasami nutswa sosai duk da cewa wani lokacin tana kewar mijinta amma tsabar kishi ke danne kewarta sabida tasan yana can yana cin soyayyar shi da amarya kilama yanzu yayi mata ciki dan tasan jarabar shi, tsaki taja afili kamin tace,

"Toh ma ina ruwana...!"

Mama dake gyangyad'i kusa da ita tace,

"Lafiyarki khadija?"

"Lafiya lau mama."

"To ai naji kina tsaki ne ke kadai yaka mata ki bud'e wayar nan yau domin mun kusa tafiya kinga makarantar su aminu ta tsaya sannan d'azu baba yayi min fad'a akan yaka mata in maidaki gidan ki."

Tun zuro bakinta tayi kamin tawuce dan lalubo wayar.

****

"kin san Allah zainab garama ki tsaya amma yau kota tsiya saina amshi hakkina kwana uku dai ai ya isheki hutu ina laifinama danaji tausayin ki."

"Dan Allah Ahmad kayi hakuri wallahi bana so bana son wannan abun haba kullum sai kace kaza."

Cewar zainab wadda ke kuka kamar wadda aka zane. tsaki yaja kamin ya cafkota jikin shi kusan da kokawa da komai yasami biyan bukata kuma saida ya kara sannan ya kyaleta, ya tashi ya bar d'akin, dakin khadijan ya nufa yana mamakin zainab anya batarasa aljanun dake sata kinshi kuwa ace abu kullun saida dambe duk irin son da take mishi?

Wayar khadijan ya fara nema kamar yadda ya saba kullun, aiko kawai yaji yau ta shiga jikin shi har wata rawa ya fara lokacin da yaji tana ringing, dauka khadijan tayi tare da sallama sam be tsaya amsawaba fatanshi kawai ta amshi sakon shi kamin taka she wayar cikin kakkausar murya yace,

"Kina jinako? Wallahi komai dare yau kidawo gida idan kika kuma k'ara kwana koda d'aya ne ban yafe mikiba khadija zaki kwana cikin tsinuwar Allah data mala'iku, kuma bazan taba yafe mikiba wallahi shawara tarage gareki ki dawo ko ki ci gaba da zama a inda kike....






*MAMAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€

[3/8, 11:18 PM] β€ͺ+234 805 777 9929‬: *πŸ’—DR.AHMADπŸ’—*

33

*NA MAMAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€

Edit by *Hajja ce*πŸ‘ˆ

*HASKE WRITER'S ASSO...*πŸ’‘
(Home of expert & perfect writer's)


*K*allon-kallo sukai tsakanin Mama da ita khadijan domin dukan su sunji abunda Ahmad d'in yace, tsora ya kama khadija sosai dan haka nan da nan tafara hawaye.

"To maye nayin kuka kuma? kitashi ki shirya mutafi yau zai hadu da fishina wallahi tunda shi mugune tashi ki kintsa bari nima in gyara jikina idan munje gidan lafiya nayi wanka, bari ingayama baba maganar tafiyar tamu."

Sai wajan bayan la'asar sannan suka sami motar da zata yi malumfashi, Aminu sai murna ya keyi da tsallen yau za akoma gida domin dama ya gaji da tuwon da akeci kullum agidan sai dai idan khadija na sha'awar wani abu sannan ayi mata shima ya samu yaci.

Har wani tsallen dadi yayi tayi cikin d'akin domin yasan duk wuya yau zasu dawo fad'an Mama kuwa tayi zai bata hakuri, dakanshi ya tashi ya fara gyaran d'akin khadijan saida yaga komai yayi mai yanda ya keso sannan yafita masallaci, saida ya fara lekawa d'akin zainab tana kwance har lokacin tana barcin wahala, dariya yayi kamin yace,

"Raguwa kawai zumata ta kusa dawowa ai nima na huta da dambe dake."

Da cefanen shi me kyau ya shigo yace gashi zainabuna tashi ki gyarama su Mama suna hanya insha Allah, aiko da saurinta ta tashi hadda dariyar farin ciki,.

Girki me rai da lafiya ta shirya, shi kuma ya share gidan tsaf da wankin bayin tsakar gidan haka domin Ahmad gwanin tsaftane kuma har yanzu bashi da kiwar taya iyalinshi aikin gida. kamin magriba sun gama komai ta shige dakinta domin wanka da sallah shiko d'akin khadija ya shige domin shiryawa shima.


Sai bayan sallar

Please Login or Register in order to submit comment