Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amsa musu ba kawai nuni yayi musu da d’akinta, aikuwa rige-rigen shiga suka farayi gaba d’ayansu dan suga me yake faruwa da maman.
Shigarsu keda wuya suka tarar da ita tana bakin gado zaune wayarta na hannunta sai dariya takeyi da alamuma tana chart ne abin yayi mata dad’i, mamaki firgici tsoro duka ya bayyana akan fuskokinsu, nan fa kowa yashiga zance da zuciyarsa to meyake faruwa?
”Ah.... yaran kirki sannunku da zuwa ”Mama Luba ta katse musu tinani da fad’in haka.
”Mama akace baki da lafiya? ”
Suka had’a baki wajan tambayarta.
”Ni kuma? A’a gaskiya ni lafiyata qalau babu abinda ya sameni lafiyar Allah nake, yanzuma nake cewa idanna karya zanje sashenku dan jiya da daddare naji iface-iface darene ya hanani fitowa ina fatan dai kafiya ko?”
Ta tambayesu tana qara kallonsu, rasa mema zasuce sukayi saboda tsananin mamaki,
”ya naji kunyi shiru, kodai wani abu yafarune jiyan, kufad’amin mana”ta fad’a tana marairaice fuska kamar mai shirin yin kuka ta d’auki yanayin alyini ta d’ora afuskarta. ”Kowa lafiya”suka bata amsa suma ile kallonta sukeyi kowa yana saqe-saqe cikin zuciyarsa.
Katse musu tinani tayi da cewa suzo su karya, duka abangaren suka karya suka d’an ta6a hira sannan suka tashi sukai mata sallama suka nufi 6angarensu.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
Tinda hafsa ta tashi take tinanin ina Kulu ta shiga? saikuma ta tina d’azu da asuba ta fad’amata 6angaren Mama Luba ba lafiya dan haka kawai data shirya ta karya saitayi 6angaren Hajiya ta gaisheta sannan tanufi 6angaren Maman. Fitarsu keda wuya ta shiga tana shiga ta tarar da Mama Luba afalo dafe da kanta tanakan kujera amma qafafuwanta da hannunta sai rawa sukeyi qwallah nata fitowa daga idanunta , atsorace Hafsa ta qarasa shiga tana tambayarta lafiya?
Itama kallonta tayi tare da sakin kuka sannan ta fad’amata duk abinda yafaru daren jiya hankalin hafsa ba qaramin tashi yayi ba dataji abinda yafaru, ahanzarce ta tashi tana kiran Haneef nan mama take sanar mata sunfita shida Larai mai aikinta, tambayarta ta sake yi again inasu Kulu? Nanma dai cemata tayi basu shigo ba.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”A gaskiya Kulu lamarinnan yabani tsoro, ni kainafa jiya kasa bacci nayi saboda naji ihun mama gajiyace ta hanani fitowa amma gashi yanzu muntaddata qalau bayan kuma Haneef ya fad’amana bata da lafiya”
”Uhummm Aunty Safiyya kind’au shekaru rabonki da kwanan agidannan, banda haka da abinnan bazai baki mamaki ba , ai senace miki tinbayan bikinku keda su Aunty Aysha rabonda gidannan ya zauna lafiya kullum cikin firgici da tsoro muke, gwandama Aunty Hamidah lokacin data haihu tazo gidannan yanayin dataga gidan yazama yasa ko arba’in bataiba ta tattara ta koma gidanta tsoronta kar d’anta ya mutu dan alokacin saidai kawai awayi gari ace wane ya mutu idan anje asibiti ace ba jinine ajikinsa, Ni wallahima Aunty Safiyya zuwa yanzu abin yafara bani tsoro ni yanzu agidannan kowa ma zarginsa nake kaina yafara kullewa duk inda kayi abinda zaka daban”
Ta fad’a tare da dafe kanta fuskarta akwai alamun damuwa qarara.
”Innalillahi wa’inna ialihi raji’un, Aikam daga yau nan d’akin zandawo da kwana bazan iya kwana ni kad’ai ba nabaro masifar gidana nazo gidanmu na tadda wadda tafita”
Ta fad’a tana kallon Hauwa .

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Bazai yuwuba wallahi sainaga bayan ta bazanji tsoro ba balle na tada hankali na wallahi indai na haifu kuma na amsa suna na saitayi danasanin had’a hanya dani dan ba qyaleta zanyi ba, kuma ina daf da qwace d’ana dan bazan bar mataba sai dai idan..................




’YAR GATAN MAMA✍️.


More comment more typing✍️.
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*


Dubun gaisuwata agareku masoya A WANI GIDA tare damuku fatan alkairi, ina matuqar godiya da qaunar da kuke nunamini, Ina alfahari daku.

Meenart 😍wannan page nakine kiyi yadda kikeso dashi😍.


🅿️5️⃣.


”Bazai yuwuba wallahi sainaga bayan ta bazanji tsoro ba balle na tada hankali na wallahi indai na haifu kuma na amsa sunana saitayi danasanin had’a hanya dani dan ba qyaleta zanyiba, kuma ina daf da tona mata asiri sannan saina qwace yarona dan bazan ta6a barmata shiba har sai dai idan ta yadda da sharad’in dazan gindayamata amma idan ta bijire to lallai zataga ta inda aikina zaifara”

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
D’aga waya tayi takira layin Kulu akashe saita canza akalar kirannata ga aunty Safiyya itama akashe haka dai tahaqura tad’an zauna tana d’ebe mata kewa kafin itama ta tashi taimata sai anjima.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Tinda su Kulu suka koma basu wani zauna sunyi hiraba saboda yau Kulu tana da baqo kuma tanason tayimai tarba ta musamman danya kwana biyu baizoba,Hafsa na shigowa 6angarennasu wani qamshin dad’i ya bugi hancinta wanda ya tabbatar mata yau akwai shagali na musamman agidan,bata wani 6ata lokaci ba haka tashiga kitchen ta zage ta taya kulu sukayi kayan tarbar baqi na girma ,yau kowa ya kalli kulu yasan tana cikin farin ciki.
”Hauwa dan Allah inason kid’an sammin kayan dad’innan nakira habybyna nima nabashi”Hafsa ta fad’a tana had’a hannuwanta alamar roqo tare da kashewa Hauwa ido d’aya.
”Uhummm Lallaima ke Hafsannan kin rainani da yawa,banda raini yaza’ai nazauna nayiwa masoyina sannan kice na baki kibawa wani gaddi wanda bai damu dakeba”Kulu ta fad’a rai ahad’e alamar bazata bayar ba.
”Nid’in zaki cewa baidamu dani ba,idan kwa hakane to kece NURADDEEN bai damu dakeba amma nidai nasan SADAM ya damu dani fiyeda yadda yadamu da kansa ehe,kuma dakike cewa kinsha wahala tare dawa akayi wahalar idan baniba?”
”Tom maida wuqar na yadda idan yazo yaci ragowar daya bari kid’ibar masa”
” Wai ke Kulunnan me kika d’auki Sadam ne wallahi baxaici ragowar d’an lukuti mai qaton cikiba ehe”Hafsa ta fad’a tana d’aga murya da alama ta fara harzuqa dantaji kulu ta raina Sadam d’inta,”Yi haquri ni duk zolayarki nake gasunan ni zanje nayi wanka idan yaso kafin nafito kid’ibi naki nima kihad’amun nawa waje d’aya saina d’auka ko”Hauwa tafad’a tana tafiya....









’YAR GATAN MAMA✍️
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



Marubuciyar
RAYUWAR MU
and now
A WANI GIDA.

Assalamu alaikum🙋🏻‍♀️Dubun gaisuwata agareku tare da fatan alkairi.

👸🏻Ayn@h @r@ab 👸🏻wannan shafinnakine kiyi yadda kikeso dashi🥰.


🅿️6️⃣.

Hakan kuwa akayi Hafsa tazuma Kulu nata a. mazubi mai kyau sannan itama ta zuba nata, kafin Hauwa tagama shirya har Nuranta yazo, Hafsa ce tamai sannu da zuwa takaimai abin ta6awa dake haka suka tsarawa kansu duk wanda yayi baqo acikinsu d’ayan zaikaima baqon abin ta6awa kafin me baqon tafito wannan kenan.
”Kai Hauwa wai yau saikin canza fuskarki ne zaki fita, wallahi ni ahakankima kinfi kyau amma kidage saikinyi kwalliya saboda wani qato mai qatoton ciki”Hafsa tafad’a tana qunshe dariyarta, Hauwa shiru tayi bata kulataba balle taji dad’i, hakan kuwa ba qaramin quluwa tayiba dan taso Hauwa ta kulata amma saita shareta ta nuna biyar tafita. Tana gama shiryawa tafara dube-duben kayan dazata saka saka wannan cire wannan hartakai inda tasaka wani less me azabar kyau gaba d’aya jikinsa baqine sai ratsin kore me turuwa da milk abinka da farar mace saiya yimata kyau ya amshi jikinta riga da siket ne tazauna tayi d’auri me V tayi kyau qamshi kawai takeyi kai idan kaganta sai kace daga qasar turawa tafito ba hausawaba , sallama tayiwa Hafsa wadda take ta cika tana batsewa dan Hauwa bata kulataba hakadai ta barta tayi tafiyarta.
Sallama tayimai murya qasa-qasa tare da sunkuyar da kanta qasa, shikuwa gaba d’ayama ya rikice yakasa koda motsa bakinsa saboda ganinta da yayi ba qaramin yimai kyau tayiba. Ta fuskanci gaba d’ayanshi ya rikice da ganinta hakan yasa ta qarasa shiga falon tazauna kujerar dake fuskantar tasa tasunkuyar dakanta sannan ta gaisheshi.
”Amincin Allah ya tabbata agareka ya haskena abin alfaharina”
abinda tafad’a kenan kanta na qasa tana wasa da zoben hannunta.
”Tare da kyakkyawar masoyiyata HAUWA KULU sarauniyar mata, Kullum ina godewa Allah dayabani ke amatsayin wadda zata zama uwar ’ya’yana,kimfi kowace mace sa’a domin kindace da halaye nagari ta hanyarki mutane da dama sukan zama na gari madallah da dake farin cikin zuciyata”Nuraddeen ke fad’a kai daga ganin fuskarsa kasan yana cikin farin ciki.
”Haskena idan bazaka damuba zanso ace kasa wani abu acikinka karna sakaka surutu cikinka ya rarake”
”Ah..! Haba aini kallonki kad’ai qosar dani yake balle kuma ace kina fad’amin dad’ad’an kalamai wanda suke sanyayamin zuciya....... Nidai nayi sa’a domin acikin maza ba kowa akewa barwar da akaminba, akabani mace mai kyau, addini, hankali, kamun kai, kinhad’a komai dan haka banda abinyi sai godiya , Nagode da karramawa kuma bari kigani”
Yana fad’in haka ya bud’e kwanukan da aka kawomai yana bud’ewa taga kowanne yaci lemonma yasha saura befi rabi ba, dariya ce ta qwace ta qwace mata nan da nan ta toshe bakinta kuma duk da haka bata dena dariyar ba. ”Au ninema abin dariyar?, aikam zaki shekara kinayi kinsan duk sanda zanzo wajanki saina tara yunwata saboda inason nazo naci had’ad’d’en girkinki me dad’i wanda ba’a manta d’and’anonsa”
Nura yake fad’i yana kallonta, murmushi suka sakarma junansu atare kafin suka d’ora da hira, haka sukaita hirarsu abin gwanin sha’awa dan matuqar kagansu sai sun birgeka dan ba qaramin dacewa dacewa da juna sukaiba.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡


Hajiya NAFI ta isa gidan yayarta lafiya tadad’e acan kafin ta dawo dan sai yamma sannan tadawo.
”KULU! KULU!! KULU!!!
Hajiya Nafi ke qwalawa kulu kira, Shigowarta kenan dan Nura bai dad’e da tafiya ba taji wannan kiran gaggawar , amsawa tayi da sauri sannan tahaura saman Hajiyan.
”Kulu tambayarki zanyi kuma koda wasa banso kimin qarya idan kuma kikamin saina sa6amiki ”
”Hajiya ina jinki biiznillahi indai nasani zanfad’amiki ”Tamayar mata kamar yadda ta fad’amata.
” Kulu jiya da daddare ina kikaje ? Kuma meya fitar dake acikin wannan darwn? Karki sake kifd’an abinda ba hakaba”
Hajiya ta tambayeta rai ahad’e kamar hadari.
Afirgice Kulu tad’ago ta kalleta kafin daga baya kuma taimata kallon d’arima tafiki awajena, saikuma tai qasa da kanta.
”Ba dake nake ba kika wani sunkuyar dakai kamar wata mutuniyar arziqi kimaza kibani amsa tinkafin raina ya 6aci”
”Hajiya Babu inda naje, kuma ni banfitaba kwata-kwata”tana gama fad’in haka ta tashi tayi ficewarta, Hajiya dafe kanta tayi da hannunta tana jinjina lamarin Kulu ita yarinyar nan ta isheta gaba d’aya halin mahaifiyarta tayo yarinya sai taurin rai, nikam indai ni ce saina binciko ina taje jiya kuma wacece wadda takama hanyarta ta kawota shashensu, nidai asanina bansan wasu mata agidannan masu saka wanacan kayanba, to wacece mai jajayen kayan? dolene na tashi tsaye dansena gano wane SIRRI Hauwa kulu take 6oyewa danni yanzu itad’inma ban yadda da ita ba. haka dai taita tinaninta har takoma d’akinta taci gaba da sabgoginta.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Mama dan Allah kici abincinnan idan baki ciba bazakiji sauqi ba kidaure kici kisha maganinki kinji mama”
Haneef ke roqon mama Luba taci abinci.
”Tom d’ana zanci kad’an gaba d’ayana ba’a dai-dai nakeba jikina duk ciwo yakeyi ”Mama ta mayarmai duk da daqyar take iya magana, haka ta daure taci abincin tasha maganin sannan bacci ya d’auketa.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Tohfa meyasa Hajiya ta tambayeni fitata jiya?
Me yasa ra 6ata rai kamar zata dakeni?
Kai...... Gaskiya akwai magana game da wannan lamarinnata dolene na tsaurara bincike akan kowa na cikin gidannan dannivyanzu kowama zarginsa nakeyi , kuma nayiwa kaina alqawarin saina tonawa duk marasa gaskiyar gidannan asiri”

Kulu ta fad’a tana buga qafa sannan ta shiga d’akinsu tana............










’YAR GATAN MAMA✍️






More comment more typing🥰
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*


🅿️7️⃣.



Kulu ta fad’a tana buga qafa tareda shigewa d’akinsu.
”Aunty Hauwa me hajiya tace miki naji kiran da alama ba lafiya”Hafsa ke tambayar Hauwa data dawo rai ahad’e kamar bata ta6a fara’aba,shiru tayi bata kulata ba ta nemi waje ta zauna tare da dafe kanta dantaji yafara sara mata.
”Wai ke Hauwa mene haka sainaitamiki magana amma kina shareni nifa na fara gajiya da wannan canjin da kikayi lokaci d’aya,Dan Allah Hauwa karki sawa kanki wata cutar ki sanyaya zuciyarki kizauna kinutsu muhad’a qarfi da qarfe mucigaba da bincike har ubangiji ya bayyana mana gaskiya,kuma ni idan zaki yadda da akwai shawarar danake ganin ita zamubi musamu hanya me 6ullewa”Hafsa ta fad’a tare da dafa kafad’ar Kulu tana kallonta cike da tausayi danta lura Yayartata na qoqarin saka abu aranta.Kulu ce ta juyo ta fuskanci Hafsa tare da riqe hannunta tafara magana kamar haka,”Hafsa Kiyi haquri ba hulaqantaki nake ba,duk sanda kikaji banbaki amsaba to banda amsar baki ne kuma kidena tinanin wani ciwo zai sameni kisa aranki kome yasami d’aya daga cikinmu da sanin Allah kuma bamai iya cutar damu inbada izininsa ba,danni nayi imanin babu qarfi ko iko d dabara wanda bana ubangijiba, komai yana faruwa da saninsa dan haka mun miqa lamuranmu gareshi shine zai mana jagora,Hafsa kaina ya kulle gaba d’ayana jina nake ba daidaiba gidanmu ya zama abin tsoro agaremu balle kuma ga baqin dazasu shigo wannan gida,kowa na gidanmu abin zargi ne kowa yana zargin kowa wannan wace irin rayuwa ce,kowa idan ya bud’i baki sai yace sirri sirridai wane irin sirri ne wannan”Tafad’a da qarfi tare da rushewa da kuka maicin zuciya,lallashinta Hafsa ta kamayi tare da kwantar mata da hankali duk da itama jitayi jikinta yayi sanyi ,suna haka saiga aunty safiyya ta shigo kallonta sukayi tare da kar6ar kayan hannunta ta zauna ta kama musu tambayoyi kamar haka.
”Nikam Hauwa kukan me kikeyi,naga fitowarki daga 6angaren Hajiyarmu kuma nashiga naga ranta a6ace kema nan nazo naganki kina kuka shin lafiya kuwa”
Hafsa tai maza ta tari Aunty Safiyya da fad’in,”Aunty Safiyya daman ko baki shigo yanzu ba dole zankira ki,tinda ta shigo tafad’an abinda yafaru take ta kuka nayi-nayi tayi shiru amma abin yaci tura”Hafsa ta fad’a tare da sakin kuka kamar wadda aka daka,”Hafsa mene haka ina tambayarki kema kina kuka,to acikinku wazaimin bayani kenan?”Hakadai suka ci gaba da kuka ba wanda yace da ita qala balle ya bata amsar tambayarta.Ganin haka yasa itama taja bakinta tayi shiru tare da d’aukar wayarta dantaga suna so su b’ata mata rai abanza a wofi.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Gidan yau acike yake da baqi dan haka kowane 6angare hidimar abinshi da abinsha na baqi akeyi saboda baqin dangin Abba ne sukazo gasu dayawa sakamakon anesa suke shiyasa sai lokaci-lokaci suke zuwa,ciki harda sa,annin su Hauwa-kulu da Hafsa su uku Fatima,Aysha da suwaiba.Gida ya hargitse da hidima 6angare daban suka sauka agidan inda ’yan matan suka ce sudai ad’akin su hafsa zasu dinga kwana haka kuwa akayi suka d’ibi kayansu sukayi b’angaren su hafsan,Yau Abba kowa yaganshi yasan yana cikin farin ciki sai kai kawo yakeyi yana ta nan-nan da ’yan uwansa,wajan Hajiya da mama sun zage kowacce sai bajinta takewa yiwa dangin mijinnata,haka dai suka wuni yau cikin murna da farin ciki,wannan kenan.


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Yau Hauwa-kulu ta gaji matuqa gaya saboda tasha surutu da kai kawo saboda baqi dan hakanema yau tana idar da sallar isha’i ta kwanta saboda tanason ta tashi da wuri.
Misalin qarfe d’aya da rabi na dare Hauwa ta farka da sauri ta tashi band’aki ta shiga takama ruwa sannan tayo alwala ta fito tad’an zauna saboda tana son ta tabbatar da bawanda yaga fitarta,tad’anyi mintina ahaka kafin tasa takalmanta tana sad’af sad’af tafice ahankali.Aunty Safiyya ce ta miqe itama saboda tintashin Kulu ta farka aikwa batai qasa agwiwa ba itama tabi bayanta,Suwaiba baquwar su kuwa daman ita batai bacci ba dan irin ’yan matannanne masu raba dare suna chartingda samari itama ganin su biyu sun fita itama tai maza tafito duk da batasan inda zasuje ba.


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Tinda Kulu ta fito batai ko’inaba sai hanyar gidan gonar gidan batare da tsoroba haka ta kutsa kai ciki taita tafiya ita kanta batace ga inda zatajeba,aunty safiyya ganin haka yasa ta fara gajiya ta tafiya ”Shin wai ina kulu takeso zuwane?”
aunty safiyya ta tambayi kanta gashi kuma bamai bata amsa ,ganin kulu na qoqarin yimata nisa hakab yas taqara sauri had’e dad’an gudu-gudu saboda taga kulu na qoqarin 6acemata.


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Tinda Suwaiba ta fito ta fara kalle-kalle tana tinanin to ina sukayi ne?
Tana cikin tinaninne taga wata mata tafito daga wani d’aki sanye da jajayen kaya dabaqin abu afuskarta hannunta d’auke da wata qwarya wadda baka ganin menene acikinta,tana fitowa da sauri tayi hanyar waje,ganin haka yasa Suwaiba bin bayanta dantaga wacece kuma ina zataje?
Tin tana tafiya tana binta ahankali hartafara yimata nisa saida tafara had’awa da gudu ...........


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Tinda Kulu ta fara tafiya bata tsayaba har.............






















’YAR GATAN MAMA✍️.


More comment more typing🥰.
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

Naji qorafinki kuma na kar6a da hannu bibbiyu🙌🏻Xeesha wannan shafin naki ne kiyi yadda kikeso da shi😘😘.


🅿️8️⃣.

Tinda Kulu ta fara tafiya bata tsayaba har saida taga saura daf ta isa inda takeson zuwa, batare da zato ko tsammaniba taga wata iriyar guguwa ta taso da qarfin gaske batai qasa agwiwa ba tatsuguna awajan tare da sunkuyar da kanta qasa saboda tinanin kar guguwar tayi gaba da ita, addu’o’i ta ringa jerowa bawani dad’ewa iskar ta d’auke yunqurinta na tashi tsaye idonta yakai kan wata silver sarqa dake qasa sai sheqi takeyi duk da qasar data bad’eta hakan bai hanata sheqi da walwaliba, sunkuyawa tayi ta d’auka ta qaremata kallo tare da damqewa sannan ta kalli kogon datake shirin shiga dakyau kafin ta tsaya tana tinani ”Kai.....! ni yanzuma shiga wajannan haka bai kamani ba dole sai nayi babban shiri tukunna”Ta fad’a ranta kafin juyo zuwa d’akinsu. Aunty Safiyya ganin tana qoqarin dawowa itama tayi sauri tarigata shiga d’akin ta kwanta kamar bataje ko’ina ba , Da sauri Kulu ta shigo tana shigowa ta bud’e kwabarta ta adana wannan sarqar data tsinta sannan tayo alwala tayi sallah raka’a biyu sannan ta kwanta.


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Tinda Suwaiba tafara bin matar na basu tsaya ako’inaba saida suka isa wajan wani surququqi. me azababben duhu da ban tsoro ba abinda kakeji sai gungunai da kakeji gwanin tsoro, Batare da Suwaiba ta kula ba sai kawai gani tayi matar nan tajuyo dasaurin gaske kafin tayi wani yunquri tini matar tadamqi hannunta tayi iya bakin qoqarinta wajan ganin ta qwace kanta amma ina tini matar tasa bakinta ta huda d’aya daga cikin ’yan yatsunta tatashi akan qwaryar hannuta bata saketa ba har sai da taga ta zuqe mata jini baki d’aya sannan tawuce ta barta anan.



🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Jinjina gareki JARUMA lallai acikin satinnan kin bud’e wuta wajan kawowa SARAUNIYA Jinin mutane masu wahalar samuwa SARAUNIYA na jinjina agareki”
Wata murya ta fad’a muryar abin tsoro tare da razanar da wanda yakejinta, Matarce ta duqar da kanta qasa alamun girmamawa ga sarauniyar tasu. Muryar nance tasake ta sake bada dautin.............
”Farin cikin da kike bawa SARAUNIYA yayi, kuma SARAUNIYA tace asheda miki gobe za’ayimiki kyautar girma awannan qungiya sakamakon nuna qaunah da kishi da kikeyi acikinta........ Sanin kanku ne wannan qungiya tamu nada girman gaske kuma duk wanda ke cikinta yasan d hakan, wajibine gaduk wanda yaga d’an leqen asiri yasan yadda yayi yakawowa SARAUNIYA jininsa idan kuma baiyi hakanba to lallai SARAUNIYA zata hulaqanta jininsa.....................



🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡


Afirgice Kulu ta farka sakamakon mafarkin datayi kuma ya gigitata, tana tashi batayi ko’inaba sai kwabarta nan ta d’auko wannan sarqar taimaza ta saka awuyanta sannan takoma ta kwanta sai haki takeyi, ”To wannan sarqar tawaye? Kuma meyasa nai mafarki and’auketa to koma tawaye sainabi diddigi, idanma ta wani ce agidannan ganinta awuyana sai sashi yai magana”Kuluce keta zance ita d’aya .
Kafin bacci ya d’auketa taji ana kirayen-kirayen sallah haka ta tashi tayi alwala tayi sallah suma sauran duk sukayi sallah masu komawa suka
koma baccinsu.....................



’YAR GATAN MAMA✍️.
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*


🅿️9️⃣.

Duk suma sukayi sallah masu komawa suka koma baccinsu........

Aunty Safiyya ce tafita saboda ta gaida baqi zuwanta keda wuya ta tarar dasu wasu sunyi jugum-jugum wasu kuwa ma kuka sukeyi kamar ransu zai fita, hankalinta ne yayi mugun tashi lokacin da idonta ya sauka kan gawar Suwaiba wadda take can gefe guda mahaifiyarta na gabanta ko qwaqqwaran motsi ta kasa yi balle tayi kuka ba abinda takeyi saibin kowa da idanu......

Abba ne ya shigo agigice rigarsa ahannu yana fad’in ”I ina... take suwaibar meya sameta, bazai yuwuba bata mutuba..... bata mutuba”Kai kana ganinsa kasan ba’a dai-dai yake ba duk yagama gigicewa.

Kafin kace me tini zancen mutuwar Suwaiba yagama zagaye gidan kowane saqo da lungu na gidan ya d’au zancen mutuwar, dukansu manyan su da yaransu suntaru a6angaren baqin masu kuka nayi masu tagumi nayi dukansu kowa da abinda yake saqawa acikin ransa kallon-kallo kawai akeyi tsakanin matan da ’ya’yan gidan, kowa nayiwa kowa kallon rashin gaskiya inda kuma kowa ya qudurci cewa sai ya bi diddigi yatona asirin mara gaskiyar cikinsu.

Sanda zancen ya isa kunnen Hauwa-Kulu ba qaramin tashi hankalinta yayi ba saboda tabbas jiya data shigo mutum hud’u ta tarar suna bacci bayan tasan su shida ne, Aunty Safiyya, Hafsa, Suwaiba, Aysha, Fatima da ita kanta Hauwa kulun, da farko tayi tinanin kota zagayane amma hartai bacci su biyar ne harzuwa safiya ita batai tinanin komai ba akai ashe fita tayi akasamu wani marar imanin ya kasheta ”Wallahi kozan rasa raina sai na binciko marasa gaskiyar gidannan” ta fad’a aranta kafin ta tashi tafita.

”Hauwa ina kike shirin zuwa yanzu bayan kina gani ko jana’iza ba’aiba?

”Hafsa yau inada babban uzuri shiyasa zanfita yanzu amma bawani dad’ewa zanyi ba kawai dai dan yazama dolene amma..... ” sai kuma tayi shiru taci gaba da shiryawa tasaka hijab d’inta taificewaeta.

Hafsa kam tarasa abin cewa dan abin ’yar uwartata yafara bata tsoro ”To waima ina Hauwa zataje anacikin wannan yanayin ” Tafad’a tare da komawa cikin mutane akacigba da zama.

D’aya daga cikin baqince tamiqe ranta amatuqar 6ace tafara magana kamar haka.

”Tabbas ICE yayi KARA amma banda haka yaza’ai yarinya daga zuwanta jiya yau ace tamutu gaskiya ’yan uwana kuduba wannan lamarin Suwaiba ba mutuwar haka kurin tayi ba lallai kasheta akayi.........

”HAJAR... Kishiga hankalinki mana wannan wane irin sa6o kikeso kiyi haka, Karna qarajin wannan zancen daga bakin wani ma bakeba ”
Hajiya ta fad’a wadda itace babbar cikinsu.

Hajiya NAFI ce ta kalli Mama LUBA itama ita take kallo atare kowace ta qurawa ’yar uwarta idanu inda dukansu abinda suke saqawa daban.

Tinda Kulu ta fita bata zame ko’inaba sai gidansu wata qawarta FAUZIYYA nan take fad’amata kasuwa tazo suje, basu wani 6ata lokaci ba suka wuce batare da 6ata lokaciba Kulu ta gama siyayyarta tas batare da tacewa Fauziyya ga abinda zatai dasuba haka suka koma gidansu fauziyyar sannan itama tadawo gida.

Sanda ta dawo gida tini ankai gawar Suwaiba makwancinta kowa yaci gaba da sabgarsa wanda yazamewa dole shi ne yake jimami, wannan kenan.


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Gaskiya Aysha abinnan yabani tsoro, kuma wallahi da gaskiyar Baba Hajar maganar datayi d’azu alamu sunnuna kasheta akayi bayan anzuqe jinin dake jininta......

”Fatima nima tinanin da nake kenan, amma tinda Hajiya tayi magana muma mubar maganar kawai, amma abinda zamui yau dukanmu bazamui bacciba sai munga abinda ya turewa buzu nad’i........

Haka dai sukaita shawarwari atsakaninsu har yamma tayi.

Dare yayi lokacin bacci yayi amma kowa nagidan yau ashirye yake yada ido yaga meyake faruwa agidan idan dare yayi.....

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡



Yauma kamar jiya Hauwa kulu ta tashi , bata 6ata lokaci ba tad’au ledar data dawo itadaga unguwa tashige band’aki da

2 Comments On A WANI GIDA
avatar
fatima-9-7-8

1 year ago

Reply

Masha allah

avatar
fatima-9-7-8

1 year ago

Reply

Yayi dadi allah yakara basira

Please Login or Register in order to submit comment