Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk wata sabga ta Abba bana shigarta bani da abokan hira inba su Hafsaba dan alokacin ko Safiyya bana kula da ita kamar yadda nake kula dasu saboda harna koma ga mahaliccina bazan manta da Ameena ba.....

Akwai wata rana da Abba yakirani domin yanason yaji silar canzawata tindakwa yafara magana harya gama bantanka masaba hakan yasa ya zuciya ya watsar dani gaba d’aya....
Yawan tinanin danakeyi shiyajamin ciwomai tsanani wanda har seda takai da mahaifiyata tazo dubani kasancewar ba gari d’aya muke da itaba saita kwana anan gidana kwananta d’aya washegari tana shirin tafiya wani hadari yahad’o nankwa akafara ruwa kamar da bakin qwarya hakan yatilastamata sake kwana agidana inda washegari muka wayi gari mukaga tarigamu gidan gaskiya.......
Hajiya Nafi tana zuwa nan tafashe da matsanancin kuka maicin rai sannan taci gaba.......
Asannan bansan shine yakashetaba kuma band’ora masaba saboda tinanina ajiline ya risketa agidana ashe mugu azzalumi shiyakashen mahaifiyata sam bansaniba sai yanzu amma dana sani wallahi da kisana bazai tsaya iya inda nayiba wallahi dasenaga bayan danginsa baki d’ayansu.... bansaniba sai yanzu daya fad’a danni yaqina inayine akan abokiyar zamana mai amana da gaskiya wadda bata kwana da wani aranta balle ta cutar da shi yauda ace nima nayi halinta da d’abi’arta daban d’aukarmata fansaba to qaddara ta riga fata.....
Tin daga wannan lokaci sena fara neman hanyar dazanbi domin naga bayan Abba kamar yadda yaga bayan Ameena haka na fara shige shige domin naga bayansa harseda Allah yakaini gun wata hatsabibiyar mata wadda take bada magani tindaga kan maganin mata har asiri duka bawanda batayi ana kiranta da SARAUNIYA👸🏻nan naks fad’amata matsalata nace sonakeyi asakama Abba ciwon da zai gwammace ace yarigada ya mutu, shewa tayi da dariya lokaci guda sannan tabani wanj magani tace nasamai a abinci indai yaci angama sannan tabani wata alewa aqaramar leda tace nikuma nasha wannan iya wuya bazai sha jininaba sannan taban wata tace nabawa yaran suduka suma sharrinsa bazai samesuba cikin ikon Allah tinda nakoma gida narasa alawar yaran narasa danhaka dare nayi sena d’auki tawa nasha sannan nakwanta bacci, tin awannan rana nafara mafarki inacikin wasu mutane kayanmu iri daya kuma dukanmu bamuda abinci saijini awashe gari bansamu nutsuwaba harseda nahad’u da mai aikina hanne aikuwa na shanye jininta tasss agaskiya nasha jinin mutane da dama saboda indai naga mutum alokacin ina cikin kwad’ayi tofa saidai wani ba shiba dan take zanzuqe jininsa na barsa anan, haka nad’aukarwa kaina alqawarin duk wanda naga Abba yanaso sain shanye jininsa tsaf bantaba tinanin asirina zai tonuba sai yau.

”Niduk ba wannan nakeson jiba sonake naji tayaya sarqarnan tazama taki”

Barister Hashim yafad’a yana kallon H. Nafi.....

”Am..... Barister namantane da zancenta, Wannan Sarqar nasameta ne awajan SARAUNIYA akwai ranar da naje qungiya sai sarauniya take fadamin mijina yananan yana neman auren wata mata LUBABATU kuma sam lubabatu bata haihuwa amma shuumace taqarshe dan haka nakar6i wannan sarqar itace zatasa baza’a taba ganeniba harsai idan nasalwantar da ita, nikumanariqi sarqata da hannu biyu dan bansan yadda akai tabar wuyana taje hannun Kulu ba, amma ayadda nasa araina rabon 6arnata tatsaya hakane shiyasa narabu da sarqata.

Haka itama tagama bayinta akayi gefe da ita sannan aka buqaci Mama Luba tafito anason jin Haneef dan wanene❓
Wani shu’umin murmushi tasaki kafin tabud’i baki tace.....
”Tabbas Haneef bad’an Abba Hasafi baneba amma ni yaronane, bari nayimuku yadda zakugane tinda ran wanka ba’a 6oyen cibi🤷🏻‍♀️.
Ni Luba naci dubu sai ceto tinkafin na auri Abba narigada nasan halinsa tare dana matarsa gaba d’aya bazan 6oyemuku ba tinda yau ranar fito da komai ne ni tin ina gidanmu sannan banyi aureba tin ina makaranta nafara bin malamai da bokaye ’yan tsibbu sanda nafara zuwa wajan wani malami ne wanda mutane ke iqirarin aikinsa yana ci da wuri togunsa mukaje da qawayena saboda munason ayimana aiki akan jarrabawa domin mu munadacikin wanda karatu bai damesu ba dan asannan mune fitinannun makaranta amma kuma saimukeso muci jarrabawa saboda samarinmu suga munsamu sakamako mai kyau todaga wannan sena zama dukkan wani al’amarina banayi senaje gun wani yadubamini kuma duk abinda yagayamin tomshine gaskiya, ahakane nadage dabin malamai da bokaye sannan nad’auki mummunan quduri nasakashi araina nadage sam bazanyi aureba sena samu me shahararren kud’i wanda duniya ta sandashi wanda idan na aureshi ni da mutuwa mun raba hanya........
Yadda nabawa malamai gaskiya ban bawa kowa ba saboda nikainama ban yadda da kainaba sai naje andubamini..
Ahakane watarana garin shige-shige na haka naje gun wani malami boka nafad’amai nadad’e agidanmu duk qannena sunyi aure sunbar ni kuma duk masu kud’i suka aura nikuwa talakawa ke neman aurena masu kud’in kuwa sedai irin wadanda babana yake cewa zaibasu ni, wanda nikuma banyadda abadani ga wani ba, haka nabujuromai da zancen ABBA HASAFI saboda yadda sunansa yake yawo awannan lokacin yafad’amin eh auranmu zai iya yuwuwa amma senasha wahala tare da bada kud’i mai yawan gaske, haka naitaiwa QAURA 6arin kud’i duk abinda na mallaka dama wanda yake banawaba haka nadinga kawomasa saboda ajawo hankalin ABBA HASAFI gareni.....
Tsafi gaskiyar mai shi..... Hakance ta tabbata gareni batare dawani 6ata lokaciba segashi yana neman aurena kanshi tsaye nikuwa naita garashi kafin daga baya nabada kai komai yayi dai-dai.......
Bayan na aureshi seda na shekara d’aya batare dana ta6a koda 6atan wata ba asannan nikuma naqagu naga nasamu rabo saboda nasamu rabo me tsoka acikin dukiyar Abba idan yamutu......
Ganin lokaci zai qurwminne yasa na shirya na tafi gurin QAURA domin inason duk yadda za’ai na haihu agidan Abba hakan shi ne cikar burina na biyu........
Na yake sanarmin yaduba sam ba haihuwa tsakanina da Abba, matuqar inason na haihu agidan sai dai idan...........




🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Dan Allah ina neman afuwarku sakamakon jina da bakui jiya ba, sannan ina neman addu’arku gareni banjin dad’ine...... Ina godiya da soyayyar da kuke nunamin........
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Allah kajiqan magabatanmu ameen👏.










’YAR GATAN MAMA✍️.
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*




🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

🅿️2️⃣0️⃣.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡


”Nan yake fad’amin yaduban sam ba haihuwa tsakanina da Abba Hasafi dan haka saidai idan zan amince masa to shine zansamu ciki, alokacin bijirewa nayi saboda yadda na kalleshi naga ba qaramin rainani yayiba dan sam Qaura bashida kama mai kyau balle ace wata mace zata yarda dashi samni qyanqyaminsama nakeji amma yau nizecewa haka, cike da takaici natashi natashi na barshi anan....
Tinda na koma gida nakasa tsaye nakasa zaune sai tinanin maganar Qaura nakeyi saboda sam yadagulamin lissafi, wayata nad’auka nakirashi tare da tambayarshi kozan iya zuwa n haihu da wanj ba se lallai shiba?
Nan yake gayan hakan bazai yuwuba lallai sedashi idan kuma naqi to zanyi danasani nan gaba nikuma asannan zuciya ta d’ebeni nafad’amai maganganu marasa dad’i inda shima yace to na haihun yagani.....
Haka narabu dashinakoma wajan wani wanda mabiyansa ke fad’in aikinsa yanaci sosai to shima hakan take bata canza zaniba dan haka kawai senaje nanemi wani saurayina MUJAHEED wanda nake mutuwar qauna tin ina gida matsalarsa kawai talakane amma badan hakaba dashizan aura.....
Munkai ruwa rana ni da shi kafin ya amince da buqatata amma saida na mallakamasa dukiya mai yawa sannan ya yadda dani, haka ya yadda na maidashi mijina ta qarfi da yaji har lokaci yayi na haihu sannan narabu dashi, kafin na haihu ba qaramar wahala nasha ba danseda na kusa rasa raina sanadin haihuwar Haneef......
Cikin sabon tashin hankali na shiga wanda banta6a tinanin zan shigeshiba arayuwata dantin ranar dana haihu bankuma baccin arziqiba kullum cikin firgici da tsoro nake kowace rana da zarar dare yayi tofa kwanciyar hankali ya qaremini saboda koke-koke iface-iface su zasu zama abokan rayuwata cikin dare, tin abin bayabani tsoro harya fara bantsoro saboda kullum ganinake Haneef yana canzamin yau ya rikid’a gobe yadawo haka yaitayi har girmansa, Lamarinsa yanabani tsoro dan hakama nafara tinanin komawa wajan Qaura saboda naji kodai canzamin yarona yayi tosai kuma wannan abuyazo yafaru......
Nice wadda na fara shigar da qara tinkafin ’yan uwan marigayiyar suzo nice nafara zuwa saboda inason alhakin kisan yahau kan Safiyya, bandan komai natsani Safiyya ba saidan nasan cewa bayarinyar gidan bace ba amma kuma ba kowa yasani gashi tana yadda takeso agidan Abba yamaidata kamar yarsa ko yaransa baya musu abinda yakewa Safiyya wannan shine dalilin dayasa na tsaneta natsani ganinta.
Haka tagama bayaninta idonta nakan Safiyya wadda duk tinaninta yanagun su Hauwa Kulu dake asibit.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Alk’ali ba k’aramin girgiza yayi dajin lamarin wad’annan mutanen ace gabad’ayansu babu tsoron Allah aransu? Lallai lamarin wannan gida ya qazanta za’a dad’e baasamu marasa imani kamarsuba, gyaran murya yayi kotu tayi tssiitt kamar ruwa ya cinyesu.

”Innalillahi wa inna ilaihi raji’un........ Abinda bakunan mutane sukahau fad’a kenan sakamakon ganin yadda Abba yafara zama acikin lokaci kad’an......
Tashin hankali wanda ba’a samasa rana, batare da zato ba segani akai harshen Abba gaba d’aya ya zazzago yayi bak’i wuluk dashi kamar bashi ba dukyacanza acikin lokaci qanqani yazama abin tsoro wanda ganinsa saidai imani kawai....
Wasu manyan qurajene masu zubda ruwa fitomasa gashi sai susa yakeyi suna fashewa abin babu kyan gani sam......
Ihu kawai yakeyi tare da neman agaji yana kiran sunayen mutane yana suyafemai amma babu wanda yaji tausayinsa acikinsu balle ataimakamai .........
Ganin Halin da yashiga ci kin qanqanin lokaci yasa imani da tsoro suka dirarma H. Nafi lokaci guda tarud’e tafara surutai kamar wata mara hankali.....

”Alk’ali katemakeni ka yankemin hukunci tinkafin ubangiji yafaran nasa, kana gani yadda ubangiji yafara hukunta mijina, nidai katemakeni ayankemin hukuncina”
Haka taita surutai harta bawa wasu dake cikin kotun tausayi, saboda yanayin lokaci ma haka aka buqaci data fad’i inda za’aje asamo su SARAUNIYA domin suma sukar6i hukunci nanta zayyane inda za’aje asamesu ayanzu.....
Ba tare da 6ata lokaci ba haka akatafi domin tawo dasu , basusha wani wahala ba wajan kawosu aikam nan aka tattarasu akaima kowa hukunci dai-dai da abinda yayi....
Abba kuwa anso jin wani abu abakinsa amma badama saboda ayadda yake bazai iya fad’in wani abu ba dan haka dole aka rabudashi tinyana abu ahankali abu yafi qarfin kansa danshi kad’ai yasan iya wahalar dayakeji ajikinsa ahaka aka fita da Abba hannu sake danba wanda ya iya ta6ashi saboda yadda lokaci guda yazama abin sai imani dukda abinda Abba ya aikata yanada muni hakan bai hana wasu tausayamasa ba dan sanda aka ratayeshi wasu basu iya kallonsa ba rintse idanuwansu sukai........
Haka aka dinga binsu daki-daki ana yimusu hukunci.....
Sanda H. Nafi taga yadda suke mutuwa gaba d’aya danasanine ya rufeta haka tana kuka tana kiran Allah ahaka akamata nata hukuncin....
Babu mace mara imani da rashin tsoro irin Mama Luba dan ita haryanzu batai saranda ba kamar yadda kowa yayi ita haryanzu bawani abune ke damunta ba kamar yadda asirinta yatonu batare da Haneef yagirma yaci gado ba gashi zata barshi batasan inda zata nemo mahaifinsaba, tana cikin wannan tinaninne aka buqaci afito da ita aimata hukunci dai-dai da abinda ta shuka, aikuwa haka aka jefeta kamar yadda addini ya tanadar mana......
Ahaka cikin jimami da samun cikakken imani kowa ya watse akafito daga kotu, dan duk taurin zuciyarka saikaji kadad’a imani idan kaga yadda akai hukuncin batare da son zuciya ko duba kud’insu ba.
Wannan kenan......

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡


Hajjo tayi-tayi da Hafsa tasamu ko ruwan shayi tasha sannan tasha magungunanta amma taqi ita tadage harsai sanda Hauwa Kulu tatashi sannan zatasaka wani abu abakinta, tin Hajjo na lalla6a Hafsa harsaida tafara rufeta da fad’a amma kamar anshuka dusa dan sam tadage bazataci komaiba.

Ba wata bace Hajjo illah kakar Hauwakulu da Hafsa itace ta haifi Ameena kuma itakad’aice taragemusu yanzun saboda yawancinsu basufiye tsayin raiba takan ziyarcesu sa, i da lokaci yanzunma Hauwakulu ce taje har gidanta tad’akkota domin tazo taga shari’a saikuma wannan abu ya afku... Wannan kenan....

Hafsa ce ta had’a kai da gwiwa tana ta kuka kamar hawayenta zai qare bakajin sautin komai acikin d’akin sai sheshsheqar kukanta, Hajjo tayi tayi taishiru amma taqi sanin dalilin kukannata yasa Hajjo ta qyaleta tacigaba da rarrashinta.

”Haba d’an Husanenena kidena zubda hawayennan haka, kiyi alwala kiyiwa mahaifanki da ’yar uwarki dake kwance addua Allah yatashi kafad’unta, ida kina kuka senaga kamar kinnunan ban isa dakeba kenan, idan mutuwar Ameena ce ta dawomiki nafikijinta saboda ni ’yatace ta cikina itakd’ai na haifa mace sonda nakemata bazai faduba amma yazanyi saidai namata addu’a dan haka kema ita take buqata daga gareki”

Hajjo tafad’a tare dasa bakin hijabinta tagoge hawayen daya zubomata......

Sallama akayi tare da shigowa,Hajjoce ta amsa musu sanadin Hafsa ta tada sallah.......

Aunty Safiyya ce riqe da hannun Haneef sewasu daga cikin baqin saikuma Aysha wadda taketa sunkuyar dakai qasa dan ita yanzu gaba d’aya kunyar Hafsama takeji ballekuma Hauwa...



’YAR GATAN MAMA✍️.
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*


Dubun gaisuwa tare da jinjina gareku makarantan A WANI GIDA Inajin dadin comment dinku over😍Son so fisabilillah😍💞💞.

My Swrt Baby Balqis wannan shafi nakine kiyi yadda kikeso dashi keda Ummu kulsum much qaunah yarana😍💞💞.


🅿️2️⃣1️⃣.


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Tinda suka shigo take qasa da kai ita bata yadda ba kunyar Hafsa takeji,Hajjoce ta kalleta tare da ta6ota tana fad’in.....

”Nikam d’iyata kizauna sosai mana idanba haka ba qafarki tayi ciwo.....

Hafsa ce ta kar6e zancen da fad’in.....”Haba Hajjo angayamiki Aysha ru6e66iya qaface da ita irin taki?
Cike dajin dad’in Hafsa tasaki ranta tana hira Hajjo taci gaba....
”Oh Ni ’yasu yau nazo inda za,aci mutuncina anakushemin qafa wadda akemin dan itama ko kallona batayi ba balle tashiga taramamini......Hajjo tafada tare da riqe baki.
Ahaka sukaita kwasar juna suna fira kafin zuciyar Hafsa tabujuromata da halinda takeciki nan da nan takoma yadda take tare da komawa bakin gadon Kulu tasata agaba kamar wata ta mutu.....

”Ayyah...Hafsa kidena tinani dazubda hawaye haka kiyimata addua Allah zaitashi kafad’unta.....
Aunty Safiyyace tadafa kafadar Hafsa tana mata magana amma sam babu alamun zata kaluta balle tad’auki zancenta ganin tayi tayi amma shiru hakan yasa tanemi guri tazauna tana tinani rayuwarsu baki dayans.
Ganin dare yayine yasa Hajjo tace duk su tashi sutafi gida idan yaso da safe sesudawo,fafur sukaqi harseda Hajjo ta6ata rai sannan suka rankaya suka tafi Hafsa kuwa daman batace tatafiba dan sanda take zolayarta tana idan yan uwanki sukazo saikibisu kuitayiwa takwarata Addu’a bud’ar bakin Hafsa secewa tayi aitafita kusanci da ita dan haka seta tafi tabarsu inyaso goben kyadawo jin haka yasa yanzu batayimata maganaba haka sukahadu suka tafi gida da nufin gobe sadawo.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Tinda suka koma gidan kowa yayi jugum-jugum kowa tinani ya cika zuciyarsa duk sunkasa nutsuwa daga masu tinani semasu tattauna abinda yafaru ahaka suka wanzu har lokacin barci,cikinsu Aunty Safiyya tashiga suka kwanta inda duktabi ta takurawa kanta wajan kula da Haneef kamar wani abu zai tafi dashi......

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Cikin firgici da razani Aunty Safiyya tafarka sakamakon iface-ifacen da sukacikamata kunnuwa tinaninta ita kad’aice taji juyawar da tayi tagansu suma sunyi cirko cirko duksun toshe kunnensu da alama sunajin abinda takeji itama hankalintane yatashi sanda tatuna yanzu Haneef yana wajanta cikin hanzari tajuya inda yake kwance domin taga lafiyarsa ga mamakinta saitaganshi kwance yana baccinsa hankali kwance yunqurawa tayi domin tagyaramasa kwanciya,cikeda mutuwar jiki tamatsa kusa dashi zatakai hannunta jikinsa kenan kunnuwanta suka amshi qarar rugujewar gini kamar wanda mota take rusau,cikin matsanancin tashin hankali ta tashi tana leqen tagar d’akin ”Ashe gaskene”kalmar data fito kenan daga bakinta sanda idonta yakai 6angaren Abba ginin wajan se rugujewa yakeyi dakansa batare da anta6ashiba tana tsaka da kallon yadda yake ginin yake fad’owa ne kawai sejin ihu da kururuwar Haneef tayi ainda yake kwance cikin matsanancin sauri tadawo dabaya cikin d’akin isarta keda wuya ta tadurqusa agabansa tare dasaka hannunta akansa yunqurinta ta tasheshi taji ko lafiya batare da zato ko tsammaniba taji tana ta6a abu me ruwa-ruwa wanda ta tabbatar da jini ne hankalintane yakuma tashi taci gaba da shafashi tana zubda qwallah wata razananniyar qara tasaki sanda taga Haneef yajuye gangar jikinsa tamiqe bata ankaraba sai ganinsa tayi yayi wata iriyar girgiza wadda atake yajuye daga kalarsa ta Haneef yakoma zuwa........


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Yau kwana uku kenan Hauwakulu na fama da ciwo amma harzuwa safiyar yau ba’asami kanta ba Hafsa tayi kukan hartagaji duk jikinta yayi sanyi gani kawai take Hauwa ma mutuwa zatai tabarta ita kadai.........

Haka Hajjo taita tausarta dukda itama ciwon na Hauwa yafara bata tsoro matuqa batai tinanin abinnakulu zaikai haryauba amma gashi abu kamar wasa yazama babba.......

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Cikin saa tasamu le6enta yafara ambaton sunayen Allah mai kowa mai komai tare dayin duk wata addua datazo bakinta tana tofamasa aikam bata d’auki lokaci tana yiba kamar shirin film taga yakama da wuta yanaci ba qaqqautawa hankalinta ne yatashi tafara ja da baya da baya inda shikuma yake yowa kanta gadan-gadan cike xa tsoro da qarewar qarfi ta qwallah wata razananniyarqara wada seta tafirgita su Aysha wanda suke bacci da dad’i babu dad’i........
🏡 A WANI GIDA🏡


LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(’YAR GATAN MAMA).


_________________________


*_______________________

______________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

_________________________
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
🅿️2️⃣2️⃣
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡


K’arar data k’wallara itace tai sanadiyar tashinsu Aysha dake bacci da dad’i ba dad’i atsorace dukansu sun tsorata k’warai da gaske saboda k’aramar k’ara Aunty Safiyyan tayiba, ga mamakinsu sesukaganta akwance da alamu mafarkin tsoro tayi dan gashinan se murk’ususu takeyi tana yamutsa fusk kamar wadda aka ajjewa damammen tuwo, Ayshace tafara ta6ata tanason ta tayadda ita daga baccin da takeyi, aikuwa firgigit tamik’e kamar wadda cinnaka yaciza, bud’ar bakinta maimakon tayi addu’ar tashi a bacci seta kama kiran ”Haneef! Haneef! ”haka taita kiransa ba k’ak’k’autawa kamar wanda tai mafarkin ya mutu, basui k’asa agwiwa ba suka nuna mata shi nan kusa da ita yana sharar baccinsa hankali kwance.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin tamik’e zaune tare da dafe kanta da duka hannuwanta tashiga duniyar tinani wanda tasan bazai yayemata damuwaba saidai ma yak’ara mata akan wadda takeda ita.
”Nikam meyake shirin faruwa dani ne, Yau d’aya amma gaba d’aya kaina ya kwance, wannan wace irin masiface haka, kai... kodai Haneef dinnan Aljani bamu sani ba?......

Haka taita maganganunta wand atinaninta azuciya takeyinsu sam batasan sun bayyana anjiba.......
Aysha ce ta dafa kafad’arta tare da fad’in.....
”Haba Safiyya kefa musulma ce kuma acikin musulmanma kina daga cikin wad’anda Allah ya azurtasu da samun ilimin Addini da na Zamani, Sannan yasanyaki acikin masusan masoyinsa Annabinmu Sallallahu alaihi wasallama, dan haka inaso kinutsu kiyi nazari akan baiwar da Allah yayimiki sannan kiyi k’ok’arin aikata alkairi kiyi imani kome yasameki daga gareshi ne , dan haka karki bawa zuciyarki damar yin tinani wanda bashi da kyau koda yaushe kizama me mallakar zuciyarki hakan seza kisamu sauqin rayuwa.

Haka dai Aysha taita tausarta har aka fara kiraye-kirayen sallar asuba wanda hakan yai sanadin tashinsu su gabatar da ita akan lokaci.

Koda suka idar da sallar sunyi addu’o’i sosai ciki
harda adduar nemawa Hauwakulu sauk’in
ubangiji.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Yau sauk’i yasamu amma abin tashin hankalin sam Hauwa bata cikin hankalinta tinda tabud’i ido taketa make-make da fuzge-fuzge dukta cire k’arin ruwan da akemata, iya k’arfi likitoci sun bayar wajan ganin anrik’eta ta daidaita amma abin yaci tura ba abinda takeyi sai gurnani da bige-bige abin duk yabi yad’agawa Hajjo hankali ba abinda take se ambaton ubangiji.....

Hafsa ce ta d’aga hannu sama tana kuka kamar ranta zai fita tana fad’in.....
”Allah kagani, kaine shaida, Allah ka kawomana d’auki Allah kabamu ikon cinye wannan jarrabawar, Allah kaduba zuciyar baiwarka kabata lafiya dan isar Annabin Rahama (SAW)”.
Haka Hafsa taita addu’a idonta nakan Hauwa wadda sam batasanma da ita ba, Ganin abin yaci turane likitocin suka had’u suka danneta aka tsikaramata allurar bacci mai k’arfin gaske, aikam nan bada dad’ewaba tabi jikin Hauwa sai bacci.......
”Hajjo dan Allah kiyima ’yar uwata addu’a kozata warke, Hajjo kiduba abinda Hauwa takeyi ni jikina yanabani mutuwa zatayi tabarni hajjo kice karta mutu tabarni ita kad’ai gareni hajjo....... ”.

Hafsa take fad’i tare da matsanancin kuka ta d’ora kanta ak’afar Hajjo wadda duk jikinta yayi sanyi, hannunta tasaka tad’ago Hafsa tare da kallonta tafara magana kamar haka.

”Haba Hafsa karkice haka mana, ai cuta ba mutuwa bace, kuka da surutai barkatai banaki bane ba dan haka kitashi kiyi alwala kiyi nafila kita adduar nemawa ’yar uwarki sauk’i, abinda yafima kinemata za6in ubangiji dan shine dai dai”.

Suna cikin hakane saiga sallamar su Aunty Safiyya sunshigo, Hannef ne yafara shigowa sannan su abayansa, wani ikon Allah shigowarsu Hauwa tasaki wata razananniyar k’ara wadda duk seda suka toshe kunnuwansu da tafukan hannayensu saboda yadda abin yazomusu abazata, bata fasa yiba gashi alamu sunnuna afuskarta da duka yanayinta dukta wahala amma hakan besa ta dena ba sema k’ara k’aimi da takeyi tare da girgiza gadon d take kaitamkar zata 6allashi, cikin hanzari aka kira likitocin suka fara nasu aikin inda suna yunk’urin yimata allura Hajjo tahana tace wannan ciwon bana allura bane abasu sallama....

Haka kuwa akayi dansu kansu likitocin sun duskanci hakan dan haka bamusu suka basu sallama......
Haka aka d’auki Hauwa agadon marasa lafiya harcikin mota daganan kuma basui ko’ina ba sai gida......

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Isarsu gida keda wuya sai abu yak’aru yaci uban nabaya, nan hankalin kowa yatashi itakwa Hajjo sai tofi takeyi tana d’uramata tare da shafa mata wani ajikinta, shafamata keda wuya duk inda ruwan yashafa se aga wajan yayi jajir kamar nama ba fata awajan.......

Aikam ganin haka ba k’aramin dagulamusu lissafi yayiba, cike da k’arfin zuciya Hajjo tasake d’aga ruwan tofin tasake watsamata aikuwa nan tafara wasu kalolin tuburar wanda suka haifi nabaya yitake kamar bazata denaba.....

Tinda aka fara abinnan Haneef yana gefe yana kallon ikon Allah, can batare da kowa yakulaba ya taso yayo kanta azabure kamar me shirin rufeta da duka, isowarsa kanta kenan yad’aga hannunsa ya d’agata sama tare da sakinta yana huci kamar wani mayunwacin zaki wanda yadad’e baiciba.....

Ga mamakinsu se gani sukayi Hauwa Kulu tamik’e sun fara kokawa da Haneef kowa na harin kowa kamar zasu kashe junansu, haka suka sallama musu dan duk wanda yashiga tsakaninsu seyaji ijinsa dan d’agashi suke su rankayashi da k’asa kamar masu neman ran mutane.........

Cike da tashin hankali Aunty Safiyya tasaka kuka tana fad’in......

”Wallahi shine, shine wallahi jiya nayi mafarki zai kasheni, ashe Hauwa yakeson kashewa kukasheshi ku kasheshi”.
Haka taita maimaitawa cike da tsantsar tashin hankali, sukuwa su Kulu basu fasaba Inda k’arfin Kulu yaik’asa Haneef yaita kilarta har seda yai nasarar kaita k’asa sannan yasarara mata.....
Sam basuga lokacin data tafi rubda ciki zata fad’iba kawai sai fad’uwarta suka gani hif ak’asa, Kanta sukayi cikin matsanancin tashin hankali mara misaltuwa gaba d’ayansu suka rufa kanta domin sud’agata......

Hafsa ce ta k’walla k’ara sakamakon ganin jini agoshin Hauwa gashi wajan yafashe sosai jini sezuba yake, suna d’agata sukaga ashe tini tadad’eda suma awajan, batare da 6ata lokaci ba suka kwasheta sai asibiti, sashen gaggawa akayi da ita nandanan aka shiga bata agajin gaggawa ansamu tafarfad’o sannan akai gyaran goshin suka dawo gida........

Tinda suka dawo Hajjo bata yadda Hauwa da Haneef sun had’u ba dan taga alamun gaba d’aya yanayin rashin lafiyarsu batazo d’ayaba bameson yaga d’an uwansa acikinsu.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Yau kwanan Hauwa biyar kenan da dawowa gida kuma jiki Alhamdulillahi basu sake rigima da Haneef ba sai yau, ba wanda yakula da tashinta kawai saijinsu akayi acan bayan d’akinsu suna bugun junansu.

Yau abu yafi nabaya dan haka saida aka samo wani...........




’YAR GATAN MAMA✍️.
🏡 A WANI GIDA🏡

LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(’YAR GATAN MAMA)



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*




🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
🅿️2️⃣3️⃣.
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡



Yau abin yazarce nabaya dan haka seda aka fita akatawo da babban malami wanda yake limanci awani masallaci dake can gaba dasu,yana zuwa yabuqaci abashi ruwa yayi alwala,bayan anbashi ne yasamu sallaya yazauna yafuskanci gabas tare da d’aga hannuwansa sama yana kad’a kai,sedaga baya sannan yace gatanan anyimata addu’a yanzu tasamu bacci.

Hafsa ce data kasa zaune ta kasa tsaye taimaza tabi bayansa tana tambayarsa.

”Malam baka fad’i me yake damunta ba,Allah sa dai ba matsafane suka shanye mata jini ba.....
Ta fad’a hawayen na zirara akan

2 Comments On A WANI GIDA
avatar
fatima-9-7-8

1 year ago

Reply

Masha allah

avatar
fatima-9-7-8

1 year ago

Reply

Yayi dadi allah yakara basira

Please Login or Register in order to submit comment