Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba shi damar kallon kowace d'iya mace ba awaje kullum cikin shaukinta yake ga yaronta shima tabarkalla kullum kara girma yake yi da wayau. waye yayi tunanin rayuwa zata zo musu a haka? sabida kowa yana tunanin rashin mahaifi shine durkushewar rayuwa, wannan ba haka bane domin Allah baya tab'a d'orawa bawa abinda bazai iyaba sai dai shi bawan ya d'orawa kanshi ma'ana be amince da kaddarar shiba.

Fitowarta kenan daga cikin makarantar sotake ta biya gidan wata k'awarta da keta fama da laulayi taga yau kwana biyu bata zoba taji wayarta nata ringing ko bata duba ba tasan mijinta ne domin kalar nashi daban yake dama.

"Hello.."

Ta furta cikin yanayi na rigima da gajiya yace mata,

"Babyna ya kike?!"

"Lafiya lau nake, ya aikin naka?!"

"Lafiya lau, sai kewarki data dameni baby ganinan a hanya zanzo in d'aukeki mudawo gida idan na huta zuwa anjima saina koma."

Murmushi tayi wanda har saida yaji sautin shi kamin tace,

"Toh shikenan amma ka tahomin da abu me sanyi yayana sabida yunwa nakeji sosai."

"Ok as you wish madam."

Samun wuri tayi ta zauna dan jiranshi yayinda take tuno mijin nata wai kewa sai kace da safe be taketaba amma yanzu biyu na rana harya fara maganar neman k'ari Allah ya rangwanta mai.

Har ya tsaya gefenta hankalinta baya wajen shi saida taji yana k'okarin d'aukarta sannan ta farga, gaishe shi tayi sannan ta zagaya ta shiga motar, madarar Hollandia me sanyi ya mik'a mata saida ta shanyeta tas! sannan tayi hamdala tana kallonshi,

Girarshi ya d'aga mata kamin yace,

"Kin dawo dai-dai ko?!"

"Sosai ma wallahi yunwa ba tayi ba."

"Ina fa tayi ai shi yasa zakiji almajiri d'an malam yana cewa iya yinwa zata kasheni."

Duk suka yi dariya koda suka koma gida kallo Mama tabisu dashi kamin tace,

"Ikon Allah daga ina haka ku kuma?"

Shigewa d'aki khadija tayi tana dariya yayin da shi kuma Ahmad d'in yayi tsaye gabanta yana sosar kanshi kamin yace,

"Mama ina abba ne banji motsin shiba?!"

"Hummmm Allah-Allah ya shiryaka babana amma dai ka dinga kula da aikinka kaji ko? ga abba can yau barcin rana ya keji."

"Toh Mama insha Allahu a ci gaba da yi mana addu'a."

"Muna kan yinta ai banana."

Da haka ya sulale zuwa b'angaran su,

"Baby na babu kara shine zaki gudo ki barni da Mama ko?"

Dariya tayi kamin tace,

"To ai tasan halin 'yan kayanta tsayawar me zanyi ni kuma..?!"

Tare suka watso ruwa sannan ta kula dashi saida ya sami nutsuwa sannan ya shirya yabar gidan itako nan yabarta tana barcin gajiya.

****

Bayan wata hudu:-

Rarrafe yaron keyi yanata zagaye gidan yana wasanninshi shi kadai kyakykyawa ne na gaske gashi lafiyayye yasan kowa na cikin gidan ga d'an karan b'arna kamar sun had'a kawance da b'era. da yake weekend ne sam kiriniyar shi ta hana uban barci wanda tuni ya keso yayi barcin amma wasannin da yaron keyi shi kawai ya keji akunnuwan shi.

Jikin shi ya zare daga na khadijan kamin ya tashi dogon wando ya saka sannan ya nufi tsakar gidan inda ya kejin hayaniyar yaron, nan ya ganshi ya fara tsallen a d'aukeshi, Mama dake gefe tana dariya tace,

"Ya hanaka barci ko? ai abba badai kiriniya ba."

Sama ya dinga cab'e yaron suna dariya kamin yace,

"Wallahi Mama motsinshi kawai nakeji ko barcin ranar ma ya kiyi, amma bari na kama Mamanshi kila in tabashi nono yayi bacci."

Yana farashan nonon yayi barci sai gashi su duka sunyi barcin har Mama wadda dama itama motsinshi ya sata zama tsakar gidan dan kadda yai wajen ruwa.

Cikin ikon Allah komai na tafiya tsaf yanda suke bukata basu da wata matsala kullum arzikinsu karuwa yake kamar yanda temakonsu ga mabukata yake karuwa lokaci zuwa lokaci suna zuwa malumfashi tare da charanci domin ziyarar 'yan uwan su.

****

"Wai kai dr. bazaka iya k'ara aure bane kaduba kaga yadda yarinyar nan take ta binka kaiko tausayinta ba kaji ne?!"

Cewar dr. Hassan wanda ke zaune cikin office d'in DR.AHMAD din suna hira, wani.......








*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[3/11, 10:05 PM] 0mmer Farouk: *💗DR.AHMAD💗*

45

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO.....*💡
(Home of expert & perfect writer's)

*KARSHE*💃🏻



*W*ani murmushin gefen baki yayi kamin yace,

"Dr. Hassan kenan, kana tunanin idanuna zasu iya kallan wata mace alhalin ina da khadija agida? To wallahi bari kaji wani abu da baka sani ba khadija ta zama wani b'angare na rayuwata na tabbata shigarta damuwa zai iya saka ni haukacewa, kowa ne bil adama daka sani yana son me kyauta ta mishi, khadija bata tab'a barina cikin halin damuwa ba kullum burinta ta gani cikin farin ciki to kana ganin nayi mata adalci idan nace zanyi mata kishiya?

Kin yi mata shine kawai sakayyar da zan mata a duniya, yanzu alhalin wahalata babu kalar wacce bata shaba, kuma kadda ka manta na baka labarin aurena da Zainab babu kalar soyayyar da bata nuna minba amma takasa iya zama dani balle wannan dana san dan wasu abubuwa kawai take sona.

Dr Hassan da khadija na saba ta zamani nazama ita na tabbata yanda muka koyama juna ba zamu iya rabuwa da junan muba domin khadija rainonace ninenan na raineta na kuma koya mata jurema bukatata tun tana kuka hartazo ta saba, tun ana zagin iyayenta yanzu har anbari, nikam bazan iya kara aure ba kai kodana cema zan kara na tabbata Mama bazata yadda ba ballema ni kaina bani da sha'awar yi my Dijama ta isheni rayuwar duniya."

Ajiyar zuciya me k'arfi dr. Hassan ya sauke kamin yace,

"Gaskiya ne dr. Ahmad kuma na fahimceka, Allah yabar kaunar tsakaninku ya kuma kore sharrin shaid'an azaman ku kuma dama gaskiya ya kamata khadija taji dad'i a wajanka kodan iyaye su sami kwarin guiwar kuma bawa yaro kamarka aure, sabida duk wanda yaga ka wulakantata tofa zaiga kayi butulci kamar yadda su sukai maka halacci domin maganar gaskiya mahaifinta babban mutum ne kuma ya rike amanarku sai dai muyi mishi fatan Alkhairi Allah ya kai lada mizani."

"Amin ai shi yasa nama fidda wani kwad'ayin aure araina domin babu wani abu dana rasa daga gareta wallahi duk jarabata bata tab'a guduna ba kullum cikin temakamin take koda bataso domin ni kaina nasan wani lokacin ina takurata amma sam bata nunawa ita dai burinta kadda inje innemi na waje, nasan ko aurena da Zainab kaddara ce kawai wallahi."


KHADIJA kenan wayayyar matashiya me matukar kyawun gani kusan yanzu ne take tashen balagarta ta cika ta batse idan ka ganta bazaka tab'a cewa wai tasan wani abu shi aure ba balle ai maganar yaro, tana da jiki me kyau sannan ga gyara da take samu kusan koda yaushe daga mahaifiyarta da surukarta boko ta fara ratsata shi yasa yanzu sai abun yayi matukar da cewa da ita.

Zaune suke fitowar su kenan daga dakin lecture ida ta k'awarta konace aminiyarta domin ita kadaice kawarta acikin makarantar sai dai wa inda ake gaisuwar mutunci dasu.

khadija ta kalli Fatima bayan sun zauna tace,

"Kai Fatee kin rame da yawa wallahi ki daure kidinga cin abinci sosai ke kanki zaki fijin dad'in jikinki kinga nima haka nai laulayin Abba har kuka nakema ya Ahmad idan zai bani amma kuma danaci sai inji dad'in jikina."

Yamutsa fuska fatima tayi tace,

"Wallahi lamarin ne da takura khadija sam banijin dad'in jikina ga fitinar Usman sam be son zaman lafiya be San yadda nakeji ba Sam.."

Dariya khadijan tayi kamin tace,

"Anzo wajan, ai in dai wannan matsalarce hakuri kawai zaki yi da addu'a amma wallahi akwai mata da yawa da suke fuskantar wannan damuwar, to amma kuma wani lokacin sai naga bawata damuwa bace indai zaki iya daurewa domin zaki kuma daraja a idanun shi sannan idan kin matsa kin rabu dashi bakisan wanda zaki fad'ama mawaba, kumafa akwai wa inda sukafi mazajen mu bukata ma kuma suna zaune da matayen su lafiya. kinga ni anyimin aure tunban san komai ba na rayuwa amma a haka naima iyayena biyayya lokacin da na fahimci manufarsu gareni domin temako ne, duk wanda ya temaki wani hakika kaima Allah zai temakeka, da babana be kai zuciyarshi ne saba yabawa ya Ahmad aurena ba na tabbata da Allah ne kadai yasan iyakar adadin yaran da zai lalata sabida yanada matukar karfin sha'awa kuma kila ciki harda ni domin yadda muke dasu babu abinda bamayi kinga da nai hakuri kuma na jure baga shiba yanzu hadda yaron mu na halak malak kuma sai dai in bada labari."

"Haka ne khadija shi yasa nima na ke son yin koyi dake wallahi sai dai nakasa wani lokacin jinake wajan ya koma kamar banawaba, sai naji duk na tsane shi musamman dana sami cikin nan ga laulayi ga lalurarshi da wanne zanji?!"

Dariya khadijan tayi kamin tace,

"Zan baki shawara guda d'aya kacal fatima, shawarar itace kimaida kayan marmari abincinki sannan ki dirfafi dafa zuma da mazarkwaila da kanunfari kinasha insha Allah zakiji wani lokacin da kankima kinaso, nikam bana huld'a da duk wani abu mesunan maganin mata amma nasan nafi karfin wulakanci ga mijina wallahi dan haka kikama mijinki tunkamin ya fara gajiya da gardamar da kike mishi yafara hango na waje inbe auroba ya bisu watarana. kinga ni yanzu bani da wata damuwa kullum cikin godema Allah nake da iyayena domin sunyi min babban gata..."

"Hakane wallahi nagode sosai khadija insha Allahu ni kuma zanyi amfani da duk shawararki na gode da tarayyarmu Allah ya raya mana Abba ya barmu tare da aminci."

"Kai ga mayen mijinki nan yazo khadija.."

Cewar fatima wadda ke nuna mata Ahmad daya faka motarshi daga nesa dasu.

Rungumarta yayi jikin shi tare da sunbatar goshinta sannan ya d'aga ma fatima hannu, tana like jikin shi ya bud'e mata motar saida ya zaunar da ita sannan yaza gaya ya shiga shima sukai gida babu ruwanshi da yawan mutanan dake kallonsu.

Bayan shekara biyu

Rayuwa tayi mawa in nan bayin Allah dad'i hankalin su kwace masu dana sani sunyi danasanin su damma Allah ya temake su sunyi kamin kasa ta rufe idanunsu, Abba ya girma sosai ga surutu kamar redio haka ga wayo sannan ga khadija da wani cikin, kullum cikin godema Allah suke domin babu abinda suka rasa ya rufamusu asiri lokacin da mutane suka so tona musu shi yasa ake son ka zab'i rufin asirin Allah bana mutum ba.

Dama dai ita rayuwa haka take yanda ka dauketa haka take zuwar maka inka kyautata niyyarka sai Allah ya cika maka inko kayi sabinin haka sai Allah ya barka da shaid'an ya taya ka jan ragamar zuciyarka Allah ya karemu daga sharrin zuciya amin.


_Duka-duka anan na kawo karshen wannan labari nawa me suna *DR.AHMAD*, Ina fatan inda nayi dai-dai Allah ya bani lada inda kuma nayi kuskure Allah ya gafarta min domin d'an Adam munsan kullun cikin aikata zunubi muke sai dai Allah ya ya femana Albarkar soyayyar shi da ANNABIN RAHMA (s.a,w)._

*SHARHI*

JIGON LABARIN DR. AHMAD SHINE.
Babban dalilina na kawo wannan labari shine, domin yiwa iyayen mu tuni akan amanar da Allah ya bamu, domin awannan zamanin ana yawan samun wannan matsalar, zaka ga k'aramin yaro da matsanciyar sha'awa amma babu kula daga iyayenshi har shi, shi yasa yanzu fyade da zinace-zinace suka yawaita.

Yaro zai nuna yana son aure amma iyaye su hana sai suce wai wani duka nawa yake da zaice aure zai yi? Kunsan dalilinshi na cewa aure zai yi? Idan baki saniba ke uwa kai uba kuna damar zaunar dashi ya sanar muku kuji sai ku magance mishi idan ba haka ba zakuji kunyar duniya kuje lahira ma kuma ku karb'i sakamako.

An yi a kusa dani nagani ganin idona inda iyaye suka hana yaronsu aure yanada shekaru 27 suka ce sai ya gama karatu yazo yayi suka ce sai ya sami aiki ya gina gida, kundai san yanzu samun aiki a Nigeria yanda yake be samu ba tsawon lokaci, 'yan mata biyu yayi ma ciki sannan ya gudu yabar iyayen kunga wa gari ya waya sunyi dana sani lokacin da babu amfani. Toh akwai iyaye da yawa masu wannan burin dan haka gara mu gyara tunkamin lokaci ya kure mana domin bako wane yaro bane zai yi tunanin tsare kanshi daga halaka ba kamar Ahmad, suna ganin da suyi azumi gara suyi zina da hannuwansu ko subi wata hanyar mummuna kanacan kana cewa wane yaron kirki babu ruwan shi kaza-kaza baki san me yake aikatawa a waje ko a d'aki ba, Allah ka shirya mana zuria ka tsare manasu.

Sannan sai ZAINAB,
Ta shigo gidan Ahmad amatsayin kishiyar khadija, to wannan wata kaddara ce da zata iya fad'awa akanki a kaina, mata da yawa bama san kishiya sam sai dai muna mantawa da rubutaccen Al'amari daga Allah wanda idan mijinki aure goma zai yi toh fa sai fa yayi shi ko kina raye ko kina mace duk kwalliyarki duk kyawunki duk dirinki duk nutsuwarki duk biyayyarki idan Allah yayi toh sai kin samu abokiyar zama.

Sannan wani shirme domin wannan dole akira shi da shirme da yawan mu zamu taso gidan mu muga mahaifinmu da mata biyu uku hudu, kilama da wayanki ya saki wata ya auro wata kintaso a irin wannan gidan sannan kizo kice waike bakisan kishiya kuma bazaki yarda da ita ba, wannan wane irin tunani ne? BABU kalar surutun da banjiba daga mutane lokacin da Ahmad ya auri zainab nayi mamaki sosai wallahi domin na san akwai babban aiki a gaban mu matukar haka tafiyar zata kasance, akwai ma wadda naji tace ita book in dai da kishiya bata karan tashi to me yayi zafi haka? zaman duniya ne bawai na kiya maba shekaru kalilan kike jira k'asa ta rufe idanun kifa A haka zamuje ma Allah da mummunan k'uduri ga 'yan uwan mu? Kuma wata kilama mahaifiyarka a ta biyu tazo ku itace ma ta hudu kuma ta shiga har aka haifeki amma ke kin hana wata ta shigo kuma idan 'ya'yanki duk mata ne kuma duk masu zuwa gurinsu suna da aure gashi suma na gidan sunce baza'ayi musu kishiya ba ki gyamin ya zakiyi da yaranki kuma suna son aure? Muyi tunani muyi ma kanmu adalci da hallaci dan Allah.


SANNAN SURUKAI:-
Da yawan mu yanzu bamu son auren wanda iyayen shi ke a raye musamman uwa mace, menene ya jawo haka?

Amsar itace mugun hali na zalinci sa ido da kuma wulakanci da wasu surukai suke gwadawa matan 'ya'yan su, kada mu manta daga lokacin da yaronki yayi aure tofa duk wani hakkin wannan mata tashi ya bar wajan iyayenta ya koma kanshi kinga hana warki yayi mata wani abu ko kyautatawa kamar kin sashi sab'ama Allah ne dan haka ki saurari hukuncinki wajan Allah domin shine ya tsara komai tun kamin zuwanki.

kudu ba kuga yanda Maman Ahmad ta rike khadija wanda daga karshe saida khadijan ta koma bata son Maman taje konan da can sabida son da take mata. kowace uwa tagari nasan baza taso akunta tama na taba tofa tunda bakiso kema kadda kifara yima d'an wani.

MALAM MAMUDA:-
Malam Mamuda yayi halacci kuma yarike amanar makota sannan ya fara ganin saka mako tun a duniya.

Eh mana tunda gashi Ahmad ya d'auke mishi dawainiyar komai sabida halaccin dayayi mishi kamin yaje wajan Allah yasamu saka mako me kyau domin yayi aiki me kyau na toshe wata kafa ta b'arna, sannan matar shi taba shi goyan baya inda ta toshe kunnuwanta daga dukkan wani gulmace-gulmace da mutane suka yita jifanta dashi.

GA KHADIJ KUMA:-
Khadija itace tauraruwar labarin dan Allah banda cigaba akwai wani na kasu data samu a rayuwarta? amsar itace babu taga ranar biyyayya dan kuwa gashinan tana karatunta tana da mijinta na nunawa sa'a sannan ga albarkar aure da Allah yaba su, kaddafa mu manta da yawa akwai iyayen mu da akaima aure tun basu da wayan kirki kuma suka zauna qalau, amma yanzu sai yarinya tayi shekaru akalla 20 kuma kuji iyayenta na maganar bata isa aureba toma idan zina batai yawaba meye zai yi yawa? abarshi a kunaso tayi karatu! karatu bawani illa bane dan tayi amma me ku aurar da ita sannan taje makarantar shifa aure daraja ne dashi wa innan igiyoyin da suka hau kanta sai kuga sanadin ta tasamu nutsuwar yin komai.

*DR.AHMAD*
Gaba d'aya labarin na shine mutane nata maganar jarabarshi tacika yawa, to wallahi kunji na rantse akwai mazan da suka fishi tsananin buk'ata kuma sunada yawa sosai acikin maza. sabida haka ni banga wani abun mamakiba dajin labarin Ahmad ke dai kawai amatsayin ki na mace kiyi addu'ar Allah ya baki miji dai-dai da yanayin bukatarki harda masu cewa wallahi babu masu irin wannan yawan buk'atar toh kuje da rantsuwarku amma mudena saurin rantsuwa akan abinda bamuda sani akai.

*ANAN NI MAMAN KHADIJA nake muku fatan Alkhairi ina fatan zaku tayani da addu'ar Allah yasa na haihuwa lafiya na gode sosai.*


*TO YOU HAJJA CE my hajja, Dota hajja nagode sosai da temakonki gareni domin kece me gyaran kusan dukkan kurakuran da ake samu a ciki da kuma rubutun, toh kundai san mace me ciki😃sai a slow na gode sosai may God bless you and jikata ihsan.*

_Sai kuma ke! Na gode da kulawarki da adduarki gareni Mamana ta kaina Maijidda musa Allah ya barmu tare._

*KUNGIYATA ABIN ALFAHARINA HASKE WRITER'S ASSO*
Allah ya kareku ya k'ara muku basira da hangen nesa Maman Khady na yinku Allah yabarmu tare

_Ummi Aisha, phatymah Zarah, Hajja ce, khaleesat hydar, miss Xoxo, billy galadanci, Aisha d/sabo, safiyya Huguma, Asmy b Aliyu, Afrah bhai, Faxyfation, Nana diso, Feedohm, Nuceeyluv, Ayusher Muhd Allah ya kara had'e kanmu_🤝








*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment