Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

binta yayi da wani mayen kallo domin gaba d'aya gani yayi kamar sauya mishi ita aka yi.

Bejima ba ya basu tsarabarsu kamin yayi alwala ya fice masallaci domin tuni anfara kiran la'asar.

"Khadija ga abincin shi ki wuce mishi dashi d'aki sannan ki aje mishi ruwan wanka, kinga idan yayi wankan yaci ya koshi sai ya kwanta ya huta ni sai managa duk ya rame."

khadija tace "eh gasiya ya rame Mama kuma saiya kara haske.

Saida ta gama shirya mishi abincin sanan ta had'a ruwan wankan sannanta d'aura alwalarta ta la'asar.

Tun kamin ta idasa sallar ya shigo kai tsaye bakin gadon su ya zauna tare da zuba mata ido.










*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[2/21, 11:03 PM] ‪+234 803 615 9696‬: *💗DR.AHMAD💗*

24

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)



*T*are suka shafa addu'ar sannan ta kalleshi tace, "sannu da zuwa ya Ahmad ya karatu ya hanya?"

Hannuwan shi ya mik'a mata tare da langab'ar da kanshi gefe guda. a hankali ta shige cikin jikin shi, tare suka sauke ajiyan zuciya kamin ya kuma matseta ajikin shi yana sauke numfa shi, jiyake yi kamar bashiba sabida yanda yayi kewarta.

Cikin sanyin murya yake furta "nayi kewarki khadija wallahi kullum sai nayi mafarkinki ashe kin kara girma ko ina na jikinki ya kuma bud'ewa da fatan kinyi murna da ganina?"

Murmushi kawai tayi mashi domin zuciyarta cike take da tsoran abinda yake nufi. Sunsunar wuyanta ya fara yana lumshe idanu yayin da yake kai hannun shi ko ina na jikinta, tanajin jikin shi ya fara kyarma tayi kokarin zame jikinta tare da ce mishi,

"Muje kaci abinci kadda ya sandare."

Tuni idanunshi sun kankance, a hankali yabi bayanta suka koma falon a baki tabashi sabida tsabar sangarta jinshi ya keyi kamar sabon haihuwa duk ci d'aya saiya sude mata yatsu tas sannan ta kuma debowa gaba d'aya ya gama shagala tun wajan cin abincin da kyar tasamu yayi wankan, ko mai be shafa ba yajata gado jikin shi har rawa yake wajan cire mata riga, masha Allah ya furta ganin yanda kirjinta ya bashi sha'awa tuni ya liketa a jikinshi kamar an lik'a mata cingum, murzarta yayi sosai ba tare daya nemi hakkin shiba, wannan tana jin dare akayi mata.


Sai kusan magriba sannan ya kyaleta tasamu sukunin fitowa waje lokacin tuni Mama tanata kwasar tuwonta.

"khadija! khadija!"

Turo bakinta ta yi tana yin kunkuni, Maman ta kalleta kamin tace "khadija me yasa hakane mijinki nata kiranki amma kinyi shiru wallahi babu ruwana."

Xikin shagwab'a tace "To Mama yanzu mafa da kyar ya bari nayi sallar isha'i ni wallahi nagaji kirjina ma ciwo ya keyi min."

Cikin lallashi Maman tace "haba khadija kidin ga hakuri mana kibashi lokacinki sabida Allah yaushe rabon shi da gida? kuma ya dawo amma harkin fara maganar kin gaji to wallahi kisama ranki hakuri da juriya domin mijinki ba hakuri gareshi ba, kuma dai dole gunki kadai zai iya bankad'e sirrin shi garama kiyi hakuri kita shi niban masan zaman me kike minba nan tunda kinci kin koshi."

Bakinta a dane ta tashi tafice, tana fita taji yayi sama da ita, ashe dama yana tsaye kunyar Maman ta hanashi shiga cikin d'akin. Kai tsaye gado ya direta yana murmushi, itako tsabar tsoro jitake kamar ta tsala ihu.

Rungumarta yayi yana shafarta aiko jikinta ya kama kyarma cikin muryar kuka tace "dan Allah kadda ka kasheni." cikin jin tausayin ta yace "bazan yi miki irin na watannin baya ba amma idan kinsaki jikinki dani fa."

********

Karad'in Aminu ya tashe shi daga daddad'an barcin da ya keyi, mika yayi a hankali tare da cire khadijan daga jikin shi, fuskarta ya kalla duk busassun hawaye murmushi yayi kamin yace "rigimam miya kawai."

Shiryawa yayi cikin farar jallabiya ya nufi d'akin Maman, saida suka gaisa sannan ya fara karyawa kunun tsamiya yau tayi da alala. yana ci suna hira inda take cewa "babana bawata matsalako sai naga dukka rame?"

"Babu wata matsala wallahi kewarku kawai kedamuna kuma kinga ga karatun ya fara mikawa."

"Toh Allah ya temaka suma su khadija ina ga daga wannnn hutun zasu shiga aji biyu.."

"Eh haka ne kam, Aminu yana karatun sosai ko Mama?!"

"Yana yi sosai kam aika san beda wasa."

khadija ce tayi sallama ta shiga cikin shirinta cikin doguwar riga ta kanti, babanta ya siyo matasu da yawa daya je kano.
Maman kawai ta gaida ta jawo abin karinta domin wata almirar yunwa takeji sosai. Tunda tashigo d'akin ya fita nutsuwar shi musamman kamshin dake tashi ajikinta, Maman tana kallan shi ita mamakin Ahmad d'i yake bata, oh zamani sai kaga yaro kamar besan komaiba amma sai kaga ba hakaba.

Tana d'ago kanta suka had'a ido harara ta wurga mishi hadda murgud'a baki. dariya yayi kamin yace "Mama d'iyar ki na hararata fa."

Tashi tayi ma tabar musu d'akin tana dariya, dawowa yayi kusa da ita tare da yimata rad'a akunne "kisauri kici ki koshi muje ki sallameni."

Ya idasa maganar yana murzar gashin kanshi tare da yin wani makirin murmush.










*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[2/21, 11:03 PM] ‪+234 803 615 9696‬: *💗DR.AHMAD💗*

25

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSO.....*💡
(Home of expert & perfect writer's)



*S*hiru tayi mishi tare da cigaba dacin abincinta sai da taji ta koshi sannan ta kalle shi. murmushi ya sakar mata kamin yace

"khadija tawa ni kadai."

Tashi tayi tayi waje yayin da shima yabita yana dariya, koda ya koma d'aki kiranta yayi tayi har saida Maman tagaji tace wa Khadija,

"Tashi kije khadija inba haka ba bazai bari mu huta ba kita hakuri kinji.?!"

Cikin sanyin jiki ta nufi d'akin, Ahmad d'in ya fara gundurarta sam be son zaman lafiya. Rungume ta yayi ajikin shi zuwa gado, fuskarta atamke sabida tasan sauran zancen.

Ahmad yana cikin jerin maza masu matukar son kasan cewa da mace koda yaushe, shi yasa yanzu daya dawo dinnan ya kejin kamar ya cinyeta domin har yanzu bejishi ya dawo dai-dai ba sabida yanda ya tara bukatar da matukar yawa, duk da cewa ya san yana matukar takurata sai dai bashi da yanda zai yi.


Yinin ranar cikin d'aki sukayi shi sai dai inza shi masallaci yake fitowa itako khadija sam babu lokacin fitowama wajanta, jitake kamar tagudu tabar gidan sabida wahalar da takesha a hannun shi.

Bayan sallar isha'i dasu kaje d'akin Maman cin abinci ko zaman kirki bata iyawa, tsoro ya kama Maman kadda ya lahanta musu yarinya tabani. sosai taci abinci kamin ta haye kijerar Maman tayi kwanciyarta kamin wani lokaci kuwa tayi bacci.

Kallonshi tayi tare da kankance idanu kamin tace,

"Babana naga alamar baka da hankali ko?
baka tunanin kaje kaji mata ciwo, sabida Allah duk irin hakurin yarinyar nan soka keyi dole saika kureta kallifa yau ko zaman kirki bata iyawa to wallahi ka kiyaye ni, na gaya maka tunda kai baka san zuruba, tashi kabani waje."

Cikin jin nauyi ya bar d'akin shi kanshi yasan be kyauta ba domin d'azu da kyar ya samu tayi tsarki sabida zafin da wajan kemata.
gaba d'aya ficewa yayi daga gidan.


Lokacin daya dawo gidan sai yayi sa'a Maman na bayi dan haka kai tsaye d'akin ta ya wuce tare da rungumar khadija wadda keta baccinta cak ya kokarta ya sab'eta.

A gado ya shinfid'eta sannan ya koma ya rufe d'akin, jallabiya kawai ya saka yarab'a gefenta ya kwanta tare da rungumuta cikin shi.


Duk wani hutu da ahmad yazo kusan akan khdijan ya kare domin tuni ta fita hayyacinta duk irin fad'an da Maman keyi da nasiha harta gaji tasa ka mishi ido saida yayi sati uku sannan ya koma school.

Khadija kam har rawar murna tayi ita kanta Maman ba k'aramar murna tayi ba daya tafi. su khadija sun shiga aji biyu yayin da komai yaci gaba da tafiya yanda ake bukata tana samun kulawa sosai wajan Mama haka iyayenta nan da nan ta dawo hayyacinta ta murmure.


Ahmad kuwa ba k'aramin yaki da zuciyar shi yayi ba kamin ya saba da rashin khadijan sai dai kullun suna waya karatu ya keyi sosai da sosai domin burin shi kenan kuma yana son ganin ya tallafama mahaifiyar shi ganin yanda tajajir ce mishi a rayuwa.










*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

[3/8, 11:16 PM] ‪+234 805 777 9929‬: *💗DR.AHMAD💗*

27

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *Hajja ce*👈


*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)





*R*ayuwa takan juya a hankali-a hankali komai ke tafiya wataran da dad'i wataran babu dad'i sai dai dole mu amsheta duk yadda tazo mana.

*BAYAN SHEKARA HUDU*:- Matashin saurayi ne zaune cikin turawa yana duba wayar shi kyakykyawa ne sosai domin kuwa farar fata kawai turawan dake tare dashi zasu nunamai amma fa badai zallar kyawu ba. sallama yayi musu tare da shigewa cikin d'akin da yake mallakin shi tun zuwan shi kasar amatsayin sa ns d'alibi.

Alwalar sallar magriba ya d'aura, saida ya gabatar da sallar, yana zaune har lokacin isha'i ya shiga ya d'orata sannan ya haye gado kewar gida ce ta ishe shi ya gaji da zaman fatan shi guda d'aya ne su idasa gama jarabawar nan ya koma k'asarshi ta haihuwa.

Wayar shice tayi ring kamar bazai d'au kaba sannan ya d'aga ba tare daya ce komai ba. Saida ta sauke a jiyar zuciya kamin tace "haba Ahmad me yasa baka jin tausayina kullum kokarin ka ganin kasani cikin tashin hankali kake wallahi ina sonka bazan iya rayuwa babu kaiba a cikinta ba dan Allah kayar da ka aureni koda baka sona wallahi zan iya zama da kai...."

Saida ya wani tab'e bakin shi kamin yace "zainab nifa bawai son kine bana yiba na gaya miki inada mata ko?"

Cikin sanyin jiki tace "eh ka gaya min."

Yace "to kinga bazan b'oye miki ba sannan ni maraya ne bani da mahaifi dagani sai mahaifiyata da kanina sai kuma matata, muba wasu masu kud'i bane hasalima bamu da komai sai rufin asiri kekuma d'iyar me kud'i ce amma in kinga zaki iya to babu matsala....!!"

Wani miyau ta had'iye kamin tace "ina sonka sosai Ahmad zan iya hakura da komai in dai zan sameka." Murmushi yayi kamin yace "ina cikin jinsin maza masu tsananin bukatuwa Zainab shima kin amince zaki aureni a haka?"

Jimmm tayi kamin tace "karka damu na amince in dai zaka aure ni zan jure maka."

"Kin yarda babu wani shagalin biki da za ayi idan mun tashi aure? domin bani da kud'in da zanyi su...."

"Na amince ahmad."

"Toho shikenan ki kwanta kiyi baccin ki gobe zamu had'u a school."

Sallama suka yi kowa ya kashe Ahmad na tunanin yadda Khadija zata ji idan taji cewar zai k'ara aure..

Cike da farin ciki ta kwanta yayin da shi kuma ya fad'a duniyar tunani, yasan kam zainab babbar yarinya ce domin iyayenta masu kud'i ne sosai a cikin garin funtuwa, itama karatu ne ya kawota k'asar kamar yadda yazo, Ahmad yana son babbar mace daga baya-bayan nan musamman yanda yake ganin surar ita zainab d'in tana da komai na cikakakkiyar budurwa tafi khadijan shi girma nesa ba kusa ba duk da cewa shekaru biyu da suka shige yaje gida kuma yaga yanda khadijan nashi tayi girma sai dai yana da burin ya kuma yin wani auren da gumin shi idan ya sami dama ya auri 'yar boko wayayya mai ji da kanta, sai gashi zainab ta shigo cikin rayuwar shi, kusan babu kalar hantara da kyarar da bai nuna mata ba amma ta nace mishi, sai gashi daga baya har yana kulata kuma bugu da kari shine yana matukar son ganin yaranshi shima, yayi mamakin da khadijan shi sam bata sami ciki ba har yanzu domin ko al'ada ta keyi to ranar data gama a ranar yake kusantarta dan kawai yaji ta samu ciki sai dai shiru kakeji wannan dalilin ya sanya tsoro ya d'arsu a cikin zuciyar shi na kodai beda lafiyane sai dai zuwan shi k'asar nan yasashi ganin wani likita ya gaya mishi lafiyan shi kalau sai dai in matar ta shice bata da lafiya, daga lokacin Ahmad ya fara d'aura d'amarar k'aro aure koda Allah zaisa yaga yaran shi.

Juyawa yayi ya kuma juyawa tare da gyara kwanciyar shi, wayar shi ya laluba tare da kiran number khadija, sai dai harta gama ringing amma bata d'auka ba dole ya hakura yayi barcin shi.

******

A bangaren khadija kuwa ta girma sosai domin a yanzu tanada kusan shekaru goma sha shidda, duk wani kyawunta da dirin jikinta ya gama fitowa bata da wata matsala ta iya komai na kula da miji gamida zaman gidan auren kusan ta haddace komai daya kamata ace tasani, domin Mamanta da Maman mijinta suna matukar kula da duk wani motsinta, tana zuwa islamiyya ta matan aure da ahmad d'in yasa mahaifinta yasa kata, sannan tana zuwa ta bokonta tunda gashi har sun shiga ss3 an zama 'yan mata. tana son mijinta fiye da yanda zan yi muku bayani domin Ahmad abin sone yana da kula sosai musamman akan abinda ya keso, kusan duk dare suna tare dashi a waya, kullun burinta taganta jikin mijinta tayi kewarshi sosai da sosai a b'angare guda kuma ga mugun kishin shi da take yi fatanta kawai kada Allah yasa ko magana da mata ya din gayi.
kullum lissafin ranar dawor shi take yi, kaika ce bitar karatu take yi..









*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[3/8, 11:18 PM] ‪+234 805 777 9929‬: *💗DR.AHMAD💗*

28

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
(MK)

Edit by *Hajja ce*👈


*HASKE WRITER'S ASSO...*💡
(Home of expert & perfect writer's)


*K*hadijat ce sanye cikin riga da siket na shadda me ruwan hoda tayi kyau sosai duk da babu kwalliya afuskarta, wani sassanyan kamshi jikinta keyi, kirjinnan nata cike yake da dukiyar fulani haka kugunta abud'e yake sannan taf da mazaunai cikinta ashafe yake irinsune matan da ake kira masu kirar coka-cola, gashinta har kafad'unta kuma baki sud'il dashi, shikanshi da kalar kamshin da ya keyi inbata mantaba yanzu shekara biyu kenan hadda wata d'aya rabonta da mijinta tayi kewarshi sosai da sosai.

Ddla murmushi ta k'arasa kusa da Maman daketa gyaran busasshen zogale, zama tayi kusa da ita kamin tace,

"sannu da aiki mama."

"Yauwa d'iyata sannunki jiya da dare babana ya k'ira lokacin ina shafai'da wutiri, kekuma kin yi barci sabida haka ki d'auko ki kirashi yanzu tunda naga be kira da safennan ba."

Kusan kamar jira ya keyi domin ringing d'aya ya d'auka tare da cewa "kashe na kira ki baby."

Tana kashewa kiran shi ya shigo saida ya sauke ajiyar zuciya kamin yace "babyna nayi kewarki da yawa ina cikin wani hali wallahi bukatarki zata kasheni ko tayi min illah..."

Cikin marairai cewa ta furta "ayya sorry yayana insha Allah babu abinda zai sameka muna tayi maka addu'a munfiso ka dawo garemu amatsayin na *DR.AHMAD* zamufi kowa murna idan hakan ta kasance...."

Kuma matse wayar yayi a kunnan shi kamin yace.

"Baby...!"

"Uhummm!" ta furta kawai tana sauraren shi domin wata sangarta yake mata ta musamman, "babyna abubuwana sun k'ara girma ko?"

kallon Mama tayi sannan ta nufi d'akinta tana murmushi, "ai yayana nikai nama girman nayi balle wani abu ajikina kai dai kawai ka gaya min yaushe zaka dawo nikuma inyi kokarin ganin kasameni yanda kake buk'ata da buri...."

wani mugun juyi yayi agodon shi, jiyake kamar daya bud'e idanun shi ya ganshi ajikinta kawai domin wadan nan shekaru hud'un da yayi Allah ne kawai ya tsareshi a daddafe yayi shekara biyu zuwan farko dole ya koma gida yayi sati biyu sannan ya dawo shinefa har yanzu bekomaba gawasu shekarun biyun sun wuce hadda watanni. A jiyar zuciya ya sauke kamin yace "ki tsumayeni nan da sati biyu insha Allah zan dawo gareku, zan kasance tare dake a koda yaushe domin nagama da kasar nan sai dai kuma da na dawo in da rabo."

Sunjima suna hira domin saida ta d'an kwantarmishi da hankali sannan ya kashe wayar itako da ihun murna ta nufi Mama ta rungumeta kamin tace "Mama nan da sati biyu zamu ganshi insha Allah saura kiris su idasa jarabawar su Mama.."

"TO Alhamdulillah mun gode Allah, Allah ya kawoshi lafiya.."

Tun daga wannan rana Maman tafara tsuma khadijan domin tasan dan nata da zafin shi zai dawo domin wan can zuwan da yayi har jinya saida khadijan tayi sabida tsabar fitinar shi.

Kusan kullun cikin gyare gyaren gidan suke d'akin khadija kuwa k'annanta tasa suka juyashi, kuma suka gyara komai tare da tayawar Maman.
kayan shi saida takuma wankesu ta gogesu sannan tafeshe su da turare ta adana haka nata.
a haka har ranar da zai dawo kasan cewar tasan ba dawuri zai dawo ba shi yasa taje makaranta inda daga nan tasanar da cewa za tayi tafiya tsawon sati d'aya sabida kadda ajita shiru dan tasan kobata fad'iba tofa bazai barta akwanakin taje ba.

********

"Dan Allah Ahmad kadda ka gujeni ka ziyarce ni koda sau d'aya ne wallahi iyaye na aure za sumin dana koma gida kuma ni kai nake so."

Murmushi yayi kamin yace "zainab kenan na cemiki babu komai insha Allah zanzo tunda ga waya, kinga yanzu dole sai naje nasanar da iyayena da matata sannan nasan ta yanda zan fuskanci naki iyayen ko?"

Kai ta d'aga mishi idanunta cike da kwallah sun jima suna sallama sannan suka rabu domin ita sai nan da sati biyu zata dawo Nigeria.

Zabi guda biyu Maman ta siyo akayi farfesunshi sannan akai mishi shinkafa da miya da wake, sai zob'o me dad'i da khadijan ta had'a mishi. sai yamma likis ya shigo gidan lokacin suna zaune khadijan tana yima Aminu k'arin karatun shi na islamiyya domin yau alhamis babu islamiyyar.

Tsalle d'aya Aminu yayi ya d'afe yayan shi, yayin da Maman da Khadijat murmishi ya cika fuskar su sannu suke jera mishi akai-akai har ya samu ya zauna kan tabarmar kuma kusa da Maman shi. bakinta har kunne take amsa gaisuwar shi, khadija ko sannu da zuwa tayi mishi kamin ta nufi bayin su domin had'a mishi ruwan wanka, da mamaki yabi khadijan da kallo kamin yace "Mama khadija ta girma sosai wallahi."

Murmishi Maman tayi kamin tace "to babana da haka kakeso tauyi ta zama? kaima baka ga irin girman daka yiba kamar ba babana ba, kakoma magidanci guda, kaje kai wanka sai kaci abinci ka huta likita bokan turai..."

A kunyace yabi bayan khadijan cikin d'akin wata nutsuwa yaji tana saukar mishi jiyake kamar an fiddoshi daga gidan yari musamman daya shaki kamshin d'akin matar shi. zama yayi gefen gadon su yana bin d'akin da kallo tare da tunano irin guruzun da suka sha shida khadijan shi, ai nan da nan tsigar jikin shi ta wani mimmik'e ya kama zare idanuwa.......











*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

*💗DR.AHMAD💗*

29

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *Hajja ce*👈


*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)



Leb'unan shi ya lashe tare dabin khadijan da lumsassun idanun shi wadda ke tsaye tana ciro mishi kayan da zai saka idan yayi wankan cikin sanyin murya tace,

"Ya Ahmad ga ruwan can na had'a maka."

Mikewa yayi ya isa jikinta tare da rungumeta ya fara sunsunar gashin kanta da wuyanta hannu wanshi kuwa tuni sun jima da fara yawo ajikin ta muryar shi a shak'e yake furta "babyna kin girma da yawa kin zama babbar yarinya ki gaya min meye sirrin?"

Dariya tayi tare da zame jikinta daga nashi tace "kai mafa kayi girma tunda harka fini kalli furkarka ga saje ga gemo, sannan kakusa ninkani tsawo ma, kuma ji kirjinka kamar me koyon karfi komai na jikinka ya kara girma da yawa..."

Dariya kawai yayi tare da kwab'e kayan shi ya shige bayin ita kuma ta kwashe kayan tare da gyara wajan.

koda ya fito tuni harta gama shirya mishi abinci acikin falonsu, tana zaune ya kirata tare da cewa "ina kika ajiye k'aramar jakar nan?" Khadija ta shiga cikin kunyar d'aki ya biyota ta bashi jakar a gadon su ya zazzageta maya-mayai ne da turaruka kala-kala tana zaune gefen shi harya gama shiryawa, sannan ya kama hannun ta.

kusan duk ita ta ciyar dashi sabida wata sangarta ya kemata ta musamman. tunda ya gama cin abincin ya like a jikinta kamar wani babyn da aka yaye, ya hanata sakat har sai da aka fara kiran sallar magriba sannan ya bar gidan itako wajan mama ta koma bayan ta gama gyara d'akin.


********

kun sani dai basaina baku labarin yanda daren nasu ya kasance bs domin kun fahimci waye Ahmad tun farkon labarin nan, khadija jitayi kamar ranar ya fara saninta domin tasha kuka kamar kamar me sai dai sam be d'aga mata kafafa ba balle da yake ganinta ta girma jikinta ya bud'e yanda yake bukatar ta.

koda ya dawo masallaci da asuba kasa barinta yayi dan haka tana gyara jikinta ta lallab'a tayi tafiyar ta d'akin Mama ta haye bayan Aminu tayi kwaciyar ta kamin wani lokaci tayi barcin mai nauyin gaske. sam Mama bata hanataba domin tasan Ahmad d'in bawani hakurin kirk'i ne da shi ba.

Ya jima yana jiranta yaji shiru dole barci ya d'auke shi ba tare da yaso hakan ba.

Maman da kanta ta shirya musu komai na kayan karin kumallo, tare suka karya gaba d'ayan su Ahmad yanata hararar khadijan sai dai ita sam tamaki yadda su had'a idanunsu waje d'aya.

Hira suka dasa a cikin d'akin Maman yawanci shi ke basu labarin makaranta da sauransu har kusan sha biyu sannan yace zai fita yaje gidan su khadijan sannan zaije banki.

kira wajan tara ya tadda awayar shi duk na zainab shaf ya mata da ita ma sai a lokacin, wayar kawai ya d'auka ya bar gidan.

Yana fita gidan ta kuma kiran shi, kuka tasaka mishi lokacin da taji ya d'auki wayar, saida tayi ta gaji sannan yace "ke dai zainab sam kuka be miki wahala sabida Allah yanzu kuma menai miki da zaki sakamin kuka?"

Jitayi kamar ta kashe wayarta sabida haushi sai dai ba zata iyaba tana son Ahmad d'in kamar ranta cikin muryar kuka tace "yanzu sabida Allah Ahmad hakama zaka ce tun jiya da muka rabu baka neminiba sannan kuma nayi ta kiranka amma baka d'auka ba kuma yanzu har kace wai mekayi min dandai kawai kaga Allah ya jarabeni da sonka ko Ahmad?"

Murmushi yayi me sauti kamin yace "naji to kiyi hakuri amma dai aikema kin san na gaya miki inada wasu iyalin ko? kokuwa so kike yi in barta alhalin shekara fin biyu bamu tare sai jiya dana dawo kuma sai na Kama wani abun?"

Jin tayi shiru, yasa shi cewa "to shi kenan yanzu dai kiyi hakuri zan kiraki da yamma yanzu ina hanya zanje wajen babana shikenan ko?"

Cikin shagwab'a ta furta "to kaddafa injika shiru kaji?" dariya yayi sannan ya kashe wayar, ba laifi itama ya fara son zainab d'in domin yana jin dad'in kulawar da take bashi.

Ahmad gari ya shige domin be wai-wayi gida ba sai wajan tara na dare, shima kusan san yine ya maida shi gidan. koda yaje gidan gaba d'aya kowacce ta sakayo kofarta dan haka yana rufe gidan dakin su ya shige, kudundune ya hangi khadijan cikin bargo, murmushi kawai yayi ya shige toilet sai da yayi wanka ya gyara jikin shi sannan ya labab'o ta bayanta ya kwanta benemi abinci ba domin ya ciko cikin shi wajan yawon shi.

Cikin barci takejin yana lalubarta tare da kiran sunanta, A hankali ta bud'e idanunta tana kallon shi arrnta sam bata son ya kusance ta sabida sanyi takeji kuma bata son wanka, sai dai tasan bata da yanda zata yi idan ya nema dole ta bashi.

Tashi tayi taje ta wanko bakinta sannan tace mai "ga abincin ka fa ya Ahmad."

Jawota yayi jikin shi kamin yace "A'a naci tuwo da baba d'azu banajin yinwa sai dai taki kawai....."

Marairaicewa tayi

Please Login or Register in order to submit comment